saboda shi ne na gwammace ba ka daina ba
dan Mama, baki ya saki yana kallon fuskar Haj.
Basira, ya ma rasa abinda zai ce mata, don
35
Бок 5
Sameera Mustapha:
bala in mamaki, da ta bashi. Ajiyar zuciya ya yi
tare da mikewa ya bar dakin, duk nacin kiransa
da take'yi, ya yi tafiyarsa tare da Kara nadama
akan abinda ya aikata, ya yi ma kansa alkawarin
ba zai kara shan wiwi a rayuwarsa ba, insha
Allahu.
Tunda ya fita gidan Alh. Ashiru ya nufa ya ba
shi hakuri akan abinda ya faru, Baban nasa ya ji
dadin hakan, shi ya raka shi gidan da Alh. Mohd
Shinkafi ya ba Mal. Sabi'u yana zaune duk
ilahirin jikinsa a sanyaye ya rika ba da hakuri,
Mal. Sabi'u ya ji dadin hakan fiye da yadda ake
zato, nan dai ya yi masa nasiha mai ratsa jiki
dama ya riga ya san matsalar sa da mahaifinsa,
don haka ya ta ba da hakuri ai tuni komai ya
wuce a nan yake cin abincin dare tare da Mal.
Sabi'u kafin ya wuce Dubai.
A nan Dubai ya hadu da wata yarinya mai
suna Raliya, Raliya Muktar, yarinya ce da ta
amshi suna gurin gasar kyau na kasar Dubai a
dalilin haka sunan Mas'ud ya bazu a duniyar
polo. Dama gashi tunda ya bar wiwi ya yi haske
ya yi kiba a lokacin ne kamanninsa da Tahir ya
baiyana, gashi dogo dashi ya yi kyau sosai Kasar
Dubai ta karfe shi sosai. Duk in da zai je yana
tare da Raliyan, bata taba yadda ya tafi ya barta
ba, a dalilin kwarjininta shima nashi kwarjinin
ya fito har ya yi yawa da 'yanmata ke mutuwa
36
Baki Biyu Sameera Mustapha:
akansa, kun san dai yadda dan wasa yake da
farin jini a rayuwar sa har dai in ya hadu.
Raliya Mukhtar Balarabiya ce da tayi fito na
fito wurin gasar kyau ta 'yanmata a London ta
zama Queen har ta fara acting film din larabci a
nan Dubai. Tana tashe a lokacin saboda kyaunta
da iya kissa, iyayenta 'yan ainihin Jordan ne sai
dai zamansu a Dubai ya kankama dan su koma
'yan Dubai.
Raliya na bala'in son Mas'ud itama kanta ba
zata iya fadar ainihin dalilin da yasa ba. Tunda ta
dora ido akansa wata rana da suka je turniyal ta
tseren Doki anan Dubai racing mehdon, ya cinye
wannan gasar ta san duk yadda zata yi ta manne
mashi.
Shi kuwa kyaunta da iya shiga shi ya rinjaye
shi ya zauna da ita sannan ya lura kasancewa da
ita ya maida shi tauraron mujalar Dubai, kusan kullum sai ka gansu a gaban mujalar su biyu, ba yadda ba su fitowa ko a rungume ko a yaya ma gani zaka yi, a hankali har ya zama ana daukarsa yin talla na kayan kamfani. Nan da nan ya zama shahararre wurin iya zama da mata don ba shi ke
neman su ba, su suke kawo kansu da kansu.
A hankali ya sayi gida a nan Dubai har da
motocin hawa, ko Nigeria bai cika zuwa ba,
tunda ya tafi sai da ya yi wata shidda sannan ya
koma shima a lokacin Alh. Mohd Shinkafi ya
37
Bak Biyu Sameera Mustapha:
neme shi, to da ya Kara komawa bai ma yi
tunanin dawowa ba don tsabar jin dadi da ya
samu a Dubai, kyaun abin ya na bugawa kullum
ya gaida iyayensa.
A lokacin da ya samu shekaru biyu da fara
kwallo a lokacin mahaifinsa ke gaya masa Tahir
zai yi aure, Baba zai sake aure nc? Eh, kasan fa
in lokacin abu ya yi, to sai anyi shi, haka ne to
Allah yasa ayi lafiya. To kai fa yaushe zaka yi
auren? Ni? Eh, kai, uhmm...zan yi Baba yana
magana yana sosa keya kamar yana kallonsa.
Ana sauran kwana biyu daurin auren Dayyiba
ya shigo gari abunda ya daure masa kai shine,
wai Tahir zai auri Dayyiba, yarinyar da yake
shirin aure, ita kadai yake so, ita kaďai yake
tunanin zai iya aure amma me yasa haka ta same
shi? An ya zai iya aure kuwa? Tabbas ya sani a
rayuwarsa yana son yara fiye da tunaninsa, sai
dai a wannan lokacin auren ya fita ransa baki
daya, don haka ma ranar da aka daura auren a
ranar ya wuce ya koma Dubai.
Suka ci gaba da zama da Raliya sai dai tunda
Dayyiba tayi aure ya fara tunanin mafita, bai
taba kawo tunanin auren Raliya ba, don sam ba
su dace ba a cewarsa, ya sani itama kar ta tasan
hakan don ita kuma bata ra'ayin yara ta ce ita ba
za ta haihu ba. Dama shi bai taba ra'ayin ya aure
ta ba, suna tare dai har ya dan ci gaba da zama
38
Baki Biyu Sameera Mustapha:
London saboda wani club da ya samu yana musu
wasa a can, a lokacin ne kuma wan sa Tahir ya
soma son jawo shi jiki, so da yawa suna haduwa
a London don idan Tahir ya je gun sa yake
sauka, don haka ne ma in suna tare baya yadda
ya aikata abinda yasan bai dace ba ta hanyar
matan da yake tare da su, akwai lokacin da Tahir
ya yi masa maganar aure, dariya kawai ya yi,
yasan yadda ya yi aka bar maganar.
Shakuwar da suka yi yasa Tahir ya daina
zuwa London sai dai yasa Mas'ud ya wakilce
shi, har ma a sanadin haka ya samar masa
business a nan London, business din da ya dade
yana nema bai samu ba. Sai gashi cikin wata
guda ya samu, dawowan da ya yi dole ya sakar
masa aikin ya ce, lallai shi ya kamata ya ci gaba.
Sam bai so hakan ba, yana gudun kada ya samu
matsala gun wasa polonsa, sai da Tahir ya gaya
ma Alh. Mohd Shinkafi ya yi masa magana
sannan ya amsa. Shi fa baya son ya takurawa
kansa da yawa, kudın da yake samu a wurin
wasan polo da talan da yake ya ishe shi zaman
rayuwarsa.
Ana cikin haka kuwa, Allah ya bashi sa'a
sosai har ya gaya ma Tahir ya kamata su saya
gida a London, da jin haka Tahir ya matsa ma
mahaifinsa sai dai suje London su ga abinda
Mas'ud ke yi, bai yi sa'a ba don zuwan ba zata
39
Bakı Biyu
Sameera Mustapha:
suka yi masa. Mata ne da maza cike а
department din sa wai party ake yi na Valentine.
Saukin abun shi baya shan giya baya shan
komai, amma taba kam kamar akansa ta samo
sunanta.
Da suka kwankwasa kofar shi da kansa ya
bude masu, take hankalinsa ya tashi, rudewa ya
yi ya ma rasa ta inda zai fara, juyawa ya yi yạ
koma ciki ya kashe radiyon da ke aika masu
kida, ya bada hakuri akan mahaifinsa ne ya zo,
dole party ya zo karshe duk yawancin su sun
buge a zare suka firfito in sun fito sai su gaida su
Tahir da ke tsaye cirko-cirko suna kallon ikon
Allah.
Da sauri ya rika kwashe kwalaben da aka yi
amfani da su ya dan gyara falon, ya bude
window don warin wiwi, sigari da giya ya fita,
ya dauko room freshner yana fesawa, a lokacin
suka shigo ya rasa abinda zai yi da kunyar da ya
ji, sun sami wuri sun zauna suna kallon shi, a
kasa kan carpet ya zauna yana gaida su, a
sanyaye suka amsa masa, sun ma rasa ta inda za
su fara. Tahir ne ya dan gyara zamansa ya ce,
haba Amir, wannan ita ce rayuwar da ka daukar
wa kanka? Alhaji ya amsa dama neman ta inda
zai fara yake yi, fada yake yi sosai ta inda yake
shiga ba nan yake fita ba, sai da ya zage shi tatas
ya kuma ce dashi, to idan haka ne kuwa tunda ya
40
Baki Biyu Sameera Mustapha:
koma baturen karfi da yaji, sai dai ya goge
sunansa a matsayin mahaifinsa, ya nemi wani
uban ba shi ba. Idanun Mas'ud sun yi jajir kamar
garwashin wuta, kamar ya yi kuka ya marairaice
murya, kayi hakuri Baba, ba zan hakura ba,
Amir na gaji da fitinarka, ya ka ke son in yi da
kai ne wai? Yanzu fa zuwa muka yi don mu baka
labarin abinda ke damun dan uwanka don a raba
aikin da yake yi a baka saboda a zatonmu ka
daina halinka na shirme, shine ya matsa in zo mu
fada maka abinda muka yanke a.....Baba don
girman Allah kayi hakuri, na tuba. Dole Alhaji
ya daina fadan saboda tashin hankalin da ya gani
a kwayar idon Mas'ud.
Ajiyar zuciya ya yi ya dube shi cikin ido ya
ce, Amir dan uwanka Tahir ba ya da isasshen
lafiya, shi ne yake son ka fara kula da dukiyarsa
ta nan da Lagos, da sauri ya dubi Tahir ya ce, me
ke damunka? Ciwon kirji ne ulcer ce ta cini ta
cinye har ta taba min zuciya da hanji, na tashin
hankali tausayin su baki dayan su ya kama shi ya
ce, shine baka taba gaya min ba, nima ban san
abun ya yi tsanani haka ba sai sati biyu da suka
wuce don Allah Amir ina son in baka amana a
hannunka, kai kadai na yadda da kai, don haka
nake son in mallaka maka duk wata dukiya da
nake juyawa, saboda ina tunanin abunda zai
kasance nan gaba. Alhaji ya riko hannun Tahir
41
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
ya ce, zaka warke insha Allahu. Tahir wanda
idansa ya cika da kwalla, ya ce ku yafe min ku
gaya kowa ma ya yafe min in na mutu don a
gaskiya.....Mas'ud ya katse shi ya ce, haba me
yasa ka ke fadan irin wannan maganar an gaya
maka ana rubuta ranar mutuwar ka a goshi ne?
murmushi Tahir ya yi ya ce, to Allah yasa muji
alheri, ya fito da takardu daga cikin jakar da ke
gefensa, ya bude duk labarin dukiyarsa ne, ya
mikawa Mas'ud gashi kayi signing, ya mika
hannu zai karba sai Tahir ya hada da hannunsa
ya rike gam, ya ce Amir ka rike wannan dukiyar
amana saboda Allah ka ji, Mas'ud ya girgiza
kansa, insha Allahu za ku yi alfahari da ni na
gode, Allah ya bar zumunci, mahaifinsu kallon
su kawai yake yi tausayinsu ya kama shi ji yake
tamkar ya karbi ciwon da Tahir yake da shi yasa
ma kansa, to amma ya zai yi kowa da nasa rai
kuma kowa da nashi zai yi amfani.
Cikin wata daya ya hađa shi da duk inda yake
aiki har zuwa Thailand, har an fara bugawa a
mujala cewa Mas'ud ya daina wasan polo saboda
anyi wasa ya fi biyu da club dinsa ba ya ciki
sakamakon haka kuma ana samun rashin sa'a.
shi kuwa ba wai ya daina ba ne so yake ya yasan
business din da Tahir ya bar masa shi yasa ya
dauki hutu na shekara daya tal, don ya samu
natsuwa. Raliya na ganin haka tasan mutumin
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
nata ya zama milloniya don haka ta fara yi masa
zancen aure, shi kuwa a lokacin a gaskiya ba
wannan ne a gabansa ba, don bai da ra'ayin aure
a wannan lokacin, gashi ko zama ma baya yi,
sam basa samun isasshen lokaci tsakaninta dashi,
rannan kawai sai ya yi tunanin ya yi weekend
din sa a Dubai, ya shirya ya tafi cike da nishadi,
abinda ya iske ne rabonsa da Raliya don maza
take kai masa a gida, wannan lokacin ma turmi
da tabarya ya kama su, sam ransa bai 6aci ba,
don dama yana neman hanyar da za su rabu,
gashi a saukake sun rabun.
Aiki sosai ya ke yi sam baya da lokacin
kansa, saukin sa abunda ya karanta kenan sannan
yana da saurin fahimta ga ilimin iya sarafa aikin
nan da nan abu ya bunkasa saboda ribar da ake
samu ta ninku cikin wata shidda da ya soma aiki.
A wannan lokacin ya hadu da wata yarinya 'yar
Yobe bafulatana ce tana da kyaun gaske a
Gombe suka hadu lokacin da yaje ziyarar
abokinsa Sa'idu. A gaskiya ya sota sosai har
yana tunanin aurenta, kuskure daya da suka yi
shine da ya santa mace tun kafin suyi aure.
Tabbas, yasan ya same ta a cikakiyar mace
wadda bata san namiji ba shi ne namiji na farko
da ya kwana da ita don haka nema ya yi mata
alkawarin zai aure ta, bai taba zaton zai same ta
a kintsattsiyar mace ba, don haka tare suke da ita
Baki Bıyu
a vanzu.
Θ Sameera Mustapha:
Jamila Abbas, iyayenta 'yan usulin Gombe
ne, zama ne ya kai su Yobe, suna da arziki daidai
gwargwado don sun ba 'ya'yansu ilimi na boko
da Islama, suna da ilimi sosai don Jamila ta na
400 level a lokacin da suka hadu da Mas'ud ga
shi zata gama kenan wannan abu ya shiga
tsakaninsu da Mas'ud, ita kam sosai ta so ta kai
budurcinta gidan mijinta, to amma a ganinta
yadda maza sukai karanci a yau zata rasa
Mas'ud in bata bashi hadin kai ba don ta lura
don son harka me gashi da iya soyayya sam bai
maida kiss bakin komai ba gashi in ya fara dole
ne maki mace duniyar da ki ke ciki. A gaskiya
rasa namiji irin Mas'ud asara ne a gunta don
haka babu abunda zai nema a gunta ya rasa.
Yana da wata goma da fara ciki ciwo Tahir ya
tsananta, sai dai Tahir ya ce, kada a gaya mashi a
wannan lokacin saboda aiki ya yi yawa sosai, har
sai da aka dawo dashi Nigeria yana asibiti ciwo
ba ji ba gani abun ya tsananta shi ne fa Alhaji ya
buga masa waya, ai bai bari ya kwana ba ya diro
Nigeria. A nan asibiti ya ci karo da Dayyiba tayi
masa kyau sosai ta kara budewa ta cika
cikakkiyar mace. Duk da yana tare da tashin
hankali irin yadda yaga Tahir ya zama sai da ya
yi mata kallon kurila saboda ba karamin haduwa
tayi ba, zuwansa kuwa da kwana biyu Tahir ya
Baki Biyu Sameera Mustapha:
cika ya bar su da jimamin rashin sa.
Da ya kama aiki a gaskiya babu ranar da zai
kwana ya tashi bai yi tunanin Dayyiba ba, sai dai
bai sani ba ko zata yadda ya aure ta ba, kafin ya
ganta ya shirya son yin auren ya so kwarai ya
aure Jamila, sai dai ganin Dayyiba komai ya
juya. Tunaninsa duk ya koma gun Dayyiba,
gashi ya kasa gaya ma kowa, ba lantana
mahaifiyarsa da ya lura baya da makiya irin
Dayyiba, sam bata san ta yanzu haka tun wata
biyu da suka wuce take damunsa akan yasan
yadda zai yi ya kwace dukiyar da Tahir ya
mallaka masu ita da Gwaggo, mahaifiyarsa bata
san a yanzu ma wanda ya ce zai takurawa
Dayyiba sai inda karfinsa ya kare ba. Saukin ta
daya ita ta haife shi shi yasa yake kyale ta yana
biye mata da to.
Jamila. Abbas kuwa abin ya fara damunta
sosai gashi dai ta gama Makarantar da yake ta
cewa ta gama, cikin dubara ya ce, da taje tayi
bautar kasa ta gana kafin ayi aure so yake in dan
ya aure ta ta zama secretary din sa, hakan ya yi
mata dadi sai dai ita ba haka ta so ba, to amma
ya zata yi dole ta yadda da shawararsa, ta tafi
bautar kasa.
Sai da Tahir ya sami shekara daya da rabi
sannan Alh. Mohd Shinkafi ya soma damun
Mas'ud akan zancen aure, shaida masa
45
ya
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
yarinyar da zai aura tana makaranta ne da ta
gama zai fada aje neman auren ta hakan yasa
mahaifinsa ya kyale shi. Jamila kuwa tuni ta
gama bautar kasar sai dai ta rasa abinda ke
damun Mas'ud ya dauke kafa zuwa gurinta ma
tun tana daurewa har ta kawo karansa gun
abokinsa Sa'idu. Sa'idu ya riga yasan ba aurenta
zai yi ba, don ko shekaran jiya nan da suka yi
magana ya ce shi fa yarinyar da yake son aure
tana nan, don haka ita yake son ya nema, dole ya
fada mata abinda ake ciki, bakin ciki babu
wanda bata yi ba, gashi ta riga ta sa son sa a
ranta. Mas'ud ya yaudare ta ya ci amanar ta don
haka ita kuma ta dauki alwashin zata shiga ta fita
a halin ko kaka sai ta aure shi, a ganinsa ya cuce
ta ya dauke budurcinta da take alfahari da shi sai
rana tsaka zai aza mata gyada a hannu to ba zai
zauna lafiya ba sai dai ya dawo ya aure ta.
Shi kam yana nan yana tunanin yadda zai yi
ya tunkari iyayensa da wannan zancen gashi
wata shidda da mahaifinsa ya dibar masa ya cika
ya ya zai yi? Yasan ba karamin aiki ya dauko wa
kansa ba don kuwa Dayyiba ko kallo bai ishe ta
ba ya lura duk ran da ya je Kaduna in ban da
kallon raini da miskilanci babu abinda ke
damunta, bata bari ma yayi mata magana ba ta
bari ma su kasance su biyu a gu daya,
mahaifiyarsa kuwa duk tabi ta dame shi akan ya
46
Sameera Mustapha: Baki Biyu
zo ta sama masa mata, bai masa kan yaje ya
ganta ba don ba wannan ne a gaban sa ba. Alhaji
kuwa yasa masa ido har ya kara watanni huрп
cur bai ce masa kanzil ba akan aure shi kansa
Alhajin ya rasa abinda ke damun yaron nasa,
namiji har namiji amma aure ya ki shi, abun sai
addu'a don haka ya sa a fara addu'a don shi kam
ya san babu mai shiryawa sai Allah (S.W.A).
Lokacin da ya shigo Nigeria gidan Gwaggo
ya sauka dama haka ya saba yi, ita din ya iske a
falo maimakon Dayiba, don ya saba ita yake
yawa gani a falon, bayan ta tarbe shi ne ta rika yi
masa fada akan abunda yake sam bai da kyau.
Tun can dama tana yi masa fadan to amma na
ranar yafi tsanani, don haka ya daure ya cije ya
fada masa ainihin abinda yake so, abin ya bala'in
ba Gwaggo mamaki sai dai tayi kokarin maida
shi ba komai ba har take ce mashi Amir, dama
zaka iya auren Dayyiba? Bazawara ce fa
murmushi ya yi ya ce Gwaggo ai ko Annabi
Mohd (S.A.W) da bazawara ya fara gashi kuma
ta girme shi ma ba ita ta karasa masa. Ta ce zan
ba da hadin kai sosai a wannan al'amari sai dai
ina so ka rike amana Amir, ya dauki alkawarin
rike amanar Dayyiba ya ce, gobe zai wuce
Gusau yasan Alhajinsa na fushi da shi, to ai sai
ma in bika mu fadi komai, to Dayyiba fa
Gwaggo? Ta ce, ka kyale ta ba sai mun fada
47
Baki Bivu Sameera Mustapha:
mata ba, kasan ta da rigima kuwa? Kyale ta
kawai sai mun fada can Gusau, don haka zan
shirya gobe mu tafi tare ayi komai a idona.
Yadda yake tunanin abin zai yi wahala amma
cikin sauki kowa ya amshi maganar mahaifinsa
ya sa masa albarka, sosai ya ji dadin hakan da ya
yi su dai fatan alheri suka rika yi mahaifiyarsa
kuwa har fushi tayi dashi duk da bai bari suka
zauna ba, gudunta ya rika yi har ya koma. Bayan
an sa ranar daurin aure sati daya.
A gaskiya rayuwa wata rana tana da sauki,
wata rana kuwa sai ta zama tarihi, abu kamar ba
ayi ba. Bai dawo ba sai ana jibi daurin aure, abin
mamaki ya hadu da Sa'idu, tare da Dayyiba,
dama ita ce kanwarsa da yake ta bashi labari,
ikon Allah.
Ya lura bata son irin kallon da yake mata, shi
kuma har a rana bai jin zai iya daina kallonta don
a taurari ita ce zahra.
Ranar sati aka daura aurensa da Dayyiba,
abun haushi an hana shi ya yi mata magana dole
ya wuce Dubai saboda akwai wasan da za su yi a
can, har cewa ya yi ya fasa yin wasan, Alhajinsa
ya ce, ai bai isa ba sai dai ya tafi daga baya za'a
turo masa matarsa, akan dole ya wuce. Ranar
Litinin, ya zamto a kullum sai ya buga ma
Gwaggo don ya ji irin shirin da suke yi, tun bata
son gaya mashi abunda ake ciki har dai ta kai ta
48
Baki Biyu Sameera Mustapha:
fada masa rashin lafiyar Dayiba, hankalinsa ya
tashi sosai amma ya ya iya, manya sun yi
magana dole ya hakura har sai sun gaji sun turo
mai matarsa.
Tunda yake babu macen da ke dasa masa
magana irin Dayyiba, ita kadai ce ke fada masa
bakar magana da baya iya kwanciyar hankali ko
dai bata san irin son da yake mata ba ne, ya sha alwashin duk yadda zai yi sai ya yi ta so shi, don
shi a duniya babu wacce yake so sai ita.
** **
Ina cikin Jirgi ina tunanin wannan karfin hali
da aka yi min, ko macen da bata aure wato
budurwa an bata 'yancin ta zaba wa kanta mijin
aure, ina nufin wadda ta balaga, sai gashi ni ban dauke ni bazawara ba amma kuma an danne min
hakki. Ina tunanin wannan lamari bacci ya
dauke ni.
Shi kuwa Mas'ud yana racing na international
world cup 2010, lokacin har sun gama kuma shi
Allah ya ba sa'a, gobe ma za suyi da wani group
din. Ya isa gida kenan, ya ga missed calls da
yawa, ya kai missed calls hamsin, shine ma
sanadin batery ya yi law. Da sauri ya bugawa
Gwaggo don nata yafi yawa. Bayan sun gaisa
take ce mashi, Dayyiba na kan hanya, ai bai jira
ba ya buga ma direbansa ya ce, maza yaje airport
49
Bakı Bivu Θ Sameera Mustapha:
ya sanar yana da bakuwa, sunanta Dayyiba
Sabi'u.
Haka kuwa aka yi, ya yi sallama da Gwaggo
ya buga airport aka ce a haka ne ga ma jirginnan
yanzu ya sauka, da saurinsa ya buga ma Kabir
Al'amin, wato Embassy na Nigeria waya, ya сe,
Eh, yana wurin don haka abun ya zama la sauki.
A lokacin ya fara gyaran gidan da gidan a barka
ce yake.
Ni kam ban tashi ba sai da Jirgi ya sauka, sai
da suka gama yi mana screening sannan
mutumin da ya gabatar mana da shine wakilin
Nigeria shi ya tambaya ko ni ce Dayyiba Sabi'u?
Na amsa Eh, ni ce, ya ce maigidanki ne ya ce in
sada ki da wanda zai kai ki masauki." Tabdijan,
lallai ma wannan mutum, isa ta mai yawa. Da
yake kyauta aka bashi ni bai da lokacin da zai zo
ya tarbe ni, zan gani wane irin zama zamu yi.
Na isa na shiga motar na wani hakimce a
gefen owners corner na sha mur, sai ka ce ni ce
mai motar, da muka isa gidan shi ya fito da sauri
ya bude min kofa, da yake da a baya nake sai
shigar ta yi daidai da ancen, shi ya riko trolly na
ya shiga gaba ina binsa a baya. Ta lift muka bi
sai da muka kai hawan karshe na uku, sannan
muka fito muka isa kofar shiga, dama tuni ya
dinga bugawa kamar zai fito waje, ya bude muka
shiga, ya ce da turanci, oga ya ce dama idan mun
50
Baki Biyu Θ
Sameera Mustapha:
iso ki yi hakuri ki jira shi yana nan zuwa, ban
amsa ba na samu wuri a daya daga kujerun da ke
falon na nutse, kai kujerar ba dai laushi ba, na
zare ido ina kallon falon don a gaskiya ba
karamin haduwa ya yi ba, littafi na ciro na soma
dubawa, wai da zummar in yi karatu sai dai sam
na kasa bana da natsuwa a tare da ni.
Ban fi minti ashirin ba, na ji ana kokarin
bude kofa, gabana ya ci gaba da bugawa. Bude
kofar ke da wuya mu kai ido hudu da Amir. Ban
daina kallonsa ba, tambaya nake ma kaina, me
kuma Amir yake yi a nan? Mece се
dangantakarsu da mutumin.....?" Ya tsinka min
tunani da ya ce, "Sorry, na bar ki kina ta jirana
ko?" Maganarsa ta zo min wata iri, ba dai shí ne
Mas'ud ba?"
Kara matsowar da ya yi guna yasa na daina
tunanin da nake yi, na hade rai duk hankalina a
tashe yake. Kayan abinci naje siyowa su
Gwaggo ba su fada min kina zuwa ba sai da na
dawo daga racing, ya hanya? Irin kallon da na
saba yi masa shi nayi masa yanzu ma ban amsa
ba. Ba ki ji ina gaida ki ba ne? na turo bakina ina
gunguni, ai sai na fashe da kuka, me ya same ki
ya matso guna tare da son taba ni, kara na saki
tare da ce masa, wallahi in ka taba ni za ka gane
kuranka, kallona ya ci gaba da yi, ni kuma na ci
gaba da kukana mai tsumar da rai, lallashi ya
51
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
soma, kiyi hakuri abinda Allah ya kaddara mana
kenan, kai dai Allah ya kaddara mawa ba ni ba,
na fada masa ina kokarin mikewa, kama hanya
nayi na ja jakata zan bar falon, ya biyo ni, ina za
ki? Ya yi tambayar a saukake, ban amsa ba na
fara kokarin bude kofa, ji na yi kofar ta ki
buduwa, nayi-nayi amma na kasa. Kaina na hada
da kofar ina ci gaba da kuka, ya matso har inda
nake ina za ki je? Ban sani ba, ni kawai ka bude
min kofa in tafi, to shi kenan zan bude maki,
amma sai kin gaya min inda za ki tukunna. Wuri
zan nema in zauna inda ba zan rika ganinka ba,
don ganinka illa ce a gare ni, ya ji zafin maganar,
amma sai ya daure ya ce, kin ga dare ya yi,
amma kiyi hakuri sai zuwa gobe...." Na katse
shi, ni kam ba za ni yadda ba, wallahi an cuce ni,
da aka yi min auren dole tsakanina da kai, to bari
in gaya maka, tun wuri ka ba ni takarda ta don
wallahi ba zan zauna da kai ba. Duk da ransa ya
baci, haka ya daure yana lallashi akan in hakura
da tafiyar nan har gobe.
Jakar ya dauka ya yi ciki da ita, ni kuma na ki
barin kofar, ina nan a gurin ya yi lallashin
duniya na ki barin wurin har ya gaji ya kyale ni,
ya yi wucewarsa, ina kallo ya bude ledojin da ya
shigo da su, ya bude ya fito da abinci kala-kala
ya saka wasu a fridge, sannan ya shiga daki ya
dade a ciki ashe wanka ya yi ya saka jallabiya
52
Baki Biyu Θ
Sameera Mustapha
fara tas, ya shigo falon ya yi sallahr Isha'i, har ya
idar ya dawo ya zauna ya sani a gaba yana
kallona, komawa na yi kamar wata 'yar
kankanuwar yarinya na tsugunna kaina a guiwa
ina kuka, a hankali tare da ajiyar zuciya.
Waya na ji yana yi da Alhajinsa, bayan sun
gaisa na ji ya ce, "Eh, ta iso tuntuni, ok, gata ya
mike ya nufo ni, ya dan rankafo ya ce gashi
Alhaji na