yaushe zakizo namatsu naganki" "zanzo se ranar juma'a, kina da matsala ne" "bani da matsala Inna kawai dai inaso naganki ne" daga cikin wayar taji ana fadin "aunty Zuhura ce" "eh Yasmeen itace" "bani ita mugaisa" daga haka Yasmeen takarbi waya tana fadin "hello sister ya kike" "lafiya lau kefa" "ina lafiya sister yaushe zakizo" "se randa Inna tafada, ina Amira" "kinganta nan , Amira ga sister Zuhura" karba Amira tayi tace "yaya Zuhura ya gida" "lafiya lau yan mata, ko nemana bakya yi" "kai yaya Zuhura nida bani da waya" "nima ai bani da ita amma ke ai gata Inna" "to dai zamuzo yau se muga juna" dariya sukai Inna takarbi wayar "to sesunzo jeki mayar mata wayarta" daga haka takashe wayar, falour takoma , "Mamy ga wayar" "yawwa kingama, bara nazo nakira muku me kwalliya kafun Yasmeen takaraso" karbar wayar tayi, ita kuma tajuya tanufi daki
kirane yashigo wayar sa, yayin da yake kwance saman bed, kanshi nakallon silin, wani kiran ne yashigo, seda yaktse na uku yashigo, kana yadau wayar, Nafeesa ce, batare da yayi magana ba yakara a kunnensa, cikin wata muryar ta yaudara tace "beb najika shiru kuma kasan dai bazan iya zama banji dumin jiika ba ko" yadda tayi maganar ne yasa gaba daya jikinsa ya saki, yace "to yanzu me kike so" "kazo yanzu" tafada cikin shagwaba, "ok bara nayi wanka" "no idan kazo sai muyi" "sai nayi wanka" "ok sekazo" daga haka yakashe wayar, yamike ya shiga toilet, bayan yayi wanka yashirya cikin manyan kaya, yafeshe jiki da turare, yafuto, bakowa falour hakan yasa kawai yafuce, batare daya shiga dakin mom ba,
"aunty munshirya" Yasmeen tafada tana zura kai kitchen din, "oh har kun shirya, amma dai kunyi sallah ko" "eh aunty munyi la'sar" Halifa ne yashigo yana faɗin "aunty dan Allah zan bisu" "ah ah Halifa yara basa zuwa se yan mata shiyasa, amma kaima zamuje se gobe kaji" Yasmeen ce takalli Amira tace "lah Amira namanta wayata kan mirror daukomun" amsawa tayi tana tafiya "bara nayiwa driver magana yakaiku" daga haka Inna tafuce zuwa compound din gidan, "Ado dan Allah zaka kai yarannan unguwa kaji" "to Hajiya su futo" komawa tayi tace musu "kuje yana jiranku" "Amira muje" daga haka suka fuce, ita kuma Inna takoma ciki,
"Zuhura kiyi wanka kizo me kwalliyar ta karaso" "tom Mamy" tafada tana shigewa, tana shiga ta fada toilet tayi wanka, bayan tafuto bata sha komai ba, tazura hijabin ta har ƙasa, tafuto, falourn tafuto tana fadin "Mamy nayi" "ok jeki cikin Waldrop dina zakiga ledar da muka karbo dinki jiya, zakiga wani material purple sa baki kidauka kisa" "tom Mamy" daga haka tashige part din Mamy, Ammar ne yashigo falourn da sallama, amsawa sukai, kallon Mamy yayi yace "Mamy nadawo" "sannu da zuwa to, yau naga kadawo dawuri" "Mamy nagajine shiyasa kawai nadawo" "ok zansa akawo ma abinci" "daga haka ya shige part dinsa" Jummai Mamy takira tasa takaiwa Ammar abinci,
su Yasmeen ne suka shigo, da sallama, amsawa Mamy tayi, suka karaso falourn, durkusawa sukai suka gaida Mamy ta amsa, kana suka koma kan kujera,
kallon kanta ta tsaya tanayi a mudubi, yadda kayan yazauna mata das ajikinta, street gown ce, tabi jikinta shape dinta ya futo, kayan ya dace da fatar ta, seda tagama kallon kanta, kana tafuto, Yasmeen ce tabita da kallo, aranta tana jinjina kyawun Zuhura, dan ko ba a fada mata ba tasan ita ce Zuhuran Mamy ce ta ce "wow yan matana ta futo, ga su Yasmeen nan sunzo tun dazu" zama tayi kusa da Yasmeen tana faɗin "sannu sister ashe kun karaso" "eh wlh sister tun dazu ma fa" "to sannunku, Amira ya kuke" "lafiya lau yaya Zuhura kinyi kyau sosai" "kai Amira " "dagaske fa sister kinyi kyau" "Zuhura tafara muku make up dinnan 5:00pm har tayi fa" "tom Mamy" tashi tayi takoma kan 1sit kujera tazauna me make up din tafara mata"
Make up ake tayiwa Ilham ana tsatso ta, ta dawo kamar aljanna, saboda kwalliyar da akai mata, ba laifi tayi ktau sosai, gown tasa light blue, me net, kawayenta kuma sukasa, material copee suma sunyi kyau, su Ilham se rawar kai take, sukuma kawayenta su Feena sunata zuga ta,
bayan an kammalawa Zuhura make up, tamike , Yasmeen taje aka fara mata, light make up akaiwa Zuhura ba hayaniya, ta kyau sosai, ga daurin data mata ya zauna, Yasmeen tashigayi yiwa, nan danan tagama mata, itama tayi kyau, dayake ita fara ce tas,
Mamy ce takalli Zuhura ta ce "yan mata na biki sa dankunne ba fa" se lokacin takai hannu kunnenta taji, "jeki part din Ammar shinace yasiyo, bansaniba ko yasiyo, kice injini ya baki sarka da dankunnen" amsawa tayi tana fucewa, Amira aka fara ma make up din, itama tayi kyau dan itama tafara zama yan mata, dan har tafara kirgen danki, dayake tafi Zuhura jiki, ita tanada kiba, knocking ta tsaya tanayi, amma taji shiru, hakan yasa ta tura kofar tashiga, bakowa falourn, bakin kofar bedroom din tayi Knocking, yana toilet yana alwalar magariba zeje masallaci, se ya fito ya tsaya gaban mirror yana gyara hannun rigarsa, knocking dinta yaji, yayi zaton Muhsin ne danyace zezi ya tambayeshi dan Allah yadau mota yau dayake duk key din motocin gidan suna gurinsa, banda na Abba da Mamy da Jawad se na Bala driver da shi dama ba a karba saboda kai yara school, izinin shigowa ya bayar, tura kofar tayi tana shiga, kamshinsa dana dakinne ya doki hancinta, tsayawa tayi bakin kofar taki karasowa, "ina yini" tafada a sanyaye , saurin juyowa yayi, idonshi ne kafe kanta, kamar ita kamar ba ita ba yake tunanin, katse mai tunani tayi tace "Mamy ce ta ce wai kabani sarkokin da dankunnen" "ok" drower ya janyo yadauko wasu yan box guda uku, yatako har inda take yamika mata, hannu takai takarba, ta juya zata fuce, jin muryarsa tayi daga sama yace, "kina nufin da make up dinan zaki futa" bata da amsar dazata bashi hakan yasa tayi shiru "ba magana nake miki ba" kada mai kai tayi alamar eh "ok to shiga toilet ki wanke ta yanzu ina jiranki" marairai ce fuska tayi tace "dan Allah kayi hakuri wlh duk anyiwa su Yasmeen, kuma Mamy bazata ji dadi ba idan na wanke" be kulataba ya ratsa ta kusa da ita ya wuce, itama sauri tayi tabi bayansa, tafuce, massalaci yawuce, itakuma ta kaiwa Mamy box din daya bata, "ok zo in samiki" zuwa tai ta zauna kusa da Mamy , karamin box din tabude, dankune ne da sarka siririya, tayi kyau sosai, Mamy ta makala mata, seda tasa mata, kana tamike, bakin mayafinta tadauka wanda Mamy tabata ta yafa, se 7:00pm Bala driver yadauke su ya tafi kaisu event din,
bayan sunje, mutane sun fara taruwa sosai, amma amaryar batazo ba, guri suka nema suka zauna, gurin ya hadu sosai, kana gani kasan da uwar kudi, gurin zaman amaryar se walwali take ga wani cake a kan table din gaban kujerar amaryar, shi kansa cake din wuta yake yana walwali, yan mata ne a gurin kala kala kuma yayan masu kudi, kowanne table maza hudu mata hudu, sukam basu zauna inda maza suke empty suka samu suka zauna su uku, yan matan nata hotuna, dj na ta sakar sauti, amma sedai wakokin turanci yake sawa, sukam su Zuhura idonsu nakan wayar Yasmeen, suna kallon hotunan Yasmeen dasukaje kasar Paris hutu wancan year din, sunata hirar su, Muhsin ne ya hango su yanufo inda suke, seda yakaraso yace "kai yan matan Mamy kun iso kenan, Yasmeen ya gari" "lafiya lau Muhsin ashe kazo" "wlh nazo, yaya Zuhura kunyi kyau fa" "kai Muhsin kyau ai se ku" dariya sukai yace "bara naje kun wadancan na dawo" daga haka ya tafi, sukuma suka cigaba da kallon wayar su,
"Ahmad inasonka sosai wlh bansan abunda ze rabani dakai" tayi maganar lokacin datake kwance saman kirjin shi, tana shafa gefen fuskarsa, "wayace dama zamu rabu muna tare" yafaa yana kara manna ta jikinshi, yana jamusu blanket, yana kara shafa bayanta, tuni itama tafara shafashi rako ina, basa gajiya da junansu, yanzu suka gama amma har feeling dinsu yakara tashi, daganan suka shiga, mantawa da a wacce duniyar suke
Feenat ce takalli Ilham tace "ke dai ki gwada mana kiga kika sani ko yazo din" "uhmm bakusan halin yaya Ammar ba" "kedai bakya san kiranshine" wayarta tadauko ta danna kiransa tana fadin "bara dai kuji da kunnenku" tasa wayar a amsa kuwa yadda zasuji, seda takatse, kana takara kira, seda takusa katse wa yadauka, "hello yaya Ammar" "inajinkj ya akai" "dama haka zance maka, dan Allah inasan kazo muyi hotuna a gurin bridal shower din" "baki da hankali ko, karki kara sani a haukanki" daga haka yakashe wayar, kallonsu tayi tace "yanzu kunji da kunnenku ai" "tab gaskiya dai kina da babban aiki a gabanki" "kunga kubar wannan zancen mu tafi kunga 8:00pm har ta kusa" daga haka suka fara tafiya, ita kuma Ilham ita da kawayenta guda biyu suka shiga cikin mota,
Zuhura da Yasmeen ne suke ta fada, Yasmeen ta dage setayiwa Zuhura hoto, ita kuma taki, dakyar dai ta tsaya ta mata guda biyu, sanarwa aka fara amarya ta iso, hakan yasa kowa ya maida hankali kan gurin shigowa, waka aka samusu wai ta shigo da amarya, ba jimawa kuwa sega su sun shigo, tana tsakiyarsu, sunata rawa har ita, har suka karaso suna rawa, kana tazauna kan kujerar, tuni kowa yafara yadaukanta hoto, Yasmeen ma mikewa tayi, taje tayimata hoto ta dawo, nan kuma aka fara gudanar da komai yadda yakamata, aka fara raba abinci dasu sancks ba abunda babu, se rawar kai take kamar ba amarya ba, bayan sun kammala cin abinci, suka maida hankalinsu kan amarya dasuke ta rawa ita da kawayenta, magana sukaji ana fadin "yan mata ashe kun iso" kallonshi Zuhura tayi tace "au yaya Jawad ashe kaine" "ita kawar taki bata magana ne Zuhura" "kai yaya Jawad tanayi mana" kallon Yasmeen tayi datake ta daddana waya tace "sister wai dama yaya Jawad be sankiba" "rabu dashi sister hakan yakeson fada" "kardai Yasmeen kanwar Mahmud" "ita mana" tafada tana kallonsa "wai kece kika girma haka, ai muna waya da Mahmud din amma be fadamun kin gurmaba" dariya tayi tace "to yaya Jawad kawai kuma seya ce ma kanwarsa ta girma" "bazaki gane dilili ba yanzu dai inason yin magana dake" kallon Zuhura tayi, itama Zuhura ita ta kalla kana tace "bara naje gaba ko nafi ganin amarya da kyau Amira muje" daga haka suka tashi suka basu gurin, kallon Yasmeen yayi yace "kai gaskiya fa kinyi kyau sosai" "Allah yaya Jawad nagode" "tun daga nesa na hangoki naji bazan iya jurewa ba se nazo, ina bukatar zan samu hadin kanki" "name kuma yaya Jawad"? "kinga Yasmeen bazan boye miki ba har ga Allah inasonki, abaya naso Zuhura amma se yaya Ahmad ya rigani, to ina fata anan ba wanda ya rigani" "yaya Jawad ba a riga ka ba, amma inason kabani lokaci nayi tunani kafun" "so nabaki nan da gobe, dan inasonki sosai wlh" dariya tayi tace "alright ba damuwa zanyi tunani" daga haka suka cigaba da hirara sh, se daga baya yace suzo yamai dasu gida, Zuhura tayima magana da Amira, suka taso suka futo, Yasmeen ce ta hau gaba sukuma suka shiga baya, daga haka suka tafi
💞 SOYAYYA DA IZZA 💞
Story and writing by Hadizatu✍️✍️
Mrs (KD)
Yar amanar jajirtattu💪💪
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page 40
_______________Bakin gate din yayi parking, yace "Zuhura bara nakai su Yasmeen gida" "ok to sister ki gaida gida, se gobe idan mun hadu" tafada tana ɓalle murfin motar, "ok sister se goben" motar yaja suka tafi, ita kuma tashiga ciki, bayan ta isa falour ta tarar da Hajiya kawai falourn tana waya, zama tayi kusa da ita, yayin da ita take waya da yar autar ta A'isha, dake aure a London, "yanzu A'isha su kadai zaki bari bazaki tawo dasu ba" daga cikin wayar tace "Hajiya akwai yar aiki ai zata kula dasu" "to shi Jamal din zezo ne" "eh mana Hajiya tare zamu tawo ai" "to shikenan sekunzo" "amma fa Hajiya Abuja zamu wuce direct anan jirginmu ze sauka, sedai mu hadu acan" "ok to shikenan" daga haka ta kashe wayar kana ta dubi Zuhura tace "oh Zainab wannan kwalliya haka, kamar ba ke ba" "kai Hajiya" "dagaske mana, har an tashi kenan" "ah ah kawai dai muntawo naga har 9:00pm tayi ma" "gaskiya dai gara da kukau tawowar ku yafi" Mamy ce tafuto tana fadin "ah Zuhura harkun dawo" "eh Mamy mundawo" "ina su Yasmeen din" "yaya Jawad yatafi kai su gida" "ok to kije kiyi wanka ki canja kaya sekizo kici abinci" "tom Mamy" kana tamike, tana wucewa
bayan Jawad yakaisu har cikin gidan yashiga, bayan yayi parkinga Amira tabude tafuta, itama Yasmeen harta kai hannu Jawad yace "haba dai ai bamu gama ba" "to yaya Jawad me ya rage" "fira mana" murmushi tayi kana takalleshi tace "to yaya Jawad inajinka" daga haka yashiga zubo mata matanganu wadanda zasu jawo hankalinta taji tana sonshi, har fa Allah dagaske yanason Yasmeen, kuma so na aure, saboda yanzu ya rage bin matan dayake ada, tun lokacin da Ammar yadawo, gudun kada Ammar yagane ya hukunta shi yasa yadena tun kafin yagane,
tsaye take gabanshi daure da tawul, tana tayashi ɓalle bottle din rigarsa, "wai beb meyasa kamatsu katafi ne, kodai ka gaji dani ne" kugunta yakama yana fadin "kema kinsan ai ba haka bane, kawai dai banfadawa mom nafuto ba" "ok to adawo lafiya" daga haka tayi hanyar toilet, da ido kawai yabita, kana shima yayi hanyar futa, bayan yafuto, yashiga motarsa yawuce, gida yanufa, yana zuwa yayi horn me gadi yabude mai gate ya shiga, parking space yayi parking, kana yafuto yashiga ciki, da sallama , amsawa mom tayi, tayin da me kunshi ke goge mata hannu da tissue, karasowa yayi ya zauna kusa da mom din yana kama hannunta, yana fadin *wow mom yayi kyau" "to ko za ai maka ne" "da queen tananan da ita za ayiwa, se ya ma fi kyau a hannunta" "uhmm wace queen kuma" "wacce nabaki labari mana" tsaki taja kana tace "bazaka manta da yar talakawan nan ba ko" "Mom kenan barama nasa Muhsin yatura mun hotonta dan naga yau Ilham tafara biki" "eh ta turamun hotunan nagani " wayar Muhsin yashiga kira, amma be dauka ba, seda yakira har sau uku be dauka ba, "ohh Muhsin ko ina yakai wayar tashi, bara na kira Jawad" daga haka ya danna kiran Jawad,
"sorry Yasmeen bara na daga waya, yaya Ahmad ke kirana" "ok ka dauka" wayar yadauka yakara a kunnensa yace "hello yaya Ahmad" "yawwa Jawad ya kake ya biki naga kun fara" "eh yaya Ahmad anfara yau" "hakan yayi, nace kanada pics din Zuhura ne katura mun yanzu dan Allah" "ayyah yaya Ahmad bani dashi, amma bara na tambayi Yasmeen, idan an samu zanturo ma yanzu" "ok tambaya" daga haka yakashe wayar, kallon Yasmeen yayi yace "Yasmeen kinada pics din Zuhura ne" "eh nayi mata dazu dakyar" "ok turamun yanzu ta WhatsApp" "ok" turamai tayi guda biyu, shima yayi forward yatura ma Ahmad,
yanajin karar sako kuwa yayi maza yashiga, "wowww" abunda yafada kenan, yana murmushi, "Mom kalli queen fa kina ganin ta ai kinsan tanada nutsuwa gata kyakkyawa" yafada yana nunwa Mom hoton, kallon hoton tayi azuciyarta tace 'ba laifi tanada kyau' afili kuma tace "malam matsa kabani guri, kasan Allah ko me zakai bazaka auri yarinyar nan ba" bata rai yayi yana mikewa yawuce bedroom dinsa, yana shiga yafada kan bed yacigaba da kallon hoton Zuhura, tayi kyau sosai gashi tayi murmushi, seya kara mata kyau, yanata kallon hoton daga baya yasa hoton kan screen din wayarsa, yamaida sa wallpaper,
bayan tashiga , tayi wanka ta canja kaya tasa na bacci, kana tafuto, tanufi kitchen, ba kowa hakan yasa tadawao falour, Abba da Hajiya ne se Mamy da ita tama mike zata shige ciki, ganin haka yasa bata karasa ba takoma, kitchen tanufa , tabude kulolin abincin ta zuba kadan saboda a koshe take, kadan kadan ma take kamar wace akaiwa dole, seda tagama ta bude fridge tadau lemo kana tawuce dakinta,
"yaya Jawad yakamata na shiga gida kaga na dade" "korata kike kenan" "no niba korarka nake ba kawadai nasan Daddy yadawo tun dazu" "ok to se gobe ma karasa" "to seda safe" daga haka tabude motar tafuce, seda tashige, kana yatayar da motarsa, yafuce, tana shiga ta tarar dasu kan dining gaba dayansu, sun cin abinci, karasawa tayi, Daddy yakalle ta yace "se yanzu kika dawo" "am Daddy yaya Jawad ne yazo" be kara magana ba yakalli Inna yace "amma dai auntyn yara jss zan kai Amira" "yo dama ai sedai jss kalle ta fa kamar ana kara hura ta kullum" dariya Yasmeen tayi tana shigewa, ita kuma Amira ta bata rai, shima Halifa dariyar yake, Amira ce tace "Daddy kama Halifa magana yana mun dariya" "Halifa ka dena mata dariya kaji" "tom Daddy yafada yana kunshe dariyarsa,
su Ilham basu tashi ba se 11:30pm, kana kowa yawatse, itakuma tabi su feenat, hotel, ta dage se tayi harkatar ta lesbian yau, dan idan aka daura zata tafi hutu kafun ta dawo, haka suka tafi, seda suka gama iskancinsu kana tayi wanka, tasa riga da wandon wata daya daga cikin kawayenta, tayafa mayafi akai, "nidai naga ya Ammar dinan zeyi, muda bamu damu da sex ba" daya daga cikin kawayenta tafada "yaya Ammar ma girman kansa da izzar sa bazata barshi yakawo kanshi gurina na, kinga nikuma na huta nima, sedai bansan yazanyi da harkata ba, dan bazan iya 1 week banyi ba" "ke kwantar da hankalinki badai futane baze barki ba, seki kiramu mu dinga turo miki yara idan ya futa, abunda ga yara nan suna ta shiga less, dakin saki kudi tuni zasu zo kiyi abunda kike so dasu ki sallemesu kafun yadawo" "hakan kuwa za ai kinga yaje can yasha zaman sa shi ze cutu ba ni ba" takare maganar suna kwashewa da dariya kana Ilham tace "ke mikomun key na nawuce, kufa shirya dawuri mu hadu acan danni tare da dasu zan tafi" "ok baki da matsala" daga haka tafuce, tana futa tahau motar ta tanufi gida.
juyi kawai yake saman bed din yakasa rumtsawa, tunaninsa daya, ta futa da make up din fuskanta, kuma mutane zasuyi ta kallonta, zuciyarsa nafaamai 'to wai kai ina ruwanka ne' shikansa ya kasa yagane dalilin damuwarsa dahakan, kishi ne ko kulawa, amma shikansa yasan yanzu yanason yarinyar, tana burgeshi sosai, nutsuwarta, da kamalarta, yanajin kaunarta sosai, yanason ganinta ko yaushe a kusa dashi, ya tabbatarwa kansa yana son yarinyar, amma gani yake bata kai yace yana sonta ba, kamar shi da mata ke binsa, taya ze bige da son wannan tatsitsiyar yarinyar, izzar shi bazata bari ya nuna mata yana sonta ba, kuma koda ma yanasonta, ya zeyi da Ahmad daya riga ya bayyana mata, sam baya kaunar ta auri Ahmad saboda yasan halinsa kuma har yanzu be sauya ba, haka yadinga tunani kala kala, ganin tunanin baze kare ba kawai yamike ya shiga toilet, yayi alwala yazo ya tada sallah, seda yayi nafilfilu, daga baya yadaga hannu yana rokon, idan son yarinyar yake to Allah yacire mai soyayyar ta azuciyarsa, kuma yabashi ikon zama da Ilham lafiya yakula da hakin da aka dora mai, yabashi juriyar jure zama da Ilham duk da bayasonta, seda yagama addu'ar sa yakoma saman bed din yakwanta,
asuba nayi yatashi yanufi masallaci, lokacin suma su Abba Jawad da Muhsin duk sun futo, hakan yasa suka rankaya suka tafi masallacin tare, bayan an idar suka tawo, Abba na tsakiyar su, Abba ne yakalli Ammar yace "idan kashiga ciki fara shiryawa don karfe 9:00am zamu wuce saboda 11:00am za a daura" a sanyaye tace "tom Abba" "ku kuma kar wanda yakoma bacci san bazamu jira kowa ba" amsawa sukai suma, suna karasa wa falourn kowa yawuce cikin dakinsa, itama Zuhura tun asuba data tashi bata koma ba, yau da kewar kawarta Maryam ta tashi, tanata tunanin ta aranta, bayan gari ya waye, tafuto tanufi kitchen, Jummai ce kitchen din ,har ta kammala breakfast tana zuzzubawa, "aunty Jummai ina kwana" "lafiya lau Zuhura kin tashi" "eh aunty Jummai na tashi, kardai harkin gama komai" "na gama dayake Mamy tace dawuri za a futa shiyasa na kammala komai" "gaskiya ne sannu" tayata Zuhura tayi suka kai dining suka jera, ba jimawa duk suka fara futowa kan dining, harda Ilham dan ita dama a matsu taje taga mom dinta, abincin suka fara ci harda Zuhura, Ilham ce ta kalli Mamy tace "Mamy ina yaya Ammar" "yana ciki me bi besan an kammala breakfast ba" "ok bara naje nakirashi" daga haka tamike tanufi part dinsa tana zuwa tafada ciki ko knocking batai ba , kallon ta yayi yace "meye haka zaki shigomun falour ba sallama" "haba yaya Ammar meye danna shigo awa nawa ne ya rage mu zauna daki daya dakai" "meya kawoki" "dama breakfast ne angama, kuma naga baka futoba" "jeki zan futo yanzu" juyawa tayi tafuce, shikuma ya hau hada takardun daya baza yasasu cikin drower kana ya mike yafuce, karasowa yayi dining ɗin, yana gaishe dasu Hajiya da Mamy kana yakara gaishe da Abba, gaishe dashi gabadayansu sukai, itama dagowa tayi itama tace "ina kwana" "lafiya" yafada yana zama kujerar dake kusa da ita, abinci takasa ci gaba da ci, juya cokalin kawai take, yana kallonta, amma yayi kamar ma besan da wata a kusa dashi ba, ganin bazata iya karasa cin abincin ba yasa tamike, Hajiya ce takalle ta tace "Zuhura yadai" "Hajiya nakoshi" "kin koshi kuma" "eh Mamy" "kodai bakisan zama anan dinne" Abba yafada yana kallonta, murmushi kawai tayi batare data ce komai ba "to shikenan idan kin shiga ciki kiyi wanka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 19