cikin gida ta fada wa Belly
da Binta abinda ke faruwa, suma sun jinjina da
abinda ke faruwa. Sun dai bata magana amma
sam hankalinta bai kwanta ba, ba ta son ta rasa
iyayenta ba tare da ta nemi gafararsu ba.
Washegari bus suka shiga irin wannan
doguwar babba ce sosai, tafiyan kwana daya da
rabi suka yi suka isa Niger, da yake ta nan suka
101
Bakı Biyu
biyo. A Kalla dai sai da suka kwana uku suna
tafiya. Da suka shiga Katsina, da za su shiga
mota ta Kaduna suka shiga. Tafiya suke yi kamar
basa yi don Suwaiba ta gaji sosai, sai wajajen
Karfe sha daya saura suka isa tashan kawo na
Kaduna. Tashan mota suka yi suka wuce Abuja a
cewar ta gara sun karasa don su huta baki daya.
Karfe biyu da minti goma sha uku suka isa bakin
Kofar gidan Tahir, dabara ta fado mata ta ce da
direba tana zuwa, ta isa bakin kofar gidan tana
kwankwasawa Baba Maigadi ya bude don abun
nan na leke yana lekawa duk da duhun daren ya
gane Suwaiba da sauri ya bude kofa ya cika da
mamaki.
"Hajiya ke ce? Shigo mana." Ya fada yana
bata hanya, ajiyar zuciya tayi ta saki murmushi
ta ce, "Ni ce Baba, ya bayan rabuwa?" Ya amsa
"sai alheri." Ta dan dubi cikin gidan ta ce,
"Tahir fa! Yana nan?" Baba ya ja dogon
numfashi ya ce, a hankali yana asibiti an kwantar
dashi yau kwanansa shidda kenan." Tuni hawaye
ya soma fitowa a fuskarta. Ba ta iya tambayar
Baba maigadi inda aka kwantar dashi ba, sai
Mal. Attahiru ne ya tambaye shi, saukin abin
mai taxi yasan asibitin, don haka kai tsaye suka
wuce.
Muna zaune cirko-cirko kowa da abinda yake
102
Baki Biyu Sameera Mustapha:
tunani a zuciyarsa, yau kwanan Tahir biyu kenan
bai san a inda yake ba, yana "comma" sai abinda
Allah ya yi, kaina na hada da guiwa ta duk abin
duniya ya ishe ni, na san na kamu da son Tahir,
to ya...Mama ce ta tsinka min tunanina da ta ce
Suwaiba! Tayi maganar a tsawace, wanda yasa.
kowa ya kalli inda take kallo. Tabbas Suwaiba
ce, naga ta jeme ta rame anya ita ce? Na mike
nima na soma tafiya zuwa inda take, don tuni
Mama ta isa gunta, tana kuka tare da rike ta
itama Suwaiba kuka take yi, na ban tausayi. Ina
tsaye daga gefe ina kallon yadda Suwaiba ta
zama, anya lafiyarta kalau? Nan aka zagaye ta
kowa da tambayar da yake mata, ita dai bata
amsa ba. An sami kusan minti goma sha uku
kafin mahaifanta suka shigo suka rungume ta
baki daya, sai a lokacin ta soma fadin abinda ya
same ta. sam bata ji nauyin fadin abinda ya kaita
ga wannan mahalaka ba, ai ni tuni jikina ya soma
rawa kamar mazari dama haka take? Idon da
muka hada da ita yasa tayi saurin mikewa ta iso
guna tana kuka, dakewa nayi na tsaya amma
wallahi tuni na tsure. Riko hannuna tayi ta ce,
don girman Allah Dayiba ki yafe min, guiwarta a
kasa take neman gafarata, ai ban san lokacin da
nima hawaye suka taru a idona ba, na ce na yafe
miki duniya da lahira, ai ban san lokacin da na
rungume ta ba ina hawaye. Daga bayan mu muka
103
Baki Biyu Sameera Mustapha:
jiwo hayaniya, doctors ne su biyu suka shigo
asibitin cikin gudu suka shiga dakin Tahir, na
shiga uku ai tuni zuciyata ta buga, kowa dakin
ya nufa, Tahir ne ke ta shure-shure wallahi nasan
ina tausaya wa kaina idan na rasa Tahir, to amma
sai naga kamar ban kai Suwaiba zama abun
tausayi ba, don tafi ni saninsa. Irin yadda take ta
surutai na ban tausayi yasa na bar wurin naje
nayi alwala na soma jera nafilfili, cikin ikon
Allah kuwa abun ya sassauta, ya farfado har
yana amsa gaisuwan mutane. Na shiga dakin na
iske Suwaiba rike da hannunsa sai sharfar kuka
take yi, tana rokonsa gafara.
Abun tausayi, duk an su sun bani bala'in
tausayi, na isa gefen sa ina dai tsaye ina kallon
fuskarta da tayi kamar ba shi ba, jini kuma na ga
an rataye ana sa mishi. A lokacin muka jiwo
sallama, muryar na san ta amma na manta ko a
ina na san ta, na kuma kasa daga idona in dube
shi, kaina a kasa ina ta son in tuno inda nasan
muryar nan amma na kasa ganewa, har ma ya
rika magana da Tahir a hankali, in ba ka saurara
ba ba za ka ji abinda ya ke fadi ba.
Gabana wani irin bugawa yake yi, na rasa
dalili ai ban san lokacin da na bar wurin ba, don
tuni marata ta cika da fitsari, don na so in gano
mai ainihin muryar. Ya Amir ne, haka na fada a
zuciyata, har na kai kofa na ji an ambaci sunana,
104
5
Baki Biyu Sameera Mustapha:
waigowan da zanyi muka yi ido biyu da Amir,
tas-tas-tas gabana yake yi, na yi saurin dauke idona daga nasa saboda a gaskiya gaba ki daya
ya canza, yayi fari ya yi kiba ashe ba karamin
kama yake yi da su Tahir ba, fuskarsa ta cika
sosai, gashi ya bar saje ya kwanta luf a fuskar
tasa, ya yi min kyau a idona...katse min tunanina
Tahir ya yi da ya ce, in kin fita ki ce da Baban
falo ya shigo. Na saki fuskata na ce, to. Tahir
murmushi ya sakar min kafin na fita, na fita
kenan sai na hadu da su za su shigo, sai a lokacin
suka yi sallah Isha'I, na fada masa da sauri ya
Karasa.
Ina toilet tunani ne ya kama ni, mamakin
canzawar Amir nake yi, ga baki, daya ya canza
kamar ba shi ba ne, kai anya shi ne ko dai kallon
tsoro nake masa? Kai ina jin dai idanuwana gezo
suke min ban lura da shi ba da kyau, hayaniyar
da na jiwo a waje shi yasa na yi saurin barin
bayin saboda ihun Mama ne yafi firgitar dani, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" Allah ya yi
wa Tahir cikawa." Ai ban san lokacin da na
koma zaune ba, kukan zuci nake yi, ba wai kuka
nake yi na waje ba, hawaye ne kawai ke gangara
daga idaniyata, kai a wannan rana ta zama ranar
tarihi a zuri'armu baki daya. Dan a gaskiya
munyi babban rashi, a raina tabbas nasan ina
tausaya ma kaina don irin son Tahir da ya shige
105
Baki Biyu Ο Sameera Mustapha:
ni lokaci daya amma gaskiya na fi tausaya wa
Gwaggo don sai da tayi suma har biyu a lokaci
daya, daga karshe ma gado aka bata.
Allah Sarki! Rayuwa kenan, gashi muna ji
muna gani Tahir ya tafi ya bar mu. Asibitinnan
kan kice kwabo. Ta cika da jama'a har babu inda
zaka zauna duk a matse ake. Da ya ke karfe
biyar saura ya cika sai aka yanke shawarar a
shirya shi ana idar da Sallah asuba sai ayi
jana'izarsa, abun jin shi nake yi tamkar mafarki
don na bala'in sawa raina Tahir zai tashi, ko
rabuwa ta ta karshe da shi, ya bani kwarin
guiwar zai tashi. To ta Allah ba taka ba, kana
naka Allah na nashi, Allah yasa mu dace ya sa
mu cika da kyau da Imani (Ameen).
Da aka yi jana'izarsa gidan Gwaggo aka
wuce baki daya, har da Gwaggo muka koma
gida, ina zaune gabda ita duk fuskokinmu a
kumbure yake har a lokacin kuma bamu daina
kukan ba, sai dai kukan zuci yafi yawa. Zaman
makoki muke yi, tuni na kara rama don dama
tuni dama ramar ta so ta yi min yawa.
Kwanan Tahir uku da rasuwa, aka kwasa
muka wuce Gusau, shinkafi a kaje sai da muka
kwana sannan muka wuce gidan Baban falo a
nan cikin Gusau, har aka yi kwana bakwai
Gwaggo bata da lafiya, a yanzu haka tana
kwance a asibiti jininta ne ya hau, ni kam ina nan
106
Baki Biyu Sameera Mustapha:
tare da ita. Sai da ta kwana shidda a asibitin
sannan aka sallame ta.
A gaskiya Gwaggo da Suwaiba sun ji jiki ba
kadan ba, ni kam rama ce nayi kamar mai ciwon tyford dina ne ya tashi.
A nan gidansa na Gusau aka ce muyi takaba,
ni ce na koma ina rarrashin Suwaiba, baki daya
ta fita hayyacinta, kai so cuta ne, da yake ni mai
zurfin ciki ce, sai dai in ta kukan zuci. Kayan
abinci babu abinda babu komai a adana mana.
Haka aka yi sati hudu jama'a suna zuwa
gaisuwa, a gaskiya Tahir ya yi jama'a sosai ga
yabo da ya samu gun mutane. Kyakkyawar
shaida kam ya same ta, Allah yasa mu ma in
tamu tazo mu cika da kyau da imani amin
summa amin.
Da aka yi sadakan arba'in, a lokacin an taro
gidan Baban falo aka yi ta addu'a. Bayan sallah Isha'i ne aka tara mu a babban falonsa na kasa,
ni kam ina daga can nesa anan ina hango manyan
iyayenmu da 'ya'yansu. Alh. Ashiru shine mai bi
ma Baban falo, shine ya bude taron da addu'a
sannan ya kara yi mana gaisuwar marigayi
Tahir, daga nan dokiyar Tahir baki daya aka
fada, ana son a raba gadon tun a yau. File ne
Barrister Kasimu shine Lauyan Tahir, ya fara
gabatar da tsarin da Tahir ya bada akan wasu
dukiyoyinsa, wadanda ba za su kasance a cikin
107
Baki Biyu 0 Sameera Mustapha:
rabon gado ba. Kamfaninsa da ke Thailand
sunan Gwaggo Hauwa ya saka ya bar shi akan
ita ce mai kamfanin halak malak, takardar aka
fito da ita aka nuna sannan ya rubuta ya bar wa
Amir amanar ya kula da kamfanin yana kuma
son a ba Dayiba wani sashi na kamfanin, wato
matsayi na board of directors. Yana da wani
kamfanin a nan Nigeria yana son Amir ya zama
mamallakin wannan kamfani nasa halak malak,
wannan kamfani ita ce wanda yake juya kudinsa
ta hanyar mai na petrol da yake Lagos.
A nan Lauyan ya yi shiru, ya yi sallama ya
zauna wani ne ya mike ya gabatar da duk wata
kaddara da Tahir ya tara. Nan fa aka fiddawa
Banki nasu aka kuma raba shi kamar yadda
addinin Musulunci ya tanadar. Ni da Suwaiba a
kalla sai da muka tashi da gidaje hudu-hudu,
bacin kudin da aka ce ya kai million biyar,
tabdijan, lallai ashe ba karamar dukiya Tahir ya
tara ba. Nan dai aka ba kowa nashi aka watse.
Ina Gusau dai ban koma Makaranta ba, da
yake an ce duk da idda da nake yi ina iya zuwa
Makarantar tunda anyi arba'in, wallahi ji nayi
Makarantar baki daya ta fita raina, na rasa dalilin
hakan, sam babu nutsuwa a tare dani, sai dai
karfin hali da nake yi in shiga mutane don kada
tunani ya yi min yawa. Tunda da Tahir ya rasu,
ba kwanciyar da zan yi ban yi mafarkinsa ba, ni
108
Baki Biyu Sameera Mustapha:
nasan na cuce kaina da na daukarwa kaina karfin
halin da ban amincewa Tahir kaina ba, a raina
ina tunanin irin hukuncin da Allah zai yi min
idan muka hadu gobe, wani lokacin kuwa idan
na tuna ya ce, ya yafe min sai in ji dan sassauci a
tare da ni, an sami kusan wata biyu da rasuwar
Tahir kafin na koma Kaduna, saboda nan da
kwana goma za'a mu fara jarabawa. Dole na rika
bin lecturers suna yi min make-up test saboda
baki daya ban yi ba.
Bayan na gama jarabawa, Abuja na wuce gun
Gwaggo, ban ji dadin yadda na ganta ba, duk ta
rame ai sai mutuwar Tahir ta zama min sabuwa,
sai dai idan ina gaba Gwaggo ina iyakar kokarin
yaki da damuwa ta saboda Gwaggo ta saki ranta.
Cikin ikon Allah kuwa ta saki jikinta don
abinci ma sosai take ci, ba karamin kula nayi da
ita ba, nan da nan ta soma kumari. Har muna
zama muna hira cike da nishadi, sai dai ni kam
sam ba haka ba ne a guna, sai na shige faki zan
ta kuka ina kuma neman gafara gun
mahaliccinmu.
Da yake lokacin nan kwana kin ba wuya sun
zo sun wuce wata ya zama sati, shekara kuwa ta
zama wata har nayi na gama idda ta. A lokacin
kuma result dinmu ya fito, ikon Allah gashi na
rike degree na a hannuna na fito da low-credit,
ban da matsala. Service muke jira a kira mu.
109
Bakı Biyu e Sameera Mustapha:
Har a lokacin ban maida jikina ba abun
mamaki sai gashi na zama Ustaziya, haka su
Amina ke kira na, saboda na koma wata shirushiru, sannan hijab din da nayi amfani dashi
lokacin da nake Idda shi din na ci gaba da
amfani dashi. Ashe mutum kan canza? Nima а
koda yaushe ina mamakin kaina, duk wata ji da
kai da iya yi na bar shi, nayi bala'in natsuwa
babu ruwana da wata kwalliya, kai smiling da
ake kira nama a da ba za a kira ni da wannan
lakani ba duk ta dama tun da namiji ya gasa ni a
rayuwa na rage, wasu abubuwan to a yanzu ma
abun yafi muni, ganin nake yi, dama haka Allah
ya shirya min rayuwata ba zan yi dacen zaman
aure ba. Kowa ne namiji nake so to sai ya zama
mini matsala gani da wata irin zuciya da in ta
kamu da son namijin sai na wahala, ko daya ke
Tahir son sa ya shige ni ne a ba zata ko don
hakurinsa ne yasa hakan oho! Allah ya zaba
mana abunda ya fi zama alheri a gare mu shi ne
addu'armu a kodayaushe.
A yanzu kam komai ya wuce daga Gwaggo
har ni mun saduda mun bar wa Allah komai yana
tafiya normal. Ina zaune a falo ina kallon Indian
film a zee aflam, hankali na na gun kallo har aka
shigo bar sani ba, da yake ina falon Gwaggo ne,
zaman da aka gefe na yasa na tsorata na dube
gunin wa zan gani! Amir ne! Da saurin gaske na
110
Baki Biyu
dauke ido na
Sameera Mustapha:
daga kallonsa. Gashi mun hada ido
da shi, ya aka yi ban ji shigowarsa ba, a gaskiya
ya canza daya wa, ya yi kiba kamar yadda Tahir
yake kai ashe ba karamar kama suke yi ba,
abunda Tahir zai nuna masa haske, shi kuwa yafi
Tahir gashi kai gashi yana da saje tun fil-azal,
yanayin sa da kusan komai sa irin na Tahir, oh!
Allah mai talita, sai dai Amir halinsa sai
shi......ya katse min tunanin da nake yi, ke baki
ga mutum ya shigo bane ba za kiyi gaisuwa ba?
Maganarsa ta zo mu a baza ta, ban san lokacin da
na murguda baki ba tare da tsuke su, na kuma
wani bata rai kamar dawo, gero ina kallonsa
dama ta gefen idona fuskarsa a sake take tun
lokacin da ya shigo, na fada cike da kasaita, ai
da zaka shigo baki yi sallama ba, ni kuwa a sani
na an koyar damu wannan, na yi shiru, sai dai
gabana kamar zai fado saboda yadda take
bugawa, karfin hali ne nake yi zaman da nake yi
agun da son samu ne da na gudu don ya maida
hankalinsa baki daya a kaina. Kallo na yake yi
kamar a yau ya taba ganina, gashi kayan da ke
jiki na ba masu nauyi bane atamfa ce riga da
sket, anyi masu dinki fitted kaina kuma babu don
kwalli, gashi kitson twixin nayi, duk da ba
kwaliya nayi ba amma nasan fuskata tayi kyau.
Dama rabona da kwalliya tun rasuwar Tahir, ban
san tunanin me ya yi ba ya mike tsaye, gabana ci
111
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
gaba ya yi da faduwan can daga bakin kofa a
jiyo muryar Gwaggo ai sai na ji kamar an sauke
min wani katon dutse. Na mike buzut na bar
wurin, abun haushi bai daina kallona ba, kai
gaskiya wannan mutumin 'A' ne sam baya jin
nauyin abinda yake yi, Gwaggo har ta je ta zauna
bai sani ba, har magana take yi masa amma sam
hankalinsa ba ya tare dashi, sai da na shige daki
na na kule sannan, na ji ya suma an sa Gwaggo
ko a jikinsa kuma kai wannan mutumin kunya
ma bata ishe shi ba, maganar dukiyar da Tahir ya
bar wa Gwaggo yake yi dama kowane wata sai
an kawo mata report, akan abunda ke faruwa.
A yau ma shekara ce ta cika ya zo da kansa
ya yi ma Gwaggo bayanin dala-dala abunda ake
ciki, tun da Tahir ya rasu, ya kan leko gun
Gwaggo ya gaida ta, sai dai ikon Allah bamu
taba haduwa ba sai yau. Ya tabbatar mata da
komai yana tafiya daidai, sannan akwai meeting
da ake yi kowace' karshen shekara na board of
directors na kamfanin don haka ana bukatar ta a
Thailand don ita ce mai kusan kashi saba'in a
dukiyar kamfaninta, ta ce haba dai Amir ni fa na
fada ma tun farko kai zaka ci gaba da kula da
wannan kamfanin, ni na baka dama na amince
maka kaje kayi duk abinda ya dace, wallahi bani
ta zargi ko zato akan ka, na san zaka rike amana.
Sosai ta kashe masa jiki bai iya gardama da ita,
112
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ajiyar zuciya ya yi to na gode Gwaggo, insha
Allahu za ki zama mai alfahari da ni...haba dai
Amir nifa na san zaka iya na san zaka yi adalci
sam bana da kwakwaton hakan. To Gwaggo,
Allah ya bani ikon rikewa. Amin ta amsa da
sauri, ji nayi ta kwala min kira ban so Gwaggo ta
kira ni yana gidan nan ba, na dai tashi na fito
sanye da hijab a jiki na, nayi kamar sallah nayi
da yake sallah azahar ya yi sallah, za kiyi? Ta tambaye ni zan dai yi ne, kafin nan don Allah
kawo ma wannan katon tazurun abinci, ta yi
maganar cike da wasa na kama hanya naji yayi
dariya, har da taba hannunsa biyu, kai Gwaggo
lokaci ne bai yi ba amma zan yi ai, haba Amir
shekarunka nawa yanzu, amma ace aure dai kа
ki shi, ka tuna fa girma ka ke yi ba wai ragewa
ka ke yi ba, a kullum shekarunka karuwa su ke
yi ina mamakin rashin auren ka, shiru ya yi
kamar baya gun. Na hadu abincin na ajiye a
gabansa ba tare da na dube shi ba, da ina ji a
jikina kallona yake yi sai dai na yi iya kokari na
ban bari muka kara hada ido ba, da na wuce
zuwa daki na ji yana ce mata, Gwaggo zan yi
aure insha Allahu, nan ba dadewa ba.
To Allah sa, daga nan na shige cikin daki na
rufe na shiga toilet don in yi alwala bayan na
idar da sallah na fito falon don da alama ya tafi.
Gwaggo na zaune akan sallaya, tana tahiya, na
113
Bakı Biyu Ω Sameera Mustapha:
samu guri na zauna, ban yi minti uku da
zamanba Asabe mai aiki ta shigo falon wai nayi
bako, abun ya bani mamaki saboda ni nasan ban
ba wani appointment ba, to waye wannan? Na
san ina da manema sosai don tunda na fita idda
na fara samun masoya sai dai bana kula kowa ba
dai Amir ba ne, wallahi in shi ne sai na bata
masa don na lura shi mutumin banza.....ba za ki
tashi ki ga mai kiran naki ba ne? na bata fuskata
tare da zunburo bakina irin na shagwaba, kai
Gwaggo ni fa ban ba kowa A.P ba, dama na ce
an baki ne kin gan ki ko to zan bata maki rai,
haka za ki zauna ba aure? Ki kiyaye ni kin ji ko,
tun watan jiya Baban Nafisa ya fara min zancen
ki, Suwaiba tana gidan miji wata hudu da suka
wuce, amma ke kin yi mirsisi baki ko sauraren
kowa, na san abunda ki ke bugun gaba dashi wai
ke yanzu ba wanda zai matsa miki kinyi auren
farko to za ki sha mamaki, don kin san kina
karkashin iyaye ne dole ne ki amince da
furucinsu. Ba za ki kama hanya ki wuce ba? Na
kama hanya in buga kafata irin na shagwaba.
Da na isa waje mota ce har mota Jeep na iske,
na tsaya daga bakin kofa sai ka ce mai tsoron
motar bude kofar motar aka yi aka fito wa zan
gani! Sa'idu ne tsohon saurayina, wanda ko
shekara dari muka yi ba mu hadu ba, zan gane
shi, don ko ban ce shi ne first love dina ba, to
114
Baki Biyu 2 Sameera Mustapha:
shima nayi sonsa, kuri na yi masa kamar zan
cinye shi, sai kuma na kama kaina na yi kamar
ban ji mamaki kafin ya iso har na fan jingina da
bangon wurin ya isowa ya yi sallama na amsa
cike da son sanin abinda ya kawo shi, shima ya
lura da hakan sai ya sha jinin jikinsa, ya ce
Dayyaba ina wuni? Na amsa, lafiya, ya muka ji
da hakuri? Mun gode Allah, na fada kaina a
kasa, ya yi shiru kafin ya ce, to-za a bani gun
zama ba ne Dayyaba, sai da na sake duban sa daga kasa har saman sa sannan na kauda fuskata
ina duban inda fararen kujeru suke na ce, bismillah.
Bayan mun zauna ne ya ce, ashe maigidan ki
Allah ya yi masa cikawa, wallahi tuntuni na so in
zo in yi miki ta'aziya amma na kasa, saboda
laifin da nayi miki, ina bakin cikin hakan kuma a
kullum na tuna, sanadin haka bana samun
isashen baci bana da kuzari, ina ta neman hanyar
da zan zo in nemi gafarar ki Dayyiba, ni na san
ban kyauta ba na ci amanar ki don na san ko ni
aka yi ma ba zan ji dadi ba, don haka nake
neman gafarar ki Dayyiba don Allah ki yafe
min."
A take naji jikina ya yi sanyi na tuno irin
yanayin da na shiga lokacin da...ya katse min
tunani na na dan dube shi na ce, ai ya wuce na
kuma daďe da yafe maka don Rahma ta zo nan
115
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
bayan kun rabu to tun a lokacin kaima na yafe
maka don na gano dama kai din nan ba mijin
aure na ba ne, ya za ki ce haka Dayyiba ai kuwa
ni mijin auren ki ne, saboda ni a shirye nake in
aure ki, murmushi na saki wanda yasa hakura na
suka bai yana, ni dai na ce maka na yafe maka
amma a gaskiya babu aure tsakaninmu sai dai
mutunci to ki bani izini mana in rika zuwa muna
gaisawa, shiru na yi ina tunani, ban ma san
abunda zance maka ba Sa'id, ni da zaka gane da
mun hakura da duk wata hulda da zai hada mu,
sai dai in mun hadu nayi maka alkawarin ko a
ina ne zan tsaya mu gaisa.
Saboda Allah Dayyiba na ke rokon ki ba don
halina ba, a gaskiya Sa'id ya daure ni ban san
dalili ba sai tausayin sa nake ji, ba dai har yanzu
ina son saba nasan shima nayi son sa a da,
daurewa dai nayi na ce to shi kenan babu laifi
kana iya zuwa. Mun sha hira kuwa dashi kamar
ba zamu rabu ba, sai da karfe shi da saura ya tafi,
na shigo cikin gida fuska ta a sake, har na manta
ranar da na saki jiki nayi hira ta nishadi, Gwaggo
na iske a tsaye da alamar ni take jira.
"Waye ya zo gun ki?" Ta yi tambayar
fuskarta babu annuri. Jikina a sanyaye na ce,
"Bakon da ya tafi?" "Eh, ai kin san dai tambayar
kenan." Uhm, Sa..i...d ne, Sa'id! Sa'id!! Sa'id fa
ki ka ce? Baki da hankali yarinyar nan, dama da
116
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Sa'id ki ke hirar ta kusan awa uku? Gwaggo
gaisuwa yazo ya yi min, Eh, gaisuwa...wallahi
abunda ya kawo shi kenan, ke dai ki ka sani ni
abunda zan fada maki shine, kada ki bashi fuska
har ya nemi shige miki, don na lura baki da wayau
ke sakarai ce, duk irin wulakancin da ya yi maki a
baya kin manta da ya hankali bai ishe ki ba, to in
ma gaisuwar ce ayi bata wuce minti goma zuwa
sha biyar, to ban yadda da hakan bà ki canza
tunani, don in ki ka yadda da yaudararen yaron
nan to ba a gidan nan ba sai dai ko can inda ba nan
ba." Bata tsaya taji abinda zan ce ba, ta wuce
dakin ta, a nan na zauna ina hawayen tashin
hankali ya zanyi da rayuwata. Komai nasa a gaba
sai raina ya baci, shi yasa nake cewa ba zan yi aure
ba, don ina ji a jikina aure ba zai taba kwantar da
hankalina ba.
Bayan sati daya da zuwan Sa'id, ya zo har na
kwana biyar amma haka zan ki fita bana sanin
halin da yake shiga. Sam Gwaggo ta ki ta damu da
al'amarina sai na yi ta fushi abincin ma sai in wuni
ban ci ba, ita kuwa tasa min ido.
Ranar Juma'a bayan Sallar Juma'a ne Baba ya
zo daga Gusau, haka muka tarye shi, muna zaune a
falo bayan sallar Isha'i Gwaggo ta ce, Baban
Nafisa dalilin kiranka shi ne, don in fada maka
Dayyiba ta fidda miji sai ayi abunda ya kamata,
shi yasa na fi so ma ayi komai kana zuwa, gabana
117
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
faduwa yake yi kamar zai fadi don ban taba sanin
Gwaggo ta shirya hakan ba, ta ci gaba.
"Sa'id take so, don haka gata nan sai ka yi
magana da ita a san lokacin da zai zo gaisuwa ya
san mu mu ma musan shi."
Ya dube ni ya soma sa min albarka, dama
Dayyiba wallahi na damu kwarai da rashin
aurenki, mamaki ya kama ni, Gwaggo ba ta fada
mishi tsakaninmu ba, ai ban san lokacin da hawaye
suka taru a idona ba, tausayin Gwaggo ne ya kama
ni, tabbas ni butulu ce, Baba ya tsinka min tunani
da ya ce, hala dan wane gari ne? na sunkuyar da
kaina kasa na ce, bakatsine ne. To ya yi kyau, ki
fada masa muna son ganinsa gobe."
Mikewa nayi a sanyaye na ce, to. Dakina na
wuce anya a rayuwata zan samu sukuni kuwa?
Gwaggo fushi take yi dani ya ya zan yi da kaina. A
ranar na kasa samun isasshen barci saboda bakin
cikin da ke tare dani, a gani na na yi wa Gwaggo
butulci.
Washegari bayan na idar da sallah, na yi saurin
isa dakin Gwaggo, na same ta kan sallaya tana
karatun Alkur'ani mai girma, Suratul Yasin take
karantawa a hankali da alama kuma tana cikin
nishadi, tabbas Gwaggo tana bani sha'awa kwarai
da gaske, tana da Ibada sam bata wasa gun addu'a da
karatun littattafan addini, Allah ya bamu daushenta,
don dai a gaskiya in ka samu rayuwa irin ta Gwaggo,
to ina son ranka gama da duniya lafiya.
118
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Zama nayi dirshan a gefenta akan tayals ina
sauraren ta, sai