bayanin
yarda akayi haka ta faru, amma har yau kinki kwantar da hankalinki
balle in ji dadin gaya maki komai."
"Bana son ji, ni dai abinda nike so kawai kace ka fasa aurena
ka sakeni yanzu, ni nafi jin dadi a zuciyata. .""ni kuwa tawa
zuciyar ta buga?, ki cire wannan tunanin kwata kwata a zuciyarki,
saboida kinsan abinda ba zai taba yiyuwa bane kika fada.
"ni kuma abinda nike so kenan", "Allah baki hakuri don Allah
ki daina wannan maganar haka nan ta isa," "ni kuma ita nike son
ayi," "dama ba nace a dainata kwata-kwata ba, a'a kiyi hakuri gobe
sai in gaya maki duk yarda akayi, in kuma baki iya daurewa ki
tambayi Halimatu yanzun dai kiyi hakuri ki taso mu shiga ciki kada
a nememu.
"Ko dai kada ta nemeka," :ita wa kenan?" "ita wacce kace ta
sameka a inda kake son ku hadu," "Hamida ban gane ba," "ka gane
in tabi katin ta karanta ta sameka inda kace ku haďu," "ohoo!!
Yanzu na fahimta, ya mike tsaye, ina zuwa jirani don Allah".
ya tafi har da dan saurinsa, sai gashi ya dawo da Abdulrashid
so gabana, yasa hannu a aljihu ya dauko katin da ta bashi yacewa
Abdulrashid ya kai mata ya karbo masa nashi da ya bata, nan take
yace okey sir, ya juya ya tafi.
Minti kamar biyar a tsakani sai gashi ya dawo ya mika masa,
ya iso ya zauna kusa dani, "gashi an karbo, kiyi hakuri daga yau ba
zan kara yin haka ba, tunda baki so," "me ye na ban hakuri, in kana
sonta kasa a warware áuran dani a mayar da ita.
"Wai ni ya su, yau da naga samu naga rashin Hamida ni dan
alkaki," na tuntsire da dariya, ganin yarda ya fada da miryar mata
kamar irin yan daudun nan har da dukan cinya da tafa hannu, cikin
dariya nace Mustapha wa ya koya maka maganar mata haka?." Yayi
murmushin da ya daga kai sama, alamar ya ji dadin dariyar daya
sani.
"Ba wanda ya koya mani, nayi ne kawai saboda in ganki cikin
farin ciki, Hamida, kalli sama ki gani," na daga kaina sama, "me
36
kaika gani?" "taurari,""amma sunyi maki ky ko?" "na tsaya na
kura masu ido.
Saman yayi bulu-bulu wanda turawa ke cewa "sky blue"
taurari sunyi haske sosai, "sunyi kyau sosai," "Allah ya haliccesu
suma kamar yarda ya haliccemu, ya haliccesu, suma dan su bauta
masa kamar yarda ya halicce mu domin mu bauta masa, kinga ko
maganar nan da mukayi bautar Allah ce mu keyi, to balle ke da
zakiyi biyayyar aure a gareni, kinga lada biyu kenan."
"Ban gane ba," ko maganar da kike yi mani yanzu cikin
natsuwa, zuciyata nayi mani dadi, shima bautar Allah ce, "tashi mu
tafi gida, kaga dare yayi," "ba kya son magana tane?," ni kuwa
bakiji yarda nakejin dadi a zuciyata ba, wai ni ne yau Mustapha
zaune kusa da mtata tanayi mani magana a hankali mai kwantar
mani da zuciya."
Sai naji ya lalubo hannuna dake saman cinyata yasa a gefen
kumatunsa, saboda dukkanmu kawunan mu na kallan sama, "bai
dace ba fa Yallabai," "in kika kirani da Mustapha, zuciyata tafiyi
mani dadi," "amma kasan bana sonka, ba zan iya auranka ba", "aure
fa ya kare mani Hamida, sai dai inyi kokari yanzu ki soni kawai,"
"to ka sakar mani hannu," "bautar Allah fa kike yi.
Fiskarsa kawai naji a wuyana, ya kwantar tare da sumbatarsa,
nayi dan hanzarin mikewa tsaye, "yana mikewa, sai kawai naji ya
rungumeni jikinsa, "mijnki ne ni fa ko kin manta?" naji ya fada a
gefen wuyana, nayi kokarin kwace jikina naja baya, "ka zo kasa
mayar damu gida," na fada cikin rawar mirya tare da sa hannu in
shafa fiskata kamar mai share hawaye.
Hannuwa na yayi saurin matsowa ya kama, anan take nasa yar
kara, saboda zafin fama mani ciwo da yayi, "me ye?" "hannuna"
"sorry, wallahi na manta da shi, sannu," "kai ma naci da rashin
zuciya yasa kake like danij nace bana sonka, ka sakeni, bazan
aureka", "duk naji, na gode, ni na janyowa kaina dana fama maki,
sannu, zo muje mu kara gaisawa da jama'a, zuwa sha daya da rabi
sai a tashi hakannan."
"Sha daya da rabi yayi yawa," "to sha daya sai a tashi sabosa
kinga yanzu goma har da mitina," yanda yake maganar, sai naji
banji dadin yarda nayi masa ba, kamar in ce yayi hakuri sai kuma
37
a
wata zuciyar tace "ke da ke neman saki," sai kawai nayi gaba zuwa komawa cikin dakin taron fatin.
*** *** ***
Duk bayan kowa ya watse an gama walimata a gidan
Mustapha, an kawoni wajan karfe bakwai da rabi na dare, wanda
dama tuni yan uwana na gidan nashi domin walimat 'budar kai" da
akayi mani, sai ya zamana, wajan tara na dare gida ya koma ba
kowa sai ni kadai.
Ango Mustapha kuwa tun takwas da yan mintina ya zo da
abokanan shi, ya gabatar dasu, a gabana, da sauran yan surutansu na
abukan anguna, da yan nasihohinsu, wanda ni bata mani rai kawai
sukeyi, tunda har yau ba abinda nike so Mustapha yayi mani, sai ya
sakeni in huta.
Ni kaina duk wata hanyar da zanbi in ga an raba auranmu nabi
ta, amma kowa sai dai yace inyi hakuri, har daddy na samu ina
kuka, amma sai ma na sihohi yayi mani yace in hakura.
Bayan sun fita ne har dashi dan rakiya, ba abinda ni kuna nayi
kokarin yi sai rufe kofar cikin dakina na sam.u gefen gado na zauna
na rabka tagumi na, ba abinda nike tunani sai ya akayi reshe ya juye
da mujiya haka, yau gani gidan Mustapha ba Halimatu ba,
Kwakwasa kofar da akayi ita tasa na katsi tunanina tare da faduwar gaba, "Hamida don Allah ki bude mani, ba wani abu zanyi
maki ba, iyakata da ke magana, ina so ne in gaya maki abinda ya
faru a tsanina da kawarki har ya zamo an juya na aureki.
Please, kada kiyi tunanin dan ni, ki bude dan Allah, sannan kiji
tsoraonsa bani ba, kiyi tunanin shi ke bayar da aljannan ga wanda
yaso, ya kuma aikata aikin kwarai, sannan kiyi tunanin shi fa ke bayar da wuta ga wanda ya kaucewa umurninsa.
Kiyi tunanin nifa na zama miji a gare ki, saboda haka duk abinda na lissafa baya biyayya gareki zata iya janyo maki dadi haka, kin biyayya a gareni zai iya janyo maki kishiyar haka, amma in kin zabi abinda kikaga yafi alheri gareki, to ni dan addua ne, in nan take na tuno irin nasihohin da akayi a babban masallacin Abuja wanda akayi a (international mosque abuja.)
38
Ba tare da na barshi ya karasa ba, na zo na bude kofa daga
kullewar da nayi mata, yana tsayc, ban tsaya kallansa ba, na juya na
koma jin shiru bai shigo ba yasa na juya na kalli kofa, sai naga ya
jingina jikin bangon cikin dakina.
Magana a hankali ya farayi mani, "wallahi Hamıda banyi
niyyar canja manufa ta ba, saboda inji dadin rayuwata ba, a'a Allah
ne ya kaddari kece matata, Hamida ina son duk wani abinda kike
so, ko da kuwa zuciyata bata sonshi, in har nasan in nayi makishi
zaki ji dadi, to zan so koma meye shi.
Sam ni bani naje nasa a canja aurena da na kawarki ba, ki je ki
tambayeta ya akayi, ina son in ga ni na gaya maki yarda akayi,
amma ganin har yanzu gani kike kamar ni mayaudari ne, shi yasa
nike ganin ko na fada maki ba zaki amince da ni ba, saboda ba so
ko daya a zuciyarki nawa."
a
Kawarki tace kince in har akayi maki auran da ni, sai kinyi
sanadiyyar rayuwata, saboda tace kince bakya kaunata ko kadan
zuciyarki, amma ina mai tabbatar maki, gurina ya gama cika, tunda
duniya gaba daya tasan nayi aure, kuma zuciyata tasan wacce ta ke
so ce ta sa'nu, saboda haka, ina mai godiya ga Allah in har akace
wacce nike so, ita ce sanadiyyar mutuwata, sannan kuma tayi mani
takaba, ko da kuwa ta kwana bakwai ce.
Amma don allah ina son in roki wata alfarma a gareki, ta ki
dan bani lokaci kafin ki kasheni ko da na kwana uku ne, saboda ki
gani, ki tabbatar, cewa ina sonki so na gaskiya, son da nasan ke ba
zaki taba yi mani irinsa ba, kawarki tace kince inkin ganni ranki
baci yake, saboda kuna da zuciyarki keyi.
"Wai ni yaushe na fadi waDannan maganganun? Sharrin da
Halimatu zatayi mani kenan, yanzu ba sai an kwana ba sai naje na
sameta ta gaya mani ranar dana fada mata wadannan maganganu."
Na nufi hanyar fita daga dakin "Hamida" na waigo na kalleshi,
"kina nufin baki fadi cewa bakya sona ba? Kina nufin baki fadi
wadannan maganganun ba,?" "wallahi ni ban fada ba," "in har da
gaske baki fada ba zo wajena yanzu," ya miko mani hannuwanshi
duk biyun daga in da yake jingine da bango.
Nayi tsaye ko motsi na kasa yi, "kin fada kenan cewa bakya
sona, zaki kasheni ki huta ko?" "ni ban fada ba, "me zai hana ki zo
39
gareni yanzu, alhalin kinsan ni mijinkine mai kaunarki," yayi shiru
tare da mayar da kansa ya kwantar a jikin bangon.
A hankali na dinga tafiya har na zo dai-dai kusa da shi amma
sai ya zamanto na kasa karasa isa jikinsa, na kura masa ido ina
kallan fiskarshi wacce idanuwansa ke lumshe yana mayar da
numfashi a hankali, nan take naji sonshi ya dawo mani sabo.
Kyawun fiskarshi ya bai yana sosai, nan take sai naji gashin
dake kwace a fatata duk ya tashi, na tambayi kaina shin ina son
Mustapha ko kuwa bana sonsa?, nan take sai naji jikina ya bani
amsa da cewa, son Mustapha ne a cikinsa.
Maimakon in isa in shafa kyakkyawar fiskar mijina, sai naji na
tsuguna kasan Kafafunsa, jin yayi shiru yasa na dago kaina na
kalleshi, amma yarda yake dazu, har yanzu ma haka, na sa hnnuna
na shafa yan yatsun kafarshi, sai a lokacin naga ya sunkuyo a kaina.
"Baki fada ba?" na daga kaina, yasa hannuwansa, ya dagoni
na mike tsaye hannayensa yasa ya tallabi kumatuna, " you love me,
now" maimakon in- amsa masa, sai kawai naji hawaye masu sanyi
sun zuba a kaumatuna, tare da ajiyar zuciya na mayar da fiskata na
kwantar a jikin hannunsa.
"Zaki zauna dani yanzu?" "Halimatu zata ce na ci
ama ", "don't to say that" itama tana gidan mijinta yanzu,"
yasa dan yatsa yana wasa da hawayen da ke zuba a fiskata, nasa
hannuna na dauke hannunsa, a hankali naji ya hadani da jikinsa, ya
rungume, wanda ya kwantar da kaina a jikinsa.
Karfe shidda da rabi na safiyar litinin na farka, naji ni mane a
jikin Mustapha, na samu na daga hannunshi da yake saman bayana,
na mike a hankali, naja wani zane dake kusa dani na daura na nufi
ban daki, amma ina zuwa sai naji na kasa yin komai, wanda hakan
yasa na samu gefe daya a cikin ban dakin na zauna dirshan kasa.
Bayan kusan mintuna sha tara, sai naji Mustapha na kiran
sunana a hankali, maimakon in amsa sai ma na tura kaina a cinyata
saboda tunanin da wane idon zan kalli Mustapha ni Hamida, ina
haka ya iso ya tsuguna agabana sai naji ya danyi yar dariya "uwar
gida Hamida," nayi shiru na kyaleshi, ya dago kaina, sai na
harareshi. 40
"Kai yau ya cancanci in biya kudin wannan kallon, sai ya
chukumoni, ya dura a jikinsa, inda ya zame ya zana kasa shima a
bandakin, ya dago kaina, wai tsotsar bakina zaiyi, na dinga gocewa,
har na zame na kwanta kasa, ya dinga dariya shima ya kwanto, ya
rungumo bayana.
"Wanka ko kin yafe?" na daga kaina alamaar E, "kudin kallaki
ko shima kin yafe?" na daga kaina, to ni ban yafe ba sai na biyaki
da kudin da ba'a rikonsu a hannu," "wadanne kudine su kuma?"na
fada kai a kudundune da hannayena," "kallansu ki gani "me zan
kalla?" "kudin" na samu da kyar na juyo, wai sai naga ya turo mani
halshensa, da yawu a jiki, "ina kudin?"
"Gasu" ma'ana dai yawun da halshe yake nufi, na dan sa
hannuna na daki bakinsa, ya kara wargajewa kwance a kasa yana
dariya.
Ko abinci bamu tsaya munci ba don gajiya, bamu farka ba, sai
karfe daya na rana, na samu na kwakwale Mustapha daga kirjina na
mike, wai ni abinci zanje in dora, wanda nike tambayar kaina me
zanyi, inna shiga kicin daina ma'ana, abincin safe ko na rana.
Na bude: firij din sashena naga ba komai ciki na ci sai kayan
sha da na makulashe, ina haka mustapha ya biyo bayana," madam"
haw are you to day? Nayi murmushi kunya ya lakaci hancina,"
"yunwa nike ji," "yanzu zan dora kicin zan shiga yanzu, ba kaine
ba," "ni ne nayi me?", "kace ayi barci," "ba gashi kin huta ba."
Wai yarda nike magana, shima haka ya keyi, ya ja hancina,
kadan, "zo muje sashena in gani ko na fiki abinci," muna shiga
bAbban falashi, naji kanshi na tashi, nan take yawona ya tsinke, har
sai da muka isa falonshi na dakinshi sai naga tebirinshi jere da
kayan abinci.
"Kai," nace, ke", shima yace," "wa yayi haka?" "kukuna" da
agida kake cin abinci?" "da a ina zan dinga ci?" "ba kunada hotel
ba?" "a'a ni in.kinga naci abincin hotel to wata kasar naje, amma in
dai a gida Nigeria ne, tare da mai dafa mani abincina nake yawo."
"Sannu" nace masa yayi dariya, "kinsa mu manya a ko ina
muna da abokan hamayya, shi yasa gudun kada a hada baki a zuba
maka wani abu ta lemu, ko abinbci, shi yasa bana cin abincin kowa,
41
sai na mamata kawai, sai kuwa in yarona ya dafa mani, yanzun kuwa sai na Hamida ta.
Muna hira yana cin abincinsa, a haka ya lura ni banaci shine fa naga ya taso ya zauna saman tabirin a gefena, sai da ya tilastani naci nima.
Gaba dayan yaransa, har da masu gadin duk get din biyu, da
gadin gidan, da ma su ba ruwan fulawa ne da sauransu, sai da ya
tarasu ya gabatar da su a wajena, da aikin kowa, su kuma ya kara
gabatar da ni a wajasu.
A karshe ya nuna mani Abdurashid yace mani shine bAbban
su gaba daya, kome nike so in bayanan, Abdulrashid zan tambaya,
shima haka ko me yake so, ya tambayeni, da na lissafa masu aikin
gidanshi sai naga sun kai kusan arba'in saboda talatin da bakwai, ga
arba'in kalilan ne babu,
Karfe biyar saura na yammar ranar, yace muje in ga wani abu,
ni kuwa na bishi a baya, har wani loko na gidan, wanda bansan
dashi ba, muna zuwa ya kaini ga wata mota, yar karamar mai kyan
gaske, an rubuta," is for my wife,"happy marriage".
"Ni Yallaßai?," ya daga mani kai alam,ar e,' haka da yayi
mani yasa nayi baya, bayan ya shigo falona ya samwni ya zauna
kusa da ni, "me nayi maki kuma Hamida", nayi maki wani laifi ne
na daga kai alamar e, meye gaya mani
"Ni fa ba dan kudinka na hakura zan zauna da kai ba, kuma kasan ba ban kudinka ba nike so. ."nayi shiru na kasa karasawa, "naji nagane ba dan kudina kike sona ba ko?," na daga kai, "to cigaba" "shine amma zaka! Zaka!! Yi mani haka."
"Oho! Na gane wallahi ba haka nike nufi ba, nayi ne kawai
saboda godiya ga Allah da nuna maki murnata da na sameki "fine Woman" ina fatan kin ganc?" nayi saurin kife kaina a cinayata
saboda kunyar da ta kamani, ya matso kusa dani," "kin fahimceni yanzu ko?" na mike na nufi cikin dakina
*** *** ***
Watana biyar kenan a gidan Mustapha, tun ina jin kunya da nauyin ya ma za'ayi in cigaba da zama da shi, sai gani har na sake
42
na saba.ni ma balle ganin yarda Halimatu ta sake a gidan nata mijin,
har wani nuna mani take, ita fa tayi auran soyayya, ba tasan ni ma
ina son nawa mijin ba, kawaici kawai nake mata lokacin, yanzun
kuwa mun niga mun goge a gidan Yallabai dina.
a
Kauna kuwa wajan mahaifiyarsa kamar ta hadiyeni, haka ma
da mukaje indiya yan uwanshi suka nuna mani kauna, balle
lokacin da bani da wata isasshiyar lafiya.
Samun cikina kuwa yasa Yallabai ya kasa fita ko wace kasa
saboda kula da lafiyata da debe mani kewar girman gidanshi ni
kadar, sai dai yakan fita ofis, ko wasu jahohin da yasan ba kwana
zai yi ba.
Amma duk wani aikin da yasan kwana za'ayi ko ya haure nan
Kasar, sai dai ya tura jabir, wanda ni kuma ko wash nace tamkar ya
saka ihu dan kulawar da yake mani, sai dai abu daya da ya dan
damar mani zuciya, shine tunda yaga ina da ciki shekenan ya daina
dokina da nuna hutawarsa gareni.
Wanda na tambayi halaimatu, tace ita nata mijin a koda yasuhe
bai ki ya huta ba, sai dai in ya lura bata jin dadi sosai, naga itama fa
tana da cikin ıan kamar ni, amma ko zuwa nayi gidan sai inga yaya
nata rawar jikin da ita kamar ya hadiyeta.
Ni kuwa in kaga Yallaßai na rawar jiki, to yaga bani da lafiya,
ko zanci in cin wani abu, to lokacin zai dinga rawar jiki yaga ya
kawo mani shi, nasan duk bayan awa daya ko lokacin da ya dan
samu dama a ofis, yakan buga mani waya yaji ya nike.
Haka kuma na tambayi Zulaihatu wacce itama yanzo take
laulayin nata ciki, tunda mun rigata samun ciki, amma tace ita wani
lokacima, sai mijnta yaga tana kuka, tukuna zai saurara mata, ko
yaganta akwance sosai, bata jin dadi.
Ni nasan yallabi na kulawa dani Dari bisa Dari, amma wannan
abun daya shine ke damuna saboda tunanin ko dai ya samu wasu a
waje ne shi yasa ya manta dani, wannan abun ne kawai ke damuna,
wanda na kasa yiwa Yallabai magana a kanshi.
Wai ko irin wani garin mukaje muka samu kwanaki, in mun
dawo, a tunanin, ya kamata ya nuna doki a akaina, amma sai in ga
shiru wanda farkon aurena da shi ba haka muke ba, nasan farkon na
kwanta jinyar laulayi amma yanzu cikina wata hudu kenan, na samu
43
na daina duk wata matsananciyar rashin lafiya, amma har yanzu ba
wani canji.
Bayan na gama gyara jikina da ruwan kunun kanwar shadda
na kallin kaina a madudi naga nayi kyaun gaske, anan take ne na
kama tananin kwaliyar ma da na zauna na bata lokaci na nayi ta,
nasan mijina ba yabbawa zai yi da ita ba, amma duk da haka ban
taba kinyi kwalliyata ba.
Na fito ina taku a hankali zuwa bayan gida inda muke hutawa
duk yamma ni da Yallabai na, ina dososhi, naga alamar kamar maba
a hankalinsa yake ba, saboda tunanin da naga ya nutsu a cikinshi.
Har na iso na tsaya bayanshi, amma bai san na zo ba, hakan
yasa na sa shantala shantalan yan yatsuna na rufe mashi
idanunwanshi ta baya, sai a lokcin naji yace, wai Allah, kin
tsoratani, my love," yasa hannuwansa ya janye hannayena, ya
zagayo dani ya kwanta a cinyarsa.
Kina son kiyi wasa da jikinki ko Hamida? Na dan langwabe
ki," to ya kake son inyi yallaßai, in daina tafiya? ko kuwa in daina
wanka gaba daya?, "ni ba haka nike nufi ba, ni dai ki daina yawan
wasa da jikinki, ni fa ko gani nayi kina tafiy. da karfi sai naji
hankalina ya tashi."
Ya danyi shiru, "Hamida tunda kika samu cikin nan naji
hankalina ya tashi mutuka," "saboda baka sin haihuwa ko kuwa
saboda me?," "ba haka nike nufi ba, Hamida waye zai haihu
duniya, sai wanda bai yarda da kaddara ba."
cikin nawa?"
a
"Kenan nice kaddara ko "a'a kada kiyi saurin
sawa zuciyarki wata fassara ta da ban," "to da nice kenan baka son
haihuwa?, ai da ka gaya mani haka da tuni na san.
"kada ki ce komai don Allah.
Ni ba haka nake nufi ba, Hamida tunanin yarda akace mani
haihuwa da wahala, shiya ke tayarmani da hankali," "waya gaya
maka haka?" "mahaifina yace mani wajan haihuwa mata na wahala
harma mutuwa akeyi wani lokaci.
To
a
yanzun ya ikake son ayi da cikin?" "ba komai, amma
koda yaushe na kallleki, sai inji hankali na ya tashi matuka," "ashe
shi yasa ka mayar da ni bola a gidanka?"
44
"Sam ba haka bane Homida," "to me ye?" "yanzun dai abar
wannan maganar, Allah ya baki hakuri shi kenan ko?" "shi kenan a
wajanka, amma ni a nawa wajan ya zama dole in yi tunanin matakin
da zan dauka a kan lamarin," haba Hamida don Allah ki bar
maganar nan ni a wajena ta wuce har a bada."
"Ni ma ta wuce a gareni." Har kusan sallah magariba muna
wajan shan iskan mu, gannim an fara kiran sallah magariba yasa
muka kwashe kayan mu, muka koma ciki.
Bayan sallah, isha ne mun gama cin abinci, na taka zuwa
shashina, daga shashin Mustapha, wanda nayi haka ne domin ni har
yanzu zuciyata na cikin ciwo da kunar maganganun da Mustapha ya
fada na game da cikin jikina
Ban tsaya yi komai ba, na mayar da kofar dakina na kulle, bai
fi minti sha biyar ba tsakani, sai naji yallabai na kwankwasa mani
kofa, ina jinshi tun yanayi a hankali, har yakai ga bugawa da dan
kafinsa, tare da ambatar sunana.
Ina jinsa ya kwana zirga zirga daga shasen shi, zuwa nawa, har
ya gaji ya koma ga waya, amma ni ma sai na dauke duk kan wayar
da ke shashena, na ajiye da ban
Kwana mu biyu a haka, wanda ni tuni na rayawa zuciyata ni da
Mustapha ya saka ni idanunsa sai na haihu, shima dan asan mai
yiyyuwa, saboda ba zan iya zama da mutumin da baya son, haihuwa
ba.
Ranar cikon na uku ne, kamar ance mani in mayar da kan
wayoyi na saboda tunanin kada a dinga bugowa daga gidan mu, ko
wani bangaren aji shiru, ban fi minti biyu da mayar da kan waya ba
sai naji wayar na kara, har na vi niyyar kada in dauka can kuwa
wata zuciyar tace in daure in dauka.
Ina kangawa a kunnena sai naji Halimatu nan muka sha hirar
mu ta wayar tarho, har ta tsayin mintuna talatin, wanda ina ajiyewa
naji wayar tarho din ta kara sakin sauti miryarshi kawai naji na gane
Yallabai din na ne, "Hamida ke ce akan waya "kana iya cigaba da
maganarka ina saurarenka" "dama ina son yin magana da ke don
Allah," "dama ni ban hana ka yin magana dani ba, na baka lokacine
kayi shawara a kaina." 45
"Ba wata shawara Hamida da zanyi ina son don Allah ki huce
haka nan, ni ma na gane nawa kuskuran please ayi hakuri gimbiya,
kwana biyu fa Hamida ban ganki ba banga beby na ba" "waye kuma
bebinka?" "Allah huci zuciya."
Daga tambaya sai ban hakuri," "ni dai a ce an huce a gani
yanzun in zo," "au dama ka damu da sha'anin mu?" "ba zan iya
baki wannan amsar ba sai in kin bani izini zuwa gareki, ke da kanki
zaki gane amsarki, in har kin tsaya mun hada ido da ke."
"yanzun yaushe zaka zo?" "in yanzun ki kace in zo sai dai in
ce ki jirani nan da minti goma," na kalle agogon da ke manne gefan
bangon arewa, karfe sha biyun rana saura minti goma sha uku,
"kana iya zuwa wajan karfe biyu na rana."
Ina jinsa yana fada, "a rage Hamida yayi mani nisa," amma
ma sai na ajiye kan wayar tarho na juya abina.
Cikin gudu-gudu sauri sauri, na samu na gama dura mashi yar
jalaf din taliya da farfesun kayan cikin rago, banda dan lemun dana
hada mashi a gefe, ma'ana lamun da nasan ya fi so a duk cikin
lemuna da nike hada masa.
Watau lemun kwakwa, ina sauke wa tare da wankana, gidana
kuwa a tsabtacensa ya ke saboda duk safiya da kwai mai yin
aikinshi na nusamman a cikin yaran Yallabai na.
Shaddace ruwan cincin bale turare nasa ajikina, na mayar da
kofar bAbban falo na rufe da madaninta, ma'anata, sai ya
kwankwasa tukuna a bude masa, karfe biyu dai dai naji an
kwankwasa kofa.
Da dan hanzarina naje na bude masa, Abdulrashid ne
hannayensa lode da kaya har naji zuciyata tayi ba dadi kadan
saboda rashin ganin Yallabai na.
Bayan hankalina ya dauke ga yiwa Abdulrashid magana, sai naji wani kamshin turare ya ratsa hancina, da sauri na juya zuwa ga kallan kofa, sai naga Yallabai na, tsaye yana dan murmushi. Abdulrashid na fita sai kuma yana matsowa dab da ni, ya kama hannuwana duk biyun tare da fadar (I miss you, you and my beby)" "na dan daki kirjinsa da kaina wanda hakan yasa ya kara hadani da jikinsa 46
sayan na tAbbatar ya ci abinci ya koshi ni kuma na tashi na
koma sha shina saboda har yanzun ina jin haushin maganganun da
ya gayamani kwana biyu da suka wuce.
Ina jin shogowarsa, a lokacin ni har na riga na kwanta, ina
jinsa ya kwanta bayana "Hamida har yanzun baki hakura ba?" "kai
ma ai kasan bakayi mani dai dai ba "baki fahimceni ba ne Hamida,
sam ni ba manufata bana son ki haifa mani yara ba, manufata shine
tausaya maki da tunanin ya za'ayi in dinga takura maki, alhalin kina
יי cikin hadare kamar wannan."
Yasa hannun ya rungumani jikinsa ta bayana, "amma dan
Allah kiyi hakuri, daga yau nayi maki alkawarin ba zan kuma yi
maki haka ba
Cikin sigar tausaya masa na miko hannuna ta baya na shafi
gashin kansa, "ni ma dan Allah ka yafe mani, 'tsayin lokacin dana
dauka ina cutar da kai, har tsayin kwana biyu, kayi mani afuwa don
Allah,"
"Na yafe maki Hamida nıma ai nasan rashin fahimtar juna ta
kawo mana haka, nayi imani da kin fahinceni haka ba zata taba
faruwa ba
tun karfe bakwai da rabi na safiyar ranar na tashi na shiga
kicin domin shiryawa Yallaßai dina kalacin safe, saboda nasan ya
dauki lokaci bai ci kalar abincin matar sa ba, tunda na kwanta
rashin lafiya da daniel ya shiga kicin, a ranar kuwa Yallabai ko
kofar gida bai fita saboda shagwaßa da sangarta da ya yini yi mani.
Misalin karfe shidda na yamma