akwatina ya dauko yana kwashen kayan yana zubawa. Me ka ke nufi ina Dayiban take? Tana
magana tana zare ido kamar irin tana magana da
danta. Banza ya yi da ita ya ci gaba da abinda yake yi, ta fusata ta isa gabansa ta hana shi ci gaba da aikin da ya sa kansa. Tana dubanshi cikin idonsa,
na ce ina take ina ka kaita? Wani irin bangaje ta ya yi sai da ta fadi ta buge kanta a bango 'kwal' tuni
kan ya kumbura, ta dake ta ki kuka duk da azabar
da ta ji. Ta kara matsowa kusa dashi sai dai bata shige masa ba, sai dai ya ci gaba da kwansan kaya
yana shirya su a akwatina, sai ta fara surutu, ni fa
ba zan yadda ba dole ne ka dawo da ita gidan nan,
so kake yi ka ci amanata, shi yasa ka dauke ta? To
ba zan yarda ba, ya dube ta da jajayen idonsa ya ce, kin ga ki fita hanyata Suwaiba, kada ranki ya baci, ke ki ka ajiyeta a gidan nan ko ni da za ki
rika yi min tambayar banza, to wallahi am warning
you, kar kiyi zaton ina shakkar fata maki rai ne,
ina kyale ki ne saboda darajar mahaifinki, if not
da tuni na san yadda na yi da ke but let me Inform
you, if am tired of your nonesense wallahi zan
kore ki daga gidana, don ba ki da amfani a guna,
baki da kunya Suwaiba, balle kuma tarbiya, wai ke
kina ganin kina da wayau da za ki maida ni sakarai
za ki san ni ba sakaran ba ne, wuri ki ka samu zan
69
Baki Bivu e Sameera Mustapha:
nuna miki nima 'A' ne, ba wai ina.....mits tsaki ya
ja, ban san ma me yasa nake bata lokaci na ina
magana da ke ba, just be careful daga yau daga ni
sai ke gidan nan, nayi kusan kaiwa bango da
iskancin da ki ke takama dashi, ki san igiyar
aurena biyu kacal ya rage kada ki sake ki bari in
baki su a cikin ruwan sanyi kin ji na fada miki,
yarinya ni na auro ta ba zaman ki take yi ba, don
haka kada ki sake min magana akan ta, I have the
right in yi abunda na ga dama da ita, babu ruwanki
da ita, ki fita hanyata in zaman aure za ki yi to, in
kuma ba za ki yi ba it should be over, I have no
regret kin gane ko?"
Duk maganar da yake yi harararsa take yi, tana
tabe baki tasan ranshi ya baci sosai, amma don
karfin hali da zai wuce ta yi saurin shan gabansa ta
yi jaking din rigarsa wai sai ya fada mata inda
Dayiba take, Suwaiba ki kiyaye ni I want to be
honest with you ki daina wannan zancen don
banga abinda ya shafe ki da ita ba, na barki nan
you can do what ever you want, na kuma raba
girki tunda na baki dama kun bani abuna zan rika
kasancewa da kowaccen ko kwana biyu-biyu that
all I concluded any kuestion? Ta fashe da kuka,
wallahi ni ban yarda ba so ka ke yi ka cuce ni shi
yasa ka raba mu naji ina son in cue kin sake min
rigata kada ranki ya 6aci, wai ke mai wayo ko
yaushe aka yi ki da zaki gwada da ni, sake min
riga na ce maki kin san halina ni mai dukan mata
70
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ne don haka sai in nuna miki gaskiya, ki ka fada
mata. Da taga da gaske yake yi ta sake shi, ta ce to
na ji ina nema hakki na yanzu daga gare ka, bai
san lokacin da dariya ta kuce masa ba, sosai yake
dariyar ta mugunta ya ce ban gane hakkin da ki ke
nufi ba, bayan kin ce kin yafe? Ba ki so. Don
Allah kar ki bani kunya mana, jiyan nan ki ka fadi
haka ko kin manta in tuna maki? Ta ce, ni wallahi
yau dole ne ka kusance ni saboda ka riga da ka
shirya hukuncin zama da mu haka, don haka daga
yau za'a fara, wannan ne baki isa ba sai dai in ki
bar gidan, nan cewa ki ka yi kin yafe don haka
nima na yafe don Allah matsa min ina da abun yi.
Ya wuce da akwati daya a hannunsa ya sa masu aiki suna kwasan sauran.
Suwaiba ta shiga cikin wani yanayi na tashin hankali, dakinta ta wuce ta kule kanta a ciki me ta
yi kenan sam bata bi abunda Jalli ya ce ta yi ba me
yasa ta manta da shirin su? Ta tambayi kanta ya ya
zata yi ta shiga uku duk abunda ta kafa ya rushe,
sannan kuma ina ya kai Dayiba? To ya za ta yi ta
bullowa wannan al'amari? Ta sake tambayar kanta,
waya ta dauka ta kira Mama, ita ma kanta ta fara
gajiya da matsalar surikar tata, yau a wahalce take
saurarenta, ta ce, Mama shi kenan na gama na bat
shirin da na fara, Mama na shiga uku na lalace, me
zan yi in gyara? Mama ki taimake ni, wai Suwaiba
ya za ayi bukatarki ta biya bayan ba ki ma kwantar
da hankalinki gu daya ba, dadina dake garaje, sai
71
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
da Jalli ya ce kiyi kokarin su duka su sake jiki da
ke, to gashi nan kin yi ma kanki, yarinyar 'yar
matsiyata ne, kin san Karamin mutum kuwa? Duk
yadda zata yi ta malake shi sai ta yi don ta gada
daga iyaycnta. Nima da kyar suka rabu dani, balle
ke da baki ma san ciwon kan.... katse wayar ta yi
bata son fada, ita zata ciwa mutunci? Suwaiba ta
jefar da wayar gefe tana takaicin dalilin da yasa
ma ta amince da Mama, ta' ma manta ita uwar
mijinta ce. Dama a ce mahaifiyarta ta halin su
daya da Mama da ta fi kowa samun yadda take so,
sam basu da kama da mahaifiyarta ko a fuska bale
hali, kana haifa mutum amma ban da hali, ta sani
mahaifiyarta mutum ce adila bata da hayaniya, to
ko shine dalilin da yasa ta zauna da mijinta lafiya?
Wayarta ta soma ringing a zatonta Mama ce, sai da
ta yi tsaki sannan ta dauka, ta duba Augustina ne
abokiyar ta ce da suka hadu a bar indan taje shan
giyar ta ita da Jessica, ita ta ma manta da su ai nan
kwadayinta ya motsa, ta dauki makulin mota ta
kunna wayar ta ce, Augustina kina ina? Ina bar ne
kwana biyu ban gan ki ba lafiya? Gani nan zuwa
kada ki tafi don Allah, ok, ina jiran ki.
Sun hadu suna nishadi da giyarsu, a haka ta
kwashe komai da ke damunta ta fada mata, hatta
muguntar da ta yi duk ta fada mata, Augustina ta
ce, to ai wannan ba makirci ba ne, abinda ya
kamata kawai mu nakasa ta kinga dole ne ya rabu
da ita. Ta kyalkyale da dariya nima tunanina
72
Baki Biyu 0 Sameera Mustapha:
kenan, bokan da nasa wannan aikin wasu sharadai
ya shirya min ni kuma kishi ya hana ni aikata
wannan sharuda nasa, ina fata wanda za ki kai ni
gunsa ba ya da sharuda? A'a baya da shi, ni mace
ce ma ba namiji ba. A ina take? Tana calaba, cross
river za ki iya zuwa? Sosai ma me zai hana ni
yaushe zamu je ni ko yau ne na shirya. Dama ai ni
na fi son irin aikin 'yan wajajen ku kamar a aza
wuka don haka da jirgi zamu ko? A'a da mota
zamu, ai ba wani nisa, haba dai bayan an ce konan
da Port Harcourt ana ten hours eh, ai ba ta nan take
ba, ke dai muje in za ki je a yau ma sai mu dawo
da yake ta buge take sai ta yadda da zancen
Augustina a can kasan ranta tana zargin hakan, to
amma ya zata yi tunda tana Bokatar aiki dole ne ta
yadda da hakan sun shiga mota suka kama hanya
gwagwala da sun yi tafiyar kusan minti sha biyar
sannan ta ce su tsaya, mota ce parke a gun, sai ta
ce su shiga wannan, ta dubi Augustina ta ce mu
koma wancan? Ta ce, eh su za su karasa da mu ta
fita tana waigen Augustina da ke kokarin shiga
gefen tuki, waigo wan da zata yi sai ta ji an saka
mata hankici a hancinta, ai bata kara sanin abunda
ke faruwa ba.
Da ta bude idonta ganinta ta yi cikin wani daki
mai tsawo, tana kan gado kwance ta mike da sauri
ai sai ta buge kanta da gadon sama, ta rike kanta
ba ita kaďai ba ce a dakin sun kai su goma sha
biyar, dalam, suma basu san inda suke ba, a
73
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
lokacin hankalinta ya tashi, tana kallc-kallen
dakin, ta dubi mutumin da ke kusa da ita ta cс, "А
ina nake? kallonta yake yi bai ce komai ba. Tuni ta
fashe da kuka ai sai aka bude dakin wani katon
mutum ne ya nufo ta, ta firgice don fuskarsa babu
Imani a cikinsa. Tun kafin ya iso gunta ta yi gum
ta tsuguna ta rufe bakinta da tafin hannunta tana
girgiza kanta, ya tsaya cak a kanta yana huci ya yi
mata magana amma a yare da bata ta ba ji ba, da
alama gargadı yake bata.
Shirun dole ta yi, ya kai hannunsa karkashin
gadon ya fito da kwano ya bata tare da budewa, ai
bata san lokacin da ta karfe tana ci ba, saboda
tsabagen yunwa. Lafiyayyen abinci ne har da
Juice, ta kwankwade sai a lokacin ta tuna abunda
ya faru karshe tsakaninta da Augustina.
To masu karatu wannan abu ya sami Suwaiba
yana iya faruwa ga duk mai irin halinta, wannan
labari da zan bada ya faru ne da gaske, matar take
nemar wa 'yar uwarta nakasa wannan ba ma
kishiya ba ce kawai adawa suke da junansu ta
nemi hallakar da ita sai abun ya koma kanta, za aji
irin hannun da ta fada za kuma aji yadda ta samu
kanta sai a biyo a sha labari.
**
Da Tahir ya dawo gidan bai damu yasan inda
Suwaibar, ta shiga ba dan dama ya gaji da problem
din ta bal ki ta ce ta tafi ba ai shi gaba ta kai shi.
74
Saki Biyu Bameer
sadakar sun fado hannun a zalimai masu yankan
kai labarin da take ji a waje a nesa yau gata ta
zama l'ictim. Ta rasa ma tunanin da ya dace da ita,
a yau tana zaunc duk wani bacci ya kaura a idonta,
tunani a yau ta soma shi, ashc haka duniya take?
Ta tuna lokacin da mahaifan ta suka nuna mata jin
dadi a rayuwarta. Sun nuna mata gata don tafi
sauran 'yan uwanta jin dadin har da lokacin da
Baban ta ya yadda da bukatar ta na ta je America
ta yi karatu mahaifiyarta ta yi bakin ciki sosai sam
bata son tafiyar ta ba, amma haka ta hakura ta
kalle ta. To a can ta kaga halaye na banza, bata da
ra'ayin rayuwa irin na 'ya'yan Muslmai cikakkiyar
sallah ma ta dai na kai tama manta rabon ta ta
dauki hijab ko gyale tasa ta ce, zata yi sallah. Ta
san yau ta mutu to tasan babu abunda zai rabata da
wuta don an ce tun a duniya ake shaidar ka a
yanzu ma da ta fado wannan wuri akan abunda ta
so ta shirya shine ya dawo kanta, hawaye ne masu
dunin suka zubo mata. A yau tana mai la'antar mai
rayuwa irin ta ta, gun neman ki ba ka nemo rama,
ita tasan hakan da Allah ya yi mata shinc daidai da
ita a yanzu wata irin nadama da dana sani ya shiga
zuciyarta, ita abun da yafi damunta shine iyayenta
da bata nemi gafarar su ba. Ta san inda ta samu
irin hali irin na mahaifan ta da bata wulakanta
kanta ba...taba ta da aka yi shi ne yasa ta dawo
hayaccinta, ta dubi wadda ta taba ta fuskar ta cike
da hawaye, ta yi saurin goge fuskar ta da zanin ta
76
Baki Biyu 0 Sameera Mustapha:
ta ci gaba da kallon matar. Tana yi mata kwanta c
amma bata gane manufar ta ba, can dai sai ta
lankwasa harshenta ta fara yi mata turanci a
hankali suke magana, matar da sauri ta saki murmushi ta ce ita ma da turancin, tasan inda suke? A'a ta fada tana girgiza kanta, muna Cameroon ne! Ai tuni hankalin Suwaiba ya tashi ta firgita sosai sai da matar ta yi samin rike ta tana shafa mata bayan ta tana kuma bata magana don kada aji su, ai wani sabon kukan ta saki, tana sharbe majina sai dai a hankali take yi. Cikin kuka
ta yi barci bata ma san lokacin ba, da asuba a ka zo aka ta dasu wai su kama hanya su tafi lokacin su
ya yi, haka aka sa su suka yi tayi har zuwa wani dakin shima kule ya ke ko window babu, aka
umarce su su zauna nan aka fara aske masu gashin kan su da aska da aka kawo kanta sai da ta canza kayan jikinta dama sauran ma haka suka yi, sannan ta zauna ana cikin yi kuwa sai a kawai kamar an ce juwa tana juyawa sai askar ta yanke ta, sosai kuwa ba kadan ba, ai sai jini ya soma zuba kamar a
bakin kwarya tuni gardawan wurin bakin kofa suka iso suna yima mai askin masifa, ita dai bata jin abunda suke fadi amma da alama ya yi kuskure
sosai ta san yadda aka yi ba sai ji ta yi an rufe mata fuskar ta da buhu aka rike, ta ita dai bata san ya
aka yi aba aka tura ta cikin mota ba tana ji bata da ikon magana. Ta san anyi tafiyar kusan awa daya
kafin aka tsaya aka jefar da ita waje ai kuwa
77
Baki Bivu Sameera Mustapha:
sanadin haka kanta ya buga dutse ta sume.
Da ta bude idon ta sai ta ganta a wani daki na
kara an daure mata kanta da kyale da sauri ta rinke
ta zauna, wata yarinya ta gani zaune gani zaune a
gefenta zaka kai shekara tara da haihuwa, buzut ita
ma ta mike ta fita daga dakin, suka shigo tare da
wata mata da alama mahaifiyarta ce ta shigo rike
da wata kwarya a hannunta, ta mike mata tasa
hannu ta karba, nono ne a ciki ai tuni ta karba
cikin lokaci kadan ta zuke ta shanye, suka karo
mata, ta karfa ta shanye.
Sai da daddare ta fito daga dakin ta iske duk
gidan a waje a wasu na kwance wasu kuwa suna
cin abinci, kai tsaye gun yarinyar nan taje ta zauna
aka kawo mata abinci, tuwo ne da wata irin miya
da ta kai baki kuwa da kyar ta hadiye ya zata yi,
dole ne ta ci.
Babu wanda yasan halin da Suwaiba ke ci don
dama mai hali da ya saba fitina kuma gashi dama
iyayenta ba su daure mata gindi ba don haka ma
sai ayi wata bata yi magana da su ba tun suna
damuwa har sun saba da shiru-shirun ta tun tana
America. Shi kuwa Tahir tunda ya yanke hukuncin
raba su ya fita hanyar ta. Mama kuwa dama ta gaji
da biye mata don ta ci ka mika gashi bata da
hakuri don haka itama a yau satin su biyu ba su yi
magana, kowa ya gaji da hali irin na Suwaiba.
Allah ya shirye ta amin.
Sai da ya yi sati ya dawo ya wuce gidan
78
Baki Biyu 0 Sameera Mustapha:
Suwaiba amma bata gida bai damu ya tambaya
inda take ba don ya saba ganin haka don haka
wanka kawai ya yi ya wuce gidan Gwaggo. Ya
kuwa iske ta a falo tana gyaran gayen latis, ya yi
sallama ya isa gunta ya zauna suna gaisuwa.
Ni kam ina daki da nayi niyar fitowa ne, amma
da naji muryar Tahir sai gabana ya fadi na koma
na zauna. Ina jin su sama-sama hira suke yi, ai
saina koma kan gado na zauna har na kusan minti
goma sha biyar da dai na ga basu da alamar yanke
hirar na dau waya na bugawa Aisha mun sha hira
har take fada min zata je aikin Hajji wannan
shekarar, na yi mata murna, da muka gama Amina
na buga ma wa bayan mun gaisa take ce min da wa
nake magana ne tun dazu sai nuna mata busy ake
yi itama tana ne mana? Ashe mun shiga ran juna
da Aisha, nake magana, to an yi calling schoolyau
she za ki shigo wani irin murna ya shige ni da baya
misaltuwa, dama na matsu in koma Makaranta, kai
don Allah Amina amma nayi murna da yanzu ai
mun gama suka bata mana lokaci, mun yi hutun
watan hudu a gida gaskiya an cuce mu, ke dai bari
Amina ta fada, ke wai har yanzu maigidan naki bai
ce ki koma gida ba? Hum ke dai bari ya yi mirsisi
ya ki cewa komai ke kina ganin zai ce in koma
bayan har kwana ya raba? Hum haka ne fa, Amina
sai anjima Gwaggo na kirana, bari in je in dawo
kila in kara kiranki, muka yi sallama na dauki
hijab na saka saboda wando ne a jikina da 'yar
79
Saki Bivu e Sameera Mustapha
matsitsiya na saka. Na isa falo sai da na ji kamar in
koma don Tahir ne zaune ya kuma tsura min ido,
kamar a yau ya fara ganina. Gwaggo ya fada yana
kallona, kin san 'yar kanwar nan taki bata da kirki?
Tana fara'a ta ce, "me tayi maka? A take hankalina
ya tashi ina kallonsa, kamar ya gane abunda nake
ciki sai naji ya ce, taso ina nan amma ko ta fito ta
yi min sannu da shigowa, oh lallai ba ta kyauta ba,
kana tsamannin itama tirka ce? kunya ce ai dà ita.
Ni dai naje gab da gwaggo na zauna ina kuma
gaida shi, abun haushi bai ma amsa ba, to me yake
nufi don ma ya samu na gaida shi? Ji nayi ya ce,
tashi ki kawo min abinci, na yi kamar ba zan
tashin ba sai da Gwaggo ta ce, baki abunda iya ce,
ba ne? Shi dai idonsa a kaina sai ka ce zai cinye ni,
kai Allah ya yi masa kallo gashi idanuwansa masu
yaudara, a kwayar idonsa yana da wani abu na
musamman da ban san ko mene ne ba.
Na shiga na hado masa abincin akan tray na kawo
na ajiye a gabansa, na mike zan tafi ya ce, ba ki yi
serbing dina ba, na koma na tsuguna ina zubawa a
flat dama fried rice ce da pepper chiken ga kuma
salad da aka hada duk na zuba masa, da na mike
zan wuce ji nayi ya riko hannuna, na yi saurin
kallonsa na kuma kalli inda Gwaggo ke zaune ita
kam hankalinta na kan T.V na dawo da dubana
gunsa na ce, da zafi fa, baki kawo abin sha to zan
kawo na fada saboda ya saki hannuna don rikon da
ya yi min zafi ne dashi, ya sake ni ai gun ya yi
80
Baki Biyu Sameera Mustapha:
jajir, kai wannan mutumin mugu ne, Allah ya
shiga tsakanina da kai na fada a raina. Na koma
kicin na shiryo masa abin sha, irin su ruwa da
kayan lemo, amma abun haushi abincin ma kadan
ya ci kayan sha kuwa ruwa kawai yasha, don
haushi ban ma kara kallon inda yake ba.
Ina zaune dab da Gwaggo na ce, Gwaggo an yi
calling school yau Amina ke fada min, haba dai a'a
ya yi kyau, ashe sai a fara shirin zuwa Makarantar,
ina murmushi na ce, wallahi kuwa Gwaggo duk
zaman ya ishe ni, dama....Tahir ya katse ni da ya
ce, Gwaggo ban gane ta yi shirin makaranta ba, ai
ba inda zata tunda ba ta san hakkina akanta ba,
haba dai wane irin bata sani ba, sai dai idan akwai
abunda take yi wanda ban sani ba, tuni idona na
kallon tasa, ji nake kamar in yi kuka don wallahi
tsakanina da Allah bana son Gwaggo ta san abinda
muke ciki, da alama ya gano irin kallon da nake
masa na rufa min asiri ne sai ya canza zancen ya
ce, Gwaggo ni fa bana cin abincin 'yan aiki, so
nake matata ta dafa min abinda zan ci da kanta.
Duk da nasan akwai matsalar girki hankalina ya
kwanta sam bana son abunda zai sa Gwaggo tasan
abun da muke ciki.
Mikewa ya yi ya bar gidan tare da jaddada shi
fa bai amince da tafiyata ba, kuka na saka wa
Gwaggo ta ce, dadi na dake baki da hakuri, don ya
ce shine za ki damu to duk yadda aka yi abunda ki
ke shukawa ba girki kadai ba ne matsalar, babu
81
Baki Biyu Sameera Mustapha:
komai Gwaggo don Allah ki roke shi in tafi, nan fa
da wata bakwai insha Allahu zamu gama. To Allah
yasa ya amince kin san dai ba zan matsa masa ba.
Sosai hankalina ya tashi na lura Gwaggo bata
son ta matsa wa Tahir na riga na san duk abinda ya
fada shi din za'ayi sai na fara tunanin abun yi, yạ
zan yi? Na tambayi kaina Aisha na buga ma wa
ina fada mata damuwata, abun takaici sai ta ce ai
laifinki ne Dayiba, ko ni ce matakin da zan dauka
kenan ta ya za'ayi aure tun watanni hudu da suka
wuce amma baki san ki ba mijinki hakkinsa na
kwanciya ba, kin manta irin fushin Allah da ki ke
tare dashi ne? Ni fa na bugo ne don ki bani
shawarar abunda zan yi in koma Makaranta ba wai
ki sani gaba kina min fada kamar wadda ki ka
ajiye ba, ai duk abunda na fada miki ba shawara ba
cc? To shi kenan na ji Allah ba ki hakuri, bata jira
abunda zan ce ba, ta kashe wayar, dama na san sai
an yi hakan tun kafin in buga mata nake zulumi
don na riga na san halin abu ta. Na sake buga mata
sai da yai ta ringing kamar ba za ta dauka ba sai
kuma ta daukan tana fadin, wallahi Dayiba kina da
ban haushi, ai matakin da ya dauka wallahi ita ce
daidai da ke, to Mama na gode...ko ba ki kira ni
hakan ba na san matsayina a gun ki don haka ba
zan baki gurguwar shawara ba. A haka dai na ajiye
ina tunanin abinda zan yi amma shawarar ta bata
ma yi tasiri a guna ba don ba yin hakan zan yi ba.
Na ga washegari bai shigo ba, kai har muka
82
Baki Biyu Sameera Mustapha:
kwana hudu ina jiran in ga shigowarsa amma shiru
ka ke ji, na buga wa Amina ko an fara lecture ta ce
ai tunda aka dawo ake ta lectures har da test wasu
departments din suka yi namu dai ana shiga
lectures sosai ranan Monday ma muna da test, ke
wai ba za ki dauki laifin ki ba, ko ya bar ki ki
dawo? Ni ban ma san ko yana nan ba, yau kwana hudu kenan ban gan shi ba da alama ya yi tafiya
inda yana garin dole'ne ya shigo ya gaida Gwaggo
safe da daddare, ikon Allah mutum da mijinshi
amma bai san inda mijin yake ba, har na tsawon
kwanaki. Lallai Allah ya ganar da ke, sai an jima
zan je in tarbi mijina yau a hannuna yake, ai abun
gori ne ma nima Allah zai bani wanda nake so tun
kafin ta ce wani abu na ajiye wayar na zauna nayi
shiru ina tunanin abun da ya dace in yi, naje na yi
dabara na dauko wayar Gwaggo na kwashe duka
numbobin sa baki daya naje maidawa na same ta
tana neman wayar na mika mata ga wayar nan
Gwaggo dama number ce na dauka, ta karba Tahir
bai bugo ba? Na yi kamar ban ji abunda ta ce ba,
sai kuwa aka fara kira ta dauka daga gani shine
aisai na samu wuri na zauna. Jira nake in sun gama
in duba number da ya kirata da shi, sun fi minti
sha biyar suna maganar, can dai na ji tayi masa
sallama na matso gunta na ce, Gwaggo ki roke shi
don Allah in koma Makaranta, wallahi har an
kusan fara jarabawa, me ya samu bakinki da ba za
ki fada masa ba? Ai ina fada masa, amma ya ki
83
Baki Sivu Sameera Mustapha:
kula ni, Gwaggo wata bakwai kadai ya rage
tsakanina da Makarantar, don Allah ki taimaka,
waya ta dauka ta kira shi, murna ce ta kama ni don
nasan in ba ita ba tabbas yana iya hana in je
Makarantar, haka kuwa tana fada masa ya bada
hadin kai ya ce babu damuwa ina iya tafiya
washegari, ai ban san lokacin da na kai dakina ba,
ina murna ban tsaya 6ata lokaci ba na soma shirin
tafiya washegari tun tara na safe na bar Abuja
zuwa Kaduna.
A Cameroon kuwa, Suwaiba ta samu kusan
kwana biyar a gidan, sai dai duk ta fita hayyacinta,
da yake gidan da suka taimaka mata gida ne na
Musulmai kuma gidan Mallamai, a dole Suwaiba
ta fara sallah, sannan da alama duk wani ji da kai
da take fama dashi ya kau. Ta zama silent bata da
aiki sai tunani da kuka, tana bakin cikin irin
rayuwar da ta daukar wa kanta. A gidan Mal.
Attahiru, mutumin Cameroon sai dai ba wai suna
cikin birni ba ne, suna cikin daya daga cikin
kauyukan garin ne. Tun usulin iyayen sa Malamai
ne a nan garin, yana da matan aure biyu da
'ya'yansu su goma sha biyu, uwargidan na da
takwas amaryar na da hudu, irin zaman da suke yi
shi ya rika ba Suwaiba mamaki, matan biyu kansu
a hade yake, suna bala'in shiri babu ruwansu da
wani abu wai shi kishi, anya sun san kalmar ma?
Ta kan yi wa kanta wannan tambayar, abinci ma
tare suke ci a kwano daya, in ka ga dan dakin nan
84
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
ba za ka babanta shi da da na dayan dakin ba, ta
lura duk inda ka zaba nan zaka kwanta, kai su ba
su da matsala, ko 'ya'yansu ke fada ba su nuna
bambanci, to ko dan suna auren Malami ne shi
yasa suke hakuri? Ita dai