irin bugawa nan ta in taga sabon masoyi da take
SO.
Kenan son Mustapha ne ya dawo mani sabo?, tambayar da
nayi wa zuciyata kenan, na duka a hankali na sumbaci kumatunsa.
Tare da kara janyo bargo na lullußa masa, şai kawai na dauko biro
da 'yar guntuwar takarda na rubuta masa yar takardar neman gafara,
ko da na mutu a can, haka na dauki jakata nayi gaba.
A bangaran Mustapha kuwa, yana farkawa ya kara mirginawa
domin ya rungumo Hamidarshi, sai yaji fili a gabanshi, ya bude
idanuwanshi a hankali, ganin gari ya waye sosai yasa ya mike da
saurinsa zuwa bandaki.
Duk a tunaninsa Hamida na kicin domin tanadar abinda za su
karya kumallo, har yayi wanka yayi sallah tare da istingifari akan
makara sallah da yayi, amma bai ji motsin Hamida ba.
Falansa ya wuce kaitsaye a tunaninsa tana kicin, sai gashi ya
leka ba kowa, nan fa hankalinsa ya dan tashi kadan, a hankali ya
dinga kiran sunanta, amma ya ji shiru, hakan yasa ya dinga bin
dakunan gidan da falofalo, amma bata nan.
Gaba dayan gidan ba in da bai duba ba, amma ba Hamidar sa,
da sauri, sauri, gudu-gudu ya dawo dakinta, sai a lokacin idansa ya
kai ga takardar da ke ajiye kan kujerar hutawa ta cikin dakinta, da
rawar hannu ya buda ya fara karantawa.
Yallabai zance ko Mustapha, ko kuwa mijin? Saboda
kwakwalwata duk taki amince mani da ta fadi wadannan sunayen,
cikin dadin rai, tun da ta kama mai sunayen da laifin ci mata amana
ido biyu ko ince baki da baki.
71
Amma duk da haka, zan daure in kiranka da sunan mijina na
"da", sannan in gaya maka har yau, bana ganin laifinka, tunda ni na
fada maka da sunan aure ba wani tsayawa kwakwaran binkice.
Ko da yake, wani bangaran kuma bani da laifi, in har na tuna
da iko na Allah tare da kaddara, saboda haka ina neman afuwarka,
tare da neman gafararka akan laifin da nayi maka na baya da wanda
zan aikata yanzun, na yanzun kuwa shine cire maka danka ko yarka
da za'a yi a jikina.
Na gaya maka ne saboda ko da garin cire abinda ke cikina zan
rasa raina, sannan ina mai baka shawara da ka bi asibitoci ka dauko
gawar danka, sannan ka canja halaiyar ka daga wacce kake yi yanzu
ta bin yaran yammata saboda gudun gaba, kada a rama ga naka
'ya'yan Hamida.
Wani jiri ne ya kwashi Mustapha, wanda har yakai ga kaishi
kasa ya kwanta tare da dafe kanshi. Tsawon minti biyar ya dauka a
haka tukuna ya samu ya rarrafa ya tashi ya janyo wayar gefan
gadonta, ya buga zuwa get, domin neman Abdulrashid Cikin
gaggawar da bata wuce ta minti uku ba sai ga Abdulrashida gaban
Ogansa, "Yallabai," "Abdul, Hamida ta mutu, ta mutu, what
"What!! Yaushe' yaushe, "Innalillahi wa Inna ilaihir raji'un",
"kamani, kamani, mu tafi nemanta, ka kaini duk wani asibiti da ke
garin nan".
Cikin kankanin lokaci har sun gama jeruwa a motocinsu,w
anda Mustapha ya bayar da umarnin a rabu biytu,w asu su tafi wasu
asibitocin, w asu kuma su nufi wasu.
Ni kuwa ahankali na motsa daga tashi barcin alurar likita, duk
da farka wata kenan, amma kwakwalwata ta gane mani ba saman
katifa jikina ya ke ba.
A firgice na nemi mikewa zaune, tare da fadar (Hazbinallahu
wani'imal wakil) a tsammanin tunanin kaina likitan ne yayi mani
hakan, amma a dan takin da bai wuce na sakan biyu ba, sai naji
muryar Mustapha a kaina.
A hankali na dago kaina in ga da gaske muryar Mustapha na ji
ko kuwa kunnena ne. TAbbas Mustapha ne rungume da ni, ban yi
magana ba, sai dai na dawo da kaina na kalli cikin gabana, in ga ko
an cire mani, gani nayi kamar dai cikina yana a jikina.
Hakan yasa na daga hannuna ahankali na laluba cikina, ba
zancan gardama ko kokwanto, saboda ina (fora hannuna dan cikina
na motsawa, me zan yi yanzu? Itace tambayar da na yiwa zuciyata,
na waiga na kara kallan Mustapha a daidai lokacin da yace mani
"Sannu, kin farka?"
Da hanzarina na chakumi wuyan Mustapha, shi kuwa sai ma
ya kama dariya, abinka ga karfin mace, sai naji na gaji dan kaina,
haushin hakan yasa na dinga dukan kirjinsa, shigowar likita ita ta
dan sa na tsaya, amma tsayawa akan Mustapha, na komawa likita
da masifar fada.
Mustapha 'yasa hannu ya rufe bakina, ina ji har suka gama
magana da likita, cewa zan iya tafiya gida, dacta na fita ya juyo ya
daure mani fiska, "wallahi in har kika ce ba zaki koma gida ba, zan
yiwa Daddy waya yanzun nan in sanar da shi".
Na sakar masa wata muguwar harará, na sauka daga gadon,
gani yayi daure fiska ba za ta yi masa ba, sai gashi ya koma magiya
da hadani da Allah cewa in muka je gida yayi mani bayani ban
gansu ba, to ya yarje mani in tafi gida.
Fadar haka yasa na yarda na bishi zuwa gidansa. A tawa
wautar, maimakon in tsaya jin bayaninsa, sai kawai na hau shirya
kayana a akwati, maganar da yake tayi mani a kai kuwa, bata zuwa
ko bayan kunnena ballantana ta shiga kwakwalwata. ana cikin haka
Hajiya Maama tayi sallama.
Baki daya muka jero gabanta, ni kuwa fiska dam da hawaye
"Me ke faruwa?" itace tambayar Maama tayi mana, kafin in fara
magana, tuni Mustapha ya rigani, "Maama wai ita gida take son ta
koma ta haihu, shine don nace a'a take ta kuka tana hada kayanta".
"Da abinda kake yi mata shi yasa take son komawa gidansu",
ta dafa kafadata, "kiyi hakuri kinji Hamida, mijinki na wahala in
baki nan, kinga lokacin baya ma da kika tafi gida gidana ya koma
da kwana.
Shima kullum mitar in je in dawo da ke gida shi ya gaji, da
kyar na dinga lallashinsa har ya hakura, amma kinganshi nan har
dawowarshi daga tafiya gidan yake kwana, amma nayi maki
alkawarin bayan suna zaki tafi gida wankan da kuke yi" "Maama to
ni kuwa ya....." Ta katseshi da tsawa, sannan ta cigaba da fada
72
amma da yaran halshen Indiyanci, wanda ba abinda nike ji sai
daidaya daga cikin wanda na dan koya wajan Mustapha.
Ni kuwa dama tuni kunya biyu ta hadar mani waje daya, ta
Mustapha, ga ta Maama da nake ji. Ta mike tsaye tare da maganar
ta ta karshe da halshan hausa, "Ka dai nemi alfarma a wajanta, in
tace zata zauna, in tace zata tafi gida to, ya rage ga naku, in kun
yanke hukunci sai ku sanar da ni, "Sai an jima kinji" nace to, ita
kuwa ta fice, Yallabai na kuwa ya bita a baya.
Da gudunsa ya shigo ya haye gado yana wantsil wuntsil dinsa,
a karshe ya tura kansa a filo, a hankali na je na zauna gefansa tare
da daga filon nace, Mustapha."
Kamar na tsira masa allura, ya yi wani figigit, ya cukumeni ya
kwantoni jikinsa," Yalla6ai Yalla6ai, wai me ye haka?," "so", son
wa?" ya tsaya ya kalleni, "so da murnar abu biyu da nikeso a
rayuwata," ya sa hannun ya shafa cikina, na lumshe idanuwana,
sannan nayi magana a hankali."
"Meye na farkon su?" Hamida," ya fada mani a kunena, da
bebina, kina jin motsin sa?, na daga kaina "nagodewa Allah ni
Mustapha, amma da wata magana ya dago kaina, "ba zaki gida
wanka ba," "abinda kace shi za'ayi yanzun ni mai neman gafarar
kace, akan abinda na aikata a bisa rashin sani," "baki da laifi
Hamida ni na janyo hakan, wai ni in rama, shi yasa naki fada maki
gaskiya tun farko, gashi yanzu da ina nan ina dana sani ta fi dubu,"
nayi dariya," magana ta biyu, don Allah daga yau kada ki kara
cewa in sakeki, raina baci yake yi kiyi mani alkawarin haka," "daga
yau, na daina in Allah ya yarda, da daukar maka alkawari akan
hakan, matsawar amma kai ma ba zaka aikata laifin yin hakan ba,"
"na isa in kara wani laifin, da za'a cire mani idanuwa," nayi saurin
tura kaina a filo," bana so Allah, ai dai nace kayi hakuri ko," "to na daina
Allah ne ya kiyayeni da yanzu an fara kirana da Mustapha mai
tabo a fiska," na dago kaina, "kaga ka daina ko inyi maka yajin
wata hudu," "wai! dana shiga uku, da nasan sai an zo ana daukata a
gidan talabijin saboda ramar da zanyi, ko ma ince na haukace, na tuntsire da dariya tare da kai bakina na rufe da nasa.
74
***
Tun wajan karfe shidda na yamma alhamis na samu jikina dayı
mani ciwo kala-kala amma hakan duk bai hani hirata da su inna
Tantu ba, da mai aikina, haka kuma ban sanar da Mustapha ba har
mu ka kwanta,
Mun gama sallah asuba, ni da Yallabai na, na samu na zame na
kwanta a cinyarsa ina jan carbi, idanyi lazimina, shi kuwa Yallabai
na yana karanta mana kur'ani a bai yane ina sauraro.
Kadan kadan na dinga jin marata na murdawa, tsaknain
murdawar marata bai fi sakan uku ba, sai gaba dayan kuguna ya
kama kara da wani juyi da kyar na samuna gayawa Yallabai cewa,
ciwo kugu nikeji.
Cikin minti goma sha takwas a tsakani sai gani a tsaye, ciwo
ya gagara zama balle kwanciya, a wauta irin tamu, sai Yallabai ya
ce in hau gado in kwanta, cikin dan karfin hali na dosana mazauna
na a gado, amma sai gani zimbir na mike tsaye.
Ganin haka yasa naga Yallabai ya fice da sauri yana kwallawa
iya lantu kira, tsawon mintina biyar su ka shigo tare da shi, ruwan
da nayi ya fara zubowa ta jikina shi ya tAbbatar mani da haihuwa
zanyi, kamar na sani iya tantu na zuwa tace masa haihuwa ce a kaini
asibiti
Amma Yallabai ba kunya ya kamani ya tsugunar yana shafa
gashin kaina, sannu kuwa a jere tafi bakwai, ina ji iya tantu ta kara
ce mashi, "a kaita asibiti ko Alhaji, "amma sai naji yace, a'a, bari
dai a kirawo dacta Amira.
Kai kawon da yake yi a tsakiyar dakina ita ta tAbbatar mani da
ba'a dauki wayar da ya buga ba, can naji ya kama fadar Alhaji
Mustapha, sau wajan hudu, tukuna naji ya fadi lakanin nasa
(inkiya) cewa Mustapha (muhab).
"Yanzu! Yanzu, kuwa ya fada har ba iya ka, tukuna ya ajiye
waya, ya zo yayi zaman dirshan a gabana, ni kuwa tini na manta da
sha'aninsu, sai dai kiran Allah da yan addu'oin da suka zo bakina.
Sama sama naji shigowar dacta Amira, ina jin Mustapha nayi
mata magiyar ta lura da ni harda ce mata wai kada ta barni in mutu,
da cewa ta haka matar babanshi ta rasu wajan haihuwa, tun dacta
Amira na amsa masa har ta kai ga yi mashi shiru.
75
Da tafiya tayi tafiya, in bude ido sai ganin Mustapha nayi
rakube a gefen gado yanata rigar kuka kamar wanda akayi wa
aiken mutuwar masoyi.
Karfe tara da kwata na safiyar juma'a na haifo yarona, a
yarda naji dacta a cikin taddin jinin da nike tsugunne Mustan
ya rarrafo ya rungumeni jikinsa yana fadar sannun da kar
dinga kada, mashi kai saboda yawan da tayi, dan kunya kuwa
inna Tantu dauke yaro tayi tayi bandaki da shi.
Da Mustapha akayi duk aikin jini nan, sai da yaga ya gyara
mani jikina tsab shi da dacta Amira ya gani a zaune lafiya tukuna
ke tamabayar inna wai me aka haifa wanda ni tun ina
durkushe nasan cewa da namiji na haifo, inna Tantu ta dauko
mashi yaro ta mika mashi.
ya
Amma dan bayar da kunya irin na Yallabai sai ya kama ce
mani, "kallarshi Hamida dawa yayi kama dacta?, dani ko? ya
tambayi dacta Amira, dacta tayi dariya tace "a'a, ya dai dauko
farinku ne kai da mamanshi da kuma gashin kansa irin naka ne,
amma sai in ga yafi kama da mai hotocan, "ta nuna hoton
mahaifin Mustapha Alhaji Najib Bauchi.
Mustapha sarkin bayar da dariya, haka ya sakamu a gaba,
har sai da dacta Amira tayi sallama damu ta fita, tare da rubuta
mani yan magungunan da zan dinga sha ni da bebi boy dina.
Cikin mintuna ashirinm da fitar dacta Amira har
mustaphana ya gama shaidawa duk yan uwa ta wayar tarho,
cikin takin awa daya da rabi da haihuwara har gida na ya fara
samuņ bakuntar mutane, karma ace Halimatu da zulaihat da
sauran yan kawayen mu, yan gida kuwa, har sun fara hallara, irin
su momin Halimatu.
Bayan dare yayi kowa ya tafi sashen shi sai su inna tantu da
"Iyami" mai aiki, zaune tsakar falo suna ta surutan hirar su, ni
kuwa na sawa jaririna idanu ina kallan kyautar da Allah yayi mani ni da Mustapha wanda ko da wasa ban taba aiyyanowa zuciyata zan auri Mustapha, balle har in haihu da shi. Hakan yasa kawai sai na tuna labarin da Halimatu ta bani na yarda akayi ta juye na zama ni ce amaryar Mustapha. 76
*** ***
Hamida lokacin da Mustapha ya dauke ki da mota kenan
ana gobe daurin auranmu, a dai dai 1okacin Abbana ya shigo
kwanar da zata kawoshi gidanku.
Du abinda ya faru tsakaniku a motar nan Abbana ya ganku,
ganin kun tashi mota shima yasa ya karya kwanar motarsa sai
gida.
Ban san hawa ba, sai dai Abbana kirana yayi ya dinga yi
mani fada, wai nasan Mustapha kike so, amma nace ni zan
aureshi, ni kuma ganin yanda Abbana ya ke fada, yasa na sanar
dashi nima bana son Mustapha yaya usman nike so, dama ranar
da Mustapha zai aiko da kaya gidan mu bakiga irin dukan da
naci ba wajan Abbana, wai ni ke ikoda kaina da zan baiwa
saurayi dama ya turo gidan mu, kinsan ranar da kyar abbana ya
amince da kawo kayan nan shima sai da jama'a suka taru a
kansa.
Ashe Abbana na tashi daga nan, ashe gidan Mustapha ya
nufa, ya tsarashe da bala'i ganin haka yasa shi kuma Mustapha
ya gaya wa Abbana duk yarda abubuwan suka faru.
Ina ganin Abbana gani yayi ko ya zo ya fadawa daddy kilan
ba yarda zaiyi ba, adole yasa ya dauki Mustapha zuwa gidanku
sannan yace nima a dauko ni,
A falan daddy Mustapha ya kara nana ta abinda ya fadawa
Abbana, wanda a gaban mamanki da yaya fada kamna shashi
kamar za'a yankani, wanda a take aka tambayi Mustapha tsakani
da Allah wa yake so a cikin mu, vace ke, ya kuma basu tAbbatar
cewa kema kina sonshi sosai
Anan take Abbana yace ya baiwa Mustapha ke, ni kuma in
auri yaya Usnan sai aka tambayeni cewa cikin kawayena wace
yarinya nike ganintana da hankali shine sai nace zulaiha, shine
su kace kada mu kuskura mu gaya maki.
Bayan nan suka je suka samu mahaifin zulaiha, yace ya
amince a baiwa sufiyanu diyarsa, bayan nan kuma suka
77
dunguma sai gidan mahaifin sufiyanu, suka yi ban hakuri tare da yi ma dansa wata kyautar.
Gudun tashin rigima yasa, aka kira sufiyanun da zulaiha aka
gaya masu, a take suka ce sun amince, anan aka kuma tara mu
mu duka aka ja mana kunne da cewar kada a gaya maki, har sai
ranar da aka daura ki ji da kunnenki,
Nayi ajiyar zuciya na kara gyarawa yarona kwanciya,
wanda sai a lokacin na daga kaina naga basu inna Tantu a zaune
in da na barsu suna hira, sai dai Yallaßai dina da ya maye
gurbinsu zaune a kujerar lokon dakina ya kura mani idanuwa
yana kallona.
Ranar safiyar suna kuwa yaro yaci suna marigayi Alhaji
Najib Baushi, wanda ni na zabl sunan, shi kuwa Yalla6ai na, da
cewa yayi asa sunan Alhaji Nafi'u "sani amini mahaifinshi.
Wajan karfe takwas na safe na samu na salale na nufi
sashen yallabaina, domin in duba ya yakwana a jiya daran suna,
samun sa nayi kwance a kasar kafet shame shame yana barci da
dan filonsa, da alama ma nan ya kwana, tausayinsa ya kamani,
wanda a take nayi tir da halaiyata ta ko in kula da nayiwa
yallabaina, duk akan kunya.
Isowa nayi na tsuguna gabanshi tare da nutsa yatsun
hannuna a cikin gashin kanshi, na dukar da kaina na sumbaci
kumatunsa, bude idanuwansa yayi a hankali, murmushin da yayi
shi ya kara mani tausayinshi.
"Mantawa kikayi dani ne?" "na isa in manta da kai, kana
zuciyata kaima kasan gidan nan ya cika sosai, amma yi mani
afuwa," na fada ina mai langwabe k
ya shafi gefan fiskata, "ni ma nasan da haka, sai dai kawai
in yi maki sannu da jama'a, na daga kaina naga tebir dinsa da
kayan abinci, "baka ci abinci ba jiya Yalla6ai?" "kinzo kin bani
ne?"
"Wallahi shigwaßaka Yallabai wani lokaci tana damuna,
yanzun na haihun ma vba zaka dinga cin abinci da kanka ba,
kullum nice yar zirga zirgar baka abinci." "ke kika koya mani,
"yanzun kayi sallah ko ita ma sai nayi maka?", "na isa, nayi
sallah ta, wajan zaman jiran ki shigone barci ya kara daukeni har
haka.
"Tashi muje in shiryaka ko," "to mama," nayi yar dariya, na
mika sai da na tAbbatar ya koshi, tukuna na ce ya shiga wanka
wankan kanshi rabinsa duk dani akayi shi saboda ina saurin in
shirya shi kafin jama'ar bakin zuwa su fara nemana.
Bayan na gama shafe masa jikinsa da mai, boyel ne ruwan
tuka wando da yar ciki da bAbban rigarsa, sabo fil, tare da
sabuwar sheme da sabon karamin wando, hularsa kalar kayance,
amma da ratsin baki a jikinta, takalaman sa bakake ne haka
agogonsa.
Na gama shiryashi tsab yana tsaye yana kallona, turaran
'ultraviolet' ne na fishe masa jikin sa dashi, yar audugar goge
fiska ta bature, ita na sa na goge masa fiskarsa, ita ta karayiin
kyan gaske "na lagwabar da kaina "na gama," na ce masa.
Ya tallabi kumatuna, "Hamida ina kika sami wadanan
kayan haka?" "dinkin sunane nayiwa mai gidana, ko nayi laifi?"
"na isa in fadi haka sai dai kawai in yi godiya ga Allah. da ya bai
ki aljanna fiddausi, shin wai a ina kika kai akayi maki wannan
dinkin mai kyau haka?."
"Wannan duk aikin Abdulrashid ne, "ni naga alama ma nan
gaba kwace mani Abdulrashid zakiyi, wannan iri sirri haka, ko
da wasa bai taba nuna mani abinda kuke yi ba na gode fa," "da
aka me?" "da wannan hidimar,""ka wuce haka."
Yanzun kuma sai ina yallaba?" "kema kinsan ba zan iya
zuwa ko ina ba, zan zauna babban falo na can kofar gida saboda
na san nima zan dingå samun baki, "har na dan juya manufata
mu tafi, sai naji ya janyo ni, "ki kula da yaron nan kada a sace
mana shi."
"Wa zai daukar mana shi Yallabai?" "mutum," "haba har
ya fita ba'a ganshi ba, "to "to kinsan ko wadanne irin mutane
zasu shigo gidan ki a yau," "E fa da gaskiyar ka in sha Allah zan
kiyaye," na langwabe kai, Yallabai dan Allah in hudu ta yi kasa
a gira mana kujeru a kafa rumfuna, kasan zamu danyi liyafa."
79
"A nawa?" "bani da kudin da zan iya bayanka," "to shi
kenan ba kya so kenan," wayyo don Allah," "sai kin biya," "to
runtse idanuwanka in biyaka, ""ya kuwa runtse idonsa, ni kuwa
nayi saurin sumbatar kumatunsa, dana zo bakinnsa, na tura masa
hallashena.
Cikin sakan biyar ya canja sauyi numfashinsa, wanda ni
kuma nayi dubara na kwance halshena," "na biya ko?," "Hamida
you care for me," na kada idanuwana tare da yin murmushi na
koma na kwanta a kirjinsa.
Ba zan iya cewa ga yawan mutanan da suka zo ba, saboda
ko yan masari wajan motoci shida suka zo wanda dama kowa
dama kowa ya sansu da zumunci.
Daga indiya ma munsha manya manyan baki kannan
maama Yallabai da sauran danginsu, alhamdulillahi, gaskiya yau
nasan ni Hamida gidana ya komawa tamkar jama'ar garin suna
kokarin tafiya masallacin juma'a
Sai da muka sami tsayin kwana uku muna barcin gajiya ni
da (junior) jiriyo na sunan yaro najib kenan saboda gajiyar taron
suna da hayaniya da muka sha balle shi dama bai saba ba.
Kwanan mu talatin da uku Halimatu ita ma ta sauke nauyin
da yake makale a cikinta inda ta haifi lafiyayyan yaronta namiji,
zama kuwa dama bai ganmu ba, saboda tun a lokacin na fara kai
kawo tsakini gidana izuwa gidan mai jego Halimatu.
Wanda yanayin hakan har tausayi Yallabai na ya dinga
bani, tunda a kullum sai dai ya yini ofis saboda ba mata a kusa,
balle dan yaran mu jiniyo.
Bayan suna da kwana hudu ne na samu na tsuwa cikin
gidana ni da dan yarona, wanda a lokacin in ka shiga gidan mu
baka jin motsion kowa saboda barcin gajiya da na rungume dana
jiniyo na muna yi.
Babu zancan bude ido tunda na kwanta karfe takwas da rabi
na safiyar ranar saboda tsananin gajiya, sai dai in na motsa inyi
kokari in sa hannun na daya da kyar in laluba inji lafiyar jiniyo.
A karon da ya zına shine na karshe a wajena, shine na daga hannuna a magagin barci, na lalubo jiniyo amma sai naji ba
80
komai a kusa dani, nayi saurin bude idanuwana, wanda tuni
cikin sakan dayan da ta wuce barci yayi masu kaura, bushewa
idanuwa ta sauka a garesu.
Saboda tunanin ko jiniyo ya mirgina ya fada kasa ne,
alamun zaman tallabar yaron da na nannade jiniyo ma babu a
duk cikin dakina showil" a cikin wani yanayin na rawar jikin
nayi wajen dakina da saurin.
Babu alamar motsi ko ka dan duk a fadin gidan namu,
amma duk da haka ban karasa karaya ba, saboda nayi kokarin
dauki "Remote, irin abun kunna talabijin ko vidio, amma ita ta
bude såshin Yallaßai ce domin în duba in gani ko Yallabai ne ya
dauke shi,
Ko ina na cikin sashen Yallaßai na duba amma ba jiniyo a
ciki, nambebin kiran Abdulrashid na daddanna, cikin tsamin
minti biyu zuwa uku sai ga Abdulrashid, ganin na tambayeshi
yace mani bai ga jiniyo ba shima, sai naji hankalina ya kara tashi
matuka.
Cikin yan mintunan da basu fice biyu ba na baza su
Abdulrashid da ragowar yaran da suke cikin habar gidan, da su
shiga binketan neman mani yaro na, bada tambayoyin da na
dinga yi masu akan waye suka gani ya shiga, da sauran ire-iren
su, amma sai suka ce mani wai ba kowa.
Bayan duk sun fice ne ni kuma da rawar jikina na dauke
wayar talho dake gefe, na na daddanata domin neman Mustapha,
buga daya na ji miryar yalllabai a kunnena, babu zancean baye
boye na zaiyana mashi cewa an sace jiniyo.
Babu amsar da yabani sai wai ya tambayeni an duba duk ko
ina na gidan? na amsa mashi da 'e' sannan ya kara cewa har
bayan gida?, ce masa nayi ya rike wayar in ruga in dubo nayi
saurin ajiye gan waya gefe na tafi da sassarfata har da dan
guduna.
Sanyi naji? Ko haushi naji?, ko kuwa murna zanyi?, "abinda
naji kenan ya ratsa mani a zuciyata a dai dai lokacin da na bude
kofar baya na hango Mustapha zaune ya zura kafafunsa a ruwan
wanka rami "swimming " rungume da jiniyo a jikinsa,
81
Tsayowar da nayi cak, ita tasa gwiyoyin kafafuna sukayi
sanyi wanda atake na durkushe kasa koma ince na zaune kasa
tare da sakin ajiyar zuciya guda biyar a jere.
Ganin haka da yayi yasa na ga ya taso ya nufo ni tallabe da
jiniyo, ga kuma talho din hannu a dayan hannunsa, ban iya ko
motsi ba, in baya ga numfashina da yake fita a kai akai, har yazo
ya durkusa gwiwa biyu a gabana.
Ga yaronki," yace mani, sai a lokacın na dago kaina sosai
na harareshi, wai sai ya tuntsire mani da dariya, ban tsaya karbar
shi ba na mike nayi cikin gida in da na sami su Abdulrashida
tsaitsaye," madam dama
Yallabai ya dga masu hannu, sannan yace su tafi. Ina ganin
sun fita na juyo na karbi jiniyo na kwantar a duguwa kujera,
sannan na waigo na sakar masa dan dunduna a gefan kafadarshi
ya tuntsire da dariya, sannan ya janyoni jikinsa.
Ashe kina son jiniyo?," "wae irin tamabayar ce wannan ni
dana haifi abina," "abinki ko abina" "lallai ma, wace ni don
Allah ya akayi ka shigo har ka daukeshi ba wanda ya ganka," su
Abdulrashid sun san na shigo, koma ince sunsan yana hannuna,
ni nace suyi shiru saboda in gwadaki ingani ko ana son abinda na
haifa."
Na tureshi ya tuntsire da dariya, "oh su Hamida masu da,
jihar an tashi hanlkalin yaran mutane, "kinsa Allah na shiga na
ganku a kwance sai naga kunyi mani kyau daga ke har jiniyo,
nan take naji sonki ya karo a zuciyata yanzu Hamida wata rana
sai ki fi son 'yayaki dani fa ko?" na harareshi, na kubuce jikina
nayi gaba wanda shi kuma ya biyoni da sauri ya dauke ni cak sai
dakin barcinsa, wanda ya ce sai na bashi amsa tukuna zai
rangwan ta ya sakeni, dan ihun da nike ne baya son jin shi, sai
yasa bakinsa ya rufe nawa.
Kwana goma sha tara ne tsakanin Halimatu da zulaihatu,
wanda itama ta haifi yaranta namiji, anan take dama nace mun
samu yan uku, Najib da Haruna dan Halimatu kenan, yanzu ga
sabo ya iso ina ajiye kan tarho din ba inda na zame sai shashen
yalllabai yana kwance na fada masa da guduna ina kiran itama ta
82
haihu lafiya," "wakenan wakenan?" "nace zulaiha mana, namiji
itama", sai kawai na ga ya kawar da kansa gefe,
Na mirgina na koma saitin fiskarsa na sassauta mirya kamar
ta marar lafiya amma Allah Yallabai ka bani mamaki a tunani na
yarda kaga na haihu a gabanka, a nawa rashin hankalin sai in ga
ko a hanaya kaga mai ciki zaka tausaya mata kayi mata fatan
Allah ya rabata da shi itama ta samu lafiyarta, ta dawo mutum
kamar ko wane mutum da yake yawo duron kasa.
To balla wacce kasani, kai Yallabai gaba bata da
kyau","wake gabar? aini bai isa inyi gaba da shiba, huldace dai
kawai bana sonyi da shi, saboda ban son yawan haduwarki da
shi.
Ya kamo hannuna, kikayi shiru,"me"zance makka",Allah
huci zuciya, nace Allah ya raya masu,najanye hannuna na
tashi,na zauna, yamatso ya rungumi kuguna daga kwancan nan,
"Hamida kada kiji haushina, wallahi ina sonkine matuka,sannan
ina kishin a dinga ganin mani ke a waje.
To balleshi da yaga samu yaga rashi kiyi tunanin saura
kwana daya a daura maki aure dashifa,haba Hamida kinsan dai
mutuwa nayi yanzu na yi imani sai ya shiga sahun zawarki".
"Me kuma ya kawo wannan maganar Yallabai? ni dai iyakaina in fada,inkagdama kadauka,sannan katuna