Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 7
in ta shigo ta gani ko ta yi kamar zata mun fada in ba nata bane sia kuwa kaga ta shiga rarrashina tana shafa mun kaina tana cewa ai dole ki yi kyauta Suhaila babanki alherinshi ya gaban a tsaya bayar da labari kinga dai shi kadai ne surukina amma ya wadatani fiye da masu surukan da yawa ya kaini Makkah sau biyu, ya kaini umara sau biyu zannuwa kuwa kullum a cikinsu nake haka alheri iri-iri laifina dashi daya ne kin bani ke da ya i in mu biyune ni da Hama a daki can cikin dakinta muke kulewa mu hau kan babban gadonta mu kwanta ta yi ta bani labarin irin fafatawar da suka yi da kishiyoyinta ni kuwa sai in ce don sun san ya fi sonkine Hama shi yasa suka hade miki kai ita kuwa sai ta yi dariya ta ce ai fa Alhaji ya soni ke in banda ya so nin ai da bakin cikin mutuwar 'ya'yana kadai ya iasa ya koreni a gidan nan, kudin Hama kullum a zinarina yake tafiya tun tana sanya mun ana sacewa ban san wanda ya cire ba har na yi wayo aka daina to ko shima Alhaji Alin ni ce mowarshi kullum bai gajiya da nunawa bakinshi ni wannan fa ita ce 'yar wajen Aisha jikar Hama ace a'a kaga yarinya yanda ta girma zo nan Suhaila a miko mun kyauta shi kuwa yana murmushi da kun rabu da ita ja'ira kullum sai ta zo ta shanye mun miyar gidana ayi ta dariya wannan dalili ya kara sawa Haima kullum cikin saya mun kayan kwalliya take kowane lokaci cikin fesa mun turare take wai dai ajini ina kamshi. Sakamakona ya fito na samu shiga Al'Iman secondary school makarantace mai tsada ga koyarwa ni kuma zan tafine da scholarship dina dana samu a gasar cowbell makarantar ta yi fice wajen bayar da ingantaccen ilimi na addini dana boko gashi kuma ana kula da tarbiya kullum da safe babana ke saukeni ya wuce wajen kasuwarshi in an tashemu kuwa shi ke daukana ya kaini gida ya yi sallar azahar ya ci abinci ya dan yi barci in an yi La'asar ya yi sallah sannan ya koma wurin harkokinshi ban dade a makarantar ba na yi fice kusan in ce daga ticoci zuwa dalibai babu wanda bai san sunan Suhaila Imam ba, jarrabawarmu ta karshe a aji daya a gaba dayan ajin maza da mata nice na zo ta daya haka muka yi ta fafatawa kullum takarar lamba daya tana tsakanina ne da wani yaro Murtala Zakari, har muka zo aji uku aka zabeni cikin masu wakiltar 30 makaranlarmu agasar 'MAN' Competation da za a yi wato "Mathematic Association of Nigeria' An fara gasar kamar yadda ake fara kowacce irin gasa mun yi nasarar cinye gasar a jiha don haka mune wakilan jihar a Abuja, inda za a yi ta kasa baki daya, mun isa Abuja aka bamu masauki ranar Juma'a muka ci gaba da shiryeshirye muka soma gasa ranar:Litinin mun fito ne kuwa a group tun isarmu hankalina yana kan jihar Legos kuma tuni har na ga Funke Faraye tana cikin wakilansu hakan yasa na gane ni da ita a wancan karon mun zone muna aji biyar biyar mun fara gasarmu da jihar Abia mune muka yi nasara mun gamu da Legos a wajen fidda wadanda zasu yi takarar kofi na farko, mun shigo dakin gasar a tare ne Legos tana shigowa ta bangaren dama mu kuma muka shigo ta Gangaren hagu, su suka nufi inda aka rubuta Legos state mu kuma muka nufi Plateau śtate, kallon da Funke take yi mun shi ne ya tabbatar min da cewar da can bata kula da gane ni ne watakula don a wancan karon sun buge mu bantsaya mata a rai kamar yadda ta tsaya mun ba, wata kila kuma don a yanzu na zo cikin sutura sosai sabanin wancan zuwan dana zo cikin fingilallun kaya a yanzu ina cikin doguwar rigane har kasa da dogon wando masu ruwan shudi tare da dan kwali shudi sai farin hijab ina kuma sanye da farin mudubi medical saboda matsalar da idona ke samu da karatu. Su suka fara gabatar da kansu Afolabi Williams, Funke Furaye sai Abdulganiyu Adediro, muma muka soma namu gabatarwar, Abubakar Hamza sai ni na ce sunana Suhaila Imam daga Al-Imam Secondary Sch. Ina wakiltar Plateay state sai kuma Mansur Garba, gaba daya aka tafa mana da haka aka soma gasar tun a zageye na biyu 'yan kallo da alkalan gasa suka soma tantancewa tun anan jihar Legos ta soma raina kanta mun amsa tambayoyin mu duka har mun amsa na Legos guda daya, data kasa amsawa, a zagaye na uku-kuwa fintikau muka yi musu a fili ya bayyna tun kafin alkalai su fada mun fitar da jihar Legos daga takarar daukar babban kofi sai dai ta yi na kofi na uku, mun fito daga dakin gasar muna tare da malamanmu wadanda suke ji kamar su lashemu sai ga Funke Faraye ina ganinta na tareta cikin fara'a don na san wurina ta zo, hannu na mika mata muka yi musabaha "Congratulation ta fada tana murmushi we are now friends in ji ta nima n ayi murmushi na ce yes Funke we are friends na rubuta mata 31 address dina na makaranta ita ma ta bani muka rabu tare da yiwa juna alkawarin za mu ringa musayar wasiku ni kam a ganina tunda muka buge jihar Legos burina ya cika don haka na shiga dakin gasar ranar da za a yi karawar karshe hankalina a kwance aganina ko kofi na biyun muka samu ni ya yi mun Allah kuma ciki ikonsa sai gashi mun buge jihar Delta mun dauki babban kofin mun fito na samu Alhaji Ali da Ibrahim ne kawai suka zo mun, babana wai bai samu zuwa ba, Yaya Ashiru kuwa dama na san ba zai samu zuwa ba, tunda yana London inda ya tafi karatu tun bara Yaya Ahmad yana jami'ar Maiduguri yana kuma cikin jarrabawa, sai da muka iso gida ne na gane ashe rashin lafiya babana yayi abinda ya hanashi zuwa ganin gasata, ta karshe sai dai na tarar har ya ji sauki tamkar ma bai yi komai ba. Jihar Pilato ta karrama makarantarmu ita ma makarantar tamu ta shirya gagarumar liyafa don karrama dalibanta wadanda ta tura wajen gasar, a ran nan kuwa Inna ta ce kawai bata halarci liyafar ba amma hatta Alhaji Ali da matarshi Hama sun je yayana Ahmad ma ya baro Maiduguri don halartar liyafar ran nan na sha kwalliya har bai yiwa in tsaya fada, na yi kyau ba kadan ba, na dauko hijab dina na dora don dokata a makarantarmu duk wata mace da ta riga ta zama baliga bata shiga harabar makarantar matuka bata sanya hijabi ba, wurin liyafar ya cika makil da bakin da aka gayyato mu kuma daliban da muka tafi gasar muna can gefc daya inda aka keba mana, sai kalionmu ake yi ana murmushi, Principal dinmu wanda yake Balarabe ne shi ne ya soma gabatar da jawabinshi cikin harshen turanci ya fadi tarihin makarantar tun kafuwwarta da irin nasarorin da ta samu inda ya bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da makarantar ta shiga gasa ba ya soma lissafo lokuta daban daban da ta halarci gasa da irin kyaututtukan da ta samu yana fadin lokaci da shekara da irin kyautar yanayi yana gangarowa har ya iso kan namu lokacin inda ya bayyana cewar wannan ne lokaci na farko da muka yi nasarar dauke kofin-da ake takarar a kanshi gaba daya dakin ya dauki kabbára Allahu Akbar da aka natsa sai ya ci gaba da cewa to ba bangaren karatun boko kadai muka tsaya ba don ko a bara dalibanmu sun shiga musabakar karatun Alkur'ani mai girma wanda aka gudanar a jami'ar Usman Danfodio dake Sakkwato kuma Alhamdulillahi dalibanmu guda 32 biyu da suka yi takara akan izifi goma da izifi talatin suna cikin daliban da suka wakilci kasar nan a musabakar karatun Alkur'ani mai girma da ala gudanar a birnin Riyad ta kasar Saudi Arabia gaba daya dakin ya sake faukar kabbara "Allahu Akbar da ya kai karshen jawabin sai ya ce dukkan nasarorin da muke samu tun kafuwar wannan makarantar har kawo yau din nan basu samu ba sai da cikakken hadin kai daga wurin iyayen yara don haka muna mika godiya ta musamman ga kungiyaR iyaycn yara ta makaranta wato PTA mun gode, Allah ya bar zumunci. Principal yana gama nashi jawabin sai aka yi ta kiran iyayen yara suna gabatar da nasu jawaban ciki har da shugaban PTA wanda ya yi magana a madadin iyayen yara da aka kamınala sai principal ya sake mikcwa ya karanta wata sanarwa ccwar kungiyar MAN competition wato wadanda suka dauki nauyin gasar da muka tafi sun bayar da scholarship na yin karatu kyauta da faliban da suka tafi gasar daliban kuwa sunc Abubakar Hamza, Suhaila Imam da Mansur Garba "Allahu Akbar, aka sake kabbara, ni kam dadine ya hanani a daidai lokacin da scholarship dina na cowbell ke shirin karewa gashi na smau na MAN competition a zuciyata na yi kewar teacher Hakeem na ce wannan duk yana daga cikin alhcrinshi ko yana ina yanzu oho? Na dai san baya Nssuka don kuwa shekaru kusan biyar ne da rabuwar mu dama kuwa ya cc mun zai dora ne kan karatun shekara guda daya riga ya fara a jami'ar an gama raba mana kyaututtuka sai kuma aka shiga daukar hotuna hoto na farko dana fara dauka shi ne wanda na yi ni da babana da Yaya Ahmad ina tsaye a tsakiyarsu ni kam dariya sosai na yi a hoton sai muka yi ni da Ibrahim sai kuma muka shiga yi ni da kawaye da malamai na yi ma ina tsakiyar Hama da mijinta Alhaji Ali. A gidanmu ma Ibrahim ya shirya mun liyafar tayani murnar gasar da muka ciwo gashi kuma ta zo daidai da ranar cikana shekaru goma sha biyar a duniya ba kananan kudi Ibrahim ya kashewa walimar ba don kuwa ya riga ya fra samunsu tunda ya kammala hidimar kasar shi har ya soma aiki a Jos Steel Rolling company a wannan lokacin kowa ya riga ya san Ibrahim da iyakacin gaskiyarshi yake sona don kuwa duk abinda zai yi na ya nuna hakan ya yi kana shiga dakin mahaifiyarshi tamkamemen hotona da nashi zaka tarar mun yi ankon kayan saki irin na fulani 33 hakanan a dakin Innarmu akwai hotona ni da Ibrahim dukansu shi ya wanke ya ajiyc a bisa wannan dalilin nema wata rana ina zaune tare da babana a falonshi ina karatun littafina shi kuwa yana kallon wa'azin Musulunci da ake yi ranar Juma'a NTA Jos sai ga Hama ta zo gidanmu kai tsaye a kofar falon babana ta yi sallama ya amsa mata ta shigo ya nuna mata wuri ta zauna shi kuwa ya koma can gefe daya ya zauna cikin girmamawa suka gaisa, Inna ma ta shiga ta gaishcta ta tashi ta fita don ta san ba wurinta ta zo ba, sun dan yi magana kadan sai Hama'ta ce mishi Alhaji wurinka na zo mu yi magana kan Suhaila don na ji mutane sun fara turowa kana cewa a basu hakuri na zo ne in roki arzikinka ina so ka baiwa Nuruddini ita na tsaya ina kallon l lama a zuciyata na ce ka ji ta jikan kishiyarta da ta ce mun da ita suka yi fafatawa shi ne yanzu take so a hada mu, ta ci gaba da yi mishi bayani sau biyu Nuru yana yi mata magana a kaina don ALlah ya dubi zumunci ni da shi jikokin Alhaji Ali ne in aka yi hakan Alhaji zai ji dadi. Shiru babana ya yi har zuwa wani lokaci sai ya ce ko da yake tasowarki ki zo da wata magana a gareni ba karamin al'amari bane kuma ya kamata tunda kika yi hakan da sai in ce miki kawai na bayar to amma al'amarin yana da girma ina so ki tayani duba matsayin Alhaiji Isma'ila a wurina yanda muke gashi kuma dan shi ya riga ya nuna alamomi na son Suhaila ko da yake maganar bata hadamu da shi ba don haka ina so ku yi hakuri idan har Alhaji Isma'ila ya nemi in baiwa Ibrahim Suhaila to sai a yi hakuri shi zan baiwa idan kuwa bai yi wata magana ba har ta kammala karatun nan to shi kenan kunga ta zama rabon Nuruddini kenan sai mu yi ta addu'a Allah ya zabar mana abinda ya fi alheri, ta ce to amin amma shi yana son ya fara zuwa zance wurinta babana ya yi murmushi ya ce ku bashi hakuri Inna idan matarshi ce ba sai ya yi wannan wahalar ba ai 'yar uwarshi ce haka itama ta hakura ta tafi ni kuwa ni da Ibrahim hidimarmu muke yi ni dai na san ba zan iya cewa ina son Ibrahim ba ba kuma zan iya cewa bana sonshi ba don kuwa na san akwai shakuwa a tsakaninmu. RAYUWAR DUNIYA Mun ci gaba da karatu mun zo SS 1 ina cikin karatuna mai dadi komai nawa yana tafiya mun yarda ya kamata tuni na kara zama 'yar gata a gidanmu Yaya Bashir ya kammala karatun digirin 34 dinshi na biyu a Canada har ma ya fara aiki a can bai dawo gida ba, amma kullum aikenshi yana bisa hanya kullum kuwa nawa aiken daban yake hakanan Yaya Ashiru duk da karatu yake yı amma in zai rubuto wasikunshi sai ya aiko mun da wani muhimmın abu ana cikin wannan hali ne ran nan babana ya saukeni a makaranta da safc kamar kullum yanda ya saba ranar kuwa ranar Alhamis nc ba zan taba mantawa ba, mun yi darussanmu guda takwas mun kurna yi practical akan Biology don haka mun fito a makare ga zatona babana ya dade yana jirana, muna gamawa na suro jakata da gudu na fito daga aji na nufi inda babana yake yin parking in ya zo ban ganshi ba na dawo na tambayi maigadi don kuwa kullum ya zo daukana sai ya zo sun gaisa watarana ma ya yi mishi alheri maigadi babana bai zo ba? Ya ce bai zo ba Suhaila yau dai kam ya mkara na koma na yi alwala na yi sallah kafin isowarshi har yara suka watse ina zaune ni kadai a cikin makaranta na kasa tafiya don kar mu yi sabani ban taba ganin wani wuni da babana ya yi lattin zuwa daukana ba sai yaubai kuma taba yin fashi ko ya turo wani ba kullum zai zo ya dauken muna tafiya muna hira yana gaya mun kin girma Suhaila daina yarda da shaġwaßa kin dasu Inna ke yi ni kuwa sia in yi murmushi in ce ai tuni na ki Baba nima kunya abin yake bani yayi maza ya ce yauwa kin gani ba har karfe hudu ina zaune a cikin makarantarmu bann san dalili ba kuka nake yi malamin mu na Biology ya fito ya ganni zaune kan kujerar roba a inuwar bishiya ya ce Suhaila "Why are you sitting here is four thirty." Na ce mishi babana nake jira, ya ce je ki gida kawai ina jin yau babanki ya manta dake. Kalmar ta kara sani kuka anya baba zai mance dani kuwa ya matso kusa dani yana bani hakuri ya miko mun kudi wai in shiga tasi na dauki jakata na ce ina da kudi na fito bakin titi. Ina isa kofar gidanmu naga cincirondon jama'a sai shiga da fita suke yi nace to ko dai innata ta haihu ne tunda tsohon cikine da ita? Da gudu na shiga gidan kofar falon babana a bude jama'a sun cika falon manyan maza-a tsaye a tsakar gidanmu sune suke kaiwa da kawowa Innata da wasu mata da ban san ko su waye ba sun yi tsit a cikin dakinta kamar basa agidan kutsawa na yi na shiga falon babana don in ga abinda ke faruwa, an dauko katuwar katifar gadon babana an jefar da ita a kasa Babana ne a kanta a kwance ga iskar fankar sama ga ta tsaye amma duk da hakak gumi na gani a jikinshi 35 babansu sa'a da Alhaji Ali sune ata wajen kanshi ban san me suke gaya mishi ba sauran mutanen dake falon kuwa duk na san su abokanshı zamanshi ne a kasuwa, daga yanda naga numfashin babana yana tafiya na ganc numfashin yana mishi wahala, durkusawa na yi aigabanshi ina kuka ina ccwa waiyo babana me ya sameka wayyo Allah na yana jin kukana ya bude ido cikin karfin hali ya kamo hannuna da kyar ya isa kiran sunana cikin haki "Suuhaiila sannunnu kinnji" Jarumtakar da babana ya yi kafin ya iya furta wadannan kalmomin shi ne ya kara firgitani kuka mai tsanani na saka wanda ya yi sanadiyar da babansu sa'a ya daukeni ya fita dani a tsakar gida ya tsaya ina Hafsatu abinda ya fadi kenan Innarsu sa'a ta fito daga dakin Innata rarrashi yarinyar nan ki bata abinda zata ci ta ce to ta rike hannuna muka shiga dakin Inna falonta Hama ce da matan Alhaji Ali dukansu sai 'yan tsofaffi da muke makwabtaka dasu can cikin daki kuwa Innata ne a zaune a kasa ta tasu Katon cikinta a gaba sai matan babansu sa'a su biyu kwanciya na yi a Kasa in ban da kuka babu abinda nake yi Innarsu sa'a tana rarrashina yi hakuri Suhaila in Allah ya yarda zai samu lafiya ai kusan barama kuna wajen gasar nan ma haka abin yayi mishi da ya sakeshi kuma shi kenan sai kika ga kamar ba shiba ne na yau din ne dai ya dau lokaci munɛ nan-shiru na ji uwargidan Alhaji Ali tana cewa yanzu kam ai Ibrahim ya kusa isa Maduguri ko me zai cewa Ahmad oho? Na gane an tura Ibrahim ne ya dauko Yaya Ahmad an soma kiran sallar magariba babansu Sa'a ya fito ya ce ina Hafsatu cikin sauri Innarsu Sa'a ta fita muna ji yana gaya mata Alhaji yana son ganin Hajiya Aisha gaya mata ina zata shiga ta je mishi da ruwan alwala bari mu je muyi sallar mu dawo ni da Inna tare muka shiga falon, inna ta durkusa gabanshi nima na durkusa kusa da ita har yanzu dai numfashin da kyar yake shiga da kyar yake fita Inna tana share hawyae ta ce sannu Alhaji yau kuma kirjin ya ki ya lafa, balle ka dan samu saurarawa Allah dai a rufa mana asiri ya baka lafiya, wannan ita ce addu'ar dana saba jin Inna tana yiwa babana a duk lokacin da ya cė ga wani abinda yake mishi ciwo babana, yayi alwala cikin tiren dana kawo mishi ya fuskanci alkibla ya yi sallar Magarib ya shafa fatiha ni da Inna muka taimakeshi ya gyara kwanciyarshi ya daga ido ya kalli inna da kyar maganarshi ke fitowa, ya ce Aisha ba zai yiwu ace duk lokacin da 36 ciwo ya samcka sai ka yi tasa ran sake samun sauki ba wani ciwon bana tashi banc na lafiya gida ne inna la gyara zama a kasa lana fyace majina da gefen zaninta saboda hawaycn dake zuba a idonta ni dai kin sanni ba ni da wata lalura ta yawan ciwo a jikina amma a 'yan kwanakin nan kin fi kowa sanin yadda nake kwana da yanda nake tashi na rasa lafiya kwata-kwata Karfin hali kawai nakc yi saboda yanda nake ganin kidimewarki idan na ce bani da lafiya, to abinda nake so ki sani shi ne Allah bai barin wani don wani idan wa'adina ya cika baki da yanda za ki yi ki yi hakuri ina kara baki hakuri ga 'ya'yana nan zan bar ki dasu ga wani ma a ciki wanda watakila ba zai sanni ba abinda ya lsaya mun a rai a yanzu shi ne su Bashir da Ashiru ba sa nan na tura a dauko mun Ahmad ko zai zo ya sameni ko ba zai samcni ba, sai Allah abinda nakc so in gaya miki shi ne lalle ne ke dašu ku kula mun da mahaifina ku rikc mun shi amana ke kin san komai ni da Inna kuka sosai muke yi inna tana ccwa wayyo na shiga uku ni Aisha me ya sameka Alhaji mc ke maka ciwo haka kake irin wannan magana? Kafın ya yi magana Alhaji Ali ya shigo shiga ciki Aisha zamu tafi asibiti ba zai yiwu ace sai,mun jira zuwan Ahmad ba kamar yanda Alhaji yake fada, Inna tana kuka sosai tace baba zan biku Alhaji Ali ya ce a'a hakuri kawai za ki yi shinr ya kamaceki a yanzu ko kin je babu abinda ya ki yi mishi muna nan a wurinki kwantar da hankalinki idan an bamu gado ne ma sai a turo a zo a daukeki a nutsu sai ki ganshi amma yanzu mutane sun yi yawa, kema ba zaki ji dadin binmu ba ni da Inna muka fito muka dawo daki kuka kawai muke yi innar su Sa'a tana bata hakuri muna ji aka fito da babanmu daga falon aka.fita dashi gidan aka nufi asibiti tunda inna ta idar da sallar isha'i bata motsa ba tana zaune a wurin duk da katon cikin dake gareta dare ya yi nisa babu wanda ya dawo balle a taſi da Inna kamar yanda Alhaji Ali ya fada sai wajen karfe hudun asuba muka ji tsayuwar mota Hama tana cewa kila gasu nan Allah Ubangiji ka jiyar damu alheri sauran tsofaffin dake tare da ita suka cc amin, sai ga Yaya Ahmad da sauri ya shigo ina Baba Hama abinda ya fara fadi kenan tana cikin gaya mishi asibitin da suka tafi sai ga dirin motoci da gudu Yaya Ahmad ya fita muna cikin sauraro sai wani mutum ya shigo ya ce wai a bada makulli za a buďe shagon waje, inan ta ce "La'ila ha illahu Muhammadur rasulullahi sallallahu alaihi wasalam" Alhaji 37 ya rasu ko? Cikin rawar jiki da rawar niurya ya ce a'a ta ce to gaya musu kawai su shigo mun dashi gida, ina makale jikin inna ina jin yanda jikinta ke 6ari tamkar wacce sanyin hunturu ke kadawa, babansu Sa'a ya shigo gida ya zo, ya zauna bakin kofar inna kamar zai yi magana muka yi tsuru-tsuru muna sauraronshi sai kawai muka ga ya fashe da kuka tamkar dan yaro dan. karami, gaba daya dakin aka daukio salati kowa ya gane abinda ya faru rudewa muka yi kowa kuka yake yi babu mai ba wani hakuri shi kenan ta faru ta karc, babana ya bar duniya muma mun zama marayu, tsawon lokaci muna cikin kidima Alhaji Ali ne ya shigo ya yi ta rarrashi yana bada hakuri har aka dan samu nutsuwa, ya wuto ya shigo har can cikin dakin Inna abinda bai taba yi ba inna tana kwance a kasa kuka take yi tana fadin 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" ya nemi wuri ya zauna a natsc ya ce ina miki ta'aziyyar mijinki Aisha ki yi hakuri abinda kawai zan iya ce miki kenan, wanda duk ya san zamanki da mijinki zai tausaya miki a yau ya zubar da hawaye idan har ta ji kin rasashi, saboda haka al'amarin ya wuce kidima ya wuce ayi kuka kawai ke kin fini sanin Alhaji bai so kowa ba a duniya kamar yanda ya soki ke da 'ya'yana a yau kun rasashiba zaku sake saduwa ba sai a darassalam, a yanzu abinda ya kamata ki yi shi ne ki nuna mishi kaunarki ta karshe ki je ki yi bankwana dash ki yi mishi addu'o'i, ki yi mishi fatan alheri ki rokai masa Ubangiji yasa alherinsa da kiak sanshi dashi ya bishi, kura-kuranshi kuwa Allah ya gafarta masa ke malama ce Aisha je ki ki yi sallama da mijinki, gashi an shigo miki dashi kamar yadda kika bayar da umarni ana idar da sallah za a fita dashi shi kenan kar ki bari ya tafi bai ji motsinki kusa dashi kina nemar mishi rangwame wurin Ubangijinmu ba. Cikin kuzari inna ta mike ta gyara ruhuwarta ta nufi waje nima na bita a baya muna alwala muna jin muryar yaya Ahmad cikin muryar kuka yana karanta mishi Suratul Yasin, inna tayi sallama a hankali a kofar dakin ta shiga ina ji ta ce Alhaji jin da na yi ta kirashi-ya sani zaton ko ta ganshi ya tashi ne a zaune wuf na yi na fada dakin ina shiga na yi ido biyu da makarar da babana yake kwance a ciki an shiryashi tsaf jira kawai ake yi gari ya waye a kaishi gidanshi na karshe ina ganinshi a wannan halin jiri ne ya debeni na yanke jiki na fardi bari sake sanin abinda ke faruwa ba, farkawa kawai na yi na ganni can ciki dakin mahaiafiyata na bude 36 idone a daidai lokacin da uwar gidan Alhaji Ali ke yiwa jariri wanka shi kuwa yana ta kyanyara kuka wanka take mishi tana fyace majina saboda kukan sharbe da take yi abinda ya kara tuna mun kafin in rasa sanin inda nake naga gawar babana a kwancc cikin sauri na wartsake na tashi zaune na hangi Hama a falo tana amsa gaisuwar mutane Allah ya jikanshi Allah ya sa ya huta tana cewa amin amin ita da sauran jama'a dake cike a falon, na matso gaban jaririn da ake wankewa ina ganinshi na san inna ce ta haifeshi kama dani yake yi kenan shima kama da babanmu yake yi tausayinshi ya kamani na ce mishi Allah sarki kai kuma mallam baka iso ba, sai a ranar da muka zama marayu babanmu yayi ta fatan ganin zuwanka gashi kun yi hannun riga a yau shi ya tafi kai kuma ka iso ta ciro shi cikin ruwan ta nade shi a tawul ta miko min shi na tuna ranar da babana ya yiwo sayayyar da ya sako wannan tawul din a ciki na zuba mishi ido hawayena suna zuba a jikinshi innata shigo hajiya Karama amaryar Alhaji Ali tana rike da ita wanka ta yi mata ta wuce ta hau kan gadonta ta kwanta, shiru, sai ga Yaya Ahmad yana shigowa ya tattare doguwar rigarshi ta zarce ya

Chapter 4 of 7