koko dai almara ce. Haj. Basira tayi
bala'in bani mamaki ta canza ko dan idon jama'ar da
ke gurin ne? da kyar na daga kafa na isa cikin dakin
na durkusa har kasa ina gaishe ta, ta amsa cike da
sake fuska. Na san ba zan iya mikewa ba don haka
sai na yi zama na a wurin, wai ina Baban shi ne ai da
kin bar masa shi, da rigimar sa za ki ji koda kan ki
daga gefen ta ashe mahaifiyarsa Suwaiba sam ban
lura da ita ba, na soma gaishe ta, waya na ji Mama
ke yi da Mas'ud ka zo ka dauki yaron nan mai
rigimar tsiya ta kashe wayar, ta dube ni ta shiga kun
Aminar ki ga baby. Na mike zan wuce, ta kira
sunana na juwo na dube ta, ta ce na ga kafafunki duk
son kubura kin dan rika zagawa don su sake, Mas'ud
ne ya shigo yana cewa Mama zaman mota ne åi jiya
ma sun fi haka kumburi, ni kam wucewa nayi, na isa
dakin da Amina take na dauki baby, ta ce anya
wannan cikin naki bai fi yadda Mas'ud ya fada ba?
Kaina a kasa ban yi magana ba, ta yi dariya kunya ta
ke ji wai? Ai ina ga tun cikin nan na wata biyu
116
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Mas'ud ya fada, na shiga uku, da mene? Ta tambayc
ni, ai ba komai ba ne Dayyiba idan Allah ya kaddaro
maka sai ka gode masa, ka rike shi. Haka na zauna
ina kallon abun mamaki, sosai Mama ta sake da ni,
ta sa a kawo wannan a kawo wancan har akan dole
na saki jiki, sai dai nauyi da nake ji na mutanen da
ke shigowa ganin nakc duk sun san halin da nake
ciki don yawancin su 'yan uwan Mama ne.
Bayan Isha'i Mas'ud ya ce, in fito mu tafi. Da
muka isa gida sai na ki fita daga motar, ya ce mun
iso fa ina son fita ne, kai tsaye na ce, tare zamu in ga
amaryar taka, dariya ya saki ashe haka ki ke? Dama
kina da kishi. Haba Baban Tahir, kasan dole ne in yi kishinka, ko ka manta kai ne first love dina? Ni na
sani ina sonka har in mutu ba zan daina sonka ba, sai
dai zargin da nake maka na yi murna baki biyu da ni
da mahaifiyarka why! Ba za ka fada mana gaskiya
ba sai.... Hannunsa ya kai kan la66ana dole nayi shiru, wannan dan bakin naki ya cika da surutu ba
comma ba fulstop, tabbas nasan kin fadi gaskiya akan baki biyun da nake yi tsakaninki da Mama,
amma tsakanina da Allah ba ina yin hakan ba ne don
wata manufa, sai don in ina neman hanya mai sauki da zan fahimtar da ke da ita dukan ku kuna da
mahimmanci a rayuwata. Ajiyar zuciya nayi, na ce
to ya aka yi ta sauko har ta tarbe ni, ban taba zaton
haka daga gare ta ba.
Murmushi ya saki da har hakoransa suka baiyana, Allah ne ya kawo karshen fitinar da nima
kaina ina tsoron ta. cikc da nasara Allah ya bani
7
Baki Biyu Sameera Mustapha:
damar warware matsala abu na farko biyc mata da
na rika yi sannan da Suwaiba da na smau ta same ta
tayi mata magana, ni kaina nayi mamakin irin ilimin
da Suwaiba ta samu, tana da ilimin addini fiyc da
yadda ki ke tsammani, ina Dubai Mama ta bugo min
waya ta ce, auren da nake cewa ina nema in fasa shi,
ta bani labarin irin asirin da Jamila ke nema, itama
din baki biyu tayi saboda idan tana tare da Mama
zata nuna mata tana sonta, sai ta fita ta rika zagin
Mama, har ma daga karshe ta kai sunan Mama gun
wani Malami akan tana son a kashe ta don ba za ta
aure ni ba Mama na kishi da ita a kaina. To ashe
Malamin na Mama ne, shi da kansa ya kira ta ya
fada mata, sannan a cewar ta ya fada mata irin matar
da nake aure, ke kenan ya ke nufi, to in fada miki
yanzu haka kullum gargadin da take yi min shine in
rike ki amana.
Jikina ya kara sanyi, hawaye cike da idona na ce
shi kenan yanzu zancen auren babu? Hannuna ya
rike in har ki ka zama mai biyayya a gare ni Dayyiba
ina sha Allahu daga ke ba wata! Tuni na saki dariya,
sirinya na ce, zan yi sweet love, I love only you. Zan
yi maka biyayya zan yi maka duk abinda ka ke so,
rungumi ni ya yi I love you too, Dayyiba there is no
one but you. Na yi alkawarin rike ki amana, sannan
babu baki biyu tsakanina da ke sai gaskiya da ya ke
ma ina son ki zama mai gaskiya tsakanina da ke
Dayyiba, na zama wallahi na zama ina fada ina
matse ido na da yake zubar da hawayen farin ciki.
Baki Biyu Sameera Mustapnа:
**
Rayuwa kenan, yau gani da Amir Mas'ud din da
nake mafarkin samu, tun ina karama, ban taba
tunanin zan kara son da namiji ba a irin matsalolin
da na samu a can baya gashi ya zame min alheri, da
ake cewa mafarki na iya zama gaskiya tabbas na
yarda don kuwa nawa ta zama gaskiyar shekarar mu,
shidda da aure tsakanina da Mas'ud mun tara zuri'a
da shi, muna da yara biyar haihuwa uku 'yan biyu
sau biyu nayi gashi muna jin dadin rayuwarmu,
muna zaune a Dubai, har a wannan lokacin bai dai
na polo game din sa ba, tsakanina da Mama kuwa
abin ba a cewa komai.
Watan da ma mutum kan canza lokaci daya, a
kullum idan na tuna irin rigimar da tsana da Mama
ta dora a kanmu, sai in ta mamakin irin yadda ta
canza farat daya in ban da ganin mutunci da
zumunci mai karfi da ya shiga tsakaninmu abun dai
ba a cewa komai hatta Gwaggo da ba su ga maciji
tsakaninsu in ka gansu a yau kace wani abu bai taba
shiga tsakanin su ba. A koda yaushe sai godiya nike
yi ga Allah (S.W.A) da ya juya mana rayuwarmu.
Ina zaune kasa kan kafet a tsakar falo na ina
tsotson kashin rago, ga ciki kuma da nake dauke
dashi na kusan wata biyar, muryar Mas'ud na jiyo ta
baya na honey me ki ke ci haka ko a kira ni muci
tare, ni dai ban gane ba, wannan cikin ya cika ruwa
na lura tunda ki ka same shi solo ne tsakaninmu,
idan na zo ci ma ba a son ba mu, daga bayan shi
Fauziya ce da Tahir, suna biye da shi da gudu
119
DOI DIyu Θ Sameera Mustapha:
Fauziya ta karaso ta rungume ni da yake ita kadai cc
ma su ne kuma sukc bi ma Tahir da ita da Mohd
sunan mahaifinsu Mas'ud muna kiransa Imam shima
din yana biyc da su yana ta kokawar bude marfin
Icc-Crcam.
Kai Fauziya don Allah kiyi min a hankali mana,
Mumy ina su Abdulkahar da Abdulhafiz suke?
Zaman da Mas'ud ya yi a gabana yasa hankalina ya
dawo gunsa, kashin da ke cikin flate dina ne bana
son ya dauka, da sauri na daukc na rike a hannuna,
dariya ya yi ya ce, kwantar da hankalinki 'yanmata
ba dauka zan yi ba.
Harara na jefa masa ina yogot dina? Na yi
maganar a shagwabc, shima tambaya ya jefo min ina
'yan biyu na? suna daki suna bacci ba dai maganin
bacci ki ka ba su ba? A'a wallahi bari ba su maganin
bacci ba, tun da ikilishi ta lallashe su bayan rigimar
da suke ta yi shine suka yi bacin maganin da ka
daukc? Kada kira basu maganin bacci, na daina
Baban 'yan biyu. Na fadi hakan cike da jan hankali.
Karshe.
Taku;
Mrs Samecra Mustapha
120
COONSHO N665022|KatisinaGetrtaaMaakket Tae1008002998600,
Bittattafan marubucivar
BAKI BIYU
SILA
LADABI
FITINAR MULKI
YADDA ALLAH YA SO
KAIDIN MACE
BAKI BIYU KAIDIN MACE
SIRALUSTTPНА SAMIRA MUSTARHA
CCovefGrrpphies
AGF Computers Fagge
07030319787
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels