yi ya ci gaba da cin
10
gyadarshi nima na shiga hankalina sai kuma ya sake kallona ya ce
rayuwa Suhaila ba abar ayi wasa da ila bane ki yi amfani da damar
da kikc da ita a yanzu ki nemarwa kanki ilimi, kin taba karanta
"Wal Asri" na cc e babana ma kullum idan na tashi da daddarc ina
jinshi yana karantata ila da "Alhakumuttakasur" ya sake kallona kin
san abinda yasa yake yawan karanta wadannan surorin a
nafilolinshi na dare? Na yi maza na ce a'a ya ce to yana rokon
Ubangijinc ya tsareshi daga shagaltuwa da al'amarin duniya kuma
kinga hatta bature wanda muke ganin tamkar komai nashi don
duniya yake yin shi shima baya wasa da lokaci sai ya ce "Time is
like a swiftly flowering river that has no shoves non bandaries it's
season were not winter spring fall, or summer but birthdays and
joys and sorrows and pains" Kin gane? N ayi saurin cewa, c, ba
don na gane fassarar abinda ya fadi ba, muna cikin haka aka kada
kararrawar dawowa break ya dauki hankerchif din daya tara dattin
gyadar shi akai ya zubar a dust bin din ajinmu ya karkade ya dawo
yana goge table dinshi yara suna shigowa yana ci gaba da yi mun
mita sai a yi ta yin jarrabawa yara suna cinyewa ana raba musu
kyaututtuka suna karba ke kuma ki tafa musu amma baki taba yiwa
kanki irin wannan alherin ba sai kullum ki zo ta karshen aji
hankalinki a kwance don kin san agida babu mai tambayarki dalilin
hakan.
Yara suka gama shigowa teacher ya dauki chalk ya nufijikin
allo ya rubuta "Arithmetic" Wato za a yi darasin lissafi. Nasa hannu
na ciro littafina na lissafi, sai da ya gama bayar da misalai yara suka
ce sun gane sannan ya bayar da aikin da za a yi a ajin nima na bude
nawa littafin na soma nawa aikin yara suka yi ta wucewa suna bayar
da takardunsu yana sanya musu hannu ni kam inata Allah-Allah
darasin ya wuce a shiga sabo in samu in mayar da littafina cikin
jakata ba tare da teacher ya gani ba saboda dalilai guda biyu na
farko dai shi ne littafin bashi da bango na kuma sha ganin teacher
yana zane yara akan falle bangon littafinsu na biyu rubutun dake
cikin littafin bai kai daya bisa hudun rubutun lissafi da aka yi a ajin ba, ina jin an kada kararrawar canjin darasi na yi maza na mayar da littafina cikin jakata teacher ya ce "Pens up past your books on my table." ya dauki chalk ya nufi jikin allon ya rubuta "Corrections" Ya yi aikin tare da yaran da suka gama da ya gama ya dawo ya gama
11
makin takardun da aka kawo sai ya kalleni ya ce bani naki littafin
jikina yana bari na ciro na mika mishi yana karba ya juya bangon
littafin ya gani sannan ya shiga bude aikin littaſin yana ganin aikin
nawa duk shafin da ya bude sai ya sa jan biro ya yi kansil X sannan
ya ci gaba da ya gama sai ya miko mun ya ce yau yaushene? Na ce
Alhamis ya cc to na baki daga yau zuwa ranar Monday ki zo mun
da sabon littafin lissafi wanda kika kofi cikakken aikin da muka yi a
ciki tun daga darasinmu na farko har kawo na yau din nan kuma
lalle in ga rubutunki in kika baiwa wani ya yi miki ko ya muna miki
amsa zan ganc jikinki kuma zan gaya miki kin ji ko baki ji ba?
Yana jan kunnenshi guda daya wai duka alamar kashedine na ce na
gane ya ce yauwa in kunne ya ji jiki ya tsira kenan.
Ran nan ina zuwa gida nacire kayan makaranta na yi wanka
na ci abinci na suri jakata na nufi wajen Ibrahim, Ibrahim dan
makwabcinmu ne wanda shi da babana suka zama tamkar uwa daya
uba daya don haka shima Ibrahim kamar wa yakc a wurina gashi
kuma ana tsokanata ta hanyar kirana matar Ibrahim shima kuma
yana matukar sona kamar ya lasheni yake yi kusan sa'an yaya
Ashiru ne ya fan girmeshi kadan amma kuma bai kai Yaya Bashir
ba ina shiga dakinshi yana kwance kan katifarshi yayi maza ya tashi
zaune matar har kin dawo ne? Na ce uhm ya kara zuba mun ido me kike so a kawo miki ke cream ko cokolet na ce ke cream ya
kwalawa Sa'adatu kira Sa'adatu kanwar shi ne Sa;a ta ce tare muka
taso ta shigo ta ce gani yaya Ibrahim, ya ce yauwa zo yasa hannu aljihunshi ya ciro kudi ya mika mata maza jeki ki sayowa Antiki ke
cream ta karbi kudin tana hararata ba tare da ta bari yayanta ya gani
ba ni kuwa na yi mata signal tare da murmushin zolaya don na san
ta tsani ace mun Antinta tunda ta san ita ke gaba dani da kwana
goma ina kwance kan katifar Ibrahim shi kuwa yana zaune a kasa
na gama gaya mishi abinda teacher ke mun da aikin da ya ban
Ibrahim ya ce to wai shi teacher wa ya ce mishi dolene ke sai kinyi
wahala kin yi karatu? Tunda ni ina yi mana na kuma ce ko baki iya
ABCD ba in sonki in na zama shugaba kuma in nadaki first lady a
haka to ina ce shi kenan na ce koya'mun kawai Ibrahim in huta
dariyar da 'yan iskan ajin suke yi mun ya ce e, to kin gano dabara to
bari azo a karo miki cokolet a haka na soma karatu wurin Ibrahim
idan na shiga wurinshi bana dawowa sai na ji barci abin kamar a
12
mafarkı sai gashi har aiki ynke bani ina yı da kaina, shima sa da yn
yi magana ya ce ke Suhaila dama fa don ba kya sauraro ne kawai
amma dubi yanzu daga farawa har kina nema ki wuce ni na yi
dariya na cc kai Ibrahim kai da kake shirin shiga jami'a shi ne zaka
ce ina shirin wuceka?
Ranar Monday ina shiga aji dama kuwa n ayi latti teacher
yana kıran sunayen yaran aji suna amsawa, "Present sir." sai gani na
shigo ya kallo agogon hannunshi ya kalleni mc ya saki latti? Kafin
ki bani amsa bani aikin da na baki nasa hannu na ciro littafina a
jakata na mika mishi yana dubawa ina ganinshi yana yin haka Va a
ko ina da ya gama sai ya ce bake kika yi ba, na ce ni ce, ya tashıi ya
je jikin allo ya rubla mun tambayoyi shige wadanda na amsa a cikin
littafin ya koma kujcrarshi ya zauna ya ci gaba da kiran sunayc ya
cc in kin amsa ki je ki zauna, na tsaya na yi mishi na gama, na ce
mishi nna gama, ya zuba ido yana kallo sai na ji ya cc a'a lEze la yana
kokari well done Ezc naga aikinka ya fara fitowa, Eze yana
murmushi tare da susar gwaguyaiyar keyarshi ya cc ai ba sai ka yi
mun godiya ba teacher ai tunda ka ce ka bani Suhaila ai kadan ka
soma gani yaran ajin suka kwashe da,dariya, har da shima teacher
yana tayasu, jeki ki zauna Suhaila na wuce na jc na zauna, linglish
ma ran nan tsaf na yi karatuna saboda na saurari lokacin da tcacher
ke koyarwa ya ce to ko ke fa? Cikin dan lokaci kadan ne kawai sai
gashi na soma fahimatr aji, Ezc kuwa ya ki ya fita hanyata, ko wane
lokaci ka ji yana cewa "Bring out your book Suhaila let us read."
Ni kuwa haushinshi nake ji sai in hantarcshi "Common respect
yourself." Shi kuwa Eze sai ka ji ya ccwa Teacher excuse me sir
Suhaila is abusing her husband."'Yan aji su yi ta dariya shi kuwa
teacher ya daure fuska yana mun fada wai mace mai zagin miji, lugudc take sha, in kuwa muka zauna shiru ni da Eze bama fada
wani shakiyin yaro dakc zaunc bayanmu wai shi Ilaruna Bello sai
ya tabani in na juya na kallcshi sai ya yi mun signal da idonshi ya
ce yana murmushi yau dai naga alamar ana ji da maigidan don
tuntuni sai kus kus nake ji, sai dai ni miyar abun da zaki yi ta warbа
nake jiyc miki da dodonkodi ko da yakc na ji Eze yana cewa dadi
ne dasu irin wadannan tsokanc tsokanen da yara ke yi min sun sanyani tsanar Ezc ba kadan ba shi kuma gashi yana son ya koyar dani in naki sauraronshi sai ka ji yana gayawa teacher, "T'eacher 13
Suhaila will not lister shi kuwa teacher sai ya juyo ya kalleni ya сe
min listen to Lzc Suhaila, or I will send you to clean the toilet."
Saboda bana son koyarwar Eze sai na zama a gida bani da
wani abin yi in banda karatu shi kuwa lbrahim bayan aikin da na je
mishi dashi sai kuma ya koyar dani wani nauyin har ka'idodin iya
lissafi ya koyar dani wato "Logic" haka nan l'uranci komai zai gaya
mun da turanci zai gaya mun in kuwa na zo ina yi mishi magana sai
ka ji yana cewa Don Allah ki yi ta yi Suhaila ke kin ji yanda turanci
yake fitowa daga bakinki tamkar kema baturiya ce zugani da
Ibrahim ke yi akan wai turancin bakina dabam yake da na saura ya
sani kowane lokacici yin shi nake yi na kuma shiga koyar da sanin
Ra'ıdar turanci part of speech da kuma linglish spelling a kowanne
lokaci dictation yake mun tun bara iyawa har na zama komai ya
gaya mun zan rubuta cikin dan lokaci na fahimei alherin teacher
Hakeem babana kuwa bai san teacher ba anma ji dashi yake yi
tamkar ya lasheshi bari Bashir ya dawo tunda kin ce ya san shi zan
turashi har makarantar ya je ya yi mishi godiya Eze ma mun shirya
saboda babana ya gaya mun cewar dama hikima teacher ya yi, ya yi
amfani da Eze don tilastani yin karatu don haka in daina kula
tsokanar da yara ke mun in suka ga bana damuwa za su daina.
A wannan jarrabawar ta second term ni ce na zo ta biyar duk
da hukunmar makaranta bata bayar da wata kyauta ga dalibin da ya
zo na biyar ni kam teacher Hakeem Lamido ya bani tashi ta
musamman har ma tafi ta wanda ya zo na dayan, sabuwar jakar
makaranta tare da sandal da farar safa, da sabon food flast wai in
cewa Inna ta kara mun mudu tunda yanzu ba wasa, nake yi a
makaranta ba.
Ran nan a gidanmu kamar a lashe ni gashi kuma yayuna
dukansu sun iso Ibrahim kuwa tara mun ke cream ya yi a gabana
kala-kala Innata sai murmushi take yi dama ta gaji da gorin da baba
yake mata akan rashin karatuna ko wane lokaci in na gaya mishi
wulakancin da teacher ke yi mun sai ya yi-murmushi ya ce ato ba
laifina bane Suhaila ai kin ga su Bashir da suka dauko komai nawa
su sun zauna lafiya a makaranta ke kuwa kin yi kama da ni amma
kin dauko kwakwalwar Aisha inna kuwa tana jin ya fadi haka sai ta
cc ai wato ni kwakwalwata bata daukar karatu? sai ya yi murmushi
ya ce a'a to kece nake ji kina cewa ita haka Allah ya yi ta a daina
14
matsa mata.
Ana ta hira kowa na fadin albarkacın bakinshi game da
Kokarin da teacher ya yi a kaina sai na yi tsagal na co yauwa Yaya
Bashir nima ya ce mun ya sankaa kakin wwi ka yi hoad boy shi
yana binka a baya da shckara daya, Yaya Bashir ya kalleni me
sunanshi kika cc? Na ce Hakeem Lamido ya ce dogo sosai ko? Na
ce c, ya sake cewa mutumin gire daga Adamawa state na cc nima
ban sani ba, don bai gaya mun sunan garinsu ba ya dan yi nazari
kadan sai kuma ya cc amma bana zaton wancan Hakeemdin ne don
kuwa shi me zai kawoshi garin nan har ya zo yana koyarwa? A
makarantarku? Ya shiga baiwa babana labarin Hakeem din da ya
sani yana gaya mishi wai wani shagwa666en yaro nc in ya tashi
dawowa hutu komai katoon ake kawo mishi amma baya sati biyu
yake karewa don in zai ci abinci tare da 'yan kwanarsu yakc cі,
kowa kuma sai ya koshi yana karcwa kuma sai ya shiga mota ya
nufi gire wai yaje karbo abinci kalli ni san gire baba, gaba daya aka
yi dariya babana yace lalle shagwaba66e ne yaya Bashir ya ce gashi
babanshi yana matukar son ya yi karatu don haka kullum baya
gajiya da zirga-zirga tsakanin gire da kakin don kar abincin Hakeem
ya kare, ya ce zai je gidą karbo wani. Babana ya ce to daman dai
yana karatun? Yaya Bashir ya ce ai yaron wani iri ne baba baya
maida hankali amma ya fi masu maida hankalin ganewa randa
Hakeem ya ce zai yi karatu ina ganin za a ga abin mamaki
Da yamma Yaya Bashir ya daukeni a motar babanmu yа
shiga gari dani yawo gidan Zoo da wurare masu ban sha'awa ya
kaini ya yi mun saye-saye har da 'yar baby, ki yi karatu Suhaila za
ki yi kyau da zama likita abinda yake ta gaya mun kenan, mun
dawo gida muka samu babanu ya dawo na kawo mishi sakamakon
da kyautar da Yaya Bashir ya yi mun data teacher Hakeem ya yi
matukar yin farin ciki yana rike da 'yar baby yana dariya, haba
Bashir ya fa kamata kai da Aisha ku kyale mun Suhaila ta girma
haka ya isa ace har yanzu Suhaila bata wuce wasa da 'yar baby ba.
A zamana a gida a wannan hutun kusan kowane lokaci a
cikin karatu nake ga yaya Bashir da Ibrahim sun dage komai zan
gaya musu sai su ce in gaya musu da turanci idan na kasa sai su ce
to in gaya musu da Hausar su kuwa sai su gaya mun abinda na fada
cikin turancin su kuma in gaya musu su ji.
15
Satinmu biyu da samun hutu ran nan ina zaunc tare da
babana a kofar gida mai yankar farce ya gama yanke mishi kenanya
shiga yanke mun nawa sai kawai na hango teacher Hakcem zai
wucc ta kusa da gidanmu, da karfina na bude baki na ce lah baba ga
Icacher Hakccm can zai wucc, kirashi mana Suhaila da gudu na
bishi, ina kwala mishi kira, tcacher, teacher, ya juyo ya ganni ya yi
murmushi hello Suhaila, na ja na tsaya, good morning teacher, ya
sake wani murmushin good morning Suhaila kin ci gayu kin yi
kyau ba kadan ba ina za ki? Na yi murmushi ba gayun zuwa
unguwa na yi ba, tcacher ina zaunene tarc da baba a kofar gidanmu
shi nc na hangoka, cikin sauri ya cc "Lah ke da babanki nc? Na ce
e, to muje mana in gaisheshi, na ce to muka taho tare, ya koma gefe
daya cikin ladabi ya tsuguna yanak gaida Babana, Babana kuma sai
fara'a yakc yi mishi yana tambayarshi mutan gida yana ccwa
lafiyarsu kalau, na fa godc maka Hakecm bisa kokarin da kake mun
akan Suhaila, Allah ya yi maka albarka, ya kara sunkuyawa amin,
ke Suhaika kira Yayanki su gaisa, na ce ai sun fita Baba sun je
gidan Alhaji Ali, ko in je in kirasu? Da sauri teacher ya ce a'a a
barsu kawai babu damuwa, watarana zan dawo mu gaisa da su
yanzu ina sauri ne makaranta zan tafi muna da meeting tare da
hcadmaster, babana ya ce to babu laifi ya sanya hannayenshi duka
biyu a aljifan rigarshi kuibi da kuibi ya ciro duk ludin dake ciki ya
hada wuri daya ya mika mishi. A'a baba na gode barshi kawai, kar
ka yi mun haka mana in ji Babana, ya ya zan baka abu ka ce a'a? Ai
kai dane a wurina, zan kuma samu lokaci in je har gidan naku don
in sadu da mahaifinka mu gaisa ni da shi.
Teacher ya kara sunkuyar da kanshi kasa cikin murya mai
sanyi ya ce ai Allah yayiwa babana rasuwa, yanzu shekara uku
kenan har da wata hudu, Allahu akbar cikin jimami babana ya fadi
haka Allah ya jikanshi Ubangiji ya gafarta mishi ni kaina tausayin
teacher ne ya kamani na rinka rayawa zuciyata yanda mutum zai ji
rayuwa ba tare da mahaifinshi ba a duniya zuciyata ta girgiza ta
tsorata kwarai na yi maza na kori al'amarin daga jikina na kara
makalewa jikin babana na kwanta kan cinyarshi tamkar dai ina son
in kara nunawa Ubangiji irin tsananin son da nake yiwa babana ko
zai tausaya mun ya barni dashi, nasihohi masu yawa babana ya yi
mishi da ya gama kuwa sai ya sake mika mishi kudin daya bashi
16
yasa hannu biyu ya karba tarc da yi mishi godiya ya talı bayan
tafıyarshi babana ya ce nutsattsen yaro mai hankali abinshi.
Ana gobe za a koma makaranta muna falon babana ni da
baba da Inna muna hirarmu ina kara duba sabbin uniform dina guda
biyu wadanda Yaya Bashir da Ibrabim suka dinka mun su Yaya
Ahmad ya shigo yana jan jakarshi wacce ya shirya kayanshi na
komawa makaranta a ciki ya zauna yana kara bayar da lissafin
abinda yake so a kara saya mishi da ya gama sai ya ce amma baba
ina so gobe kafin in koma makaranta in kaiwa Yaya Ashiru katin
fatan alheri kan jarrabawarshi ta karshe da zai zana saura sati daya
ne za su fara babana ya yi murmushin jin dadi ya cc Ashiru zai
gama secondary bana kuma nan ba da dadewa ba zaka gama kuna
fara karatu a jami'a shi kenan kun girma kenan Allah ya sanyawa
karatunku albarka, muka ce amin, tsawon lokaci muna hirarmu mai
dadi kafin muka je muka kwanta washegari cikin zumudi na yi
sammakon shiryawa, sandal din teacher da safarshi na saka ga
sabon uniform kaina kuwa kamar kullum ya sha ribons sai kamshin
turaren Innata nake yi na rataya sabuwar jakata da food flast dina
suma dukansu na teacher ne na kama hanyar makaranta.
Yarinyar ajinmu dana fara gamuwa da ita ita ce Jummai
Musa na yi hanzarin karasawa wajenta don mu jera mu taſi tare sai
na ji tana cewa ta kusa da ita rabu da ita kawai mu tafi kin ji sai
aukin dinka uniform bata da ilimin komai daga shigarmu makaranta
zuwa yanzu an dinka mata sun fi ashirin, sai dai duk a banza mu
masu zuwa da tsofaffin mun fita tunda ai an ce in ungulu ta biya
bukata wai zabuwa sai ta tafi da zanenta, suka kyalkyale da dariya
na wuce na bar Jummai tana ce mata ko lamba biyar din da aka ce
ta dauka ko a jikina don na san bata kawai aka yi, ina hawa kan
kwalta din da zata kaini makarantarmu sai ga teacher akan mashin
teze zasu wuceni na kwalawa teacher kira har sun gotani mai
mashin ya tsaya da gudu na isa gareshi na samu ya gama karbar
canjinshi na ja na tsaya ina haki ya juya ya kalleni cikin murmushi shagwa6arki ta yi yawa Suhaila wato duk inda kika ga mutum sai kin kwala mishi kira lahh tcacher ko? Baki san sunana bane kike
kirana da lah teacher? Na yi murmushi na yi shiru yana kallona, kwalliya kika yiwa makarantar haka? Ko da yakc Ezc...ya bude baki cikin zolaya na yi maza na bata rai, ya canza zancen kina da
17
kyau Suhaila amma na gane duk kyanki da nake gani a unı form kin
fi kyau a kayan gida gashi nıamanki ta iya gyaraki.
Na ce to baka ce ka yi murna da takalmnka ya yi mun daidai
ba? Ya zarc ido yana kallon takalmin ni kuma na kara turo mishi
kafa daya gaba wai ya ganı sosai ya ce oh yes I am very lucky
Suhaila na zabi abinda ya yi miki daidai na gode da kika sako mun
shi na gani kin ji? Na ce mishi to, yaya baba ya soma tambayata
muna taſiya, na ce lafiyarshi kalau har muka iso makaranta hirarmu
muka yi.
A Kofar aji ya miko min takardunshi ya wuce ofis din
headmaster don yin signing na shiga aji ina gogewa teacher kujerar
da zai zauna da tebur din da yake doro littattafai, don haka naga
yanayi kafın ya zauna, sai ga Ilaruna Bello ya shigo yana ratayc da
jakarshi a kafada, yana rera wakarshi mai dadi cikin turanci wacce
yara suke yayinta a lokacin tare da yin tafiyar nigogi yana ganina ya
Isaya ya zuba mun ido har yana cire fankon madubin dake idonshi
wanda glass din shi ya gama zubewa ya rike a hannu wai ya kara
ganina da kyau, ya dan juya ya kalli wanda ke biye dashi ya ce
mishi anya Danladi ba za a yi juyin mulki a anguwarnan ba kuwa
Danladi ya ce kaima dai ka gani ka fada wai an yiwa 'ya mummuna
miji, ai tun kwanan baya na so in gaya wa Eze ya fa yi hattara in
baiyi da gaske ba, na ga kamar ana shirin kwace kyautar da aka yi
mishi,. Eze wanda yanzu ya fara jin Hausa sai dai baya mayarwa
sosai yana fahimtar abinda suke fada, ya yi tsalle ya hau kan benci
ya ce yana fada "No one will ever take away Suhaila from me I
will fight him with all my power, ya dunkule hannu ya daga sama
nuna alamar karfi tare da kaiwa iska naushi, yana kwatanta wai
bugun da zai yiwa teacher, 'yan mazan ajin suka rude da ihu suna
cewa muna bayanka Eze mun shaida an baka 'yan mata, kuwa sai
dariya suke yi, teacher yana shigowa ajin ya yi tsit kowa ya nufi
gurin zamanshi, good morning sir, morning how are you, what is
the laughting about? Yana tambayar dalilin dariya daya tarar ana yi
kowa ya yi shiru, bai wanda ya yi magana ya nuna wata yarinya
Rabi Halliru ya ce ta tashi ta gaya mishi dalilin dariyar da ya tarar
ana yi, a ajin ta mike tsaye cikin turanci take mishi bayani.
"Nishadi kawai muke yi teacher ganin dukanmu mun tafi hutu
kuma mun dawo lafiya, yayi murmushin jin dadi ya ce haka ne to a
18
A
tashi dava bayan daya kowa ya bashi labarin yadda yayi hulunshi
aka soma tashi ana ba tcacher labarin hutu wanda duk ya kasa sai
tcacher ya umarccshi ya fito gaban allo ya tsaya, na kusa dashi ya ci gaba har aka zo kaina, nima na tashi na soma bashi labari tund aga
tarbar dana samu agida kan sakamakona wanda ban kai musu
irinshi ba, kyaututtukan da aka yi mun yawan icc-crcam din dana y
watanda dashi yawon da Yaya Bashir ya kaini, irin sayayyar da yayі
mun 'yar bebin da ya sanya a ciki kashedi da Babana ya yi ni abar
mishi ni in san na girma mu'amalata da 'yan uwana har kawo
dawowata makaranta babu abin da ban fada ba dana gama sai ne
wannan shi ne karshen labarin yadda na yi hutuna gaba daya ajin ya
dauki tafi tun kafin teacher ya bada umarni rab rab rab, sai da
teacher ya dakatar da su lEze ya mike tsayc ya ce "Is a nice speaking
teacher." 'Yan aji suka kwashe da dariya, teacher ma ya tayasu
dariyar tare da cewa "Ycs Eze is a nice speaking and it shows me
how a good teacher, you arc isn' it? Yes sir Eze ya amsa.
Kwana biyu muna cikin gyaran makaranta kafin muka shiga
karatu sosai da sosai, inda muka shiga sabon darasin lissafi teacher
ya rubuta wanda ya ke shirin misali a kanshi a jikin bango kamar
yadda al'adarshi take a kullum in zai shiga sabon darasi kafin ya
bayar da misalin sai ya yi tambaya wa zai yi wannan aiki ni kuma in
yi mishi wata kyauta, yau ma hakan ya yi tambayar wa zai amsa
mana wannan ni kuma in bashi agogon hannuna, ya cire agogon ya
dora akan tebur dinshi Danladi Audu ne ya fara gwadawa da ya
gama teacher ya ce ka yi kokari amma ba haka bane, ya koma ya
zauna gabana sai faduwa yake yi ina so in jarraba amma tsoro ya
hanani, sai na yi kamar zan daga hannu sai kuma in noke ban san
teacher ya ganni ba sai na ji ya ce "Yes Suhaila go and try." Na
tashi na je na dauki chalk a ma'ajin chalk dinmu na nufi jikin allo
na fara aikin sai dana gama na juya na kalleshi yana rubutu a wani
littafi na ce mishi sir ya dago kanshi ya kalleni tare da cewa uhun,
na ce na gama, ya zubawa aikin nawa ido ni kuma na koma gefe
daya kirjina yana bal bal bal, ina jiran abinda zai gaya mun sai na ji
ya ce gaya mana yadda kika yi kika samu amsa, na koma jikin allo
na soma tun daga farko ina gaya musu na cire wannan cikin wannan
na hada wannan da wannan na ninka shi sau wannan har na kawo
inda na ce musu gaba daya dana tara saı na sami wannan amsa, na
19
kalleshi na cc ga hanyoyin da na bi na samu amsa, ya yi murmushi
ya ce kin yi daidai Suahıla, ku lafa mata na koma kujcra na zauna
ya goge allon ya yi ta bayar da misalai har sai da aka gamsu sannan
ya bayar da aikin da za a yi a lokacin teacher ya gama marking
takardu ya ga agogonshi a ajiyc akan tebur ya ce a'a Suhaila bakı
dauki agogonki ba? Na ce a'a teacher barshi kawaı, ya ce to shi
kenan ya mayar hannunshi ya daura, washegari kuwa lokacin brcak
har na dauko food flask dina zan je wajen kawayena, da suke jirana
sai teacher ya kirani na dawo yana kallona yana dariya Suhaila mai
kawaye me kika kawo muku yau? Na bude mishi agadene soyayye
a cike da miyar tumatur mai wadataccen kayan cikin saniya, a ciki
ya yi dariya ya ce to ga