tarho gefen gadona ta sa kara,
nayi yunkurin in dauka Yallabai ne, ya yi saurin mirginawa ya
dauka jin ya tintsire da dariya ya ambaci sunan yaya Usman yasa
ayi saurin tashi tare da karasowa wajan sa, saboda nasan Halimatu
na kusa
Amma da kyar Yallabai ya amince muka gaisa, wai a cewarsa,
in muka fara hira dadewa zamuyi in barshi ba abokin hira, amma ta
wayar naji yana cewa Halimatu gobe zai kawoni in Allah ya kaimu.
Bayan na yini gidan Halimatu har zuwa karfe biyar na yamma
sai gashi ya dawo, wanda tunda ya ajiyeni ya tafi ofis acewarsa
yanzun ma kutowa yayi ya bar jabir a can.
47
A tunanina gida zamu wuce, sai nagan yayi hanyar unguwa
maitama gidan mu kenan da murnata, na shiga gida muka gaisa da
su har izuwa karfe shida har da mintuna biyar na yamma, bayan nan
kuwa, sai gidan ma'ama wanda acen muka kai har karfe takwas na
dare.
Amma wani abinda Mustapha yayi mani shine, kiri-kiri ya ki
yarda mu biya gidan Zulahatu saboda kishin sufiyanu da na fiskanci
Yallabai nayi, ina kallo aka bi ta kofar gidan su da ke unguwar area
4 wuse market. amma yaki yarda ko gaisawa in leka muyi da ita.
Kwana ni da Yallabai dina tamkar biyu ne a tsakani, amma
ango da amarya, duk da dan cikin jikina yana son ya iakura mani da
yan wasu abubuwan ga dan yawan motsi da ya dameni da shi, wai
shi ya fara girma, dan wata hudu din da yayi.
Kwance nike a cinyarsa a falonsa wajen karfe takwas ko na
dare motsi nayi sai ya sumbaci koshina, tare da tambayar yaya dai?
Ma'ana nufinsa ko na gaji ne da kwanciya
Cikin yar hirar nishadi da muke yi da yan wasannınmu, na
samu na sako zancen gidan zulaihatu, anan take sai naga Yallaba
ya hade fiska, a cikin wasa na fara zaulayarshi."
Yallabai Zulaiha fa, haka ranar ma fa ka ki mu biya gidanta
kai Yallabai na lura dai nema kake ka hanamu zumunci da ita aka
abinda bai shafeta ba," "ya isa haka nan don Allah."
Na mike zaune daga saman cinyarsa da nike kwance, tare
mikewa tsaye, saboda nasan maganar da zan fada sai nayi nesa
Yallabai, gudun kada insha marin tsautsayi.
"Ni bana son in ga ka kullaci sufiyanu, sufiyanu ba ruwans
ballanatana matarsa, laifin na gareni ni da nace ina son in aureshi
na dan yi murmushi, wai da yanzu fa shike da cikin jikina."
Nan take naga Yallabai ya dago kansa da sauri, ni kuwa gan
haka yasa na yi saurin tafiya zan shige cikin daki, waigowar
zanyi sai naga Mustapha ya biyo ni da saurinsa.
Karasa rugawa nayi cikin daki, na kwanta tare da makalka
filo, ina kiran na tuba, na tuba," isowa yayi ya cire filon hannuna
tsiya ya dagani zaune da dan yatsansa ya nuna ni sannan ya fa
magana,
48
"Wallahi kika kara yi mani irin wanwan maganar sai na bata
maki rai sosai", na samu na sauka da dan hanzari na ina yar dariya,
"amma kasan dai gaskiya na fada ko?" mai makon yayi magana sai
na ga ya tashi da saurinsa har wata 'yar rawar, jiki yake yi
Ni kuwa sai na kara yin gaba da guduna, "Hamida, "Hamida
wallahi kada ki kuskura ki zubar mani da ciki wajan wasan wauta,
shine har ki ke gudu, wallahi ." kafin ya karasa fadar
wata maganar ni kuwa har na kaiwa kofar dakin sa karo ta cikina
Na dawo da baya sai gani kasa kwance wanwar, yayi saurin
zuwa ya dagoni, ina ta wani irin nishin wanda na fasarashi, a nishin
wahala yanda Mustapha ya nuna mani shine ga haushi a tare da shi
na kamar yayi mani dukan tsiya ga kuma tausayi da na fuskanci
yana ji nawa.
Nasan dole tasa Mustapha ya daukeni ya dora agadonsa, amma
sai naga ya koma gefe daya ya tsaya yana kallona, cikin wata irin
yanayin miryar da ta zamo kamar ta aro nayi mashi magana.
"Iya taimakon da kake ganin zaka iya bani kenan?" "ki kira
sufiyanu ya zo ya aimaka manki, wannan ma da kika ga nayi na yi
shine kawai saboda bebina da yake jikin ki, wallahi! Wallahi!!
Wallahi!!!, in har kika kuskura bebina ya samu wani lahani a jikin
ki sai nayi maki abin da duk tunaninki ba zai kawo maki shi ba."
Ficewa yayi da saurinsa kamar zai kifa kasa, nan take na
mayar da kaina na kwantar saboda bazan iya tashi ba, balle har in
samu in bishi domin neman afuwa a gareshi.
Karfe uku na dare na farka a firgice saboda wani matsannan
cin ciwon da marata da kuguna keyi, haka yasa na dinga laliban
Mustapha, amma sai naji ban ji shi ba, hakan ya dan bani kwarin
gwiwar lalubo makunnin fitila da ke gefen gadan mu na kwanciya,
saboda in kara tAbbatarwa kaina ina Yallaбai na ya tafi.
Hasken da ya gauraye fakin baccin Yallabai shi ya tabbatar
mani mai dakin baya cikin dakin, na samu na ja jikina na mike a
hankali na shiga bandaki, amma wata firgita da nayi na mike tsaye
la saurina daga zaman fitsarin da nayi akan farar tukunyar bature ta
in bayan gida.
Ko daya ban karajin wani ciwo ba saboda tsoro da tashin
ankali dana shiga, a lokacin dana zauna yin fitsari, a maimakin
Λα
fitsarina kuwa sai naga jini ya maye gurbin zubar fitsari, hakan
kuwa shine sanadiyyar firigtata, tare da fitowa daga bandakin ba
shiri.
Zaman da nayi gefen gadan Yallaßai, nayi imani ba zai taba
yaye mani faduwar gaba da fargabar dana samu kaina a ciki ba,
hakan yasa nayi kokari na mike na samu da wani karamin tawul
nayi kunzugu da shi gudun kada jini ya kai ga 6ata mani jikina,
A sannu a hankali na dinga labe labe har na fito fatan Yallabai,
gabana ya kara faduwa da karfin gaske da naga Yallabai kwance a
falonsa saman daguwar kujera.
Ya zame mani dole in isa in nemi gafarar Yallabai, hakan yasa
na cigaba da tafiyata in karasa in da yake kwance, waigowa yayi ya
kalleni, sai naga ya kawar da kansa gefe, nan take sai naji jikina
yayi sanyi tamkar na kutsa kaina a firizar kwance.
Amma duk da hakan da yayi mani bai hana in isa gareshi ba,
ina isa sai naji na tsuguna gabanshi kawai, nayi imanin yana jina,
ma ko juyo da kanshi bai yi ya kalleni ba.
Kara daurewa nayi na dafa gefan cinyar hanrunsa tare da
fadar, "Mustapha," "me ye, ki tafi ki kwnata kawai " ya fada mani
tare da ya juyo kanshi ya kalleni na, a take anan dan ragowar
karfin da ke zuciyata ya tauye sai dai kawai hawaye naji sun tsiyayo
mani a kumatuna.
ba
Cikin karfin hali na mai kararriyar zuciya nace mashi,
"Mustapha jini," "what?" ya fada da karfi tare da mikewa zaune,
"me kika ce?" ban iya kara fada ba, sai dai kifa kaina da nayi a jikin
kujera na sa masa kuka.
Dagoni yayi tare da girgizani da karfi "ki fada mani mana, me
naji kin fada? ina magana kinyi mani shiru," "jini", "da gaske ki ke
ko kuwa?" "da gaske ne," ya sakeni yayi shiru tare da dafe kanshi
da hannayensa biyu.
Tashi yayi ya fice daga falon, hakan ba karamin tayar mani da hankali yayi ba, na mike da niyyar in bi bayanshi, amma sai marata taki daukata, dole tasa na koma na dukusa saboda wani azabtaccen
ciwo da take yi mani, sai da na sami kusan minti sha biyar sannan
na iya dan daddafawa na mike tsaye, amma duk da haka sai naji na kasa daga kafafuwana. 50
Dole tasa na koma na zaman wanda zauni yar ma ta gagareni,
sai gani na zame kasa na kwanta, ni kaina ban san iya tsayin lokacin
da nayi ina birgimar ciwon da nayiwa lakani da ciwon mutuwata, а
cikin wannan halin ne naji Mustapha ya daukeni.
Ban yi tunanin bude idanuwana ba, saboda ni kaina nasan ba
zan iya daukar nauyin budasu ba, ba abinda Mustapha baiyi mani
ba, domin yaga ciwon da nike birgimar ya sakeni, amma ko sauki
sauki ma banji ba.
Ni dai ina jin muna wuce motoci jefi jefi, amma ba zan ıya
cewa ga lokacin ba, ko ince karfen agogon bature nawa ta nuna a
lokacin, amma duk da idanuwana rufe suke bai hana kunene jin yan
surutai da hayaniyar tashin miryoyin jama'a ba.
Ban tAbbatar da in da muke ba, sai da naji tsinin allura ya ratsa
fatar hannuna, sannan na tAbbatarwa kaina da asibiti muka zo
Ina bude idanuwana ba abinda su ka gani sai wata 'yar
madaidaiuciyar agogon bango da ke saitin gadona sai naga karfe
uku na ranar, ko ban san iya awanmina ba, nasan dai na jima a
asibitin nan.
Bayan duk yarı sunnu sun tafi wanda suka tafi da sunan
faduwa nayi na samu wannan ciwon, saboda hakan Mustapha ya
fada masu, sai na zamo ni daya a dakin asibitin, hakan yasa a nan
take sai na fara tunanin ina Mustapha?, kenan Mustapha yayi fishi
da ni? ban kara tuna komai ba, sai gashi ya shigo da Abdulrashid
bayansa dauke da ledoji
Abdulrashid ya matso ya fara yı mani sannu, sannan ya fita,
tare da cewa Mustapha, sai kamar karfe nawa zai dawo daukarshi,
amma ta harshen turanci, zanyi maka waya, abinda Mustapha ya
bashi amsa kenan Abdulrashid ya amsa da okey sir ya fice abinda
Abdulrashid na fita Yallabai na ya iso bakin gadona ya tsaya
tare da dafa goshina da yar sumbatar goshina, "ya jiki?"ya ce mani
a dai dai lokacin da yake shafa gashin kaina.
Cikin sanyin mirya na amsa mashi cewa da sauki, tare da ce
masa ya gafarceni don Allah, gani nayi Mustapha ya daga kai na ya
dora a cinyarsa sannan ya sunkuyo ya kara sumbatan kumatuna.
"Ki daina wannan maganar don Allah, Allah ne ya kaddara ta
sanadiyyar yinta zaki hadu da wannan ciwon, in dama zamu kara
51
1α
godewa Allah, shine da ya bar mana fan bebinmu, sai dai mu kara
kiyaycwa kawai.
Murna, dadi, su suka dirar mani a zucıyata nan take wanda
hakan yasa nayi saurin cewa Yallabai na gode yayi yar dariya tare
da dan lakatar mani hanci kada a kuma maimaitawa na dan rufe
idanuwana alamun kunya da na dama
Shigowar Ma'ama ita tasa naga Mustapha ya daga kaina da ke
cinyarshi ya dora a filo, ya mike yana yan soshe soshe wuya wai shi
kunya, wanda ni ya sakarwa kunya, tunda na kasa bude idanuwana.
Abinka ga babbar mace, sai ma ta nuna ba san abinda ake ciki
ba, bata fi mintuna ba sai ga mamana ta shigo da inna tantu dauke
da kayan kwnoni a hanunta, idona rufe nayi saurin wajen naji suna
gaisawa da ma'ama amma ko kusa dani bata matso ba sai dai sun
gaisa da Mustapha har tayi mashi ya mai jiki.
Ina jinta tana gayawa ma'ama cewa ga inna tantu nan ita zata
awaje na ina ji tayi wa ma'ama bayanin cewa iya tantu kanwar
daddy din muce, ni kuwa a lokacin da na dan kyalla idana sai naga
ba Mustapha a cikin dakin, hakan ya tAbbatar mani ya fita kenan
Karfe takwas na dare su mamana da sauran wasu daga cikin
yan dubiya ta suka tafi, wanda fitarsu ke da wuya naji Mustapha ya
shigo yana yiwa ma'ama magana da irin yaransu na indiya.
Ban iya yaran indiya ba saiu dai kala mai fai daya, saboda
haka bansan maganar da suje yi ba, sai dai da maganar tasu tayi nisa
naji ana fadar ba ayarda ba, da cewa ko da yaushe da yansauran
tsirarin kalaman da Mustapha ya koya mani
A haka dai na hada na fahimci a kan kwana wajena suke
magana wanda naji Yallabai na cewa shi zai kwana tare da ni ita
kuwa ma'ama tana yi mashi gardama a karshe naga ma'ama ta fice
ta bar mashi dakin, tare da fadar maganar ta ta karshe da kalmar
hausa, "na gaya maka kada in kuskura in ji labarin ka kwana aа
sibitin anan sai da safenku.
Hajiya ma'ama na fita, naga Yallabai ya zauna daya daga cikin
kujerun da aka zagayc dakin dasu, "kushin," a hankali na kira sunan
sa, ya dago kanshi sai na ware hannayena alamar ya taho,
Bai yi wata gardama ba ya taso ya zo ya zauna gefanm gadona
sanna ya dan shiga hannuna ya kwanta a kirjina, a hankali na dinga
52
shafar gashin kansa da magana cikin natsuwa da nuna tausayawa a
gareshi, ta ya hakuri ya bi abinda Hajiya ma'ama ta ce.
Nan ya kama yi mani miratar wai ko ya koma gida ba zai iya
wani barci ba, "ke kinsani ko na koma gida ba zan iya barci ba,"""na
sani Yallabai, amma ni a nawa gani kayi hakuri kabi abin da mahaifiyar ka ke so saboda a ganina ko ka zauna nan kayi barci, to barcin kuwa bashi da amfani tunda mahaifiyar ka na kule da kai.
Hakurin ka kawantacan shi ne alheri a gareka, haka na dinga
lallashinsa harya hakura tare da cewa sai sha biyun dare zai koma
gida shima, sai da na cigaba da bada hakuri tukuna aka hakura za'adinga tafiya sha daya na dare.
Maimakon dadi sai haushi a wajan Yallabai na, saboda
wucewar da za'ayi da ni gidanmu, da an sallameni daga asibiti,
domin hutu da likita ya bani, shi ma kuwa sai da nasha sabon aiki a
wajan Yallabai na, da kyar na samu na shayo hankalinsa ya hakura.
***
1
Alhamdulillahi, ni kam Hamida ina samun kulawa matuka
saboda duk safiya ko dare sai Yallabai ya zo, banda ma'ama ita ma
kullum tana tafe a hanyar zuwa gidanmu, a bokannan Yallabai ma
haka Abdulrashid kuwa gidan mu ma komawa yayi tamkar nasu
saboda komai shi Yallabai ke aikowa ya kawo kafin ya iso
Bangaran mamana da daddy ba zance komai ba saboda duk
abinda likita ya ce shi kuwa suke bani.
Sai da na samu tsayin wata daya a haka, sannan Mustapha ya
zo mani da labarin zaiyi tafiyar gaggawa zuwa kasar itali shi da
jabir a cikin satin nan, tabbas naji banji dadi ba, sai dai na dan nuna
ban damu sosai ba saboda gúdu kada Yallaßai na ya gane ya rushe
tafiyar, gata ta karuwar muce itama.
Yau kwanan goma sha biyu da tafiyar Yallabai (kasar Itali)
domin taron bude wani sabon kafanin takalma, wanda hadin hannu
ne da gwannatin kasar.
Tafiyar ta kamashi ne a ba zata, wanda ta kuma zama dole ya
tafi tare da amininsa Jabir, hakan yasa dole ya bar mani
Abdulrashid, domin kulawa da duk wani abun da zan bukata,
53
Abukan Yallabai kuma kullum zirga zirga suke akan
dubani, wanda hakan ya kan rage mani tsananin tunanin rashin mai
gidana a kusa da ni, wanda Hajiya maama kuwa, duk kwana biyu
sai tazo taga yar sirikarta da lafiyar abinda danta ya bari a ciki.
Hakan ba karamin dadi yake yi mani ba, ganin yarda aka
mayar dani yar gata ni Hamida gashi gidan mu bani aikin ko ninke
kayan da na cire, wadan da zan saka jikina ma, sai dai in gan su in
saka, wannan kuma duk aikin 'yar Kanwata ce Aina'u
Dakin mamana nike kwanciyata ina barci, domin nawa dakin
za'a shiga a gyara mani shi ni kuwa dama aikin tsayuwa bai gannin
ba, tunda na samu matsalar cikin nan nawa.
Karar wayar gefan gadon mamana ita ta tashe ni daga wani
barcin da nike mai dadin gaske, cikin fan tsoki na na dauki kan
talho din da ke gefen gado na kanga a kunnena, tare da fada,
"assalamu alaikum,"
Amsa sallamar kawai naji amma na gane miryar bakon
italiyan, 'sai ka tasheni barcina mai dadi, sai kasa na haifo maka
yaro mai gutsurarran kunne," na fada cikin magara irin ta
shagwaba.
"To"be sorry" banyi zaton kina barci ba, ganin ranace, gashi
gidan ku gidan jama'a amma duk da haka, a fuwan, ki kuma
gayawa bebi kada yayi fishi yanzun zaki koma barcin, yayi hakuri
inzo in ganshi da kunnuwansa biyu.".
Na danyi dariya, "baka gajiya wallahi da sa mutum dariya ni
ya bakunta?" "bako ai ya kusan dawowa, ki tarye shi yau da karfe
uku na dare a filin jirgi, domin bako ya gaji da jama'a garin wasu
ba matarshi akusa dashi balle dan bebinsa.
Kinga daga filin jirgi ai sai gida ki hadawa bakonki abinci
ko?" "a'a bako ya ciko cikinsa tun a garin jama'a, in kuwa na jirgi
yake so, to ya ci ya koshi, domin har yanzu matar bako jinyar dan bebin bako take yi."
Muka sa dariya gaba daya, "ke matar bako, kada kiyiwa bakon
naki haka," "amma ai shi bakon dai in mai hankaline ai yasan ba zai
so matar bako ta fito cikin dare taryar bakonta ba, ko bako yana so
taci karo da azzalimai a hanyar zuwa tarar bakonta?"
54
Yayi dariya, "Hamida kenan, akwai iya dubara, yanzu dai
kinyi wa dan bakonki wayau kenan, ya ji zai rama in ya iso ga
matar bako, yanzu dai ki koma ki cigaba da barcinki, ko shima sai
bako ya ririgaki ne?"
"wallahi da zan samu ina so bako," "to tsaya in fara ririgaki,
kina jina, amma kwata ki rufe idonki," to kinyi, to goshin nan zan
fara, yar bebina, kiyi shiru, yar lele ta bako, goshinki da haske,
kuncinki da laushi wuyaki da gwabi,"
ni kuwa dariya kawai ni ke, tare da cewa, "kai Mustapha, har
kasa na harareka a waya "kai! kai!! kai!!!, to, inazo kuwa sai na
biya kudin wannan hararar," "ni ma in biya na raino, gashi kuwa har
na soma barci," nayi sauri na kife kan talho din in ba haka ba
kuwa,sai mu kai wani lokaci, dan yallabai ba gajiya zai yi ba.
Tun asuba, nayi wankana, na gyare jikina, na kawo turaririka
na goge jikina da su, tare da daukar rigar baccita na mayar a jikina,
duk dan jan fada ga yallabai, gama shiryawata kuwa, yasa na koma
na shige cikin bargona, tare da kashe fitulun dakin da nike kwana,
waini barci nike.
A wannan yanayi ra sanyin watan karshen "december", wanda
ni kuma na koreshi da shiga cikin bargona mai laushi domin samun
wadataccan dumi a jikina.
Karfe takwas da rabi na safe, naji tashin miryarsa a bAbbab
falan gidanmu, hakan yasa na juya na baiwa kofar dakin baya waiui
a dole barci ni ke yi.
Ina jin shigowarsa, har da mayar da kofa da kullewa da
makulli, a zuciyata nayi yar dariya, shi kuwa har wani sanda yake
wai manufarsa kada ya tasheni, a hankali ya bi har ya hayo gadon
ya zauna dai dai in da na mayar da fiskata.
Ina jinsa, ya sumbaci kumatuna, tare da janye bargon da na
lulluba, zuwa wajen cikina shima ya sumbaci cikina, tare da dan
lailayashi alamar yaji ko lafiyarsa kalau, sai lokacin na bude
idanuwana a hankali ina mai nuna alama daga barci na tashi.
Da saurina kamar gaske nayi saurin tashi na fada jikinsa wai ni
murnar dawowarshi. Shi kuwa sai dariya murna da farin ciki yake,
ya dagoni, "ya bebina?" na dan bata rai kadan "shi kadai ka sani?".
55
"Na ısa ayi-wa bako afuwa, ya kika wayi gari?", "lafiya kalau"
"ina fatan kai ma ka dawo lafiya, da fatan kuma tafiya tayi
пasarа???", "Alhamduhillahi, tafiya tayi kyau sosai, amma ni ban
tsaya an karasa komai dani ba, kasarce naji duk ta isheni, Jabir na
baro in an gama shi ya taho
"Kai yallabai yanzu ku tafi tare kai kuma sai ka taho ka barshi
can", "to ya zai yi, shi ya dan saba sosai da barin iyalinsa gida, ni
kuwa kinga ban saba ba, ina laifi wannan ma da nayi."
"Shine kuma sai kayiwa mutane sammako a gida," "su bani
matata su gani in zan kara zuwan masu, to balle ta kaini ga
sammako," "kenan ko gaisuwa ba zasu samu ba?" "na isa, wannan
ai daban, in dai har zanje gaishe da Hajiya maama to zan kuwa
gaishe da suma nan gidan, saboda kinsan duk daya suke a gareni.
Cikin wata yar yananin sigar wata manufa Mustapha ya yi
mani magana, "ni yanzu na zo in biya hararar da akayi mani a
waya "wasa fa nake kai ma kasan..... ," kafin in karasa yayi
saurin hada bakina da nashi,
Mintuna ashirin da kusan biyu daki na ya samu bakuntar shıru,
tamkar ba kowa a ciki, wasnnnin shiru kam shi na biyewa Mustapha
mukayi amma cikin cikon minti na ashirin da uku, sai naji
Mustapha na nema canja wasa
Hakan ya sa na nuna masa alamar ba'a hada wasa biyu a
lokaci daya a kare lafiya, ba tare da anyiwa wani cikin yan wasa
ciwo ba, amma a take sai Mustapha ya nuna mani, shi mai iya shiga
cikin wasa kala hudu ne ya fita ba tare da anyi fada da shi ba.
Maganata da nayi ita ta kawar da shi run da dakin yayi
"Mustapha kasan dai ba zai yiyyuba, ka tuna sharuddan likita "ba
komai a duk Allah ya kaddara zai faru zai faru ki kyale managar
likita kawa."
"A gidamu Yallabai?" "taso mu tafi wani hotel din," "haba
kaima kasan maganar da ka fada ba mai yiyyuwa ba ce ba," "to
yanzu ya kike son inyi? Wata biyu fa, har da kwanaki," "ka manta
likita wata uku ya bayar," "kwana nawa ya rage a wata ukun bai fi ashirin ba." fa Hamida."
"Ni dai don Allah abar wannan maganar ma muyi hira kawai
'bazan iya ba," "ni kuma ba zai yiyyu ba," "ko," "gaskiya kayi
56
1
tunani kaima," "ki daice haka kika zaba wa kanki shi kenan magana
ta wace.
Abin bai kai na zafi har haka ba," "nace magana ta wuce, ayi
wata, in kuma ba wata in tashi in tafi, ina son in je in gaishe da
maama, ban je gidan ta ba nan kawai na taho daga tashi na.
A hankali ya mirgina ya sauka," "ni zan tafi, saboda ina da yan
abubuwan yi, wata kilan in dawo an jima, in kuwa ban samu
dawowa ba, to kilan sai gobe in Allah ya kaimu" ina zaune ni dai
ina kallonshi har ya gama maganar sa, ya sun kuyo ya sumbace ni a
goshi ya tafi, ni kuwa na bishi da kallo har ya fita.
*** *** ***
Wane irin fishi Mustapha yayi dani haka?, harda zai dauki
kwanaki har takwas ba shi ba wayar shi, balle dan aike, shin ko ya
samu wata ne ban sani ba?.
Nayi tsoki na mike daga zaman da nayi a gadona, na shirya jikina, na ficewata falo abina, tunda nasan tunani ba magannin da
zai yi mani, tunda bani da ikon fita.
Misalin karfe sha daya na safiyar litinin dai ne akace mani ga
Abdulrashid, dama mamata bata falon ta shinta kenan ta shiga
sashen daddy, a tunanina ko shara zata yi masa, ni da Aina'u ne
kawai a falon, ita ma dan ta dauki jarabawar wucewa makarantar
gaba da primary"
A nan nace tace ya shigo tunda dama da mayafina, a jikina da
ma ni da shi nike yini a jikina, saboda kunyar a ganni da tikeken
ciki a gabana har na wajan wata takwas.
Bayan mun gaisa da shi ne da tambayata ya karfin jikina, duk
na amsa masa da lafiya kalau, sannan ya cigaba da fadar sakon da
aka turo shi da ya fada.
"Madam dama Yalla6ai ne yace in kawo maki sako", ya sa
hannu a aljihu ya zaro wata ambulan ya miko mani, "kaya na cikin
mota suma ya ce in kawe maki."
"Yayi tafiya ne?" "a dai sanina bai yi wata tafiya ba," "1о
yanzu yana ina?" ni dai tunda jiya da ya zo ya kawo mani wannan
sakon ya i har yau bai dawo ba" "kenan bai kwana gida ba?" "Е,
57
to, gaskiya bana jin ya kwana gida," tunda ya dawo daga tafiya yana kwana gida?"
"Hajiya wannan tambayar ba tawa bace, nasan dai anan yake kwana," Abdulrashid ya fada yana murmushinsa, nan take sai naji
kaina ya sara dan cikina ya juya take marata ta daure, duk da yanayin sanyi muke ciki, amma hakan bai hana gumi tsiyaya a
jikina ba,
"Bai gaya maka yana da tafiya zuwa wani gari ba, ko kasa,"
"bamu yi maganar haka dashi ba tunda ya dawo, ni fa nayi zatan
yana nan gidan sai jiya da dare ya zo ya kawo mani wadannan
kayan yace a kawo nan."
"Tun jiyan kuma bai dawo gida ba?" "E sai dai yau da safe
yana bugo waya mun gaisa," "me yasa kuke barinshi fita shi daya,
kullum nan yake kwana, dama na tambaye ka ne saboda in nuna
maka kuna son kuyi sakaci da aikinku,
Yanzu da ba nan yake kwanaba, da ya kenan, ku kuma ba kwai
binshi ko abaya ne ku dinga kulawa da shi, kunsan dai irin su
oganku, sun tattare da hadari sosai, don Allah ka dinga kiyayewa
Abdulrashid."
"To madam daga yau zan kiyaye, tunda kin bayar da izini, ni
zan koma, yace in da wata matsala ki fada," "ba komai ka koma ma
da kayan da ka zo da su kace masa wadan can da ya kawo mabasu
kare ba, kuma daddy na ma ya kawo wasu jiya," "to Hajiya ni na koma."
Na bude ambulan din da ya miko mani na zari naira dubu biyu
na bashi, "wannan a saiwa iyali lemo, ragowar ka mayar masa kace
ya tuna fa, jiya ya bani wasu ko ya manta ne?" "to Hajiya ya karba
tare da yi mani sallama ya tafi
Idanuwana a rufe na isa daki, saboda ba sa ganin gabana sosai, ba abinda na kawo a zuciyata illa na zauna kasa na jingina da gado,
tare da yaye mayafin jikina, hade da tube rigar jikina domin in samu in shanya cikin gabana ko dan cikinsa ya samu wadataccen iska. Ni na jayowa kaina komai, tunda lafiyata kalau amma naki arbar bakuncin Yallabai, "innalillahi wani inna ilaihir raji'un," shi kenan mijina ya zama( iska ma biyin mata, na zame jikina kasa 58
na kwanta rasidina ko ba siginta sai mustaphja ya bani shi (saki),
tunanin da nike yi kenan
Haka na yini a ranar ina ta mirgina a tsakar dakina na gidan
mu, har karfe takwas na dare, sallah kawai take tayar dani daga
kwanciyata, abinci kuwa, suna jere a gabana ban taba ko daya ba.
Sai ma da na gama sallar magaribq ne, sai na ji dan barci na
neman