garin nan ba ne, ya na iya, dole na hakura
na rika fada masa hanyar da zai bi.
Muna isa ban bari ya tsaya ba na bude kofa,
ina kallonsa ta wutsiyar idona murmushi yake yi
yana girgiza kansa, ban jira Gwaggo ba na fita
kira na ta yi tana cewa kin ko dauko ledar kayan
nan? Gabana ne ya fadi, kwarai naji haushin
kaina, na kuwa manta dashi a gida, dubara ce ta
fado min na rika yi mata magana ina sakin
murmushi, Gwaggo mu bar ma kayan daga baya
na kawo..." Amir ya katse min maganar da nake
yi, ya ce ki zo muje mu dauko tun da na lura ba
nisa da gida, haka kuwa maza ki je ku dauko ni
na karasa ciki mu gaisa, uwar mantuwa. Tana
maganar tana tafiya zuwa cikin gidan,
wayancewa nayi na kauda bacin raina na shige
bayan motar na zauna, dama an ce idan ka ga
fada zai fi karfinka to sai ka maida shi wasa.
Ina sauraron inga mun tafi, amma sai na ji
18
Baki Biyu
shiru, na
Sameera Mustapha:
gano abinda yake nufi, bana son in yi
masa magana gashi har lokacin sallar La'asar na
gabatowa, don haka dole na fito na shiga gaban
motar, a take ya tada muka fara tafiya, shin wai
me ke damun mutumin nan? Tafiya yake a
hankali sai ka ce yana jin tsoron hanyar, tsaki na
buga na ce, aikin banza, magana naji ya yi a
bazata da wa ki ke tsaki? Matse bakina nayi tare
da bata fuska ban ce komai ba, ya ci gaba da
tukin kamar dai yadda ya fara, ji nake kamar in
bude motar in fita wallahi..... ya tsinka min
tunani da ya ce, baby ni fa har yanzu ina kan
bakana akan ina sonki! Ya dube ni, ni kuma na
juya masa keya, ya ci gaba, kuma aurenki nake
son yi...." Na yi saurin tsaida zancen da yake yi
cike da tsiwa na ce, kada ka fara ba zan iya auren
ka ba, saboda mene? Ya yi saurin fadan hakan,
saboda bani sonka kuma baka kai matsayin da
zan aure ka ba, nima nayi saurin bashi amsa, da
alama maganar ta duke shi, sai dai bai kara cewa
komai ba, sannan ya soma tafiya cikin gudugudu, har muka kai gida na dauko ya mai do ni
bamu sake wani zancen ba, a raina kuwa wani
irin dadi naji kamar in yi tsalle, zan fita na ji
kofar a rufe, na sha jinin jikina ba tare da na dubi
inda yake ba, na ce, zan fita.
Kallona yake yi sosai na ji a jikina kuma ina
kallon sa ta wutsiyar idona, ajiyar zuciya ya yi
19
Baki Bıyu Sameera Mustapha:
ya ce. kina nufin ban kai matsayin da za ki so ni
ba? Ya yı tambayar a kuntace da wata irin murya
mai zati, dadi ne ya kama ni, da na ji irin bakin
cikin da na sa shi, na amsa shi cike da isa na ce,
"Eh haka ne, ni ka ganni nan bana burin auren
irinka, ko zanyi auren da manya zan yi don kaga
ko aure na na farko ai ba irin ka na aura ba, mai
mata na aura, ni na fi son cikakken namiji da
yasan hakkin aure, wanda ya kuma taba sanin
daci da dadin zaman auren kai din nan kafi
dacewa da macen da bata san zamantakewar aure
ba, budurwa irin ka, dariya ya saki a tunanina ina
zaton zan bata masa ne, ashe ni aikin banza nake
yi, ya ce to idan Allah yasa na aure ki fa? Ya yi
tambayar a kasaitance, nima murmushin na saki,
don na lura idan ban yi masa hakan ba zai manna
min karamin hauka, to wannan kuma hukunci ne
na Allah babu mai ja dashi, kin fadi gaskiya
yarinya, bari in barki sai anjima, idan na dawo
daukar ku, da na ji ya bude motar ban wani tsaya
na saurari karshen maganar tasa ba, na shigewata
gidan Aisha.
Na isa ciki na samu an taru sosai, nesa na
samu wuri na zauna bayan na gaisa da jama'ar
da na sani, sama-sama, nayi shiru ina tunani,
yadda muka yi da Amir. Aisha ce ta karaso guna,
ke me ya same ki haka ne, kin yi sanyi?
Bayan ta kuma Amina ce, Halima na can na
20
Baki Biyu Θ
Sameera Mustapha:
neman ki ajiyar zuciya nayi na ce, himm, ku bari
kawai menene bai faru ba ma, ku bari in baku
labari, dama ni ba sallah nake yi ba, don haka na
záuna in fada musu labarin tun farko irin
soyayyar da muyka yi da shi sai dai ban fadı irin
sonsa da burge ni da yake yi ba, a wancan
lokacin bar wannan a raina. Na bar shi a
matsayin sirrina, ni kadai.
Amina ta jinjina kai lallai 'yar uwa kinyi
advanture da yawa, dan tarihinki baki daya
yadda ki ka san fim, to ke ki aure shi mana! Na
shiga girgiza kaina ba zan taba iya aurensa ba,
mutumin da ya daga hannu zai daki mahaifina?
Allah ya tsare ni mahaifiyarsa kuwa bani da
makiyiya irinta, don ta nuna sam bata kaunar
jininmu. Yanzu haka fa ko ga mu ga maciji ba
ma yi da ita, ajiyar zuciya Aisha tayi, Allah ya
sauwake. A lokacin Anti Sakina ta iso gun mu ta
ce, ana can fa ana neman mai jego mutane na son
tafiya gashi ko hoto ba a yi ba, nan muka mike
baki dayan mu muka shiga mutane.
Sai bayan Isha'i Amir ya zo daukar mu. A
gida ma haka ya takura min, ina zaune a daki
yau ko hira ban yi ba na yi bacci. Washegari da
karfe tara Gwaggo ke ce min zata Gusau tare da
Amir, sai jibi za su dawo. Jikina ya yi sanyi
sosai, na kasa tambayarta dalilin tafiyar tata.
Dama ita bata jin nisan garin nan ta maida shi
21
Bakı Siyu Sameera Mustapha:
kamar daga Kaduna zuwa Zaria, sam ban kawo
wani abu na tsakanina da shi ba, ban ma ganshi
ba suka wuce.
Kwanan Gwaggo uku a Gusau ita da ta се
kwana daya zata yi, kullum kuma muna waya sai
dai ban tambayarta dalilin zamanta can. Sai da ta
kwana biyar da daddare na buga mata waya, bata
dauka ba, ban sa komai a raina ba, a tunanina
kila tayi bacci tunda wajajen karfe tara ne na
dare.
Washegari na sake nemanta da safe na се,
Gwaggo yaushe za ki dawo ne wai?"
"Yar kanwata nima kaina ina kewarki, ko za
ki sa direba ya kawo ki ne?"
Na yi shiru ina tunani, ban jin zan iya zuwa
Gusau a wannan lokacin ba, yadda a koda
yaushe Baba maganarsa ba ta wuce ta in fitar da
miji in yi aure, tun baba bata tanka min gashi
itama ta soma takanas ta bugo min waya don
haka na ce, ba sai ma na zo din ba zan hakura
har ki dawo yaushe za ki dawo? Insha Allahu
ranar sati zan shigo 'yar kanwata."
Ba mu jima muna hira ba muka yi sallama,
daga nan na shirya na je gidan su ya Saidu, nayi
sa'a yana gida kuwa muka zauna sai hira muke
yi cike da nishadi har na manta kewar da nake
tare da ita, da na tashi tafiya Umma ta ce lallai
22
Baki Biyu Sameera Mustapha:
sai dai in kwana tuna Gwaggo bata nan ban musa
ba kuwa, ba abunda nake so in ga ranar da
Umma da Baba za su hadu. Tare muka kwana a
daki daya har take bani shawarar in fidda miji in yi aure, na ce da ita insha Allahu komai ya zo karshe zan fidda miki in yi aure.
Da safe tare muka karya da ya Saidu yake
fada wa Umma Baba ya kira shi jiya ya ce yaje gobe, ta saki fuska ta ce Allah ya kai mu goben. Bayan La'asar na ce zan koma gidan na ga
Amir tsaye a gefen motarsa ya latsar wayarsa, ya Sa'idu kuwa sai da ya kai daidai gun sa sannan
ya tsaya abun mamaki cike da murna suka
rungume junansu suna dariya tare da tafa hannu,
zare ido nayi ina kallonsu cike da tambaya a
tattare da ni, menene dangantakar su? Ina suka
san junansu? Dama sun san juna? Tambayar da
na jerowa kaina kenan ikon Allah na fada a
baiyane shi ya tunasar da su ina tsaye a kusa da
su.
Dama kasan mutan gidan nan? Amir ya yi tambayar, labarin da na baka wata uku da suka
wuce ai wannan ita ce yarinyar da a sanadin ta
na hadu da biological father na, ok, dama sune? Kana nufin Baba Sabi'u mahaifinka ne? of
course ya fada, ya dube ni dama kuma kun hada
dangantaka tsakaninku? Kwarai da gaske ai
mahaifiyarta uwa ce a gun mahaifina saboda
23
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Inna yake kiranta, what a co-incidence this world
is a very small place.
Ni kam gajiya nąyi da saurarernsu nayi
shigewata cikin gida duk da ina son jin labarin
da suke wa junansu, ba su shigo ba sai bayan
Isha'i ashe fita suka yi, Sa'idu shi ya fara
cegowa a cewarsa Amir na waya a waje, kin san
kuwa Amir shine babban abokina? Na ware ido
ina kallonsa. Tun muna matasa muka hadu a
America tare muka fara karatu, kuma tare aka
kore mu saboda irin halaye na kuruciya da muka
sa kanmu kin san halin kuruciya yana dariya
yana bani labari, lokacin da taba bani labari
soyayyar da kuka yi tsakanin ku har da rabuwar
ku, kaina a kasa yake a wannan lokacin, ya ci
gaba da cewa kin san yadda Amir ke son ki
kuwa? Ya yi tambayar yana kallon fuskata,
wallahi da na san ke ce da tuni na hada ku,
hawayen da ya gani a fuskata yasa ya dakatar da
abinda yake fadi na ce to ni bana son sa yaya
don Allah mu dai na wannan maganar don bana
bukatarta, sukut yake kallona to Allah ya
sauwake, ya fada tare da mikewa, ni zan wuce
dare na yi da sauri na goge fuska ta haba dai ya
Sa'id karfe tara fa, sorry Sister akwai inda zamu
ne da abokin nawa kila in shigo nan kafin in
wuce Gusau saboda tare da abokina zamu wuce.
Bayan na dawo daga rakiyar Sa'id na kulle ko
24
Baki Biyu Sameera
ina tunanin wannan al'amari. Babu yadda Allah
ba ya hukunta al'amari, gashi dai Ya Sa'id ya
zama dan uwana, na jini ga kuma Amir ya zama
shi ne babban aboki gun Ya Sa'idu. Da irc-iren
tunanin da bacci ya dauke ni kenan.
Ranar sati da karfe sha biyu saura, Gwaggo ta
dawo daga Gusau, ni kam ban sani ba don barci
nake yi. Sai da biyu saura na tashi na, shige bayi
nayi wanka tare da alwala, tunda na tashi yau
naji bana jin dadin jikina, duk a sanyaye nake ko
baccin da nayi ne? na tambayi kaina, da na idar
da Sallah na saka jallabiyanta baka ce mai
duwatsu, shiga ta falo na lura da alamar baki a
gidan kayan goro ne da su cigum, sweet, biscuit
kwali-kwali sai a lokacin na lura da Gwaggo
zaune a kan sallaya tana lazimi da gudu na isa
gun ta ina murna itama rungumu ni tayi cike da
kulawa, kai Gwaggo shi ne ki ka je ki ka yi
zaman ki to ba gani na dawo da abun alheri ba,
na dube ta cikin ido na ce kwarai da gaske
dawowarki a waraka ce a gare ni a yau ban san
dalili ba, duk jikina a mace na rasa me ke damun
jikina, ba dai tyford dina zai tashi ba, ke ba wani
tyford igiyar aure ce ta hau kanki 'yar kanwata!
Aure na fada tare da zaro idanuna waye, gabana
kuwa saboda tsananin bugawa da yake sai da na
dafe shi da hannaye, na baki daya. Aure! Na
25
Bakı Biyu Sameera Mustapha:
sake maimaita kalmar, Gwaggo ta ci gaba da
cewa aure kuwa yau din nan aka daura shi da
Mas'ud, Gwaggo ina fata ba zolaya ta kike yi ba,
kin ga yanayin zolaya a tare da ni ne? ko na taba
yi maki wasa irin wannan? Hawaye ne ke
ambaliya a fuskata, na ci gaba da kallon fuskar
Gwaggo ina son in gano in da zancen ta ke
fuskanta, amma sai naga babu wasa a tare da ita,
kai na na kwantar a kan cinyarta ina kuka wiwi,
ina fadin kai Gwaggo ya zaku yi min haka? Me
yasa ba za ku bani 'yancin da Allah (S.W.A) ya
bani ba, an ki a baki 'yancin yanzu da aka daura
sai ki dauri aniyar kwatarwa kanki wani 'yancin,
ki nemi mijin da aka daura miki ki ce ya sake ki.
Mikewa tayi tana ci gaba da fada, ta inda take
shiga ba nan take fita ba, a nan na ci kuka har na
gode Allah, a take kuma sanyin da nake ji ya
dawo. Da kyar na koma dakina, bana son in yi
ma Gwaggo taurin kai, na riga da nayi alkawarin
bani kara bari in yi fushi da ita akan wani abu
don haka bayan na idar da Sallah La'asar na fito
falo ya Sa'idu na iske tare da Gwaggo suna hira,
ya kallo ni ya na murmushi ya ce, amarya kenan
kukan da na saki yasa ya daina zolayata, na isa
gun Gwaggo nasa kaina a kafadarta ina rera
kukana a hankali. Ya Sa'idu ya shiga yi min
nasiha da ban hakuri, a raina na ce, ko ba ka fada
ba hakuri ai ya zama dole, tun Gwaggo na share
26
Baki Biyu Θ Sameera
ni har ta soma lallashi, haba 'yar kanwata ni fa
dadi na da ke ba ki jin lallashi."
Har dare abu daya nake yi akan dole Gwaggo
ta matsa min nake cin abinci haka na daure nake
taunawa. Bari jima ba kuwa na dawo da shi baki
daya duk na amayar da abincin, Gwaggo bata
damu ba sai dai zafin da taji jikina ya dauka.
Washegari şai da muka je asibiti gashi duk
tsawon daren amai nake yi, don haka Likitan ya
ce za'a sa min ruwa ko da na wunin rannan ne,
tuni bacci ya dauke ni a lokacin da aka sa min
ruwan.
Can cikin bacci na ji Gwaggo na waya, a'a
Mas'ud da sauki, ta samu sauki bacci take yi
yanzu sai da ta gama wayar sannan na bude
idona, cikin yardar Allah kuwa na samu sauki
aka sallame mu, an bani magunguna zan dawo
allura na kwana uku, kai wannan wace irin
rayuwa се.
Cikin kwana biyu na zabge na rame, Gwaggo
dai kullum in ban da lallashi babu abinda take yi.
Washe gari tunda safe Baba da Babah suka zo
Kaduna na tabbata, Gwaggo ce ta yi masu
magana, suna zaune a falo Gwaggo ke kwala
min kira, na fito gabana ke faduwa don fuskar
Baba da na gani babu sassauci, naje dab da
Gwaggo na zauna don gudun kada Baba ya duke
ni, ya ce ke wai yarinyar nan me ki ka maida mu,
27
Baki Bıyu Θ Sameera Mustapha:
matanen banza ko? To baki isa ba wallahi ba zan
ja wata doguwar magana da ke ba zan bata miki
idan har ki nemi bata min, saboda na lura ke so
ki ke yi ki watsa mana kasa a ido....sallamar
Haj. Maryam ta katse masa hanzarinsa. Ta iso
ciki tana duban inda Baba yake, nan da nan
shima Baba ya maida kallonsa akan ta ya furta a
hankali Maryam! Ta amsa tana zama kusa da
Gwaggo, falon ya yi tsit na lura Babah ta gano ta
don haka sai ta tsinka shirun ta ce, Allah yau ya
hada mu Maryam, ina kwana? Ta amsa da
muryar nan ta ta, ta sanyi, suka kuma gaisa da
Baba, Haj. Maryam ta ce, haba don Allah ya
zaku rika yi mata fada haka bayan ba laifin ta ba
ne, babba ta ce ya za ki ce ba laifinta ba a yau
dinnan da muka lisafa shekarun ta kusan uku
kenan rabon ta da aure, ta dube ni a'a baki
kyauta ba 'yar nan duk da aure lokaci ne, nan fa
Baba ya amshe maganar ya ci gaba da fada ta
inda yake shiga ba nan yake fita ba, tun ina kuka
har na daina don ya dawo nasiha kuma, haba
Dayyiba ina so ki yarda da kaddara, ki dauka
kaddarar aure ne ya same ki ki mika wuya gun
Allah ya yi miki sakayya.
Nasihar da Baba ya shige ni sosai, sai a
lokacin na fara tunanin to, waye mijin? Dan
wanne gari ne? menene sunansa tukunna? Duk
kaina nake tambaya, kuma babu mai amsa min
28
Baki Biyu Sameera
su sai na tambaya amma sai na yi gum da bakina.
ina sauraren nasihar su. Baki dayan su suke
magana kai yanzu ma lallashi aka koma daga
haka kuma Haj. Maryam ta rika zaya ne min irin
kuncin rayuwar da ta shiga, gashi kuma a yau ya
wuce ya zama labari, Baba shima na shi ya dan
fada har a karshe ya ce. Dayyiba don girman
Allah kiyi hakuri ki rike auren ki ba don hali na
ba don Allah na ce, tausayin mahaifina ya kama
ni, haushin kaina na fara ji da gaske ne dai
abinda suke cewa ni ce zakka a cikin 'ya'yansu.
na shiga uku, astagfirullah na fara ambato a cikin
zuciyata tare da neman gafarar su. Baki dayansu,
abin dadi na shine duk sun yafe min, na kuma
dauki alkawarin zaman aure.
Wunin ranar Sallah nake ta yi ina neman
gafarar Allah, ina neman sassauci daga gare shi.
Tun daga ranar ban fasa ba, kwanansu Babah
biyu har sai da ta leka gidan Haj. Maryam abun
gwanin sha'awa, sun kulla kawance na aminci
tsakaninsu.
Na sami kusan sati biyu a gida ni ban ga
mijin ba, ba kuma ban damu in san shi din ba, ni
dai na daukar wa kaina alkawarin yin biyayya ga
Iyayena da kuma yiwa mijin biyayya. Gwaggo
ce ta tsinka min tunani ta ce, sai ki shirya gobe
zaki wuce dubai gun mijinki, gaba na ne ya fadi
ban ma san yadda aka yi na kasa amsa wa
Bak Biyu Sameera Mustapha:
Gwaggo ba sai da na ji ta ce, ba da ke nake ba ko
ba ki ji ba, da sauri na ce na ji Gwaggo sai Allah
ya kai mu goben.
Ban tashi shiri ba sai da daddare, akwati daya
tal na shirya sai kit da hand bag din da na rike.
Washegari da karfe biyar muka wuce Abuja
da yake ta can zamu tashi, ni an bar ni a duhu, ko
a dan yi min bayanin waye shi, na lura mutumin
zai yi girman kai, ace sati biyu da aure bai taba
nemana ba balle ma in ce na taba jin muryarsa,
da alama ikonsa zai yi yawa. Ni dai ina neman
tsari da sharrin wannan aure.
Sai karfe sha biyu na dare muka yi boarder a
Egypt Air, karfe sha biyu da minti ashirin muka
tashi.
**
WANENE KUMA MAS'UD?
Mas'ud Mohammad Shinkafi, wanda aka fi
sani da Amir, sanadin an rada masa sunan
mahaifin Haj. Basira shi yasa tayi masa lakani da
Amir. Shi dai Mas'ud ya tashi yaro ne da baya
jin magana da ya zama samari kuwa tantiri ya
zama saboda da ya gama secondary sch. Ma da
daurewar gindin mahaifiyarsa aka tura shi
America.
Haj. Basira tana bala'in ji da shi, kun san ana
20
Baki Biyu Sameera Mustapha:
cewa tangararen yaro ko mutum ya fi shiga rai,
don haka Haj. Basira bata taba yarda da duk
wani abu na rashin ji da ake cewa yana da shi da
ya ke duk a cikin 'ya'yanta sun fi shakuwa. An
sha kawo kararsa gun ta na irin ta'asa da yake
aikatawa, ga yaran gari sai ta auna shi da sharri
ne aka kulla masa.
Mahaifinsa kuwa ba su taba shiri ba saboda
hali irin nasa, wani lokacin ma sai ya kwana uku
ba a gida ba, akwai sanda ma aka taba daure shi
saboda yawon dare da shi da abokansa, a cewar
su party suka fito. Tafiyarsa America kuwa a nan
ya hadu da Sa'idu Balarabe, shima din ba
karami ba ne gun rashin ji. Dalilin korar su kuma
da aka yi daga America shine sai da kwaya da wiwi da suka sa kansu, sai da suka sami sati biyu
a prison sannan aka sa su jirgi aka dawo da su gida Nigeria. Mahaifin Mas'ud ransa ya 6aci sosai, saboda yadda ya maida kansa, hatta askin kansa dabanne, kan ya cika da gashi anyi kitso
wani wurin kuwa an aske shi ga shan wiwi, shi saukin sa baya shan kwaya, don Alh. Muhammad sai da ya kai shi sicartrac aka kwada
shi tas. Babu abinda yake sha sai wiwi sai dai inda abun yake da sauki ba wai ya cika sha ba
ne, amma akwai shan sigari sosai a tare dashi. Daga karshe dai dole ya maida shi (A.B.U Zaria), nan ma shiriritar suka sa a gaba, don a
31
Bakı Biyu Θ Sameera Mustapha:
nan suka Kara haduwa da Sa'idu aka ci gaba da
shakiyanci.
Ta bangaren mata kuwa, sai dai su bi Mas'ud
don bai damu da su ba, har abokansa suka fara
zargin ko shi dan ludu ne, abin kuwa ba haka ba
ne, shi ne dai baya ra'ayin mace a wannan
lokacin. Business admin yake karantawa,
maimakon ya gama a shekara hudu a'a sai da ya
shekara bakwai sannan ya gama, kai shiririta irin
ta Mas'ud sai addu'a.
A
lokacin da zai gama ne ya soma son
Dayyiba, ba don komai ba sai don idaniyarta, ya
rasa abun da yasa yake son idanuwan Dayiba,
suna yi masa kama da na 'yan Chainise, abu
kamar wasa sonta ya yi masa yawa a ransa, sai
dai bai iya fada mata ba saboda a lokacin 'yar
Karamar yarinya ce dole ma ya daina tunanin ya
fada mata don yasan 6ata lokacinsa yake yi,
mahaifiyarsa yake tsoro bata taba son jin koda
sunan mahaifin Dayyiba so da yawa idan ta
zauna tana yi masa zancen su sai ya rasa laifin
su. Ya kan biye mata ne don ya lura babu mai
mara mata baya a 'ya'yanta sai shi, amma idan ta
tura shi yi masu wani abu bai taba gwada yi ba.
Ana cikin haka ne ya fara zuwa Kaduna yana
buga polo ball, wasan nan ta hawa doki ana buga
kwallo da sanda. Ga shi dama a nan Sa'idu yake,
don haka bai da matsalar gun zama, ya kan dauki
32
Baki Biyu Sam
lokaci mai tsawo a Kaduna wurin wasa a
cewarsa lesson yake dauka, mahaifinsa kuwa ba
yadda ya iya da shi, addu'a kawai yake masa,
Allah ya shirya shi. Mas'ud bai taba damuwa da
arzikin da yaba yayinsa, Idris shine mai kula da
duk wani dawainiyar mahaifinsu, anan Zamfara
zuwa Sokoto sai Tahir da shi kuma dama Allah
ya yi maşa goshin arziki.
Tunda kuma yake bai taba rokonsu abun
hannunsu ba, duk da ba wai suna nuna masa
halin komai ba ne shi dai ne halinsa yake haka.
Abin su bai taba tsone masa ido ba, so da yawa
mahaifinsu na yi masa kwatanci da su amma sai
ya yi murmushi ya ce, Baba ai kowa da irin
arzikinsa, nima zan samu ne idan nima ina da
rabo, ya kan kira shi mara zuciya sai dai bai taba
damunsa ba, shi dai ya fi son rayuwa mai sauki.
A nan Kaduna ne aka fara tura shi Dubai, da
yake suma suna son duk wani wasa da ya
kasance da Doki ake yin sa. Da ya dawo hutun
sati ne, ya samu Dayyiba na S.S.1 ta girma,
kyanta ya karu, yana yi mata son zuciya daya ne,
da ya furta mata kuma ta burge shi tayi saurin
amince masa, duk da akwai rashin wayewa a tare
da ita, amma tayi masa daidai sun fara soyayya a
boye shi babu abinda ke damunsa idan
mahaifiyarsa Haj. Basira ta gano akwai soyayya tsakaninsa da Dayyiba, sai kuma gashi a daidai
33
Bakı Biyu Sameera Mustapha:
lokacin suka sami matsala da ita, ya lura tana da
rashin kunya, ya kuma aikata abinda bai taba
tunanin aikata shi a rayuwarsa ba, da ya daga
hannu zai duki Mal. Sabi'u, tabbas yasan yana
da rashin kunya da tsokana da shiga abinda bai
shafe shi ba, sai dai a gaskiya tsakaninsa da
sa'an sa yake wannan baya yi da manya, amma a
lokacin da yake bacin zuciya da rufewar ido
gashi dama sai da ya sha wiwi sannan hakan ta
faru, sai da ya aikata wannan abu ne da
hankalinsa ya dawo jikinsa ya yi bakin cikin
abinda ya aikata, har ta kai Haj. Basira ta kore su
sanadin sa, sam wannan abu bai burge shi ba a
ranar ma bai kwana a gidan ba, wiwi kuwa ya
sha ta har ta tashi halaka shi.
Washegari don hankalinsa ya dawo jikinsa ya
koma gida, kai tsaye sashen Mal. Sabi'u ya wuce
amma sai yaga sun tashi, gun Haj. Basira ya
wuce yana yi mata tambaya, Mama ina su Mal.
Sabi'u? ta saki fuskarta ta ce, meye ruwanka da
su, da zaka zo kana min zancen su, ko sallama ba
ka yi ba balle gaisuwa, ya sami guri ya zauna ya
ce, Mama kina nufin kin kore su? Ta washe baki
tana dariya, ai kayi min daidai yaro na kasan tun
yaushe nake son su bar gidannan, gashi yanzu a
sanadin rashin mutuncin da ka yi masu sun bar
יי
gidan a saukake, yaro ka biya Mamanka..."
mikewar da ya yi tasa ta bar maganar da take yi,
34
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ransa ya yi baki ya rasa abinda ke yi masa dadi,
kai! Ta fada a tsorace, me ke damunka ne wai?
Idanunsa jajir kamar gauta ya kai hannunsa biyu
kansa ya koma ya zauna. Shin me ke damunka
ne ina tambayarka dan Mama, (haka take kiransa
wata rana saboda irin shakuwar da ke tsakaninsu
har dai idan ya dadada mata rai). Huci yake yi
kamar zaki, nan da nan ta shiga taitayinta batą
taba ganinshi cikin yanayi irin wannan ba, ta
matsa dab dashi ta ce, shin kana da lafiya kuwa?
Ta kai hannunta kan goshinsa, babu alamun zafi
sai zufa. Shiru tayi tana karantar halin da yake
ciki, Mama ya fada ta dube shi, ina shan wiwi ta
zaro ido, ban gane ba ta fada muryarta na rawa,
kana shan wiwi haba dan Mama yaushe ka
fara?"
Yana girgiza kansa ban sani ba I can tell na
dade ina sha Mama, ya riko hannayenta duka
biyun Mama ina son in bari ya ya zan yi?
Tausayinsa ya kama ta, itama ta rike shi kam ta
ce, kayi niyya dan Mama a zuciyarka za ka daina
da yardar Allah, Mama saboda ita na aikata
wannan mugun abu ga Mal. Sabi'u, ba da son
raina ba, mikewa tayi tana harararsa, ai dama
kana da na sanin abinda kayi wa Mal. Sabi'u ne?
idan