na leko na yi mata sannu na
turo kofata na kulle na koma na kwanta Sharif ya zo ya yi ta bugun
kofar haba Suhaila dan bude mun mana ina shiga ma zan fito kin ga
56
a
a lun xuwanki gidan nan sau biyunc kawai na yi, ki yi hakuri
mana, da gudu matar Sharif ta nufi sashin uwarshi tana cc mata to
gashi nan ya je yana buga mata kofa zai hanamu barci ni da yara,
sai na ji motsin uwarshi da saurinta da alama tana rike da sanda
hannunta don naji sanda ta kwada mishi maza ka tali dakin matarka
gata can tana jiranka wannan yarinya da ka like mata in banda
jarabarka da rakumanka ashirinka ka karba ka basu ita suka tafi da
ya liye maka sai ka bayar da rakumi biyu ka auri wata ka ga ka
samu sauran sha takwas sakarai ko inna majandicc ita ba zan yarda
da wannan sakarcin naka ba, haka ta turashi dakin matarshi ta kulle
kofa.
Washcgari ina zaunc a dakina ina goge hotona da babana da
Yaya Ahmad sai ga Sharif ya shigo na yi wul'na suri kwano zan fita
kamar zan kaishi wani wuri sai Sharif ya cc a'a dawo ki zauna ba
zama nazo yi ba balle ki gudu ki barni takardar saki na kawo miki
na sakcki ungo takarda ki kaiwa babanki llamza tunda kin ki ki
rinka bar mun kofa a bude to gara ki tafi kawai ku je gidan Hamza
in kinga can din ya ſiye miki dukan da zai rinka yi miki ma kadai
ya isheki don zan tsaya inga ya biyani rakumana daya karba tunda ni dai ban mori komai ba a jikinki kwanta kwata ya tashi ya fita ya barni a zaune rike da takarda na kasa fahimtar dariya zan yi in yi
murna ko kuwa ihu zan yi in fashc a kuka? Ga takardar saki na
samu bayan na rasa wurin zama Mallam Ahmad ya rasu gidan baba Hamza ba zai zaunu ba a wurina ba sai an gayamun ba to amma yanzu a halin danake ciki ina na dosa?
Ina cikin wannan lunani sai ga uwar Sharif da saurinta tana tambayata zaman me nakc yi har yanzu ban tafi ba ko kuwa a
gidanmu naga ana zaman aurc ba tarc da ana baiwa maigida hakkinshi a shimfida ba? Ban ce mata komai ba jikina a sanyaye na tashi na gyara bujen sikct dina kudina da zinarina tarc da warawaran inna suna ciki na dauko zanin inna da na lullube hotona dashi na lullubeshi na rungume ina waige waigen abinda yake
lafiyarki
dakin sai na ji ta sake cewa fito mana gani nan fa ina jiranki in ga idan kajinki da talo talonki kike lissafi zan rinka kula dasu har kafin babanki ya gama biyan Sharif rakumanshi sai ki zo ki kamasu.
cike da
zullumi
Ina rungume da hotona na kama hanyar Bengazi zuciyata da tsoron abinda zai faru inna je na cewa baba 57
lamza aurcna ya mutu ko me zai faru dani oho? Na tuna Mallam
ballc a
Ahmad yana nan ma irin dukan da baba Ilamza yakc mun
yanzu da baya nan, ina cikin tafiya a dajin sai ga Sharif a zaune kan
wani dutsc a gefen hanya gabana ya sake faduwa ban san me zai yi
mun ba, sai naga ya saki murmushinshi mai kama da yake ya ce zo
nan Suhaila zo mu shirya kinga ina sonki bana son sakinki mamana
ce ta sani na sakeki amma in kin yarda zamu rinka yi ko sau daya
nc a wata zan hakura a hakan sai kawai in rinka yin mancji da
uwargidana tunda ita ta saba dani har kafin ranar na ki ta zo bana
son tafiyarki Bengazio gidan IHamza kc kadai Hamza mugunc na yi
shiru ina jin Sharif na san gaskiya yakc gaya mun, to amma shima
mugun ne don tare suke dukana shi da baba Hamza, sai dai na sami
muguntarshi bata karasa ta Baba Hamza ba, tsawon lokaci yana
rarrashina har zuciyaša ta soma saduda kamar in bishi mu koma
gida sai na tuna nasihar da teacher Hakecm ya taba yi mun ya ce
"Ahways take a stand on what you believe is right never believe in
what others believe in." Ma'ana rinka tsayawa ki dage kan abinda
kika yarda shi ne daidai kar ki yarda da abinda wasu suke ganin shi
ne daidai dinsu na kalli Sharif na ji tsoron ce mishi ban yarda da
jawabinshi ba don ganin daga ni sai shi ne acikin dajin, na ce to na
yarda Sharif amma yanzu-idan na bika muka koma mama zata san
kainc ka biyoni ka bani hakuri don haka bari in je gida sai baba
Ilamza ya dawo dani ya ce yauwa, Suhaila kin yi tunani to bari in yi
miki rakiya in fiddake duhun bishiyoyin can kinga ai yamma ta yi,
na ce to.
Ina shiga gidan Baba Hamza shi na fara gani yana ganina ya
zaro ido cikin tsawa ya tambaycni me ya kawoki yanzu? Na
tsuguna na gaisheshi ya sake tambayata dalilin zuwan nawa, jikina
yana bari na gaya mishi Sharif ne ya sakeni. Saki? Ya sake fadi da
karfi ya zuba mun ido na wani-lokaci sai na ji ya ce ai dole ki yi
yawon aure saboda sakarci ya yi miki yawa ko uwarki abinda yasa
ta iya zama wuri kďaya don dan uwana ya yarda da zama bawanta
ne amma ai ni sanda yake raye kullum naje wurinku da bakin
cikinta nakc dawowa ta yi ta yi mishi shagwaba wai maimakon abin
ya bashi haushi sai kaga yana murmushi na zuba mishi ido ina
kallonshi, daina kallona kar in sa tsinke in karasa miki wadannan
holokon idanuwan naki sai aukin girma basu ganin komai ai kansu
58
1
a
a
a
D
i
e
mai sunan Malam ya zo zai mun rashin kunya wai da zamu taho an
gaya mun kina da lalurar ido amma da aka zo ba a sake kulawa an
kaiki asibiti ba, ya sosa kanshi yana cewa to ina fama da iyalina
yaushe zan ce zan kai wani ido asibiti tunda dai ba makancewa na
ga kin yi ba? Shi wannan ja'irin yaron ina jin in banda Bashir yana
nan da dukana ya yi, na san zai iya don duk cikinku shi kadai ne ya
yikama da uwarku ina jin halinta ya dauko, kafa mishi ido nayi ina
kallonshi ai ba za ki daina kallon nawa ba? Ban ce mishi komai ba,
ya ci gaba da wannan ai aikin banza ne ma acc Sharif ya sakeki ni
dai kinga ba zaki dawo mun gida ki zauna ba ba zan iya ba, ba zan
iya ba, yana girgiza kai nuna alamar ba zai iya din ba, ba kuma zan
barki ki koma can kasar ba ko don in rinka samun 'yan uwanki suna
zuwa kasar nan akan kari yanzu ina barinki kika tafi shi kenan ko
za su zo sai an dauki lokaci mai tsawo, tunda ila uwarku Allah ya
kashc ya bata an rainan mata 'ya'ya an mutu an bar mata ya dago ya
kalleni ai baki daina kalllon nawa ba, ya rarumo wata sanda zai
bugeni na yi wuf na karta da gudu na nufi hanyar gidan Sharfi ina
shiga duhu na koma na nufi lambun baba Sharif dake bayan
gidanshi na buya ina jinshi yana cewa fito maza Hindu mu bi bayan
wnanan ja'irar yarinyar mara mutumci har gida zan kaita sai mun je
gaban Sharif in bata kashi don kar ya dauka ina goyon bayan rashin
mutuncin da take yi mishi dama tun kwanaki ya fara gaya mun kar
fa in ga ta haihu in dauka wani morewa ya yi shi har yanzu in ta
bijire sai an bashi rakumanshija'irar banza tana nema ta jawo mun
tsiyar Sharifjimawa kadan sai na gansu sun fito su dukansu biyun
suna rike da dogayen sanduna sun nufi hanyar gidan Sharif cikin
sauri don kuwa dare ya fara yi gashi hanyar ba kyau ina ganin sun
yi nisa na fito da gudu na keta daji ina nufin bin duhun dare in yi
tafiya in samu in isa tashar jirgin kasa ko zan yi sa'a in samu jirgi
mai tafiya Sudan in shiga, tafiyanake yi babu tsayuwa, bana kuma
waiwaye don tsoron abinda zan gani a bayana, kara kutsawa nake yi
cikin dajin yana kara bani tsoro sai dai babu yanda zan yi ba dama
in juya gudun ceton rai nake yi al'amarin ya zama mun gaba kura
baya siyaki igashi dai ina tsoron dajin dake gabana, wanda nake
kara shiga to amma ba zai yiwu in koma baya ba na sani idan baba
Hamza ya kamani yau to ko bai yi sanadin rayuwata ba dukan da
zai yi mun ba mai kyau bane, dare ya yi nisa tafiya nake yi babu
59
damar tsayawa duk da gajiya babu damar kwanciva saboda sanin
halin danake ciki ina cikin wannan taliyar wanda ko kukan tsuntsun
da na sani bana ji sai kawai na yi kicibis da gasken aladun daji
suma sun yi dare cikın sauri suke tafiya, na tabbatar in suka ganni
tawa ta karc addu'o'i iri-iri nake ta karantowa nan da nan na tuna
wata kissa da muka taba karantawa a makaranta cewar aladun daji
basa cin mushen abu ko mataccc sai kawai na mike shamc-shame a
kasa na yi shiru tamkar bana numfashi ta inda nake kwance ta nan
suka nufo tsoro ya kamani na ji tamkar in zabura in ruga da gudu
naga wannan ma ba zai fissheni ba don kuwa ba zan iya gudun da
zan tsere musu ba, ina kwancc anan ina kiran sunaycn Allah tare da
rokonshi kariya daga sharrin wadannan mugaycn dabbobi masu
hallaka dan adam sai kawai na ji motsinsu ta gefena ji na yi tamkar
sun tsaya a kaina kamo na yi ina sauraro in ji ta inda za su fara
yagoni ina nan ina kwance tun ina jin motsinsu har na daina ji ban
tashi ba har sai da na ga alfijir ya keto sannan na mike na ci gaba da
tafiya, na isa tashar jirgin kasa dai dan rana tana bullowa daga
gabas a gudanta tun kafin ta bayyana sosai na shiga binciken jirgi
mai tafiya Sudan babu sai mai tafiya Libiya ina cikin haka naga
shigowar Baba Hamza da Sharif tashar jirgin nan jikina ya dauki
rawa tamkar wacce taga ajalinta hankalina ya tashi na rasa yanda
zan yi da rayuwata tsoro ya rufeni na kidime na tabbatar in har suka
ganni a yau to ni kam zan iya cewa tawa ta kare.
Na yi kokari cikin hikima na fita daga cikin tashar jirgin nan
na koma bayan bukkokin da aka yi can gefe don hutawar ma'aikatan
tashar jirgin na shiga wani lungu dake tsakanin wata bukka da tsibin
sharar da ake tarawa a wurin na buya na jawo ledoji da
tsummokaran dake zube cikin sharar na rufe kaina na saje da ita ina
nan wurin a makure ji nake tamkar in daina numfashi don kar
shigarshi da fitarshi ya fallasani sai kawai daga bayani na ji wani
hannu ya tabani cikin wata murya kuma da tsoro ya hanani ganewa
macece ko namiji? Na ji ance mun na riga na ganki tashi kawai mu
tafi.
Da kyar na iya waiwayowa in ga ko waye? Sai naga fuskar
wata tsohuwace dattijuwar mace mai kimanin shekaru hamsin da
biyar a duniya murmushi take yi mun irin murmushin dake kara
bayyana maka muguntar mai yin shi buyar me kike yi? CIkin rawar
60
jikin da na kasa tsayawar na co mata babu komai ta sake wani
murmushin ban cika son ganin kyawawan mutane yara kanana
kamarki suna Rarya ba, na riga naga mutancn da suke nemanki
wasu mazane guda biyu gasu can na zaunar dasu na gaya musu zan
nemo musu ke don tun shigowarki tashar nan hankalina yana kanki
duk da tsummokaran da ke jikinki kyanki a bayyane yake gayan
gaskiya 'yan mata ko in nuna musu ke in karbi kudin da suka ce za
su bani in naganar musu ke.
Cikin rawar murya na ce mata nima ina da kudi kin gansu, na
nuna mata tulin kudaden da nakė dasu tun daga na Libiya har na
Nigeria na fiddo kullin zinarin na buſe mata ta ganshi ta zaro ido
tana lashe baki kamar wata mayya na ce zan baki zinarin duka idan
har kika taimakeni na samu jirgi na bar wurin nan ta miko hannu
wai in bata na ce a'a na mayar cikin aljihuňa na zuge na ce sai kin
kaini inda nake son zuwa ki sani a jirgi mai tafiya Sudan kema ki
shiga jirgin mu tafi Sudan tare kina kaini can shi kenan zan danka
miki zinarinki ki dawo nima in hau mota in tafi garinmu ta zuba
mun ido tsawon lokaci ban san tunanin me ta yi ba, sai ta ce babu
jirgin Sudan sai na Libiya in kin yarda mu je in kaiki Libiya a can
zan samar miki mota zuwa Kasarku, na ce to mu je, ta kira wani
cikin ma'aikatan dake loda kaya a jirgi ta fiddo kudi daga aljihunta
ta bashi ta ce mishi ka 6oye mun yarinyar nan cikin kayana da zan
tafi dasu Libiya inna dawo kuma kaima ka san ba zan barka haka
kawai ba, ai ba yau muka soma harka da kai ba ya ce mata to amma
ba farashin da kika saba bani zan karba ba don wannan nima naga
masu nemanta sun kuma yi mun tayin alherin mai yawa na dai ji
tausayinta ne kawai don ban san abinda ke tsakaninsu ba, ta ce to
mugayene sayar da ita suke son yi ni kuma zan tserar da ita ne
amma zan yi maka kari kar ka damu ya ce to.
Sia da ya koma ya gyara lodin nasu ya samu wurin da zai
sakani sannan ya dawo ya tafi dani a boye, wani dan kankanin
filine da in banda gudun ceton rai nake yi babu yanda za a yi in iya
shiga nan na kwanta aka dauko wani katako mai fadi aka dora a
kaina ya makale jikin buhu da buhu ko motsi bana iyawa aka ci gaba da shirya kaya akanshi wai a haka zan isa Libiya tafiya mai
bata lokaci tunda a jirgin kasa ne ba mota ba duk da haka cikin
zuciyata murna nake yi ina yiwa Ubangiji godiya.
61
Jirgi ya cika mafi yawancin fasinjoji sun zauna kan
kujcrunsu daga inda nakc kwance ina hango Hajiya tana zaune kan
kujcra kua da inda ta jsan an sakani na kosa kwarai jirgin ya tashi
don tun yanzu ji nakc tamkar in yi ihu don matsin ya kai matsi ana
cikin haka sai kawai na hango wani mutum yana tafiya da saurinshi
tamkar zai ci tuntube, Sharif da Baba Hamza suna biye dashi suma
saurin suke yi kamar za su ci da baki suna isowa inda Hajiyar nan
take hakince a zaune sai na ji ya ce wannan yarinyar da kuka yi
mun kwatancenta na ganta wurin wannan matar ku binciketa ta
nuna muku inda take Hajiya ta dago kai ta kallesu a wulakance
cikin yatsunar fuska at ce wai kwa wannan yake nufi? Tamkar bata
san abinda suke nufin ba, ni kama ina cikin kaya dama a matse nake
ga zafi ai ina jin wannan maganar sai kawai gumi ya rinka feso mun
ta ko wacce kafa dake jikina, na jini a jike shárkaf kamar an kwara
mun ruwa mutumin ya kalleta cikin fushi da facin rai tare da daka
mata tsawa ke kar fa ki nemi kawo mun bariki dama tunda na ganki
da yarinyar nan na lashí takobin rabaki da ita ba zan bar ki ki kaita
inda kiek kai sauran ba ina cikin kokarin hadaki da hukuma ne sai
ga wadannan mutanen da suka yi mun bayani kuwa na gane sune
masu ita shi yasa na nuna musu ke ta sake cewa kai Mallam ban fa
fahimceka ba ya ce za ki fahimceni da kyau, bari in gaya miki don
ki san na sanki da kyau, tun ba yau ba nake sai ido akan kaiwa da
kawowarki a tashar nan ba tun yau ba na gane sana'arki batun yau
ba na san ke masharranciyace, batun yau ba na san ke lalatacciyace,
babu kuma abinda kike sha'awa irin ki lalata na baya dake, na riga
na ganeki baki da wata sana'a sai safarar yara mata kananan kina
tsallakewa dasu kina kaisu kasashen turawa kina sayar dasu su
zama bayin turawa ko ki sanya kyawawansu a sana'ar karuwanci
kina karbar kudin idan suka tashi dawowa mu kuma su taho mana
da tsarabar kanjamau, ina cikin buhuna cikina ya sake bada
kulululu, a zuciyata na ce wato shigana hannun Hajiya ma yana
nufin na sake tsunduma ne cikin wata masifar ba kubuta na yi ba,
an ki cin biri ne ak aci dila ko in ce an gudu ba a tsira ba na sake
cewa wannan shi ne anyi gudun gara an fada zago, kin tsufa baki
san kin tsufa ba, mutumin ya ci gaba da magana dama kin hakura
kin saduda kin gane taki ta kare, yanzu maza basa sonki basu da
sha'awarki saboda kin tsufa na ce miki kin tsufa da karfi yake fada
62
tamkar da gayya yake gaya mata tsufan nata baki da sauran farin jini, mamorarki wurin maza ta kare, ko kyauta kika basu kanki ba
za su yi ha don suna ganin yara kanana masu jini da maiko a jiki gata nan ya sake nuna musu ita da dan yatsa in kun barta ta tafi ruwanku ku rikcta ta nuna muku inda ta 6oye muku matarku, ko kuma ku hadata da hukuma.
Hukuma? Sharif ya fadi da karfi yaushe zan tsaya jiran wata hukuma, ai bani matata kawai zata yi ko kuma in kasheta, jikin Hajiya yana bari tamkar mazari ta tsorata kwarai da yadda Sharif ke kaduwa a kanta sai bari yake yi tamkar sanyin hunturu ke bugunshi tnobacin ya shiga bacin rai mai yawa ta soma kokarin yin magana tana cewa uh uhuh ban san me take shirin fadi ba sia kawai naga caraf Sharli ya rike makogoronta da hannu daya, ya tallabo keyarta da daya hannun don rikon ya yi mishi dadi sosai yana cewa nuna mun inda take ko kuma in aike dake inda kakanninki suka dade da tafiya suka bar mutane da sharrinki, lalatacciyar banza. Shakar da Sharif ya yiwa matar nan ya yi yawa nan da nan wahalar duniya ta isheta, ta soma kokarin nuna mishi inda nake tana cewa to ka sakeni in nuna maka inda take? Ina take? Ya daka mata tsawa, cikin kaduwa da azaba ta soma cewa gata nan nasa aka boye mun ita ni kam tuni na saki fitsari saboda firgita da tsoro a
inda nake kwance, cikin buhuna.
Sai mun sadu a littafi na biyu.
63
HASSAN BOOKSHOP MIGA
Bayan Masallacin Abacha
Kasuwar S/Gari Kano.
Cover by:
AGF GRAPHICS FAGGE
C/O ANKA-GRAPHICS FAGGE
08028182666
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels