abinda
zan biya ku dashi ba sai addu'a, amma wani
hanzari ba gudu ba, ina so a tambayi Tahir ko
yana sonta..." Gwaggo ta katse shi kada ka
damu Baban Nafi'u, Tahir da ne mai biyayya
yana da karamci ga sanin darajar iyayensa, shi ya
bani zabi ni kuma nayi tunanin hada shi da 'yar
kanwata mu dai hadin kan ka muke so.
Nima wallahi ban da matsala, na bada hadin
kai fari-bisa-dari, Allah yasa a dace, a kuma yi a
sa'a, gaba ki daya aka amsa (amin).
17
Saki Biyu. Θ Sameera Mustapha:
Tahir tunda ya bar garin Gusau Lagos ya
wuce ya rasa gane kansa, wani irin nishadi da
farin ciki ke shigarsa, da alama ya fara son
Dayiba to why her, ya tambayi kansa, ya yi
soyayya sau da yawa a rayuwarsa, tunda ta rasu
jin dadinsa ya kare, to amma a wannan lokacin
farin cikinsa na so ya dawo, menene amfanin
mutum na da kudi amma ba ya da wadda ke
bashi farin ciki? Duk kudin ka idan ba ka da
wadda zata maida maka martanin so to gaskiya
kana da babban gibi a rayuwarka yana ji a
jikinsa lallai Gwaggo ta yi masa zabe daidai da
shi, tuni duk bakin cikinsa da raunin da yake
fuskanta ya kau, sai farin ciki a tare da shi. Nan
da nan ya soma maida kamanninsa cikin
Kankanin lokaci.
Tunda Mama da Suwaiba suka bar falon nan
suke tunanin shirin da ya dace ayi don kada
wannan aure ayi shi, hankalin Mama ya gama
tashi, baki daya ta tsani iyalan Mal. Sabi'u shi
kađai ne asirinta bai ci akan sa ba, duk da wani
lokacin zata ga kamar ya yi sai kuma daga baya
ya barkace, don haka ta yanke shawarar zuwa
gun Boka Jilli da bata da wanda ya fishi duk a
cikin bokayenta, ita ta rasa dalilin da yasa Mal.
Sabi'u yake son shiga harkar ta, don me ne zai
hada jininta da zuri'arsa, shi ne abu na karshe da
tayi tunani akansa, gashi tunda maiyar nan (haj
18
Baki Biyu 2 Sameera Mustapha:
Hauwa kenan) ta sa baki tasan kamar anyi an
gama. To amma ba za ta yarda hakan ta faru ba,
don sam layin Tahir ya fi karfin na Dayyiba, su
da ke matsiyata mene za a ci da su, kananan
mutane ai sai irin su idan ana maganar manya
kuma manyan ne dai dai da kansu amma zata yi
maganin su.
Bayan kwana uku, jira take yi taga ko Tahir
zai shigo amma shiru, abun ya kara kona mata
rai, wai me Tahir ya maida ita ne, bai taba nuna
kishinta, kuma a matsayinta, ta mahaifiyarsa duk
a cikin 'ya'yanta shi ne zakka a gare ta, shi kadai
ne bata iya juyawa. Ta yi ajiyar zuciya da ta tuna
wansa Idris shi baya iya aiwatar da komai sai ta
ce ayi, duk abinda zai yi sai ya sanar da ita gashi
da gudun zuciyar ta wani lokacin da gangan take
takura masa, sai Amir shi a daya so ya fi karfin
ta saboda shaye-shaye da yake yi, amma daga
baya kamar an yi ruwa an dauke shima juya shi
take yi, har gara Amina bata cika sa ta cikin jerin
'ya'yanta ba, don ma tausayi take bata, karamin
yaro ta aura da bai da komai don haka me zata ci
da shi su je can su karata, dan autanta ne ma ya
biyo ta sak shi yasa take ji dashi. Duk wani asiri
da za'a binne a wuri da koma karbowa shi ke yi,
babu abinda bai sani ba a game da ita, dukkan
Malamanta ya san su.
19
Saki Siyu e Sameera Mustapha:
To me yasa Tahir shi daban ne, komai ta
shirya a kansa sai ya lalace, ku duba ku ga dai
duk aikin da aka yi akan aurensa da Suwaiba, ba
Karamin kudi suka kashe ba, amma abun ya ki
dadi a son ranta Suwaiba ta mallake shi ko ba
komai ta raba shi da Haj. Hauwa, amma abun ya
gagara, a kullum ma soyayyarsu karuwa take yi.
Amma ba komai, zata shawo kan Tahir zata yi
duk abun da ya dace, ko menene shi zata yi har
sai ta cimma burinta.
Boka Jilli da ta maida shi tamkar
mahaliccinta nan zata dole ne ya yi wani abu da
zai hana ayi auren nan, dole ne a fasa shi za su yi
shiri ne sosai.
Suwaiba kuwa ta fitini kanta da kuma tayar
da hankalinta sosai, ita ya zata yi ne? Ba ta taba
tunanin zata hada namiji da wata ba, dole ne tasa
Mama gaba ta hana wannan aure dama gata da
shegen kwadayi, tun lokacin da suka yi aure tasa
ta ta bude mata account duk dukiyar nan da
mijinta yake da shi bata gode ba, babu abinda ya
fi daure mata kai idan ka ganta kamar ba ta rike
kudin, a kulluyumin tana nan kamar bata cikin
hayyacinta, to zata cika ta da kudin don dama
Tahir ba ya rabuwa da sa mata kudi a account
din ta ko da ba su shiri, da zuciyar ta ta tuno
mata da Jessica kuwa, wani irin dogon tsaki taja,
ita ta ja mata duk wata masifa da take ciki, yanzu
20
Baki Biyu 2 Sameera Mustapha:
ta gaji ma da daukar nauyin ta kurar ta zata yi,
ita fa yanzu Tahir take so, ba za ta iya rabuwa da
shi ba, zama da shi yanzu ta fara, don haka zata
yi komai akan ta same shi. Ta kudiri niyar raba
shi da yarinyar da aka bashi ko ta halin ka-ka.
Karo suka ci a kofar falo ita da Mama, yauwa
dama ke nake nema, ina ki ka shiga ne? mama ta
fada tana dubanta. Nima ai ke nake nema Mama,
ina so ki dauki mataki akan auren Tahir, ki sani
fa ni ba zan zayna da kishiya ba, don ban ga ke
da Mummy kůna da ita ba (kishiyar), don haka
nima ba zan zauna da kishiyar ba, haba kwantar
da hankalinki, ki ke dai je ki shirya muje gun
Jilli, komai zai canza kada ki damu, buzut ta
mike ai ni a shirye nake babu wani shiri da
zanyi, Mama ta dube ta daga samanta har kasa,
night gown ce da ta kwana uku a jikinta bata cire
ba, anya ma ta yi wanka? Ta tambayi kanta,
sannan ta ce, ina nufin kije kiyi wanka..." ta
katse ta cike da fushi, ni ba zan yi wanka ba ki
tashi mu tafi bana son yin wankan ai ba dole ba
ne wanka ni fa abunda ya zama dole gare ni shi
ne warware auren nan da wannan munafukan
suka kulla. Mama ta lura yarinyar ta fita hayyacinta sam bata tare da jikinta, dole ta kyale
ta. wani dan Raramin gyale ta saka akai suka
wuce.
21
Bakı Siyu Sameera Mustapha:
Boka Jalli sai da ya saurari abunda suka zo da
shi ita Suwaibar cewa ma ta yi a nakasa Dayiba,
ko ma a kashe ta kawai kowa ma ya huta, Bokan
ya yi dariya tabbas mu masu iya kisa ne amma ki
bari mu nuna musu, irin mu mu nuna musu
wulakanci a rayuwarsu, yana magana yana
kyalkyatar dariya sai kuma ya bar dariyar ya
bata fuskasa, ya cę, wani hanzari ba gudu ba, an
nuna min akwai auren nan Tahir zai yi aure!
Kuma kema za ku zauna, sannan idan muka ce
zamu kashe ta to tare zaku mutu." Suwaiba ta
zaro ido tsoro ya shige ta, a'a a bar na kisan a dai
nakasa ta Boka, a nakasa ta.'
To sai dai wannan zamu nakasa ta zata zama
bata da wani amfani, ba a gun mijinta kadai ba
har da iyayenta sai sun gaji da lalurar ta, ta
washe baki tana taya Bokan dariyar da yake yi,
ke ya fada cike da daga murya, ya isa haka, а
tsorace ta kama kanta. Sai dai akwai wasu
sharuda da zan gindiya miki, dole ne ki bi shi
idan ba haka ba ba zai yiwu mu kama mijinki ba,
yana da karfi sosai saboda yana da ibada bai
hada komai da ibadarsa ba, don haka ina so ki
kula ki natsu in fada miki abinda za ki yi, ta yi
saurin gyara zamanta, ta ce ina jin ka Boka.
Tuni bakin Mama ya mutu, ta bar abun
tsakanin Suwaiba da Bokan don a gaskiya duk
rashin imaninta bata taba kawo tunanin ta yi kisa
22
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
ba, ta raba mutum da duniya ba, ashe komai ka
ke yi akwai wanda ya fika, don haka ta maida su
hoto ta kali Suwaiba ta kalli Boka suna ta
bayanin su tsakaninsu.
To ina son ki shirya zama na fahimta
tsakaninki da mijinki, ban gane ba, za ki gane ne,
ina nufin ki ba mijinki hadin kai kuyi zaman
lafiya, ki bi shi da duk abinda yake so ko ki ka
san zai sa, ku zama kusa da shi kiyi shi saboda
ya saki jiki da ke, don a yanzu din nan da nake
baki labari digon sonki ba ya tare da shi, ya nuna
mata wani dutse da ke gabansa an diga masa
paint baki wannan zuciyarsa ne, idan dutsen nan
bai koma ja ba to ina fada miki ke dinnan baki a
zuciyar sa baki daya. Ta fashe da kuka, na shiga
uku ni Suwaiba ya zanyi da raina? A'a bana son
kuka hadin kanki nake so idan kina son wannan
aikin ya yi, a dole ta sassauta kukan ta don a
tsawace yake mata magana. Muryarta na rawa ta
ce, ya ya zanyi boka me zan yi ya so ni? To ki
bude kunnuwanki da kyau ki saurara, ina son
idan kin koma gidansa, ki zama mai biyayya a
gare shi, ki zama mai son abunda yake so, idan
kika yi haka dole ne ya sauko, ya saki jiki da ke,
anan zan rika gani, don dutsennan da na nuna
miki zai rikida ya koma ja, idan ma baki yi ba to
ba zan gani, don idan dutsen nan bai koma ja
40
23
Bakı Biyu e Sameera Mustapha:
baki dayansa, aikin da zan yi maki ba zai yiwu
ba.
Da sauri ta ce, don wannan ai kadan ne, zan
bishi ko don bukata ta biya, ya yi kyau to ina so
ki bashi hadin kai dari-bisa-dari akan auren da
yake son yi, don na ga duhu a auren kila ma ba
za ta fi wata ba ta bar gidan, wai amma na ji
dadi, ai ban gama ba ya fada yana fitar da wasu
kullin magani sun kai ashirin, kala-kala kuwa.
Hajiya matso kusa kema ki ji ke kin san
ka'idojin aikina, idan aka kauce dole ne a sake
daga farki, eh gaskiya ne na sani.
A cikin kankanin lokaci ya zayyane masu
komai yadda za su yi amfani da shi, ita dai
Suwaiba saurare take yi, amma kila kwara uku ta
rike suma din don kalar ledar maganin daban ne.
Bayan an kwana biyu, Mama ta bugawa Tahir
ta ce tana son ganinsa, bai bata lokaci ba ya je
Gusau, ya yi mamakin irin tarbar da suka yi
masa su dukansu, Mama ba ba Suwaibar ba.
Haka aka yi masa girki kala-kala, duk da ya
bayyana mamakinsa a fili, ba su nuna masa wani
abu ba, Mama sai jan shi da hira take, yi can ta
ce ga abinci can da Suwaiba ta shirya masa, а
zuciyarsa ji ya yi ba zai iya cin abincin ba, duk
da yana jin yunwa ya mike kuwa ya je ya bude
kololin yana dubawa, sakwara ce da miya ugu
tasha egusi, sai farfesun kayan ciki da kuma
24
Baki Biyu Sameera Mustapha:
papper chicken sosai abincin ya shiga ranshi, sai
dai bai yadda da shi ba, don haka ya dauki ruwa
yana sha ya ce Mama gashi shigowa ta kuwa sai
da na ci abinci gun Hassan, amma babu damuwa
zan ci anjima ajiye min, kallon kallo suke yi da
Mama da Suwaiba, ya gani a fuskokinsu, basu ji
dadin hakan ba, sai ya share kawai ya ci gaba da
cewa, Suwaiba na maida aurenmu, tunda baki
wuce iddar da ke kanki ba, sai ki shirya mu wuce
tare, dadi ne menene? Itama ba ta sani ba ya
tsinka mata tunani da ya ce, bari in fita zan dawo
da daddare akwai wani member na house of reps,
da nake son gani, Mama ta ce haba dai ko
hutawa ba za ka yi ba? Mama dole ne mu je
neman na abinci, ko tayi mana addu'a kawai. To
shi kenan Allah ya tsare ya bada sa'a.
Tabdijam ya fada a ransa yau za ayi ruwa ya
shigo gari basu sa in sa da Mama ba, anya
wannan abu gaskiya ne? Ya tambayi kansa, to
zai bi su yadda suka shirya kansu, sun jira shi har
dare amma bai dawo ba, takaici kamar Mama ta
fashe, amma ya zata yi an ce dole ne su lallashe
shi ya saki jiki da su, sai wajajen karfe sha dayan
dare ya bugowa Suwaiba waya yana fada mata
meeting ne ya tsayar da su yanzu haka basu tashi
ba suna nan suna tayi don haka sai ta shirya gobe
su wuce, ta shagwabe masa kai Dolly tun da ka
shigo garin nan nake son ganin ko fa abincin da
25
Baki Bivu. e
Sameera Mustapha:
na yi wahalar yi ma ya zama a banza kenan, shi
ma sai ya biye mata ya ce, oh suith a ba wai da
gangan ba ne ki san fa dole mu nemi kudi
saboda ku, ta yi dariya na jin dadi, to shi kenan
Dolly babu komai Allah ya kai mu goben suka yi
sallama.
Lallai maganar Boka Jalli ya soma zama
gaskiya, to amma anya ita zata iya sharing din
namiji da wata kuwa? Gashi da alama gida daya
zamu zauna, duk dai da kanta take magana. Тo
shi kenan za'a gani ya zaman zai kasance don ta
san zafin kishi ta yana iya birkice komai.
Tare suka koma da Tahir sai da suka biya
Kaduna gun Gwaggo sannan suka wuce Abuja,
sai dai ba su sami Dayyiba gidan ba.
Washegari suna karyawa ta dube shi tana yi
masa barkwanci, ango, ango kasha mai, ya ce ke
kuma uwargida sarautar mata. Yo kai amaryar a
ina za ta zauna? Sai da ya hadiye dankalin da ke
bakinsa, sannan ya ce, a can side, ya nuna da
hannunsa. Ta dubi inda hannunsa ke nuni, gefen
shima kusan irin nata ne dakuna biyu da toilet a
ciki sai dressing rooт.
Ajiyar zuciya ta yi, to Allah ya sa muyi
zaman lafiya kai kuma ka kwatanta adalci
tsakaninmu, har a ransa ya ji dadin furucinta, sai
dai ba ya son ya nuna mata hakan don dai ya lura
wannan zaman da alama tana son suyi zaman
26
Baki Biyu Sameera Mustapha:
lafiya, ya yi gyaran murya da yasa ta dube shi
amma idanunta sun kankance don tsabar kishi,
ya gano hakan shi yasa ya ke son ya kwantar
mata da hankalinta, don haka ya rike hannunta
ya ce kada ki zarge ni wallahi nima ban taba sa
ran zan auri mata biyu ba, kaddara ce na sani kin
sani a baya muna zaune cikin kunci amma nayi
miki alkawari in har ki ka dage aka yi zaman
lafiya a gidannan, to za ki same ni mai sauki da
adalci insha Allahu."
Duk da hawayen da suka taru a idonta, haka
ta daure ta hadiye su ta na cewa, to Allah ya
baka ikon yi. Ta karasa cin abincin nata, shi dai
ya yi saurin barin gidan kada shirin da suka fara
ya barkacе.
Yana tafiya ta shige daki ta kwalla ihu tana
kuka tare da magiyar ta shiga uku anya zata iya
bada hadin kai kamar yadda Boka Jalli ya
bukata? A wannan ranar ta sha kuka, akan dole
ta hakura don ita kanta kukan ya ishe ta.
Wannan karon kam ta ga canji sosai a tare da
zaman su, ko dawowar da yake yi cikin dare ya
daina, a Masallacin da ke hade da gidansa ma
yake sallah magriba, ita ta san da zata daure a
zauna lafiya to da ba karamin dadi zata ji ba,
amma sam bata ma taba kawo batun hakuri a
zuciyarta ba, don ganin take yi an cuce ta, ita ba
zata iya ba zama da kishiya, tana ita din ce za ta
27
Baki Biyu Sameera Mustapha:
zauna da wata aba wai kishiya, tana hakuri ne
kawai don su cimma nasarar su. Babu ranar da
ba a barbada mishi magani cikin abincinsa,
kuskuranta daya bata tatance kwantancin da aka
ce ta zuba, sai dai ta auka, a ganinta idan an zuba
da yawa zai fi aiki da sauri kila ma ya ki auren.
Amma ba ta san tana 6ata shirin Boka Jalli ba
ne.
Tare suka hada lehe, babu abinda aka saya
guda daya, duka biyu ne yadda ya yi wa Amarya
haka ya yi wa uwargidansa, set biyu na akwati
ya yi masu, ta zabi nata har da mota ya canza
mata sannan baki daya ya canza yanayin gidan, a
kala falon gidan ya kai guda uku, sai dakin shi
da yake dauke da waiting room sannan kuma a
ciki akwai dressin room.
Shi dai Tahir bai taba zuwa tadi ba, a
tunaninsa sai Gwaggo ta ba shi izini, amma ya ji
shiru. Tun da aka bashi mata yake jiran ya ji anyi
masa iso don su gana da Amaryar tasa. Ana
saura sati uku daurin aure ya je Kaduna, amma
bai samu ganin Dayyiba ba, daga gidan Gwaggo
sai ya wuce gidan abokinsa, ya tarar ma Badiya
ba lafiya, amma taji sauki. Bayan sun gaisa yake
bata labarin abunda ya kawo shi Kaduna, ko tana
da masaniya akan abunda ke faruwa ko yarinyar
(Dayyiba) bata sonsa ne?
28
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Ita dai Badiya ta san Dayyiba ba karamin
dace tayi ba, gashi sam ta ki ta kwantar da
hankalinta duk ta lalace ta fita hayyacinta..." Ya
katse mata tunaninta, Mamana wai me ke faruwa
ne? Ya za'a bari ya hadu da matar ba, ballantana
su gana, shiru ta kara yi don bata san abunda
zata fada masa ba, ta ma rasa ta inda zata fara,
sai ta wayance tayi fara'a, ta ce kai kuma mene
ne na sauri, hala ba ka santa ba ne?
"kin san Allah zan iya cewa ban san ta din ba,
don ina ga sau biyu na taba ganinta a gidan
Gwaggo, shima din ba kallon kurilla nake mata
ba, don na lura bata son in yi mata magana." Ta
yi dariya ta ce, kai Tahir baka da dama. To kila
Gwaggon taka ita tasan dalilin rashin baku
damar zantawa da juna, don haka sai ka same ta
don kun fi kusa, ai nayi kusan aikatawa, ke dai
Mama next zuwa da zan yi dole ne in ganta, kin
san fa tunda Gwaggo ta kulla wannan al'amari
sai na ji dadinsa, na samu kwanciyar hankali,
gani nake yi duk matsalata ta kau, na samu
natsuwa kuma da Dayyibar, wani irin bala'in
tausayi Tahir ya ba Badiya, in ya san irin tashin
hankalin da ake yi da ita akan auren sa da ya
tsinka mata tunanin da take yi, Mamana bari in
wuce sai na kara shigowa,Allah kara sauki. Ta
mike ta raka shi.
29
Saki Biyu e Sameera Mustapha:
**
Ina school mun gama jarabawar ranar muna
tare da Amina, sam bana sha'awar komwa gida
don a ranar aka ce Tahir zai zo gidan, sai na bi
Amina gidanta. Ina zaune a falonta nayi shiru
ashe Amina tana ta yi min zance ni kuwa ban san
ma tana yi ba, don na yi nisa a tunani. Ta zauna
gab da ni ta ce, "habna 'yar uwa, ki sani aure fa
ba mutuwa ba ce, ki sassauta ma kanki mana,
kada fa wani ciwo ya kama ki, na ce dama na
mutu Amina da na huta, wallahi bana son sa
bana kaunarsa, gashi bana son in ki yi wa
Gwaggo biyayya, na daukar wa kaina alkawarin
ba zan taba kin abunda ta nuna sha'awar in yi
ba, hawaye ne duk ya bata min fuskata, ya ya
zan yi da rayuwata? Na tsani family din su baki
dayan su. To ai ke Dayyiba ba ki so ne ki gane,
don Allah ya halicce shi a gidan ba shi zai sa ya
zama daya da su ba, ba fa mahaifiyarsa ta rene
shi ba, ni kuwa ina kyautata zaton shi halinsa
daban ne, idan shi halinsa daban ne da na
familinsa to ki sani shima ai namiji ne ni fa babu
abunda bana so a rayuwata, irin namiji na tsane
su, basu da amana, mayaudara ne in ban da burin
su su maida mata bayin su ba su da komai a akan
ta, don haka ne a kullum nake kara nisanta kaina
daga gare su.
30
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Amina sosai ta zauna ta ce, "haba Dayyiba,
ana baki kina roko, ki sani sa duk wannan hali na
maza da ki ka zayyana duka mata ma na dashi, a
karshe ma in fada miki mace ita shaidan ce, duk
da ba a taru an zama daya ba dole shaidancin
wata ya fi na wata. Tabbas maza a yau sun zama
abunda suka zama, amma ki sani mata ma hakan
suke shi yasa a gun Allah zunubanmu daya ne, a
kan aiyukan mu, shi Allah bai bambanta ba,
dukanmu bayinsa ne babu wanda ya fi wani face
wanda ya fi tsoronsa, abunda nake nufi anan shi
ne, kiyi wannan aure saboda Allah kiyi auren
nan saboda bauta masa da biyayya a gare shi,
tunda shi ya umarce mu da muyi aure mu raya
Sunnar Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi. Bari in dan baki labari, ko in
ce tarihi akan wani lokaci da Annabinmu
(S.A.W) yana zaune shi da taron mata a ciki har
da Nana Aisha (Allah ya kara yarda da ita) kin
gane taron an yi shi ne musamman dan a fadi
halayar maza ma'aurata wato ina nufin
zamantakewar da mata ke yi da mazajen su, kin
san duk watà damuwa da mata ke ciki a wannan
lokacin tare da mazajen su suka zayyana? Amma
to make the story short, ta mike ta bude dorowar
da take ajiye "disc" din ta ta zaro guda biyu ta
kawo min ta ce, gasu ina so don Allah idan kin
samu dama ki saurari wadannan "CD disc din
31
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
ki ji abinda ya kunsa, na karba ina kallon
rubutun da aka yi wa'azin marigayi Sheikh
Ja'afar Mahmud Adam ne, zaбаbбun loссосі
bakwai akan aure da tarbiyya (1) Mata a
Alkur'ani mai girma (2) Siffar mace mumina (3)
wacece mijinta yafi? (4) Bita-zai-zai (5) Tarbiyar
yara a Musulunci (6) Hakkin 'ya'ya a kan
iyayensu.
Ta ci gaba, "Ba ke kadai ba ya kamata duk
wadda ta ji sanarwar nan ta nemi kaset ko disc
itama ta saurara ta ji ma kunnanta abinda ya
Kunsa.
Ke kin san mace kuwa Dayyiba? Ina so ki
sauko ki lura, wallahi mu ma mayaudara ne, mu
ma muna son mu maida namiji bawa in dan mun
samu dama, sannan mu ma ai maciya amana ne,
na dakatar da ita na ce, na sani mu ma muna da
namu amma maza sun fi, him bari in fada miki
wallahi kowa kansa ya sani, amma in an zo fadin
gaskiya a fade ta, bari kiji wani dan misali,
akwai wani mutum mai arziki yana da dukiya
sosai, bai cika zama ba yana da mata uku,
kowace yana tafiya da ita wata shidda-shidda
kamar yadda suke tsarawa, matarsa ta biyu ita се
shaidan a gidan, don ita za a ce kamar yafi
dasawa da ita, saboda barikancinta ne oho! Tana
fita zina sannan ya dauki dansa na fari ya bata
amanarsa, taje tana kwana da yaron suna aikata
32
Baki Biyu Sameera Mustapha:
aikin assha! A uzubillahi mina shaidanin rajin,
na yi saurin fada, ta ce eh kwarai haka ya faru, don Allah mi za ki kira wannan cin amana ce yaudara ce shin me za ki kira wannan labari da
na baki?
Ajiyar zuciya nayi, labarin ya sa jikina ya yi sanyi, lallai ana abubuwa a duniya, Allah shi kadai yasan irin zunuban da muke daukar wa
kanmu, Allah ya shirye mu, Allah ya shirye mu
abunda nake iya fada kenan, ban iya cewa komai
ba ta ci gaba don Allah 'yar uwa ki kwantar da
hankalinki guda daya ki karbi kowacce kadara
ce ta zo maki, na turo baki ni fa Amina bana son
wannan mutumin ne, ta mike cike da jin haushi,
to kada Allah yasa ki so shi, na gaji da baki
shawarar....haba kawata, wallahi na yadda da
duk abunda ki ka fada, ni dai kawai bai min ba
me yasa ba za su bani dama ba, in zabi wanda
nake so? shiru tayi ba ta ce min komai ba, na san
takaici ne ya ishe ta, na san hakan, haka muke da
Gwaggo ma a kullum har ta gaji tasa min ido, sai
dai in in ta koke-koke na amma bata ce min kala.
Nayi saurin canza hirar, Anty Amina ina
Abdulkadir din ki da sauki ko? Yau na zama
Anty, to tunda na fada miki gaskiya, a'ah
wallahi ba haka ba ne na dai ji an gidan ku haka
suke kiranki, ke dai ki ka sani, Abdulkadir kuwa
a gaskiya da sauki, ban dai san waje ba, kin san
33
Saki Biyu Sameera Mustapha:
fa shi gyara a hankali yake shiga, a gaskiya
saukin da na gani shine irin daren da yake yi a da
ya daina, don yanzu haka anan abincinsa yake da
Krafe goma tayi zai shigo ya ci muyi hira, sannan
nayi masa tambaya akan shaye-shaye ya yi min
rantsuwa ba shi ne da shaye-shayen ba Dahiru ne
dan yar mahaifiyarsa, lokacin da ya yi hutu a
gidanne yake sha, dalilin barin gidan ma kenan
da ya gano ya yi masa magana ya yi fushi ya tafi
abunsa.
To Allah ya shirya, na mike tsaye ina dubedube, ta kalle ni ba dai tafiya ba? Tafiya kuwa
zan yi don na san wannan mutumin ya tafi, na
fada ina kallon agogo, kin ga har karfe shida
tayi, sai Allah ya kaimu gobe, hum ke fa saura
mana papper uku next week, zamu gama ke dai
bari yadda ki ka san ana jan kwanakin sai sauri
suke yi ban san me yasa ba, kenan dai nan da sati
biyu za'a fara biki gashi kin ki fitar da anko,
mits nayi tsaki na ce, ke da Allah rabu da ni
ankon me? Zan fitar sai ka ce dama auren so zan
yi, ke fa ki ka dauka aure zan yi, amma ni a guna
da auren da babu duk daya.
Amina kallona take yi bata ma san abunda
zata ce ba, Allah ya ganar da ke amma kin fi
karfina. Da sauri na bar gidan naje gida amma
abun mamaki gidan namu akwai baki, motoci ne
har