dauketa, tunanin kada in barshi yayi nisa ya hanani yin salla
isha cikin lokaci, yasa na daure, sai dai dan gyangyadawa da na
danyi a kwance
Wajan takwas da rabine mamana ta shigo dakin nawa, a
lokacin na danyi nisa kadan a barci na maganarta ce ta tasheni,"
"Hamida wai lafiya kuwa yau?" "mama bana jin dadi so sai, marata
ce ke yi mani ciwo," "amma “а ki ka bar Mustapha ya fita baki gaya
mashi ya kai ki asibitiba,."
Mamaki da faduwar gaba suka saukar mani a lokacin daya,
amma gudun kada mamana ta gane cewa wani abu ya hadani da shi,
shi yasa na ki nunawa a fili, sai dai na wanyance da mayar mata da
amsar tanbayarta kawai
"Mıma gani nayi bata yi mani ciwo sosai shi yasa", "amma
kika ce mashi ya tafi ke barci zaki yi?" "mama"..... a"....." "mama me
maganar me zaki shirya mani yanzo, dama baki san a kuma yanzu
kuke ni ke da ke, wai ke ba, kin zo gidan ku shine in mijinki ya zo
sai ki koreshi.
Baki isa ba, mu bamun kawoki gidan nan ba domin mu kashe
maki aure ba, bari Alhaji ya dawo, in shaida masa duk irin
abubuwan da ki kewa mijinki, gobe ki koma gidan mijinki tunda mu
zaki mayar mutanan banza, mutane na tsaye a kanki kullum a tafe
ba shi ba ba mahaifiyarsa ba, a bokanan arziki kullu cike da falo,
amma zaki zubar mana da mutuncin mu a idon su, baki isa ba
wallahi," ta fice a fusace abinta.
Me zanyi daga kwance? alajabi, ko mamaki, ko kuwa in yi
tunanin ya akayi?" sannan yaushe Mustapha ke zuwa ina korar shi,
nayi-kwafa daga kwance kenan Mustapha rijiya yayi mani na fada,
ko kuwa gadar zare ya kulla mani na je na taka na fada ciki?, zan
rama, ita kadai na fada na mayar da kaina na kwanta abina.
59
Yunwace ta tasheni, tun karfe uku na darc, sai gani ina bude
kwanonin sanyayyan abincina, a karshe sai gani darshan ina ta
lomar abincin da nayi wa yaji tunda fuminsa, dan ma dan arzikina
daya a cikin filas din zuba abinci yake da na ci dumamman firji dan
sanyi.
Karfe shidda da kwata na safe na zsme na kwanta a kan abi
sallata, bayan na idar da lazimi na, barci ne mai dadin gaske y
ratsa idanuwana, na mika hannuna na janyi filan saman gadona, nа
kwanta da shi sai barci
Kamar ance mani bude idanuwanki, ina kuwa budewa sai naga
Mustapha a tsugune gabana ya kura mani idanuwa, nayi wani irin
saurin tashin da har sai da kuguna ya amsa, amma duk sai ya zama
a banza saboda Miustapha har ya fice daga dakin
Abinka da mai ciki, har yar jin yar sakan takwas nayi, kafin in
yunkura in tashi amma ina isa falo sai naga babu alamar sa, amma
hakan bai hanani binsa har kofar gida ba, amma kyalin motarsa
kawai na hango ta fita get.
Tsayuwa nayi turus da katan cikina a gabana, saboda mamakın
da lamarin Mustapha ke bani, wai ni Mustapha ke gudu, kamar wata
wacce ta kamo da ciwon haukan, na dare daya, na juyo jikina
sanyaye, saboda yanzun al'amarin yafi karfina.
a
Ban san mamana na falo ba saboda kaina a sunkuye yake sai
da naji fadanta na ratsa mani kwanyar kaina" "yanzu na ganewa
idanuwana, munafukar Allah, har da wani fita wai ace taje rakiyar
shi.
Sai dai yace mani in kwance kike a kyale ki ba zai shiga ba, ni
na tilasta mashi gashi na janya mashi korar kare," "wallahi
mama........" "wallahi da me, ki rufe mani baki mara kunya kawai
ta wuce ta barni a tsaye.
Gai da na bita da kallo sannan idanuwa na suka kai ga agogon
baugaran bangon da tabi, sai naga karfe tara saura minti biyu, na
wuce daki na zauna gefan gado
Tunanina daya shine, Mustapha ya gane na san bai kwana a
gida, shine ya bi ta wannan hanyar domin ya kulla mani sharrin da
zan koma gidan sa a dole, zai kwashi kashinshi a hannu in dan ni
Hamida Haruna masari. 60
Duk abinda ke faruwa nan ba wanda nayiwa kuka, sai yanzu
shima fadan da daddy na ya dirarmani da shine tun dawowarsa, bani
da dirar yin wata gardama, ko ince bansan anyi ba, saboda in nayi
haka na karyata mamata a gaban daddy kenan.
A lokacin ya bugawa Mustapha waya yace ya zo ya tafi da ni
gidanshi a yanzu ni kuwa ganin yarda ran daddy yabaci yasa na
dinga kuka ina bashi hakurin ya gafarceni ba zan kuma yin haka ba,
ban kuwa tashi ba, sai da naji iyayena sun gafarta mani, duk da
nasan bani da wani laifi akan zargin da suke yi mani na korar
mijina
Daddy ne yace in je in shirya kayan dana san ina amfani da
shi, ragowar in barsu, in an shirya su daga baya a kawo, nace to
kawai saboda bani da yarda zanyi sai yanda su kayi da ni.
Ina zaune akan sallayata na idar da salla isha, sai ga maustapha
ya shigo tare da sallamar sa, na daga kaina na kalleshi, na mayar da
kaina na sunkuyar, saboda ni ban san abinda zance mashi ba yanzu
in kara laifi.
Zaunawa yayi a daya daga cikin kujerun dakin," "kin shirya
kayan?" sh'ma shirun dai nayi ina ganin gani yayi ba zanyi rnashi
magana ba, sai naga ya tashi ya fara daukar kayan da na shirya a
gefen,
*** ***
Yau kwana uku da komawata gidan Mustapha, amma bazan
iya cewa ga takamai man wajan da yake kwana ba, saboda rabona
da shi tun a mota. Har yanzu ban sa shi a idanuwana ba, saboda ina
sashena na kulle kaina a ciki.
Abinci kuwa sai dai in sameshi a tebir din sashena in har na
bude falon, wannan kuma nasan aikin mai dafa abincin gidan
Mustapha ne.
Wanda na san duk karfe goma na safe, sai ya shigo yayi mani
share share da goge goge da sauran anyukan sahsena, haka ni kan
bar dakin nawa da dare kamar wajan bakwai da rabi, saboda kawo
mani abinci. 61
Ikon Allah ranar cikon na kwana hudu, na bude daki domin
kawo mani abinci dare kamar yarda na saba na koma falo na zauna
ina jiran ya shigo ya kawo sai kawai naga Mustapha ya shigo ya
zauna shima yayi shiru.
Ba abinda nace masa, shima kuwa haka sai "Daniel" ya shigo
da kayan abinci a hannunsa, ina kallo ya shirya tebir din ya fice.
Ban tsaya jiran komai ba, naje na ci abinci na, na shige dakina na
mayar na kulle.
Farkawar da zanyi sai najini kwance jikin wani abu kamar
mutum, salatin annabi (SAW) abakina na tashi zaune a firgice na
kunna fitila gefan gadona, Mustapha na gani kwance a gadona, sai wani murmurza idanuwa yake na nuna alamar farkawa daga barci yayi.
"Amma ka cuceni Mustapha da ka hafa mani jikina da naka," "Hamidi nine fa," "ko kai ne me zai hana in ki kyamarka "(kyankyami)""kyamafa Hamida", "kwarai saboda kasan dai ni
jikina jikin mutunci ne, me zai kai ka ka hada jikina da jikin da ya saba chakada da na 'ya'yan iska."
"Yayi murmushi daga kwance in da yako, "Hamida kenan, in kinyi wani abin wani lokutan kikan bani dariyar da take sakani
mamaki, saboda a tunani na kamata yayi ace tun kafin ki aureni ya kamata kiyi bincike akan ni ko waye, amma sai kika makaro, amma
wani lokacin kuma sai inyi tunanin aikin san ni ko waye tun kafin ki shigo gidana.
Ma'ana tun kafin ki shigo gidana nasan kai san ni dama can mai hada jiki da 'yayan iskane, amma kuma sai kika bani mamaki da kika yarda tun farko na hada jiki da ke har kika samar mani bebi, alhalin kinsan halaiyata.
Samunki yasa na dan lafa kadan, amma cikin yan kwankin nan da kika yankar mani catin konnawa ga harkata, shiyasa na koma ruwa tsindim har ma suka janyeni ina kwana wajansu domin tAbbatar sun gamsar dani....."
"Ciki kakeyi wa ta kama? To kaje ka karbo abina ka a waja
karuwanka
likita, amma ni nayi imanin ba zan haifeshi ba, sai kaje ka samu can su haifo maka 'ya'ya ba dai ni ba
62
"ni ba na bin karuwa, ki sani yammatane danyu ake kawo
ma
fitilar gefan gado kawai naji a hannuna ni kuwa saboda 6acin
rai ban san lokacin da na jefa mashi ita ba a fiska da kanshi, cikin
sakan uku, sai jini ya fara fita jikin fiskarshi, ya dago kai ya kalleni
da fiskar da jini ya fara yiwa wanka, yayi murmushi ya sauka ya
fice daga dakin nawa.
Jikina naji yayi sanyi bayan fitarsa, amma a zuciyata na zancan
wata nadama, haka da na sami zuciyata shi ya kara bani kwarin
gwiwa da inyi kwanciyata, sakan uku ban kara ba, na kashe fitila ta
nayi kwanciyata,
Hayaniya naji tayi yawa a cikin gidan mu haka yasa na lalubi
abin kunna fitila na kunna domin inga ko karfe nawa, karfe uku da
asirin da hudu na dare, atake nayiwa kaina tambayar ko lafiya?.
Ban tsaya jiran amsa ba, na mike na daura zani, na dauki
hijabin sallata, na rufa domin fita in ganewa idanuwana abinda
akewa hayaniya a cikin dare kamar haka.
Ina isa sashen Mustapha tun a bAbban falo na ga yaransa, suna
ganina suka kama mika mani gaisuwa da jajan ya mai jiki, na bisu
da cewa da sauki kawai na shige ciki.
A falon sa abdurashid ne da " Daniel" suna yi masa sannu, ina
shiga suma suka juyo kaina suna yi mani sannu da mai jiki, na amsa
masu suma, anan Abdulrashid ya ke gaya mani wai da suka je
asibiti har gilashi aka cire mashi a goshinsa, na dan nuna hankalina
ya tashi a gaban su, amma suna fita na kalleshi sama da kasa na
tabe baki.
"In dai mutum sunansa mayaudari kadan ma ya fara gani,
cikın da kake takama da shi kuma, sunansa matacce, yan zun kuma
sai kaje ka kira 'yammatan, karuwan naka su zo suyi jinyar ka," na
juya na tafiya ta, ina jinsa ya biyoni yana yi mani magana, amma ko
waigoshi banyi ba, har sai da muka shigo falona. dakina Ganinshi har falona, yasa na yi saurin shigewa na
mayar na kulle, irin kalamanda yake fada tsaye a bakin kofata, su
ka fara sa zuciyata ta fara karaya, amma kuma duk da haka na kasa
jin zan iya bude mashi kofa ta. 63
Shirun da naji yayi shi ya baiwa zuciyata ko ya gaii va hakura,
hakan yasa ni ma na kashc fitila ta nayi kwanciyata.
Abinka da mai ciki sai barci, ban tashi farkawa ba sai bakwai
harda minti uku na safe, subahanallahi na fada daga bude
idanuwana, saboda ganin gari ya wayc ba sauran zancan sallah
asuba, bakin ciki ya dirar mani a zuciyata, saboda na san Mustapha
ya janyo mani na rasa sallah asuba mai lada da falala.
Rarfe tara saura asirin da daya na kammala shiryawa tsab, a dai
dai lokacin kuma na bude dakina domin isa falona in karya
kumallo.
Ba wanda idanuwana suka gani sai Mustapha kwance a
tsakiyar kafet din falona, ba abinda zance Mustapha zai iya gani
saboda ganin yarda fiskarsa ta kumbura a rude na isa kusa da shi da
niyyar kamashi, amma a take sai zuciyata ta tunano mani
maganganun 'yamatan karuwansa da yayi mani a daran jiya, sai
kawai naja da baya
"Me ya kawoka daki na?" "dan Allah Hamida ki taimaka mani
bana ganin komai wallahi," kishi da haushinsa su suka danne dan
tausayin nasa dana fara ji, "kıki tafiya can wajan karuwan
yammatan naka suyi jinyarka?"
"Don Allah ki daina hadani da karuwai," "ya fada cikin
sansanyar mirya, "Karya nayi maka? kai da bakinka ka fada haka"
"naji na dauki duk wani laifi da kuke tuhumata da shi, amma fa a
yanzu kafin in sami sauki, in har na samu sauki zan iyayi maki
cikakken bayanin harki gane cewa ba gaskiyar magana na fada
maki ba.
Yanzun dai don darajar iyayenmu, da girman Allah ki taimaka
mani saboda Allah, inna sami lafiyata sai inyi maki
bayani ""ni bana son wani bayani naka can, to ma wai
bayanin me zaka yi mani in dauka, alhalin kai da bakinka ka fada
mani wannan saboda haka yanzu kayi kokari ka samu mai taimaka
maka, ka samu lafiyarka.
Karbo in kuwa ka warke, sai ka sa yaranka su fara neman
maka asibitin da zaka je ka auko danka ko 'yar ka, inma tayi ka
samu, duk dai kasan naka ne," na juya abina na tafi zuwa cikin daki.
64
Na samu sama da mintuna goma, ina zaune bakin kujerar da ke
dakina ganinsa nayi ya tashi yana laliban hanyar fita kamar
makaho, kai tsaye kuwa ya nufi bango ya kai wani mugun karon da
ya sa na tashi a firgice, ina kiran "innalillahi" wanda dawowa da yayi da baya ya fadı, tare da kara daka kwaryar kansa da kasa haka
ni kuma ya yi dai dai da isa da gudu da nayi na tsuguna na tallabeshi.
A take naji na baiwa kaina haushi, da kara tsanar zuciya irin
tawa, hakan yasa, na kamashi da sauri zuwa gadona, wanda shi
kuma ko magana ya kasayi na kuwa san duk zafin buguwa ne da yayi.
Sai da na barshi ya sami wajan mintina biyar yana kwance ni kuma ina rikeda hanunsa, sannan na kamashi zuwa ban daki domin
wanke baki, sai ga baki da kyar yake daguwa saboda kumbura da yayi haka da na gani yasa na tarvi ruwan a dumi a hitar ruwan zafi
ta saman bandaki na.
Ba tare da na fita neman abın gasa masa ba, kawai na cire
dankwalin kaina na tsoma shi a ruwa, dan rirrike hannuna alamar
yana jin zafi, shi yasa na karajin zuciyata ta karaya, sai hawaye,
wanda nasan ba zai gansu ba, tunda saman idanuwansa duk a
kumbure suke
Ganin haka yasa na taimaka masa yayi wanka cikin bahon
wanka da na cika da ruwan mai dumi sosai, domin ya samu karfin
jikinsa.
Da kyar na samu ya sha ruwan shayı, shıma sai da na hada da
magiyar tukuna amma ina gama bashi a take sai ya kama rawar
sanyi zazza6l, da hanzarina na ware bargo rufar da ke saman
gadona na rufa masa,
Na mike da nufin in nemo Abdulrashid domin ya je ya dauko
likita, sai naji sallamar maama, da yar rudewata na mike na taryota
ina cewa shigo ki gani maama.
Amma dan karfin hali irin na Mustapha sai da ya nemi tashi
zaune, itace ma tace, a'a ya kwanta anan take cewa wai Abdulrashid
ne yayi mata waya yanzu ba da dadewa ba, yace wai gilashine ya
fado maka a bandaki da daran jiya.
65
Maimakon inji ta kara tarairayar dan nata, sai ma naji ta hau yi masa fada, "dan shirme irin naka, ya za'ayi ka tafi asibiti cikin dare ba tare da samin matarka ba, ko so kake yaran naka su rainata, "Hajiya lokacin ta na barci shi yasa.
Duk da haka ai lalurace sai ka tashe ta kamun ka tafi asibitin,
yanzun da ta farka cikin dare fa,""wai Hajiya duk Abdulrashid din
ne ya gaya maki haka?," "a'a nice na tambaye shi, a tawa fahimtar
ne na gane, saboda bin amsar da yake bani" "na daina to maama kiyi hakuri, dama ni ganin duka yaushe ta dawo gashi ba'a san
yawa tashe hankali shi yasa ban tashe ta ba, amma na daina maama kiyi hakuri kema.
"Yanzu da baki dawo ba ya samu wannan ciwon da yaya? Koda yake dama da ba kya nan can. ." Sallamar Aina'u ita
ta katsi magana maama ta ajiye kayan hannunata ta durkusa har kasa ta gaishe da maama, sannan ta gaishe da Mustapha wanda ke nade cikin bargo yana ta rawar sanyi.
A nan tace ai tare su ke da su daddy da mamana, Hajiya
maama, ita ta tashi ta fita wajansu, wanda nasan suna bAbban falo
ne na farko, tana fita Aina'u ta kıra matsowa tayi wa Mustapha sanni.
Har dakina su daddy suka shigo suka duba Mustapha, abinka
ga manya ko miniti sha biyar ba su hada ba, suka ce su sun juya, ni kuwa rakiya har kofar bAbban falo da zumbuleliyar hijabita wai ni kada daddy na yaga tirtsetsen cikina.
Saboda ni ko zaman da nayi a gida daddy na ba zai iya cewa
ya taba ganin cikina ba tunda ba kullum cikin manayan riguna nike ga zumbuleliyar hijabita.
Ina dawowa daki, su Mustapha kayan kwadayi sai ceewa yayi wai meye firdausi ta shigo dashi a kwano, da ledoji, nayi murmushi nace masa ni ma ban buda na gani ba.
A dole ya sani na bude kayan ledojin nan kayan shaye shaye ne kala-kala, irin na kwali da na gwangwani sauran tarkace kala- kala na ci shima, a kwano kuwa dambun naman kazane. Amma saboda kwadayi irin na Mustapha cewa yayi yana сі, shi da likita ya hana tauna abinci ko ma wane iri ne, na dan 66
harareshi, sannan nace masa, "da wane bakin zaka ci kana sane dai
kace likita ya hanaka cin komai sai mai ruwa."
Buda mani baki yayi wai shi dai zaici, kamar dai yarda
sakatattun yaran nan ke yi, dariya ma ya bani, saboda ganin yarda
fiskarsa ta Kara kumburewa.
"Kayi hakuri in saka maka su a firij in kaji sauki kaci," "na
kiya ni dai ki tauna mani, "in tauna maka? Wallahi Yallabai baka
gajiya da abin dariya, to in na tauna maka kuma in fito dashi in saka
maka a baki ko yaya?".
"Ki dinga bani da bakinki," "na taße baki, "ba dai Hamida ba,
kaje ka gama hada baki da yammatan waje sannan ni kuma yanzun
in hada da kai, Allah.
"Don girman Allah ki daina yin irin wadannan maganganun,
na gaya maki cewa, yanzun duk abinda zakiyi mani kiyi mani shi
don Allah kawai, in har da rabon in tashi, to in na tashi daga
kwanciyar rashin lafiyata, zan gaya maki gaskiyar komai.
Ina cikin bashi, sai jama'a suka fara sallama, dole tasa na sa
Abdulrashid ya kamashi zuwa bAbban falo, tare da fito mashi da
kztifa a falon saboda yawan jama'a 'yan dubiyar mai jiki.
Kwana shidda da yin haka, amma kullum gidan mu cike yake
da jama'a yan sannu da jiki, jiki kam yayi sauki, saboda yanzun
yana gani sosai, amma farin dinkunana fiskarshi ne fasu warke ba.
A wannan rana, ya samu yayi wanka ya fito su ni kuma nayi
dan goho da tirtsetsen cikina ina dan shafa masa mai, da tattausa
masa jikinsa, sai Abdulrashid yayi sallama, daga kan da zanyi sai
naganshi da wata kyakyawar mata tana binsa a baya
Riga da siket ne irin dinkin mu na hausawa watau atamfa
kenan, amma sufar jikintace ta nuna mani cewa ita kabilace," "nayi
sauri na ja mayafin rufa da ke gefena, na rufawa Mustapha a jiki,
fiskata kuwa tani ta canja daga yar fara'ar da nike zuwa shan kunu,
na kanwa ma kuwa.
Bakinta a washe, da irin munafikin ladabin nan nasu na yare,
ta tsuguna har kasa ta gaishemu, Mustapha kuwa kamar wanda aka.
Watsawa ruwan kankara, saboda tashin da yayi da sauri ya zauna
tare da washe mata baki yana amsa gaisuwarta.
67
Harara na sakar masa, haka yasa naga yayi saurin jan mayafin
da na rufa masa ya kara gyara rufar jikinsa, gudun kada ta tafi dani
a bakinta, gashi tana ta rabka mani madam, yasa na daure na amsa
mata gaisuwarta ciki ciki.
Abdulrashid ne ya jere mata gaban ta da dan kayan sha, zuwa
na motsa baki a saman wani dan tebir da ya janyo gabanta, tukuna
naga yayi waje shi kuma.
Irin kallan nan na kasan ido shi Mustapha yayi mani a yau,
kallan da na dan dauki lokaci ba'ayi mani shi ba, raina ya kara yi
mani kuna matuka, har nayi niyyar tashi in tafi, sai naji ya fara yi
mani magana.
"Hamida wannan itace 'Abegail, ma aikaciyace
maaikatanrmu, da turanci naji yace mata wai nice matarshi
a
ta kara cemani sannu kamar nice mabani da lafiya, ina jinsu
suka dinga hira abinsu, har ta dan tsawon mintuna kamar sha biyar,
sannan naji ta kara magana cikin harshen turanci "I am going wai
manufa zata tafi.
"Au nama manta ban tambayeki su "Eno" ba", "sunan lafiya,
sai "week End zan kawosu su dubaka insha allahu," "Allah ya kamu
naji yace mata sannan ta tashi tayi mana sallama, har da sunkuyarta
kamar zatayi mana sujada, ni kuwa a dole na washe mata bakin
borin kunya, balle da naji yace mata ta gaishe da mai gidanta,
kafa yasa ya dan tureni, "su Hamida kishi", "wai ba dole ba, ai
nayi zaton ire iren 'yanmatan naka ne suka ga kwana biyu basu
ganka ba, shine suka biyo bayanka," "kina bani mamaki,"
"mamakin me? Kai ka fada da bakin ka ko kana.
Sallamar su zulaiha ita ta tsayar mana da magana ni da
Yallabai, a take Yallabai ya daure fiska ganin sufiyanu ya shiga ni
kuwa a kunyace na mike da katan cikina na kawo masu dan lemun
kurbawa.
In ajiyewa gaban su, sufiyanu ya fara fada fada shawara, shawara, "ki bi a hankali kada ki fadi kike tafiya da sauri haka, wai
ina masu aikin ne, gaskiya ya kamata yallaba ka sama mata mai tafiyar da gidan nan kafin ta haihu, kalle yanda take fa, sam ba zan
iya ba, zulaihatu tuni ta daina irin wannan "of and down din."
68
nLaifin wa?, ka tambayeta malam sufiyanu, ita tace ba tasan
mai aiki, ko ince masu aiki mata kasan dai zan iya ajiye mata
ma'aikata dari kullum in har ta bukaci haka."
Jin magana na neman yin zafi yasa nayi saurin katsi ta da
magana su Halimatu, hakan yasa naga Mustapha ya sunkuyar da kai
da gani ranshi a bace yake, ana haka ikon Allah ya jefo mana su
Halimatu da yaya Usman. Haka yasa falon yayi dadin hira.
***
Sai da na samu sati uku ina jiyar Yallabai, amma, yanzun da
ganinshi kasan ya warke sumul, ko tabo ma babu a fiskarsa, sai dai
dan kofar jan da bai saki fiskar bany
Hakan yasa na fara fita tawa hidimar zubar da cikin jikina,
koma in ce cire fan dake jikina, a lokacin ma nayi wankana ina
shiryawa domin zuwa gani likita a yau litini wanda likita ya bani
lokacin ganinshi. a
Mustapha ne ya shigo dauke da robar "freesh milk"
hannunsa, yana sha, tsaye yayi yana kallona ni kuwa ban fasa
shiryawata ba, ganin na dauki jakata na rataya tare da sa takalmana,
yasa naji yayi magana, "ina zaki ne?" "unguwa," "what?" wa kika
tambaya?" "tafiyar bata tambaya ba ce, amma in kasa hakuri, za'a
kira ka kaje duk in dama naje. Na fice abina.
C: and Amma da yake Mustapha mai dakakkiyar zuciyane, ko in
mai jan ajine, ko kadan banji ya biyoni ba," AL-HASAN
HOSPITAL" na wuce kaina tsaye, naje na samu likita kamar yarda
mu kayi dashi, maimakon yayi mani abinda naje nema, sai ya tsaya
yi mani yan nasihohi, wai kara in hakura in haifeshi, in yaso in
nmijina ya ki karba sai in mika maganar ga iyayena.
Ganin sam naki saurararsa, yace to ya amince zaiyi mani, in zo
gobe karfe takwas na safe, nayi godiya tare da kawo kudin aikinshi
na biyashi har da na yan jiyar kwana uku.
Falona na sameshi kwance shame shame a kasa kan kafet, da
dan hanzarina na isa wajan shi, "lafiya?" "lafiya kalau kadaicine ya
dameni kin tafi kin barni ni kadai," "to tsayawa zanyi inyi gadinka
ko yaya kake nufi? kaima kayi tafiyarka inda za a kula da kai mana.
69
"Ina gareni in da za'a kula dani wanda ya wuce nan, "yanzun
ko??" "ko a baya," "yanzun dai zo zauna muyi magana da ke, tunda
naga har yanzi zargin da kike yi mani a zuciyarki yana nan",
kalleshi nayi murmushi.
na
"Ni wallahi ma mamaki kake bani kiri kiri kana neman kа
mayar dani yarinyar da aka haifa yau, wai zargi, ni ke zarginka
abinda ka aikata a filin Allah, kaga dai baka kwana a gida, na biyu
yaranka da kansu suka tAbbatar mani cewa baka kwana gida.
Na uku da bakinka maka fada, saboda haka kaga ba zancan
zargi a cikin maganata, sannan da baka aikata hakan ba to me ya
kaika yi mani karya a gidan mu", "or" Hamida kada ki fassarani
haka, wallahi ""na fassaraka ko ka fassara kanka"
a
"sam wallahi Hamida ban aikata laifin da kike tuhumata
akanshi ba," "to meye dalilin ka na aikata haka, ya mike tsaye daga
kwanciyar da yake, hakan yasa nima na shige dakina na mayar na
rufe da karfin gaske.
Bajewa nayi kasa na tula cikina gaba, ba abinda nike tunani
sai, cin amanar da Mustapha yayi mani, farkon abubuwan da suka
faru suna dinga dawo mani a zuciyata, wanda anan take na baiwa
kaina laifi, tunda ban tsaya nayi cikakken bincike nan halaiyar
Mustapha ba.
Maimako inyi kukan zubar da hawaye, sai kawai na sa kara, ya
shigo da gudunshi, "lafiya" sai ya gani zaune dirshan ya iso ya
tsuguna a gabana, "Hamida?" "ka fita tunda ka gama cutata," "wai
duk me ya kawo wadan nan abubuwan haka?," "kaje ka tambayi
karuwan yammatan ka."
"Innalillahi wa'innailaihir raji'un," Hamida maganar ce har
yau bata wuce ba, ni fa zaulayar ki nake
י
gidan . sallama muka ji a falona, hakan yasa
ya fita, ina jinshi suna gaisawa da jabir, wanda tuni ya gaya masa
cewa banajin dadi, suka shigo suka yi mani sannu, ni ma na bisu da
yauwa, dalilin haka ne yasa jabir ya ce Aisha matarsa ta tsaya sai dare tunda ta sameni ba lafiya.
Anan suka yini har dare suna tafiya nayi wankana, daga dan kwanciya ina jiran shigowar Mustapha domin mu karasa maganar 70
dazu, sai barci ban farka ba, sai bakwai saura miniti biyar na safe, a
gurgujen nayi wanka nayi salla.
Wanda shi kuma Yallabai na yana ta barcinsa bai masan na
zame jikina daga nasa ba, har na rataya jakata, tare da kintsa jikina
tsab, amma Mustapha ko motsi baiyi ba,
"har zan fita na juyo na kalleshi tausayin shi da haushinsa su
ka dirar mani a lokaci daya na matsa na tura hannuna a gashin
kansa wanda duk ya hautsine a wajan barci, abinda haushi wai sai
naji zuciyata tayi