daure ina sha.
Tausayin Tahir yasa na kasa sakewa, har na dan
fada kwata-kwata share Mas'ud na yi, yau
satinmu daya da kwana biyu ba mu yi magana
ba, wayata kashe ta nayi idan suna magana da
Gwaggo kuwa barin wurin nake yi in kuwa ta
matsa min kuka nake sa mata dole ta kyale ni.
Kwanan Tahir goma yana fama sai dai anyi
dace don a gaskiya ya samu lafiya, har da wasa
yake yi yanzu ya dan yi kumari. Ina daki ina
sallah La'asar naji shigowar Mas'ud, yadda ya
ga Tahir a hannun Gwaggo shima har sai da ya
tsorata, tambaya ya rika jefa ma Gwaggo, me ya
same shi Gwaggo? Ya aka yi ya zama haka?
Rashin lafiya dama yake yi? Na ji ta ce masa, bai
da lafiya Mas'ud, ya ma ji sauki ai, ya dade rike
dashi ni dai ina daki jira nake yi ya shigo in
balbale shi, har da haushin Gwaggo na ji da bata
fada masa sanadin ciwon Tahir ba, ji nake kamar
in je falon in yi masa.... Jin sallamarsa dakin
yasa na daina tunani, na dube shi yana rungume
da Tahir din, shi kuwa ya yi kwance a jikinsa
kamar ya san shi ne mahaifinsa, ya ya dai sweet
heart? Ban daga ido na kalle shi ba, kuma ban
ma shirya tarbon sa ba, yana kallona har ya isa
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
inda nake zaune. Tahir da na gani yasa na fara
kwalla, me ya faru ne bab....na hana shi ida
abunda ya yi niyar fadi, na ce menene ma bai
faru ba, kasan ciki ne da ni?
"Ban gane ba! Ciki?"
"Eh mana, shi ne dalilin ciwon Tahir, don
haka ne ma nake jiran ka dawo muje a cire, don
cikin na affecting dinsa duba ka ga yadda jaririn
nan ya koma kamar mai kwashoko, ciwo ya ci
shi ya cinye."
"Tashi
دو
mu tafi tun wuri kafin lokaci ya
wuce."
Zan mike na ji ya riko ni ya ce, "Haba
darling, tsaya ki ji.
"Ni ba abinda zan ji, sai amincewarka, in da
ba don Gwaggo ba da tuni na fitar dashi." Yanzu
kam shima fuskarsa ta yamutse, tsawa ya daka
min wanda yasa na natsu. Tahir kuwa ya fashe
da kuka don shima ya firgita. Ya miko min shi.
"Bashi nono." Ya umarce ni.
Dole na amshe shi nasa mai kan nono a baki
ya amsa kuwa ya yi shiru, abin takaici ficewa ya
yi ya bar ni nan, kuka na saki ina kara tausaya
ma Tahir. Haka na ci kuka na na hakura, da na
gama bashi nono na kai shi gun Gwaggo za ta yi
masa wankan dauri.
Kwanan Mas'ud uku amma babu abinda ke
tsakaninmu sai gaisuwa, ya share ni, abun na
103
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
daure min kai, shin ni ke da laifi ko shi? Na lura
in ban da hidima da dansa babu abinda yake yi,
kullum yana tare da shi dalilin haka zaman daki
na koma yi, don irin haushi da rashin son
ganinsa da nake yi, nima nayi banza da
sha'aninsa ko kallo bai ishe ni ba, Gwaggo ta
same ni ta ce, ina jin duk yadda ku ka yi da
Amir, nasan halin ki, da wauta, kadda ki zubar
da cikin nan tunda gashi Tahir ya soma samun
sauki sosai, ki rika kula da ci da shanki, ki saki
ranki, ki yi hakuri, dibi yadda ki ka zama duk
kin jeme, don Allah ki kwantar da hankalinki,
insha Allahu babu abinda zai faru, Allah ya
sauke ki lafiya."
Kwallan idona na goge, tun daga lokacin
kuwa na dage da cin abinci ba don komai ba sai
don Tahir ya samu isasshan ruwan nonbo,
Mas'ud kuwa har a lokacin ba ma ko magana.
Haka ma ya yi shirinsa ya wuce Gusau daga can
ya ce da Gwaggo zai wuce Dubai.
A bakinta na ji tafiyarsa har da sakon kudi da
ya bar min, abun na bani mamaki, wai me yake
nufi shi bai dauki laifinsa ba ne? Har ya ke fushi
dani? Ni ya kamata in yi fushi da shi ba karfin
halinsa ya yi yawa wannan shi ne Hausawa ke
cewa a duka ka a hana ka kuka.
Cikin ikon Allah Tahir ya warware sosai har
ya soma maida kibarsa, ciki kuwa ya ci gaba da
104
i
Baki Biyu Sameera Mustapha:
bunkasa ha rya kai wata biyu, ba mu waya da
Mas'ud sai dai ya kira Gwaggo su sha hirarsu,
sau da yawa muna tare da ita yake kira. Tun bana
damuwa har na fara, da da hali da na ce taba ni
in ji koda muryarsa, sai dai taurin kaina ya hana
ni, watannnin Tahir uku da rabi gani da ciki wata
biyu, ikon Allah.
Ranar Alhamis na shirya zan fita gidan
Umma na ke son zuwa, Gwaggo ta ce Mas'ud ya
ce, kada in sake fita sai da saninsa, don haka in
buga masa, na ce ki fada masa don Allah ba zan
fada ba ai kina da abinda za ki neme shi ki buga
ki tambaye shi, har raina abun ya bata min rai,
na koma daki na dauki waya ta na bude na buga
masa, ya dauka bai yi magana ba. Ni na fara
gaida shi ya amsa da jin yadda yake maganar ya
matsu in fadi uzirina ya ajiye, daurewa nayi na
ce dama ina son in fita ne ban amince da fitar
taki ba, yana gama fadin haka ya ajiye wayar,
kallon wayar na dinga yi, a gaskiya na shiga
wani hali na son Mas'ud.
Sonsa nake yi a kullum, hana ni fitar da ya yi
bai min ciwo ba sai ma dadin muryarsa da naji
dama mun ci gaba da magana, bakar maganarsa
bata ma 6ata min rai ba, kewarsa ta dame ni,
gashi girman kaina ya hana ni in neme shi dole
fitar ta ta fita raina baki daya.
Hirar da suke yi da Gwaggo kadai ke sa in
105
Baki Biyu Sameera Mustapha:
1
zauna falon ko duk inda take zaune don a
gaskiya ina bukatarsa kusa dani, ban da ikon
kuma yin wani abu a kai.
Tahir na da wata kusan biyar cikina kuwa na
da watanni hudu har ya soma baiyana don in ka
ganshi ka ce ya yi wata shidda, don sosai ya fito
sauki na daya har a lokacin ba wanda ya sani ko
su Aisha ban fada ma ba sai dai ya yi na su Anti
Nafisa, suma Anti Badiya ta fada masu dan ta zo
nan gida gaida Gwaggo ta gani, tsiya kuwa na
sha ta har sai da na rika kwalla. Gwaggo ta roke
ta ta kyale ni sannan ta bari, Anti Fiddausi kam
kira na ta yi ta ce ke zarin na ki ma ko arba'in ba
za ki bari kiyi ba? Ki ka dauki wani cikin, duk
iyashegen da ki ke mana? Haka itama ta gama yi
min tsiyarta ajiye waya yana iya dole na hakura
tun ina kuke-kukena har na daina.
A kalla sai da mukai wata biyu da rabi kafin
Mas'ud ya shigo gari, muryarsa kawai na ji suna
gaisawa da Gwaggo ya sa na ji wani irin farin
ciki, sai ka ce dani yake hirar, ina daki amma ina
lekensa ta kofa, ya yi kyau sosai ga saje da ya
bari ya yi kwance a fuskarsa, kai Mas'ud dan iya
ado ne, ya yi shigar sa a saukake, yadi ne mara
nauyi a jikinsa, ya yi bala'in kyau a idona. Ban
da halin zuwa falon don kunyarsa nake ji, ji da
nayi ya ce, zai fita yasa naji bakin cikin hakan,
wulakanta ni Mas'ud yake son yi, gashi sonsa ya
106
Baki Biyu 3 Sameera Mustapha:
bunkasa ha rya kai wata biyu, ba mu waya da
Mas'ud sai dai ya kira Gwaggo su sha hirarsu,
sau da yawa muna tare da ita yake kira. Tun bana
damuwa har na fara, da da hali da na ce taba ni
in ji koda muryarsa, sai dai taurin kaina ya hana
ni, watannnin Tahir uku da rabi gani da ciki wata
biyu, ikon Allah.
Ranar Alhamis na shirya zan fita gidan
Umma na ke son zuwa, Gwaggo ta ce Mas'ud ya
ce, kada in sake fita sai da saninsa, don haka in
buga masa, na ce ki fada masa don Allah ba zan
fada ba ai kina da abinda za ki neme shi ki buga
ki tambaye shi, har raina abun ya 6ata min rai,
na koma faki na dauki waya ta na bude na buga
masa, ya dauka bai yi magana ba. Ni na fara
gaida shi ya amsa da jin yadda yake maganar ya
matsu in fadi uzirina ya ajiye, daurewa nayi na
ce dama ina son in fita ne ban amince da fitar
taki ba, yana gama fadin haka ya ajiye wayar,
kallon wayar na dinga yi, a gaskiya na shiga wani hali na son Mas'ud.
Sonsa nake yi a kullum, hana ni fitar da ya yi
bai min ciwo ba sai ma dadin muryarsa da naji
dama mun ci gaba da magana, bakar maganarsa
bata ma 6ata min rai ba, kewarsa ta dame ni,
gashi girman kaina ya hana ni in neme shi dole
fitar ta ta fita raina baki daya.
Hirar da suke yi da Gwaggo kadai ke sa in
105
Baki Biyu Sameera Mustapha:
zauna falon ko duk inda take zaune don a
gaskiya ina bukatarsa kusa dani, ban da ikon
kuma yin wani abu a kai.
Tahir na da wata kusan biyar cikina kuwa na
da watanni hudu har ya soma baiyana don in ka
ganshi ka ce ya yi wata shidda, don sosai ya fito
sauki na daya har a lokacin ba wanda ya sani ko
su Aisha ban fada ma ba sai dai ya yi na su Anti
Nafisa, suma Anti Badiya ta fada masu dan ta zo
nan gida gaida Gwaggo ta gani, tsiya kuwa na
sha ta har sai da na rika kwalla. Gwaggo ta roke
ta ta kyale ni sannan ta bari, Anti Fiddausi kam
kira na ta yi ta ce ke zarin na ki ma ko arba'in ba
za ki bari kiyi ba? Ki ka dauki wani cikin, duk
iyashegen da ki ke mana? Haka itama ta gama yi
min tsiyarta ajiye waya yana iya dole na hakura
tun ina kuke-kukena har na daina.
A kalla sai da mukai wata biyu da rabi kafin
Mas'ud ya shigo gari, muryarsa kawai na ji suna
gaisawa da Gwaggo ya sa na ji wani irin farin
ciki, sai ka ce dani yake hirar, ina daki amma ina
lekensa ta kofa, ya yi kyau sosai ga saje da ya
bari ya yi kwance a fuskarsa, kai Mas'ud dan iya
ado ne, ya yi shigar sa a saukake, yadi ne mara
nauyi a jikinsa, ya yi bala'in kyau a idona. Ban
da halin zuwa falon don kunyarsa nake ji, ji da
nayi ya ce, zai fita yasa naji bakin cikin hakan,
wulakanta ni Mas'ud yake son yi, gashi sonsa ya
106
Baki Biyu
Sameera Mustapridя
yi min yawa a zuciya ta, sha'awarsa ta min
gyambo a ruhina, na shiga uku wannan wane irin
so nake yi ma Mas'ud haka? Hawaye ne ya ciko
min idona, tabbas dama sonsa na tun can asali
yana tare da ni, ni nake yaudarar kaina.
Bai shigo gidan ba sai bayan sallah Isha'i,
dama tuni na idar ina jiran shigowarsa, Gwaggo
tasa Asabe ta shirya masa abinci yana ci suna
hira, kunne na kuwa na sauraren duk wani kalma
da suke fadi can naji ya ce, Gwaggo aure zan yi
a tunanina ban yi zaton na ji da kyau ba, na kara
saurarawa gabana kuwa sai ya shiga faduwa da
sauri-da-sauri, ya ci gaba, Gwaggo na gaji da
halin kanwar ki bata son a na yi iyakacin
kokarina Gwaggo kin san nayi kokari, da alama
Gwaggo tausaya masa tayi, don a sanyaye take
maganar, gaskiya ne Mas'ud nayi shaida haka
wallahi har a raina ban ga laifin ka ba sai dai
kasan ita Dayyiba kuruciya ce ke damunta, ka
Kara hakuri da ita.
Gwaggo dama akwai yarinyar da na nema
nayi mata alkawarin zan aure ta, dalilin Dayyiba
na fasa auren yarinyar, Gwaggo yarinyar taki
aure ta ce, ni take so shine muka hadu da ita da
naje Gusau gun Mama. To kin san dama Mama
ta riga tasan da yarinyar, 'yar ina ce ina fata dai
ba 'yar Dubai ba ce, a'a Gwaggo 'yar nan ce
sunan ta Jamila 'yar usulin Gombe ce, to ai babu
107
Daki Biyu Θ Sameera Mustapha:
laifi ko ba komai Allah ya baku daman auren
mata hudu Mas'ud Allah ya yi maka albarka, na
gode Gwaggo da irin fahimtar da ki ka min, haba
dai Mas'ud ko ba don kana auren Dayyiba ba
Allah fa ya baka dama, don haka ni zan baka
hadin kai dari bisa dari, Allah ya hada kansu
idan anyi amin ya fada, nan suka shiga wata
sabuwar hirar, ni kuma na yi zaune ina kuka,
bakin ciki ne? tashin hankali ne duk sun taru sun
yi min yawa, tabbas ni na ja wa kaina, hakuri
kam Mas'ud ya yi shi, to wai ya ya zanyi da
raina ne? A duk lokacin da na dau mataki akan
Mas'ud sai dai ni in ki nasara. To ni kuwa na yi
niyar kwato matsayina gunsa, insha Allahu auren
da zai yi ma sanadin na sai ya fasa shi, ba don
komai ba ko don yadda ya ce yarinyar tana tare
da Mama (Haj. Basira), zan zama sanadin hana
wannan aure sai dai ban hana in dama ra'ayinsa
son yin auran ba, to zan iya ba shi hadin kai ya
nemi wata, dama ai ni bana jin tsoron zama da
kishiya, don ba yau na fara ba, zama na da
Suwaiba na iya zama da koda mace goma ne ba
ma uku ba.
Ranar haka na ta sake-saken yadda zan yi da
hanyar da zan zame ma Mas'ud rai wada in ba
ita babu, haka na tashi ina jero nafilfili saboda na
kasa baccі.
Washegari Amina na kira a waya da jin yadda
108
Baki Biyu Θ
Sameera Mustapha:
nake magana tasan babu lafiya, don haka ta ce,
in yi hakuri ga ta nan zuwa don ko jin abinda
nake fadi bata yi ba don yadda kuka ya ci
karfina, tun a falo na tare ta da yake nasan
Gwaggo bata nan, ko gaisuwa ba mu yi ba na
fada mata abinda naji Mas'ud ya fada wa
Gwaggo daren jiya, na kare da cewa, Amina ki
taimake ni ki fada min abun da zan yi da zai sa
ya janye auren da yake son yi, riko hannayena
tayi ta ce Dayyiba ki natsu ki saurare ni, ki sani
aure daga Allah ne, idan Allah ya riga ya shirya
hakan ba yadda zamu yi, duk da Allah ya ce
tashi in taimake ka, zamu bi ta hanya a saukake
kuma insha Allahu za'a dace, idan dai dama zai
yi don rashin son da yake ganin kina yi masa ne
ai har da ke ciki Dayyiba, duk yadda za'a baki
shawara baki dauka, yadda Mas'ud ke hidima da
ke da kin hakura kin kwantar da hankalinki da
kin gama mallake zuciyarsa, babu wacce zata ga
Mas'ud bata kara kallonsa ba, ki duba ki ga ya
aure ki a matsayin bazawara ki sani fa bai san ke
budurwa ba ce, ya kamata kema ki sauko ko don gwaninta da ya nuna na yin hakan, hannunta ta
kai kan cikina, nayi saurin kallonta, ta ce ba dai
ciki ne da ke ba? Humm Dayyiba kenan, ashe
rashin lafiya Tahir sanadi ne har muna ce miki
hakori ne kai Allah ya yi miki zurfin ciki Dayyiba. Ni dai tagumi na maka ina saurarenta,
109
Baki Biyu Sameera Mustapha:
wata nawa ne? hudu, na fada ina dubanta. Allah
ya sauke ki lafiya, anya cikin nan bai fi wata
hudu ba? Allah watanninsa kenan, mun dade
muna tattauna ta inda zamu fara, bata tafi ba sai
da Gwaggo ta dawo.
Yau bai shigo gidan da rana ba sai lokacin da
ya san zai ci abincin dare, dadin da naji shine da
.ya yi wa Gwaggo a kwana lafiya, ina jin haka na
tashi na saka wata irin nighty da iyakar ta
cinyata, dama tuni Tahir ya yi bacci, har da
turara jikina nayi da turaren wuta, ni kaina nasan
ba karamin kyau nayi ba, abaya na saka na jе
gun Asabe na tada ita don har tayi bacci na ce,
taje daki na ta kwana da Tahir. Na isa bakin
kofar dakin da nasan yake, ban jira bata lokaci
ba na sa hannu na murda kubar kofar, sa'a nayi
don kofar a bude take.
Na shiga a hankali falon ba kowa kuma wutar
a kashe, sai dai haske da ya dan fito daga cikin
dakin bacci, a sanda na isa ina lekawa yana
zaune kan table da laptop a gabansa yana
latsawa, yana sanye da farar singilet da gajeran
wando, gashinsa ya yi luf-luf a jikinsa, ya yi min
kyau sosai. Da hanzari na bar wurin na cire
abayar dake kan nighty na, na zare ribon din da
ke daure a gashi na, dama nayi kitson kalaba
gashi ya kwanta a bayana, ajiyar zuciya nayi
kafin na yi karfin hali na kama hanyar dakin,
110
Baki Biyu Sameera Mustapha:
cikin sa'a kuwa ya jiwo sanadin motsin da ya ji
idonsa akaina, tabbas tarkona ya kamu don ya
kasa dauke ido a kaina, biron da ke hannunsa ya fadi kasa, da alama rudewar ganina ne, ya sunkuya zai dauka nayi şaurin karasawa inda
biron yake na dauka, kallona ya yi ya koma
zaune, ni kuwa cike da kissa na zare rigar sama
na rage da shimi, wadda komai nawa ya kasance
a waje, na haye kan cinyarsa muna kallon juna.
Duk wata kunya na kauda ita, na rika
kallonsa cikin idonsa na ce, I miss u, na soma
kissing din fuskarsa a hankali, na kai bakina kan
kunnansa ina cewa, I love you, na kai hannuna
kan kirjinsa cike da son tayar masa da hankali,
na tube masa singiletin da ke jikin nasa, duk da
ban taba yin hakan ba nasan nayi nasara don tuni
yanayin idonsa suka sauya sun koma kamar mai
jin bacci, ina ganin haka na mike so nake in ga
ko ya kamu da sinadirin da na saukar masa, na yi
kamar zan bar wurin da yake, riko hannuna ya
yi, ya yi magana muryarsa a sarke, ina kuma za
ki? Tuni na karanto abinda ke ransa, mikewa ya
yi ya kai hannunsa ya sabule 'yar shimin da ke
jikina a saukake, ya dauke ni cak ya aza tsakiyar
gadon dakin, ko wutar daki bai kashe ba, ya
soma aiwatar da wani irin soyayya, nima kuma
ina maida martani, na bashi hadin kai fiye da
yadda yake tunani, a ranar har da sumbatu
111
ya
Baki Biyu Sameera Mustapha:
rika yi, ni kaina na ji dadin yanayin da muke ciki,
bamu natsu ba sai da muka murji juna son ranmu.
Da Asuba na riga shi tashi, nayi wanka na wuce
sashen mu, karfe tara saura na gama hada mashi
breakfast, na dau waya na kira shi, ringing biyu tayi
ya dauka. Na yi saurin cewa, Hello! Ya amsa da jin
muryarsa a sake take, na ce dama abincin kari
ne.....ya katse ni, ayya ai na riga nayi, ya yi shiru, ni
kuwa wani irin abu-na ji da har na kasa magana, ya
ci gaba, na gode ban amsa ba kuma ban kashe wayar
ba, o.k to ba damuwa ban zan aiko a karba don ni
har ma na bar gidan ina side na aikin da nake yi, a
sanyaye na ce, a'a bar shi kawai na hada na rana. To
shi kenan, karfe nawa zan turu?"
Karfe daya ko bayan azahar, it's ok, sai Allah ya
kai mu. Sai a lokacin nasan nayi sakaci da har ban
san irin abunda Mas'ud yake ciki ba, dole in tashi in
rungume mijina.
Cikin kwana hudu na gama janye hankalinsa,
tuni muka zama tamkar dama haka muke, ni kaina
abun na ba ni mamaki, ashe abun haka yake da sauki
dama ni ce na so in yi ma kaina sakiyar da ba ruwa?
Abunda na yi shine abincin sa ni da kaina na ke
hadawa, zan tabbatar da na yi abinda zai iya ci
dadina dashi ba ya tadan abinci, komai ka ba shi
yana ci, wanka ma tare muke yi, da baya zaman
gida, amma tun ranar da na iske shi daki ya fara
dawowa gida hatta break ya fito gida zai dawo.
Da ya sami kwana takwas aka yi masa waya
cewa Amina ta haihu, muna zaune tare dashi a falo
112
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
bayan ya gama cin abinci ya ce, in shirya gobe zamu
Gusau, murna ta kama ni ko ba komai na dade ban
ga su Babah Mairo ba, in ban da waya da muke yi. A
daren nake ta shiri, da na fadawa Gwaggo ta се,
Allah ya tsare ya kai lafiya.
Washegari tun karfe bakwai saura muka kama
hanya, don haka muka isa da wuri. Na yi murna nan
ganin iyayena cikin koshin lafiya, sai da muka samu
kebewa da Babah nake fada mata auren da-Mas'ud
yake son yi, daga farko fada ta rika yi min, ashe
Gwaggo ta riga ta fada mata komai daga baya kuwa
lallashi ta rika yi har ta hada da nasiha.
Da yamma ina zaune falo gab da Babah, ina cin
tuwon masara da miyar kuka, nayi matukar kewar
tuwan Babah, daga bakin kofa na tsinkayo sallamar
Mas'ud ya shigo bayan Babah ta amsa masa yana
rike da Tahir hannunsa, Tahir kiwya ne da shi, baya
yadda da kowa daga ni sai mahaifinsa, da yake yana
shan madara agun sa yake tunda muka shiga garin
Gusau, ya sami wuri ya zauna kasa kan kafet yana
gaida babba, na lura akwai suruku ta tsakanin
Mas'ud da Baba, ai Tahir na kyalla ido kai na ya
soma soma son zuwa wurina, Hassan ya shigo ya се,
ana sallama da Baba waje. Tana fita ya matso kusa
dani ya ce, honey me ki ke ci haka baki ma damu da
shigowarmu ba? Na yi banza dashi, Tahir ya soma
rigima na karfe shi na sa masa kan nono a baki,
Mas'ud ya ci gaba da kallona, ki shirya muje gun
Amina. To! Kawai na ce na ci gaba, da cin abincina.
Bayan na gama na mike da kyar na mika masa
113
Baki Biyu Θ
Sameera Mustapha:
Tahir, kallo na ya yake yin yana dariya, haushi ya
kama ni na wuce na shiga dakin Baba.
Dressing na dauka sosai lace ne mai bala'in
tashi, a Dubai Mas'ud ya sai min shi, kallon lace din
green ne amma matured da ka gani kasan ba karami
ba ne, ni kaina na san nayi bala'in kyau, duk da
ramar da ke tare dani, amma nayi haske sosai ga shi
fatar jikina ya yi mul-mul kamar 'yar morroco na
saka flat slippers baka ke na fesa turare na fito na
tarar ya fata na ce da Baba zamu gidan Haj. Basira.
Da sauri ya bude min kofa na shiga, ya shigo ya
miko min Tahir da ya soma son yin bacci, na
rungume shi da muka fara tafiya ya rika duba na
yana murmushi, da muka hada ido harara na galla
masa, ya ce wai me nayi miki ne? Tun jiya da muka
iso ko wayata an ki dauka, laifin me nayi? A fada
min kada ciwo zuciya ya kama ni, na zumbure
bakina, a shagwabe cike da kisisina na ce, babu
komai, haba honey ta ki fada min ya za ayi in san
laifina baki fada ba.
Jiya kana tare da amaryar taka ne? Na ida zaman
ina kallonsa, ajiyar zuciya ya yi ya ce, wace amarya
kuma? Da yake maganar ta zo masa a baza ta sai duk
yanayin fuskarsa ta canza. Ba au re zaka yi ba? Na
fadi maganar babu jin komai a tare da ni bai amsar
sa da nake son ji. Ya ci gaba da tukinsa a hankali
kamar baya so, wa ya fada miki aure zan yi, a bakin
ka naji murmushi ya yi sannan ya yi parking a gefen
titi. Ya juwo sosai yana duba na, Dayyiba ban taba
tunanin zan yi tunani in yi aure ba sai lokacin da ki
114
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ka murje ido ki ka nuna min kiyayya kiriri, ki ce ba
ki son haihuwa da ni, in kin manta in tuna miki kin
san cikin Tahir haka ki ka so zubar min da shi da na
yi asararsa, yanzu kuma kina son ki zubar da wannan
to don Allah me ki ke so in yi? Wallahi kin ji
rantsuwar musulmi da kin zubar da cikin an da ba
karamin abu zai taso ba, to daya ke Allah bai
kaddara fitina tsakanina dake ba sai ya sauya miki
shawara, sannan zance aure tabbas na nema kuma
ina kai, hawaye ya zubo min jin hannunsa nayi a
fuskata, baby don't cry kin san fa kina tare da
condition, sannan bana son ki bata wannan kwalliyar
taki kin yi kyau sosai. Aure za ka yi da gaske? Na
tuba ka yi hakuri ba zan sake ba nasan nayi kuskure
kayi hakuri, murmushi ya yi yana dai rike da fuskata
tare da goge min hawaye, ya ce kada in yi auren
kenan? Ban iya cewa komai ba na sunkuyar da kaina
kasa. Fita ya yi daga motar ya zagayo guna ya karbi
Tahir, ya bude baya ya kwantar dashi ya dauko
tissue ya bani gyara fuskarki zamu yi magana an
jima. Ban musa ba na karba na goge fuskata da yake
da Foundation a fuskata bata wani lalace ba mun isa
cikin gidan da gani gidan a cike yake, na fito da
sauri na dauki Tahir, kawo shi in rike maki shi na ce
a'a ni zan rike shi ina magana ina lullube cikina,
dariya ya saki, kunya ki ke ji kada a gan ki da ciki?
Na murtuke fuska ba tare da nayi magana ba, ki
kawo shi, ni dai ka kyale ni, na kama hanyar shiga
gidan don dama gida ba bakona ba ne, a raina kuwa
ina tunani ırın badakalar da za'a yi.
115
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
Da na isa ciki da Amina muka fara haduwa,
murmushi ta saki ta iso guna ta karbi Tahir budc ido
ya yi ya fara kuka ta miko min shi tana min kallon
tsab, hannunta ta kai kan cikina, ba dai ciki gare ki
ba? Jina yi kamar in nutse da kunya, ikon Allah ta
fada ta riko hannuna muka isa dakin Haj. Basira
gashi Tahir ya soma rigima abun mamaki Haj.
Basira ta iso ta karbe shi ta ce, kai yaron nan ka cika
fitina, geshi Maman taka ba cikakkiyar lafiya ne da
ita ba, jikina ya yi sanyi na sa kai na kasa, shin
mafarki nake yi