Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 8
kallan saman dakinsa, jin motsi na na fito ma, bai sa ya dago kanshi ba, har sai da na zo, na tsuguna gabanshi. "Gani" na fada a sanyaye, wannan maganar da nayi ita tasa ya juyo ya kalleni a sace, a tunanina, yana zaton har yanzu ba kaya a jikina, bai ce mani komai ba, sai dai shima gani nayi ya tashi zaune, ya rarrafo da gwagoyinsa, har gabana. Kanshi a sunkuyé ya fara magana, "ni nasan kaddara, ba zan zama jihili ba a bisa, abinda Allah ya tsara mani, Hamida ni nasan Allah ne ya kaddara mani auran Halimatu, saboda haka ba zanyi ja da ikon Allah ba zan auri Halimatu Hamida, Kuka na sa da karfina, ni kaina nasan murna ce, saboda sai na kama fadar, "nagodewa Allah ni ma yau na cika alkawarin dake kaina na gode Mustapha, na gode, Allah ya baka tukuicin alajanna 13 firdausi 12 "Ya isa! Ya isa!! Dan Allah Hamida ki jira ingama maganata tukuna, ya dago ya kalleni, "nasan nayi iya kokarina, akan in guje auran da kike sani inyi, amma gashi yau ya zamanto kin samu nasara a kaina ta hanyar da ban taba zatan zaki samu ba. Nayi bakin ciki kwarai da gaske, akan cewa bake zaki zamo matata ba, nasan kuma zan kasance cikinsa har abadan duniya, kenan har aranar da rayuwata zata zamo "the end" Hamida nasan ina sonki, so na tsakani da Allah, amma gashi yau dubarata ta kare ba yarda zanyi in zamo miji agareki. Yayi shiru, amma ki sani, ba zan taba son kawarki ba har abada, sanna abu na biyu, in munyi aure da kawarki kada ki kuskura ki zo gidana da ziyaça, sai dai in mutuwa nayi, in ba haka ba, duk ranar da kika shigo gidana, koda bana kasar, to da na dawo zan saki kawarki, wallahi saki uku. Wanda hakan zaiyi sanadiyyar mutuwar naki auran da tsiya, saboda haka, tun yanzu ki san dubarar yi ke da kawarki, ya dan sassauta mirya, Hamida ina neman alfarma a wajenki dan Allah." Nasan nayi rashin ki, amma don Allah alfarma da za kiyi mani, ki amince mani inyi sallamar ka:she da ke," "kamar yaya? Nafada da dan saurina, "kamar ki saki jiki dani muyi sallamar karshe dake" "ban gane ba har yanzu," "manufata ki amince mani in matso kusa da ke, jikina ya dan hadu da naki haduwar karshe," duk da nasan bakya sona, amma ni zaki taimakawa don Allah." "Wai yaushe kaji nace bani sonka, ni bana son kazafi, na dan yunkura zan tashi, sai naji yayi saurin roko hannuna, tare da mikewa tsaye shima, "maganata ta bata maki rai ne? kiyi hakuri ba da niyyar haka na fada maki ba." Duk da fiskata bata kallasa, amma jikina naji yana tausaya masa, ko dan yanayin da naji yana magana, tamkar wanda akayiwa mutuwa sabuwa. Hakan yasa hawayen idanuwana suka dinga fitowa da sauri da sauri, dab da jikina ya matso, "ranki baya so ko?" ya fada mani dai dai wuyana, nayi alamar zanyi gaba, sai naji ya karasa janyoni jikinsa ta bayana. In da yasa hanunsa daya ya runguma cikina, dayan hannun kuwa yana ga wuyana ya hada da kirjinsa, wuyansa na sama 13 kafadata, hawayen fiskarsa, na tsiyaya cikin wuyana ni kuwa dama tuni na riga na saki kuka mai tashin sauti, nasa hannuna na rike silin hannunsa. Bayan kamar minti goma ne na, kira sunansa, ko ban fada ba, na san mirya ta a sanyaye ta ce Mustapha, na danyi shiru kadan, zan tafi," maimakon inji ya sakeni, sai naji ya kara matseni jikinshi. Ni kaina ban san lokacin da na tura hannuna a gashin kansh ba, mai taushin gaske abinka da gashi ba irin namu ba, jinsa nayi yayi ajiyar zuciya, tare da juyowa muka fiskanci juna, yasa hannuwaya tallabi kumatuna, tare da hada gashina da nasa, "Hamida imiss you for ever," "zan tafi. Ina ganin tallabar da yayiwa kumatuna zuwa inda fiskata ta dagi sama nasa so yake ya hada bakina da nasa, haka yasa na girgiza kaina alamar a'a "please," yace mani, sai ma na same jikina nayi gaba, tare da daukar hijabina da take gefe daya. Har na kai kofar fita ta bAbban falo, sai naji yayi magana, "ki jira in rakaki mota mana," na tsaya har ya iso, ya karbi jakata da take hannuna. Ba wanda yayiwa wani magana a cikınmu, har muka je kofar fita daga gidan, bayan mun sako daga yar motar lifta mai kama da motar wasan yara, ta gidan wasan yara, (children's park) ba tare da yace in tsaya ba, naji yana yi mani magana. "Ya zakayi akai kaya gidan su Halimatu?, kinsa ban san gidansu ba," "kawo jakar in baka katin da zai kaika har gidansu, ni kuma yanzun in na tafi, zan biya ta gidansu in fada, cewa zasu je, da yamma ko banda yamma bane ba?". "da yammar ma yayi Hamida tunda kince haka," ina bude jaka sai naga dunkulin kudin engila" Pound stiling" na dago kai na da şauri na kalleshi, "bana son wata magana, ni ne na baki, nima gudunmawa tace, Allah ya baku zaman lafiya." "Yallabai." ya daga mani hannu, "in bakya so, ki yar ni ki bani katin kawai nace," na duba na dauko masa katin, "na gode," "ba komai, kigodewa Allah ba ni ba, bawansa, ya zaro hankici daga aljihunsa, "ki gyara fiskarki," na karba, tare da goge fiskata sosai. 14 Har get din gidan shi na biyu ya rakanı a motata sannan ya fita ta taga ya dan leko, I miss you, kawai ya fada ya ja baya, ban bashi amsa ba, na ja motata nayi gaba. Kayan kwalliyar cikin jakata su nayi fakin da motata gefen titi, na gyara fiskata su, sannan na tashi motata tare da kara kallan kaina ta madubin gaban direba naga fiskata fas, kamar bata sha kuka ba. Kai tsaye gida na nufa, ba tare da bata lokaci ba, na cewa mamana tayi wa momi waya cewa saurayin Halimatu yace yau da yamma zai turo bakin iyayensa domin gabatar da kansu, nayi mata bayanin cewa yanzu ya je gidan biki yake gaya mani haka, ba dubarar da banyi masa ba, amma ya ki saurarata, shine nace bari in rugo gida in fada. Amma yanzun zan je in sanarwa halimatun, sannan in koma gidan bikin, da murna mamana tace sai na dawo kafin in fita, sai da na bugawa safiyanu waya muka gaisa, a' nan ne nake ce masa, in yana da hali, ya sameni gidan su Halimatu wajan karfe uku na yamma saboda wata mahimmiyar magana da nike son nayi da shi, "dama mai neman kira, to ina ga ance sarki yana kiranka," da murnarsa yace, zai zo in saurareshi a lokacin, ina isa gidansu Halimatu, abin mamakin, sai na sameta da yaya Usman sunata hira harda tuntsirar dariya. Wani haushi ya kamani a take, da kyar ma na gaishe da yayan nace mata ta zo ina jiranta, sai ta koma in mun gama da kyar ta taso, wai ita kada abar yaya shi kadai. Bayan mun shiga dakinta ne, nake yi mata albishir da yau za'a kawo kayanta daga gidansu Mustapha har da murnata kamar zan tashi sama, amma wai sai naga tayi shiru, na dan dafata, Halimatu ya bakiyi murna ba abinda kike nema ya samu nan da sati biyu kina dakin Mustapha. "Hamida ni ba abinda zan iya cewa, face in ce Allah yayi maki sakaiyya da abinda yafi wanda kika yi mani, na gode, na gode, Allah ya saka maki da aljanna firdausi, na aikawarin da kikayi kokari kika cika mani, gashi kuma kin rike mani amanata na gode. Amma kuma, sai wani hanzari, Hamida, hanzarina kuwa shinc, tunda Yaya Usman ya dawo daga karatu, naji kuma zuciyata ta tashi 15 daga kan Mustapha, ta koma kan Usman, Hamida ba zakiyi mani afarma ki auri Mustapha ba?" Wani wawan duka na sakar mata a cinya, har wata irin kara ta saki mai karfin gaske, "in ma wasa kike to ki dawo sai ti, in ba haka ba, zamuyi tashin hankalin da bamu taba yinsa da ke ba, kuma ki sani, aure ke da Mustapha ba fashi, tunda ke kika riga kika firta kin a sonshi da farko. Ke da kinga irin walakanci da zubar da mutuncina da nayi da cin fiskar da akayi mani duk akanki, har ki fara fadar wannan maganar marar kyau haka," na kara harararta, "wallahi kin bani mamaki Halimatu, ban taba tunanin zaki wulakantani ba, ki ci fiskata ba kamar haka," "Me nayi maki kuma Hamida, wallahi ni da zuciya daya na fadi wannan maganar, kinga ke dama ba wani tsayayyan saurayi gareki ba, kinga sai kawai muce dama ke kikewa kanki kamfai ba wata ba, ke kunya kike ji ki fadi gaskiya a baya shi yasa kik. "Kinga! Kinga!! Bana son maganar yara, ni fa ba yarinya bace, shima kuma Mustapha haka, sannan ke baki isa ki sa ni yin abinda zai zubaar mani da mutuncina ba, kin dai sani da farko, kuma nayi maki, amma ina tabbatar maki yanzun baki isa ba. In gaya maki magana ta karshe, shine yanzun haka maganar nan taje kunnan Abbanki da momi, saboda haka nasan shirin karbar baki kawai zasuyi, in kuma kika kuskura kikayi musu ko wani ja akan abun nan, to zan kuwa tona maki asiri saboda haka, shawara ua ga ke, bani ba. Ni yanzu haka inada wanda zan aura, wanda ni ma tare da ke za'ayi komai, tare kuma za'a kaimu dakunan mazajenmu, kinga ritata ni, bacin munyi da bakona zaizo nan gidan, da gidama zan afi, amma yanzun zan je mu zauna da momi, ko nasamu wasu yan shawarwari game da auran da zamuyi. Ke kuma ta rage ga naki, ki koma wajan wanda ya hure maki kunne, marar hankali da ke kawai, daga mutum ya dawo daga turai, ba binkice ba komai sai kice shi zaki aura, wa ya sani ko ya dawo mana da kanjamau ko wani. 16 "Kinga Hamida ya isa haka nan, ya ishcki hakanan ki fita tun kafin raina ya kara bасі. "ya baci mana ina ruwana, ni kinsan iya bacin ran da na samu kafin in samo maki Mustapha, ranki ya fado don Allah in har kin isa ke sunanki Halimatus sa'adiya, sai in san kina 6acin rai. Ni yanzun har da wani abinda zai firgatani kuma, wanda ban gani ba, lokacin yi maki kamfai, har yau din nan sai da naga abinda yafi komai tayar da hankali, wallahi Halimatu baki da mutunci ko kadan," nayi tsoki nayi gabana kyaleta a daki zaune. Bayan mun gama gaisawa da momi ne na gaya mata yau suna da baki, nayi mata bayanin Mustapha dalla dalla, nan take momi ta mike, ta barni, sai dakin Abba ina zaune ko yunkurawar tashi banyi ba, mamana tayi sallama da daddy suka shigo Baki daya sashen Abba, suka shige, cikin kamar mintina arba'in da bakwai sai gasu sun fito gaba daya kafin karfe biyu na rana kuwa, gidansu Halimatu ya fara cika da jama'ar arziki. Karfe uku saura kwata safiyanu ya baiyana, bakinshi kuwa kamar anyi mashi albishir din zuwa makka aikin hajin ba zata, kamar yanda Halimatu da yaya Usman suka tashin tsiya daga kujerun zancensu, ni kuma haka muka dauki kujerun zuwa bayan gidansu Halimatu. A inda nike sanar dashi in ba takura ina son ya aiko da kayan auransa shima, zuwa gobe, saboda gida an takurani wai da Halimatu za'a hadamu ayi mana aure. Nan take ya hau murna, harda cewa in bashi izini ya aiko da su a yau shima da yamma, na nuna masa ya dai hakura sai gobe saboda gidanmu a yau ba kowa duk ana nan karbar kayan Halimatu. Yanda naje na samu Halimatu a kwance tana kukan dani nasan na rabuwa da Usman ne, nima haka na shiga imotata sai gida na haye nawa gadon na fara nawa kukan rabuwa da Mustapha, da auran da bansan sunan saba da zanyi. Ni dai nasan bani son sufiyanu, amma zuciyata ce ta amince mani da auranshi, wanda har karfe biya da minti goma tayi, sannan na daure na mike domin in gabatar da salah la'asar din da na kasa tashi inyi tunda na shigo. 17 *** *** Saura kwana biyu daurin aurammu, ni da Halimatu, wanda kullun sai munyi rigima da Halimatu akan auran da zatayi, korafin kuwa da ta faye yi mani shine na har yau bataga Mustapha ba, wani nata bai san Mustapha ba, ga fittitika anan ta zuwa, amma ba Mustapha a ciki. Wanda tun korafinta baya damuna, har ya zamo yau kam ya dameni, wanda hakan yasa na duba naga ta fini gaskiya, a baya tana ce mani ya aiko mata da sakon gaisuwa a takardu, da yan kayan amfani a ledoji, wai a gaya mata yayi tafiya zuwa indi'a domin gaya masu bakinsa ya taso. Amma gashi har yau saura kwana biyu, ba Mustapha, aiken ma ya daure kafar yisa, ni dama tun farko da ta fada mani, nasan ba wata tafiyar da yayi, koma yayi ta ba zata wuce kwana biyu ba, amma ragowar kwanakin yana garin nan. Bayan mun gama yin fada kace-kace da Halimatu, har da yan zage zagenmu, da saurinta ta fice ta bar gidan. mu, ni kuwa sai na dauki kanwaya na danna nabar gidan Mustapha. Sai da tayi kara ya kai sau biyar, tukuna aka dauka, wanda a farko nayi masa ne ta talho dinsa ta hannu, amma ba,a dauka ba, hakan yasa na juya zuwa ta cikin gidansa in ji ko yana kusa. "Waye ke magana, nan gidan Alhaji Mustapha Mahab ne," abinda wanda ya dauka ya fada kenan, "sanu ko," nace masa ya amsa da yauwa," "dan Allah Alhaji Mustapha nake son magana da 'shi," "Hajiya don Allah kiyi hakuri Yallabai ne yace kowa ya ke son magana da shi ace masa yayi hakuri sai bayan sati biyu. Amma don Allah kiyi hakuri ki bugo nan da kwana biyu, a lokacin sati biyun ta cika kenan, ina fatan ba zaki samu damuwa ba," "kai waye ke magana?" "Hajiya sunanan Abdulrashid", "au Abdul rashid ne, kace masa nice Hamida ke magana dashi." "Nan take ya canja murya zuwa ga ladabi, "sannu sannu madam rike yanzu zanyi mashi magana, Allah yasa ya saurareni, saboda yau kwananshi goma sha biyu a daki kwance, ya hana a ganshi, sai dai lokacin abinci ka wai yake bude kofarshi. Ina zuwa bari in gwada in gani," "bayan kamar minti hudu sai gashi ya dawo, "hello! Hello!! Madam kina kan layi?" "ina jinka 18 Abdulrashid," "wallahi madam yace nace koma waye ace ya bugo nan da kwana hudu," "ka gaya masa nice?," "e na gaya mashi, sai yace wai in wani abu kuke bukata ki fada in kawo maku yanzu." "Ka koma kace masa nace, magana ce kawai zanyi dashi, bama bukatar komai daga gareshi," "haka shima bayan yan mintina sai gashi ya dawo, "hallo madam," "yace ba zai iya sauraren ki ba, amma wai in maganar ta zama dole, ki baiwa kawarki Halimatu nambar wayar ta bugo masa, sai ki fadi mata maganar ta gaya mashi, bayan haka bai kara komai ba." Kaje ka ce mashi........" "don Allah madam kiyi hakuri wallahi yace in na kara zuwa kofar dakinsa bakin aikina, ni inaga wani abu ke damunsa, da zaki iya zuwa da kanki da yafi, mu kanmu abun yana damunku gashi yace kada a gayawa hajiya," "hi kenan na gode Abdulrashid, sai anjima." Wani bakin ciki ne ya taru a kahon zuciyata ya takareni, wai ni Mustapha zai wulakanta, kamar bani na hadashi da Halimatu ba, hannuwa biyu nasa na rabka tagumin bakin ciki, nayi kwafa nayi tsoki sunkai talatin a cikin mintuna ashirin da daya. Hakan naga ba zata taba sani in hrice ba, sai naga Mustapha ido da ido a yau ina haka ba, abu uku zan hadawa kaina a lokaci daya ga bakin cikin maganganun da Halimatu ta ke gaya mani, ga bakin ciki na Mustapha, ga auran da bazan iya cewa ga sunan sa ba, zanyiwa kaina shi. Na mike na yayimi hijabinta, da dan nakullin motata sai waje, mutanan da suka cika gidanmu yan biki sai magana suke yi mani da masu tsokanata, amma washe musu baki kawai nayi na wuce abina. Ba wani canji da ua gani a wajan yaran mustapha yanda suke mani a baya, yauma haka, hakana wucesu suma ina yake masu hakora. Sai da na kwankwasa takai goma, amma ko motsi banji anyi ba a falon Mustapha, bakin cikin haka yasa nayi ma kofar wani wawan duka, wanda na jirashi ya kai biyar ba tsayawa. Allah yasa fiskata gefe take kallo da nasha mari, saboda hannun Mustapha kawai na gani a baje bakin kofa, har ya dan taba wuyana "me ye haka kai kuma" "me kika zo yi ke kuma?," sai naga yana neman mayar da kofa ya rufe. 19 Nayi saurin sa hannuna a jikin inda za'a rufe kofar, amma sai Mustapha ya datsa kofar da hannuna a jiki, duk da kofar katako ce, amma bai hanani jin wani mugun zafi da radadi ba, Karar da na saka mai karfi ita tasa yayi saurin bude kofar, shima ya kara mirtsike mani yan yatsuna, cikin saurin da bai kai sakan ba na durkushe kasa nasa ihu ina waiyo Allah, tare da dura hannuna a kaina. Da rudewarsa ya iso ya kamani, "sannu innalillahi, mugani na fizge hannuna, "ni ka sakar mani hannu, bayan kana sane kayi mani haka sai na samu na mike ina yarfe hannuwana, ji nake tamkar in ciresu in zubar in huta, na nufi kofar komawa daga inda na fito. Amma Mustapha ya biyoni a baya, "Hamida Hamida, kada kiyi mani haka tsaya dan Allah in ga hannunki ko hankalina ya kwanta" "ba wani mayudari, dama nasan a baya yaudarata kaso kayi Allah ne ya bani sa'ar gane ka, gashi yanzu tun ba'ayi nisa ba, na gane manufarka. Gabana ya tarayye, "dan Allah ki tsaya inyi maki bayanin" bana son wani bayaninka, ni dama ba wani abu ya kawoni ba, matarkace take ta kukan baka zuwa wajanta, kuma ba wanda ya taba ganinka a danginta, in kaga dama kaje in baka je ba kuma dan kanka, nayi gaba abina. Har na tashi motata yana tayi mani magiya ko kara kallan inda yake banyi ba, naja motata. Ina isa gida na samu sufiyanu zaune abisa akujera da wasu kawayenmu suna ta hira abisu, yana hangoni gaba dayan hankalinsa ya dawo kaina, amma na rasa yarda zanyi inyi masa fara'a a fiskata ganin haka da sufiyanu yayi yasa ya taso da sauri ya taryeni. "Me! Me! Me yafaru ne na ganki haka?" da kyar na danyi murmushi na nuna mashi hannuna na hagu, wanda yanyatsun sun kumbura sosai, "yayi saurin rike mani hannu, hankalinsa a tashe,' ya akayi haka ta faru? Me ya sameki ne haka?". Zame hannuna nayi tare da guntun murmushina," motace ta datse mani 'yan yatsu, a gidansu Halimatu," "muje in kaiki asibiti kilan ma kin samu karaya ayatsun, "ka barshi, ba komai zai warke, amma yanzun dama gidan kamu zanje su duba mani ko na samu targade amma bana zaton karaya." 20 3 1 "Sannu yacce dani," na danyi mashi kallon naji dadin tausayin da yanuna a gabana, "kaji safiyanu kamar wacce ta datse yanyatsun gaba daya," "ke wannan fa bAbban ciwo ne, gani kike kamar wasa sai naga ya waiwaiga, sannan ya kara matsowa dab dani har da rage sautin tashin maganarsa. "Ba ciwon wasa bane ba fa, zai iya hanaki cın amarcinki fa ya janyo mani hutun dole," na harareshi nayi yar tafiya ina murmushi kunya, "kai wallahi. Ya biyoni, "karya nayi? "ni ba ruwana, "tare da kara hararrarshi, "zan biyaki hararra nan taki bayu ba sai nan da kwana uku," nayi saurin cigaba zuwa shigewa gida, ina mai alamun jin kunyarsa, "Hamida Hamida tsaya zan biyoki har cikin gidan kinsan dai nima gidan mu ne" "is left for you" "bata rage garenmi ba amma zai ragegareki nan gaba kadan ban tsaya bashi amsa ba, na shigo cikin gida da saurina ga kunya duk da rufeni, saboda mutane da ke kallamu. Na danji dadin yanda sufiyanu yayi mani wanda haka ya dan lafar mani da zuciyata, hakan yasa nima nayi wanka na na sake kayan jikina, domin kawai ya gani yaji dadi a zuciyarsa. Tabbas nayi kwaliya mai kyan gaske da boyel mai ruwan kalar kayan sojoji faudata na shafe fiskata da jita, wanda kwallin da nasa, shi ya boye jan da idona yayi na kuka, jan-jambaki mai turin bakibaki, shi na shafa a la66ana. Na kawo man gashi na shafe gashina da yasha kunan shampoo na taję shi na rabashi biyu na tibke, sarkace ta dayimon din ingila na sa a wiyana"diamond" na kawo zobinanta biyu nasa a hannina, banda kunnena da nasa dan kunnata. Gajerun takalmane a kafata, mai ruwan hoda shima mayafin dana yafa kalar takalimin kafatane, daurin dankwalin da anyi kuwa yadan langwaba kadan, yafa mayafin kanshi sai da nayi shi yar da zai birge duk wani wanda yake kallona, ba ma sufiyanu kawai ba, wanda akayi kwalliyar dominsa. A karkace ake yafashi, baiyana yafa mayafinnan, sai wanda ya gani da idonshi ni Hamida, tararan fancy, na fesa a jikina irin turaranda sai an matso kusa dani, za'aji kanshinsa. 21 Tun daga hangoni sufiyanu ya mike tsaye, daga kujerar da yake zaune, ba abinda idansa keyi, sai kallona, wanda naso yanga da 'yan yatsun hanuna, amma ciwon jikinsu shi va hanani sakin hannuna na haggu ya wataya kamar yarda na so. Kallan da sufiyanu ke yi mani shi yasa kawayena da ke zaune suna dabe mashi kewa suka waiga gaba dayansu, kamar sun hada baki sukayi shewar nan ta yan makaranta, tare da cewa kin fito kinyi kyau, ki iso ango ya biya ki kudin kwalliyar ki." Murmushi kawai nake masu, ina isowa sufiyanu ya kauce daga inda yake tsaye, "sai naji yace, "sanu ga kujera," manufarsa kujerar da yake zaune zan zauna, nayi mashi kallon da zai sa ya kara sona a zuciyarshi, nace masa, "in baka zauna ba zan zauna a kasa." יי" To tsaya! Tsaya!! Ina zuwa in dauko maki wata kujerar, "meye aikina ni kuma?," "ki zauna in ta kallanki" gaba daya muka sa dariya har da su, Zulahatu, itace taje ta dauko mani kujerar zama, tace ango na hutar da kai," "na gode hajiya Zulahatu, kin biya kema.' Na zauna muka cigaba da hira kafin karfe hudu na yamma, mu fara shirin tafiya. A Mun samu kamar mintuna arba'in da biyu da zama hirarmu, sai mai gadi ya zo yace ana sallama da ni, a wajan get, na tambayeshi ko waye, sai yace wannan mai zuwa dan baturan nan, Yana fadar haka, na gane Mustapha ne, take anan na tambayi kaina me Mustapha yazo yi kuma? Hakan yasa na mayar da kallona ga yan yatsun hannuna da na shafesu da Lanis bon ya karasa gutsire mani su ke nan?, na fada a zuciyata, sannan na kalli angona. "Angon Halimatu ne zanje don Allah in ji ko lafiya, ya dan daure fiska, "kada ki dade ina jira" "yanzu zan dawo Zulahatu ga ajiyar angona nan a hannun ki" na mike na hau taki daya bayan daya na nufi get. Ina fita get na faure fiskata har da kashe ido daya dan tsananin inyi masa kallan wulakanci, ba sallama ba komai na hau magana, "me ya kawoka gidanmu, ko ka zonan ma ka karasa gutsure mani ya yatsina, wallahi baka isa ba, ko ka tafi ko insa yaran unguwa su jefe mani kai." Ya dago kansa da ke sunkuye a jikin sitiyarin motarsa, "kiyi hakuri dan Allah, dama zuwa nayi ki rakani wajan 22 C Halimatu saboda zuciyarki tayi maki sanyi, na san yanzu kin dauki fishi dani "Sai na rakaka gidansu Halımatu, to kada Allah yasa kaje, ni dai tunda angona na kusa dani, alhamdulillahi ku kuwa kujecan ku karata ni baruwana kaga tafiyata wajan angona, saboda minti biyu ya "Don Allah ki saurareni ba wani abu yasa na biyo ta nan ba, saboda kece kika hadamu da ita, kamata yayi kuwa ranar haduwar mu ido da ido da ita, ace shima ke kika gabatar dani a wajanta, kiyi mani arzikin haka, in kikayi hakuri saura kwana bai fi hudu ba in bar maku kasar gaba daya." "Sai dai kaje ka tambayi angona inya amince, saboda bana son bata masa rai," "sai ni ki ke son batawa rai ko Hamida?", ban tsaya bashi amsar komai ba nayi gaba abina. Ko zama banyi ba, na hango Mustapha ya shigo get din gidan mu, ban nuna na ganshi ba na zauna kujerata, har da canja salo zama, da canja kallo da nikewa sufiyanu, ammata wutsiyar idona ina kallon Mustapha, tare da tunanin Allah yasa a gama lafiya. Da fara'ar sa suka gaisa da sufiyanu, shima haka angon sufiyanu, sannan na dago kai nace "Alhaji, wannan shine Alhaji Mustapha muhab angon Halimatu, Yallaßai wannan shine sufiyanu angona," ta wutsiyar ido Mustapha ya harareni wanda nasan ba wanda zai gane hararta yayi, sai ni. "Dama cewa tayi kuna tare shine na shigo mu gaisa, tare da tambayar ka bani aronta zamuje mu hadu da Halimatu domin yin wasu shirye shiryen da dole sai mmu uku zamu yi su, saboda lokutan baya nayi tafiya shi yasa, jiya na dawo". "Ba damuwa gatanan ku tafi," "a'a ka tashi mu tafi tare da kai, kaima ai anyi wasu shirye shiryen da kai ko? Na cewa sufiyanu, Mustapha ya kara sakar mani wata hararar karkashin ido, nima take na rama. a "Ke dai ki tafi, ina nan ina jiranki, kada ki zauna kinsan dai yanzu ina bukatar ki kusa dani, "you know "to shikenan, amma da mun tafi tare, kasan nima banajin dadin barinka kai kadai." "Gasu Zulahatu da yasira da sauransu, ai kwa tayani zama ko? Suka amsa da E" "shikenan amma Zulahatu ga amanar agona nan, 23 kada ki yarda wani abu ya 6ata masa rai, in lokacin salla a zahar ya karasa ki shiga gida ki dauko maku bAbbar dadduma, yanzu zan dawo kada ki bar maini shi da yunwa," "kai wannan dokoki naki Hamida sunyi yawa, ko dai ki saka angon naki aga ba ku tafi tare, aka danyi dariya sannan na mike tsaye. Nasan Mustapha na kallona, shi yasa na canja kallo da magana, har da durkusawa gaban sufiyanu, "sai na dawo kayi mani addu'a sai in tafi, ya danyi sumi-sumi da baki, sai ya to fa mani a goshi, ya sunkuyo kadan, "a dawo lafiya," nayi murmushi, "Allah yasa," "kar ki zauna da yunwa fa," na daga masa kai alamar to. Mustapha kuwa sai kallonmu kawai yakeyi

Chapter 2 of 8