An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
BAKI NIYU
HNL
by samira mustapha
HAUSAВООК.COM
2
BAKI BIYT
SAMIRA MUSTAРНА
Baki Biyu e Sameera Mustapha
HAKKIN MALLAКА (М)
Sameera Mustapha
GODIYA
Ga Allah (S.A.W), da ya bani fasaha da ilimin
rubuta wannan littafin, sannan ga Maigidana Alh.
Aliyu Sulaiman da ya ba ni goyon bayan rubuta shi,
sai ga Iyayena Alh. Mustapha Haliru Bulasa da
kuma mahaifiyata Haj. Fatima Yahaya, Allah ya
Kara daukaka ku, amin.
TALLAFI
Ina godiya gare ki, Halima K/Mashi, da ki ka tallafa
min, ki ka ba ni karfin guiwar rubuta wannan littafi,
Allah ya kara budi, Allah kuma ya barmu tare, amin
summa amin.
TUKUICI NE GA
Nusaiba Sa'id Moh'd, Najib Sa'id Moh'd, Anisa Sa'id
Moh'd, Abduljalil Sa'id Moh'd, Arif Sa'id Moh'd
INA KAUNARKU
Anti Murja Bande Sokoto, Mama Sa'a O.P.U
Hauwa'u Iya (lya mai kosai), Baba Abu
BUGAWA A NA'URAR COMPUTER:
NAFI'U SALISU
08038981211-07028573535
2
Baki Biyu
ه
N
a farko ina so..." Ya dauki waya
ya mika mata, "ki buga wa
Gwaggota ki bata hakuri akan
wulakancin da ki ka yi mata." Ta ce a ranta, “shi
wai wannan ba ya da mantuwa ne, abunda ya
faru wata biyar da suka wuce sai ya dawo dashi."
Ta karba ba tare da son ranta ba, ta buga don
dama number Gwaggo ce akan wayar, bugu biyu
ta dauka, hakuri ta rika ba Gwaggo wanda ya
dauki tsawon minti goma tana magana, bayan
sun ajiye ya ce, sai sharadi na biyu ina son ki
rika yi min abinci da kanki don bana son abincin
dan aiki, ta dube shi ban iya ba, zan koya miki a
hankali za ki ioya, ni na ke yiwa kaina abincin da
zan ci, ko a office in kin lura ina da kitchen a
ciki ni nake yiwa kaina, na kuma fi cin vegetable
kin gane, da sauri ta ce eh, ina ganewa, ina son
duk in za ki fita in sani, sannan ina son sai kin yi
sannan sai mu daurawa kanmu sabon aure ba
tare da kowa ya sani ba, in kuwa za ki tonawa
kan ki asiri shi kenan ni dai ba zan yadda in
kusance ki ba in ba Istibiradi ki ka yi ba, kin
yadda da sharuda na? ta dan kauda idonta gefe ta
me ka ke nufi da Istibiradi? Hmmn ba ki san
abinda ake nufi ba? Ta girgiza kanta, ban sani
ba, to ina so ki fada min gaskiya tsakaninki da
Allah ba ki taba having sex ba? Gaban ta ya fadi
sosai, ta ce No!no! tana girgiza kanta ban taba ba
3
Baki Biyu Sameera Mustapha:
cike da mamaki ya ce, za ki rantse min? eh,
kwarai zan rantse maka don wallahi ban taba
kwana da da namiji ba a rayuwata, ta shigo sosai
cikin jikinsa, abinda ta fada shi yasa jikinsa ya yi
sanyi har ya biye mata. A nan falon ya murje ta
ta murje shi son kasance cikin jin dadi sai da
suka natsu sannan ya dube ta ya ce shekarun ki
nawa? Ta amsa çike da jin dadita ce, ashirin da
tara ya tsora mata ido tabbas gaskiya ta fada, a
ransa ya ce, to ko shi yasa bai same ta cikakkiyar
mace ba, bai sani ba ta talafo habarsa ta ce,
Dolly kai fa shekarunka nawa? Ya yi dan
murmushi, ya ce talatin da uku, don't tell me
shekaru hudu kawai kaba ni yes! Shekaru na
kenan, tun daga ranar suka sami junansu, shi dai
yana biye mata ne ba don komai ba sai don tayi
masa rantsuwa, sannan shekarun ta sun yi nisa.
Kwanciyar hankali sun samu, don a kullum
suna tare a kicin suna girki, har ta soma iyawa
kuwa soyayya sosai suke yi, a kullum kuma suna
tare ita tasan Tahir namiji ne dole ne kowace
mace ta so shi don yana da komai da mace ke
bukatar namiji ya samu, gashi kyakkyawa ga
halitta sannan gashi gentleman babu ruwan shi
da matar da bata shi ba, ita ta san tayi dacen miji
wani gefe na zuciyarta kuma sai ta tuna da
Jessica kawarta kuma aminiyarta, da sauri takan
kauda tunanin Jessica, koda yaushe tana cikin
4
Baki Biyu Sameera Mustapha:
koyon girki sai dai shi ya rasa dalilin ta na rashin
iyawa, a haka dai yakan faure ya ciko ya dan yi
kuskwarima sannan ya ci.
Sun sami kamar shekaru uku suna soyayyar
su a cikin shekarun ne suka haifi Nana Asma'u,
a haka dai suke sai dai ita a wannan lokacin ta
daina girki don ko ta girka baya ci, to meye
amfanin girka masa, sannan bata son Gwaggon
sa, shi yasa suke samun matsala, ita kuma a
ganin ta tunda ta samu Asma'u me ruwanta
dama ta riga da ta sa wa ranta, da ko diya daya
tal zata haifa, ta bata tarbiya da ilimi da zai
amfani yaron, tun da ta haife ta, take allurar
planing sam bata wasa, duk bayan wata uku tana
zuwa ta yi sai dai bata fada mishi ba, kai kowa
ma bata fada ma ba.
Suna da shekaru biyar da aure, Jessica Jojo
wato abokiyarta ta America, wadda aka fi sani da
JJ ta dawo cikinr ayuwarta, suna ganin juna suka
rungume junansu, suna shafan junansu sai kace
tare da namiji suke, ai basu tsaya ko'ina ba sai
bedroom din Suwaiba, sa'ar su daya ba kowa a
gidan, maigidan ya yi tafi. Asma'u kuwa tana
Makaranta. A nan suka murje junansu ka ce miji
da mata, ashe dama Suwaiba lezbiyan ce? Hmn
ikon Allah dole ne ta rasa virginity din ta ko ba
da dan namiji ba, kai wannan rayuwa ta yanzu
sai a hankali. Ko me suke sha'awa da junansu
5
Saki Biyu Sameera Mustapha:
oho! Tana mace kina mace, Ubangiji Allah ya yi
mana sassauci, ya shirye mu ya kuma kare
zuri'armu daga sharrin zina da luwadi, amin
summa amin.
Sai da suka natsu sai kuma Jassica ta janye
jikinta tana shan taba, tsab Suwaiba ta gano
laifin ta ta matso sosai cikin jikinta ta ce haba
sweeti am sorry, ban san yadda nima nayi saurin
canjawa ba kawai abun is a dream, domin ke kin
san ina ki, harara Jassica ta wurga mata ta ce,
dalla can bayan tun a America da ki ka hadu da
dan iskan mutumin nan ki ka share ni, ni na gani
a idonki a tun lokacin ki ka daina sona ni ce
kadai nake hauka a kanki gashi yanzu ma ai ni
na biwo ki, haba sweety kiyi hakuri har yanzu
ina son ki a kullum ina tunanin ki sai dai na san
ba zan samu halin komawa America ba ina
dawowa iyayena suka matsa min in yi aure. Тo
ba a can mun shirya yin aure ba ko kin manta?
Sai a lokacin ta tuna fa, lallai sun shirya yin aure,
to ya ya zata yi tunda namiji ya shigo rayuwarta?
Ita dadi ma ta ji da Jessica ta zo don yanzu za ta
sami wadda zata debe mata kewar namiji, don
dama ita ba gwanar bin maza ba ce. J.J kiyi
hakuri tunda yanzu kin zo, I will be with you all
my life I promise you. Jessica tana bala'in son
Suwaiba ya zata yi dole ta hakura ta rungume ta,
suka ci gaba da shashancinsu.
6
Baki Biyu Sameera Mustapha:
Tun daga lokacin Suwaiba babu ruwanta da
harkar Tahir, don boys quarters ta sa aka
gyarawa Jessica, a can suke haduwa su sha dadin
su, shi dama maigidan tund aya ga Jessica ya san
ba karama ba ce, dole yasa ya barta gidan don
kada shi bai da kirki sai dai ko in kallan da
Suwaiba keyi masa ya soma damunsa, dole ne ya
shiga damuwa tunda shi mai bukata ne, sannan
shi ba mai neman matan banza ba ne; tun tana
wulakanta shi ahr ya hakura ya daina biye mata
tun da dama 'yar buturiyarsa shima tana garin
don haka kowa ma ya ci tsinkensa babu babbaka.
Da abun ya yi yawa, sai ya kori abokiyar tata
daga gidan, akan dole ta bar gidan ba karamin
tashin hankali aka yi ba, don nacin Jessica ta се,
ba inda zata sai da ta kama mata gida nan kusa
da su, cike da sa'a kuwa suka samu, don haka a
kodayaushe suna tare.
Asma'u tana da shekaru bakwai a duniya ta
ce ga garin ku nan, ba wani ciwo ta yi mai jinkiri
ba, sai dai duk taimakon da Likitoci suka yi ba
su iya ceto rayuwar ta ba, a lokacin ne Christina
budurwar Tahir da Jessica suka hadu, ashe 'yan
uwa ne, kuma dukkansu abu daya suke so, wato
ita JJ tana tare da Suwai ita kuma Christina tana
tare da Tahir, abun ya basu al'ajabi, dama ita
Christina a London take da yake iyayenta anan
7
Baki Biyu Ο Sameera Mustapha:
suke, amma abun mamaki ba wanda ya fada wa
'yar uwarta sirrin ta. kannan su kan su basu
yadda da junansu ba don dama kowa ya san
matsayin kowa.
Suwaiba ta shiga damuwa sosai a wannan
lokacin diyar ta daya tal tilo da take ji da ita, ita
kaďai ce kwanta a wannan lokacin, shima Tahir
abun ya dame shi amma da yake shi namiji ne
dole ya fita dauriya, sun je asibiti har kala hudu
amma babu bayani, duk da ita kadai take zuwa
aka ce mata lafiya lau take, shi kan shi Tahir
abun na bashi mamaki, yadda za'ayi ace 'ya
daya ya haifa a rayuwarsa bai san matarsa ce
bata so ba.
Ana cikin haka zaman dai babu dadi a
tsakaninsu a koyaushe ya je da maganar gun
Gwaggo shi take ba laifin, ta kuma ba shi hakuri
shi ne fa ana cikin haka rannan ya dawo gida, ya
iske gidan a kulle da ya tambayi maigadin gidan
shima ya ce bai ma san fitar su ba, shi dai yasan
a kullum suna fita ita da wannan kawar tata JJ,
kenan yake nufi, dirshan ya zauna kan benchin
baba maigadi, tuni zuciyarsa ta rika harbawa don
tsabar bakin ciki, idanunsa suka juye zuwa ja, ya
yi kokarin danne damuwarsa amma ina, ya ce
Baba dama haka take fitan Baba ya dan yi shiru
ka fada min Baba, ka sani fa amanar gidannan na
baka, idan ba ka faďa min ba wa zai gaya min in
8
Baki Biyu Jance
dan san da fitar ta ko abunda take yi da ban
tambaye ka ba, dama aikin ka ka kula min da
amanar dukiyata da iyalina, ko ba haka ba?
Ajiyar zuciya Baba maigadi'ya yi, bai taба
son ya hada Alhajin da iyalansa ba amma shi
kanshi ya san tun ran gini tun ran zane, tun da
tun auren su ma matar bata da natsuwa to ya isa
ya fada ya bata aure. Tahir ya san abunda
Suwaiba ke yi ya yi nisa tunda har Baba maigadi
baya son ya fadi laifinta, inda ita matar kwarai
ce da tuni ya soma bayani, ya karanci baba, tsoro
yake ji ya fada masifa ta tashi a gidan, ya
sassauta muryarsa ya ce, Baba don Allah ka fada
mini tsakanin ka da Allah me Suwaiba take ciki?
Ba wai ka hada ni da ita ba ne, gyara nake son yi
don haka nake son jin abunda ke faruwa. Eh! To
a gaskiya iyalan ka ba wai ba su da kirki ba ne
sai dai matsalar su daya ce, irin kwashe-kwashen
abokai da suke yi, to irin abokanne ke juyar wa
da iyalan naka hankali. Baba kayi min bayani da
kyau ban gane ba...." Hon suka ji anyo kuma an
sa sauti sosai a motar, sai ka ce irin gayunnan
'yan shekaru sha biyar da suka fara balaga. Baba
ya mike zai bude kofar gate, Tahir ya dakatar
dashi, shi ya fita ta karamar kofa ya jiyo muryar
Suwaiba tana cewa kai dan tsoho ka bude min
gate mana me ka ke nufi? Da yake dare ya yi
sosai, don karfe sha biyu saura a wannan lokacin
9
Baki Biyu e Sameera Mustapha:
ta lura ba ya da niyar budewa, don haka ta haska
masa wutar mota ful light kuwa, ji ta yi kamar ta
saki zawo ba ta taba tsammanin Tahir ba ne, a
take ta kashe wutar baki daya ta ma rasa me zata
yi, da saurin ta ta kashe sautin da ke tashi jikin ta
tuni ya fara rawa, Jessica ta ce, meye haka? Ya
za ki kashe min waka, da jin yadda take magana
a buge take shi bai iso gun su ba, shi bai bude
masu gate din ba, to me yake nufi ne? Suwaiba
ta fada a fili, JJ ta ce, ke wai na lura tsoron dan
iskannan ki ke yi, da ni ce ke da tuni na kashe shi
na huta, mutumin nan ya cika takura, haka kawai
zai rika maltreating din ki kamar 'yarsa, shin ba
ki san rights din ki ba ne? macen aure tana da
'yanci kema ya kamata ki nuna masa matsayinki,
its your life ba nashi ba da zai rika juya ki kamar
yadda ake soya kwai, ko da yake na ga fa a
Africa mace ba ta da ikon kanta sai abunda aka
ce da ita, shi zata yi, sai a lokacin Suwaiba ta
tuno fa da gaske ne abunda Jessica ke fadi, shin
me yasa mace ba ta da 'yanci anan, sai abinda
aka kayyade mata shi zata yi? Ta tuna a can
America abunda ta ga dama shi take yi, babu mai
takura mata, so nawa ma suna haduwa da matan
aure a club amma babu ruwan mazajensu, to don
me ita zata bayar da kanta, don kawai yana
mijinta humm miji? Ta sake fada tana 6ata
fuskar ta, ai ina wurin ta ne da shi da babu duk
10
G
Baki Biyu 2 Sameera Mustapha:
daya, don baya bata hakkinta a matsayin sa na
mijin aurenta.....Tahir ya katse mata tunani da
ta ga ya koma cikin gidan ya kuma rufe karamar
kofar a tunaninta ya hakura, sai kuma suka ji
shiru sun sami tsawon minti sha biyar suna hon
amma ya yi banza da su.
Su koma inda suka fito, ya fada a zuciyarsa
yasan matakin da zai dauka, zai yi maganin
wannan masifar, dama abunda ya so ya kauce wa
kansa kenan tun lokacin da Mama ta ce ya auri
Suwaiba, na daya baya sonta, na biyu ba ta da
tarbiya, na uku bata da addini, tun da suka yi
aure bai taba ganin tayi sallah ba. Sau da yawa
yakan yi mata dubara suyi sallah tare randa bai
ce su tare ba to fa shi kenan rannan ba za ta yi
sallar ba, daga karshe kulle gate din ya yi da
kwado ya shige gida abunsa.
Sun kai minti talatin a gun suna buga kofar
gidan, kafin dai daga karshe suka hakura suka
tafi. Washegari da safe ma Suwaiba ta zo gidan a
kulle ta kasa karasawa ma cikin gidan. Ana cikin
haka sai ta wuce gidansu, tana kukan munafurci,
kai mace-mace sai Allah.
Karya da gaskiya ta shirya ta fada, shi
mahaifin nata har ya soma gajiya da matsalar
aurensu, ya dai saurara amma bai ce komai ba,
daga karshe dai ta matsawa mahaifiyarta ta buga
mashi waya ya zo aji dalilin sa na kulle gida ya
11
Baki Biyu Sameera Mustapha:
barta. Haka kuwa aka yi, da ta nemi wayar a
kashe take duka wayoyinsa a kashe. Ta rasa inda
zata sa kanta don tashiga uku idan iyayenta suka
gano matsalar da ake ciki, gashi ita dai zuciyarta
bata sha'awar rabuwa da shi, don a gaskiya duk
macen da ta sami miji irin Tahir ta gama jin.
dadi, duk da ba ta kyautata mishi tasan yana iya
hakuri da ita, abunda ya fi bata haushi shi ne,
yadda yake nuna mata rashin so kiri-kiri, shi sam
bata gabansa, ko suna tare sai dole ya
zamaninshi ba don yana ra'ayi ba. To amma duk
da haka bata taba kawo tunani rabuwa dashi ba
don tasan mutuncin ta a idon iyayen ta shine
zama da miji, don haka Jessica ma kauda mata
sha'awa, amma ko kusa bata kai matsayin Tahir
a gunta ba shi yasa ba yadda Jessica bata yi su
gudu wata kasa da ba za a taba zaton zata ba ta
ki.
Ta sami kusan kwana hudu a gida amma
babu labarin Tahir, hatta Mama nemansa suke yi
ruwa jallo amma ba su samu ganin sa ba, abun
mamaki ashe Tahir na Kaduna gun Gwaggo,
yana yi mata rigima akan zai yi aure kuma ita
yake son ta sama masa mata.
Wani tunani ne ya fado wa Suwaiba, akan
bari ta je Kaduna ta gani ko yana nan a can,
karya ta yi wa mahaifinta akan Gusau zata je
Mama ta ce ta je can, dama shi ido yasa mata
12
Baki Biyu 2
Cmnra Miictanha:
Sameera Mustapha:
don ya gaji da shari'ar, ba Gusau ta je ba Kaduna
ta wuce cike da sa'a kuwa ta sami Gwaggon
gida, kuka ta fashe mata dashi ta rika ba Gwaggo
labarin gaskiya da karya, ana cikin haka ne Tahir
shima ya shigo har ya juya zai fita, Gwaggo ta
bashi umarnin shima ya sami wuri ya zauna a yi
ta ta kare, duk da abun ya dagawa Suwaiba
hankali sai ta dake ta kara maimaita abinda ta
fada wa Gwaggo, shi kam Tahir kansa yasa a
kasa yana sauraren wannan shiri na Suwaiba, sai
bayan ta gama Gwaggo ta dubi Tahir ta ce,
"tsakaninka da Allah haka labarinnan yake?" sai
da ya dubi kwayar idon Suwaiba, ya ce Gwaggo
a dauko Alkur'ani mai girma kowa ya yi
rantsuwa." Gwaggo tayi ajiyar zuciya tana yi
masu magana a hankali, itama kanta abun ya ishe
ta daga karshe dai ta ce, tana son ta ji matakin da
Tahir ya yanke don bata son su tafi su kara
dawowa, don haka don Allah su yi hakuri da
junansu, a lokacin Tahir ya ce Gwaggo ni aure
zan yi buzut! Suwaiba ta mike kamar kazar da ta
taka wuta, tana wani gintse fuska tare da girgiza
kanta cike da mamakin furucinsa, mene ka ce?
Ta fada a kasaitance, aure! Uhmm ana shirin yin
abin tashin hankali kuwa, kara maimaita kalmar
ka in ji, bai tanka mata ba, to ka kiyaye ni, kana
ji na ka kiyaye ni don ni fa da ka ke gani ba
kanwar lasa ba ce, ina fata da wasa ka ke yi?
13
Baki Biyu 0 Sameera Mustapha:
Gwaggo sake baki tayi tana kallonta, a ranta
kuwa mamaki ne, menene oho ma ta rasa me
take ciki, Suwaiba ta tsinka mata tunani da ta ci
gaba da cewa, wallahi ba zan yadda kayi aure ba,
don ni bana iya shearing din namiji da wata don
da za a halicce ni ma ni kadai aka halitta ka sani,
ta nuna kanta, ko a gun iyayena bana da 'yar uwa
ni kadai ce mace. Tahir ya katse ta a'ah ina ce ke
kadai aka haifa ashe baki kai ba, ke bari in fada
miki baki isa ba, kin yi kadan ke nama sake ki
saki daya, ki je in kin samu miji ma kiyi aure, ba
zan zauna da ke ba..." Haba Tahir, Gwaggo ta
mike tana salati, ranta ya 6aci sosai a gabana a
gaskiya ban ji dadin abinda kayi ba, ke!ke!!ke!!
Suwaiba ta katse ta, munafuka ai ke ce sanadin
komai..." maganar da bata karasa ba kenan ta ji
ajiyar mari a fuskarta, tas!tas!tas! ka ke ji, sai da
ta fadi kasa, zai kara dukanta, Gwaggo ta tare
shi to shi ne fa ta bar wurin a guje ta banke kofar
falon ta fice daga gidan.
Gwaggo fada sosai ta yi ma Tahir, sam bata
saurari abunda ya ke so ta fahimta ba, sai bayan
sati daya da ya yi tafiya ya dawo ne, Gwaggo ta
saurare shi da yake ta sauko, Gwaggo ya kamata
ki bani dama in fadi abunda ke damuna, at least
na yi hakuri na kusan shekaru tara amma ban
samu nasara ba, don Allah Gwaggo ki tausaya
min ki taimake ni in samu farin cikin da nake
14
Baki Biyu 2 Sameera Mustapna:
nema nima fa mutum ne ina da feelings, ajiyar
zuciya Gwaggo ta yi, tunda yake magana ji take
kamar ta zubar masa da hawaye don sosai ya
bata tausayi, tabbas yana bukatar canji ko zai
samu sassauci daga lokacin da suka rabu har ya
yi rama sosai, don haka ta saki fuskar ta da fara'a
ta ce, haba dana sai ka ce ba namiji ba, to shi
kenan naji kaje kayi auren Allah ya sanya alheri,
bai san lokacin da ya dawo kusa da ita ba, farin
ciki kuwa tamkar ya zuba ruwa a kasa ya sha,
hakika kana neman sauki Tahir, amma ina so ka
maida Suwaiba dakinta kafin kayi aure. Zan
maida ta Gwaggo na gode da hadin kan da ki ka
bani, na gode, amma fa ke za ki zaba min matar,
ayi haka kuwa dannan? Eh, mana Gwaggo
kinsan za6in Mama ce Suwaiba, yanzu kuma
zabinki nake so. To shi kenan dan albarka, zan
nema maka da sharadin in har na nemo ta babu
fashi, da ita din dai za'ayi, babu fashi Gwaggo
ko ya ya take na amince. To shi kenan ka bani
lokaci.
A ranar ya bude ciki ya ci abinci sosai. Tun
da ya auri Suwaiba jin dadinsa ya kau, ya ma
manta shi yasan zabin Gwaggo shi ne daidai da
shi, ba za ta yi masa zabin tumun dare ba, ya
bala'in yadda da ita, ya tabbata ba za ta zabo
masa 'yar marasa tarbiya ba. Allah sa a dace
(amin summa amin).
15
Baki Biyu 2 Sameera Mustapha:
Bayan ya samu natsuwa, Gwaggo ta ce, su
shirya su tafi Gusau don Suwaiba na can gara ayi
komai akan idon su, komai ma ya kare, hakan
ya yi masa dadi kuwa.
A babban falon Alh. Mohd Sani Shinkafi aka
taru har da mahaifin Dayiba Mal. Sabi'u, tunda
aka yi auren Tahir baban falo bai taba shiga
harkar auren ba, sai a wannan lokacin. Sai da ya
ba wa kowa damar magana, a karshe dai ya dubi
Tahir ya ce, Tahir na san ka da hakuri, då gudun
zuciya. Ni dai shawara ta gare ka ka kara hakuri,
idan kuma auren zaka yi ka yi adalci.....ihun
Suwaiba ya katse ma falon Baba maganar da
yake yi ta fashe da kuka, tana magiyar ita baza ta
yadda ba. Tuni ita ma Mama ranta ya baci ta
lallabi hannun 'yarta ta suka bar falon. Baban
falo dama yana tur da irin tarbiyar Suwaiba
tunda ya ganta yasan ba 'A' ba ce ta kai 'Z' a
lokacin ya cewa Gwaggo to ke fa Tahir ya ce ke
ya bar wa zabin mata, ina fata kin samar masa?
Ta yi murmushi tana duban Mal. Sabi’u, ta ce ai
ni auren gida ma nake son dan nawa ya yi, ba
kuma kowa na zabar masa ba sai 'yar kanwata
Dayyiba!" Ba Tahir kadai ya saki baki ba har da
mahaifinta, don abun ya zo masa a ba zata, Tahir
yana dubanta ya ce, dama Gwaggo akwai aure
tsakaninmu? Sosai ma, ka mance cousin dinmu
ce? Ba mu haďa komai da ita ba mahaifiyarta ce
16
Baki Biyu Sameera Mustapha:
'yar uwarmu, itama cousin din mahaifinmu сe,
ikon Allah zuciyarsa tayi fari tas, bai san mi yasa
ba wani irin farin ciki ke shigar sa ta ko ina a
jikinsa, a idonsa kuwa ya ma manta yadda
Dayyiba take, don sau biyu kadai ya ganta. Sai
dai ya lura yarinyar akwai ji da kai, to amma sai
ya samu natsuwa da kwanciyar hankali da zabin
Gwaggo, Allah ya sa haka ya fi zama alheri.
Haj. Hauwa ta lura Mal. Sabi'u ya shiga
damuwa, ta gyara murya ta ce, Baban Nafi'u
(haka take kiransa) anya shirin nan ya yi maka?
Ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce, a'a wane ni, in
ce bai yi min ba, babu abunda zan ce sai fatan
alheri, a rayuwa ta ban ga abunda zaku bukata in
ki yi muku ba, bana fatan in taba kin duk wani
abunda za ku nema a guna, don ni ban ga