An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HAMIDA
2
HNL
AUNTY MARYAM KABIR MASHI
AUNTY MARYAM KABIR
MASHI
HAUSAВООК.СOM
Harafi Publlshers KaAure Ni
BILKISUHAMUHD
lhaji Yusifari Abba Gana" "mutumin Maiduguri ne, dan Aasalin unguwar kabala kwastum, iyayensu da kakaninsa duk
anan aka haifesu, su kuma yan kabilar yaran, 'canuri" ne,
wanda ita kuma matarshi, hajiya yaya aji 'ita kuma iyayanta yaran
shuwa arab ne, kenan kyawawan fararen matan nan na shuwa da
muke samun labari.
Alhaji yusifari Abba Gana dan kasuwa ne, wanda da farko
maaikacin gwamnatine,, aikine ma ya mayar da shi abuja da zama
bAbban birnin tarayyar Nigeria, a cikin aiki ne ya fara dan harkokin
kasuwancinsa lokacin yana parm-sec a ma'aikatar, ilimi ta jaha. A
garin nasu na maiduguri, girma ya samu ya dawo aiki Abuja a
lokacin.
Wanda daga baya ya rubuta ritaya da kanshi wanda a yanzun
haka bai isa yin ritayar ba, tun lokacin da yana aiki a Kano, suka
hadu da mahaifinmu, wanda shima a lokacin yana MD
Yanzun haka mahaifin Halimatu yana daya daga cikin manyan
yan kwangila na abuja, gashi ya hada da kasuwancinsa na kaikaya
Kano, yanzun haka shine shugaban yan kwangilar gina gidae a
Abuja, sannan kuma shine ciyaman a harkokin kasuwancinsa na jahar Kano,
Hajiya yaya aji wacce muke cewa mome macece mai kyan
gaske, sai dai a wajanata su Halimatu suka dauko gajarta da fari
amma gajeran hanci, na babansune.
Halimatu Abba Gana farace, yar shuwa da ganin ta kaga kyakkyawar mace ga gashinsu na shuwa, har tsakiyar bayanta, farar
macece, mai dirin gaske sai dai dan abu daya da yayi mata kancal, shine dogon hanci da bata dashi, hancinta na da dan tsayi, amma bawai zamu kirata mai dogon hanci ba,
Farar fatata ita ta boye dan bAbban bakinta, sai dai akwai da
idanunwa, masu kyan gaske, gajeriyace, amma ba gajiriya dukus ba, ko da yake kuwa yasan iya tsayin shuwar asali.
Su bakwai ne mamansu ta haifa, mata uku, maza hudun, wanda a yansun haka yaya, Anas yayi aure da dansa daya sai madu da uliya su kuma suna karatu a jami'ar Zariya.
2
Mun hadu da Halimatu tun muna Kano da zama, wanda dama
iyayenmu maza sunsan juna amma haduwata da ita, yasa zumunci
ya kara karafafa a tsakanin mu da kuma iyayenmu.
*** ***
Tsawa ya daka mani tare da niyar hawe ruwan cikina, nayi
kokarin gocewa amma yariga ya kure mani da yawa, bayan ya jishi
kwance dai dai a ruwan cikina, sannan yasa hannunshi a hannuna
daya dake dukanshi ya hada hannuna da nashi ya matsigam sannan
yasa dayan ya dago kaina da karfi?
Kinjanye maganar kokuwa?" na girgiza kaina alamar ban janye ba, "ni ka kasheni ni ka kasheni," na juyar da fiskata gefe, ina kukan saduda, saboda nasan bani da matsira, maimakon inji ya
cigaba da abinda yayi niyya, amma sai naji ya mayar da kaina ya ajiye a hankali.
Shafa gefen fiskata ya kamayi tare da gashin kaina, sai naji ya
sumbaci goshina da wuyana, na kara sakin kara mai tsanani, abin
mamaki sai naji bakina yana karanta mani addu'o'in da na dade ban
karantasu ba a takaice ma ni bansan na haddacesu ba, saboda ban
taba gwada yinsu a kaina ba, sai dai in na dauko littafin addu'o'I na
da na rubutasu aciki.
Allahumma inna naj'aluka fi nuturihim wana'uzu bika min
shukurihim, allahuimma anta adhudi, wa'anta nasiri, bika ahilu
wabika asulu wa bika ukatilu, hasbunal lahu wa ni imal wakilu.
Allahumma la sahla illa maja'ala tuhu sahalan wa'anta tajialu
hazna iza shi'ita sahlan, duk lokacinda aka tsorata da abu ko wani
mutum.
Can naji ya juya da kaina sosaı, "look at me Hamida, ina sonki
sosai a zuciyata ba zan iyayi maki komai ba yanzu, tunda kin riga
kin tsorata dani ya sumbaci gashina, sannan ya mirgina ya kwanta
kasa, saitin fiskata, ni kuwa dama kuka kamar zan balle kirjina.
A hankali ya fara magana, wanda hakan ya sani bude idona na
kalle shi, "ki tuna ni namiji ne da ban taba sanin abinda kika zaba
ba, saboda haka dacewa yayi ace, in ya kama mani dole in yishi,
kamata yayi in yi shi a cikin natsuwa, balle ya kama da wacсе
zuciyata ke kauna zanyishi, "ya yi shiru.
3
"Ni ka kasheni in huta, ni nafi son mutuwar. ""ba zan
kasheki ba Hamida ki tuna ni mai Raunarki ne,ki amince Hamida in
aika da kayana gidanku," "ni bana so, ni bana so, ni kana so, ni ka
יי kasheni ni ke so
Na samu na mike tsaye, da dfan saurına, ban tsaya neman
komai nawa ba, nayi kofar fita, amma kamar dazu, a kulle take
gam, na dinga dukan kofar ina kuka, amma ko motsawa batayi ba,
na sulale na tsuguna tare da kifa kaina jikin kofar na cigaba da
kuka.
Ko dan ba takalma a kafarshi, shi yasa banji tafiyashi ba, sai
dai jinsa nayi ya tsuguna kusa dani, "bai dace ace kina kuka ba, ki
tuna kece fa kika zabi hakan, tunda kina son cika alkawalin da kika
daukar mata ko?
Na juyo na daka masa harara, "mugu" na fada, "kada ki kuma
yi mani irin wannan kallan, wallahi kika kara, sai na nuna maki ni
mugune a yau, tashi kije ki gyara jikinki tukuna ki tafi gida, bama
gida zaki ba, na manta, saikin zauna na karasa maganata," "ba zanyi
ba," "wallahi baki isa ba."
"Za kayi mani ne da tsiya? "bazan shirya ki da tsiya ba, amma
tunanin da nayi niyyar yi maki sai in fasa," "fasa mana," ya daka
mani wata muguwar tsawa tare da zare idanuwansa gaba daya da
fadar," "tashi ki je kiyi wanka ki gyara jikinki nace,"abinda da na
riga na tsorata dashi, sai gani na mike sume sume nayi cikin-gida.
Ko ina na shiga sai nasa makulli na kulle, har nakaiga bandaki
wani daki nayi wankan na sa kayana duk a cikin minti da basufi
goma ba saboda cikin gaggawa da tsoro nayi shi.
Da kyar na fito da kaina bAbban falon da na baroshi, nazo na
sameshi, yana kaiwa da kawowa a tsakiyar falansa ya dago ya
kalleni, "ki koma akwai kayan kwalliya a cikin akwati a dakina
kije ki gyara fiskarki kamar yarda kika shiga gidan nan, bazaki fita
a haka ba kisa ace mani dan iska".
Ban tsaya wani neman ba'asi ba, nayi baya, yanda na barshi
dazu, haka na dawo na sameshi, ni kuwa sai a lokaci ma naga
mayafina da takalmana, na tsuguna na dauka na yafe, tare da rike
takalmana a hannu, danwalina ma a hannu na rike shi.
4
Ta gaban shi nazo na wuce wai ni zan tafi ba tare da yace in
tsaya ba, sai dai naji miyarsa na fada mani magana, "Karfe gomana
safiyar gobe, ina jiranki ki zo mani a natsi, in kin janye maganarki,
gobe din zan turo da kayana gidanku.
In kuwa kina nan akan in auri wacce kika bani, to ki zo da
shirin ki cikin nutsuwarki, kuma da sharadi.
Bana son kuka, in kuma kika wuce goma da rabi zuwa sha
daya da rabi zaki iya ganin jama'ata da kayan aurena a gidanku,
saboda na gama yanke hukunci cewa, na fitar da dayan sharadina,
yanzu sun zama biyu, watau na fitar da kisa, saboda ina ganin banyi
ma wayau ba in har muka bar duniya a tare."
Bance masa komai ba, na wuce abina, har na naye yar motar ta
fita, sai naga shima ya fito, ban tsaya sauraransa ba, na tasheta nayi
gaba.
Dole tasani da na fita, na dan jinkirta saboda ba da motata na
zoba, a tasa muka zo, ina tsaye, shima sai gashi ya fito, ba tare da
yace komai ba ya zagaya ya shiga motar da muka zo da ita, haka
nan ni ma na shiga saboda bani da yanda zanyi.
Wajan walimar mu ya mayar dani kamar yarda mukayi da
Halimatu, ban tsaya sauraran me zai fada ba, na bude nayi gaba
abina, ko waigoshi ban yi ba.
Yanda naga rana haka naga dare, ina zaune dungurgur akan
sallayata, ba wani abu nike ba, face rokon Allah ya foranı a kan
Mustapha, ba wani abu ya hanani janye maganar Halimatu ba,
bacce gudun kada tace naci amanarta, ko na karya mata alkawali,
duk da na fahimci yanzu Halimatu hankalinta naga yaya Usman
amma ina ganin duk da haka, ba fita zanyi ba.
A tunanin da nake, in da wani abu can ya rabasu, ta watakilan
na dan fita, amma ni na kudura a zuciyata, ko da Halimatu bata auri
Mustapha ba ba zan taba iya auransa ba, saboda gudun kar zargi ya
shiga a tsakanina da Halimatu.
Nan take daga zaune, sai na fara tunana yanda girman alkawali
yake a wurin Allah, da ayoyin na musamman da suka sauka akan
alkawali da amana.
5
Kamar in da Allah (SWA) ya fada a suratul ina'ida aya ta (11),
"Allah (SWA) yace, ya ku wadanda kukayi imani, ku cika
alkawurrа.
Haka a cikin suratul isra'il aya zu, shima anyi magana akan
guman alkawali, ka in da Allah ke cewa,
"kuma kada ku kusance dukiyar marayu face, sai da sifa
wadda take itace mafi kyau har ya isa ga mafi karfinsa.
Kuma ku cika alkawalin lallai alkawari ya kasance abin
tambayawa ne."
Haka kuma da na koma 6angaren amana, shima banga sauki
ba ko kadan, saboda na tuno inda Allah ke cewa."
"Lallai mu, mun gifta amana ga sammai da kassai, da duwatsu,
sai suka ki daukaria kuma suka ji tsoro daga gareta, kuma (mutum)
ya dauketa lalle shi (mutum) ya kasance mai yawan zalunci, mai
yawan jahilci."
Har izuwa ta saba'in da uku, na tAbbatarwa kaina bani da wata
hujjar da zan ci amanar Halimatu, ko inyi gigin karya mata
alkawarin da na daukar mata.
Nayi tunanin in r.a biyewa son zuciyata, zan kuwa taradda
bacin ta a gobe kiyama, ya zama dole ko da zan rasa rayuwata inyi
kokarin ganin nabi sahun muminai na gari, wanda Allah ya
tanadarwa aljannarsa mai ni'ima.
Nan take na kara daga hannu na sama ina mai zubar da
hawaye ina rokon Allah da ya yafe mani zunubai na wadanda na
sani da wadanda ban sani ba, nasan kuwa cikin su har da yawaitar
hada jikina da nayi da namijin da ba mijina ba, ba kuma maharramina ba.
Duk da nasan nayi hakane akan in ga nayi kokarin cika
alkawarin da ke kaina, amma nasan in na mutu a yanzu zan hadu da
azabar Allah. matukar ban nemi gafarar sa ba, hakan yasa na
karanta addu'ar neman gafara, na rufe da ta amsar addu'a da
gaggawa.
Bayan na gama sallah asuba ne, sai na dan zame jikina na kwanta a saman abin sallata, abinka da na kwana a zaune bansa
lokacin da barci ya daukeni ba, sai dai tashi naji nayi a firgice tare da fadar "(Innalilllahi wa'inna ilaihir raji'un).
Ban tashi ganin ko karfe nawa ne ba a lokacin sai dai ganin
karfe goma saura munti ashirin da daya nayi a jikin agogon dakina
ba wata tsayawa komai, wanka kawai na shiga, ban tsaya bata
lokacina ba ga shafc shafe, na suka kayana, bayan na saka kayan
nema, nadan mirza mai a tsaye tare da yar hoda, gudun kasa mama
na ta tambayeni ko lafiya.
Atamface yar sufa helan na saka dinkin Umberra mai
wadataccan hannu amma sai gani na zurma hijabi ta, na rataya yar
kawa tafiyar, watau jaka, na suri yan takalmana a hannun na fita,
dakin mamana na fara shiga, amma ban sameta ba, sai "Aina'u na
gani tana dan ninainke mata kaya a saman kujera, nan nema take
gaya mani sau biyu tana shiga fakina ta sameni ina barci, mamace
ace kada ta tasheni.
Shashin daddy na nufa nayi sailama na shiga amma ba kowa a
falon na daddy na, sai da na dan kara sallama da karfi, sai gasu sun
fito tare da mamana, gaba dayanana zube a gabansu, don kunyar
ganinsu tare da nayi da alama kuma yau cikin nishadi suke, duk da
nasan ina dadewa ban fahimci sunyi hayəniya ba a tsakaninsu.
Ina nan tsugune har suka zauna, sarnan na kara matsawa kusa
dasu na gaishesu, dan bayanin da daddy ya tsaya yi mani, shi yasa
naga agogo ta nuna mani goma da rabi har da minti bakwai, tamkar
incewa daddy yayi shiru hakannan amma nasan bani da damar cewa
haka.
A nan ne yake tambayar mamana cewa har yau bamu gama
bikin bane, maman tace masa, ai daga yau mun gama, a haka nayi
sallama dasu na fita da saurina kamar in kifa kasa.
Karfe sha daya da minti goma sha tara na tsayar da motata a
harabar gidan Mustapha, wanda a dai dai tsayawata na ga wasu
dattawan mata su shidda da akwatuna a gabansu, amma nasan suna
nesa dani, da alama ma basu ganni ba.
Kamar zan kifa, na haye lifta sai kofar falon Mustapha ta
farko, a dai dai tsayawata, naji yar hayaniya na tashi a bangaren da
yanuna mani na mamanshi in taso kawo masa ziyara, da kuma bakin
yan indi'a ko Baucihi.
Da sallama mai karfi na shiga cikin talan, amma banga kowa
ba, dan tsaye nayi na mintina daya zuwa biyu tare da kara kwalla
=
sallamata, aınma naji shiru, nasan cikin tsoro tsoro, nike, amma
hakan bai hanani yin gaba ba, zuwa cikin gidan sosai, ina tafe ina
sallama tare da kiran sunansa.
Amma har sai da nakai ga kurewa kuryar dakin barcinsa,
amma banga kowa ba, hankalina kam ya tashi, nayi baya da saurina,
ina zuwa dai dai fita inyi bAbban falo sai muka hade da shi, wanda
har dan tsoro naji kadan.
Yayi dan muimushi kadan, "ashe zaki zo?, gasu can zasu tafi
gidanku, kai kaya, amma dama na danyi masu dubara, da su dan
bari sai bayan anyi sallah azahar, saboda shi zai tAbbatar mani da in
da kika sa Gana, bismilla, mu koma ciki ko," "a'a muje can falon
dai," "ya dan girgiza kai, "to sarauniya, ai duk abinda kikace shi
za'ayi," na dan so in harareshi amma gudun maganarshi ta jiya, shi
yasa ko kallanshi banyi ba.
Bayan na dan dosana na zauna a kujerar, kamar mai tsoron
kujerar, shima ya zauna ta nesa dani," "ina sauraranki," "ni bani da
zabin da ya wuce ka kasheni in huta," "amma na gaya maki jiya
cewa na janye wannan sharadin ko?" "mai zance maka, ni dai
abinda zance yanzu, bai wuce kaji tsoron Allah ba, sannan ka
taimaka mani in cikawa iyayena burinsu na suga sun auraddani
lafiyayyar yar da suke alfahari da ita, sam Mustapha yanzu na gane
ba sona kake ba tsakani da Allah, kamar yarda kake fadi, nasan
halittar jikina kawai kake sc.
a
Ba dan komai ba, dan kaga kasa iyayena cikin bakin ciki da ni
kaina, ka san ...," ya daga mani hannu, "ba doguwar magana
na tambayeki ba, magana kwaya daya na tambayeki, shine e, ko a'a,
in kin zabi auran kawarki, to bismilla mu tafi daki, da sharadin ba
ihu ba kukan da zai tayar mani da hankali, saboda ina son natsuwa а
lokacin.
Ki tuna wacce zuciyata ce ke mafarkin auranta a matsayin
uwar 'ya 'yanace zan kebe da ita, saboda haka, dole ne in kasance
cikin nutsuwa, duk da nasan nima ba'a farin cikin zan aikata abinda
nike son natsuwa ba a kansa.
In kuwa kikayi mani haka, to zan bayar da okey yanzu a tafi
kai kaya gidanku, in kuwa kin tsaya, ba fashi yanzu za'a kai kayan
nan gidan aminiyarki ta ke ko ko kawama?, ohon maki."
8
Ya mike tsa, "to! To!! In jira fa," sai naji hawaye sun taho mani, nayi sauri na mayar da shu, "amma Mustapha ba zaka so ayiwa kanwarka ko yarka haka ba,""wannan kuma ke ta shafa, ni dai ina sauri ne, saboda na bar iyayena suna jirana, nan da kike ganinsu duk kannan mahaifina ne da yayyansa uwa daya uba daya, sai kuwa yan uba Kalilan kinga kuwa ba wasa a tsakanina dasu. Ya tuntsure da wata irin dariyar da ban taba ganin yayi ta ba, "alkawali ko?" sannu gibiyar gaskiya, yau kya fada in dan nine, ni ki sani abinda zuciyata bata so, kije kiyi murna kiji dadi, ni ki barni cikin kuncin rayuwa, bagara muyi kuncin tare ba, common okey! Okey!, ina jira fa.
Ga Allah na dogara, saboda alkawalinsa zan cika, dan haka kawai sai na mike ina zanje?" na fada a sanyaye "dakina, ki je ki shirya kafin in iso," na taho har zan wuce ta gefansa, ya dan kira
sunana a hankali, dama mai jiran haka, sai nayi tsaye cak, saboda a
nawa tunanin cewa zai yi ya hakura, amma sai naji shi dab da-ni. "Ki tsaya muyi sallama da ke, tun kafin kunyarki ta kamani, Hamida naso ace na aureki ne haka zata kasance a tsakaninmu,
amma duk da haka, ki sni, kada kiyi zatan zanyi maki haka akan
kiyayyane, zanyi ne, saboda son da nike maki na gaskiya, Hamida
nayi gaba ban tsaya jin kalmomin da zasu kara mani haushi -ba,
amma sai naji ya riko hannuna, dama kuma maganar a sanyaye yake yi mani ita, tamkar wanda aka gane yayi sata sannan yayi
nadama daga baya.
"Karkiyi mani haka Hamida," sai naji ya hadani da jikinsa ta bayana nayi sauri na goce jikina," "kaga nifa ba karuwa bace ba, da
mutuncina, yanzuma dole......." Yasa hannun ya rufe bakina tare da
mayar da hanniwansa ga kumatuna.
Har zan fizge jikina, sai a take na tunano maganganun mamin
su Halimatu, in da take ce mani ta hanyar nuna mashi ina sonshi, tanan zanci nasara ga duk wani abinda nike nema, hakan da na tuna
yasa na dafa hannunsa daya, tare da mayar da kaina na kwantar a
jikin tafin hannunsa.
Sai a lokacin nayi kokarin na karaso da hawayen da ke makale lokon idanuwa na. 9
*** ***
Zubowar hawayena a hanunsa, shiyasa naga ya dan rude, ya dago kumatuna na kalleshi, "Hamida don't you love me?" sai na
karasa fasa kukan sosai nayi saurin fadawa kirjinsa sai naga yayi
saurin kara rungumeni jikinsa, abinda ban taba yarda ya shiga
tsakanina da shi ba.
"I love you Hamida, please, you should love me," can cikin
sheshshekar kuka nace masa, "who said I don't love you?" ya dago
ni a hankali ya tallabi kumatuna, zaki aureni?" "na daga idanuwana
na kalleshi, hawaye ne shima a fiskarshi, a binda ban taba tunanin
Mustapha zai iyaba, watau kuka.
Cikin yanayinda zan kara rudashi, na sa hannuna, na shafo
hawayen fiskarsa, sai na dawo da hannuna, na sa ina lashe hawayen
nasa yayi saurin rike hannuna, yana girgiza kansa, hakan tasa ya
hada goshina da nasa, nayi saurin lumshe idanúwana jinsa nayi ya
sa hannun ya tallabi kumatuna, kamar ance bude idonki, sai naga
lebena ya hadu da nasa, da alama, so yake mu tsotsi bakin juna.
Ni kuna hakan da na gani, shi yasa na danyi dabarar fwace
jikina, nayi gaba, zuwa dakin daya umarceni da zuwa dazu, /anda
na waigo na ganshi ya durkushe kasa, tare da kifa kanshi ga
cinyarshi daga durkushen, shi ya tAbbatar mani, cewa na durmiyar
da Mustapha zuwa shiga tarkona.
In jin tahowarsa, bayan na wanda samu kusan mintuna sha
takwas a dakinsa zaune, nayi sauri na cire hijabin jikina tare da
dankwalin kaina, wanda gashin kaina ya bazu a saman kirjina wani
ya koma bayana ya kwanta.
Nasa hannun na cire sarkar da ke wuyana da dankunnen
kunnena a dai dai lokacin ya iso kofar dakinsa ya tsaya, a hankali
na dorasu saman yar durowar da ke gefan gadansa, "sedd bead" sai
a lokacin na daga kaina na kalleshi, wanda shi kuma yayi saurin
kawar da idansa ga kallona.
"Ni ba zan iya cire kayana a gabanka ba, kunyar ka nike ji," ba
tare da ya bani amsa ba, sai ya juya ya fita, sai da ya koma falo,
sannan yace, "na fita cire, ana jirana a waje," gabana ya kara faduwa. A zuciyata nace, ba lamani kenan a wajan Mustapha, a take
na dinga karanto "hazbunallahu wani'imal wa'kil,"
10
Tare da kara karanto wannan addu'ar ta kare garkuwar jikinka, dukiyarka, gidanka, daga barayi ko gobara, ko mai niyyar yi maka
asiri, ko kana kokonto za'ayimaka asiri, ko anayi maka, to idan
muka dimanci yinta safe da yamma, ma'ana sallah asuba data, magariba.
To kamar munci makiya yaki ne, haka wuta haka barayi, ALLAHUMMA, ATA RABBII LA'ILAHA'ILTA ANTA ALIKA TAWAKKALTU WA'ANTA RABIL ASHIR AZIM, MASHA ALLAHU KANA FAMA LAM YA SHA'A LAYAKU A'A LAMU AMALLAHA ALA KULLI SHAI IN QADIR, WA'ANNALAHA QADA HADAMIN KUKI SHAI'IN WA'AHASA KULLI SHAI'IN ADADA, ALLAHUMMA INNI A'UZU BIKA MIN SHARRI NAFSI WAMIN SHARRI KULLI DABBATIN ANTA AKHIZUN BINA SAYATIHA INNA RABBI ALAKULLI SHA'IN RADIR.
A take anan kuma na tuno addu'ar da malamin isalamiyyar mu
ya ke yawan nanata mana ita, yanda ya gaya mana falalarta, shine
ya bamu kissa a kanta ne kuma har yau ban mantata ba, (KAMIN
ATIN KALI'ATIN GAL'ABAT FI ATIN KISIRATIN BI
IZINILLAHI WALLAHU MA'ASSABIRIN,)
Nan take kawai sai na daga rigata na cire na jefar gefe daya
"ina cire wa ina karanta (YA LADIFU) ba adadi a bakina, ban tsaya
komai ba, sai na cire shimin jikina, amma kunma sai naji na kasa cire
rigar mamata.
Nan take sai na zame na sauka daga gadan, saboda tausayawa
kaina da nayi, a hankali naja zanena izuwa kirjina, watau daurin
Kirji kenan na koma na kifa kaina a jikin katifa, sai a lokacin ne naji
asbe har yanzun hawaye ne ke ta zuba daga idanuwana.
Na daga kaina na sa hannun na janyo hijabina na saka, domin
rufe jikina da yake tube, habar hijabita nasa na goge hawayen
fiskata, dai dai lokacin da na mike tsaye ni kuma.
Kofar dakin naje na tsaya, tare da ce masa," "na shirya" cikin
rawar mirya, ya dago kanshi da yake sunkuye ya kalleni, sannan ya
kara mayar da abinsa yarda yake, "shiga ciki ina zuwa," haka kawai
ya tada mani, fadar hakan kuwa, yasa ni ma nayi baya zuwa cikin
dakin, tsaye nike kusa da gadan kwanciyarshi, wanda na samu
11
kusan minti biyar a haka, ina niyyar in kara komawa kiranshi, sai
naga ya shigo, sai da na bari ya kawo tsakiyar dakin, sai kawai nayi
saurin cire hijabina, ina mai kara ci gaba da karanta "YA LADIFU"
a zuciyata.
Kamar wanda aka haskewa fiska da cocilan, naga yayi, ma'ana
yayi saurin sa tayan hannayensa yana kare fiskarsa ganin haka da
yake, tare da alamar tsayawa, da yake, ita tasa ni kuma na nufoshi
gadan-gadan da saurinsa, ma'ana tunda yaki isowa shi, ni bari in
sameshi a inda yake tsaye.
Ji nayi yana fadar kalamai kamar uku da karfinsa, "Me ye
haka Hamida? Kina da hankali kuwa? ashi dai baki da hankali ban
sani ba?" hakan da yake fada bai hanani cigaba da tafiyata ba.
Ganin ban daina ba, naji yace "SUBUHANALLAHI" da
Karfinsa yayi baya a guje, yana fadar, ki sa kayanki ki zo ki tafi
gida, fito maza-maza da sauri, ki tafi gida, ashe baki da kwakwalwa
kamar haka."
Ganin ya yi baya a guje, ni kuma shı yasa na durkushe kasa,
nasa kuka, ni kaina nasan kukan murna, hade da na bakin ciki nike,
saboda ban san ba, ko yace ba zai auri Halimatu ba, na dan dauli
mintina a haka, sannan na tashi na kama saka kayana jikina na rawa
saboda in je inji kuma me zaice inyi ban da wannan.
Kwance yake saman rest chair' kujerar hutawa. ya nade
hannuwa a kirji yana