so danta ya auri irina" matsawa yayi kusa da ita yakamo hannayenta yace "kinda matukar daraja da kima agurina kinda hamimmanci agurina queen kidena jifan kanki da wadannan kalaman zuciyata namun zafi inkina fada" "yaya Ahmad dan Allah ka rabu dani kamar yadda mahaifiyar ka tafada" "bazan iya ba queen har abada" "aikam yazama dole yaya Ahmad" "queen an riga da anbani ke kuma zamuyi aure Abba ya tabbatar mun da hakan" ware idanuwanta tayi tana kallonshi "kwarai kuwa kina kammala secondary zamuyi aure" "amma yaya Ahmad mom dinka fa" "su Daddy zasuyi magana da ita" numfasawa tayi kana tayi shiru, Yasmeen ce tafado dakin, "ah kace lovers ne aciki" dariya Ahmad yayi yace "bakya rabo da tsokana" "kitashi muje Mamy nata nemanki zamuje gidan kwalliya" "tom bara natshi mutafi" daga haka tamike tadau mayafinta, "Yasmeen ki kulamun da ita fa" "baka da matsala yaya Ahmad" daga haka taja hannunta suka fuce, shima fitowar yayi, yanufi bedroom dinsa dan yanzu jin shi yake fes, Jawad ne yakwashe su yakaisu gidan kwalliyar, bayan an kammala musu suka shirya tsaf , sunyi kyau sosai kamar yar tsana, bare ma Zuhura kamar kasace ta, leshi ne baki me adon golden, dinkin fited gown, ta mata kam ajiki, hips dinta yafuto sisai, bayan an gama musu Jawad yakoma ya kwasosu yadawo dasu gida,
"kai Ammar kanan mutane nacan suna ina ango" ko kallonshi beyi ba yaci gaba da latsa wayarsa, zama Ahmad yayi kana yace "nidai katayani murna burina yacika" "name fa" yayi maganar a hankali, "yau Abba yabani queen amatsayin wacce zan aura" besan sanda wayar hannunsa ta subu ce ba tafadi kan bed din "kamar ya" "eh yadda kaji yanzu tana gama secondary da sati guda zamuyi aure" innalillahi wa inna aikaihi raji'un, abunda yake ta mai mai tawa azuciyarsa kenan, afili kuma yace "gaskiya ne natayaka murna" daga haka be sake cewa komai ba yadau wayarsa, shikam Ahmad tashi yayi yanufi Waldrop dan dauko kayansa, azahiri danna wayar yake, amma badini bemasan ina yake dannawa ba, zuciyar sa ce take fadin 'Ammar watakila yarinyar nan ba alkhairi bace atare dakai kacire sonta azuciyar kawai' haka yadinga tunane tunane azucuyarsa
bayan magaruba kowa ya gama shiryawa tsaf , za a tafi dinner, banda ango dabemasan za ai wata dinner ba, Mamy ne da aunty Aisha suka tafi bedroom dan sanar dashi, suna zuwa suka tarar dashi zaune kan kujera ya dafa kai, karasawa sukai , Mamy ce tace "Ammar meke damun ka haka" dasauri yadago kai yana fadin "no Mamy am fine" "ok tashi ka shirya" "Mamy shirya wa kuma" "eh zamu wuce dinner na ne" "dinner kuma" "eh Ammar dinner" aunty Aisha tafada, "amma aunty Aisha meyesa ba a sanar dani ba" "kaga Ammar bikin dangi ne bazaka ce zamu yi biki salam ba" "to amma" "kaga banason wani zance kayi abunda nace" shiru yayi ba kara magana ba, "A'isha bashi kayan nan ya shirya muna jiranja a kasa" mikamai ledar hannunta aunty Aisha tayi kana suka fice, ji yake kamar kurma ihu saboda zafin da zuciyarsa keyi, komai yahade mai, yau bashi da sa'a a rayuwarsa, dahaka dai yatashi yayi wanka ya shirya, cikin kayan dasu Mamy suka kawo mai, shadda ce coffe se kyalli take tamai masifar kyau, amma sedai fuskar nan a murtuke ba walwala,
Duk anfara ya watsewa an tafi gurin dinner, suma su Zuhura duk sun tafi, ita Ahmad ne yatafi da ita, Yasmeen tayi tayi yabarta su tafi a motar Jawad yaki, hakaya dauketa suka tafi, suna su Mamy dasu mom Ilhasn dasu Inna su aunty Aisha da sauran iyayen ango da amarya duk suka tafi, su Hajiya ne kawai a gidan dan sunce bazasu zo ba, se su Abba dasuke part din Daddy, shima Ammar seda su Mamy suka tasa shi gaba suka tafi suka ce yajira amarya a can, gaka dai yabisu suka tafi, tunda suka je Ahmad be bar gurin Zuhura ba saboda yana tsoron kar wani yazo gurinta, ita ma taji dadin hakan dan batasan zama ita kadai, dan Yasmeen bata zama guri daya, tana filin rawa,
suna nan zaune sukaji ana fadin, ga amarya da ango nan zasu shigo, hankalin kowa yakoma gurin, awaje kam su aunty Aisha sun dage Ammar se ya rike hannun Ilham, shikuma yace baze wani rike hannun taba, haka dai suka kyaleshi, waka aka samusu, suka shigo, kawayen amarya kuwa na bayansu, Ilham se washe baki take kamar me tallan makilin, dan kyau tayi kyau ba karya, coffee din material tasa me adon golden, shima coffe din kaya yasa, fuskarsa a tamke ba alamun wasa, haka dai harsuka karasa gurin zamansu, suka zauna, nan aka fara gudanar da bikin, sunyi liki kamar hauka, sun watsa kudi, dan kaf cikin family din ba wanda beyi liki na kuzo mu gani ba, shikam Ammar kamar gunki, baya motsi, itakam Ilham da aka kusa tashi tayi rawa ita da kawayenta kamar hauka, Zuhura kam suna zaune tare da Ahmad, sedai yatashi yaje yayi liki yadawo, Yasmeen tayi tayi Zuhura tazo su shiga filin rawa taki, bayan antashi Ahmad yadau Zuhura suka wuce gida, suma ango da amarya suka tafi a mota daya,
suna komawa gida yana fitowa daga mota be jira komai ba yashige ciki, bedroom yawuce, yana zuwa yacire kayan jikinsa ya fada toilet, bayan yafuto yayi sallar Isha, lokacin 11:00pm har tayi, bayan ya idar yakoma kan bed ya kwanta ya rufe idonsa kamar me bacci,
dakyar Ahmad ya rabu da Zuhura ta tafi , kana shima yashige, tana zuwa tashiga toilet ta wanke fuskar ta tas, kana tayi alawala, tafuto tadau hijabi tayi sallah, bayan ta idar tahau gado ta kwanta dan ta gaji sosai, aikam tuni bacci yadauketa, Yasmeen kam nacan tare da Jawad sunata hira,
"kardai har kayi bacci" yanajin shi amma yamai banza, har Ahmad yayi wanka yayi shirin bacci, shima kwanciyar yayi, yana kwantawa wayarsa tafara kara, wayar yadauka yana fadin "hello Nafisa ina jinki" "haba Ahmad kamarya kana jini" "eh kamar yadda kikaji" "ok yau bakazo ba kuma kasan bansan zama nikadai" "tau ina wani uzuri ne shiyasa" "to kazo da safe Please" "bazan miki alkawari ba" "ina son ganinka ne" "to kijira ni kozanzo sai gobe da daddare" "karfa kaki zuwa" "kinga ya ishe ni zanyi bacci ne" daga haka yakashe wayar, Ammar najin duk abunda yake, azuciyar sa yafara ayyana 'dama Ahmad haryanzu be rabu da matan banza ba, kuma yakeson auren Zuhura' har Ahmad yayi bacci shidai be samu bacci ba,
Ilham kam se sharholiyar su suke ita dasu Feenat, acewar zasu jima basu hadu ba, dan haka yau kwana sukai suna harka, safiyya nayi suka shiga shiri, dan yau za a kai amarya, Ilham shiryawa tayi cikin leshi fari me adon coffe, tayi kyau, batai make up ba,
yana tashi ya shiga wanka bayan yafuto yashirya cikin milk colour, yasa hula, yayi kyau bakarya, shi ya matsu su tafi ma, dan haka yasauko kasa, su Mamy ne dasu Inna dasu aunty Aisha, "ango harka shirya kenan" "aunty Aisha na shirya" "to zumudi kake ka tafi amaryarka" bece komai ba yakalli Mamy yace "Mamy karfe nawa zamu tafi" "karfe 2:0ppm" "kai Mamy se mun kai 2:00pm" "eh ai kamar yanzu ne " kai yasa yafuce yafuce daga falourn, yana futa ya nufi garden din dake gidan yaje yazauna, shi kadai,
Zuhura natashi tayi wanka, Yasmeen ma wankan tayi, suka shirya cikin shadda, ta Yasmeen brown ta Zuhura light pink, sunsha duwasu, dinkin doguwar riga, cikin gidan suka nufa dansu gaisa, karo sukaci da Amira, Zuhura ta kalle ta tace "lallai yarinyar na nifa tun lokacin da kuka zo rabo na da ita" "tanacan ta samu kawaye yan mata sunata shagalinsu" "kai yaya Zuhura kumafa kunacan kuna shagalin naku" "ah lallai to wuce" "yawwa yaya Yasmeen" daga haka tashige , suma suka shige falourn, gaishe da kowa sukai, "Zuhura kunyi breakfast ne" "yanzu dai zamuyi Mamy" "muje nazuba muku" daga haka suka bita, abincin ta zuba musu komai, kana suka futo, zama sukai suka fara ci Inna ce tazo gurinsu tana fadin "baku ga autana ba" "Inna kibarshi kawai idan ma ya bata shikenan mun huta da tsokana" Zuhura ta karashe maganar tana dariya "zaki ci gidanku Zuhura" "aunty autanki fa ya zama saurayi kibarshi kawai" "shakiyan yaranan bara naje na duba shi dakaina" bayan sun kammala suka tashi suna fucewa, suna futa Jawad yakira Yasmeen, hakan yasa ta wuce kawai, ita kuma Zuhura gidan tashi ga zagayawa, garden din gidan tagano hakan yasa tanufi can, tana zuwa tashiga zagaya gurin, kanshin turarensa take ji duk inda taji kanshin turarensa seta gane shine, saboda kamshinsa na dabanne, cigaba da zagaya gurin take tana kallon flowers din dake garden din, hangoshi tayi zaune kan kujera ya juya baya, tagane shi, hakan yasa ta nemi hanyar futa daga garden din, kadangare ne yazo ya gifta takan kafarta, aikam tafasa uban ihu har tana faduwa kasa, jikinta na rawa ta rumtse idonta, dan ta tsani ganin kadangare ballantana ya tabata, saurin juyowa yayi, ganinta yayi zube a kasa tanata kuka, nufarta yayi yakamota ya tadata tsaye, karkarwa jikinta, kamata yayi ya nufi inda kujeru suke da ita yazaunar da ita, se lokacin ta bude idonta tana waige waige, se kuna ta kalle shi, shima kura mata ido yayi, kana yabude baki yace "meya faru" "kadangare ne ya hau kafata" numfasawa yayi kana yace "shine kika cikawa nutane kunne da ihu" shiru tayi tana sunkuyar dakanta, shina be kara magana ba, kawai dai yana kallonta yana tunanin wai zata auri Ahmad yarinya karama da ita rayuwar ta lalacewa zatai tunda haryanzu Ahmad be dena neman matan banza ba, jin shurun yayi yawa yasa ta dago ta kalleshi, idanunsu ne ya sarke dana juna, yakasa dauke idonshi haka itama, sunkai 15mint ahaka, kana yadawo daga duniyar tunanin daya fada, yace "tashi kitafi" tashi tayi jiki ba gwari tawuce, idanuwansa duk sun kashe mata jiki
💞SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Ina masu bibiyar books dina😃to ina muku albishir da sabon book dina😁dana fara rubutawa✍️✍️ me suna YAN BIYU NE ina baku shawara ku bibiye book din nan😇dan akwai chakwakwa kiya kala kala zaku nishadantu🤣zakuma ku wa'azantusosai kudai kawai ku bibiye kafun free page yakare ku biya kan naira
300 kacal ba tsauwalawa😍ina alfahari daku🤩 masoyana😍 kune kwarin gwuiwa ta😀i love you so much❤💔my pans😘
ina godiya da addu'o'in ku🙏🙏🙏
dayacce kuke yabon book dina💅💅 duk da shine nafarko, gudiya buhu buhu😂😂
nice taku har kullum Hadizatu wacce kukafi sani da (MRS K D) kucika da bibiyata nukuma zanci gaba da nishadantan daku😀😀
https://chat.whatsapp.com/FPb99RjggTbAcCFg1aFrVx
page 43
________________Karfe 2:00pm aka fara shirye shiryen kai amarya, bayan kowa ya shirya, su Abba sukace suna bukatar ganin matan zasuyi magana dasu, haka suka rankaya gaba daya suka nufi part din daddy, bayan sunje kowa yanemi guri yazauna, Abba ne yayi gyaran murya kana yace, "ba komai ne yasa muka tara ku ba illa kan maganar auren Ahmad damuka riga muka yanke shawara iya mu, kawai dai zamu fada muku ne a matsayinku na iyayensu mata, Ahmad yazo mana dazancen yanason yarinyar gurin Habiba matar Alhaji Aminu wato dake zaune agida na Zuhura kenan" mom ce ta waro ido tanasan jin karashen zancen "mun fahimci yarannan suna san junansu hakan yasa muka yanke shawarar hadasu aure kamar yadda Ahmad ya bukata" Daddy yafada, "ke kuma kiyi hakuri naba da yarinyarki batare dana ji ta bakinki ba, amma idan bakiso bazamuyi maki dole ba tunda yarinyar kice" Abba ya karashe maganar yana kallon Innna, baki ta bude tace "aini duk abunda kuka yanke akan ya'ya na to bani data cewa saboda bamu da tamkarku, Allah yabasu zaman lafiya" ammeen kowa ya amsa banda mom data cika tayi fam, "amma ni Ahmad be taba sanar dani yanason Zuhura ba" Mamy tayi maganar, Hajiya ce tace "to yanzu yaushe kuka sa bikin"? "Hajiya munyanke idan ta kammala secondary za ai" "to hakan yayi" tunda aka fara mom ce kawai batace kala ba, har aka tashi, Allah Allah take taga Ahmad dan fada na cinta, sedai har aka futo kai amarya bata ganshi ba, futowa akai Ilham tasha alkyabba se kamshi take, aka sata a mota, kodan kukan amarenan ma ita batayi, su Zuhura ma duk suka shiga mota ita da Yasmeen, bawanda yaje raka amarya, saboda ga su Mamy ga Hajiya ga aunty Aisha ga Innar Zuhura, shi Ammar su Abba ya diba da Alhaji Aminu yajasu suka tafi, Ahmad kam sun rigada sunyi sallama da Zuhura, a haka dai suka dau hanyar Kaduna,
basu wani dau lokaci ba suka isa, Mamy ce tace kar a kai Ilham yanzu abari se dare zatayi yar walima kawayenta da ke nan zasuzo, haka a ka fara shirye-shiryen walima, shikam Ammar part dinsa yawuce ya kulle bema san me sukeyi ba, Zuhura Yasmeen da Amira taja suka nufi dakinta, nan sukai wanka suka huta, kana suka kara shiryawa, suka futo gurin walima, malamai Mamy ta gayyato mata sukazo sukai, nasiha, ba laifi ancika sosai, ilham kam wani kayan takara sawa, ba a tashi ba se karfe 6:30pm lokacin za a kira sallar magaruba, futowa yayi dan ya tafi masallaci yaga mutane, be tsaya tambaya ba ya sa kai yafuce, bayan yadawo sallah, still yakoma part dinsa, wanka yashiga, inda yayi wanka yafuto yazauna ya shirya tsaf cikin shadda ruwan omo yayi matukar kyau sosai se tashin kamshi yake, jin cikinsa yayi fayau ba komai, hakan yasa yadau waya ya danna kiran Mamy, tana dagawa tace "son ya akai" "Mamy yunwa nakeji" "ok bara nace Jummai ta hada ma" "Mamy ta hada tabawa Zuhura ta kawo mun" "ok naji zata kawo ma" daga haka Mamy ta kashe wayar, falour tashiga tasamesu gabadayan su a zaune tace "Zuhura jeki gurin Jummai kice tahadama Ammar abinci ki mikamai" amsawa tayi tana mikewa, Mamy taci gaba da sallamar bakin ta, se bayan kowa yatafi tashiga bedroom dinta tayi alawala tayi sallah, sukam su Inna da aunty Aisha tuni sunyi sallar su , bayan tayi tafuto falour tasamesu, "ace Ilham tafara shiryawa time yayi" aunty Aisha ce ta mike tanufi bedroom din Ilham, ita kuma Inna tana zaune , bayan Jummai tahada mata abincin takarba tanufi part dinsa danta kaimai, kofar abude take hakan yasa ta tura tashiga, tana shiga taganshi zaune kan kujera yana kallo, yamata kyau sosai, zuciyarta ce tace mata 'kin manta ango ne fa' wata zuciyar kuma tace 'dama can kullum shi cikin kyau yake' jin shirun yayi yawa yasashi kallon bakin kofar, tana tsaye tana kallonshi katseta yayi da cewa "kona zo na karba ne" dasauri ta dawo daga duniyar tunanin ta wuce ciki, ajiyewa tayi saman centre table, kana tadau plate tafara zuba mai, bayan ta zuba takoma gefe ta tsaya, zauna yafada yana kallonta, zama tayi, shi kuma yafara cin abincin, yanaci yana kallonsa ta kagu yagama ta kwashe kayan tafuce "dagaske kina son Ahmad" tambayar ta doki dodon kunnenta, saurin kallonsa tayi taga bama ita yake kallo ba television din dake falourn yake kallo, shiru tayi ta sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannunta, kallonta yayi yace "bake nake tambaya ba" ji take kamar ta kurma ihu saboda kunya, to ita me zata ce, ganin tayi shiru yasashi cewa "ok kina son shi kenan, kuma zaki aure shi, yayi kyau" ita dai bata dago kai ba, amma kana ganin ta kasan amasar eh ce, cokalin ya dire kan plate din, har yana bada sauti, kana yakoma ya jingina da kujera ya rufe idanunsa, baki yabude yace "dauki abincin kije" bata kawo komai ba tamike da sauri tadebe tafuce, ya jima idansa a rufe zuciyarsa na tafarfasar kishi,
kai amarya aka fara tafiya, hakan yasa Zuhura shigewa daki dan batason zuwa, sukam su Inna daga can gida zasu wuce, haka aka ranka ya aka tafi, gidan ta yayi kyau ba karya, falourn ya hadu, saman bene aka wuce da ita, aka kaita dakinta, su aunty Aisha ne sukai mata nasiha sosai kana suka rankaya suka wuce gida, aka barta ita da kawayenta su uku, su Inna gida suka wuce, dansun gaji likis, ita kuma aunty Aisha tabi su Muhsin suka koma gida, dawuri tayi shirin bacci ta kwanta danta gaji, aikam tuni bacci ya dauke ta, Ammar kam har 11:00pm be tafi ba, seda Mamy da aunty Aisha suka bishi part dinsa, suka sameshi, haryanzu yana yadda yake, sallamar suce tasashi bude ido, yana kallonsu, zama sukayi, kana Mamy tafara magana "son yakamata katashi kaje ankai amarya tun dazu" shiru yayi bece komai ba, kafadarsa Mamy ta dafa tana fadin "Please ka daure ka sauke nauyin da Allah ya dora ma, Ilham yar uwar kace, ko yaya kayi wani abu akanta bazanji dadi ba, ko kanaso ka ganni cikin bacin rai" kada mata kai yayi alamar aha ah "to please ka taimaka mun katashi katafi gidan ka" "kwarai kuwa Ammar yanzu ba kai kadai bane koya zaka iya yin abunda zaka tauye mata hakkin ta kuma kashiga fushin ubangiji" jikinsa ne yayi sanya, hakan yasa yakama hannun Mamy yace "no Mamy base kun rokeniba zanyi abunda kuka ce" "yawwa muje nabaka kayan da aka siyo ka tafi dashi" aunty Aisha tayi maganar, daga haka yamike, kazar dasuka sa asiyo da sauran abubuwa suka mika mai, kana ya musu se da safe yawuce, motarsa ya hau yanufi gidansa, yana zuwa yayi horn me gadi ya wangale mai gate ya shiga, bayan yashiga ya tarar ba kowa a falour hakan yasa ya haye sama, hayaniyarsu yaji, kofar ya isa yatura, suna zazzaune kan bed din, karasawa yayi, kowacce acikin su ta zuba mai idanu, zama yayi yana kallon Ilham yace "me suke har yanzu" "am dama siyan baki suka tsaya" "me baki da hankali ko" tsuru tsuru tayi da ido, ya kallesu yace "ku tashi ku tafi" da sauri kowaccen su taja jakarta suka fuce, bayan sun futa, Feenat takalle su tace "gaskiya yanzu na dena ganin laifin Ilham akan son guy dinan, kut gaskiya ya hadu" "ashe bani kadai nake kallonsa ba, ai dar ne gurin kyau" "nifa wlh nasamu wannan ko da duka sena zauna dan babu abunda babu atare dashi" harsuka shiga mota suna gulmarsa,
ledar ya ajiye mata saman bed yace "gashinan ki dauka kici nasan kinajin yunwa nina wuce dakina se da safe" kafun tayi wata magana har ya bude kofa yafuce" ledar ta kalla kana ta bankade mayafin kanta, tana fadin "wai me wannan mutumin ke nufi ne" yana shiga dakinsa yafada toilet yayi wanka yadau kayan bacci yasa kana ya kwanta da tunaninta a karkashin ransa,
yau bata iya tashi da wuri ba saboda gajiyar da tayi, se karfe 9:00am ta tashi, tayi wanka tashirya ta futo, kitchen tanufa, Mamy ce da aunty Aisha se Jummai dake wanke wanke, Mamy ta tsugunna ta gaisar kana ta gaida aunty Aisha kana ta gaida Jummai, "Mamy ba abunda zan taya ku" "ah ah Zuhura mun kammala ai" daga haka tafuce, aunty Aisha ce takalli Mamy tace "aunty Khadija yarinyar na birge ni akwai hankali" "ah ai Zuhura akawai hankali" bayan sun kammala breakfast, Mamy ta hada a basket tabawa driver yakai gidan Ilham, sukuma suka shirshiriya kan dinning, duk suka hallara suna breakfasta din,
me gadi Bala driver yamikawa ya shigar dashi ciki, dama Mamy ta sanarwa da Ilham za akawo musu, hakan yasa tafuto ta karba, zama tayi a falaour, tazuba taci, kana ta kunna tv tana kallo, se karfe 11:00am yatashi, yana tashi yayi wanka yashirya, yafeshe jikinsa da turare, key dinsa yadauka da wayar sa ya fuce, beyi tunanin shiga bedroom dinta ba, ya sakko da niyayar yafuta, samunta yayi kwance kan kujera, ga kulolin abincin duk a bude, ga jarkokin lemo akasa ta zubar da ledojin chocolate din data shashsha, tsayawa yayi yana kallonta, bama tasan yana kanta ba, hakan yasa takara jefar da ledan data gama cin chocolate din, baki ya bude yace "meye haka kika mayar da falour kamar bola" saurin mikewa tayi tana faɗin oh katashi ashe, "tambayar ki nake" "idan natashi zan kwashe ai" "kije ki gyara mun bedroom dina" wani kallo tamai kana ta kawar da kai, shi kuma yasa kai ze fuce, da sauri tace "bakai breakfast ba fa" juyowa yayi ya kalli kulolin abincin dukansu a bude kana yakalle ta yace "ahaka zanyi breakfasts din" kana ya fuce, waige waige take dan ita bataga abunda tayi ba, komawa tayi ta kwanta, tana cigaba da shan alawoyinta
bayan yafuta gida yanufa, yana zuwa ya tarar da Abba ze futa, gaisawa sukai, kana yashiga cikin gidan, duk suna falour banda Zuhura da tanacan tana bitar karatun islamiyya dan sunfara screening din sauka, asabar ta gaba za a gudanar da saukarsu, zama yayi kana ya gaishe su gaba daya, suka amsa, aunty Aisha ce takalle shi tace "ah ah naganka da sassafe" "aunty zanje office ne" "bazaka bari ka gama cin amarcin ba" "aunty aimu aikinmu ba a mai haka na ceton rai ne" "gaskiya kam naceton rai ne" Hajiya tayi maganar tana kallonshi "Mamy inason coffee" "ok Muhsin ina Zuhura ta hada mai" anzo gabar da yake so dama ita yakeson gani, "Mamy tanacan tana bita na screening din saukar mu" "oh hakane fa to fadawa Jummai ta hada mai" amsawa Muhsin yayi yana mikewa, kallon Mamy Ammar yayi yace "saukar me kuma" "next week saukar sufa" girgiza kai kawai yayi, Jummai ce tazo dauke da cup din coffee din, tdugunnawa tayi ta gaishe shi ya amsa kana ta mikamai, karba yayi ya fara sha,
seda ta tabbatar karatunta ya zauna ba gargada, futowa tayi, daga dakin nata, falour ta nufa, lokacin shikuma ya mike ze tafi, karasowa falourn tayi, tana zama kusa da Mamy, kallonshi tayi tace "ina kwana" batare daya kalle taba yace "lafiya lau" daga haka yace "Mamy zan wuce" Muhsin ne yazo yana fadin "yaya Zuhura ana nemanki a waya" yafada yana mikamata wayar, karba tayi takara a kunnenta, kawarta ce ta islamiyya takira tace Muhsin y hadata da Zuhura, mikewa tayi ta bar gurin, da kallo Ammar yabita, zuciyarsa ce tace 'watakila fa yarinyar nan Ahmad ne yakirata' "me kake kallo kuma kace kuma katafi" Hajiya tafada tana kallon sa, se lokacin yadawo hayyacinsa, daga haka yasa kai yafuce, bayan ta gama wayar tazo takawowa Muhsin wayarsa,
"ai naga yaron ba laifi yanada hankali shima" "to nidai kawai sedai nace Allah yabasu zaman lafiya tunda tanasansa" "ammeen dai"
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 19