Mama har ta so ta manta ba
Dayiba kadai ake so ta jawo hankalinta ba, har
da Tahir. Tabdijam, ashe akwai aiki ja a
gabanta! Mama ta katse ta, ta ce kina jina ko kin
san fa aikin da yake son yi ba zai yi ba sai kin
52
Baki Biyu Sameera Mustapha:
tabbatar sun saki jiki dake, eh, na sani ta fada a
ranta kam tasan tana da aiki.
Na yi wanka na yi shiga cikin wani yellow
lace mai bala'in kyau na yi kyau sosai, na wuce
dakin Suwaiba itama ta yi shiri cikin super
holland tare muka yi breakfast, ni dai nasa nayi
dacen abokiyar zama na lura ba ta son ta ga
bacin raina. Na sami kwana shidda a gidan
amma babu ruwana da Tahir, bamma ganinsa
kila sai dai in hange shi da nesa saboda muna jin
horn din sa ko karan gate za mu shige
dakunanmu, ni da Antin tawa mu kulle yadda
kasan mun ga dodo.
Ita kam Suwaiba in tà shiga daki in ban da
dariya da jin dadin abunda ke faruwa babu
abinda take yi, tasan ta riga da ta tsoratar da Dayiba, da alama burinta na son cika don ta ga
alamun Dayiba sosai ta yarda da ita, ta fada a fili sakaryar yarinya da hankali bai ishe ta ba, kowa
ta taba ganin ya yadda da kishiya oho! Ta kara
kyalkyacewa da dariya sai kin bar gidannan kin
koma gidan ubanki.
Har na cika wata daya a gidan Tahir ba
abinda ke hada ni da shi, sai dai in je gun
Suwaiba mu sha hirarmu muyi kallon films din
mu babu ruwanmu, mu ci mu sha shine aikin mu,
na kara jin dadi da Makarantarmu taje strika dan
haka hankalina a kwance ni har mantawa ma
53
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
nake yi wai ina da aure ko kuma aure ne ya kawo
ni gidan nan. Gashi cook din gidan ya iya abinci
sosai, bamu aikin fari balle na baki, 'yan aiki ne
birjik a gidan, musamman ta bani 'yan aiki biyu
suyi min hidima, a dakin na, abin mamaki na yi
kiba nayi kyau duk wata rama da duhun da nayi
ya washe, ni kaina nasan na sami lafiya, a
gaşkiya ina jin dadin zama da Anti Suwaiba, ba
kadan ba, sam ba za ka ce mu kishiyoyi ba ne
don mun yadda da junanmu.
A wannan lokacin ne, Gwaggo ta dawo zama
Abuja, dadi a guna kamar in yi me, gidanta
babba ne sosai, zaka iya kiran gidan 'garden
house' don itace ne da furanni zagaye da gidan, a
gaskiya gidan ya yi min bala'in kyau mijinta ya
bata halak malak ko ya mutu babu wannan gida a
gado, gashi bene ne mai hawa daya, dakuna
kuwa birjit a gidan, ita da kanta tazo ta dauke ni
ashe wai Tahir ya yi tafiya zuwa Thailand har
ma ya yi sati biyu a can ni kam bam ma sani ba,
na so kwarai in maida gidan Gwaggo wurin
zuwa amma ta ki bani fuska don haka dole na
hakura na daina zuwa, duk da akwai nisa
tsakaninmu. Sosai Gwaggo ta ji dadin ganin
yadda na kwantar da hankalina, kamar ta hadiye
ni, ita a ganinta na hakura bata san dan nata
mugun mutum ba ne.
54
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha
Tahir ya sami kamar wata daya da rabi da
tafiya Thailand, Suwaiba kuwa a koyaushe tana
bani labarin irin zaman da suke yi da Tahir har
bata jin kunyar gaya min ko kusantar ta baya yi
sai dai duka da take sha shima din don ta fada
masa gaskiya akan zaman da yake yi da matan
waje kila ba ya sha'awarta ne don a kullum yana
tare da su saboda in ki ka ji irin matan da yake
fita da su irin masu class din nan ne to ke kuwa
irin matannan menene baza suyi maka ba don su
ma ake ka, shi yasa wasu matan masu son auren
namiji mai kudi sun shiga uku don basu san
abunda zasu aura ba. Na ce, ni kam Anti baya
tsoron cutar da ake dauka yanzu sanadin haka?
Ta tabe baki uhm ke dai bari kawai Allah ya
kare mu. A raina kuwa cewa nayi Allah ya
kyauta ma in bada kai har nima in samu ai nesanesa dai. Shakuwa sosai maka yi da Anty
Suwaiba saboda komai tare muka yi fita kadai ne
bana yi, bana binta sai dai taje ta dawo.
Ana cikin haka kuwa aka yi wa su Anti
Badiya transfer Abuja, sai dai ita a yan ya take,
washe garin da ta tare gidan ta naje nayi mata
wuni ta ce, lallai yarinyar fa kin ji dadin aure kin
ga yadda ki ka zama kuwa? Kamar iya
Balarabiya na ce kai Anti kin cika tsokana ke dai
zancen haka kin ga ki ban da ki kayi kuwa? Ke
cikin da nake dauke da shine shi yasa na yi ki
55
Baki BiyU e Sameera Mustapha
ban nan Anti ina shi ke nan dai duk mun bar
Kaduna? Ke dai bari dama Tahir Allah sai ya
saka masa kin san fa shi ya nema masa aikin a
MTN shine aka bashi manager a dai marketing
deptement a nan Abuja, Allah ki rike mijin ki
yana da mutunci sosai, a raina cewa na yi a fuska
ba da mutanen waje....ta tsinka min tunanin kin
ji abunda nake fada kuwa? Na ce eh, ina jin ki,
haka dai mukai ta hira, tana bani labarin irin
abun alherin da Tahir ke yi masu.
Haka muke ta zaman mu cike da nishadi,
haka kuma ina kiran Baba da Baba a waya,
Gwaggo kuwa ai babu ranar da bana kiranta. Ina
kicin in dan dafa abinda zan ci, ranar in
kwadayin indomie kuma yadda nake dafa ta tun
a gidan Gwaggo haka nake sha'awarta, tun
wadda Asabe ta koya min ita nake yi kuma ita
kadai dama na iya dafawa. Na gama dafawa na
juwo kenan muka yi ido hudu da Tahir a bakin
kofar kicin din ya saka hannayensa a wandonsa
ban san lokacin da plate din hannuna ya sullube
ya fadi kasa ba, tas ka ke ji, ina kyarma na gaida
shi, sam ban san lokacin da jikina ya fara rawa
ba, shi kuwa sakin fuskarsa ya yi ya amsa ya ce,
kiyi hakuri, ban san zan baki tsoro ba, amma
kuma nayi sallama ashe ke baki ji ba, yay ina
'yar uwarki? Ya tambaye ni yana kallona, na dan
motsa bakina kamar bakin na min ciwo
56
na ce,
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
uhm-uhm ta fita ne? tambayar da ya jeho min
kenan na sa ido na kasa na ce, ni ma ban sani ba,
ya dan shigo cikin kicin din ya ce, idan ta dawo
ki ce ina son ganin ku a falona, bayan sallah
isha'i.
Ba tare da ya jira amsa ta ba ya wuce, a raina
na c,e kaji mutum sai zuciya kamar shi kadai ne
mai ita, ina cikin sake-sake na na ji sallama Anti
Suwaiba na yi saurin isa gunta kafin in ce wani
abu ta ce, tana kallona Tahir ya dawo ko? Na ce
eh, tun dazun amma Anty kin dade har ma ya
tambaye ni in da ki ka je. Rabu dashi da Allah,
ina yake ne? wallahi ban sani ba, ya dai ce in kin
dawo in gaya miki yana son ganinmu a falonsa
bayan Sallah Isha'I. Ta tabe baki ta ce, to Allah
yasa dai lafiya, don abinda mamaki neman me
yake mana? Na yi ajiyar zuciya da ta baiyana na
ce amin.
Bayan mun gama cin abinci na shiga bayi
nayi wanka, nayi sallah magariba ina zaune dai
akan sallaya ban tashi ba na dauko Alkur'ani
mai girma ina karantawa, har aka kira Sallah
Isha'i, sannan na tashi na yi na idar har da
shafa'I da wutiri. Na yi abina, na yi shafa na fesa
turare na dauko engilish wears dina riga ce bodyhug saboda ta dan matse ni pick cetana da
taushi rigar sai na saka sket jeas dina yakai min
har kasa, na saka slippers fari tas, na fauko irin
57
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
dan hijab dinnan da bai sauka sosai ba saka, na
kulle daki na na wuce dakin Anti. Itama kanta
sai da ta kyasa kwalliyata duk da bata fada ba
amma na gani a idonta.
Mun same shi zaune a falonsa yana kallon
MBC 4 ana wani programme din na oprah sai
muka sami wuri can nesa dashi muka zauna
kujera daya muka tsura maşa ido. Ya dauki
remote ya rage volume na TV, sannan ya ajiye
remote din a gefensa, ya dube mu, ni dai nasa
kaina kasa saboda bana ma son mu hada ido. Ya
gyara zamansa shima yana fuskantarmu sannan
ya ce mu bade wannan meeting din da addu'a a
karanta kula'uzai har da Fatiha, sannan sai
Ayatul Kursiyu. Haka din muka yi cikin minti
uku muka shafa ya ci gaba. Suwaiba ya kira
sunanta ke ce babba don haka da zan fara, na san
tunda aka kawo Dayiba gidannan ya kamata in
tara ku muyi magana, amma hakan bai samu ba
shi ne a yau nake son in san wane shiri ko
shawara za ki bamu akan yadda zamu zauna? Ina
nufin ki zaba mana yadda zamanmu zai kasance
na baki dama.
Ta bata fuska sosai ta ce, wane zama kuma ka
ke so muyi bayan wanda mu ke yi? Ka ga mu dai
muna zamanmu lafiya da Dayiba kar ka zo ka
canza mana tsarin da...." Ya katse ta, ba wai ina
son in 6ata maku zamantakewar ku ba ne, a'a
58
Baki Biyu Sameera Mustapha:
amma kin san ina da hakki a kanku ba wai na
auro ku ba ne don in yi decourating din gida na
ba ne sai don da ni da ku muyi rayuwar aure mai
kunshe da nishadin rayuwa.
Suwaiba ta mike tsaye ta ce, kai da Allah can, kai har wata nishadin aure ka sani a rayuwar
aure? Bayan muzguna mana da ka ke baka gani
ba don yanzu kana bukatar wani abu a gunmu
shi ne zaka zo mana da dadin baki da dai ba mu
san halin naka ba, mu ka barmu yadda muke ba
ma son wani canji. Hakkin da ka ke ikirarin kana
da shi a kan mu kuwa mun yafe bama so...." To
ni ban yafe nawa hakkin ba, ya za ayi kenan?
Wannan kuma kai ya shafa, uhum ni kaga tafiya
ta saboda ban ga amfanin wannan meeting ba na
rashin gaskiya." Tana kama hanya nima na tashi
buzut na bi bayanta, sai ka ce ya biyo ni muka
bar shi nan zaune. Ni kam Anti tayi min daidai,
don na gani a fuskarsa ransa ya yi bala'in басі.
Tahir yana nan zaune a inda yake na tsawon
minti ashirin yana tunanin abun yi, don ya lura
Dayiba ta amince da Suwaiba sosai, ta riga da ta
bata shi gare ta, to yasan matakin da zai dauka.
Ya mike ya shiga dakinsa, a zaton Suwaiba tana
da wayo ta manta ita tana da nata shima yana da
nashi ko don taga yana biye mata? Ya canza
kayan da ke jikinsa ya saka T-shirt fara sol, an
rubuta (Tommy hilfiger) da jan kala sai wando
59
Sakı Siyu Sameera Mustapha:
Jeans sky bluc, ya gyara gashin kansa kace bai
aje mata biyu ba, tamkar fan saurayi duk da
yana da dan jiki sai dai na ce maku "He is not fat
but he is huge" da ya ke yana da wadataccen
tsawo shi yasa ba a ganin hakan ya wuce sashen
Suwaiba kai tsaye ya san suna can.
Ina zaune na kwabe hijabi na na lankwashe
Kafafuwana kan kujerar da nake zaune akaі
muna ta hirarmu da Anti Suwaiba cike da
nishadi sai jin sallamar Tahir muka yi daga
sama, kallonsa a kaina ya tsaya na yi maza na
saka hijab dina ya yi kamar bai ga abinda nake
yi ba. Ya sami wuri ya zauna ya ce, Suwaiba ina
son ki bani aron kanwarki zamu fita ne. ta kawar
da fuskarta da tsabar bakin ciki ta ce, ni me
ruwana da fitarku, in ta ga dama ta bika ni bai
shafe ni ba, don dama ai zamanka take yi. Ya mike
ya nufi inda nake zaune, ke tashi mu tafi,
hankalina tuni ya tashi na ma kasa mikewa gabana
kuwa kamar zai fita don tsabar harbawa da yake
yi, ya iso inda nake, ji na yi ya kamo hannuna ya
mikar da ni, sai dai hankalina na kan Suwaiba, ji
nake yi kamar in yi fitsari don tsabar tsoro, ji nayi
ina cewa Anti bishi? Ta dan washe baki kadan ta
ce, bismillah ni kar ki tambaye ni ai shi ya ajiye ki
bani ba ni babu ruwana. Na dubi shi tuni har ya
fara jana min fara tafiya, wallahi hawaye ne kawai
bai fito min ba, amma kuka ma na kusan yin shi.
60
Baki Biyu
Mictanha:
Sameera Mustapha:
Sai da muka kai bakin kofa sannan ya juya ya kalli
Suwaiba ya ce, sai mun dawo.
Haba wa, Suwaiba ihu ta rika yi tana kuka kan
bakin ciki, ta rasa abunda ke mata dadi a
rayuwarta, ai saboda tsabar takaici 6ata masa
lokacin da ta rika football da kayan dakin ta ba, ta
gano Dayibą tana bala'in tsoron Tahir ya zata yi ta
sa Dayiba ta rika kai Tahir dole ne ta nemi wani
hanyar don ta cimma burinta.
Tafiya muke yi ba mai cewa dan uwansa wani
abun, da yake ni ba 'yar gari ba ce, sam ban san in
da zamu ba. Gabana ne ke faduwa ina kuma
addu'ar Allah ya tsare ni daga sharrin wannan
mugum mutumin, sai da muka yi kusan isa na
gano gidan su Anti Badiya za mu, a raina na rika
godewa Allah, tare da ajiyar zuciya.
Mun shiga gidan ita da maigidanta suna ta
hirarsu, gwanin ban sha'awa, kafafunta na kan
cinyarsa yana matsa mata, duk sun kumbure.
Sahabi ya mike yana mana iso, kuyi hakuri fa
kofar a bude take, in ji Tahir, haba ba komai a
same muka bar kofar bude. Na isa gun Anti ina
gaida ta, sannan na gaida Sahabi, ya amsa ya ce,
ya amarci? Murmushi na yi ban ce komai ba, na
wuce cikin dakin Anti, biyo ni tayi dakin. Bari in
kai masu abun sawa a baki sai in zo. Muryar Tahir
na ji yana cewa, Dayiba nemo min abunda zan ci
yunwa nake ji, tuni na bata fuskata, me wannan
mutumin yake nufi? Sam ban san Anti na dakin
61
Sameera Mustapha: Sakı Bıyu
ba, na yi tamkar ban ji shi ba, sai da ta dan matso
kusa da ni sai ta cc, ke ba ki ji abinda Tahir ya
fada ba ne? Na mike ina turo bakina, Anti kam
kallona take yi kamar a ranar ta taba ganina, ni
wallahi wannan mutumin so yake ya dame ni, to
kada ki kai masa, anya kin san abinda ki ke yi
kuwa? Da sauri na wuce kicin na iske tuwo da
miyar taushe ga kuma farfesun kaji da fruit salad,
uhum su Anti iya abinci kalla-kalla ni kam ina zan
iya tuka tuwo balle kuma hada miyar. 'Na ma rasa
ta inda zan fara, don a gaskiya komai ban iya ba,
hatta serving na abinci ban iya ba, tsayawa na yi
ina kallon kololin da na bude, muryar Anti na jiwo
na tsinke don firgita nayi, a'a wai ke lafiyanki
Dayiba? Mits, tsaki ta yi ke kam kin shiga uku,
komai ba ki iya ba, ban ga amfaninki ba wallahi
kina mace amma common serving baki iya ba, to
balle girkin abinci, to ya ku ke yi ne? Na ce ai
muna da cook ne shi ke yin komai ya shirya a table
ah lallai kun hadu, tana magana tana hadawa tray
naga ta dauko da plates guda biyu ta saka tuwon a
daya miya a dayan sai ta dauko wani mai zurfi ta
zuba farfesun sannan ta dauki abun sa fruit salad
shima ta zuba ta jera akan tray ita ce to 'yar hutu
dauka ki kai, murmushi na yi na ce, kai Anti ni tafi
ki kai masa kada ya biyo mu kicin, na dauka ina
tafiya a hankali, gudun kada in zubar, gashi tray ya
yi min nauyi a hankali na iso na ajiye a can nesa
da shi maimakon in kai gabansa, har a zuciyata
62
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ban dauka na yi wani abu ba ne, daga bayana naji
Anti ta ce, yauwa sai ki dauki dan karamin table
din can ki kai kusa dashi ki dauki abincin ki aza
akai, na yi yadda ta ce, na san kallona yake yi, sai
dai ni na ki in daga ido in kalle shi, haka kuwa na
bar falon ba mu hada ido ba, na koma daki zan
zauna anti ta ce ba ki fa gama ba, saura ruwan sha
da juice, anya Dayiba kin san aikinki kuwa? Na
mike ina gunguni ita kam kallona take yi tana
mamaki.
Da na dawo ta ce, don Allah dan matsa min
kafafuna, wallahi ciwo suke min. Na zauna ina yi
mata, ta ce 'yar uwa na lura kina tare da damuwa,
me ke faruwa ne? Ai ji nayi idona ya kawo ruwa,
sai hawaye zarrr, da sauri ta sauke kafafunta ta
dafa min kafadata, fada min abinda ke damunki
insha Allahu zan baki shawara da ya yi daidai da
ke."
Na dube ta da jajayen idona, na ce, Anti ni dai
ban san me yasa ba na tsani namiji, haushi sukc
bani ki sani ba tun yanzu ba, a'ah tun farkon so da
na fara zan fada miki abinda kowa bai sani ba,
firts love dina a rayuwa shi ne 'Ya Amir', na ga
alamun mamaki a fuskarta, saboda babu wanda ya
san haka. Na ci gaba da fada mata, ban taba son
namiji a rayuwata ba kamar yadda na so Amir.
Tun bai sani ba har ya fahimci hakan, ana wa
tunanin shi ne yaso ya yaudare ni ya furta shima
yana sona, a lokacin ina aji uku na secondary da
63
Saki Bivu e Sameera Mustapha: Mustapha
muna tare da kawaycna Zainab kawata ce a nan
(F.G.G.C) Zaria, take gaya mana labarin wata
Kawarta da ta yauydari kanta ta mika wa
saurayinta kanta, saboda irin tsabar yadda da tayi
dashi duk da shine ya nuna mata kada ta damu da
komai in dai tana tsoron wani abu ne to shi ai
aurenta zai yi, wallahi anti ya maida ita tamkar
matarsa, da kanshi ya samo mata pills take sha wai
don kada ta yi ciki, daga Karshe bace mata ya yi Anti kin san yadda Baba itama tana tsoratar da mu.
akan samari to shi ne fa na daukar wa kaina
alkawarin kame kaina daga da namiji, kai da ireiren wadannan labaran na zama ina bala'in tsoron
da namiji shi ne fa Ya Amir da na kwallafa wa
raina shi, shi yaso ya yaudare ni shine fa na sa wa
kaina kin su... "Me ya yi miki da ki ka yankewa
kanki wannan hukuncin?" Miyau na hadiye ina
kallon ta, na ce a gaskiya na farko mahaifiyarsa sai
kuma shi da yake nema shige min, ni kuma a
gaskiya tunanina iskanci kan fara daga shafan juna
ne, shi ne na yanke shawarar rabuwa da shi. Tun
kafin abun ya yi nisa gashi duk da shi kaďai raina
ke so. Anti ta ce, sa'id fa? Ai shima kin so shi,
sosai kuwa Anti amma kin san bai kai yadda naso
Ya Amir ba, gani nake ba zan taba son kowa
yadda na so ya Amir a rayuwata ba, Tahir fa shi da
yake matsayin mijinki a yanzu? Tambayar ta yi
min wani iri, don na lura Anti tana son duk wani
abu da ya shafi Tahir, na lura suna shiri sosai, ban
64
Baki Biyu Θ Sameera Mustapha:
iya cewa komai a kansa, na yi shiru ina kallon
kasa, baki daya nayi shiru kuma na kasa ci gaba,
can na tuno da abinda Anti Suwaiba ta fada min
akan sa, don ban san komai akansa ba, ni na san
dai mugu ne. Anti fa manemin mata ne."
Murmushi ta yi ta ce, 'yar uwa kina nan fa lokacin
da Anti Nafisa ke fada mana abinda zamu yi idan
muka fuskanci irin wannan matsalar, hakuri za ki
yi ki yiwa Allah Ibada, ni dai a yảu Alhamdulillahi
zan ce, an a gaskiya Sahabi ya yi sauki akan
farkon aurenmu, ba komai ba ne kuma sai addu'a
da kuma kauda ido daga al'amuransa. Ni dai ina
saurarenta amma a gaskiya ban dauki shawararta
ko daya ba, don inda ta san waye shi da ta bani shawarar rabuwa dashi......ta tsinka min tunanina
da ta ce kina jin abinda nake fada kuwa? Na girgiza kaina alamun "Eh, ta ce tashi muje falo
kada suga mun kyale su.
Suna zaune sai hira suke yi, Tahir sai dariya yake yi yana cike da nishadi, ka ganshi sai ka ce
da gaske a waje zaka ganshi lamai-lamai, cike da saukin kai, muna shiga gida zai fara nuna halinsa
na rashin mutunci.
Bayan munyi sallama da su mun bar gidan sai muka kama hanya. Tafiya muke yi naga ya wuce hanyar gida, na dan dube shi ta gefen idona,
tukinsa yake yi hankali kwance, na kalli agogon da
ke makale a motar, karfe goma saura, ina zai kai ni cikin daren nan? Ai tuni hankalina ya tashi, gabana
65
Baki Biyu Sameera Mustapha:
kuwa sai faduwa yake yi. Ban dai yi masa magana
ba don bana son komai ya hada mu. Sai can ya
tsaya gaban gate a lokacin na lura da gidan
Gwaggo ne, ai sai hankalina ya kara tashi wallahi
duk sai na tsinke, fargaba na ya karu. Ina tunanin
abunda ya kawo shi gidan Gwaggo yanzu. Ya yi
parking ya fita, a sanyaye nima na bude na fita. Bа
dai karata ya kawo ba? Duk sai na ji babu dadi,
ban san lokacin da na ce dashi, "Don kada ka gaya
ma Gwaggo abunda ke faruwa." Jin maganar ya yi
daga sama, hannunsa na kan kubar kofar ya dube
ni nasa kaina kasa, kasa-kasa yake magana. To
naji ba zan fada ba, ai ban san lokacin da na yi
ajiyar zuciya ba.
Sai da aka bude mana kofar, Gwaggo na zuane
a kan kafet tana shan kayan itace, tana kallon wani
Hausa film, mamaki ne a fuskarta, amma sai ta
share tana yi mana sannu da zuwa. Naje dab da ita
na zauna ina gaida ta. Bayan mun zauna sosai
Tahir kam shima shan kayan itacan yake yi, yana
fadin, Gwaggo film ake kallo haka? Uhm, kai dai
na kasa bacci shi ne na fito na kunna, lafiya na
ganku da daddare haka? Daga idon da zan yi muka
yi ido hudu da shi, ya saki murmushi 'yar kanwar
ki na kawo miki ku dan zauna. Gwaggo ta dube
shi ta ce, ban gane ba, wani abun ya faru da ka
yanke hakan? Babu komai Gwaggo, sai a hankali
za ki gane, amma ko yau da muka yi magana da
kai Tahir na ce maka akwai abunda ke damunka,
66
Baki Biyu
52
Sameera Mustapha:
koda yake dama halinka ne, kai ba ka fadin
damuwarka sai randa ta yi wari don haka Allah
yasa haka ya fi zama alheri da sauri ya ce (Amin). Gwaggo na raba masu girki kwana biyu-biyu, Haj. Hauwa bata son ta takura wa Tahir tasan yana
da babban dalilin yin hakan, ko ba komai tasan
Tahir na da bala'in hakuri, yana iya hakurin fiye
da shekaru goma akan abu, don haka ta ki ta kara
yi masa wata tambaya don dama tun ba yau ba ta
gano yana cikin damuwa. A sarari fara'a tayi ta ce,
to madalla, Allah ba mu hakurin zama tare, amin
ya fada yana mikewa. Ni zan wuce sai da safe. Gwaggo ta dube ni na dan kwantar da kaina a
gefen ta. To 'yar shagwaba, an dawo ma fara
zaman lallashi kenan na yi murmushi kai Gwaggo
ni wallahi ba ki ji dadin da na ji ba, kamar ya san
abunda nafi so kenan zama da ke a rayuwata, baya
gun sa ta Gwaggo ina fa zai dame ki tunda baki da matsala sai ta shagwaba. A raina kuwa tunani nake
yi meye dalilin yanke wannan hukuncin ni ban
taba ganin anyi haka ba, ai wannan ba gidansa ba
ne har zai shirya kwana mutumin nan akwai ikon
banza. Ban hakura ba na dubi Gwaggo na ce,
"Gwaggo hala ana yin haka nan ai ba gidansa ba
ne da ya shirya hakan, wa ya fada miki? Gwaggo
ke ki ka ce Baba ya yi maki gida fa da fa a nan, in
ji ni ko ko dai ki ka dauka hakan dan ni ban san
mun yi wannan maganar da ke ba, in ce an ce
kayan ciki ne ya zuba maki? Hum ta fada tana
67
Baki Biyu Sameera Mustapha:
murmushi, wannan gidana ne, ni na sayi abuna da
taimakon Tahir, shi ya biya kashi saba'in cikin dari
ya kuma mallaka min gidan halak-malak, tabdijam
wannan wane irin kudi yake da shi? Na fada a
zuciya ta, ta ci gaba ai ba karamar rigima aka yi ba
da Baban Usman (Alh. Shehu Magaji take nufi)
shi sai dai in zauna tare da iyalansa ni kuma dama
Kaduna nake son zama, saboda bana son tashin
hankali tsakanina da matarsa, na fi son nesa-nesa
bana son takura, ana cikin haka sai aka yi masa
transfer Lagos dama yana da gida a can amma ba
girma sosai, shi ne fa abun ya lafa ya amince
'ya'yansu na nan a nan saboda Makaranta da shi da
matarsa suke zama Lagos duk ranar Juma'a sukan
dawo suyi week end a nan, to ni me ya dame ni,
Allah ya ba ni in ce bana so, so kin ji yadda aka yi
Allah ya kawo saukin saboda shi dama ba
azalimin kowa ba ne, sannan yana aiki ne da niyar
mutum. Ajiyar zuciya na yi ina kara so da kaunar
Gwaggo, ita dai Allah ya yi ta mai tawakkali da
duk abinda ya same ta, ta kan yi hakuri sai ya zo
ya wuce. Muna nan muna hira har sha biyu ta
wuce tare muka kwana dakin Gwaggo a ranar
wallahi na sake na yi bacci sosai, ranar har da
miyaun bacci, na dade bana bacci hankalina a
kwance tunda na shiga gidan Tahir.
Suwaiba sam ta kasa bacci damuwarta ita ce
ina ya kai Dayiba, ga shi shima ya ki ya shigo gida
balle ta tambaye shi, kwata-kwata bata rintsa ba
68
Baki Biyu Sameera Mustapha:
saboda ta fitini kanta. Da Asuba ta ji motsi da
saurinta ta fito falon ta ganshi zai shiga dakin Dayiba, ta yi saurin bin bayan sa zuwa ciki,