biyu daya ford ce dayan kuma landguriser,
34
Baki Biyu. Sameera Mustapha:
sam ban sa komai a raina ba don nasan kila
bakin Alhajin gida ne don idan yana gari dama
yakan yi baki irin wadannan.
Kai tsaye na shiga falo, kaya ne aka baje ana
ta kallo, Anti Badiya ta ce 'yar halak tun dazun
ake neman ki ina ki ka shiga ne, ga kayan lehen
ki nan an kawo, harara na wurga mata tare da
6ata fuskata, ban ce komai ba na juya fuskata, ai
sai muka yi ido hudu da Suwaiba, irin kallon da
tayi min ya ba ni mamaki, sakin fuskar ta yasa
faduwar gabana ya lafa, anya ita ce ko dai ban
lura ba? Na tambayi kaina, dole nima na saki
fuska ta nayi mai da mata martani na gaida ta,
sosai ta yi fara'a tana amsawa, wato bani kadai
abun ya ba mamaki ba, duk wanda yake falon
kallonta ake yi don ina zaton ba a taba zaton
haka daga gare ta ba, ni dai na karasa dakina ina
tunani, anya abunda Tahir ke fadi akan baiwar
Allah nan gaskiya ne? kai namiji namiji sai shi,
dama na sha jin labarin idan namiji na son aure
ko saki ga matarsa to yana iya shirya abunda
matar bata ma taba kuskuren yi ba, bandaki na
shiga sai da na watsa ruwa na fara alwala abun
mamaki sai na ji hawaye na fitar min daga idona,
ba ji ba gani, dole na daina alwalar na zauna kan
water system ina kuka, a kalla na samu minti
talatin sai naji ana kwan-kwasa kofar bayin
muryar Mama Hadiza naji (yar babba ce a zaria
35
Baki Siyu Sameera Mustapha:
take aure) tana cewa ke Dayyiba za ki fito daga
bayin na bakinki tun dazun suke jiran ki, da sauri na mike na fara sabon alwala cikin minti
biyu na fito tana nan dai tsaye a wurin wai ke
wace irin yarinya ce, ba ki ko tsoron abunda ke
bayin, wucewa na yi na fara sallah, hadawa nayi
da Isha'l sannan na saka jallabiya ta, babu
abunda na shafa ina zaune bakin gado sai ga Anti
Badiya ta shigo, tashi muje uwargidanki ta ce ki
zo kuyi sallama tana so su wuce masauki.
Gyalena na dauka na yi saurin rike hannun
Anti, ta gano abinda ke damuna, don haka sai ta
biye min. Muna isa falin gun Gwaggo na je na
zauna a kasa kan kafet kamar daga sama sia na ji
Suwaiba ta ce, amaryarmu tun yau muka fara
sayen baki ne, baki daya aka yi dariya, ni kuwa
sai naji na fara jin kunyarta, mikewa tayi ta zo ta
zauna kan kujerar da ke kusa da Gwaggo ta dan
rankwafo don in ji abunda take cewa, kwali ta
azamin akan cinyata ta ce, amarya ga sako mai
mahimmanci, ango ne ya ce in baki, kuma ki
bude ki saurara zai neme ki, dama a dalilin
wannan sakon naki tafiya har sai na isar da
sakon ango zuwa gare ki, ni dai kaina na kasa
gabana kuwa kamar zai fito, ni dai sai na ji ta
kwanta min, tausayin ta kuma ya kama ni, kai
anya zan iya wannan.....Suwaiba ta katse min,
tunanin da nake yi ta ce, to asha hira ce, to amarya
36
C
Baki Biyu Sameera Mustapha:
lafiya, mu dai bari mu tafi Gwaggo tayi saurin
cewa, to Allah ya sanya alheri, ya baku ikon
hakuri da junanku, baki daya falon aka amsa
(amin).
Gwaggo ta dube ni, haba 'yar kanwata dubi
yadda ki ka maida kanki duk kin rame sai ka ce
mai cewo, dubi idonki yadda suka kumbura sun
yi dara-dara kamar tsokar nama, wai me yasa
baki ji abunda ake fada miki ne, sabon kuka na
saki na aza kaina a cinyarta, kuka nake yi sosai,
haba Dayibba ba tun yau ake lallashinki ba, shin
ba ki san aure shi haka yake kamar haßо ba?
Lokaci ne dashi, in Tahir ba mijinki ba ne za ki
ga ranar ko ta daurin aure ce a fasa don ba mai
auren matar wani haka ma mace bata auren mijin
da ba nata ba, don haka ki kwantar da hankalinki
Dayyiba, ni dai ban ce komai ba, kuma ban daina
kukan ba, Mama Hadiza ta ce, ke Hauwa kin
manta yarinyar nan mai shegen taurin kai duk
maganar da za ki yi mata ba ji zata yi gara ma ki
kyale ta in ta gaji da kan ta zata daina.
Anti Badiya ta jeho min atamfa, karamar
super English a gabana, gashi nan ki nuna ma
kawayen ki in za su yi, anko din ranar yinin biki
ne, mikewa nayi na har wurin ina kara gunjin
kukan da nake yi, ina ji Mama Hadiza na
kyalkyatar dariya, tana yi min tsiya. Ni dai dakin
Gwaggo na shige na ci gaba da koke-koken da
37
Baki Bivu 2 Sameera Mustapha:
nake yi, ada ban dauki abin serious ba, amma
abun sai Kara zama gaskiya yake yi na ma ace ni
ba matarsa ba ce sai ranar daurin auren in mutu
ko a fasa.
Tun daga wannan ranar na kara figewa sai
kace kazar da ake cire gashin jikinta, na kara ta
da hankali na sosai, kayan lehen a washegari su
Amina da Aisha suka zo suka gani, Gwaggo
kuwa har da basu katin daura aure wai su
gayyato 'yan makarantarmu, ba yadda bata yi da
ni in diba in kai makaranta ba na ki.
Kwana biyu da kawo lehe sai ga Tahir ya zo,
abun haushi na shirya zan je Makaranta ina so in
fita da wuri ko da karatu in yi, sam bana iya
karatu sosai a gida saboda tunanin da nasa ma
kaina. Ina jin su suna falo da Gwaggo sai hira
suke yi na rasa yadda zna yi in fito saboda
dakina a cikin ta falon ya ke, na kai minti ashirin
ina shawarar yadda zan shiga falon wata zuciyar
ta ce, ki wuce kawai, wata zuciyar tana bani
shawarar in hakura har sai ya tafi tukunna, daga
sama na ji budewar daki na sai da gabana ya
tsinke saboda tsabar fargaba, Gwaggo ce ba tare
da ta ce min komai ba ta riko hannuna, ya ya zan
yi dole ne in bita, sai da muka kai gun zama
sannan ta ce ku gaisa ina zuwa.
Kaina yana kasa amma ina ji a jikina kallona
yake yi, muryarsa na ji yana cewa, 'yanmata
38
Baki Biyu 6 Sameera Mustapha:
babu gaisuwa ne ko ko kin dauki dayan side
dinne in fara gaida ki, haushine, takaici ne ban sani ba, turo baki nayi ina kuma wasa da gyalen
da ke kaina, kai wannan mutumin akwai kallo,
na tabbata ina daga ido za mu yi ido hudu dashi,
shi yasa na dake naki dago idon nawa, wallahi ban san sadda ya dawo kusa dani ba, maganar sa
na ji akaina, sai da na firgita daya ke muryar sa
irin mai girman nan ce sosai, dama ai shima ba karami ba ne yana da jiki ba laifi.
Ban san lokacin da na daga idona muka yi ido hudu da shi ba, da sauri na maida idona kasa, na kuma ce ina kwana? Bai amsa ba in ban da aikin
kallo babu abinda yake yi, kai wannan wane irin
mutum ne dama haka yake? Na tambayi kaina, to kurwa ta kur in kai maye ne, sai dai ka ci kanka,
don ni na fi karfin ka, jin nayi ya ce, dauko min
wayar da na aiko miki, tsam na mike wani irin
dadi naji dama ina tunanin yadda zan rabu da ita,
don duk abinda ya fito hannunsa bana so.
Shi kuwa a ransa burge shi take yi don ya lura
farar kura ce ta cika tsoro, ashe ba karamin aiki
zai yi ba ya lura da yanayin ta ko in ce ya
karanci bata ra'ayinsa, kallon da ta yi mai yasa
ya gano wani abu a kwayar idonta, murmushi ya
saki ya ce, Allah dai ya kawo ki hannuna za ki so
ni ne.
39
e Sameera Mustapha:
BaN Biyu
Ina zuwa na ajiye a gefensa, na koma can
kujerar Karshe na zauna, bai ce komai ba ya
dauka ya bude wayar yana hadawa, lebel nawa
ki ke? Ban tanka masa ba na yi shiru, ya ci gaba
da gyaran wayar sa shima ya yi shiru, sai da ya
gama na ji ya mike duk hankalina ya tashi don
naga alamar guna ya nufo, a take na soma jin
fitsari don tsabar fargaba, wayar ya ajiye a
gefena, ya ce amarya rowar murya ake min ba za
ayi min magana ba, ba komai akwai lokacin da
za ki yi ne, ta shi in ajiye ki Makaranta, Gwaggo
ta ce min za ki je Makaranta, duk da murya ta na
rawa na ce kai tafiyarka amma ni ba zan shiga
motarka ba, a kan me? Ya yi tambayar cike da
kasaita, Eyee! Mutumin nan da gaske yake yi, to
ban zan shiga ba....muryar Gwaggo ce ta tsinka
min tunanina, ki tashi ya rage miki hanya mana,
ni bana son Gwaggo na yi min haka, sai ka ce ta
san ba zan iya musa mata duk abunda ta bukaci
in yi ba, to ko ta gane ne, na ji yana cewa
Gwaggo bari in ajiye ta in dawo, Gwaggo ta ce,
to Allah ya kiyaye.
Dakina na shiga, sai da na shiga toilet na yi
fitsari sai kuma na fito na rasa ma abunda zanyi
da zai ba mutumin nan haushi, sai da na yi kamar
minti goma sha biyar sannan na fito shima din
don naga lokacin paper na karatowa ne.
40
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Na fita yana zaune a cikin mota, ko ina a kule
yake. B.M.W ce baka sai sheki take yi, gashi
ansa tinted glasses sai dai ba mai duhu ba, da
gangan na bude kofar baya na shiga na zauna ni
kaina naga kokarina. Na dake kuma sai kace
motata, muryar nan dai tasa na jiwo sai da na yi
shock kai muryarsa ta cika girma da yawa, ya ce,
ki dawo gaba mana 'yanmata, ina jin sa amma
nayi banza da shi, bai bata lokaci ba ya bude
motar ya fita, na daga kai ina kallon abunda yake
niyyar yi, kofar baya ya bude ya ce, kin san
Allah zan fasa kai ki kuma zan hana ki zuwa
Makarantar nan, wa ya yi losen? Ke! Don haka
kiyi abinda na ce ko hakan ya faru da ke ai ba
san lokacin da na fita ba kafin in shiga ya
tambaye ni ina wayar da na baki? Ba so magana
ba amma kuma na yi tunanin kada ya hana ni
zuwa Makaranta, na san idan ya furta hakan to
ko Makarantar zai hana in je ta baki daya. Tana
falo na fada ina gintse fuskata, ya tsaya kawai
yana kallona, ni kam juya masa bayana nayi ma
ina shafa littafin da na rike, zagayowa ya yi ya
ce, ki je ki dauko wayar nan, ko in yi abinda na
yi niyya.
A gaskiya tun kafin ya yi magana kwarjininsa
da girmansa sun takura ni, da sauri na bar wurin
na koma na dauko wayar, ina shiga ya ja motar,
ba wanda ya yi magana na tambaye kaina haka
41
Baki Biyu @ Sameera Mustapha:
yasan makarantar, na cije nayi shiru sai tafiya
yake yi da abun ya ishe ni shine na ce Kaduna
University fa nake, ya juya kan mota muka
kama hanyar Makarantar, a raina na ce lallai
mutumin nan yana so ya ce wani abu, muna isa
cikin Makarantar da saurina zan bude kofa,
amma ta ki ta bude, ya ce babu ma godiya za ki
fita? Na gode na fada da sauri. Batun wayar da
na baki ki sani idan na nema naji ta a kashe ko ki
ki dauka zan yi sanadin da za ki daina zuwa
Makarantar nan don dama ni ba son ta nake yi
ba. Harararsa na yi, ki harara da kyau na dai fada
miki.
Har na fita daga motar ban kara kallonsa ba,
zan wuce ya ce, karfe nawa za ki gama lectures
din? Na so in yi banza dashi amma sai na tuna da
maganar Makaranta da ya yi min, don haka ba
tare da na kalle shi ba na ce, ai za'a zo daukata,
ji nayi kawai ya wuce da motarsa, na ce a fili
kamar yana ji na, wai shi wannan mutum me
yake nufi so yake yi ya takura min, to wallahi ba
zan dauka ba, yau dole ne ma in yi wa Gwaggo
maganar Makaranta ta ai samu na ya yi ina yi zai
zo da kakalensa na iya yi ya ce ba zan zo
Makaran....Amina ta taba ni a bayana, lafiya?
Da ke da wa ki ke magana? Mtsss na ja wani irin
tsaki mai tsawo na ce bari ke dai wai wancan
mutumin da aka hada ni aure da shi bakin cikin
42
Baki Biyu Sameera Mustapha:
ci gabana a rayuwa yake yi, to wallahi zan yi
maganinsa danni ba zan yadda ba, wane irin ci
gaba ne ya hana ki samu wani illimin da nake
nema yake ikirarin zai iya hanani in ya ga dama,
to ta Allah ba ta shi ba, Amira ta lura, raina ya
baci da yawa, jan hannuna tayi zo mu je kinga
har kowa ya shiga class kin san fa wannan ita ce
paper karshe, sai da gabana ya fadi, na dai daure
na matse muka shiga aji.
A ranar muka yi paper karshe ina tunanin a
gaskiya jarabawar karshen nan sai Allah, don sai
na zama confuse baki daya na fita hayyacina, da
na isa gida ma rigima na rika yi wa Gwaggo, tun
tana kula ni har na bata haushi, kayan da na ga
ana shigowa da su shi ya kara sa na yarda lallai
ba karamin shiri suka dauka ba, duk wani tunani
ma ban san irin wanda zan yi ba. Dole na koma
'yar daki, da yake anan Kaduna za'ayi komai tun
ana saura kwana uku daurin aure 'yan biki suka
fara isowa ni dai ina daki na kule kaina a ciki,
babu kuma wanda ya bi ta kaina. Daya ke ba
wani event za'a yi ba da yawa ranar sa lale ne
ma aka shirya shi tamkar dinner, wannan aiki
Anti Badiya ne da Anti Fiddausi a ranar sai da
Gwaggo ta nuna min bacin ranta sannan na
yarda naje gyaran kai, Amina da Aisha suka raka
ni, Aisha ta dube ni tana min dariya, ban tanka
taba daina lura so take yi, in yi magana. Har aka
43
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
gama mun gyaran kan nawa a kumbure nake jira
kawai nake yi in fashe.
Tahir ya neme, ni a waya yakai so talatin
amma na ki dagawa, na kuma saka ta a silent
don haka ma wani kiran bana ji bana gani kai
tunda ma ya bani wayar bana daukar wayarsa.
Da daddare bayan anyi sallar Isha'i, zo ku ga
yadda gida ya cika fam da mata. Ni kuwa cikin
milk and chocolate colour na wani hadadden
material mai kyalli, aka shirya ni, a wurin shirin
ban da ikon in ki dan Gwaggo tsaye tayi a kaina,
Anti Nafisa ita ke yi min make up. A gaskiya
nima kaina ban gana ni din ba ce don na yi kyau
sosai tamfar ba ni ba. A gaskiya an shirya shi
sosai an kira mata masu kidan kwarya aka cashe,
ni abunda ya fi daga mun hankali na shi ne,
yadda Anti Suwaiba tasha rawa, kowa ma na
mamakin wannan al'amari, ikon Allah, ta lika
min kudi 'yan naira dubu-dubu da dari biyar
babu iyaka, kowa kuwa sai san barka suke yi
min akan nayi dacen kishiya, ni kam a raina
tausayin ta nake ji. Hotuna munyi-munyi har na
gaji, haka aka ci aka sha aka raba alherin da aka
yi na auren aka watse.
Washegari ne akai yi min kunshi mai dan
karan kyau har da stones aka sa min da yake
dama ina period. A ranar tare da abokaina muka
wuni.
44
Washegari kuwa karfe goma da rabi na safe
aka daura aurena da Tahir, anyi haka ne don a
ranar ake son a wuce da ni Abuja. Ai kuwa karfe
hudu da rabi na yamma muka isa, nan ma wani
taron Anti Suwaiba ta hada min na musamman,
kayan sawa ma iri daya muka sa, sai da dan ni na
saka ashoke ne a kaina da kuma kuguna. Kowa
na yaba hali irin na Anti Suwaiba, da yake baza
ayi dinner ba, kafin takwas na dare an watse sai
ni da abokaina, Aisha da Amina kam mazajen su
suka dauke su, tare da abokaina muka kwana.
Washegari breakfast sai da muka tsalake babu
abunda ba ayi ba, da yake su Anti Badiya a guest
house din mijin Anti Fiddausi suka sauka, sai da
aka yi sallar Azahar tukunna suka shigo gidan,
sun ja min kunne kamar yadda iyayena suka yi
min nasiha, na dube su ina kuka na ce, Anti in fa
akwai abunda ke damuna, meke damunki? Sun
tambaya duk a lokaci daya, Baba fa ba ta zo
bikin nan ba don ban ganta ba, na kara fashewa
da kuka, anti Nafisa ta ce, gaskiya bata samu
zuwa ba sai a ranar daurin auren suka zo tare da
Baba, hala ba ku hadu ba da aka kai ki gun Baba
lokacin. da za'a taho nan Abuja? A'a, ni ban
ganta ba, to hala Baba na bari a ganta ne aka
gaya miki? Ai ko mu ma bamu gantan ba ko irin
nasihar nan da ake ba dawa sai dai su Gwaggo
suyi, amma ita kam gudu take yi na tsayar da
45
Baki Biyu Sameera Mustapha:
nan, na tsuguna gabanta ina lallashinta. nima
hawaye ya zubo min, daga sama Tahir ya shigo
dakin amma yana daga bakin kofar dakin, Anti
Suwaiba na ganinsa ta hau zaginsa, Allah ya isa
tsakanina da kai mugu azalimi, kai wane irin
mutum ne wai? Iye ina tambayar ya za'ayi ana
kawo yarinya za ka nuna halin ka gare ta, to sai
Allah ya saka min, bai jira ta gama ba ya wuce
abunsa, ta dube ni tana cewa, sam ban so ki ji
abun da ke faruwa ba Dayiba, amıma ya zanyi
zafi ya yi zafi dama haka yake Anti? Na fadi
hakan muryata na rawa don a gaskiya hankalina
ya tashi, ni na san bai da halin kirki, saboda
mahaifiyarsu haka take da mugun hali....Anti ta
tsinka min tunani, ta ce kada ki damu 'yar uwa,
wata rana sai labari zai daina ne, amma Anty
shekararku nawa da auren bai daina ba? Ai kuwa
sai ta soma shekarar mu ta takwas kenan amma
kullum dukan safe daban na dare daban, ni na
ma manta yaushe na ga dariyarsa, yana da
mugun hali da baki zato in kin ganshi a hili za ki
ce gentleman, amma wallahi mugun mutum ne,
baya da imani ko kadan, gashi da 'yanmata waje
ba ya iya kula da iyalansa amma su 'yanmatan
sai su ci mai isarsu, ko kinsan wani lokacin har
gidannan yake kawo su? In kuwa nayi magana a
gaban su zai ci min mutunci har da duka ma.
47
Baki Biyu Sameera Mustapha
Mun sami kusan awa biyu tana bani labarin
Tahir, ji nayi ina bala'in tsoron sa, ni na sani
namiji namiji ne, to wai auren dole ne? ni dai a
rayuwa ta ba zan taba dacen miji ba, ga tsoron sa
ga tsanarsa duk a tare dani, ni dama bana kaunar
namiji mai duka, to dole ne in kama kaina, zan
san yadda zan yi insha Allahu sai ya rabu da ni
ba zan iya ba.
Da ta lura na shiga damuwa sosai, sai ta dafa
ni ta ce, kada ki damu ba zai kasance a kanki ba,
amma iyayenki a gaskiya basu yi zaben kwarai
ba, sai dai kila ya daina.
Ranar sukuku na wuni kamar wadda kwai ya
fashewa a ciki, da wuri na nemi duk abunda nake
bukata na shige daki, na kulle da makuli.
Suwaiba kam tasan ta kulla mugun abu, don
haka sai ta rika kyalkyatar dariya, tana tafa
hannunta a can cikin dakin ta. Ta san ta gama
tsoratar da Dayiba, wayiwa! Ta fada a fili sai
naga karshenki, ta tuna a jiya da yamma sako
taje karba a tashan Abuja daga gun Mama, ita fa
so take yi ta nakasa Dayiba wajajen bayan
magariba ta zuba magani a bakin kofar dakin
wai idan ta taka to ta takan amma tsab ta ganta ta
shigo falonta, dalilin kukan ta kuwa shine, Tahir
na shigowa gidan ta bishi dakinsa, da ya ganta
ya gani a fuskarta, masifa ce tafe da ita don haka
sai ya share ta ya ci gaba da abunda yake yi. Ta
48
Baki Biyu Sameera Mustapha:
sami wuri kan lazyman cushion dinsa ta zauna
tana kallonsa, can dai ta ce, ango kasha kamshi,
hala saurin me ka ke yi ne naga kamar zaka tashi
sama? Ta yi mai tambayar da alamar ta zo da
magana, ya dube ta yana murmushi, a'ah ke
kuma mutum ya yi aure ai dole ya yi sauri ya
sami ni'imar amaryarsa, ta kai hannunta kan
kirjinta don ji tayi kamar zai fito waje don tsabar
bakin ciki, me kake nufi? Ya sake dubanta ban
gane me nake nufi ba, amarya ke jira na fa ba
kema kin kira ni baka kusance ni ba sai da na
kusan shekara gidanka? Cewa fa kayi na riga da
na gama yawon gantali, itama ai haka ne don
haka ba zan yadda ba itama haka zaka yi mata
don da alama mata fini yawon iskancin don na
lura gogaggiya ce gata dama fara ce to ai fararen
mata yawancin su....ya katse ta, ke bana son
zancen banza, kina jina ko tun shigowar ki na
lura kin shigo da shirin ci min mutunci, to ba zan
dauka ba, kin gane ko, na fada miki tun farko
auren nan ba na yi ba ne don in wulakanta ki ba,
Suwaiba insha Allahu zan kwatanta adalci
tsakaninku, dariya na fitar hankali ta saki,
adalci? Ta tambaye shi kai din ne zaka yi adalci?
Ta sake tambayarsa, tare da girgiza kanta ai ni
bana yadda da duk shirin ka in fada maka, ni fa
na fada maka tun farko bana shearing din da
namiji, saboda ni haka har ya hana ta ci gaba da
49
Baki Biy Sameera Mustapha:
magana, ashe za mu gani dani dake wa zai fadi
gaskiya, kuma waye mai ikon gidannan ina zaton
ni ne? to bari ki ji in fada miki duk iya yin ki
kiyi amma ni kuma ni ne mai yin abunda na yi
niyar yi in kin ga dama ki zauna in kin ga dama
ki tafi duk abunda ki ka shirya ma kanki ki
aiwatar ke ki ka sani.
Ni kake fadawa haka? To ni kuwa zaka gani
sai ka san ko ni wacece, sai ka san ni mace mace
mai 'yanci a rayuwarta, abunda na zaba shi zan
aikata. Ta wuce fuu tana gunguni ya bita da
kallo, anya yarinyar nan tana da hankali kuwa?
Ya fada a ransa, ko da ya ke laifinsa ne da ya ki
daukar mataki akan ta tun farkon yana gama
tunanin shine ya wuce dakin Dayiba yana murda
dakin ya ji shi gam har sau biyu yana gwadawa,
ya san ayi haka don ya lura itama yarinyar 'yar
tsiwa ce. A sanyaye ya bar gun ya fice daga
gidan baki daya don tsabar takaici gun
Christiana ya wuce.
Bai shigo gidan ba sai da asuba har ya shiga
dakinsa ya yi wanka ya yi sallah ya ji ihun da
Suwaiba ke yi har a ransa ya san shiri ne shi yasa
bai bi takanta ba sai da ya gama shirinsa tsab
sannan ya fito dauke da suit case dinsa da ka
ganshi da kaga ya yi shirin fita office. Yana isa
kuwa ya ganta tare da Dayiba, ya karanci tsana
daga idon Dayiba, yasan Suwaiba ta riga da ta
50
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
hada boom da. haka ne ma bai nemi sanin komai
ba, ya yi ficewarsa, yana tunanin ta inda zai
bullowa wannan al'amari.
Washegari ma ina kwance da asuba kamar
jiya naji ihu, yau kamar abun yafi na jiya don
cewa take yi, na shiga uku jama'a a taimake ni
na shiga uku na lalace zai kashe ni...." Ai ban
san lokacin da na kara shigewą cikin bargona ba,
gabana kuwa kamar zai fito don tsoro, kuka na
saki ina tausaya wa kaina, can na ji an yi shiru
don haka na yi tunanin ya fice na bude kofa a
hankali ina leke, babu kowa na fita na kulle
dakina da hanzari na isa dakin Suwaiba, yau ma
a kasa na ganta zaune duk ta fita hayyacinta, na
karaso gunta ina yi mata sannu, sabon kuka ta
saki, nima sai na bita mukai ta kuka sai da ya
ishe mu, ta riko hannuna ta ce, Dayiba kina bani
tausayi tun ba akai ko ina ba Tahir ya fara nuna
miki halinsa yau kwananki hudu a gidannan
amma kin fahimci abunda maigidanmu yake yi
na kara sakin sabon kuka ni nasan haka rayuwa
ta zata kasance ba zan taba kaunar da namiji ba
har in mutu, ban gane ba Dayiba ai a take ban
boye mata komai ba akan mazajen da na so a
rayuwata suka ci amanata, ta dan rungume ni ta
ce, kada ki damu sai dai ina yi mana jajen auren
mutum irin Tahir, saboda dai a gaskiya ke
yarinya ce karama bai kamata ki fado irin
51
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
hannun namiji irin wannan ba, saboda sam
jikinki bai saba da wahala ba, tabbas hankalina
ya yi bala'in tashi, tsanar Tahir kuwa karuwa
take yi a zuciyata, sai ka ganshi ka ce mutumin
kirki ne, amma ashe mugu ne, oh! Allah ni kam
na shiga uku ko sati ban yi ba amma bakin ciki
ya karu a rayuwata, a gaskiya Gwaggo ta cuce ni
ba kadan ba, ko da yake ba laifinta ba ne, bata
san ya canza ba a zaton ta yana nan yadda yake
da yana gunta to amma ai dama mutum kan
canza halinsa me yasa ba za ta fahimci haka ba?
Anti na ji ta tabo ni ta ce, kada fa ki sa wannan
abun a ranki tashi ki je kiyi wanka kin san har
yau ba a daina zuwa ganin daki ba, kada a shigo
a same ki haka. Na mike jikina duk ya yi sanyi,
na wuce dakina.
Suwaiba yau kam rawa take yi har da juyi, ta
gano Dayiba ta tsani Tahir tsab ta gani a kwayar
idonta, to sai kin bar gidan nan, waya ta dauka ta
bugawa Mama tana bata labarin yadda suka yi,
Mama dai ta tunasar da ita sharudan da Jilli ya
basu, na su shawo hankalin su baki daya ne, ta yi
shiru tana sauraren