agogo na kawo miki tunda kin ki karbar
nawa, jiya. Na sa hannu biyu na karba tare da yi mishi godiya,
agogon mai dan siririn igiya gwanin sha'awa na juya zan fita ya ce
zo ki sanya a hannunki tukunna in gani na ce to na dawo ina
sakawa, ya taimakeni ya daure mun ya tambayi lokaci na gaya
mishi ya yi murmushi ya ceo ai na dauka baki san agogo ba nima na
yi murmushin na tafi bayan ya bani kullin gyada mai gishiri.
A jarrabawarmu ta karshe a wannan lokacin ni ce ta biyu
abin mamaki sai ga Eze a na uku teacher da kanshi ya yi mamaki,
har yana cewa yaya aka yi haka? Dal oa u yi gaba da teachern ta
shi kuwa Eze ko a jikinshi murna ma ya i yani.
Mun shigo aji biyar na kara zage uantse sosai kan karatuna
shi kanshi malam mai Arabic a wannan lokacin ji dani yake yi,
teacher Hakeem kuwa bana ajinshi amma kullum a lokacin break
sai na leka ajinshi na gaisheshi in kuma karbi gyada in tafi wurin
kawayena, muna cikin karatun second term aka zabeni cikin dalibar
da zasu wakilci makarantarmu a gasar "Cowbell Competation" da
makarantar ke shirin shga a office din headmaster aka turamu aka
yi mana bayani tare da bamu wasiku da aka ce mu kaiwa iyayenmu
ana sallamarmu da gudu na nufi ajin teacher Hakeem na shiga shi
kađai ne tunda lokacin break ne Suhaila kina sanin kina kara girma
kuwa? Yaya za ki fado min aji da gudu'haka? Na ja na tsaya sorry
teacher sauri nake yi in zo wurinka in riga kowa gaya maka cewar
ina cikin masu tafiya Cowbell competation din da za a tafi wani irin
lallausar murmushi ya yi ya ce "I'm happy for your luck Suhaila, sai
dai tun satin can na sani na yi shirune kawai ban gaya mik ba ina
20
nan a mecting din da hcadmaster yayi da malamai ya ce su bashi
sunaycn yara 'yan aji shida masu hazaka ana cikin bayar wa
malamarku ta nemi abata damar bayar da dalibarta guda daya
bayani mai gamsarwa ta yi kafio headmaster ya amince da daukar
daliba daga aji biyarya lumshe idonshi ya bude a hankali ya ce ina
Mahari dake zan kums lumshe idonshiya buar da za ku daukowa
makerantarku, na ce ka jira teacher ina zaka tafi? Ya dan yi
murmushi, ya ce zan tafi karatu Suhaila,abinda ya sa kika ganni ina
karantarwa a makarantar nan rasuwar mahaifina ne,ya kawo haka
in banda babana ya rasu da yanzu ina shckarata ta hudu a karatuna a
jami'a, ya danyi ajiyar zuciya, ya ce baka san tashin hankali ba
Suhaila sai ran da ka rasa mahaili sai ki ga kun zama tamkar da
kuna cikin wata rumfa maiyawan ni'ima akayayc runfar aka barku
cikin zafin rana ga iska ta ko ina ruwa ma in ya zo ya bugeku na
kalli teachercikin tausayi na ce ka yi hakuri teacher tunda ma ai
gashi ya wucc ya dago ido a hankali ya kalleni ya ce zai wuce dai
Suhaila in ina raye. A yanzu dai abubuwa sun soma gyarawa
rasuwar mahaifina naga abubuwa da yawa shi yasa kullum bana
mancewa da yi mishi addu'a a kowace sallah da na yi ko kin san
rasuwar babana ne ya yi sanadin zuwana garin nan? Na kalleshi na
ce da a ina kuke? Ya ce Yola har yanzu ma iyayena da 'yan uwana
duk suna can na ce kakarka mai soya maka gyada mai gishiri fa?
Ya yi murmushi ya ce a Yola take in ta samu mai zuwa ne take
bayarwa a kawo min ni kuma sai in rinka ci a hankali don kar ta
Kare ba akawo mun wata ba, A yanzu zan tafi jami'ar Nigeria ta
NSUKKA iyayena suna Yola ko zamu sake saduwa sai Allah shi
kadai ne masanin abinda zai faru a gobe amma kafin mu rabu zan
baki shawara ko a wane hali kika samu kanki ki zama jarumar
kanki, kar ki rinka yin fata a baki kawai rinka hadawa da
jarumtakar a aikace, wani masani mai hikima sai ya ce "Lifes
success is provercated more on action than in word." Kin gane?
Na ce mishi e teacher sai dai bana son ka tafi ya hada hannayenshi
wuri daya ya zuba mun ido cikin murmushi ya ce Suhaila kenan ya
zama tilas in tafi karatu don neman ci gaba kinga yanda kike ke
kadai mace a gidanku? Haka nakc ni kađai namiji a namu gdian gashi mahaifinmu ya rasu kullum fatana bai wuce in maye musu gurbin ubanmu da muka rasa ba kinga kuwa hakan ba zai yiwu ba
21
sai na tsaya da kafafuna don haka zan tafi oeman ilimi Suhaila don
shi ne tushen kowane ırin alhairi a rayuwa.
Na ce haka ne teacher sai dai to ina so in rokcka ya ce rokenı
Suhaila ni kuwa ko menene zan yi miki, na ce ka jria mu dawo daga
competation din mu kafin ka tafi gani nake kamar idan baka nan ba
zan iya ba, cikin sauri ya cc no no Suhaila kar ki taba daukar haka
kar ki danganta nasararki a rayuwa ga kowa shi yasa na ce miki ki
zama jarumar kanki ina so in yi tasiri mai karfi a zuciyarki amma
bana so ki dauka ba za ki iya komai ba sai in ina kusa dake, ba haka
banc zan jira dawowarku daga gasar agaskiya ma dai jin da na yi
kina cikin masu tafiya shine dalilin daga barin aikina a wannan
watan, ina so in ga shirshiryenki ni da Halima in da hali ma in
tayaki na ce to na gode teacher, yanzu dauki wannan takardar maza
ki kawai baba a gida na ce to cikin hanzari na fita daga ajin teacher
na nufi gidanmu.
Gada-gadan makarantarmu ta shiga shirin tafiyarmu gasar
cowbel, duk abinda ya dace ayiwa dalibai masu shirin tafiya gasa
an yi mana, ana cikin haka har ranar ta iso.
Ranar Talata 6/5 aka fara an kuwa kasa gasar ne rukuni
rukuni har guda hudu wato ABCD, 'yan Group A za su kara da
group c, group B kuwa za su yi da group D, sunan makarantar mu a
group B ya fito saboda haka sai a rana ta biyu muka fara tamu gasar
inda muka buga da makarantar Township primary school wacce ita
a group D ta fito a haka aka fara gasar wacce aka yi kwanakin
talatin cif ana fafatawa daga karshe kuwa mune muka zaına zakaran
makarantarmu ce ta karbi kyauta ta farko saboda ita ce ta zo ta daga
don haka kuma mune zamu zama wakilan jiharmu a gasar cowbell
ta kasa baki daya, wacce za a gudanar a Legos cikin karshen
shekara, mun ci gaba da karatu a makaranta ga kuma lesson din da
ake yi mana da yamma a makarantar don shirin tafiya gasar kasa
baki daya da zamu tafi a Legos ana haka ran nan teacher ya kriani
ya shaidamun cewar jibi zai tafi Yola zai gama shiri daga can zai
wuce Nssuka ina isa gida na gayawa babana washegari da safe
babana ya ban envelop a like mai nauyi ya ce in kai mishi ni kuma
lunda ya ce in kai mishi hotona sungumar album dina na yi wanda
duk cikinshi babu hoton kowa sia nawa na kai mishi na ce ya zaba
na kuma bashi kyautar babana. 22
Tcacher ya gama kallon hotunana ya zabi guda biyu
wadanda ya ce sun fi masa kyau game da kyautarbabana kuwa a
gabana ya bude kudine masu yawa, a ciki teacher ya yi shiru yana
kallon kudin tsawon lokacin kafin ya iya yin magana, Suhaila ban
san abinda zan cewa baba ba, sai dai kawai na san shi ne mutum na
farko da na yi sha'awar in kusanceshi ya zame mun uba tun bayan
rasa mahaifina da na yi in kin je gida ki rokar min shi Suhaila ya
sanyani cikn 'ya'yanshi ya rinka yi mana addu'a, tare don ni kam na
dade da rasa addu'ar mahaifi, hawaye suka taru a idon techer ni kam
tuni na rigashi yin kukan cikin hanzari ya mike ya shiga rarrashina,
ina tsaye gindin windon ajinmu lokacin da teacher Hakeem ya gama
sallama da ticoci abokan aikinshi ya hau acaba ya tafi.
Mun ci gaba da karatu mai tsanani har zuwan karshen
shekara inda muka shirya muka nufi Legos an fara gasar cowbell
competition ta kasa baki daya ranar Alhamis an sanyamu a group C
don haka mu da A muka bude gasar an fafata gasa mai zafi a
tsakanin makarantu abinda ya tabbatar wa jama'a da cewar dukkan
makarantun dake wurin sun zone da niyyar tafiya da kofin da ake
gasar a kanshi duk da haka cikin taimakon Allah mun samu,
kawowa rukunin karshe na gasar inda zamu yi takarar kofin mu da
jihar Legos ran nan kuwa tun safe teachers, dinmu dake tare damu
suka kammala shiryamu ni kam-in ka ganni sai ka dauak gasar gayu
na zo teacher mu ta aji biyar ta yi matukar gyarani gashin kaina ya
sha adon ribons uniform dina gashi sabo ya kuma ya dauki guga ya
tsaya mun kan gwiwa ga farar safa da sandal sabo sai dan siririn
agogona wanda, kakata Hama ta kawo mun daga umra tsawon
lokaci ana kara yi mana huduba tare da jaddada mana
muhimmancin cin kofin kafin muka hallara a dakin gudanar da
gasar jihar Legos aka fara baiwa damar su gabata da kansu wanda
ya fara fadin sunanshi shine Abdulwaheed Akanbi sai Funke Faraye
ita ce a tsakiya sai kuma Bolaji Adelekan sannan aka dawo kanmu
Daniel Ison shi ne na farko sai na ce sunana Suhaila Imam daga
makarantar Giring Primary School ina wakiltar Pleateau state sai
kuma Ali Abbas mun fara gasar inda a zagayen farko muka yi
canjaras a zagaye na biyu dana uku ma haka aka sako wasu
tambayoyin guda shida muka amsa uku uku abin har ya baiwa mai
gabatarwar dariya ya sake kawo wasu jihar Legos ta amsa tata
23
daidai mu kuma aka karanto mana tamu ni da Daniel muka amsa
tare ina cewa B yana cewa C Quite Master ya nemi sanin amsar da
zai dauka sai kawai lDaniel ya ce C sai Quite Master ya ce sorry C
is not correct B is the answer shi kenan gasa ta Kare, jihar Legas ta
yi nasara a kanmu ni kam kifa kaina na yi kan tebur dake gabana
kuka sosai nake yi har zuwa lokacin da aka soma bayar, da
kyaututtukan ban daina kukan da nake yi ba da kyar commissioner
ilimi ta jiharmu wacce ita ce ta wakilci Pleateau State a wurin ta iya
rarrashina har na iya karbar mana kyautarmu inda muka dauki
Karamin kofin.
Na fito kenan daga wurin sai ga teacher Hakeem a tsaye ya
harde hannayenshi a kirjinshi ai ni kam da gudu na isa wurinshi
saura kadan in Kankameshi sai kuma na ja na tsaya lah teacher ashe
ka zo? Na fadi cikin murmushi tare da dora hannuna a baki alamar
mamaki, congratulation Suhaila abinda ya fara fadi kenan, na rage
fara'ar dake fuskata na ce to ai bamu cinye gasar ba teacher gashi ka
taso daga Nssuka ka zo ganin gasar ban kuma cinye ba hawaye suka
sake cika idona suna shirin su ci gaba da zubowa ya ce No Suhaila
stop crying failure isn't failure unless you don't learn from it." Na sa
hannu ina share hawaye ya miko nashi hannun yana tayani tare da
cewa na taso daga Nsukka don ganin gasarki na ganki kin burgeni
"Winning is not everything but making the effort to win is."
Ma'ana ciye gasar ba shi ne komai ba amma Kulia aniyar cinyewar
shi ne wani abu kin yi komai Suhaila sa'a kawai suka fi mu don
haka daina jin haushi kin ji na ce to na sake muka shiga hira da
teacher yana bani labarin zuwanshi Yola da Nssuka har yace wai
kakarshi mai gyada tana gaisheni na yi dariya na ce a ina ta sanni da
zata gaisheni? Ya yi murmushiya ce Allah na gaya mata ni da wata
yarinya Suhaila muke cinye gyadarta da take aiko mun na yi idariya
na ce su baba ma sun zo ya ce e na gansu a cikin wurin da muka
kalli gasarku har mun gaisa da shi da Ahmad da wani Ibrahim ya ce
mun shima danshi-ne amma ban ga kun yi kama ba, na ce e dan
makwabcinmu ne ya sake cewa banga Bashir ba, na ce la ai yaya
Bashir ya tafi Canada watanshi kusan uku kenan ya tafi karatun
digiri dinshi na biyu. Very lucky shi kam wallahi I'm happy for
him, na ce kaima in sha Allah kana da sa'a teacher, watarana sai
labari ya yi sauri ya ce in sha Allahu Suhaila mu je in yiwa Baba
24
sallama zan koma na ce mishi to na rakashi ya yi sallama da babana
na sakc biyoshi don in yi mishi rakiya na mika mishi kudin da
babana ya cc in bashi ya ce gaskiya ba zan kar6a ba Subaila ai abin
ya yi yawa, na zuba mishi ido ina kallonshi na cc haba teacher,
babana ya maka alheri ka cc bka so? Ya yi sauri ya ce to lalle kam
na yi kuskure in na yi haka ban kyauta ba, yi hakuri Suhaila in kin
koma wajenshi ki yi mun godiya ki kara tuna mishi cewar ya
sanyani cikin addu'o'in da yake yiwa 'ya'yanshi, na ce ai na gaya
mishi ya ce zai yi maka ba zai mantaka ba don kuwa duk abinda zan
zama ta fuskar ilimi kaine tushen wannan alherin, teacher ya yi
murmushin jin dadi ya kamo hannaycna guda biyu danashi
hannaycn ya rike ya ce duk inda kika samu kanki Suhaila na rokcki
ki zama mai tsare mutuncinki ki dage kan nemarwa kanki ci gaba
don babban kuskuren dan adam a rayuwa shi ne ya hada hannu ya
zauna ba tare da yin komai ba, ma'ana "The greatest mistake а
person can make is doing nothing." Byc bye Suhaila sai watarana
watakila zamu sake saduwa wata kila kuma shi kenan in mun tun
ajuna mu yiwa juna fatan alheri ya sake cewa bye bye Suhaila
daidai lokacin da ya saki hannayena ya juya ya kama tafiya ba tare
da yana waiwaye ba.
Cikin sanyi da rawar murya saboda hawayen dake
gangarowa a idona na ce bye bye teacher Hakeem Allah ya baka
duk abinda kake nema a rayuwarka na alheri na gode maka da
taimakonka ne na samu kawowa inda nake tsaye a yau, abinda na fadi kenan bayan tafiyar teacher gani nake tamkar iska zata dauki maganata ta kaita cikin kunnenshi ya ji abinda nake fadi game dashi.
Mun dawo gida Pilato jiharmu ta yi murna da kokarinmu ta yiwa makarantarmu kyautarmu kuma dalibai ta bamu schoolarship,
na yin karatun shekaru uku a kowacce makarantar secondary sch da muke so matukar dai a cikin jiha take, a makaranta kuwa komawa karatu sosai na yi a aji shida aka zabeni hcad girl, haka nan nima sunana ya shiga cikin kyallen da ake rubuta sunaycn yara da makaranta ba zata manta dasu ba, a haka na kammala karatuna na primary inda na fita ina da shekaru goma sha biyu. ASALIN IYAYENA
Ni Suhaila Imam mahaifina Alhaji Mahmud Ahmad wanda
25
suka yi mishi da ake kira Imam saboda lakabin da iyaycnshi
wannan sunan a dalilin cin sunan kakanshi da ya yi ba dan Nigeria
banc asalinshi mutumin Libiya ne wani gari da ake kira Bengazi ya
zo Nigeria ne zuwanshi na farko shi da mahaifinshi Malam Ahmad
wanda yake dan kasuwa ne yana fatauci tsakanin Nigeria da Libiya
in zaizo ya taho da dardumai in zai koma ya tafi da fatu ya yi
abokan hulda sosai tun daga Kano, Bauchi, Plateau babu inda baya
kai kayanshi in ya zo ya ci gaba da zuwa da danshi Mahmud har
kawo lokacin da shi Mahmud ya kawo karfi ya soma jagorantar
ayarin da babanshi yake turowa zuwa Nigeria shi kuwa Malam
Ahmad ya zauna gida ya huta, a cikin wannan hali ne soyayya la
kullu tsakanin Mahmud da 'yar mai masaukinsu Aisha, al'amari
yayi karfi a tsakaninsu inda har Malam Ahmad ya taso daga
Bengazi ya zo har Jos don ya nemarwa danshi auren Aisha, Alhaji
Ali wanda shi ne mahaifin Aisha ya yi matukar farin ciki don kuwa
tuni yake sha'awar halaye, dabi'u da rikon addini irin na Mahmud,
inda aka samu matsala kawai shi ne wurin Hama mahaifiyar
yarinyar wacce kuma ita ce matarshi ta biyu, ita kam a lokacin da
mijinta ya shaida mata shiru ta yi bata ce mishi komai ba, tsawon
lokaci yana sauraronta da dai yaga bata da niyyar yin magana sai ya
ce mata Hama ke fa nake sauraro kin dai san ba tun yau ba nake
baki labarin wannan yaron, nutsuwarshi gashi kuma da riko da
addini, na kuma san zai riketa don kuwa yaron mai kokarin neman
na kanshi ne.
Тa се Malam ba fa bana son Mahmud bane amma nisan
kasarsu nake gani yanzu a dauki yarinyar nan a kaita har Bengazi
shi kenan ni kuma shi kenan? Ta soma yi mishi kuka shi kuma ya
zauna shiru yana kallontá cikin nazarin al'amarin sai ya ce to ai shi
ne nake so in ji ta bakinki amma ya ya zan yi da malam Ahmad
dubi yanda ya taso daga kasarsu ya zo kan maganar.
Ta shiga share hawayenta ta ce bani da yanda zan yi tunda
bani da ikon hanaka yin iko da 'yarka in kaga basu itan su tafirda ita
a barni ni kadai shi ne daidai shi kenan na amince zan ci gaba da
yin hakuri in kuma kara rokon Allah ya kara mun dangana babu
komai bata sake cewa komai ba.
Bayan sallar Isha'i Alhaji Ali ya sake komawa wurin bakin
nashi bayan sun ci abinci sun yi hira sai ya sake sako maganar da ta
26
kawo su ya ce Allah gafarta malam yana mai kallon malam Ahmad shima ya fuskantoshi suka fuskanci juna sosai sai Alhaji Ali ya cc
mishi wannan yarinya da Mahmud yake so wacce ya taso ku a kanta
na kasa zartar da hukuncin ba ku aurenta ba tare da aminccwar
mahaifiyarta ba ba wai ina so in nuna muku mahaifiyarta tata tafi
karfina bane ko kuma ita din bata amince daku ba a'a uwarta
macece mai biyayya sai dai ina jin tausayinta kwarai ta wahala
matuka wajen wabin Yaya Aisha ita ce 'yarta ta shida amma ita ce
kadai a raye a yanzu haka wannan dalili yasa nake so in rokeku
alfarma ku rokar mun Mahmud ya zabi wata cikin 'ya'yana guda
goma sha uku mata maza, shirin a yanzu haka akwai sa'o'in Aisha
guda uku duk wacce ya zaba cikinsu na yi alkawarin zan daura
musu aure a yi biki a baku ita ku tafi tare ba sai an je an dawo ba,
tunda wurin yayi nisa da yawa, ba zan ji shakkar baku ita ba komai
nisanku don a dakinsu suna da yawa.
Malam Ahmad ya fahimci jawabin Alhaji Ali sai ya yi mishi
alkawarin shawartar danshi Mahmud da ya zabi wata abinda ya
zamo mai wuya kwarai wurin Mahmud canza Aisha da wata cikin
rarrashi Malam Ahmad yake gaya mishi zabi wata mana Imam ai
na gansu wadanda Alhajin yake fada sun ma fita farar fata, summa
fita kyau tsawo kawai ta fisu, Mahmud ya ce ka gafarceni baba ba
kyau nake nema ba wurin Aisha ba farar fata ba ai na baro fararen
mata a kasar mu, ita din nake so ina son tane kawai zuciyata ce ta
zabar mun ita ba kuma zan iya musanyata da wata ba taimakeni
baba ka taimaki rayuwata ka tausayawa maraicin uwata da na yi
lokacin kuruciyata ka bar ni in auri Aisha, ta yaya zan taimakeka
Imam Malam Ahmad ya tambayeshi, a hankali ya ce mishi in na
zauna a kasar su za su bani ita itama Aisha ta gaya mun tana sona
zata iya bina ko ina ne, to amma tana tausayin halin da mahaifiyarta
zata shiga in ta tafi Bengazi ta barta a nan ta dauki lokaci mai tsawo
tana kokarin fahimtar dani yanda mahaifiyarta ta dauki son duniya
ta dora akanta.
Maganar Mahmud ta zowa Malam Ahmad a bazata nan da
nan ya fusata ya rufe dan nashi da fada don me zai ce zai baro
Kasarshi iyayenshi, 'yan uwanshi, da arzikinshi ya ce zai dawo wata
bakuwar kasa don kawai a bashi mace? Ka yi hakuri baba ka
gafarceni in har na bata maka ya tashi ya fita.
27
Cikin kwanaki uku ana mahawara tsakanin da da mahaifi
Malımud ya amince da bin mahaifinshi su koma kasarsu amma
maganar sakc wani zabin babu cewa ya yi ya hakura dasu dukansu,
itama Aisha ta shiga cikin matsanancin hali ganin halin da Mahmud
ke ciki na kasa daidaituwar al'amari sai dai babu yandda zata yi duk
da dinbin son da take yiwa Mahmud ba zata iya juyawa
mahaifiyarta baya ba ta bijire ta bisu kasarsu ta barta ita kadai don
haka sai ta koma addu'a har Malam Ahmad ya soma shirye-shiryen
ya tasa danshi a gaba ya koma dashi kasarsu yaya aka yi yaya aka
yi sai kuma ya hakura ya shaidawa Alhaji Ali cewar yaya kake gani
in har Mahmud zai zauna a kasarku zaku bashi 'yarku?
Alhaji Ali ya yi farin ciki ya cc sai in sanya a daurin aure
tare da biki ku shaida daurin auren kafin ku tafi kasarku, haka
kuma aka yi Hama ta mallakawa Mahmud gidanta da ake haya
kyauta tace ta bashi har abada ya zauna a ciki shi da matarshi
maimakon ya je yana neman wurin zama aka yi biki aka gama
Malam Ahmad ya koma kasarsu shi kuwa Mahmud aka barshi da
amaryarshi suna zaune cikin farin ciki girmamawa da kwanciyar
hankali Hama kuwa tasa hannu hiyu ta rungumi Mahmud ta
maidashi shi ne dan nata ta jashi a jiki, har ya saki jiki sosai da ita
ya riketa tamkar mahaifiyarshi komai yake ciki wurinta yake neman
shawara in kuwa ta san yana cikin wani hali to bata hutawa sai ta ga
ya fita daga ciki bisa wannan dalili sai kauna da soyayya ta kara
karfi tsakanin Mahmud da matarshi cikin shekara guda na zamansu
ya mallaki jari mai karfi don haka sai ya tsunduma cikin harkar
goro ya mallaki shago a kasuwa duk shekara kuwa in watan babbar
sallah ya zo sai ya ziyarci mahaifinshi a Bengazi.
Shekaru biyar da yin aurensu Mahmud ya kammala ginin
gidanshi wanda a lokacin mutanen gari suka yi ta bayar da labari a
kanshi da ya shirya tarewa a gidanshi sai ya debi takardun gidan
Hama ya tasa matarshi a gaba suka je mata hira kamar yanda suka
saba sai da za su tafi ya kawosu ya bata ya yi, mata godiya Hama
kuwa ta tubure ta ki yarda ta ce ita kam ta riga ta bashi ma take
dashi in banda shi da matarshi? Ganin da Hama ta yi Mahmud yaki
karba ya sa ta ce to in baya so ya mallakawa matarshi haka kuwa ya
yi ya tare a sabon gidanshi shi da matarshi da 'ya'yanshi guda uku
Bashir, Ashiru da Ahmad bayan su kuma a sabon gida aka haifi
28
Aliyu, Jabir sai Hamza sai dai su ukun basu rayu ba.
Gidanmu yana makwabtaka da gidan Alhaji Isma'ila wanda muke kira babansu Sa'a yana da matanshi na aure guda biyu Ramlatu da Hafsatu wadanda suke matukar zaman lafiya tamkar
'yan tagwaye, Ramlatu uwar gida tana da 'ya'ya tara ita kuwa
Hafsatu tana da bakwai cikin 'ya'yanta akwai Ibrahim da Sa'adatu
babana da babansu Sa'a sun yi zama na amana zama na 'yan
uwantakar Musulunci zama na kauna da ganin girman juna gidanmu da gidansu Sa'a tamkar 'yan uwan junane a sanina babansu
Sa'a ya tafi Bengazi tare da babana a lokuta dabam-dabam
Babana mutum ne mai alheri gashi da wadata iyali mutune
sun yi mishi shaidar cewar shi kam har Allah Allah yake yi ya ga
mabukaci ya zo neman taimako wurinshi sabanin wasu masu halin
da sai ka zo gabansu ka gama tona ashirin cikinka ka gaya musu
halin da kake ciki sai sa shi yi maka rantsuwar karya suna gaya
maka damuwarsu wacce ta dame taka ta shanye ni dai 'yar gata ce ta
karshe kuma shagwababбiya ce ta kin karawa duk da tsayuwar
babana kan hana shagwabanin da yake yi misali idan ya dawo gida
ya tarar Inna tana yi min wani abu na shagwabawa baya gajiya da
yi mata fada, wata rana ya dawo gida ya tarar Inna tana bani abinci
a baki tana kirga munin loma a lokacin nan kuwa ina aji uku ne na
primary school yana ganin haka ya bata fuska ya sanya hannu a
aljihu ya ciro kudi ya bani ya ce maza sayo ice cream ki zo na karbi
kudi na fita jikina a sanyaye don na san fada zai yiwa Inna shi yasa
ya koreni ina shiga zauren gidanmu sai n aji ya fara cewa wai ni me
Aisha take nufi dani ne sau nawa nake gaya miki ki bar mun
yarinyar nan ta girma ashe ban ce ki daina bata abinci a baki kina
kirga mata loma ba? Da gudu na juyo na shigo gidan tuni har Inna
ta fara kuka tana ganina ta yi maza ta share hawayen ta kamar babu
komai ta shiga kawar da kwanuka shima baba maza ya yi ya
maiyace ya bar fadan na mika mishi kudinshi na ce bana son ice
cream din.
Tsayuwar dakan babana bai hanani zama shagwababbiya ba
saboda in ya hana a shagwabani a gida to gidan Alhaji Ali fa? Da
wayona na san Hama tana goyani har sai da na daina jin dadin
goyon na ki don kaina ta dorani a cinya kuwa wannan bai zame
mata matsala ba kullum sai na je gidanta inna taso daga makaranta
29
kullum kuwa ka'idane zan samu ta ajiye mun wani abu mai dadi in
kuwa kawayena suka bini to ina shiga zan fara raba musu abinda na
tarar a dakin