Zuhura tawa shiyasa nake kara sonki" Nadra tafada tana rungume ta, to yanzu duk munji ki mana shiru" muhsin yafada yana bata rai, dariya sosai Zuhura takeyi, hakan bakaramin dadi yasa Ahmad ba, ahaka har suka isa school din, bayan yayi parking suka futo su duka, class suka wuce, shi kuma suka wuce office din principal, bayan sun shiga ne suka gaisa, dama sun gama magana da Mamy dan haka kawai cike-ciken takardu yamata akabata uniform dakomai tace mata ko gobe ma tafara zuwa, murna kamar me agurin Zuhura ranta fari tass, daɗin ma dataji shine ba a dawo da ita farko ba, ss 2 aka kaita saboda taga yarinyar ba laifi duk da ba privert tayi ba amma ba laifi tana da kokari, daga haka suka futo daga office din suka nufi parking space, jiyake kamar mata da miji shida ita azuciyarsa , gaba daya yau yana cikin farinciki dan iya murmushinta ma ya isheshu
💞💞 SOYAYYA DA IZZA 💞💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 23
_______________Kallonta yayi yace "ranki ya dade inajin yunwa fa" bata kalle shi ba tace" toba nace zan hadama breakfast kace na barshi ba" ayyah sorry ganinki danayi ne yasa nadena jin yunwar ma" duk da bata gane meyaka nufiba tayi murmurshi, " wow wannan murmushin ai sekisa na sume miki" dariya maganar tabata hakan yasa ta tuntsire da dariya, kallonta kawai yakeyi, seda yaji sitiyarin motar na neman kwacewa yasa shi saurin kallon gabansa, gefen titi yanema yayi parking, kallon shi tayi da alamar tambaya, shima kallonta yayi yanacewa" Zuhura akawai abunda nakeso nagayamiki" inasan dan Allah ki nutsu ki fuskance ni" tom" abunda tafada kenan, juyowa yayi yana facing dinta yace " Zuhura bazan boye mikiba kaunarki tafaramun yawa a zuciyata harta kai matsayin da bazan iya cigaba da boye miki ba, ina sonki zuhura ina kaunarki inasan rayuwa dake har abada" amma yaya" katseta yayi tareda riko hannayenta su duka yana cewa"Please Zuhura karki ce bakya sona dan Allah kitaimakamun" tausayi yabata taga kamar ita da ba kowan kowa ba namiji kamarsa yana rokon ta, ido yakuramata yana jiran amsan dazata bashi, " yaya Ahmad kaga ni yarinya ce baze yiwu nadauko soyayya kuma ga karatu dazan fara" Zuhura bawai iya soyayya ta nakeson ki karba ba inaso ki amince nazama mijinki" saurin kallon shi tayi tace "miji kuma"! " yes Zuhura miji nidai kawai kibani dama" tom shikenan amma" Please dan Allah ya isa tunda dai kin amince mun" yanzu dai mijinki najin yunwa" bata kulashiba tajuyar da kanta gefe, " in munje gida zaki hadamun breakfast ko naje restaurant naci" kawai muwuce gida" angama ranki ya dade" daga haka sukanufi gida.
be tashiba se karfe 10:39 shima saboda ze shiga hospital dinshi ne, wanka yayi yashirya cikin kananun kaya yayi bala'in kyau, falour yafuto dan yayi breakfast , bakowa a falour , shigowa sukai suna ta dariya, kallon mamaki Ammar yashiga yiwa Ahmad a zuciyarsa yana cewa ' taya akai yarinyar nan tasaba dashi' ganin bashi da amsa yasashi cewa" inason coffee" to tace kawai, tashige ciki kitchen tashiga danta hada musu breakfast, Mamy da Inna tagani a kitchen din " kai Mamy ashe kuntashi" muntashi tundazu ai kinsan yau Hajiya zata dawo" ya school din"? lafiya lau mungama komai gobe zan fara zuwa" masha Allah" islamiyya ma gobe zaki fara zuwa" ita Amira sedai nakaita dakaina inna samu lokaci" lah namanta su yaya Ahmad suna jirana nakai musu breakfast" ji shashanci dan Allah" Inna tafada , dariya Mamy tayi tace" Allah ya taimake ki mungama hada breakfast din" yaya Ammar yace ahadamai coffee" to seki maza ki hadamai ai kikai musu" hadawa tashigayi dayake yanzu tama iya hadawa sosai, bayan tagama tadauki tire din kayan abincin tafuta, suna zaune Ahmad yana taimai hira shikuma yamai banza yana danna wayarsa, karasowa tayi ta ajiye kayan akan dining din, saving dinsu tayi ta ajiyewa kowa, shikuma tahadamai da coffe dinsa, Ahmad ne yace" sannu gimbiya mu gode" murmushi kawai tayi tabar gurin, coffee din yadauka yafara sha seda yagama yamike , Ahmad ne yace " bazakaci wani abu bane" no ya isheni" shikenan seka dawo" daga haka yafuce, motarsa yayi wa key yanufi hospital, yana isa office dinsa yashige kan kujerar sa yanema yazauna gaba daya jiyake ransa a bace kuma shi kansa besan dalilin bacin ranba, nurse ce tashigo tana fadin, doctor ana bukatar ka a theater room, an kawo wata mata bazata iya haihuwaba, kai kawai yadaga mata alamar yaji, daga haka tafuce, tashi yayi yasa kayan operation , jiki ba kwari yafuce, yau kwata kwata Ahmad be futaba, Nafisa tamai har 6 miss call dama sauran yanmatansa dasuke sharholiya, be daga kiran kowaba yau, yana zaune a falour, dankawai ya dinga ganinta, sun kammala komai na girki yau abincin gargajiya akai a gidan saboda Hajiya zata dawo, 1:00 suka gama jera komai akan dining, wanka Mamy tashige dantai itama Inna tawuce dakinsu danatai sallah, Zuhura ce ke karasa shirya kayan a dining, Ahmad ne yakaraso gunda take, kallonta yayi yace, "gimbiya ta sannu da aiki" yawwa ya Ahmad kaima sannu" kinaso natayaki ne" yaya Ahmad rufamin asiri kar azo a ganka kana aiki" aikam kinsa sena tayaki" yaya Ahmad dan Allah kabari karkayi" tom nabari amma sekince, " my honey kabarshi " yadda ya lankwasa murya ne yasata kwashewa da dariya, shima dariyar yake , Jawad ne yashigob, kallonsu yayi cikin mamaki, karasa wa gurin yayi yana fadin, " yaya Ahmad yau kuma kyautar me aka muku ne"? dariyar suka dena suna kallonshi, Ahmad ne yace " babar kyauta makuwa me girman gaske" ah natayaka murna wacce kyauta kenan" kallon Zuhura yayi yace, " senan gaba zaka ga kyautar" ganin tagama shirya komai yasa tabar gurin, dakinshi Jawad yawuce, yanashiga yacillar da wayarsa da key din motar, " ya Ahmad mekayi haka dan meyasa zaka rigani" daka bari nacinma burina akanta " gaba daya bakin ciki ya ishe shi , dahaka dai ya shiga toilet ya watsa ruwa, itama tana shiga dakinsu tashiga toilet tayi wanka tayi alwala, sallah tayi kana tashirya riga da wando ne rigar har gwuiwa, mayafi tasa tayi rolling, kallon kanta tayi a mudubi, jitai kamar bazata iya fita da kayan ba, Nadra ce ta shigo da gudu tana fadin, " aunty Zuhura kifito mutafi Mamy tagama shiryawa, bata amsa ba tana dai tsaye gaban mirror, inna ce tashafa addu'a datai ta kalli Zuhura tace " Zuhura bikiji yarinya namiki magana ba" oh Inna banji taba" tace fa hajiya tashirya kumadai kinsan tace dake zasu tafi" Allah Inna banajin zan iya futa da kayannan" bakomai kifuta dasu ai naga rigar takai gwuiwa" tom Inna bara mutafi" tom sekun dawo" daga haka suka fuce, duk sun hadu a falour har Ilham, shigowa sukai ita da Nadra, Mamy ce ta kalle ta tace " ah Zuhura kinyi kyau sosai" dariya kawai tayi tasamu kasan carpet tazauna, Mamy ce tace mata, " meye haka kuma sekace wata bakuwa kitashi ki hau kujera" tashi tai tahau kujerar, itakam Ilham kamar ta fashe jin ance Zuhura tayi kyau musamman ganin yadda su yaya Ahmad duk suka zuba mata ido, Jawad kam jiyake kamar zuciyarsa tafashe, azuciyarsa yace, ' yanzu dole nabar ma yaya Ahmad ke' kece kalata Zuhura inasanki amma dole na hakura nabarma yaya Ahmad' shikam Ahmad ba abunda yake se kallonta yana murmushi, Mamy ce tace, " wai Ammar haryanzu be dawoba" bara nakirashi awaya" wayarta tadauka kiranshi tayi, dai-dai lokacin dayake futowa daga threater, dauka yayi yana fadin " Mamy " Ammar kana ina ne kaifa muke jira zamuje dauko hajiya airport" Mamy kuje kawai banajin zanje" aikam dole kaje kai maza kadawo abbanku ma yanzu ze karaso" ok ganinan" daga haka takashe
💞💞 SOYAYYA DA IZZA 💞💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 24
________________ Abba ne yashigo , ganinsu yayi sun taru a falour, "ah duk kun shirya kenan" wlh mungama dama kai muke jira se Ammar, sannu da zuwa sukai mai su duka, itama Zuhura sannu da zuwa tayimai, amsawa yayi yanacewa, " ya makarantar taki kunje yaudin ne" eh munje gobema zan fara zuwa" to Allah ya taimaka Allah yabada sa'a" ammeen" daga haka ya shige part dinsa , Mamy ce tamike tabishi, Ahmad yamatsa kusa da Zuhura ya rada mata yace, "kinyi kyau sosai my queen" murmushi kawai tayi, Ammar ne yashigo ganinsu yayi duk a falour, Ahmad yakalla dake kusada Zuhura, Ilham ce tace " sannu da zuwa" tafada tana wani juya ido, ko kallonta beyiba , yace ke kawomun coffee, ta san da ita yake , tamike tanufi kitchen, seda tagama tahadamai coffe din ta wuce part dinsa danta kaimai, shikam yana shiga yafada toilet dan ya watsa ruwa, tura kofar tayi tashiga bakowa a falour , bedroom din tawuce nanma bata ga kowaba, coffe din taje gaban mirror ta ajiye, harta juya zata tafi tajuyo muryarsa yana cewa" nabaki umarnin tafiya ne" ah ah naga baka futo bane" to dauko mun coffee din ki kawomun " tom" ta amsa, coffee din tadauka takaimai, karba yayi yana fadin "ke kika zabo kayannan" ah ah" to waya zabo miki" wacce kace takaini" ok yafada yana kara kai coffe din bakinsa a karo na biyu, " karki kara sasu daga yau" kallonshi tayi tace "saboda me" saboda sunmiki kyau dayawa karki kara sasu" tom kawai tace" zan iya tafiya" no sena gama" mikomun lotion dincan" gaban mirror din tanufa ta daukomai, ta mikamai, "zauna kan kujera" ba musu tazauna, amma gaba daya ita ba a nitse take ba, gashi daga shi se tawul a kugunsa, mutsu-mutsu take yi alamar zaman ya isheta, yana kallonta yanuna bemasan tanayi ba, Ilham ce a falour gaba daya hankalinta yaki kwanciya ganin Zuhura tayi part din Ammar, tashi tayi tanufi part din, shan coffee din yake yana kallonta jefi-jefi , kamar ba wanda ake jiraba, itakam tagaji da zama sotake yace mata ta tafi, shi kuma yaki fada, shi kansa besan meyasa bayasan ta tafiba, haka kawai yake jinshi cikin nishadi, Ilham ce tashigo dakin , kallon Zuhura tayi tace "ke meya zaunar dake anan" kame-kame tafara alamar tatsorata, kallonta Ammar yayi , yayi murmushi kana yace, "ni nace ta zauna" ok to tashi kifuta"tom tafada tana mikewa zata tafi" Zuhura yafada , akaron farko daya fadi sunanta , juyowa tayi tace "na'am" karbi wannan cup din kitafi dashi" karba tayi tai maza ta futa, kallon Ammar Ilhmam tayi tana cewa" wai kai meye hadinka da wannan yarinyar" be bata amsaba yaci gaba da shafa lotion din a jikinshi, "kasandai koya naganka da wata mace dole zanji ba dadi amatsayina na matarka" dagowa yayi yana kallonta yace" ke kidena proud da cewar zaki zama matata" ko yanzu zan iya cewa nafasa " dama nasani baka sona ai dauramaka ni akai" kamar kuwa ki sani" Nagode yaya Ammar" ok futar mun daki" baseka koreniba zanfuta" daga haka tafuce shikam ko a jikinshi yaci gaba da shiryawa, bayan yagama shiryawa yafuto ba karamin kyau yayi ba, suma su abba da Mamy duk sun futo, dan haka tafiya sukai, bayan sun isa airport dinne basu fi minti 5 ba jirginsu hajiya ya sauka, farace tas idan kaganta kai kace ba jikokinta bane, Abba ne yatafi gurinta rungumeshi tayi , tana dariya, karasowa sukai, Mamy ma rungumeta tayi tana mata sannu da zuwa, suma sannu da zuwa sukai mata gaba dayansu,zuhura ma kallonta tayi tace"sannu da zuwa" yawwa sannu yarinya" ya hanya" lafiya lau usman ina kuka samu wannan kyakyawar yarinyar" Hajiya muje dai gida, daga haka suka nufi mota " ah ah nifa bazan hau motar dan iyayinnan ba kar inje ya cillar dani a hanya" dariya sukai har shi Ammar din yace" aikam dai kika hau cillar dake zanyi" dariya suka kumayi , kana suka shige mota, bayan sun isa gida Mamy tasa Zuhura takaima Hajiya akawatinta dakinta da aka gyaramata, wanka tayi tafuto , dining suka nufa su duka, saving dinsu Zuhura tayi, Hajiya ganin dambu yasata washe baki tana fadin "kai amma dai Allah yamuku albarka abunda nake sha'awar ci" ai Hajiya nasan kinasan dambu shi yasa nasa amiki" aikam kin kyauta" to sukuma su dan iyayi kuma me zasu ci" ganasunan zata zubanusu" oh wai bazasu ci abincin gargajiya ba waisu turawa" wlh kuwa hajiya " daga haka takammala zubawa kowa, ta wuce zata tafi taji muryar Hajiya nafadin " ke yar nan kizo muci abincin mana" ah ah zanci acan" ah ah zonan tawo kusada ni kizauna kici kema kinji" bayadda ta iya hakan yasa tace to, zama tayi abincin tazuba , kawai dai ci take dan ba a sake takeba, seda suka gama tas, tana gani sun fara tashi itama ta tashi tawuce ciki, Hajiya ce tace , " wai usman ina kuka samo yarinyane gatanan kyakyawa" labarin abunda yafaru yabata tun daga farko har karshe, ta tausaya musu sosai, dahaka tashige dakinta danta huta, Zuhura kam nashiga tafara cewa Inna zata ci abinci, nunamata kular Inna tayi tace taje ta diba, diba tayi takoma gefe tana ci, amira ce takalleta tace" aunty Zuhura kinga jirgi" eh nagani kato makuwa" ba irin nawasan Nadra bane" eh yafi nata girma sosai" haka sukai ta hira harta gama cin abincin tawanke bannunta, dukansu kowa yabar falourn duk sun shige ciki, Abba da Mamy ne kawai a zaune, Abba ne yake waya yana fadin" wato Alhaji Aminu sabida kaji Hajiyar ka ta dawo ka kirani ko"? yi hakuri abokina kasanfa dole nazo naga Hajiya" gaskiya kam to seyaushe zakazo"? yau dinan ma zan zo da daddare" ok to seka zo" daga haka yakashe wayar" wai kaida wa kaketa wayane"? wlh Alhaji Aminu ne yaji Hajiya tadawo yace zezo da daddare" to Allah yakawoshi" ameen" futa Ahmad yayi, gurin Nafisa yanufa dan ta dameshi da kira, yana zuwa yayi knocking , budewa tayi, shiga yayi, wasu mata yagani su biyu , ba marabarsu da tsirara kallo su yayi a wulakance sukan suna ganinsa suka fara kissa da kisisina , sedai sun makara dan Ahmad yanzu ya rage maitar mata, yana shiga tabishi, "haba me yasa zakamun haka tun yaushe kace zakazo" nagayamiki ina wani uzuri ne shiyasa ban zoba" ok yanzu kana cikin shiri ko" no baby banjin dadi yanzu" anya ba watace takwace mun kaiba da kaida kafun na nema kanema kusan sau uku" kafadamun kodai yanzu bakajin dadi nane" no baby bahaka bane yanzu banajin dadi ki bari se next time" amma banji dadiba" ok nizan wuce" kai tun yanzu" eh inada abunda zanyi" daga haka yanike , futa yayi , bayan ta rakashi ta dawo, " kai anya ba watace takwace mun shiba" daya daga cikin yan matance tace" kema tun yaushe ake miki kizo murakaki gurin wani boka wlh daba wannan maganar ake ba aida tuni ma kunyi aure" aini sadeey tsoron irin wadannan nakeyi" to shikenan seki tazama kina zaune ganinsama seya gagareki" shikenan zanyi tunani
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 25
__________________Su Inna ne suke ta shirya abincin dare, ita kam Zuhura tana can tana bacci, karfe 6:30 da bakon abba yazo, dukansu suna falour , gaggaisawa suke yi, Abba nata tsokanarsa baya zuwa amma dan Hajiya ta dawo yazo, hajiya tace "kasamuma yazo din danni ko usman" wlh kuwa Hajiya" Aminu wai haryanzu bakai aureba ne" Hajiya haryanzu dai banyiba " Aminu badai kai niyyar yi ba ace tunda Hafsa ta rasu ka kasayin aure" Hajiya zanyine" za kai to se yaushe" dariya yayi yace hajiya nan kusa" Abba ne yacemai su wuce masallaci anyi magaruba, daga haka suka fuce gaba dayansu harsu Ahmad, dasu Ammar dayake kowa yana gida, itama Hajiya dakinta tanufa dantai sallah, bayan sunyi sallah sun dawo ne, Mamy tace musu , su taso anshirya abinci, tashi sukai suka nufi dining, kitchen Mamy tawue danta debo sauran kayan, Inna tagama hadasu , shigowatai tana cewa, Inna Zuhura tayani diban kayannan mukaisu sunyimin yawa" diban kayan sukai, a dining suka samesu a zaune, gaishe da kowa Inna tayi tayiwa Hajiya sannu da zuwa, amsawa tayi tana cewa " mahaifiyar Zuhura ko" eh" Allah sarki munta ganin girke- girke sannu da kokari" murmushi tayi kawai ta tashi tashige ciki, shikam alhaji Aminu ya tsura mata ido kamar me, be dauke idonsa ba harseda takulemai, saving dinsu Mamy tayi, sannan itama ta nemi kujara ta zauna, se 7:30 ta tashi , ita kanta tayi mamkin baccin datai , toilet tashiga tai wanka tayi alwala, kana tafuto tayi sallah, bayan ta idar da Sallah ne Inna tashigo, "kardai se yanzu kika tashi" wlh Inna nima bansan anyi magaruba ba" toni banasan baccin la'asar dinan karki karayi" tom" ga abinci can kije ki zuba" tom" daga haka tamike , abincin tazuba tafara ci, bayan sun kammala cin abinci suka taba hira kadan kana yace ze wuce gida, sallama sukai da Hajiya da Mamy, kana Abba yatafi rakashi, parking space yarakashi, kallon Abba yayi yace, " nikam usman naga wata agidanka" wa kenan" wacce suka zo da uwargida kawo abinci" oho ai a gidan take a zaune" to nifa gaskiya tayimun na yaba da hankalinta" to ai ba komai zan sa matar gidan tamata magana" yawwa dan Allah kataimakamun ni ko gobema ashirye nake" dariya Abba yayi sosai yace"kai mutumina kaida ake tacewa kayi aure kaki" bansamu wacce tayimun ba se yanzu" yo ka kwantar da hankalinka kamar kasameta" Allah abokina "kwarai kuwa"to nagode" daga haka sukai musabaha , motarsa yashiga megadi yabude mai gate yafuta, seda yafuta Sannan Abba yadawo, su Hajiya ya tarar a falour shima zama yayi "kallonshi Hajiya tayi tace "Usman yadai naga kadawo cikin farin ciki" Hajiya abun farin ciki ne yasaamemu" to me kenan" Mamy tafada tana gyara zama " Alhaji Aminu ne yaga mahaifiyar Zuhura yanaso" me alhamdulillah" Mamy tafada tana washe baki "kai mu gode Allah" wlh kuwa Hajiya naji dadin maganar nan" yanzu ke yakamata kisameta kuyi magana" hakane yanzu makuwa" daga haka tamike tanufi dakin su Inna, tana shiga tagansu sunata hira sukuma su Amira da Halifa sunata bacci, sallama tayi, suka amsa su duka "ah hira ake tasha ne"dariya sukai yi, Mamy ce tace " Zuhura kikaima Ammar coffee" tom" tafada kawai, Mamy tayi hakanne dan Zuhura ta futa tayi magana da Inna, Mamy ce takalli Inna tace " Inna Zuhura inason nayi magana dake" to Hajiya inajinki" abokin Abba ne dayazo yau yagankin ya yaba da hankalinki , to yace wa da Abba mumuki magana, muji taba kinki" Hajiya amma kinga ai inada ya'ya kuma ina zankaisu inaganin be kamata nayi aureba" kafadarta Mamy ta dafa tace " wannan duk ba hujja bane, ya'ya kuma ko mu zamu rike su" hakane Hajiya to indai kun amince nima na amince" yawwa haka yakamata kice Allah yatabbatat da alkairi" ammeen" daga haka Mamy ta tashi tafuta, bayan tahada coffee din tawuce part dinshi, tana shiga taganshi a falour a zaune, sallama tayi cikin nutsuwa, dagowa yayi ya kalleta, karasawa tayi inda yake, tsugunnwa tayi tace "ga coffee din" kallonta yayi cikin mamaki yace "nace akawomun coffee ne" Mamy ce tacemun nakwoma coffee" ok to bani" mikami tayi yakarba , mikewa tayi zata tafi yace "dawo nan" dawo wa tayi yace " me yasa dakin kawomun kike son tafiya ne, kuma inna gama waye ze futa da cup din" kayi hakuri" daga haka bata kara cewa komai ba tanemi kasan carpet tazauna " ya school din naki"? "ai se gobe zan fara zuwa" to Allah yabada sa'a "ameen" dahaka ba wanda yakara cewa komai, gabadaya tagaji bacci ma takeji ga ba damar yimai magana, tana wannan tunanin har bacci barawo yasaceta, shikuma shan coffee dinsa yake hankali kwance, seda yagama tas yajuya gareta, bacci take hankalinta kwance, tanamai kyau sosai musamman idan tana bacci, saukowa yayi daga kan kujerar da yake, yamatsa kuda ita, fuskarta yataba alamar ta tashi, ko motsi batai ba balle ma ta tashi, hancinta yakama yaja, aiko dasauri ta tashi tasa kuka, hannunsa yasa yatoshe bakinta, kokarin cire hannunsa take, amma takasa, alamar tayi shiru yamata da dan yatsansa, shiru tayi takama kanta da yanzu tagane inda take, " ke daga cewa kijira shine zakimin bacci" bansan nayiba" oya tashi ki tafi" daga haka ta tashi tafuce, tana futowa tawuce dakinsu tana tangadi, tana shiga tazube kan bed se bacci
"biki fadamun ya kukai da mahaifiyar yarinyar nan ba" kar ka damu amince" dagaske" kwari makuwa" aikam safiya nayi zan kirashi na sanar dashi dama yanata kirana" aikuwa dai kafada mai ta amince koyaushe ma za a iya daurawa" ai bazama mubari satinnan yacinye ba a daura aurenan ba" gaskiya dai haka yakamata" ga kuma hidimar bikin Ammar sati ɗaya ne ya rage mana" to ai ba wani abu za aiba komai akwai shi gidansa yananan a ajiye" ai wai maganar lefe " kinga ko a rana dayane zaku iya siyan jayan lefen" to shikenan Allah dai yakaimu da rai da lafiya"ameen"
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 27
_________________ Dasafe tana tashi bayan tagama komai, itama taje ta tashirya tafuto cikin uniform, ash da fari, skirt be iya gwuiwa ash colour, se farar riga me dogon hannu ,se hijabi fari, safarta tasa fara tarufe mata har kwairinta, jakarta tagoya, uniform din sun mata kyau sosai, Bala driver ne ya shigo yace musu insun kammala yana jiranasu, sun gama komai dan haka kawai suka fuce, har cikin makaranta hakaisu, class Nadra da Muhsin suka wuce, ita kuma office din principal tawuce, bayan taje ne, principal din ta hadata da wani malami daya kaita ajinsu ya gabatar da ita, hakan akai aji yakaita, ya gabatar da ita, gurin zama yanunamata, mutum biyune mata itace ta uku, bayan malamin yafuta ne, daya dag cikinsu takalleta tace, "nice to meet you my name is islam" thank you" dayarce tace "nikuma my bame is walida" ok nice to meet you all" danaka suka saba har suka fara fira kamar su san juna, malami ne yashigo hakan yasa duk sukai shiru, gaishe shi sukai, kana yabasu izinin zama, koyar dasu yashi yi, kuma ba laifi kuma suna ganewa, bayan yafuta ne, Walida takalli Zuhura tace"amma dai kingane ko" murnushi tayi tace "eh nagane" indai akwai Abinda yashuge miki duhu ki tambaye mu inshaallah" murmurshu takarayi tace "karku damu indai naga abinda bajganeba zan tambaya, Nagode da kulawa" bakomai ai yanzu munzama daya" Zuhura taji dadin yanda suke nunamata kulawa,
Abba ne yakira alhaji Aminu yasanar dashi sungama magana koyau yakawo kudi, yayi murna sosai har yace yau zezo, bayan sun kammala magana yakashe wayar,
Ammar yana part dinsa be ma futoba har anyi azahar ko break fast be fito yayi ba, dan yau ma kwata-kwata bayasan fita hispital, yana zaune a falour yana aiki a laptop dinshi, wayarsa yadauka yakira Mamy "hello Mamy insan coffee" au bazaka futoba yau kenan"? Mamy ina aiki ne shiyasa" ok to
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 19