suke yi sai dai ina
matukar kula da Inna kullum'sau biyu nake mata wanka in na sayar
da kaji na in saya mata sabuwar riga, ban taba samun 'yanci a
zamana da Sharif ba irin wannan lokacin don shi yana da wata
ka'ida da ya sanyawa kanshi baya kwana dakin mace mai goyo sai
in ta yaye. Kullum sai na nunawa Inna hotona ni da babana da Yaya
Ahmad nayi mata bayani akansu har itama ta saba in ta ganni tsaye
47
kusa da hoton sai ta rinka
miko hannu tana cewa uh.,..... sai in yi maza in dauko mata in ce za
ki ga kakanki ne Inna? ta cc uh in tsuguna gabanta in ce mata kin
ganshi shi ne kakanki shi ne ya haifeni rasuwarshi ce ta sa na zo
garin nan har na haifeki wannan kuwa kawunki ne bayan shima
kina da wasu kawun nan da wanc da wane, in yi ta lissafo mata su
watanta goma ta soma tafiya gata tubarkallah, ko daya ke ta dan
dauko Sharif kadan amma ta fishi kyau nesa ba kusa ba, don ta
dauko farar fatata da gashina gata da wayo ko ya mata magana nake
yi don na kosa ta zama abokiyar shawarata ita ma kuma tana son
maganar ta yi ta jagwalgwalawa, tun ba a ganewa har ta soma
bayyana watanta goma sha takwas, Malam Ahmad ya matsa mun
sai in yayeta da dai na gane Sharif ne ya ke son yayen sai na ki na
ce sai ta yi shekaru biyu, muna cikin haka tana da wátanni ashirin
yaran gidan suka kamu da bakon dauro ko kyanda itama inna ta
kamu tare da su aka yi ta jike-jike ana basu hankalina ya yi matukar
tashi, gashi in ina kwance kusa da ita sai ta rinka jawo rigata kusa
da ita in na ce menene inna? Kin ki shan nono amma kina ta jawoni
jikinki sai ta ce mamana ni sonki ni sonki ni sonki, tausayinta ya
kara kamani in ce mata nima ina sonki inna, ina sonki ina sonki kin
ji. Ta ce to naga dai abin ba zai fissheni ba, gari na-wayewa na
goyata na kama zakaruna guda uku na hadasu wuri daya na daure
na sasu a kwando na nada gammo na daukesu na nufi Bengazi da
nufin in naje in sayar dazu zakarun in kaita asibiti, ina iasa na samu
Malam Ahmad a kofar gida yana ta fara'a da ya hangoni ina isowa
na tsuguna na gaisheshi na gayamishi abinda ke tafe dani ya ce
kwanto ta inganta na kwanceta na mika mishi ya kalleta ya zuba
mata ido cikin tausayawa, kamar zai yi kwalla sai ya juyo a hankali
ya kalleni ya ce Allah sarki Suhaila ashe baki san mutuwa ba a
wannan yarinyar ta rasu tuntuni tana goye a bayanki baki sani ba, ta
rasu Mallam? Ya ce e gata kuwa, na yi bak'n cikin mutuwar Aisha
ba kadan ba, na hakura, satina biyu na koma gidan Sharif gidan ya
yi min bakikkirin na rasa abinda zan gani a cikinshi in dan ji sanyi
ga fitinar Sharif kullum kwana muke yi muna zaga gidan wai shi a
dole sai wani abu ya sake hadamu ni kuwa na kasa kai ni na
gwammace gara in rinka kwana cikin dabbobi da in kwana da
Sharif. 48
Ran nan mun kwana a haka babu barci ina ganin alfijir ya
fara ketowa na yi maza na dauki tuluna na nufi hanyar rafi don in
debo ruwa ni kadai don dai ina rabu da masifar Sharif ina cikin
tafiya na taka dutsc na fadi na bugi wani dutsen dakc gabana
tsawon lokaci ban san inda nake ba, don zafi sai kuma can na dawo
cikin hankalina na shafa bakina n aji yanda ya sundume, ya yi nauyi
na taba inda hakorana suke na ji suna nan na dauki gammona,
tunda tulu ya fashe ina isowa gida matan gidan suka yi ta yi jaje
kafin a jima kuma sai na ji suna cewa wai tulun da na fasa yau shi
ne na goma sha tara tun zuwana gidan, kwana biyu a jere na ki
zuwa ko ina ina jinyar faduwar da na yi inata aikin gasa bakina da
ya sundumce, mutan gidanmu duk sun fice ina kwance a dakina,
Sharif yana ta aikin baiwa 'ya'yun rakumarshi ruwa sai na ji an
kwada sallama da karfi muryar dá na jin ta firgitani da gudu na yi
waje a rude ina fita na hangi Sharif yana tafiya wajen mutanen da
suke yi sallamar, wasu dogayen mutane su uku suna tashe da dan
karamin yaro da gudu na nufi wurinsu Yaya Bashir na hango da
Yaya Ashiru da Yaya Ahmad, wayyo Allahna abinda nake fadi
kenan bujen siket dina ya tadiyeni na fadi a kasa da gudu Yaya
Ahmad ya zo ya dagani na kara da gudu na barshi anan a tsugune
na isa wurin su Yaya Bashir irin taryen da ya saba yi mun na daga
ni sama sannan ya direni a kasa na kalli yaron da suke tafe dashi na
sureshi na rungume na ce baba kaine ka girma haka, muna tahowa
ina cewa kai kun canza yaya kun zama manya dana ganka yau Yaya
Bashir sai naga kamarka sosai da babammu, ashe dai sak kake
dashi, suka dan yi murmushi shi kam yaya Ahamd har lokacin yana
tsugune yaya Ashiru ya kama hannunshi tashi kawai Ahmad suka
biyomu a baya, na kaisu dakina na shimfida musu dardumar da na
saka da hannuna suka zauna, sai kallonsu nake yi ina ta murna sun
yi girma sun yi kwarjini sun yi matsanancin kyau mai bayyana
asalinsu, ina rungume da dan autanmu wanda ya yi girma sosai na ajiye mishi kwanon dabino, a gabanshi muna cikin gaisawa, Sharif
da mahaifiyarshi suka zo suka soma gaisawa bayan tafiyarsu Yaya Ashiru ya kalleni ya ce ke Suhaila baki da wayo ne da kika ga wahala irin wannan ba zaki gudu ba, sai ki zauna a cikinta? Na dan yi murmushi na ce kasawa na yi sau biyu ina kokarin gudu sai su Baba Hamza da Sharif su kamoni kuma in sun kamani duka sosai
49
suke yi mun in yi ta jinya ka gani ma na nuna mishi tabon dukan
dake jikina, tsit din da dakin ya yi ya sani na fita da riyyar kama
kajina in sa a yanka musu su sin yi musu girki, sai ga Maman Sharif
da saurinta matar da ba kasafai take kulani ba saboda wai ina
nunawa danta Kiyayya ta ce in bari kawai ita zata yi na yi mata
godiya na koma wajensu na samu Yaya Ahmad yana cewa to a biya
shi rakumanshi mana mu tafi da ita Yaya Bashir ya ce a dai bi
al'amarin a nutse aure bashi da babba ba shi da karami ku yi
magana dashi a kebe na zauna ina tambayarsu Yaya Inna? Suka ce
kalau dinta ta ce a gaisheki, na ce Allah sarki Hama fa? Suka ce ita
ma haka tsawon lokaci ina tambayarsu mutanen gida suna bani
labari da hira ta yi tsawo sai na cc ai da har na fara hakura da sake
saduwarmu, Yaya Ashiru ya ce haba Suhaila bamu dawo bane
kawai, Ahmad kuma al'amura sun mishi yawa, ga karatunki ga
canjin rayuwa da aka samu ga Inna babu lafiya, da karfi na ce bata
da lafiya? Yaya Bashir ya ce ke ta riga ta ji sauki gama hotonta
muka zo miki dashi ya ciro ya bani na karba na zubawa hoton ido
ina kallonta, shekaru uku cif rabona da ganinta, maman Sharif ta
kawo musu abinçin da ta shirya musu ta dan zauna ta kara
tambayarsu mutan gidan gida suka ce mata lafiyarsu suna gaishesu,
sun dan ci abinci kadan muka tsunduma hira, ni kam ina, kankame
da Abba ina basu labarin Aisha yarinyar da na haifa na basu hotonta
da suka nema suka ce wai za su kaiwa Inna ta gani, Yaya Ahmad ya
fita wajen magana da Sharif shi kuwa Yaya Bashir yana zaune shiru
sai kallon yanar da ta mamaye rufin dakina yake yi shi kuwa Yaya
Ashiru yana ban labarin bayan saduwa musamman zamanshi a
London yanda ya ji labarin rasuwar Baba ya ce mun abinda ya
hanashi dawowa a lokacin shi ne ya riga ya karbi wani aiki akan
contract na shekaru uku gani ya yi ko ya dawo abinda zai yi ba mai
yawa bane, tunda ALlah ya riga ya yi ikonsa, don haka ya sa ya
hakura ya zauna ya kammala aikinshi tukuna na ce to yanzu da ka
dawo fa me kake yi? Ya ce ina shirye-shiryen wurin zama ina gini a
filin baba dake jikin gidanmu Yaya Bashir kua ya sayi gida a Abuja
yana can da zama ya kafa kamfanin shi na hadin'gwiwa tare da
wasu injiniyoyi guda hudu ga katinshi ya miko mun, nasa hannu na
karba ina dubawa, an rubuta 'Engineer Bashir Imamkaai lambar
gidan dana office, na yi murna da ganin hakan yanzukuma muna
50
shiryc-shiryen bikin Bashir na zaro ido na ce daga zuwanshi har ya
samu mata, Yaya Bashir ya dan yi murmushi ya ce ta dade Suhaila
na tafi na barta tana aji hudu na secondary school tun lokacin muka
shirya to na yi shekaru bakwai na dawo tana jirana shi yasa kika ga
kamar an yi sauri na ce to Allah ya sa ayi a sa'a, ya sunanta? Y ace
Hamamata, na yi dariya na ce Hama kenan Allah ya sa ta yi irin
halin Hamarmu suka ce Amin, Yaya Ahmad ya dawo ya zauna
mutumin nan fa ya ki mu nunka mishi rakuman nashi ma ya ki
karba wai shi yana son Suhaila, tsawon lokaci suna tattauna yanda
za su yi da Sharif, akan aurenshi ya ki yarda da duk ta yin da suka
yi mishi Yaya Bashir ya ce abar wa Allah lamarin kawai amma ke
Suhaila yaya ba kya wani abu na taimakon rayuwarki ina kudaden
da Ahmad ya ce yana aiko miki dasu? Na ce ni ai ban taba samun
wani sako ba, daga gida kuma Malam Ahmad ma haka don baya
6oye mun komai nashi inda ya samu aike da ya gaya mun suka dan
yi shiru, matan gidanmu suka dawo daga gona suka zo suka gaida
'yan uwana Yaya Bashir ya kira Sharif ya kalleshi a hankali ya ce
mishi kana son zama da Suhaila ko? Cikin sauri ya gyada kai tare
da cewa e, ya ce to kar ka sake dukanta daga yau za kuma mu dawo
cikin shiri nan da watanni shida mu yiwa Suhaila gida a Bengazi ta
zauna kusa da Malam Ahmad zaka yarda ko? Ya yi sauri ya ce e, ya
kawo kudi masu yawa ya baiwa Sharif hannu biyu ya saka ya karba
yana godiya, sai Yaya Bashir ya ce ka kaiwa mahaifinka da muka
gayar wannan kuma naka ne ya sake bashi wasu da suak fi na farko
bayan fitar Sharif sai Yaya Bashir ya kawo kudin Libiya masu
yawa ya bani ya kuma bani kudin Nigeria ya ce in adanasu don ko
zan samu zuwa gida kafin su dawo kuma ga katinshi nan na
gidanshi in na samu zuwa na ce to nasa hannu biyu na karba ina
godiya na karbi na matan gidanmu na je na raba musu suka yi ta
zuwa godiya, nasa hannu a bujen siket dina na ciro warawaran inna
da tun ban fi sati biyu a Bengazi ba na ciresu a hannuna saboda
sunbulewar da suke yi asakamakon ramar dana yi na ce su mayar
mata Yaya Ashiru ya ce a'a in ajiyesu kawai in suka mayar mata
zata gane ramace ta kamani sanyansu su kuwa za su ce mata ne
kawai sun zo sun sameni lafiya, shi kenan na ce to na mayar aljihuna, yaya Bashir ya sake kallona ya ce ki yi hakuri Suhaila, ki
kara imani da cewar duk abinda ya sameki mukadddarine, ko
51
dayakc a wauta irin namu sai muna ganin kamar inda muna nan
baba ya rasu babu wanda ya iasa ya daukoki ya kawoki cikin
wannan wahalar itama Inna aka barta cikin wahala ga bakin cikin
muluwar baba gashi an rabata dake wanda na sani shi ne ya haddasa
mata ciwon zuciya....da karfi na kurna musu ihu na ce wayyo Allah
na! Ciwon zuciya Inna take yi? Na shiga kuka sosai da kyar suka
iya rarrashina ta fa ji sauki Suhaila in banda haka ai da ban gaya
miki ba, ko ba ga botonta nan ita da Abba na kawo miki ba har
bayan La'asar muna tare, Sharif ya yi ta kaiwa da kawowa yana
kokarin faranta musu Yaya Baashir kuwa komai ya yi musu sai ya
yi mishi godiya, Yaya Ahmad ne dai Sharif ya kasa burgeshi shi
kam a sonshi a tilasta Sharif kawai ya sakeni tunda ya ki karbar
tayin rakuma ashirin da suka yi mishi maimakon goma da ya ce ya
baiwa Baba Hamza a kaina na juye dabino da cukui din da nake
dashi na hada da dardumar sallar da na saka na bayar na ce su
kaiwa Inna da Hama da kuma Hamamata budurwar Yaya Bashir
rana tana gab da faduwa lokacin da muka yi bankwana dasu a inda
suka ajiye motarsu da direban da ya tukosu.
Muna komawa gida ni da Sharif ina kuka yana lallashina har
muka dawo na samu 'yanci da sassauci daga wahalar aikin da Sharif
da iyayenshi ke yawan sanyani tun bayan tafiyar su Yaya Bashir
zuwa gona ne dai tunda na huta kwana biyu naga kullum idan
Basma bata nan sai kuma Sharif ya nemi zuwa mun da rana sai
kawai na koma binsu gonar kawai muke tafiya tare sai dai in na je
bana aiki shinfida zanina nake yi a gindin bishiya in yi barcina mai
dadi in ji dadin guje-gujen da zamu kwana muna yi ni da Sharif
cikin dare in har girkina ne abin ya kai makura ran nan ina jin
Sharif yana gayawa Basma da ta tasa shi a gaba wai ita baya kwana
binta da gudu kamar yanda yake mun, ya yi tsaki ya ce to meye ai
duk gudun da muke yi ba komai bata yarda in kamata kuma kin san
tsoron hakoranta nake ji kin ga tabon da ta mun ja'ira dashi zan tafi
lahira shi yasa naso data fadin nan da hakoranta na gaba sun zube
kinga da cizonta ba zai yi tasiri ba, washegari da safe sai ga aike
daga Bengazi cewar Mallam Ahmad bashi da lafiya tun tafiyar su
Yaya Bashir kuwa zuwana biyune cikin watanni hudu cikin sauri na
shirya na kwashi duk kudina na zuba a bujen siket dina don in kai
Mallam Ahmad asibiti ko dama abinda yasa nake barinshi a gida
52
bani da kudine na isa Bengazi ana sallar Azahar ina shiga na yi
alwala na yi sallah, Mallam Ahmad yana kwance shiru ko motsi
baya yi na debo ruwa mai tsafla na wanke mishi baki na tsaftaceshi
Isaf na kawo madarar da na zo mishi da ita na shiga bashi a hankali
da zokali yana hadiya, can jimawa sai n aji ya ce Suhaila kin zo пc?
na ce mishi ec, Malam ya ya jikin? Yace da sauki na yi mishi alwala
ya yi Azahar da La'asar na ce to Mallam ina da kudi zan kaika
asibiti, ya yi murmushin karfin hali ya cc Allah ya yi miki albarka
Suhaila na yi murna na kika ga 'yan uwanki ina rayc kc da su Allah
ya yi muku albarka Allah ya ji kan mahaifinku Mahmud tsawon
lokaci yana mun bayani a hankali ina sauraronshi har ya cc mun shi
dama tuni ya san ana yi mana aikc baba IHamza ne baya bamu
namu, ya yi shiru ne kawai bai gaya mun ba, don baya so in kara jin
zafinshi a yanzu abinda yakc so dani shi nc idan har wa'adinshi ya
cika rai ya yi halinshi to in rikc dangin mahaifiyar Babana su din
mutanene masu zumunci da karimci in kuma yi hakuri da baba
Hamza kamar yanda ubana ya rayu yana hakuri dashi kuka na rinka
yi ina ce wa wayyo Mallam in ka mutu ka barni a nan kasar ni
kadai yaya zan yi dawa kuma zan rayu? Na yi kuka har na gaji
tunda Malam ya ki tafiya asibiti tilas na hakura na kyaleshi ina
jinyarshi a gida kwanana uku da zuwa ran nan ina shanya kayanshi
dana wanke ya yafutoni da hannu na yi sauri na zo gabanshi na ce
gani Mallam ya nuna mun tukunyar da yake kaki ya tofawa a ciki
wacce take cike da kasa, ya ce jawo tiren can ki juyc kasar kakin
nan a ciki ban yi mishi musu ba, na yi hakan sai ga wani katon kulli
na tsuma a cikin kasar ya ce zinarine ganewa na yi ana sace shi shi
yasa na yi mishi wannan hikimar 6oyeshi na baki tuni na so in baki
sai naga za ki yi ta wahalar 6oycshi kar ki yarda babanki Hamza
yagani zai kwace na ce mishi to shima na jefashi cikin bujen siket
dina na korma na gama aikina, kwanana goma ina tarc da Malam
Ahmad ran nan tun safe jikinshi yayi tsanani, sosai hankalina ya
tashi na shiga tsoron abinda ke shirin faruwa, kuka na wuni ran nan
ina yi duk lokacin da hankalin Mallam ya dawo .jikinshi daga
suman da yakc yi ina zuba mishi ruwa, idan ya ga hawayc suna zuba a idona sai ki yi hakuri Suhaila ki kwantar da hankalinki in sha Allahu Ubangiji yana sanc dake zai baki mafita na alheri kan al'amarinki ranar Alhamis da daddare kusan dai dai lokacin da
53
mahaifına ya bar duniya haka shima Malam ya bar ta aka wayi gar
Juma'a aka kaishi kabarinshi aka barni ni kadai a dakir. sai masu
zuwa gaisuwa duniya ta kara mun fadi na tuna mutuwar babana da
abinda hakan ya haifar mun na tuna mutuwar diyata inna da bakin
cikin dana gamu dashi na kewarta to ga Malam Ahmad shima ya
rasu mutumin da tun zuwana Bengazi shi ne ya zame mun uwa da
uba shi ne nakc zuwa wajenshj in yi kuka ya bani hakuri shi ne in
talauci ya gallabeni nake zuwa in gaya mishi ya dan tsakuro wani
abu ya bani in je in sayar don in samu abin biyan bukatar rayuwa,
to gashi na rasashi, wannan shi ne kurunkus wane hali kuma zan
tsinci kaina bayan mutuwar mallam? T'ambayar da na yiwa kaina
kenan, tun kwananshi uku baba ya ce in fito daga dakin za su duba
abinda ya bari suka yi ta fito da dukiya ni kaina nayi mamakin irin
dukiyar dake cunkushe cikin dakin Mallam amma hankaľinshi bai
kwanta ba tunda bai ga zinari ba, gashi matarshi ta riga ta tsegunta
mishi cewar Rahila tana satar zinarin don haka sai ya ce ita ta dauke
rikici ya kaure a tsakaninta yana cewa ta dauki rabonta ita kuwa
tana bai isa ba, ganin da na yi ba a yi maganar ana bin Malam bashi
ko ba a binshi ba yasa na samu wani dattijo amininshi da kullum
suke wuni tare ko ya san da wani bashin da ake binshi ya ce e, da
kam an bishi basussuka amma zuwan jikokinshi duk ya biya sai dai
ya yi alkawarin zai gyara wancan lambatun da yara ke fadawa, bai
samu ya yi ba, don a ranar ya kwanta ciwo da za a samu a yi shima
zai amfaneshi tunda niyyarshi ce na ce to nawa ne zai yi ya gaya
mun na kawo kudin na bashi nan da nan aka kama aikin. Aka yi
kwana bakwai, na kama hanyar komawa gidan Sharif, zuciyata cike
da alamu ran rayuwa dana gani a zaman duniya da na yi na shekaru
goma sha takwas ko sha tara wani lokaci nauyi da kunci kan sani
manccwa da yawan shekarun nawa, in rinka ganin kamar kadanya
rage in cika tamanin ksai in n ayi nazari sosai sai in ga ashe wai har
yanzu ban cika ashirin ba a duniya, al'amarin ya ban mamaki in gaji
in ce kai wannan duniyar ma dai ashe ba karamin dadewa ake yi a
cikinta ana gwagwarmaya ba, na iso gidan Sharif bai yiwuwa in
kwatanta yanda nake ji wani lokaci sai in ga kamar da zai yiwu in
ligo zuciyata a inda take sagale to da watakila na dan ji dadi don
ciwon da take yi mun ya kai inda ya kai gaba daya mace macen da
aka yi mun sun dawo mun sabbikewar rayuwata cikin 'yan uwana ta
54
dameni gani da wani irin miji wanda har yanzu na kasa sabawa
dashi don ko yanzu Sharif ya zuba mun ido sai in ga kamar kallon
mayu yake mun ni kadai nakc rayuwata ni kadai nakc tsugunc a
dakina.
Ji nakc kuma tamkar ni kadai ke rayc a duniya, idan na tuna
kalmomin Malam Ahmad da yake yi mun in yana rarrashina yana
son kwantar mun da hankali irinsu ai wannan ba komai bane
Suhaila kan abinda ya taba samun wadansu kuma gashi ya wucc
musu sai tarihi kema watarana in dai kin yi yawan rai sai dai ki
bayar da labari sai in tsinci kaina da yin tambayar ko yaushe ne zai
wuce, bayan kullum abin sai karuwa yakc yi sai ka yi kokari ka yi
dauriya ka yi jarumtaka ka saba da wannan sai kuma wani ya sakc
bullowa, yazo ya fama na da din duk su haďu su zama sababbi?
Ni kam duniyar a yanzu tsoro sosai take bani gani nakc
tamkar juyawar da take yi ba komai take kawowa mutane ba illa
karin fargaba, da zullumi da tsoro in na ga mutum yana daga jijiyar
wuya kan al'amarin da ai taka kara ya karya ba mamaki yake bani in
ce wannan dadi yake ji tunda har wannan dan abin zai 6ata mishi
rai.
Na zo gidan Sharif nà samu wani sabon canjin kuma a da can
kafin tafiyata Bengazi bani da matsala da kowa tsakanina dasu
girma da arzikine kawai, tunda ni dai bana shiga harkar wasa da
dariya don ban ga abinda zai sani wasan ba balle har abin dariya
aganina tun mutuwar babana da rabani da uwata da aka yi da
dangina da karatuna aka baiwa Sharif ni zan iya cewa ranar da su
yaya Bashir suka zo ne kawai na san na yi dariya, to yanzu na dawo
na samu mutan gidan gaba dayansu babu mai kallon inda nake ko
ina kwana nace musu da kyar zan samu mai amsawa, sai wani shan
iska suke yi na yi iyakacin tunanina na san ban yi fada da kowa ba,
ko Sharif da nake zamanshi a gidan ni ban taba tankawa
måganarshi ba, ko ta arzikine balle ta fada da dai naga ban yiwa
kowa laifi ba suka dauki wannan matakin a kaina sai nima na yi
watsi dasu hidimata nake yi. Ina zaune a dakina tadin zuci nake yi
na gaji na yi watsi dashi na ce ke Suhaila kama kanki kawai ki
daina wadannan zantukan da ba za su iya fissheki in kika yi hakuri
rayuwar duniyar ma guda nawa take? Fadan da Yaya Bashir ya yi
mun ya fado mun kan lalle ne in bambanta kaina damutanen da na
55
wai har
tarar a gıdan in rinka ibada akan kari in kuma cin kajina
raguna da nakc dasu in rinka yankawa ina soyesu ina adanawa a
langa in rınka cin abina in sun kare zai kawo mun kudin sayen
wasu, lalle ne in yi kokari in yi kiba kafin ya sake ganina in kuwa
ba haka ba to shi kam zai yi fushi dani, tashi na yi na kira wani yaro
na ce ya kamo manyan zakaruna guda biyu ya yanka ya gyara mun
su ya kawo mun na shiga kicin ina girki farfesun kajina sai kanshi
suke yi tun sanina da matar Sharif macece mai tsananin kwadayi in
taga abinda ranta ke so tuni zaka ga yawun bakinta ya tsinke ta yi ta
fama dashi tana son tsayar dashi jawo kujerar ta ta yi ta zauna a
gaban murhunta muka juyawa juna baya, sai na ji ta ce ni fa babu ni
cikin hadin kan da ake yi miki maman Sharif ce dama ta ce mu
daina harka dake wai sai har kin dangana kin daina kullewa Sharif
kofa, na ce ai dama shi ne dalili, shi ne kema kike tayasu to ai
shikenan ni dama ina yi saboda kene don naga kina son Sharif da
yawa, shi yasa nake kullewa don ya yi ta zuwa wurinki, to amma
tunda kema kina tayasu fushi dani akan hakan to daga yau zan rinka
bar mishi kofar ya bude shi kenan ko? Sai mu zauna lafiya, ta yi
maza ta ce Allah Suhaila ni dama bana fushi dake baki ga kullum
ina zuba miki ruwa a randa ba ina dai kin yi miki magana a gabansu
ne don kar ace na ki bin umarninta kawai.
Na ce ai shi kenan ni na gama magana ta shiga yi mun hira
iri-iri wai dai in san bata fushi dan na gama farfesuna na raba biyu
na dauki rabi kaza daya na baiwa matar Sharif kaza daya na ce ita
da 'ya'yanta ta shiga lashe tukunyar tun kafin ta kwashe naman ciki
tana cewa kai Suhaila duka wannan to ke me kika ci kenan? To
Allah Antina na ce Amin na fita na bar ta na koma dakina ina
lissafin sauran kwanakin da suka rage su Yaya Bashir su zo na san
dai in sha Allahu za su zo ba za su taba yaudarata ba, na ce ace dai
in suka zo su roki Sharif su tafi dani in gano Innata na yi maza na
kawar da wannan dana tuna nasihar Malam Ahmad ina yake ce
mun, sanyawa zuciya burin da aka san samunshi zai wuya shi ke
karawa dan adam wahala rayuwa, ina kwance akan gadona na kasa
na ji matar Sharif tana juye mun ruwa a randa na gane tana yi ne
wai dai in san ita tana tare dani na tashi