dama kuma dan shi
nake yi, na mike muka tafi tare da Mustapha. Har makayi nisa da
tafiya, bai ko kalli inda nike zaune ba, balle wata magana ta hadamu
da shi.
Titin da zai fitar damu daga unguwarmu, mai tama dai dai nan
naga Mustapha ya kashe mota, ni kuwa sai ma na kalli bangaran
marfin sashena, tsawon minti biyu tukuna ya fara magana.
Kin san saboda ke na tsaya, amma kika kalli wani 6angaren,
duk dan ki kara mani wani hasuhin," "haushin me zan kara maka,
kai ba mijina ba?, ni nayi zaton ko motarce ta lalace shi yasa,
sannan ganin in na kalleka haramun nake kallo, shi yasa na juyar da
kaina gefe, amma tunda magana gareka, kayi kokarin kayita da
wuri saboda kasan fa aroni kayi, wanda ka aroni a hannunsa fa yana
can yana ji.
"Bana san wannan maganar ta isa haka nan, "just looking at
me" na waigo na kallshi, "me kika gani a idona da jikina?" "banga
komai ba," "ki kalleni sosai Hamida," jin ya rage sautin miryar yasa
na kalli bangaren wajan motar.
"ki kalleni sosai Hamida cikin tsakinina duk na rame saboda
ke, Hamida bazan iya auran da zakiyi mani ba, dan Allah ki yafe
mani shi, nasan zuciyarki za tayi kuncin naki auran kawarki
ba
"Me yasa kake mayarda zance baya Mustapha, na fada
amma fa nima sai naji miryata ta rage zakin da takeyi a dazu,
"saboda ina kaunarki sosai a zuciyata, dan Allah ki kalleni Hamida,
21
pa dan na isa ba, na juyo na kalleshi muka hada ido da shi, wanda
sai a lokacin naga kwayar idansa ta koma ja, sumar gashn kansa ma
tasan jikin Mustapha ba lafiya.
Me kika gani? na kawar da fiskata gefe "ba komai sai ciwon
ido da naga idan ka nayi," "yayi wani dan murmushi mai tashi da
dan kadan din sauti, "kinsan abinda ke damuna, nayi imani kinga
abinda kwayar idona ke so, kin san ke take so Hamida.
"to yanzu duk me ya kawo wannan maganar, ka san, "is too
late," "wallahi is not too late,' in kin bani izini yanzu in je in mayar
a daura mani auran da ke," "kenan mun zama maciya amana ko?"
"sam ba cin amana bane, san kaine, kin san kuma duk duniya ba
farkon abinda ya cancanci dan adam ya so, illa ya so kanshi, kafin
son kowa."
Amma ni wallahi zuciyata tafi sonki fiye da kaina kinga kuwa
don naso kaina a kanki ai na yiwa kaina adalci kenan""yanzun dai
zaka wajan Halimatu ko ka fasa?" "ni dama ba wajanta zani ba.
Wajanki na zo,".
"Amma kasan bai cancanta ba ko?" "saboda me kikace haka?”
"saboda yanzu na zama matar wani," "walla'i kika kara fadar
wannan kalmar sai na wulakanta maki rayuwa yanzun nan".
Ni zan koma gida," "sai kin dawo," ya juyar da kansa gefe, ni
kuwa kokawar bude kofa nike, amma taki budewa, na dawo da
kallona gareshi.
"Why?" "da akayi me?" "da ka rufeni," "au baki san wajan
budewa ba ne? ko da yake ba mamaki, baki faye shiga motata ba,
tsaya in bude maki,"
gaba dayanshi ya kwanto jikinshi a jikina, mai makon ya bude,
sai naga gelas din motar duk sun rufe," "me ye haka Mustapha,
jikinane da ya hadu da mahadinsa, sai ya ji ba zai iya rabuwa da shi
ba, ni ba ruwana, jikina ne, Hamida."
"Mustapha bai dace kayi mani haka ba, kasan fa in
hali
Hannunsa naji a bakina, ya rufe maganar da zanyi, "Hamida
ilove you, I cant marry your friend", amma kina son bata mani raina
33 da yawan yi mani maganarta.
25
Na saukar da ajiyar zuciyar da ta dan fito fili, "yasa
danyatsansa yana zagaye la66ana, "kiyi hakuri, na baki haushi ko?"
nasa hannuwana na tureshi, sam na manta da ciwona sai a lokacin,
hakan yasa na famashi sosai, na dinga yarfe hannuna ina wash!
Wash!! "Kaga ni kaja na fama hannuna, dama zuwa kayi ka karasa
gutsure mani shi."
"Wayyo mu gani, mugani!! Har kinsa hankalina ya kara tashi
sosai, "naki nuna masa har sai da ya kamo hannun da tsiya, "kai!
Kai!! Kai!!! Yanzun Hamida kika zauna hirar banza da hannunki
kumbure haka, kila ma karaya ce.
Jaki mahaukaci, wai shi yana son mace amma bai iya kula da
rayuwar ta ba," "waye shi, "na fada ina wash, mahaukacin da kika
baro yana jiranki," ya fada a dai dai lokacin da ya tashi mota,
hankalinsa a tashe bai zame ko ina ba sai asibitin dake kusa
damu."
Da shiga abinka ga babban mutum, nan da nan aka yı mana
jagora sai wajan likita, muna shiga yace wai matarsa ce ya kawo, ta
samu matsala a hannu, nan likia ya tayashi murna, da Allah ya
sawake, sannan yace yaga hannurı.
Yana fara taba hannun nace wash! Wash!! "dacta da zafi fa"
"to sannu! Sannu!! Sai kin daure," ina kallan Mustapha kamar yasa
ihu, ko ban sani ba nasan abu biyu Mustapha yake batawa fiska,
shine zafin da nike ji wanda ba zai iya cire mani shi ba, sai
lagwaiwaita mani hanun da likita ke yi.
Likita ya saki hannuna ya kalli Mustapha, "Yallabai ina jin sai
dai a kirawo mai gyaran hausa, amma na duba ba karaya bace, ba
tsagewar kashi ba kila dai targade ne, ko gocewa, wannan sai masu
aikin gargajiya, ya danyi shiru.
"Yauwa, inji likita, "a kwaı wani yaro da muke kira yana yi
mana ire-iren wannan aikin in ya taso, in ka amince a kira shi," "ba
komai, ba komai a kirawo shi amma ai zata warke, zuwa anjima
ko?" likita yayi dariya wadda nima har kunya sai da ta kamani.
Cikin zaman minti ashirin sai ga wani yaro ya shigo,
shekarunsa na haihuwa sayi ashirin da biyar bakine, amma da gani
bakinsa mai kyaune, ya shigo ya zauna shima tare da gaishemu,
Lanka amsa, sannan ya gaisa da likita.
26
"dama wannan hajiyar zaka duba mana hannunta ka gano
mana me ya same hanun nata, saboda muji dadin bata magani," "to
tallabai. yaron yana zuwa ya tsuguna gabana, Mustapha na tasowa
daga kujerarsa shima, ya tsuguna gefena, kamar inyi dariya, sai dai
na dan dakc.
"Irin damkar da yayiwa ya tsuna, tasha ban ban da ta
likitawajan zafi, ai kuwa nace, "kai! Kai!! Wash, kai da zafi fa
sosai, kayi a hankali," sai yasa hannu daya a tafin hannuna, dayan
kuwa ya fara taba 'yan yatsuna.
"Dakata dakata!! Dakata!!! Kaga da zafi fa, ga mani yarda
akayi inji mta, "alhaji hakuri zakayi ya duba mana, saboda abun ne
sai wanda yake aikin shine za iya ganewa," likitane yake baiwa
Mustapha hakuri.
"To! To!! Shi kenan kayi mata, ni ba ruwana ısaya in fita, ni
ba zan iya gani ba, da ciwo fa," ba wani zancen ciwo kishin tsiyane
na kada a taba mani hannu, ke damunshi, amma duk da haka, sai
gashi ya kasa fita.
Wanda ni kuma tun ina daurewa, har sai gani ina zubar da
hawaye, a haka mai gyaran hannu ya gayawa likitu cewa targadeee
yan yatsun uku sukayi, dayan kuwa gocewa ce, nan take likita yace
ya kama mani targaden, ko ince ya gyara mani hannun gaba daya.
Sai gani ina kuka ina rike Mustapha, saboda wani irin tsananin
zafi da naji yana ratsa mani jiki, da kyar na samu na daure aka gama
mani, sannan likita ya rubuta mani magunguna, har da na shafawa a
yan yatsun.
Muna shiga mota, dukewa nayi, na cigaba da zubar da hawaye
da suka rage mani na zafin ciwon hannuna, jin Mustapha nayi ya
daga kai na, baice mani komai ba, sai dai yasa gefan rigasa yana
goge mani hawayen fiskata, "da zafi ko?, sannu dan ba yanda za'ayi
in cire shi daga jikinki ya dawo kaina, da nayi maki.
Yayi shiru, da nasan haka zaki sha wahala, da ban kawoki ba
ni na janyo maki ciwo har haka ko? Sannu, sannu haka ya dinga
lallashina, har ya samu nayi shiru, sannan yada mota muka tafi.
Mai makon mutafi wajan Halimatu, sai naga mun tsaya a
.SAIHAD STORE' sai naji yace in jirashi, minti goma sha biyar da
27
shigarsa, sai gashi ya fito da yar bakar leda, a hannunsa, sai da ya
shigo ya zauna tukuna ya miko mani ledar.
"Kayan gyaran fiskatane ki gyara fiskarki, gudun kada mu
koma a dinga tambayarki" "na dan harareshi, "ni ba zan gyara ba,"
"Hamida tausayinki nake ji yanzu, da sai na biya ki kudin kallon da
kike yi mani kinyi mani shi a ofishin likita, yanzu ma kin kara zan
rama, ne
Nayi shiru bance kõmai ba, ki gyara mana, "sai ka fita," "ina
zani ni da matata "ni ba matarka Bace Halimatu ce
mat
Kafin in karasa ya fice daga motar, bayan kamar minit goma,
sannan na fito nima, na. gama," bai kalleni ba ya bude mota ya
shige, na shigo nima, ko rufe wa banyi ba, ya kanayi imani fada.
"Ban gaya maki in muna tare kada ki Kara ambatar-stınan wata
ko wani ba, na lura-ke dai Hamida kullum kin, tison kiga raina a
bace," "Allah huci zuciyarka ni das yanzu mayar dani gidanmu don
Allah," "yaushe ne kuke fatin naku?" Karfe biyar na yamma in sha
allahu mun fara, "a ma zakuyi? A BUK Gust INN.
Bai ce komai ba ya ja mota, zaka zo ne?" inna samu dama."
"zan iya gaya mata hakan?" ko na zo ba dan ita zanzo ba." "dan
wa zaka zo? ke "ni Mustapha waigo ya kalleni, sai naga yayi
murmushi.
"Hamida ina son in ji kin kira sunana, sai inji sanyi a zuciyata,
yanzu har naji bacin raina ya kau. zanzo wajan fatin na ku, amma
kada ki kurkusara kiyi mani abinda zai bata mani ra, "to ni kuwa
ina ruwana da zuwanka balle in kai ga bata maka rai, kai da ka zo
saboda matarka."
"Wacece matata?" "ita ha "Ya kalleni, "to ba zan
ce Hamida ba kuma ya tuntsure da dariya, "sai tsoro da kinsa
vanzin na kara yi-maki wani kamun hannu, na harareshi ba sai in
some maka ba yanzun wai kila maki Sani hawan jini," mu kayi
dariya ya kawoni har gidan mu ya ajiye da tabbatar mani zaizo
wajan fatin mu
Hankalina gaba daya yana ga Kofar shigowa dakin taron fatin
namu, ganin kowa ya gama shigowa, har an fara addu'ar bude taro,
amma ba Mustapha, duk da nasan ban gayawa Halimatu yanda
28
mukayi da shi ba, amma duk da haka sai naga yau Halimatu tanata
fara'a ta saki jiki sosai, ba kamar baya ba.
A zuciyata ba abinda nike cewa, sai yaya Mustapha zai yi mani
haka?" bayan angama addu'a an shafa cikin abokan sufiyanu wani
ya mike kenan zai fara magana sai kawai naga fiskar Mustapha ta
shogo dakin taron, ban san lokacin da na mike tsaye da sauri ba,
tare da fadar Halimatu ga angonki."
Gaba daya kallo ya koma ga Mustaphan da ake takewa baya,
wani abun da ban fahimta ba, shine Mustapha na shigowa, naga nan
take ana canja, mazauni, ma'ana sai naga sufiyanu ya tashi daga
kusa dani, mazauninshi na ango ya koma kusa da Zulahatu, yaya
Usman naga ya koma mazaunin kusa da Halimatu, mazaunin
sufiyanu shi kuma Mustapha ya zauna.
Kafin in gama mamaki, har mai magana ya fara da cewa
"jama'a kada kuga anyi haka ku dauka wani abu, ba komai muna
tafiyar da tsarin ne tamkar tsarin turawa, saboda kara hada zumunci.
Anyi taro lafiya, an kuma tashi lafiya, wanda mu duka
hankalinmu a kwance, saboda Mustapha bai nuna wani abu ya shiga
tsakanina da shi ba, ya saki jiki sosai da Halimatu, sii dai abu daya
da ya so ya bani haushi shine, yawan shigewa sufiyanu da naga
Zulahatu nayi, wanda na kasa daurewa, har sai da nayiwa sufiyanu
magana.
Amma sai yace mani, ba wani abu, saboda ni Zulaihatu ke yin
haka, dan gani raina ya dan sosu, har na dan samu waje daya ni
kadai na zauna, yasa Mustapha, ya zo ya tambayeni ko lafiya,
gudun kada Halimatu taji yarda naji yasa ban tsaya bashi wata amsa
ba, nace ba komai, kawai na mike na shige cikin mutane.
Komai lafiya kalau, har ranar daurin aure tą zo, ranar asabar da
yamma karfe hudu za'a daura auranmu, wanda yan masari da mai
maiduguri suka bada lamanin, ayi a nan garin abuja, saboda kada a
baiwa jama'a wahala da yawa.
Karfe goma na safe, zuwa karfe uku na rana, akayi walima ta
musamman wacce Mustapha ya hadata a matsayin walimar iyaye da
manayan baki, wacce za'ayi a naicon, mada din in an dawo daga
daurin aure, saboda in an dawo daurin aure, zamu zauna a nan
29
naicon hotel din har su dawo, a in da mu kuma zamu kara shiryawa
da angunanmu, zuwa hotel din Prince hotel.
Domin tamu dina fatin wanda zamuyi yamu-yamu yara, wanda
zai iya daukar mu har karfe sha biyu na dare, hakan yasa anguna,
suka roki alfarma abar kai amare sai lahadi, wanda itama ranar
lahadin za'ayi karatun Qur'anic and Recitation da yar fadakarwa,
zuwa la'asar a masallacin Abuja, watau National Mosque. In an fito
za'aci abincin iyaye na Allah bada zaman lafiya da a zahar bayan
sallah, a koma har zuwa karfe biyar sai a tashi bayan nan ne da dare
za'a kai amare gida jansu.
*** ***
Taro yayi taro a Hotel dan naicon wanda ko ban fada ba kasan
an hada manyan Nigeria a wajan, sa da aka dinga gaisawa da
jama'a, mu yara da su iyayenmu kansu, wanda hakan ya dauki awa
daya lafiyayya, takuna aka bayar da izinin a zauna.
In da duk tebir mutum hudu ne, da kayan sha, a gaban su, mu
kuwa tebir din mu, mu hidda ne ni da sufiyanu, sai Halimatu da
Mustapha, sai bAbbar kawarmu Zulaihatu, da yaya Usman a gefen
mu, mun zama shida kenan.
Wanda muna can saman fakin taron, "gefen da iyayenmu
suke, sai dai ba'a jere da su muke ba, Mai makon in ga an fara kawo
abinci sai naga manyan kasa sun fara tashi suna magana daya bayan
daya da turanci, abinda ya daure mani kai shine in da iyayen
anguna da amare suka dinga magana daya baya daya.
A wajan kalaman Daddy na sai naji yana cewa ya gode Allah
da ya kawoshi auran yayansa uku gaba daya, saboda dole yayiwa Baban Halimatu kara yasata cikin yayansa biyu su cike uku kenan. Ban damu ba, saboda ina tunanin, ni da sufiyanu yake nufi, sai ita Halimatu Alhaji Nafi'u Sani, shi ya zamo madadin mahaifin Mustapha, bayan sane Hajiya Hindatu ta fito tayi nata bayanin godiyar ga Allah, bayan nan sai Alhaji Yusufari Abba Ghana mahaifin Halimatu, in da yayi godiya ga Allah da Allah ya kawoshi auran yarsa, da kuma yayan amininsa su biyu.
30
Sai kuma mahaifin safiyanu yayi shima in da naji yana mika
godiyarshi ga mahaifin Zulahatu, da iyayenmu, nan take nace, oho
dai sufiyanu yariga ya zama nawa, Zulaihatu sai dai ta samu wani.
Shishshigi nace a zuciyata, da naga mahaifin Zulaihatu ya tashi
yana bayanin wai ya gode Allah da Allah ya kawoshi bikin yarsa
Zulaihatu, nan take, sai nace a zuciyata, to ko yayana shi zai auri
Zulaihatu, sai naji wani irin sanyi a zuciyata, saboda Zulaihatu ta na
da halaiya mai kyau tun muna makaranta.
Bayan nan ne aka danyi yan kide-kide da yan wasannin
kwaikwayan turanci, wanda zuburdaya, yayi da mutanansa bayan
su, sai Papa Ajasco shima yayi da mutannansa, yan waka kuwa har
da yan koroso da Bodan katsina su Dan maraya, sani Dan indo.
Sai da aka samu wajan awa uku anayi tukuna aka bude taro da
addu'a aka fara cin abinci, inda da aka gama aka yi sallah a zahar
aka dan bata lokaci wajan kara gaisawa zuwa uku da rabi na
yamma, daga nan, aka dunguzuma sai daurin aure.
Sai aka barmu yan mata kawai, in da mu kuma muka shiga
dakunan hotel din muka huta, wasu kuma suka fara yin wanka,
gudun kada azo ana jiranmu, iyayenmu mata kuwa tuni an kaisu
gidajansu.
Kamar a mafarki naji mai magana da lasifika a cikin talabijin
din da muke kallo sama-sama yana cewa, yau Allah ya kawo ranar
da aka daura auran (HAMIDA DA MUSTAPHA NAJIB BAUCHI)
wanda mutane suka fi sani da (MUHAB), Har tashi nayi na tsuguna
gaban talabijin, amma mai magana sai kara mai-maitawa yake
dalla-dalla.
Har ya zamu na dagowa ragowar kawayenmu masu surutu,
cewa suyi shiru in ji, amma mutumin nan da ya fada Halimatu da
yaya Usman, ya fada sai inji yace wai sufiyanu da Zulaihatu, karshe
sai na karajin yace Hamida da Mustapha.
Na dinga kwallawa Halimatu kira a rude, ina cewa," zo kiji
mai rahotan nan yana shirme, muyi sauri muyi waya a gayawa su
daddy su sa ya gayara, wai sai naji Halimatu ta ce mani, "Hamida
kenan, (baki san reshe ya juye da mujiya ba)".
"Ke da Allah ana maganar kwaba da dan rahoton daurin aure
keyi ke kina wani zakwalo wata karin magana can," cewa fa yake
31
wai keda yaya Usman, ni da Mustapha, shashasha, kinga, bari in yi
saurin yin waya kada duniya tayi zatan da gaskene.
"Ai ba karya banc ba fa Hamida, abinda yake fada shine
gaskiyar magana, cewa an daura maki aure da Alhaji Mustapha
Muhab, wanda ni kuma gurina ya cika na auri wanda nike kauna
yayanki Usman, shi kuwa sufiyanu, ya samu sakaiyya da Zulaiha."
"Wace irin maganar banzace kikeyi haka? Kin san kuwa abina
kike fada Halimatu?" " Sani kuwa, kuma ni ba maganar banza na
fada ba, maganar gaskiya na fada, kuma magana ta riga ta kare,
tunda an riga an daura, sai ki sani daga yau Mustapha ya zama mijin
Hamida Haruna Masarin katsina.
Bata karasa ba na mike, "wallahi bai isa ba, abinda kuka kulla
mani kenan ke da Mustapha, wallahi bai isa ba, shi din me" "a dai
iya baki, saboda miji ba wasa bane kada a kwashi lodin zunubi tun
yau."
a
"Wallahi Halimatu bani son wulakanci, in bakiyi mani shiru ba
zan gungunduma maki ashar yanzu, banza,banza marar hankali."
"sannu Hamidar hankali, kinga in zaki je ki shirya ki shirya, kin san
tunda an daura yanzu za su zo mu tafi ko kin manta muna da sauran
abubuawan yi a gaban mu? Hamida matar Musta. nayi
saurin dana mata duka a cinya da karfi wanda yasa tayi shiru dan
dole.
Mayafina na samu na yafa na samuna dauki jakata na rataya
sai hanyar fita, ina kaiwa kofa wata kawarmu saude mudi ta biyoni
wai mayafinta ne na dauka, na waigo nace mata," in kineda karfi,
fizge daga jiikna, nayi gaba ina jinta tana cewa tsaya mana ki gani
in ban fizge ba," ban kulata ba nayi gaba.
Ni nasan banzo da mota ba, ga filin hotal din ba kowa sai
tsirarin mutane, sai kuwa masu gadi, amma hakan bai hanani taka
kafata in fita daga harabar hotel din in samu mota ba, ina kawowa
get din hotel din, motocin mustapaha da na jama'a gaba daya suna
kawo kai.
Jin anyi wani jan birki da duk wanda ke kusa sai da ya razana
da ko haďarine za'ayi, hakan yasa nima nayi saurin waigawa sai
naga Mustapha ya fito daga mota da tayi haka da saurin sa ya
nufoni, ban fasa tafiyata ba, har yazo yajera dani.
32
"Hamida kada ki bani kunya a gaban jama'a zanyi maki bayani daga baya, nasan dama dole ki ji abin a bazata kiyi hakuri, ki daure ki nunawa mutane, dama kinsan komai, saboda abin nan da ya fara
na family ne ba dole ne ba jama'a su sani," "ka sa a kaini gida," "muje in kaiki, "bana so" "to naji! Naji!! Zo mu je in sa akaiki, "don Allah ki saki fiskarki."
Na dan juyo har da murmushina, kamar dama muna cikin hirar
soyayya da shi ne, sannan nace, muje kasa a kaini gida," don Allah
kiyi mani arzikin in kaiki, ko mai zakiyi mani kiyi mani shi a mota,
kada ki bani kunya, ki duba jama'ar da suka taso daga nisan duniya duk saboda mu".
Duk magiyarsa ban amince ya kaini ba, sai na wayance masa
da jama'ar da ya tara, da kyar ya amince da hakan. Ina zuwa
gidanmu, gidan a cike makil da jama'a na samu na ratsa na shiga
dakina na kulle kaina a ciki.
Tambayoyi na dinga jirowa kaina na ya akayi haka ta faru?
Shin ko dama can tarko Halimatu tayi mani ta turani wajan
Mustapha?, ko da hada baki suka yi da Mustapha bar sani ba?
Amsoshin tambayoyina nasan sai Halimatu ce kawai zata. iya amsa
mani su.
Hakan yasa na koma na kwanta a gadona, ba abinda nike
tunani, sai ya ma za'ayi in auri Mustapha, wanda har yau zuciyata
bata gama amincewa da shi ba, me nayi kenan ina zauna da
Mustapha a matsayin /mijina?, daga bangaran gefan zuciyata naji
ance mani cin amana.
Nayi tsoki, wai an daura mani aure da Mustapha abinda
zuciyata ta fada kenan, to ya akayi har haka ta faru ban sani ba?
Kenan ban cikawa haliamatu alkawarinta ba? Sai naji hawaye sun
cika mani ido, saboda tunanin duk wahalar da nasha ta zama ta
banza kenan tunda gashi a karshe ya zamana naci amanarta, tAbbas
ba zan auri Mustapha ba, sai dai yasan yarda zaiyi da auransa da ke
kaina.
Kara naji dai-dai lokacin da hawayena suka karasa
gangaraowa, na daga kallina na kalli gogon gefen gadona, karfe
biyar da rabi na yamma, kenan na samu minti talatin da baro hotel
din. 33
Karfe shida da mintina uku, naji an kwankwasa kofar dakina,
kiran sunana da naji anayi shi ya tAbbatar mani da miryar Halimatu
ce, ina jin shirun da suka ji nayi ita tasa suka daina, amma bayan
yan mintina kadan sai naj wayar gefan gadona tayi kara, ban ki
dauka ba, saboda ban sanko waye yayita ba, na dauka tare da
sallama ta, miryar mustapha da naji ya ambaci sunana a sanyaye.
Tare da cewa, "Hamida kada kiyi mani haka, please ki zo mu
tati," ita tasa na kife kan wayar, tunanin zai kara bugowa,yasa na
daga kan wayar na ajiye gefe, bai fi mintina goma ba. Sai naji
miryar Daddy yana yi mani magana.
"Ba zata bude ba ko me?" "E daddy mun kwankwasa ta ki
bude mana," miryar Halimatu kenan, "bude mana," na mike da
rawar jiki na bude kofa, mai makon inga daddy na shi da su
Halimatu sai nagashi tare da musatapha, "baki san mutane ne ke
jiranki ba, shine za'a buga maki kofa ki ki budewa, wani irin rashin
hankaline haka, kai kuma kayi tsaye kana kallanta,ba zaka zabga
mata mari ba, shashashar kawai shirya ki fita ko in dawo maki
yanzu," yayi baya da saurinsa, na koma da baya ni kuma zuwa
cikin dakina, jin an rufe kofa shi yasa na juyo, Mustapha ne ya
rufeni a dakina," "dalilin tambayar da nayi masa kenan, "kada a
gane mani mata, kinsan fa kaya zaki canja ko?.
Na harareshi, kada ki kuma yi mani wannan kallan, in kika
kara zan zo in biyaki yanzu ko kina musu?," bance komai ba, na
bude akwatina na dauko kayan da zansa, ina jin tafiyarsa ya nufoni,
amma hakan bai san na daga kaina ba.
"Karbe wadannan ki sa, "ya miko mani yar karamar jakar matafiya, "ina da kaya ni ma wanda mahaifina ya din ka mani"
"nasan da su amma wadannan nike son ki sa a matsayina ni kuma
na mijinki," sai ya ajiye ya koma gefen gado ya zauna," mutane na jiranmu a waje, nasan kinsan da haka."
"To ka fita in sa kayan ki," "ba in da zan fatia in zaki sa ki sa," "da wannan fadan ba kara ka zo ka dakeni ba" "Allah baki hakuri
na daina, bari in runtsi idona saiki saka," yasa tafin hannayensa duk viyun a fiskarsa, na figi jakata na shige ban faki na kulle, ina jinsa yana cewa yau ne karshe, gobe kamar haka sai yarda nace," a
zacıyata nace ba dai ni Hamida ba.
34
Sam wajan 'happy day na kasa hada ido da Halımatu sunar
fatın namu kenan, to balle sufiyanu bawan Allah, wanda shi naga
ma ya hakura va ungumi Kaddara, shi walwalarsa yake cikin
jama a ni kuwa tun da na zauna a kujerata ta amarya ban tashi ba
har yanzu, tun ana rokona in yi wani abu, bar kowa ya kyalcni, suka
kama harkonkinsu
Shu kanshi ango Mustapha, yana can cikin jama'a yana ta
hidimarsa, kamar ance daga kanki, sai na hango Mustapha da wasu
yan mata hudu, sai dariya yake yi masu, na tafc bakina, a zuciyata
nace, "dawa zalayi haka kana gida nan can ana sharholiya da 'yan
mala.
Amma kuma sai na kasa kawar da kaina daga kansu, ina cikin
kallansu naga duk ragowar ukun sun tafi, sun barshi tsaye da wata,
can naga ta bude jaka ta miko mashi yar karamar takarda, duk da ba
a kusa nike ba, amma na fahimci katin adreshine ta bashi.
Ina kallo dai naga yana waige-waige, da alama wani yake
nema, can sai naga ya kira daya daga cikin yaransa, sai naga ya
bude weta yar jaka ya mika wa wannan budurwa farin abu, hakan
ya tabba.ar mani shima nasa katin ya bata.
Wai anan take sai naji wani mugun bakin ciki ya taso mani a
zuciyata, shin wai me Mustapha ke nufi da baiwa budurwa
katinsa?," nan take haushin kaina ya dirar mani a zuciyata, na me
Уг ва г02. me yasa ua zuwan ya kamani dole ban taho da motata
ba.
Ma yaudart ya sanıi ya sameni, shine har ya fara hirar wata,
na mike na fice daga dakin taron hotcl din, na fita na samu tsakiyar
wasu bishiyoyi fulawa na zauna, na mayar da kaina na kife a
cinvavina. wai sai naji kamar zanyi kuka, na dago kaina nayi kwata.
Bae Ja 1sokyarda kaina na kifa a cinyata.
Hamida! Hamida!! Naji yana kira, ko ban daga kaina ba nasan
Mustapha ne, ke kirana, inaji yana tambayar mutane tare da cewa
daya daga cikin yaransa va je ya tambaya masu gadi ko sun ga na
Bike
Ina jinsa ya dawo yace masa masu gadi sunce ba wanda va
fita, ina ji yace duk su shiga cikin hotel din su nemoni, shi kuma zai
duba a harabar hotel din.
35
n
a
a
Γ
Kanshin turaransa da nike kauna sosai shi naji a
hancina,hakan yasa na daga kaina yana tsugune a gabana, "kin tayar
mani da hankali sosai, why," "saboda bana sonka bana son abinda
kayi mani,"ya taso ya zauna kusa dani, "nace zanyi maki