Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 8
irin rayuwar da suka daukar wa kansu suna burge ta, ina ma ace itama zuciyarta ta zama irin ta su. Idan ta koma gida tayi kwantacin abunda suke yi ita da kişhiyarta Dayiba, ita tasan ba wanda zai damu da dacewar ta don sam bata da kirki, kai a Nigeria bata da wanda take shiri da shi 'yan uwanta ma bata damu da su ba ko waya ba su yi, iyayenta ma sai suyi wata bata yi magana da su ba, haka zata zauna tana kuka tana tuna irin halayen ta na banza da tayi a baya. Cikin kwana ki nan bata da sukuni ko kadan a rayuwarta, in ta tuna da abun son ta kuwa Tahir sai ta kara bakin cikin halin da ta shiga, bata samun bacci da daddare saboda tunani da ya yi mata yawa. Da yake dakin amaryar aka ajiye ta saboda duk 'ya'yanta ba mai kwana gunta suna dakin uwargidan dama gefen Baban su dabanne, ita ta lura da yanayin halin da Suwaiba ke ciki, don haka a wannan daren da ta ji Suwaiban ta suma kuka shine ta matso kusa da ita ta dafa ta, Suwaiba tasan haka sai ya faru saboda bata iya 6oye damuwarta, ai sai ta saki kukan baki daya a daren kukan tausaya ma kanta tayi, ita kam belly bata iya cewa komai ba, itama hawaye ne ke zubar mata a ido, duk wanda ya kalli Suwaiba ya san tana cike da 85 Baki Biyu Samcera Mustapha: damuwa, to amma ya zata yi sai hakuri tana rungume da ita har sai da ta sassauta don kanta, sannan ta dago suna kallon juna, idonta dai bai daina fitar da kwalla ba, ta ce ki taimake ni don Allah Belly ta riko hannunta, ta ce zan taimaka daidai gwargwado, ki fada min abunda ke damun ki, ki sani ba zamu ta6a sanin abunda ki ke ji ba sai in ke ki ka fada mana, tunda ki ka zo gidan nan muke tambayar ki duk da ba laifinki ba ne da farko kina tare da firgita da har ba ki iya cewa komai, ki godewa Allah na ki yazo da sauki, saboda karfin halinki." Ta rike hannunta da karfi wanda yasa Suwaiba ta kalle ta, "ki fada min daga inda ki ke zamu taimaka maki insha Allahu, ki koma in da ki ka fito." Suwaiba ba ta san lokacin da ta soma bata labarin rayuwarta ba, tun tana karamar ta har lokacin da ta kai kanta mahalaka. Belly ta ce, "kada ki damu ke ki gode wa Allah, ya baki ikon ci gaba da rayuwarki, don haka ki shirya gyara kanki ki natsu ki roki Allah gafara, Allah maji rokon bayinsa ne, haka kuma Allah gafururrahimu ne, insha Allah zamu taimaka maki ni da 'yar uwata, kafin ki koma...." Ta katse ta "Ni ba zan koma ba, sai na ga abunda na zamar da rayuwa ta, ina son in san adinina don haka in zaku bani dama in zauna da ku in kowa to da kun kyauta min." 86 Baki Biyu Ο Sameera Mustapha: "Haba, ai mu abun farin ciki ne a gare mu, don haka Allah ki kwantar da hankalinki, insha Allahu gobe zan samu 'yar uwata in fada mata sannan mu fada wa maigidanmu. Tun da ta bace bata taba samun bacci irin na yau ba, har ta so ta makara. Haka aka yi kuwa, washegari Belly ta fada wa Binta abunda ake ciki, sosai tayi farin ciki da wannan abu ai ba su jira wani abu ba suka sami mijinsu da wannan zance, shima ya bada goyan baya dari bisa dari. Tun daga lokacin Suwaiba ta shiga Makarantar Mal. Attahiru, da kanshi yake koyar da ita suna karanta Alkur'ani mai girma a kullum, sai sauran littattafai irin su fikihu, sira, Hadisi, da dai sauransu. Aka raba kwanakin da za'a rika karantawa, ai cikin ikon Allah kuwa Suwaiba tana ganewa, da yake kun san an ce 'sa kai wanda ya fi bauta ciwo' in ji 'yan iya magana. Ta kuwa kwantar da hankalinta, duk wani aiki na gidan tare suke yi, hatta daka da bata taba ko taba tabarya a rayuwar ta ba, sai gashi a yau har ma da girki tana yi, ba ma akan murhu ba, a'a akan dutse da aka jera sannan ba da itace ake girkin ba, da kara ake yi. Kai rayuwa kenan, babu inda bata kai mutum, a rayuwar Suwaiba bata taba sanin akwai wahala a cikinta ba sai yau gata tsamotsamo a cikinta, Allah yasa mu dace, amin. A Nigeria kuwa, ni kam abun sai hamdala, 87 Baki Biyu Sameera Mustapha: gashi na kama karatu sosai, babu wasa a cikinta don muna shekarar karshe a yau sati na uku kcnan a Kaduna, amma ba mu yi magana da Tahir ba, sai dai kuma abun ya fara damuna, tabbas nasan Tahir yana da kwatancin halayen da Gwaggo ke fadi, to amma abunda ban gane ba shi ne, irin halayen da Anti Suwaiba ta fada min har yau ban ga ko daya daga cikin su daga gare shi ba, na tabbata idan wani namijin ne to ba yadda za'ayi yasa min idon yana kallona, a wannan zamani idan zan tuna yau kusan wata goma sha daya kenan da aurenmu sai dai babu abinda ya faru tsakaninmu, kuma sam bai taba nuna damuwarsa. To ai dama shima ba sona yake yi ba kamar yadda nima bana sonsa, don haka baya da laifi. To menene dalilin wannan aure da ba so a cikinsa saboda Allah! Su iyaye ba za su tsaya su kwantar da hankalinsu gu daya ba, su yi tunanin abunda ya dace da mutum ba, wani lokaci..." wayata ta tsinka min tunanina, da na duba number Tahir ce, a raina na ce, dan halak kamar yasan tunaninsa nake yi. Sai da tayi ta ringing kafin na dauka. "Hello!" Ya ce, "Assalamu alaikum." Na amsa masa, sannan na yi saurin fara gaida shi. "To ya karatun?" Na amsa a dakile. "Lafiya." "Ni ban gane ba Dayiba, anya kina da number wayata?" "A'a ban da shi." Na yi saurin ba shi amsa, ya dan yi shiru kadan ya ce, "Dayiba ni nasan na aure 88 Baki Biyu Sameera Mustapha: ki ne da zuciya daya, amma da alama ke har yanzu ba ki gano hakan ba." Shiru nayi ban ce komai ba, sai ya ci gaba. "A yau kusan watanni biyu bamu tare, amma ko ki bugo ki ji ya nake, ko gaisawa muka yi ai ba laifi ba ne ko, tun ina sa maki ido har na gaji shin me ki ke so in yi ne? Duk na ma rasa ta inda zan fara 'yar kanwar Gwaggo me ki ke so in yi miki ne? Ina daga miki kafa ne don bana śon in takura ki, ba na son in fiye son kai da yawa amma ke na lura ba ki ma gano hakan ba. Ina lura dake kayan lefe ma ba ki taba sawa ba to a nan na gano ba karamin kiyayya ce tsakanina da ke ba, shi yasa na yi kokarin kauda idona akan al'amuranki, sai dai ke ba abunda ya dame ki, saboda tsabar rashin son da ki ke min." Jikina ya yi sanyi da bayanin Tahir, tunda na daina son da namiji a rayuwata, wallahi ban taba tausaya masa ba sai yanzu, ni nasan ina yin abunda ba daidai ba, to amma ko na so in daure in hakura da kaddarar da ta same ni, sai in kasa. To menene abin yi? Tambayar da na jeho wa kaina kenan. Ya tsinka min tunanina da ya ce, "Hello! Kina jina kuwa?" Da sauri na amsa na ce, "Eh, ina jin ka me ki ke so in yi wanda zai ba ki ikon ki sauko muyi zaman aure tsakaninmu?" Hawaye ne ya taru a fuskata, amma ban yadda sun gangaro ba, na kasa cewa komai sai dai a raina ina tausayawa kaina, ina kuma tausayawa Tahir don a gaskiya duk da ban san shi sosai ba, yana da 89 Baki Biyu Sameera Mustapha: hakuri, a da na dauke shi daya da sauran maza, a gaskiya yanzu na gano ba kowa ke da halin wane ba, to me zan ce masa? Ban san lokacin da na motsa baki na ce "kayi hakuri ba, nima kaina abun ya bani mamaki, da alama shima abunda ya ji kenan, don da sauri na ji ya ce, "Babu komai ai hakuri ya zama dole, ko in dawo ne mu hadu?" "Ba aiki ka ke yi ba?" Na tambaye shi. "Gaskiya aiki ne sosai a tare da ni, nan Thailand, amma ban sani ba ko idan nasa aka yi maki visa za ki zo ba." Shiru nayi ina tunani, anya ayi haka? Ka daure dai har ka dawo nan kaga saura 'yan watanni in gama karatuna." "Haka ne, ai ni na ma manta da karatun Dayiba, wallahi bukatarki kawai nake yi." Murmushi na yi, na ce, "To ka bari in gama karatun sai ayi zaman da hujja." "To shi kenan, Allah ya nuna mana, sai dai ina יי son in nemi alfarma daya daga gare ki." "Ina saurarenka, Allah yasa zan iya." יי "Insha Allahu ma za ki iya, ai ba wahala." יי "To shi kenan, fadi abinda ka ke son." Sai da ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Don Allah ki rika bugo min waya muna gaisawa, ki sani ko muryarki na ji hankalina zai kwanta." "Ai kuwa insha Allahu zan fara, kada ka samu damuwa." Ya ci gaba da cewa, "To shi kenan, Allah yasa, kila ma in shigo nan da sati biyu masu 90 Baki Biyu zuwa insha Allahu." "To Allah ya yadda." Θ Sameera Mustapha: Nan dai muka yi sallama. Tabbas da alama Tahir daban ne a cikin 'ya'yan Hajiya Basira, kila ya dauki hali mai sauki irin na mahaifinsa ne, mahaifinsa yana da saukin kai sai dai ba za ka gane hakan ba sai idan kana kusa da shi, a da shima ina yi masa kallon irin Attajiran nan masu wulakanta Jama'a, ashe ba hakan ba ne ni na dauka haka, saboda tsabar Kuruciya. Na daukar wa kaina alkawarin zan rika buga masa kamar yadda ya bukata a kalla sau biyu a wuni. Haka din aka yi, ina buga masa wayar kuwa sau biyu a wuni, safe da yamma. Shi kuwa da rana da daddare tun bana sakewa muyi hira har na fara. Sai muyi kusan minti talatin muna hira da daddare duk da shi ne ke yawanci hirar kuma bai wuce hirar aikinsa, a gaskiya suna aiki, kai kama samu dadin dukiyar da ka tara wahala ce, a gaskiya rayuwar dan Adam baki daya wahala ce, kamar yadda Allah (S.W.T) ya fada, talaka bai huta ba, mai arzikin shima bai huta ba, a kowane sati zai sa a sa min kudi a account yanzu haka cewa nake yi ya bari haka nan har in kashe wadannan ya ki, ina ganin a jiya alarm dina ya shigo an turo min kudi a account da na duba sai naga ina da kusan million daya da rabi, na shiga uku ina zani da wannan kudi haka? Shin shi ba ya jin zafin su ne a rayuwata ta duniya ban taba tunanin zan rike kudi 91 Baki Biyu Sameera Mustapha: masu yawa irin wadannan ba, duk da kyautar da nake yi don a kowane sati dole ne in aikawa Baba a kalla dubu hamsin, Baba kuwa dubu talatin shima kansa Baba yana min gargadin in yi a hankali kada fa in zama irin matan nan masu daukar wa kansu in da ba su kai ba, nakan fada masa ba ni nake yi ba wallahi haka Tahir yake min ni bana ma sanin zai turo sai dai in ji alert kawai. Na tashi ina da kwadayin son kudi, amma wallahi yanzu tsoron kudin ma nake yi, don ban taba tunanin zan samu hakan ba. Allah kenan, babu abinda ba ya iya yi cikin lokaci kankani. Suwaiba kam an zama 'yan Daji, har da fulanci ta soma yi, duk da ya banbanta sosai da na nan kasar, gashi sallah, ibada baki daya ta dauka ta rungume abun gwanin sha'awa. Cikin watanni biyu da kusan rabi Suwaiba ta canza rayuwarta, ikon Allah, gashi a yau ta zama mace mai kamun kai, wadda tasan hakki da darajar addininta, tun tana kyamar abincin gidan har ta soma son abincin, gashi ta koya ta iya zama garin kamar dama da haka ta tashi, duk da tana tunanin gida a ranta haka ta daure tana ci gaba da zama so take yi ko izifi talatin ne ta kai kafin tayi tunanin tafiya, da yake tasa kai ta maida hankali sosai gashi nan har ta kai goma. Ni dai ina Makaranta ina zaune gidan amina da yake mijinta ba zama yake yi ba, kuma gidan da 92 Baki Biyu 2 Sameera Mustapha: dakuna sosai, sannan sashen sa daban nc. Gwaggo ta kira ni take bani labarin Suwaiba ta bace tun wata uku da suka wuce, hankalina ya tashi sosai don rabo na da ita kenan watanni kusan hudu kenan yanzu, ba shiri na wuce Abuja. Ai kuwa haka din ne Suwaiba bata gida maigadi ya ce tun da ta fita da daddare bata sake dawowa gida ba, abun da yasa bai yi magana ba shi ya zata da sanin maigidan, wayoyinta baki daya a kashe suke. Tahir shima sai da abun ya kai wata biyu shine ya soma damuwa da rashin sanin inda take, ya san halinta kowane irin tashin hankali su kai, bata wuce kwana uku zata neme shi, don bata iya gaba ba, to shi kuma da ya ji shiru shi a zatonsa ta amince da sharudan da ya zayyana mata ne akan ba za ta zauna ba shi yasa ma bai neme ta ba. Mama ce take ta neman wayanta, ita kuma ta zata fushi take yi da ita shi yasa bata nemanta a waya, don bata manta ranar da take mata fada akan natsuwa ta kashe mata waya shi yasa ta fita batun ta. Ana cikin haka ne Mama dai ta shirya ta je Abuja, yadda Suwaiba ta bar gidan haka ta iske shi a lokacin kuwa ana kusan wata biyu kenan da ta bar gidan. Yadda dakin yake a yamutse duk yawancin kayan alatun dakin a fashe suke ga shi dakin ya yi kura, shi ya tabbatar mata da Suwaiba bata gida, shi ne fa ta kira Tahir ya fada mata abunda ya sani ta yi mamaki da Suwaiba ta tsallake ta ta wuce 93 Baki Biyu Sameera Mustapha: gida mahaifanta, to fa Mama sai ta dauki zafi da 'yar uwarta, ita a cewarta ya za'ayi irin haka ta faru har yarinya ta tashi taje gida amma a kasa kiran ta a fada mata, shi ne da ta fito ta ke tambayar maigadi kwananta nawa rabonta da gidan? Ya ce, wata biyu kenan ita kuma sai kawai ta wuce Gusau ta yi banza da 'yar uwar tata, shi ne lokaci ya ta tafiya, Mama dai abun ya daure mata kai, ta kasa hakura ta buga wa mahaifiyar Suwaiba tana nuna fushinta akan abunda ke faruwa, Hajiyar Suwaiba ta ce, wa Suwaiba ai bata Lagos, rabon su da ita tun lokacin daurin auren Dayiba, haba dai Mama ta fada hankali a tashe, ka dai ki ce bata tare da ke? Humm, in dai Suwaiba ce waya ma sai taga dama muke yi, tabbas kwanan baya na neme ta waya shiru, har sau biyar duk da ba a lokaci daya ba da yake kin san halin ta da rigima zato na ko miskilancinta ne ya motsa don sai tayi wata ni ba mu yi magana ba, ba akan komai ba sai don ina mata fada akan irin rayuwar da ta daukar wa kanta. Mama na jin haka, ta sake neman Tahir ta fada masa abinda ake ciki, nan fa aka fara nemanta gidajen 'yan uwa da abokanta da aka santa tare da su. Abu kamar wasa, yau kusan sati biyu kenan shiru, sam mahaifanta ba su damu sosai ba, a cewar su kila ta gudu ta koma America ne in tai tsami ta dawo, Allah ya shirye ta. To akan haka ma aka bar shi kenan ta gudu ne 94 Baki Biyu Ο Sameera Mustapha: saboda anyi mata kishiya, wasu kuma su ce fadan da suka yi ne da Tahir yasa tayi fushi ta buya, don ta daga ma mutane hankali. Humm hali kenan da yake kowa yasan halin Suwaiba da fitina shi yasa kowa bai yi mamakin 6acewar ta ba, 'yan uwan ta ma sam basu damu ba, saboda dama sun san zata iya kwantacen abunda ya fi ma hakan, a gaskiya na yadda da ake cewa yanzu dabba ake kiyo ba mutum ba ne, shi yasa ma aka ce a lahira ana amfani da irin shaidar da aka yi ma mutum, Allah ya shirye mu yasa mu gama lafiya (ameen). Kwanana biyu a Abuja na koma Kaduna don kowa ma harkar gabansa kawai yake yi. Suwaiba fa? Tana nan a Cameroon rayuwa gaba ki daya ya juya, ita kanta tana mamakin kanta, ashe mutum na canza hali akan tashin hankali? Ita kam ta gani a kanta, iyayenta babu abunda ba su yi ba akan ta natsu ta zama mutuniyar kwarai amma ta ki gashi don kanta ta natsun dama ai Allah ne ke shiyarwa sai dai mu muyi kwatankwacin namu tarbiyan ga 'ya'yanmu, saboda shiryuwa na gurin Allah, Allah yasa mu dace (Amin). Gashi yanzu Suwaiba ta zama mutum, sallah bata wuce ta ga yawan nafilfili da kuma Istigifari ga Allah, haka cikin dare zata rika sallah tana addu'a tana kuka ita ta san tayi ba daidai ba a da, babu abinda take godiya ga Allah akai sai yanda ya nuna mata yadda rayuwa take 95 C Bakı Biyu e Sameera Mustapha: gashi a yau ta samu ta kuma dandani rashi ta kuma gano matsalar ta, kuma ta dauki aniyar ceto rayuwarta daga halaka. Allah ya ganar da wadanda ba su ganc ba (amin). Ya kara shiryar damu baki daya. Sai da Tahir ya sami kamar wata uku rabonsa da gida, ni kuma a lokacin na sami hutu, duk da ba wani hutu ba ne na sati daya ne, a ranar da muka yi hutun a ranar na koma Abuja, don Gwaggo ta turo mota ta ce in zo gida. Abun mamaki Tahir na nan, sai dai wai bai jin dadi, a gaskiya ya dan fada ashe wai tun a can baya da lafiya, karfin hali ne yasa ya zauna don ya karasa aikin da ya kai shi. Ulcer ce gare shi, sosai ta kama shi, a yanzu haka ko abinci baya iya ci sai dai abu ruwa-ruwa, ba karamin tausaya masa nake yi ba, ko magana bai cika yi ba, a dalilin haka ne nake cusa kaina a al'amuransa, gashi sam baya son zancen asibiti sai dai Doctor ya zo gida ya duba shi. Ina da kwana hudu a Abuja, ciwon Tahir ya tsananta, har sai da aka kwantar dashi National Hospital a nan Abuja. Abu ba na wasa ba ne, don ba a bari ma aje gunsa, ai tuni hankalin family ya tashi, mahaifansa da 'yan uwansa sai tururuwa ake yi ana duba shi, duk da ana hana ganin nasa. Ni kam abun ya soma bani tsoro, don da aka tambayi Doctor abinda ke damunsa cewa sukai jininsa ne ya hau sosai, ga kuma ulcer tayi masa yawa don gyambon har ya kai hanjinsa, suna so suyi masa 96 Baki Biyu Sameera Mustapha: aiki ne to amma kuma ba za su iya yin aikin ba har sai jininsa ya sauka. Jikina ya yi sanyi sosai, nan da nan kuma na rame don ina tunanin abunda nayi masa, yana matsayin mijina idan ya mutu bai yafe min ba ya zanyi in ban da rike hannuna da ya yi sau biyu bai taba ko runguma ta ba, na shiga uku, duk wanda ya kalle ni yasan ina tare da damuwa ba kadan ba, ko abinci ba na ci kwata-kwata, wallahi ba Karamin tausaya wa kaina nake yi ba, a wannan lokacin. Sai da ya kwana uku bai san inda yake ba kafin jininsa ya sauka aka shiga da shi tiyata. Na lura ciwonsa ya yi tsanani da yawa, saboda Doctors shidda ke kansa, ai ban san lokacin da na fara kuka ba, Gwaggo ce ta rike ni tana lallashina ta ce, ke ba a haka ai ba kuka za ki yi ba, kiyi masa addu'a, ji na yi Gwaggo ta bani tausayi don idan ta rasa Tahir nasan ba ni ce mai rashin ba ita ce. Mikewa na yi naje nayi alwala na soma sallah, nafila da yake karfe uku ne na rana. An dauki kusan awa uku suna tiyata kafin suka fito, Doctors sun nuna za'ayi nasara akan aikin da suka yi shi ne dalilin da yasa kowa hankalinsa ya dan kwanta kenan. Sai da muka yi sallah La'asar kafin ya farfado, zo kaga yadda kowa ya rika hamdala tuni asibiti ta cika da 'yan uwa da abokan arziki, na ga Mama tare da 'yar uwarta sun fita, sai dai ko kallo ban ishe ta ba, da na gaida ta ma ko kallon inda nake 97 Saki Biyu e Sameera Mustapha: bata yi ba, dama inda ba don Jama'ar da ke wurin ba ni me ruwana da ita. Bana son in yi rashin kunya ko rashin hankali shi yasa ban damu da abunda tayi min ba. A daren ranar Baba da Baba Mairo suka iso, Tahir har yana dan kokari ya yi magana. Tunda ya farfado ban samu ganinsa ba, saboda manyan mutane da ke dakin gashi na matsu in je gunsa in ga saukin da ake cewa ya' samu. Sai bayan magariba lokacin mazan sun tafi Masallaci nayi saurin kutsa kaina dakin, abun haushi bacci ya dauke shi, dole na hakura na fito ina lekensa ta glass din da ke kofan dakin, a raina na ji sanyi na kuma ga fuskarsa tayi min kyau kamar ba mai jin jiki ba. Daga inda nake ina kallon yadda fuskar tasa ke sheki tayi sumul-sumul, Allah ya baka lafiya na fada a fili, sai da na samu kusan minti ashirin a tsaye. Kafin na je don in yi sallah magariba, na rasa gane abunda zuciyata ke nufi ba dai na fara son Tahir ba? Na ji a cikin jikina akwai wani al'amari da yake son samuna akan Tahir, na furta a waje, Allah ya baka lafiya Tahir. Addu'a sosai nayi a wannan daren don har lokacin bai tashi ba yana barci. Washegari bayan munyi sallah Asuba, ni dai yanda naga dare haka naga safe, ni jira nake yi ya tashi in ganshi ko hankalina zai kwanta, ina zaune a gefan gadonsa na jingina tare da yin tagumi, 08 sunana ya kira a hankali da sauri na mikc ina kallon fuskarsa, tayi kyau sosai, murmushi ya saki wanda yasa na ji wani irin abu a jikina, ban san lokacin da na samu wuri gab dashi ba na zauna, ina yi masa sannu. Yana amsawa a hankali, ina tausaya masa sosai a raina ban san lokacin da hawaye ya soma zubo min ba, riko hannuna ya yi na dube shi, girgiza kansa yake yi a hankali. "Kada kiyi kuka, kiyi min addu'a, na dan yi shiru kafin na ce, kayi hakuri da abunda nayi maka ai sai na saki kukan baki daya, nasa kaina akan gefen hannunsa a kalla nayi kusan minti talatin a haka kafin na hakura na dago kaina. Shima fuskarsa cike da kwalla ya rike hannuna gam, kada kiyi kuka na yafe miki har a zuciyata. Ai tun daga lokacin na sami sanyi a zuciyata tare da daukar wa kaina alkawarin insha Allahu zan zama mai biyayya da bin dokar auren Tahir dake kaina, tausayinsa ya kama ni na rasa ta ina zan fara taimaka masa. Karfe takwas saura na safe Doctor ya shigo ya duba shi ya ce a fara bashi ruwan lipton da cokali, abun ba wuya, yanzu kam komai ya zo da sauki da da ne sai ya kwana uku amma gashi yanzu kwanansa daya har zai soma shan wani abu. Daga lokacin kuma 'yan uwa akai ta zuwa gaida shi, sai bayan azahar naje gida nayi wanka na saka doguwar riga baka cean yi mata kwalliya 99 Bakı Bıyu 2 Sameera Mustapha: da dutsina a wuyan rigar da kasan hannun, duk da fadawan da nayi rigar ta yi min kyau ba kuma komai na saka a fuskata ba. Fararen slipers na saka, dawo asibiti abun mamaki asibitin ya cika dam da mutane, ban kawo komai a raina ba, saboda tunda aka kwantar da Tahir mutane ke zuwa gaishe shi, sai dai na yau yafi samun mutane.......tunanina ne ya katse da na lura fuskokin kowa babu annuri, gabana bugawa yake yi kamar zai fito...daga gefe Gwaggo ce kwance Baba ce akanta, tana yi mata fitara meke faruwa ne? na tambayi kaina sannan gaba ki daya na tsinke na karasa gun su na tsuguna. Anti Badiya ce ta riko hannuna kuka take yi sam babu sassauci, can daga nesa Mama ce itama kukan take yi, 'ya'yanta kuma zagaye da ita. Ba dai Tahir ne ya rasu ba? Na fada hakan a raina kuma hawaye na zuban min kamar ruwa. Na rike hannunta nima na Anti meye ya faru? Ta ce tana dubana na ciwon Tahir ne ya tashi, kin fita kenan sai ya fara fizge-fizge sai da aka sama sa oxygen, na shiga uku na fada ina hawaye. Da kyar aka ciwo kan abunda ya taso ma Tahir, suma kan su Likitocin ba su yi tsamanin yana da rai ba, ba don nishinsa da yake fita daidai ba, sai da muka kwashe kusan awa uku kafin Likitocin suka fito daga dakin suka ce basa son a shiga ciki sai washegari. 100 Baki Biyu. Suwaiba a can Cameroon ta rasa abunda ke yi mata dadi, yau kusan kwana hudu kenan tana fama da faduwar gaba ga kuma mafarkin da take yi marasa kyau, duk hankalinta ya koma gida, ta so ta yi shekara a nan har ta sauke, a yanzu ba ta da buri da ya wuci ta sauke Alkur'ani mai girma, sai dai da alama ba za ta iya ba don duk ilahirin jikinta ya yi sanyi, yau ma haka ta wuni bata jin dadin jikinta. Ba wai ciwo take yi ba, a'a jikinta ne kawai yake a mace, tana tare da kasala. Da ta fita gun karatu, Mal. Attahiru ke ce mata anya lafiya ki ke Suwaiba? Ba ta 6ata lokaci ba ta fada masa abinda ke damunta, ya numfasa ya mike tsaye ya ce, ina zuwa. Dakinsa ya shiga ya rufe. Tana nan zaune na kusan minti sha biyar kafin ya fito ya zauna ya ce, Suwaiba ina so gobe ki shirya muje garinku, naga da abunda ke faruwa kuma abun ya shafe ki. A sanyaye ta yi masa godiya ta ce, "To Allah ya kai mu." Da ta isa

Chapter 6 of 8