Basira da ba zata matsa min
ba, shi ya tsinka min tunanina da naji ya riko
hannuna da ke kan fuskata ya ce, come on
Smiley, kukan ya isa haka, kina wahalar da
kanki da yawa, sam mutum in nan bai da kunya,
kunya dai bai santa ba, a gaban Gwaggo fa yake
min haka, babu yadda zanyi ni kuma in hana shi
abunda yake yi, don kada Gwaggo ta kara jin
haushina, karshe ma rungumo ni ya yi yana
lallashina kamar wata 'yar shekaru biyar, shafa
bayana yake yi, ai ke ki ka ja me ya kai ki
tunanin zubar da ciki?
Gwaggo ta kama hanyar daki tana cewa, zan
shiga ciki Mas'ud, Allah ya tsare, sai mun yi
yawa." Ba ta jira jin abinda zai ce ba, tayi
shigowarta daki, tana shigewa yana lalubo
bakina ya soma aikin nasa, ban ga alamun yana
son bari ba gashi idan yana kissing dina sai ya
rika kara, a hankali na cije shi a harshe, da sauri
ya dube ni cikin ido ya ce, lafiya? Idonsa sun yi
jajir na marairaice a shagwabe na ce, amai zan
yi, ki yi mana ya fada yana son ci gaba, na dan
janye kaina, nan fa gidan Gwaggo ne don Allah
kayi hakuri, zo muje sashen..." ban bari ya
karasa ba na maida bakina cikin nasa na riga na
san in dai ba minti goma zuwa sha biyar ya samu
87
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
ba ba zai kyale ni ba, ai kuwa sai da ya cika
adadin lokacin sannan ya rabu dani, ashe baby
kin fara sanin halina, that is good, zo muje gun
mota ki karbo ma Gwaggo tsaraba."Mun isa gun
motar yana rike da hannuna, ya ce da direba ya
bude but, ni in rasa direba nawa ne da Mas'ud
kullum sabuwar fuska zaka gani, kwalayen
drinks ne da su kayan shayi na lura babyna na
ciki drinks yake so ko? Ya yi tambayar yana kai
hannunsa kan cikina, shi wai ba san nan ba irin
Turai ba ne da ake baiyana sirrin ma'aurata?
Gashi da nacin tsiya idan ya yi niyar yin abu sai
ya yi shi kila idan bai yi ba mutuwa zai yi.
Agogon hannunsa ya duba ya ce, it's time,
zan wuce ki kula da kanki, ban san me ya kai ni
ce masa ba za ka bari sai da safe ba? Murmushi
ya saki, dole ne in tafi saboda gobe da karfe
takwas na safen London ina da meeting kafin
lokacin nake so in isa, Jirgin mu zai tashi da
karfe dayan dare na yau, yanzu Abuja zan wuce
insha Allahu."
Ajiyar zuciya nayi na ce, "To Allah ya kai ka
lafiya." Rungume ni ya yi, na gode da addu'arki,
a zahiri kamar mutumin kwarai a badini kuwa
Allah kadai ya sani, sai da ya wuce sannan na
shiga cikin gida, tsoron hada ido nake yi da
Gwaggo, don nasan fushi take yi da ni. Tana
kwance a kan gado da alama ta fara bacci, na
88
Baki Biyu Sameera Mustapha:
kashe wuta nima na hau gado har zan kwanta, na
tuna ban yi sallah ba, saukowa nayi na shiga
toilet nayi alwala na fito nayi sallah.
Washegari na lura Gwaggo fa fushi take yi
dani sosai, bata dauki abun da sauki ba, don
haka na rika shisshige mata, sai dai ta ki sakin
jiki dani. Na kira su Amina na sanar dasu na
dawo, ihu sukai tayi suka ce suna nan zuwa.
Kamar hadin baki, tare suka shigo gidan cike
da murna, muka rungume juna, kowace da
'ya'yanta, muka shige daki bayan sun gaisa da
Gwaggo mun shiga Aisha ta ce, Amina gaskiya
ki ka fada, Dayyiba ta zama 'yar can, na harari
Amina, me ki ka ce na yi kuma?" Ta yi fara'a ta
ce, mene ma ban fada ba, Aisha fada mata mana
ke ba komai ta ce ba illa irin sha'awar zaman da
ku ke yi da maigidan naki, na ja tsaki, ni na zata
wani abun ne ma, kin ga yadda ki ka zama kuwa
'yar uwa? Kin yi kyau kamar an canza miki
halitta. Kai Aisha bana son sharri, wallahi ba
karya na fada ba, Amina ta ce anya wannan
kyaun da naga an kara babu bayani? Zan yi
magana Asabe ta shigo da kayan ciye-ciye ta
ajiye suka yi mata sannu, ita kuma ta gaida su ta
fita, ai Aisha na bude kular abinci da yake jallof
ce amai ya taso min, da gudu-gudu na isa bayi na
amaye da juice din da ke cikina. Sai da suka
taimaka min, irin kallon da suke min yasa na
89
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
fashe da kuka. Ikon Allah suka fada baki me
akai maki kuma? Na zauna can nesa da abincin
ina share kwalla, Amina guda ta saki tana
Kyalkyalewa da wata irin dariya na keta, Allah
ya kama ki yarinya, Aisha ta ce ciki ne da ke
Dayyiba? Kema sai kin tambaya in ga idon
wadda ta ce ita ko aure tayi sai ta shekara sannan
zata yi ciki, dole na saki murmushi na tuna
lokacin da na fadi hakan, Aisha ta yi dariya ta
ce, kai na fa tuna haka ki ka ce, to ya aka yi ne?
na galla mata harara na ce, ba zan fada ba, 'yan
gulma kawai." Nan fa sukai ta tsokanata, share
su nayi ban ce komai ba, don ban da bakin
magana, tare muka wuni har sai bayan La'asar
sannan suka fito za su wuce, yaran su sai wasa
suke a tsakar gida, Gwaggo ta ce, mun gode da
zumunci da bata nan ma kuna lekowa, Allah ya
yi maku albarka, bayan sun wuce na shigo ciki
na zauna dab da Gwaggo na ce, kai Gwaggo
Allah ba zan kara ba, wauta ce ke damuna, Allah
Sarki, wadda aka haifa yau. Ai ban san haka ba,
je dai ki halaka kanki da rashin wayau, ke
dinnan ke ki ka dauki halin 'yan fari don Nafisa
kam ba haka take ba, duk a gidan ku ke ce mai
hali haka, ni dai addu'a zan taya ki dashi, Allah
ya shirye ki. Tun daga lokacin kuma ta sauka,
waya ce ta yi ringing, Gwaggo ta dauka, ta ce,
a'a Mas'udu, sannu Mas'udu, ya hanya? An isa
90
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
lafiya?" Da alama ansawa yake yi, ta yi shiru
tana saurarensa, can naga ta dube ni, ta ce ban
sani ba nima kila wayar bata yi ne, ai kana kira
ka ce? Gabana ne ya fara faduwa, tabbas naga
kiransa amma mirsisi na ki dauka, ta kara
dubana tare da miko min wayar na ansa na sa.a
kunnena muryata ciki-ciki na ce, "Hello!" Ya
amsa "Kina lafiya?" "Lafiya lau." Na amsa a
takaice, hala har yanzu jikinne? A'a yanzu babu
abunda ke damunki? Ya tambaya Eh, na fada ya
yi shiru ban san abinda ya yi tunani ba, sai kuma
ya ce, to sai da safe. Na ce to na kashe, Gwaggo
dai na ji na amma bata ce komai ba.
Tun da na dawo Kaduna ba inda nake zuwa,
ko nan da gidan Anti Badiya Gwaggo ta hana,
sai da nayi kwana hudu tukun ta ce muje tare ko
awa daya ba mu yi ba muka koma gida, ina ga
tun ranar ban kara fita ba, Mas'ud kuwa a
kullum sai ya neme ni a waya sau uku a rana
wani lokacin da gangan sai in ki dauka. Haka dai
rayuwar ta rinka tafiya sama-sama muke dashi,
sai da ya sami wata daya da sati daya sannan ya
zo.
Ina zaune a tsakar gadon dakin da nake duk
da ba a dakin nake kwana ba amma kayana na
dakin, dakin Gwaggo nake zuwa in yi
kwanciyata, jin an taa kofar yasa na kalli kofar
in ga mai shigowa. Mas'ud ne ya shigo fuskarsa
91
Ο0
Baki Biyu Sameera Mustapha:
cike da fara'a, kasa motsi nayi daga inda nake,
naga ya kara kyau sosai yana sanye ne da
Kananan kaya a jikinasa, sky blue jeans ne da Тshirt fara tas an yi zane da kalar blue da ja, tayi
masa kyau sosai, matsowar da ya yi ya zauna
dab da inda nake zaune yasa na dube shi ya ce
"Ya ya dai baby?" Ya yi tambayar yana neman
taba ni, ba yadda zan yi in hana shi, na rasa
dalilin da yasa in dai Mas'ud ya matso jikina, sai
jikina ya yi sanyi, duk da kin sa da nake yi a
zahiri. Tabbas Mas'ud namiji ne cikakke da zai
iya sace zuciyar mace cikin kankanin lokaci,
bakinsa da yake kokarin sawa a nawa yasa na
dawo daga duniyar tunanin da na shiga, kai
mutumin nan akwai iya salo, ga iya wasanni na
ma'aurata shi yasa bana shakkun in dan na
sassautawa raina muyi zaman aure tsakanina
dashi, zan ji dadin rayuwata.
Haj. Basira ce ta fado min a raina, kuma tuno
zancen da suka yi a kaina da Gwaggo da karfin
gaske na janye kaina, me ya faru? Ya yi
tambayar ta cikin makoshinsa, don ya riga da ya
yi nisa, mikewa nayi niyar yi amma na kasa,
saboda rike ni da ya yi, me ki ke nufi ina za ki?
Ban yi magana ba amma ina kokarin kwace
kaina daga gare shi, babyna nake son in taba, ya
fada tare da mikewa tsaye. Haushi ya bani da har
kwalla ya cika tab a fuskata, ya saki hannuna ya
92
Baki Biyu 3 Sameera Mustapha:
ce wai Dayyiba ya ki ke son in yi ne? Am trying, kin sani kullum kuma ina fada maki how much I
love you, ya ki ke so ne? ka rabu da ni, ka sake ni shine abinda nake so. idanunsa a lokacin sukai jajir ya tsaya yana kallona, da alama ya ma rasa abinda zai ce, wannan kalma da ki ka fada saki ba zai taba faruwa ba, don haka na ke baki shawarar ki ma daina wannan tunanin..." ni kuma ba hakan zai sa in so ka ba, fuskata ya tallabo da hannayensa biyu masu taushin gaske
ya ce, Dayyiba me zan yi maki ki so ne? wallahi ke kadai nake so a rayuwata, me nayi maki da ba
za ki iya yafe min ba? Duk abinda ki ke so Dayyiba ki fada min, I promise, I will do it for you, I love you."
Ni kaina nasan hakan, to amma me yasa yake yi min baki biyu ne, idan ina tare dashi sai ya
nuna nice abun sonsa, idan yana gun Haj. Basira kuwa sai ya nuna mata ita ce majibincin shi, baki biyun shi ke kashe ni yake hana ni sakewa da shi, ya tsinka min tunanina da ya soma kissing dina ta ko ina a fuskata, har ya koma kan bakina, dole na kyale shi har ya samu natsuwa.
Kwankwasa kofar dakin yasa ya sassauta bai iya amsawa ba, ni ce naje gun kofar na bude, Asabe ce ta ce "Sa'idu ne ya zo yana falo." Na
amsa to, jikinsa a sanyaye ya iso gun kofar ya се bari in je in ganshi, ya fice ban san lokacin da
93
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha
wani irin tausayinsa ya kama ni ba, ban san
dalilin da yasa nake tausaya masa ba duk lokacin
da nasan baya cikin farin ciki. Na tuno irin son
da nake yi masa da sai dai wani lokacin idona na
tuna irin zaman da muka yi a Dubai, ina jin dadi
a raina to kodai har yanzu ina sonsa ne? a
sanyaye na dauki abaya na fita da nufin in gaida
Sa'idu.
Kwana uku ya yi ya koma London, ya ce min
wani business ne ya samu a can da 'yan shelf
suma mai ne sana'ar su, bai takura min ba sai dai
wasanni da ya kasance tsakaninmu sosai.
Cikina na da wata biyar, duk wani ciwo na
rabu dashi, ji na nake tamkar ba mai juna biyu
ba, gashi har ya fito ga cin tsiya komai ci nake
yi, a wuni sai in yi ci shidda ba abin mamaki ba
ne. shi yasa nayi kiba sosai, muna kuma dasawa
da Mas'ud tun ina kin sakewa dashi har takai ma
na fara nemansa a waya, mu yi hira. Idan ya yi
tafiya yakan dauki lokaci bai zo ba, idan ma
zuwan ya yi bai wuce kwana uku zuwa biyar ya
koma, idan kuwa ya yi sati to Gusau ya je. Kirikiri Gwaggo ta hana ni zuwa Gusau, ba ma
Gusau ba ko nan cikin Kaduna ba ta bari in je
ko'ina, don haka kullum ina gida in dai ba awo
za ni asibiti ba.
Haka rayuwa tai ta tafiya har ciki ya kai wata
94
Baki Biyu Sameera Mustapha:
tara, da nakuda ta tashi kuwa cikin dare wajajen
karfe goma sha biyu saura, dole muka shirya
zuwa asibiti. Muna isa da minti talatin da shidda
na haihu, wai na ji abunda mata ke ji, Allah ya
raya mana 'ya'yanmu, yasa musu albarka, amin.
An sami da namiji fari sol da shi.
Washegari tun safe aka sallame ni don
Alhamdulillahi da ni da baby lafiya lau, Gwaggo
kuwa murna kamar zata yi me, dakin da nake
aka maida dakin jegon, nan da nan Gwaggo ta
rika kira tana sanar da mutane abin alherin da ya
faru. Nan da nan 'yan barka aka fara tururuwa
shi kuwa gogan nawa karfe goma na dare ya iso
Abuja, ya bari sai da safe amma ya ki ya biyo
dare ya iso sha biyu na daren, lokacin ina bacci
ga baby gefe na, shima baccin yake yi. Kai na da
na ji ana shafa min yasa na bude idona a hankali,
sun yi jajir saboda bacci nake yi mai nauyi,
ganinsa gabana yasa na saki fuska ta, ya mike ya
zaga daya gefen ya dauki babin yana yi masa
addu'a tare da sumbatarsa, kallon su kawai nake
yi saboda sha'awar da suka bani, fuskar Mas'ud
cike take da murna sosai, a lokacin wani irin
sonsa ya murdo ni, har sai da na ji nauyi da
muka hada ido da shi, na san ya gano hakan shi
ne dalilin zuwa inda nake, rike da jaririn a
hannunsa ya riko hannuna yana murzawa, ya ce
cike da kulawa, ya jikin ki? Murmushi na saki na
95
Baki Biyu
Sameera Mustapha:
ce da sauki, sai dai na rasa dalili nauyinsa nake
ji, ban san wannan abu ba. Mun dan jima yana
nuna min farin cikinsa ya ce, na riga na zabar
masa suna, Tahir za a sa masa, hawaye ne ya
ciko idona, na ce, hakan ya yi daidai, Allah yasa
mahaddacin Alkur'ani ne, wanda kuma zai
amfane shi duniya da lahira.
Kwanana uku da haihuwa gida ya kara cika
da mutanen Gusau, kun san Gwaggo da jama'a,
Mas'ud kuwa set na akwati ya yi min har seti
biyu, sha biyu kenan baby kuwa set daya, abun
dai sai wanda ya gani, zinari kuwa sai da ya saka
set hudu har da daimond. Da na yi masa magana
sai cewa ya yi ai ban yi maki lefe ba, ni sam na
ma manta da lefen.
Ranar suna an cika sosai, yaro dai ya ci suna
Tahir. Haj. Basira ko kira bata yi ba balle ta zo
suna, ban ma sarai ba. Wajajen karfe hudun
yamma aka fara lunchen, abin mamaki sai ga Suwaiba, mun rungume junanmu don murna, har
tana ce min bana da kirki, na bata hakuri muka
yi canjen number waya.
Suna kam ya yi armashi sosai, don sai bayan
Isha'i aka watse, sai 'yan Gusau ne sukai saura,
suma washe gari kowa ya kama gabansa.
Mas'ud ya sami kwana uku bayan suna, ya
fara shirin tafiya a cewarsa tare zamu tafi, ya
sami Gwaggo yana zayyane mata irin tsarin da
96
Baki Biyu Sameera Mustapha:
tara, da nakuda ta tashi kuwa cikin dare wajajen
karfe goma sha biyu saura, dole muka shirya
zuwa asibiti. Muna isa da minti talatin da shidda
na haihu, wai na ji abunda mata ke ji, Allah ya
raya mana 'ya'yanmu, yasa musu albarka, amin.
An sami da namiji fari sol da shi.
Washegari tun safe aka sallame ni don
Alhamdulillahi da ni da baby lafiya lau, Gwaggo
kuwa murna kamar zata yi me, dakin da nake
aka maida dakin jegon, nan da nan Gwaggo ta
rika kira tana sanar da mutane abin alherin da ya
faru. Nan da nan 'yan barka aka fara tururuwa
shi kuwa gogan nawa karfe goma na dare ya iso
Abuja, ya bari sai da safe amma ya ki ya biyo
dare ya iso sha biyu na daren, lokacin ina bacci
ga baby gefe na, shima baccin yake yi. Kai na da
na ji ana shafa min yasa na bude idona a hankali,
sun yi jajir saboda bacci nake yi mai nauyi,
ganinsa gabana yasa na saki fuska ta, ya mike ya
zaga daya gefen ya dauki babin yana yi masa
addu'a tare da sumbatarsa, kallon su kawai nake
yi saboda sha'awar da suka bani, fuskar Mas'ud
cike take da murna sosai, a lokacin wani irin
sonsa ya murdo ni, har sai da na ji nauyi da
muka hada ido da shi, na san ya gano hakan shi
ne dalilin zuwa inda nake, rike da jaririn a
hannunsa ya riko hannuna yana murzawa, ya ce
cike da kulawa, ya jikin ki? Murmushi na saki na
95
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ce da sauki, sai dai na rasa dalili nauyinsa nake
ji, ban san wannan abu ba. Mun dan jima yana
nuna min farin cikinsa ya ce, na riga na zabar.
masa suna, Tahir za a sa masa, hawaye ne ya
ciko idona, na ce, hakan ya yi daidai, Allah yasa
mahaddacin Alkur'ani ne, wanda kuma zai
amfane shi duniya da lahira.
Kwanana uku da haihuwa gida ya kara cika
da mutanen Gusau, kun san Gwaggo da jama'a,
Mas'ud kuwa set na akwati ya yi min har seti
biyu, sha biyu kenan baby kuwa set daya, abun
dai sai wanda ya gani, zinari kuwa sai da ya saka
set hudu har da daimond. Da na yi masa magana
sai cewa ya yi ai ban yi maki lefe ba, ni sam na
ma manta da lefen.
Ranar suna an cika sosai, yaro dai ya ci suna
Tahir. Haj. Basira ko kira bata yi ba balle ta zo
suna, ban ma sarai ba. Wajajen karfe hudun
yamma aka fara lunchen, abin mamaki sai ga
Suwaiba, mun rungume junanmu don murna, har
tana ce min bana da kirki, na bata hakuri muka
yi canjen number waya.
Suna kam ya yi armashi sosai, don sai bayan
Isha'i aka watse, sai 'yan Gusau ne sukai saura,
suma washe gari kowa ya kama gabansa.
Mas'ud ya sami kwana uku bayan suna, ya
fara shirin tafiya a cewarsa tare zamu tafi, ya
sami Gwaggo yana zayyane mata irin tsarin da
96
Baki Biyu Sameera Mustapha:
シ
ya yi ta ce, sam ba za ayi haka ba, sai dai koda
sati hudu ne in samu a gurinta, rai bace ya bar
garin ko sallama ba mu yi ba, har sai da ya isa
Thailand ya bugo min, kullum muna waya
shakuwa kuma na karuwa tsakaninmu.
Cikin sati uku da haihuwa mun yi bul-6ul da
ni da jariri mun yi kyau sosai, muna shan tattali
gun Gwaggo, mun shiga sati na biyar ne Mas'ud
ya zo Kaduna, ya tadda ba ma nan mun je asibiti
don murna da ta kama ni, har da zazzabi na rika
ji, sai karfe biyu saura muka dawo na wuce daki
na yi sallah. Tahir na gun Gwaggo, wajajen hudu
da minti goma Mas'ud ya shigo gidan. Muna
zaune falo, muna hira da Gwaggo ya shigo ido
ya kura min direct kuma guna ya nufo, ya zauna
daf da ni, Gwaggo da ta ma rasa abinda zata ce,
sai cewa ta yi a'a Mas'udu ashe kana gari? Ya
amsa Eh, ina nan yau dinnan na shigo. Asabe ta
ce, kun je asibiti lafiya waye bai jin dadi? Та се,
gata nan mun ce tayi mata kamun karfi, ayya ya
nuna tausayawarsa gare ni, tare da kai hannunsa
kan goshina, ni dai nauyin Gwaggo yasa komai
ma na kasa yi sannu ya fada a raunane, ina Tahir
yake ne? Da sauri na mike, ya riko hannuna ina
za ki? Kokarin fisge hannuna nake yi, ina kallon
inda Gwaggo take, shi kuwa ko a jikinsa, a
lokacin Asabe ta shigo falon rike da Tahir, ya
saki hannuna ya je ya amshe shi yana washe
97
Sameera Mustapha:
baki, inda Gwaggo take zaune nan naje na zauna,
bai nuna min ya damu da hakan ba, Tahir har ya
yi bacci na amshe shi na kwantar dashi a daki
ina jin su suna ta hira da Gwaggo naji dadi da
bai biyo ni ba.
Bayan mun yi sallah Isha'i ne Gwaggo ta ce,
na ga rawar kan mijin nan naki ya yi yawa, don
haka ki yi kokarin kame kanki, don ba ki mayi
arba'in ba...." Sallamar sa tasa ta daina maganar,
mikewa nayi ina gaida shi naje na shirya masa
abinci na wuce dakina, kula hira suka yi har
Gwaggo ta gaji ta ce da shi zata kulle kofa, to da
alama ya gano ta sai dai bai musa ba ya fita.
Washegari haka nayi ta doje masa don na lura
sosai Gwaggo ta sa mun ido, don haka ranar ma
ba mu wani hadu sosai ba, sai lokacin da ya
shigo muna sallah isha'i, na gaida na kawo masa
abinci, kwanansa biyu kenan yau, ya ce jibi zai
wuce bai ma yi maganar komawa ta ba, wannan
lokacin.
Da karfe sha daya saura na safe ina zaune
gaban mirrow ina shafa mai, don a lokacin nayi
wanka sai ganinsa nayi kamar wanda aka jeho,
duk da na tsargu da irin kallon da yake min sai
na dake na ci gaba da abinda nake yi, karasowa
ya yi ya sance ribon din da na daure gashina da
shi, da yake a kwance gashina yake sai ya zubo
ya yi kwance a bayana, na kasa magana don
98
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
wani irin abu da na ji a jikina. Mikewa nayi
gabana ya fara faduwa, nayi niyar barin wurin
amma na kasa, ya ce kin san fa tunda na zo ba
mu gaisa ba, mun gaisa mana, a ina? Ya
tambaya, a takaice tare da riko hannuna, jikina
tuni ya fara rawa, ni kaina abin na bani mamaki,
to ko don yadda Gwaggo ke gaya min in nisance
shi necoho! Tsoro na ake ji ne kuma Dayyiba?
Na girgiza kaina, a'a ko ba kiyi missing dina ba?
Na yi na fada da sauri, to shi ne ki ke guduna?
Yana magana ya rungume ni yana shafa ta, ina
son kamshin jikinki baby, cikin dubara ya kai
bakinsa kan nawa, haba tuni na manta duniyar da
nake ciki, sam ban taba sanin nayi missing dinsa
ba.
A takaice dai ban san lokacin da na bashi
hadin kai 100% ba, muka more junanmu. Mun
murji juna kamar ba zamu bari ba, sai dai da
muka natsu na fara share kwalla, ya rungume ni,
lafiya? Ya tambaye ni, Gwaggo ta ce kada in
yadda in baka hadin kai, saboda me? Nima ban
sani ba, to ke kin san dai ba wani abu ba ne kо?
Ya fada yana kara bina da wasanninsa masu
tsada. Ba mu gaji da junanmu ba, muka rabu don
kiran Sallah azahar da aka yi, sai da na fito na
tuna da Tahir, tuni na isa gun Asabe na dubo shi
yana nan yana bacci, Gwaggo kuwa dama bata
nan gidan Umma taje, mahaifiyar Sa'idu, dama
Baki Biyu Sameera Mustapha:
sukan yi wa junansu ziyara, Mas'ud kuwa bai
wuce kwana hudun ba ya wuce.
Kewarsa nake yi sosai, na tsińci kaina da so
da Kaunar Mas'ud a raina, har ina manta zargin
da nake masa, waya akai-akai muke yi yanzu, ga
shakuwa a hankali ya soma shigar mu. Bayan
sati biyar da tafiyarsa, ya gaya min zai je India
daga nan zai wuce Chaina, akwai business din da
yake son ya samu, na shigo da barkono zuwa
Kasar London da yake su dama barkono ba nasu
bane, basu da shi, na ce dashi zan taya ka addu'a.
A wannan lokacin ne Tahir ya soma rashin
lafiya, zawo yake yi babu sassauci, wuni daya tal
yaro ya zube sai hanci da ya rage masa duk
hankalina ya tashi na rasa abinda ke min dadi,
muna asibiti gun Likita yana duba shi, na lura
Gwaggo tafi ni damuwa, Doctor ya ce, yana son
ya duba ruwan nonona, ban jira komai ba na
bada aka shiga laboratory, don a duba.
Mun samu kusan awa daya sai da aka sa
mashi ruwa a gaskiya yana jin jiki sosai. Da
Doctor ya shigo ya tambaye ni, Madam kinga
period din ki kuwa tunda ki ka haihu? Gabana ne
ke faduwa, saboda tsabar fargaban da ke tare
dani, ban iya amsawa ba sai girgiza kai da na yi,
yaushe ki ka gani? Ya tambaye ni, na kuma cewa
a'ah ban gani ba, ya yi dan rubutu ya ce, ki zo
office ina so muyi scanning mu gani da alama
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
ciki ne da ke, na zaro ido na wanda tuni ya ciko
da kwalla, bin Doctor nayi, ai kuwa haka din ne,
ciki ne ya tabbata don har ma yana cikin sati na
hudu, oh ni na shiga uku da wane ido zan kalli
Gwaggo?
Doctor kuwa sai da ya yi mata bayani ya
kuma ba da shawarar in za abar cikin to a ci gaba
da ba Tahir nono saboda ruwan nono na yana da
kyau, idan ya bi jikinsa zai warware. Kunyar
Gwaggo nake ji don haka na ki sakin jikina.
Itama bata ce min komai ba, dole na ajiye kunya
gefe guda na zo har inda take zaune na ce, murya
ta a sarkake, "Allah ba laifina ba ne." ta dube ni
fuskarta a sake, ai laifin nawa ne ko? A'a
Gwaggo wallahi shi ne ya bi ya dame ni, ki
tambaye shi, in ce masa me don me ya neme ki?
To ai ga abinda nake gudu nan ya auku, Allah ya
baku lafiya daga ke har dan naki.
Gwaggo ai Doctor ya ce, za'a iya cirewa,
harara ta dalla min ni wannan ba da bakina ba,
sai ki fada ma uban rashin kunyar abinda ya
faru, idan ya bada bakin ayi sai ayi, amma ni
kam ba da miyaun bakina ba.
Haka aka yi, kwananmu hudu a asibiti, Tahir
ya dan ji sauki, Gwaggo ta nemi a sallame mu
tun da kashinsa ya dan yi daidai, muna komawa
gida muka shirya kasuwa zamu a hada masa
maganin hausa (gargajiya kenan), an ko hadu
101
Baki Biyu Sameera Mustapha:
masa don babu wanda ba a bashi ba, har da na
shafawa aka hado masa. Tuni renon Tahir ya
koma gun Gwaggo, nima an hada min na sha,
duk da bana son maganin haka na