An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
BAKI NIYU HNL
3
by samira mustapha
HAUSABООK.СOM
BAKI BIYU
Baki Biyu Sameera Mustapha:
HAKKIN MALLAKА (M)
Sameera Mastapha
GODIYA
Ga Allah (S.A.W), da ya bani fasaha da ilimin
rubuta wannan littafin, sannan ga Maigidana Alh.
Aliyu Sulaiman da ya ba ni goyon bayan rubuta shi,
sai ga Iyayena Alh. Mustapha !Haliru Bulasa da
kuma mahaifiyata Haj. Fatima Yahaya, Allah ya
Kara daukaka ku, amin.
TALLAFI
Ina godiya gare ki, Halima K/Mashi, da ki ka tallafa
min, ki ka ba ni karfin guiwar rubuta wannan littafi,
Allah ya kara budi, Allab kuma ya barmu tare, amin
summa amin.
TUKUICI NE GA
Nusaiba Sa'id Moh'd, Najib Sa'id Moh'd, Anisa Sa'id
Moh'd, Abduljalil Sa'id Moh'd, Arif Sa'id Moh'd
INA KAUNARKU
Anti Murja Bande Sokoto, Mama Sa'a O.P.U
Hauwa'u Iya (lya mai kosai), Baba Abu
BUGAWA A NA'URAR COMPUTER:
NAFI'U SALISU
08038981211-07028573535
2
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ar Sa'id ya mike zai wuce sai na ji HiBaba ya ce, "Sa'id Balarabe Ruma."
Ba Sa'id kadai ya saki baki yana
kallon Baba ba, har da mu da muke zaune a
wurin. Ya aka yi Baba yasan cikakken sunansa?
Baba ya ci gaba, "kai dan Asiya ne 'yar gidan
Dalhatu?" Da sauri Sa'id ya koma zaune yana
duban Baba ya ce, "haka ne, ni ne danta na fari
sai dai Alh. Balarabe ba shi ne mahaifina ba,
mahaifina ya rasu ban ma san shi ba, don kafin
יי Mamanmu ta haife ni ya rasu.'
Nan da nan idanun Baba suka juye suka zama
jajir, kamar garwashin wuta. Da alama
hankalinsa ba ya tare da mu, dukan mu kallonsa
muke yi mun kasa cewa komai, Gwaggo ce tayi
karfin hali ta ce, hala Baba Nafisa kasan
iyayensa? Ajiyar zuciya Baba ya yi kafin ya
dago ya dubi Gwaggo ya ce, ba za ki gane ba
Hauwa, wadannan sune usulina, ina ga rabona da
su tun ina dan shekaru ashirin da haihuwa a
duniya. Cike da son jin dalinsa Gwaggo ta ce,
ashirin fa ka ce, to menene hujjarka, na yake ma
kanka wannan hukuncin? Murmushi ya yi na
bata kai zuci ba, ya ce, Baba komai za ku ji
komai insha Allahu amma ina son sai na koma
Gusau gun babba sannan zan fadı ainihin labari
na ya dubi Sa'id ya ce, yaro kana iya tafiya sai
mun ne me ka, Sa'id cike da tashin hankali a
3
Baki Biyu Sameera Mustapha:
idonsa, ya ce, Baba don girman Allah ina son jin
aini irın dagantakar mu tsakaninmu don haka ina
neman alfarma nima ina son bin ko rannan da
zaka je Gusau sororo baba yake kallonsa, jin bai
yi magana ba Gwaggo ta ce, babu damuwa kana
iya zuwa amma fa shi gobe zai koma, don haka
ma tare za mu wuce a goben, ba damuwa zan iyà
bin ku zuwa can sai dai ina son don Allah kuyi
min uzuri sai na tashi daga ofis sannan zan kama
hanya don Allah kada a fara zacen sai na iso ina
so kwarai in san danganta kar mu da ko. Baba ya
ce, kada ka damu ba zan fada ba insha Allahu sai
ka isa tukunna.
A sanyaye kowa ya bar falon don abun akwai
daure kai gashi yadda yanayin Baba ya canza
fiye da yadda ku ke tsammani, ransa a bace yake
sosai duk wani annuri da sakin fuskarsa ya kau
lallai da alama babu sauki sai gurin Allah, Allah
yasa muji alheri, ashe muna da alaka da su Sa'id
shi yasa ake cewa muna kama tabbas nima ina
ganin kamar tamu har dai yau dinnan sai na ga
sun mafi kama da Baba, ikon Allah wannan abu
akwai daure kai. Duk yadda aka yi akwai
dangantaka mai karfi tsakanin mu don ban taba
zaton zan yi yi saurin sauka da abinda Sa'idu ya
yi min ba, amma lokaci daya na ji bana iya ci
masa fuska, nan da nan na ji duk na kasa ma ci
masa mutuncin da nayi kudurin yi masa, can
4
Baki Biyu 3 Sameera Mustapha:
cikin zuciyata yana da wani kima da ba zan kira
shi so ba, sai dai na rasa menene wannan abu, to
ai koma menene zamu ji in Allah ya kai mu
goben.
Washegari kuwa tun goma na safe muka bar
garin Kaduna zuwa Gusau, sha biyu da rabi
muka isa, sai bayan La'asar Sa'id ya iso, sai da
muka yi sallah sannan muka zauna falo, mutum
biyu ne kadai ba sa nan don su suna da nisa Anti
Fiddausi da kuma Anti Badiya, Baba ya fara
bamu labarin rayuwarsa a Katsina.
ASALIN MALAM
Ni cikakken dan usulin Katsina ne, a nan
cikin wani gari da ake kira Ruma, mahaifina
Alh. Bashir Ruma, da mahaifiyata dukansu 'yan
Ruman ne, to da yake ma su 'yan uwan juna ne, kun san Katsinawa da son yi auren gida. Duk da ba tare ake zama ba, sai dai kuma tushen mu daya. Mahaifin mu suna da yawa a gun iyayensu, don mahaifinsu mata hudu ne da shi
bayan haka ma akwai wadanda ya aura suka
rabu su biyu suna kuma da 'ya'ya da shi. A
lokacin ni ina dan aji daya a Primary mahaifina
ya rasu.. Ni kadai ke gare shi, gaba da baya sai
dai mahaifiyata da ta sake aure a dutsenma, ba ta
ma yi tunanin tafiya dani ba saboda tun rasuwar
Babana kanina ya dauke ni. Ina nan tare da Baba
5
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Hassan sai dai sam bana jin dadin gidan saboda
yadda matarsa ta gallaza wa rayuwata, saboda
tsabar wahala sai da na taba guduwa zuwa gidan
wan Babana, da kyar aka maido ni, gashi shi
kuwa Baba Hassan ba ya iya hana ta duk abinda
tayi shine daidai, ana cikin haka Baba ya bar
Ruma ya koma Funtua, da yake shi Manomi ne
sosai gashi sana'ar noma ta karbe shi sosai, don
haka ne ta cire ni Makaranta baki daya ta ce, ai
gara in rika taya Baba Hassan noma, wannan shi
ne dalilin da yasa ban yi Makaranta ba,
wulakanci da wahalar rayuwa ba wadda ban gani
ba. Muna! Muna!! Allah shi ne zai yi min
sakayya, amma ta gallazawa rayuwata ta duniya,
haka zan ga 'ya'yanta na zuwa Makaranta amma
ban da ni.
Da na girma lokacin ina da shekaru sha
takwas a gun noma babu abinda ban iya ba har
na koya tuki da motar Baba Hassan sai dai ko shi
bai san na iya ba.
Wata rana naje sayen abincin rana da yake
akwai gun saidawa a kusa da inda muke aiki, na
hadu da Maryam, aiki take yi ma mai abincin
Maryam ta shiga raina tunda na aza idona
akanta. Ai ban jira wani abu ba nayi mata
magana cikin ikon Allah kuwa muka fahimci
juna, har na soma zuwa gunta hira, a saukake da
na san 'yan uwanta baki daya kuma suka amince
6
Baki Biyu Sameera Mustapha:
da ni, da ya ke da kun san muna aure da wuri, da
kuma ba Makaranta ake yi ba, iyayenta suka
soma yi min zancen aure, ban jira komai ba naje
nayi wa Baba Hassan magana. A zahiri ya nuna
min farin cikinsa, sai duk jikina ya mutu don na
gani a kwayar idonsa kamar abinda bai masa dadi ba.
Bayan kwana biyar da yi masa magana ne ina
gun aiki Dalhatu dan Baba Hassan na uku ya zo
nemana, Baba ne yake kirana a gida kuma ya ce
mu zo maza-maza tare da Dalhatu, abun ya bani
mamaki da ba za a bari in dawo gida ba, awa
nawa ya rage in bar wurin aikin, na tambayi
Dalhatu abinda ke faruwa, ya ce Baba Usman ne
ya zo ai ban san lokacin da murna ta kama ni ba,
duk a cikin su na fi sakewa da shi, don shi ke
kwatar min 'yancina idan ma za'a danne.
Cike da farin ciki na isa gunsa muna gaisawa,
sai dai na lura ransa a bace yake kwarai, ga su
muna da mijinta a gefe dukkan su fuskarsu ba
kyau, Baba Usman ne ya fara magana, kai da
gaske ne ka fitar da wadda ka ke so? na sa kai na
kasa ina murmushi, na ce, eh gaskiya ne Baba, to
Muna ta ce kun yi maganar Asma'u diyar
kanwarta da ita, akan ita ce zaka aura! Kuma ka
amince da hakan?
Gabana ya na bugawa na daga ido na kalli
Inna fuskarta babu kyaun gani ta wani bude
7
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
hanci tana rarraba ido kamar....Baba ya ce kana
jin abunda na fada, haka maganar take? Kada ka
cuci kanka don ba kowa zai zauna da matar ba
sai kai, Baba a gaskiya ni Maryam nake so ba
mu taba maganar Asma'u da Inna ba. Baba
Usman ya yi murmushi na gamsuwa ya ce, da
kyau shi kenan an gama kana iya tafiya, da zan
bar wurin naji Inna ta soma ba har da cewa to sai
ta ga yadda za'ayi ayi zaman auren, ita da renon.
yaro shine don ka kai munzalin aci moriyarka
zaka yi min butulci, to wallahi in kun san wata
ba ku san wata ba, Baba Usman ya riko hannuna
ya jani waje, rabu da ita ba abinda zai same ka
sai alheri, butulci akan ka aka fara yarinyar fa
bata da hankali ma, irin yarannan ne da ba a
haife su da lafiya ba, masu zuwa duniya da
matsalar ciwo irin ta shanyewar kafa, ko wani
gefen jikinsu dai a nakasashe ne, shine ta zabar
maka don kai ne baka son dadin rayuwa, tsana
ce karara Inna take nuna min ta yaya zan auri
mace irin Asma'u bayan ni nasan ina da komai
da ake son cikakken namiji ya mallaka, ba wai
na ce ita Asma'un ba mutum ba ce, a'a amma
gaskiya ba zan iya zaman rayuwar aure da ita ba.
Ba a maida sati ba, su Baba Usman suka
dawo nema min auren Maryam, ai kuwa anyi shi
cike da sauki, don har mahaifin Maryam ya ce a
gama komai kafin a tashi. A take kuwa aka yi
8
Bakı Biyu Sameera Mustapra:
komai don har da Sadaki aka yanka a lokacin aka
kuma sa ranar aure, nan da wata daya da rabi
albishir din da Baba Usman ya zo min dashi
kenan, tun da aka sa ranar aure da Maryam
abincin gidan Baba Hassan ma na daina ci, kirikiri zan ga alamun barbaden magani a ciki, cikin
gidan ma na daina shiga saboda irin wulakancin
da Inna Muna ke yi min, ita da yaranta.
Ana saura kwana biyar daurin aure aka fara
zuwa daga Ruma, aka kuma hado min sha uku ta
arziki, daga gun 'yan uwa da abokan arziki na
mahaifina, dama nima na dan tara nawa
komatsai aka hada aka kai a matsayin lehe.
An daura aure ranar Juma'a bayan anyi sallah
Juma'a, a ranar kuma muka tàre da Maryam a
gidan kawunta, da aka ara mana sai dai iyayena
sun ce Ruma za mu koma don akwai gidan
mahaifina da ya bari. An dai bar shi akan sai
mun yi sati biyu anan sai mu wuce can.
Bayan kwana uku da aure abin mamaki cikin
tsakiyar dare na rika jin kamar ana buga mana
kofa, Maryam na gefena tana barci, na mike na
isa gun kofar ina leke, babu kowa a gurin don
haka na bude kofar tare da dauko buta don in
zaga, ina tsalake kofar dakin, ji nayi kawai na
soma tafiya tunanina ya 6ace, ban san abinda
nake ciki ba tafiya kawai nake yi, ni dai ban san
abinda ke damuna ba har na smai tsawon kwan
9
Bakı Biyu Sameera Mustapha:
ashirin da bakwai ni dai ban san yadda aka yi ba
sai gani a kasar Zamfara, cikin ikon Allah a nan
na soma sabuwar rayuwa, sam bana son a
ambaci sunan garin. Katsina, a rayuwata cikin
ikon Allah, Allah ya hada ni da mutumin kirki
irin Alhaji Moh'd Shinkafi, wani lokacin zaka ga
kamar ba a cikin hankali kaina nake ba đa yake
idan lokacin wahala ya kare sai kaga abu ya
wuce kamar ba ayi ba. Sai da na samu kusan
shekaru goma sha uku sannan na soma samun
natsuwa, can zaka ga na tuna da su Baba Usman
wani lokacin kuwa sai in tuna da Maryam, sai
dai ban taba fada ba, sai a wannan lokacin,
bayan haka ma Mairo ta taimaka min a rayuwa
don sanadinta na kara samun lafiya abinda yasa
sauran matana suka fita kenan, da a gaskiya sai
mai hakuri ke iya zama da ni, da yake ina da
rabon 'ya'ya gashi kuma na haifa, bai fi ma
shekara uku ba da na kara samun isasshen lafiya
sanadin wani Malami da nake karbar magani a
gunsa.
A gaskiya Mairo Allah sai ya saka miki ko ba
a nan duniya ba, to a lahira ina rokar miki
aljanna fiddausi.
Sharkaf nayi da hawaye da jin wannan labari
na Babanmu, ashe rayuwa haka take? Kana nan
baka damu da mutum ba shi nema yake yi yaga
Karshenka, tabbas sammu aka yi wa Baba.
10
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
Muryar Sa'idu ce ta tsinka min tunanina, da
ya ke maganar cikin kuka ya ce, anya ba kaine
mahaifina ba! Furucinsa yasa kowa ya maida
hankali gunsa. A gaskiya sai a lokacin naga
kamanni tsantsa da mahaifinmu ne Sa'idu yake
kama shi yasa ake ganin kamarmu dashi ashe
photocopy din Baba ne, ikon Allah wani abun
sai Allah, baki daya falon ya yi tsit ana kallonkallo mu kalli Baba mu kalli Sa'id, da ya ci gaba
da cewa, mahaifiyata, sunanta Hajiya Maryam
Balarabe sannan ta bani labarin mahaifina ya
rasu tun kafin a haife ni, sannan wani lokacin
kuma takan ce min ita bata san yadda aka yi suka
rabu da ita dai ta wayi gari bata ganshi ba, kukan
da Baba yake yi shi ya dakatar da Sa'idu, ya се
Allah ya isa tsakanina da Inna Muna, idan ita ce
sanadin abinda ya same ni, Sa'idu kam shima
kukan yake yi, ya isa gun Baba, ya sa kansa kan
cinyar mahaifina yana kuka wiwi, dole Baba yа
daina kukan yana lallashin Sa'id.
Abu kamar a fim, Sa'id ya kuma zama wa а
gare ni, wannan abun al'ajabi ne a gare mu, baki
daya. Ga kuma murnar ganin dan uwanmu,
Allah shine abun godiya da ya nuna wannan
al'amari cikin sauki. Sai da aka natsu sosai duk
wani hawaye ya bushe sannan ne Sa'id ya ce,
mahaifiyarsa na nan a Kaduna tana aure. A
gaskiya wannan al'amari ya yi mana dadi,
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Gwaggo ta ce, ah wani abun sai Allah, Sa'id ya
zo neman aure gashi abu ya juya to Allah ya kare
mu daga sharrin dan adam, amin muka amsa
baki daya.
Mun kwana biyu a Gusau ranar Lahadi Sa'id
ya ce, zai koma Kaduna don zuwa office,
Gwaggo ta ce, to ai gara mu ma mu koma tunda
abun ya zama haka, Allah ya ba kowa rabonsa
amin. Mun kama hanyar zuwa Kaduna, abinda
na lura dashi shi ne, yadda Sa'id ke jin kunyata,
ni kam wallahi ko a jikina dadi ne ya yi min
yawa.
Washegari Sa'id ya zo ya dauke mu zuwa
gun mahaifiyarsa, saboda na matsa ina son
ganinta, Gwaggo ta ce, ai har sai kin gaji da
ganin nata tunda yanzu an zama daya. Gida ne
babba sosai bayan an bude gate mun shiga,
motoci ne cike da gidan, ga tsarin gida irin
ginnan na da amma har a yau bata wuce lokacin
ta ba. Har mun isa falo wanda a cike yake da
kayan alatu irin na zamani, Sa'id ya ce, mu
zauna bari ya yi mata magana, bayan minti biyu
sai gasu sun fito, wai a gaskiya mahaifiyarsa ba a
bar ta a baya ba gun kyau, fara ce ba ka taba
cewa ita ta haifi Sa'id saboda tana da jiki mai
kyaun gaske.
Jikinta a sanyaye ta rika fara'a tana gaisawa
da mu cikin natsuwa, kusa da Gwaggo ta zauna,
12
Baki Biyu Θ Samecra Mustapha:
muka hada ido da ita, ta fadada murmushinta, ta
ce ke ce Dayyiba? Nima na sakı murmushin na
ce, eh! Ni ce ai ga kamanni nan sak dai da mahaifinku, shi kuwa jininsa ya cika karfi, baki daya aka yi dariya. Cikin kankanin lokaci aka cika mu da kayan abinci sannan ta saki jiki sai
hira suke yi da Gwaggo nan da nan suka shiga hira kamar da can sun san juna da aka kira
azahar 'ya'yan ta suka rika shigowa suna gaida mu, ikon Allah Halima dama ke kanwar Sa'id
ce? Eh, wałlahi ta fada ta iso inda nake zaune
dama ku ne 'yan uwan Ya Sa'id da ya bamu labari jiya? Mune Halima, Umma haka suke
kiran Hajiya Maryam ai tare muka yi state University (Kasu) kai haba dama ashe kun san junanku, Allah ne bai yi ba kuwa da mun hadu don a cewar yaya sai mun je mun gaisa, to gashi
ai a saukake mun haďun. Ta ja ni zuwa cikin dakin su, muka shiga sabon hira.
'Ya'yan Haj. Maryam uku da ya Sa'id hudu
kenan Hálima ita ce 'yar ta ta uku, saboda-akwai
adama ita ee babba sai autan ta Sagir, Babansu Soja ne, belgeria balarabe ruma, babba ya san shi
tun a funtua shi ne saurayin Haj. Maryam na farko kafin Baba ya santa, dama ai an ce matar
mutum kabarinsa.
Wai har yanzu baki yi aure ba Halima? Haba
dai nayi muna gama school, Sai dai har yanzu
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
ban haihu ba, aiya! Allah ya kawo, ke fa ba ki
haihu ba? Humm! Ban haihu ba kin san
naigidana ya rasu! A ya yi hakuri wallahi ya
Sa'id ya fada mana, Allah ya jikansa amma ai
kamar ya yi shekara da rasuwa ko? Eh!
Shekarunsa biyu da wata shidda, yaushe za kiyi
aure? Ta yi tambayar tana murmushi, ajiyar
zuciya nayi kafin na ce to sai Allah ya kawo
mijin to kunna, kai dai 'yar uwar a yadda ki ke
din nan kice ba ki da manema gaskiya ban yadda
ba, haka ne to ko in ce gwanin ne ban samu ba,
na fada ina dariya. Hira sosai muke yi da
Halima. Karfe biyar saura Gwaggo ta ce, in fito
mu tafi, a gaskiya sam ban ji komai a tare dani
ba sai godewa Allah da nayi akan yadda ya
shirya abun.
Da muka isa gida muka zauna ni da Gwaggo
muna tattaunawa akan family din mu, da na
Sa'id, take bani labarin Haj. Maryam har da
karamin hauka tayi da Baba mu ya bace, cikin
Sa'id kuma da ta samu sai da ya kai wata hudu
sannan aka sani. Bayan ta haihu bacewar Baba
ya zama mata sabo saboda karamin Sa'id.
Bayan sati daya da faruwar haka sai ga Baba
Usman da Baba Salihu sun zo gidan Gwaggo,
sun dade sosai kafin suka ce za su wuce Gusau,
ranar Asabar gun Baba mu. Ni kam da
karambani sai da na kai su gidan Anti Badiya,
Baki Biyu Sameera Mustapha:
sun yi murna sosai da ganinta, da son samu ne da
na kai su gun Anti Fiddausi a Abuja, amma da
muka yi waya da ita sai ta ce, mu bar shi za ta 70
Kadunan dama ranar Laraba.
Anti Fiddausi ta zo Kaduna da alama wani
cikin gare ta, kai Anti ke dai kullum haihuwa?
Harara ta Gwaggo tayi ta ce, tafi can ke kenan
kullum mita akan yayin ki da kannanki, na
haihuwa, Allah na roke ka ba ta, haihuwa ba
sassauci in ga yadda zaki yi, kai Gwaggo ki
daina min wannan fatan don ni so nake ko nayi
aure sai na samu irin shekaru hudun nan kafin in
haihu, to ai su ba kan su zabi ba don ga
Maimuna nan ma itama da cikin, a'a lallai ni
kam ai ko haihuwar farko nayi, sai yaran dan
tasa kafin in kara haihuwar, ita dai Anti Fiddausi
bata ce min komai ba sai dai murmushi da take
yi.
Zumunci sosai ya shiga tsakaninmu da
mahaifiyar Sa'id yawanci muna zuwa gidan ta
itama tana zuwa gidanmu, itama Halima a nan
kusa da gida take aure, tana auren Soja ne itama,
a karkashin mahaifinta yake Major Jibril
maiwada, shima kuma mahaifinsa Sojan ne,
aminin Baban Halima ne.
Wata ranar Alhamis nayi shiri cikin lace ash
ne da ratsin fulawa ja, dinkin fitted ne na dauko
a baya sai dai ban riga na saka ba na isa gun
15
Bak Bry Θ Sameera Mustapha:
Gwaggo na zauna muna dan taba hira, sai bayan
sallah azahar zamu fita zamu suna Aisha cc ta
Kara haihuwa, ke kin fauko ledar kayan kuwa?
Na mike ina dariya lah! Kin ga har na manta ke
dai kin cika mantuwa, wata rana ma nasan sai
kin ce kin manta da kanki, na kara kwashewa da
dariya kai Gwaggo na wuce dakinta, dawowan
da zan yi na işke Amir ya shigo falon, kamshin
turarensa ya biyo ko ina, ba tun yau nasan
kamshin turarensa ba, don haka gabana ya shiga
faduwa, na rasa kuma dalilin hakan. Babu abinda
na ki jini da irin halinsa bacin irin kallon da yake
min, na tsani haka sam bana kaunar wannan abu,
abunda ya fi bani haushi da shi kuma babu
ruwanshi da Gwaggona, nan kallo na zai ta yi
magana na dainawa take, da zarar ta ga inda
hankalinsa ya koma kaina abun haushi kuma
abayar da zanyi amfani da itama akai ya zauna.
Duk na bi na tsargu da irin kallon da yake
min, ko gaishe shi na kasa. Kai tsaye kofar fita
na kama, Gwaggo ta ce hada masa abinci
Dayyiba, raina ya yi bala'in baci, sai dai ya na
iya, dole ne in yi. Da na hada abincin ma Asabe
na ce ta kai masa.
Haushi ya karu a gare ni, saboda ya kusan
awa daya da rabi suna hira da Gwaggo da abun
ya ishe ni dole na koma falon na wuce dakina, a
lokacin na ji Gwaggo na cc masa, babu damuwa,
16
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
zan yi mata magana, wata abayar na dauko, na
yafa na isa falon kamar zan fashe, Gwaggo kam
ko a jikinta na lura hirar nayi mata dadi, ringin
din wayan hannuna tasa hankalinsu ya dawo
kaina, sam bana yadda mu hada ido da shi, na
kara wayar a kunnena. Amina ce ta rika yi min
sababi na rashin zuwa, bata bari na ce komai ba
ta kashe wayar.
Na isa gun Gwaggo ina yi mata magana, cike
da shagwaba, kai Gwaggo lokaci fa na tafiya, ai
dama fita zaku yi ne? ko kallon inda yake ban yi
ba na ci gaba da abinda nake yi, Gwaggo ce ta
amsa masa, Eh, fita zamu yi, kawarta ce ta
haihu." Ok, to muje in sauke ku mana, a'ah bar
shi kawai, kada mu bata maka...." Ya katse
Gwaggo kada ki damu Gwaggo ina garinnan har
zuwa gobe saboda ina son zuwa Gusau. Idan ku
ka gama sai ku kira ni in dauko ku, a take raina
ya yi baki na bala'in tsukewa, amma babu yanda
zan yi don haka na sha jinin jikina, sai da ya fita
Gwaggo ta ce, min kin san Amir ke yake so? ji
na yi kamar in yanka ihu, sai dai nayi kokari na
kama kaina, kuma na yi kamar ban ji abunda
take fadi ba, itama kyale ni tayi muka kama
hanyar fita, da sauri na shiga gidan baya ina
wani huci ina turo hanci na cika fam kamar
ballon.
Abun takaici kuma ashe na zauna inda zai
17
Baki Biyu Sameera Mustapha:
rika ganina ta cikin mirror gaban motar, hada ido
muka yi dashi ya sakar min murmushi, harara na
sakar masa nayi saurin komawa dayan gefen, ina
kallon gefe na da muka hau titi, ya ce Gwaggo
ina zamu ne? ta ce, ai Dayyaba ta san gidan don
haka sai ki rika fada masa hanyar da zamu bi,
yanzu kam na kai karshen kulewa na tunzuro
bakina, ina magana unguwar Dosa za mu je, ya
dan jiwo da kansa sai fa kin nuna min ba wai
nasan