Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
yanzu a hali da nake ciki na fara tsanar jarumtakata, kai in takai ce miki na saduda da duk wani kudiri nawa. Cikin tsananin mamaki Lushmaira ta dubi Shadilat ta ce. "Ke kuwa akan me yasa.?" Gimbiya Shadilat ta yi wani kayataccen murmushi ta dubi Gimbiya Lushmaira ta ce. "Kc kuwa mai kike tunanin zai saka ni a cikin irin wannan hali in ba soyayya ba, ya ke aminiyata ina so ki sani a cikin 'yar gajcriyar tafiyar da muke, sakamakon rashinki a tare da ni, sai Yarima ya ke zuwan min lokaci lokaci yana taya ni hira, a wannan lokaci ban yi aunc ba 16 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI tsananin soyayyarsa ta shiga cikin raina." Kafin Shadilat ta gama zuwa karshen maganarta gaban Gimbiya Lushmaira ya yanke ya fadı wani irin kishi ya turnukcta, da kyar ta iya kawar da damuwarta ta dubi Shadilat cikin nuna rashin damuwa ta ce. "Amma dai kc kuwa kin yi asara a kan soyayya ki zubar da irin burukanki tabbas na yi dana sanin kulla kawance dakc, domin kuwa a tafiyata bana son sakarci ni kuwa ban dauki soyayyar komai face sakarci in har zaki yi soyayya to babu shakka ke sakaryacс." Wannan magana ba Karami bakantawa Shadilat rai ya yi amma sai ta yi murmushi ta cс, "Ko da zaki rabu dani, ba zan ji takaici ba tun da dai ina tare da gwarzon namijin duniya kuma shugaba ga wannan tafiya ina so kuma ki yi sani, Yarima Zaiyan nc kadai zai iya yin nasara akan dukkanin kudirinki domin kuwa a yanzu a kaf cikin wannan nahiyar babu sadauki mai karfinsa da kwarjinsa dan haka kada ki taba tunanin kcсе zaki iya sokc daya idaniyar Maciyar Burukul Kursum, kuma shi ne zai zama gwarzon karni a cikin wannan gagarumin yaki da za a kwafsa, TURBAR GASKIYA--4 MADAKIN GINI tabbas idan ya zamo abin gabarki a yanzu zai zamo abin son ki a nan da wani dan lokaci mai zuwa, ina mai shawartarki da ki yi biyayya a garc shi domin ki samu saukin bakin cikin rugaza miki kudiri da zai yi. Koda gimbiya Lushmaira ta ji wannan ba tu sai ta fusata ta cire hannu daga rikon da Shadila ta yi mata ta bar gun cikin tsananin fushi, tana barin gun kuwa ta shiga wani sahu a na ci gaba da tafiya. A dai-dai wannan lokacin kuwa aka tsaya yin sallar Azahar, wannan damar ce ta sa Gimbiya Lushamaira ta samu guri ta zauna dukkanin abubuwan da Shadilat take sanar da ita nan take ya dinga dawo mata, wani tsananin kishinta ta ji, tabbas a yanayin jarumtakar da Yarima yake nunawa zai iya zamowa gwarzon karninmu dan haka abinda ya kamata ta yi shi ne ta ta yi kokarin da zata zamo itama-za a yabeta tana da masaniya ko da bata kai kokarinsa in har ta zamo masa na biyu to bai isa ya yi mata wani kuri ba, da wannan tunanin Gimbiya Lushmaira ta ta shi ta tafi ta yi alwala, sai dai lokacin da ta dawo daga yin tsarki sai ta 18 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI hango Shadilat da yarima Zaiyan suna hira har da kyalkyalewa da dariya, wannan abu ba karamin yi mata ciwo ya yi nan take wani tukokin kishi ya rufeta. Koda aka idar da sallah za'a ci abinci bata bari ta je inda Shadilat take ba saboda yanzu haushinta ma take ji, a haka aka ci gaba da tafiya. **** A can kuma san sanin su Sarki Madhan lokacin da suka iso bakin filin da za yi wannan yaki sai suka tsaya da tafiya nan take kuma aka kama kafa tantun domin a samu huccwa kafin su samu sako daga jama'ar Sarki Abu Zaiyan. Koda aka kammala da kafatuntunan su Sarki sai Sarki Madham Sarki Tarma da kuma Sarki Husaka suka kadaice a cikin nasu tantin da dubu da irin abubuwan da yake gabansu. Koda yin shiru na dan wani lokaci kowannensu yana tunanin abin da zai faru, sai Sarki madhan ya yi ajiyar zuciya ya dubi Sarakan gudu biyu ya се. "Ya ku Sarakai 'yan uwana yanzu ya kuke tunanin jama'armu da muka turo don yin 19 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI kwantan 6auna don su hallakar da wasu daga cikin jaruman Sarki Abu Zaiyan ta hanyar yi musu ruwan kibiyo. Da jin wannan ba tu sai Sarki Huzuka da Sarki Tarmas su ka ajiye zuciya a tare sannan suka tsai da kallon su ga Sarki Madham Sarki tarmas yа сс. "Lallai kam akwai abin duba a cikin tafiyar tasu dole muna bukatar mu san abin da ya faru ko sun samu nasara ko kuma basu samu ba domin mu yi yunkuri yin wani tunanin tun kafin su Sarki su iso wannan fili a fara yin yaki dasu." Shi kuma Sarki Husuka sai ya ce, "Wannan haka yake, amma kuma ta yaya kuke ganin zamu san samun nasararsu, tun da dai kun sani ba mu tura su dan su je su yi nasara su dawo ba, mun tabbatar da cewar konar bakin wake su kai, domin kuwa babu wanda zai sha a cikinsu, fatanmu dai su yi barma ko yaya take." Sarki Madhan cikin karfin gwiwa ya cc, "Babú ko kokwanto za su samu nasara abin da ya kamata yanzu mu yi shi ne mu kara nemo wata hanyar da zamu yi amfani da ita dan samun biyan bukatarmu." 20 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI e Kafin wani daga cikinsu ya yi wata magana sai Shugaban dakaru na birnin Sarki Husuka ya shigo cikin tanti cikin rissanawa ya cc.BIBWB "Ya shugabana Sadauki Askam ya iso cikin mawuyacin hali tare da gawarwakin duka dakarun da ya tafi da su.M ihs2 sbo isaKoda suka ji wannan ba tu sai dukkaninsu suka cika da firgici ainu, har sai da aka samu dan lokacin sannan suka dawo hayyacinsu, Sarki Husuka ya yi saurin duban Sadaukin Rauwal ya сe, "Ka koma ku duka ku saurari fitowarmu. Sannan ina so kafin nan ka tura Dan leken asiri dan gano mana a halin yanzu a ina abokan gabar mu suke." swogse Koda jin wannan ba tu sai Sadauki Bhan Rauwal ya yi sujjada ga Sarakan sannan ya fice. UR Fitarsa ke da wuya sai Sarki Tarmas ya cc, "Tirkashi lallai sai mun yi da gaske domin kuwa jama'ar nan sun gano mu, kuma ba za su tabа yarda da duk wani shirin da za mu zo mu su da shi ba domin kuwa za su cc yaudara cc, kuma sanin kanku ne gaba da gaba da su ba karamin ta'adi za su yi mana domin Kasar Baitul Haural sun kware wajen iya yaki mamaya a duk duniya 21 TURBAR GASKIYA --4 A-AY MADAKIN GIN duk wanda zai yi gaba da gaba da su a fafataa filin daga babu shakka sai sun sha jininsa sai sun samu nasara akan ku, don haka yanzu sauya shir ya zama dole, mai kuke tunani wata shawara za ku zo mana da ita?" Koda Sarki Husaka da Sarki Madhan suka ji wannan jawabai na Sarki Tarmas sai dukkaninsu suka yi shiru na rabin lokaci. Daga R bisani Sarki Madham ya ce "Ai kuwa in haka ne tusa ta Karewa budari domin kuwa ni ban ga ta yanda za a yi mu samu nasara akan Sarki Abu Zaiyan ba in har ya zama dole yin gaba da gaba da su babu nasara. AATey nild s Bisir Da jin haka sai Sarki Husuka ya yi saur dagowa ya cc, "Bai kamata mu dinga sagewa kanmu gwiwa ba, kamata ya yi mu samu hanya mafi dacewa damu domin yin gaba da gaba da su koda za'a samu nakasu. A yanzu a cikin tafiyarmu muna da manyan Dakaru da ko a duniya za a sasu a cikin sahun manyan dakarum duniya, abinda ya kamata da a yi shi ne, a yanzu takc mu jarraba tura dan sako da mun tabbatar da i sowar su mu shailanta musu cewa za'a yi yaki amma ba na mamaya ba, za a yi yaki irin :22 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI yakin na gasa, ma'ana jarumi da jarumi, ni na tabbata idan suka aminta da haka to babu shakka za mu iya yi musu a sarar manyan dakarunsu." Da Sarki Husaka ya zo nan a cikin batunsa sai dukkaninsu suka yi shiru na tsawon lokaci kana suka dubi juna. Sarki Madham "Ai kuwa in har za su amince da wannan ni kaina ina kallon samun nasara amma kuma amincewarsu shi ne badakalar." Da jin haka sai Sarki Husaka ya сc, "Ai sai mun jarraba, kumaishi mai nema ai yana tare da samu." Nan take su ka yi na'am da wannan ba tu suka nemo Sadauki Rauwal ya shigo ya sanar dasu gabatowar rundunonin kasar Baitul Haural har sun kafa tantuna sun fara fito da kayan makamansu. Koda suka gama jin wannan batu sai suka sanar da shi sakon a sanar da dan aiki ya je zuwa ga sansaninsu domin isar da sakon da suka tanadar musu. Nan take ya karbi sakon ya bayar aka kai ba dauki tsawan rabin sa'a ba dan aikin ya dawo. 23 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI Cikin girmamawa ya mikawa Sarki Husaka Sarki Husaka ya mikawa Madham nan take sai Sarki Madhan ya warwareta ya fara karantawa suka kasa kunnc cikin doki sun jin abinda yake kushe a ciki Zuwa ga azzaluman Sarakai marasa son gaskiya ba su bawa Turbawa gaskiya baya, hakika, tabbas ko yanzu mun gano cewa tsoro ne yake bibiyarku har yasa kuke neman sassauci daga irin azabobin da za ku riska, ina son ku sani babu tudun da a ba hawansa ake ba, abinda zai hana kasar Baitul Haural su sassaraku su mai da jininku abin shan Kasa, shi ne karbar addinin mu na gaskiya, wato addininmu, ina son ku yi sani mun yarda da dükkan irin zabin yaki da zaku zo mana da shi, sai dai ina so ku sani duk wanda kuka zaba ba za a daina yinsa har sai an ga wanda ya ci nasara. Daga Sarki Abu Zaiyan dodon kafurai. koda ya zo nan a cikin karatunsa sai su duka suka dubi juna daga bisani kuma sai suka kece da wata shu'umar dariya mai firgita mai saurarc, koda kammala wannan dariya sai suka fito suka sa a ka kira manyan jarumin na kowace 24 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI kasa daga kowanc Sarki kowane Sarki akwai gawurtaccen Sadauki ashirin a cikin ashirin kuma aka zabi goma wanda suka fi kwarewa ya zamana sun kai su talatin kowannensu ba sai an fada ba da gani kasan maye zai ci mutum. Lokacin da aka fito da da Wadannan samudawan Dakarun kowa dakc gurin sai da gabansa ya yanke ya fadi da ganinsu domin kuwa mamaki ne ya kama su suka rasa ta ina aka fito da wadannan samudawan abinda jama'a basu sani ba shi ne kebantattu ne da aka boye su ake kuma kula da lafiyarsu ake saboda kada ciwo ya kama su su mutu, irin mutuwar cuta ba a filin daga ba. Domin a ganinsu wannan ba Karamar asara bace. Acan kuma sansanin Sarki Abu zaiyan lokacin da dan aiki ya baro sansanin sai Sarki ya tara manyan kasar da dukkanin jama'ar da ake tafe dasu. Koda kowa ya nutsu sai Sarki ya numfasa ya ce, "Ya ku jama'ata ku yi sani cewa wannan shiri ne abokan gabarmu suka zo mana da shi, domin sun san cewar idan har muka yi yakin mamaya da su 25 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI suna ganin za mu samu nasara a kan su, sai suka yi dabara suka bukaci da mu yi yakin daidaiku za su iya samun nasara a kanmu, shi ne dalilin da ya sa suka bukaci da ayi wannan yakin. Sarki ya ja numfashi yana kallon jama'arsa sannan ya ci gaba da cewa. "Hakikanin gaskiya suna da manyan sadaukai masu kumari, da za su iya samun nasara a irin wannan yakin, amma ni zan nuna musu cewar ba ma dogara da wani a cikin gogaiya da juna, zan nuna musu da Allah muke takama dan haka na hutar da kowa a cikin mayakana, ni da Sarkin yaki Safwan da kuma Yarima Zaiyan mu kadai ne zamu dinga karawa da wadannan dakaru har sai mun ga karshensu, in har kuma sun sauya mana yarjejeniyar da muka Kulla a tsakani to babu shakka za mu tarc su mu yi yaki da su babu ji babu gani" Koda Sadauki Zaiyan da Sarkin yaki 26 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI Safwan suka ji wannnan Sanarwa sai kawai murna ta kama su, ka ji maza, maimakon su ji tsoron wannan gumu da za su yi amma su farin cikin suke. Lokacin da wasu daga cikin manyan mayakan kasar Birnin Baitul haural suka ji wannan sanarwa sai bakin ciki ya kama su, domin kuwa ba haka suka so ba tuni sun fara wasa makamansu saboda kawai suna ganin lokacin da za su wasa jininsu ya yi, amma jin wannan sanarwa sai yasa wasunsu har zubar da kwalla su kai. A cikin masu kuka kuwa har da Gimbiya Lushmaira hankalinta ya yi mutukar dugunzuma ainun da kyar ta iya cin abincin da aka rarraba musu, ita kuwa Shadilat sai ta danne duk da ta so a ce ta yi wani a bu a cikin wannan yaki. A wannan lokaci da Sarki Abu Zaiyan da Yarima Zaiyan da kuma Sarkin yaki Safwan suna tsakar filin gurin da 27 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI suka yada sansani su uku suna tattaunawa, fuskar Yarima Zaiyan da ka gani kasan cewar yana cikin tsananin bakin ciki. Aikuwa suna nan tsaye sai ga Kora ta tokare sararin samaniya lokaci guda kuma hargowar kafurai ta cika kunnawansu ta batse. Koda Sarki Abu zaiyan ya ga wannan sai ya yi murmushi ya cе. "Matsoratan sun fito ya kamata ace دو mu shirya dan a fara gwagwarmaya. Koda jin wannan batu sai Yarima Zaiyan ya ce, "ai kuwa in haka ne bari na isa gare su na sanar da su cewar su shirya." Sarki Abu Zaiyan ya ce "Ka zama cikin shiri kawai ai sun fi ka gaggawa domin suna ganin cewar akwai nasara. Aikuwa Sarki bai yi aune ba ya ga alamun sun fara kewaye filin gurin har ya zamana an ajiyewa shugabanninsu kujerun alfarma da za su zauna. nan take shi ma 28 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI Sarki ya fara sa jama'arsa da su kewaye filin nan da nan ya zama ankewaye filin gurin baki daya. Sarki da Yarima da' Sarkin yaki kuwa sai suka kara kebancewa da fara shiri. Daya daga cikin Manyan Adawan Su Sarki Madham sai ya fito tsakar fili da wani garjejiyar gudma a hannunsa wanda tsaye da kauri Gudumar zata iya yin girman garjejen kato, sannan hannunsa na dama kuma rike yake da wata karkuwa, katon sai faman ihu yake yana dokan jikinsa yana huce yana aibata addinin musulunci. A wannan lokacin su Sarki Abu Zaiyan ba su ma fitar da wanda zai fara karo na farko ba. Koda ganin wannan kato yana ta ihu da wadai ga musulunci sai ran Yarima Zaiyan ya baci ya dane dokinsa da alamar 29 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI zai hau ya tunkari wannan sadauki. Sarki abu Zaiyan sai ya yi tsawa a gare shi ya dakatar da shi, ya ce, "Bana bukatar ka tunkari wannan wannn aikina ne, kafin wani ya yi yunkuri sai Sarki ya zaburi doki ya nufi filin cikin kuwa da kabbara. Daukacin abokan gaba ganin Sarki a cikin wannan fili sai suka cika da mamaki Sarki Tarmas da sauran sakaran sai suka fara murna suna masu kara yiwa Wannan kara sadaukin karfin gwiwa. Saboda ya yiwa Sarki farad daya wanda yin hakan tamkar samun gawurtacciyar nasąrarsu ce. Shi kuwa Sarki sai ya yake ji kamar shi suke kara karfin gwiwa ya kara yiwa dokinsa kaimisabin da ya kara basu mamaki lokacin da Sarki ya isu kusa sosai su suka lura a she babu makami ko garkuwa a hannunsa. Wannan abu ya kara sawa suka saka 30 TURBAR GASKIYA--4 rai na samun nasara. MADAKIN GINI Lokcin da Sarki Abu Zaiyan ya isa ga wannan Sadauki batare da wani makami ba, sai doka tsalle tun saura baifi taku goma a tsakaninsu ba ya dira a gabansa. Taron 'yan kallo suka mai da kansu sama suna ganin yanda Sarki abu Zaiyan ya wulwula a sararin samaniya. Shi kansa Sadaukin dake ta faman jijjiga jikinsa yana kurari ganin irin shillon da Sarkiya yi sai abin ya ba shi mamaki amma kuma da yaga Sarki Abu Zaiyan a gabansa kamar giwa da 'yar karamar 'yarta sai ya 6ace da wata shu'umar dariya. Yana dariyar yana nuna Sarki da hannunsa yana kara kyakyacewa, wannan dariya da wannan Sadauki ke yi sai ta fusata ran Sarki Abu Zaiyan ya dunkule hannunsa da niyar ya dankarawa wanna 31 TURBAR GASKIYA--4 MADAKIN GINI basamuden Sadauki duka, sai aka daka masa tsawa daga bayansa, wannan dalili ne yasa ya fasa aniyarsa ya juya don ganin mai aikata wannan sako a gareshi. nekan sKoda ya waiga sai yaga Sarki madhan Sarki Husaka, tare da Sarki Tarman suna nufowa inda yake tsaye. iB Koda ganinsu sai Sarki Abu Zaiyan ya yi murmushiya kuma dubesu Pa wufakance ya yi kaki ya tofa a tsakaninsu. nollinyin wannan kaki a garesu yasa sauran dakarun suka fashi dawani hargitsantsan ihu na kai Bara suna masu gyara makamansu suna kokarin yin kan Sarki abu Zaiyan a fusace, sai Sarki Tarmas ya daka musu tsawa suka tsaitsaya. OUN RORY avish S asA can ma gefe sansanin su Sarki kuwa sai Yarima Zaiyan da Sarkin yaki Safwan suka nufo su a fusace. Sarki Abu Zaiyan ya yi saurin dakatar da s ed 132 TURBAR GASKIYA-4 MADAKIN GINI Koda akaa samu nustuwa na dan lokaci kuwaa na yi dan uwansa kallon banza, sai Sarki Abu Zaiyan ya dubi dukkan Sarakan uku a wulakance ya ce, "Ina mai bukatar ku bamu fili domin fara gugaiya da abokan gaba a sanina daku banda Karfin baki da surutun cece kuce babu wani abu da kuka fi kwarewa akai nan fili ba gurinku bane dan haka ku koma mazauninku ku kalli yanda jini zai tsiyaya a kan kasa, yanda harshe zai karci kasa, lallai ba zan gusheba ina gidadddaba wadannan Samudawa face na ga bayansu dan haka ku koma ku yi saurare ku kuma zuba idanuwan." Koda Sarki Tarmas da kuma sauran sarakan suka ji wannan umarni daga Sarki Abu Zaiyan sai suka hada baki suka bushe da wata shu'umar dariya keta. Wannan dariya ce ta fusata ran Sarki ya daddage ya doka musu tsawa wacce ta 33 TURBAR GASKIYA--4 MASAU MADAKIN GINI yi sanadin tsayar da dariyar ta su, sannan ya nuna su daya bayan daya ya cе. Dukkanin wanda ya kara yin sakaci a cikinku yanzu take zan tsaida numfashinsa ya zamana na yi masa bakin ciki da ganin gagarumar bajinta da za a yi a wannan filin daga." Saboda iirin kakkarfar lafazi gami da budaddiyar muryar da da Sarki Abu zaıyan yayi amfani da ita sai dukkaninsu jikinsu ya yi sanyi suna ganin zai iya aikata abinda ya fada sai suka yi gum. Da kyar Sarki Madhman ya maso kusa da Sarki ya ce, "Ya kai abokin gabarmu muna so mu san yawan Dakaru da za a yi wannan kwafsawar da su domin sanin adadin zai amfanar da mu da ku, mu gane dawa-dawa za a kara.?" Koda jin wannan ba tu sai Sarki Abu Zaiyan ya ji wannan ba tu sai ya yi murmushi ya ce, Bana bukatar sanin 34 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI Π yawan dakarunku daga gareku domin na riga na 'yarga yawansu su kimanin talatin ne, wadanda aka tace daga manyan Zakarun a cikin kasashenku, kamar yanda dukkanin giman wadannan adawa naku suke kuma rike da manyan manyana makamai masu tsananin girma da bantsro to ina mai sanar da ku cewa yawa Dakarun da zasu fito filin da mutum uku ne kacal, NI Sarkin yaki sai kuma Yarima Zaiyan kuma a dukkaninsu babu wanda zai fito filin daga da makami ko garkuwar kare kai, sai a ciki a filin ne zai kwace na Makami kare kai da na barautar rayuwa mu yi gutsi-gutsi da sassan jikin Sadaukanku sannan a kowanenmu zai kara da mutum goma daga cikin talatin din da kuka tanada duk wuya duk rintsi wannan ba zata canza ba, da yardar Sarki Allah mai iko mai yin yanda ya so daga garcshi nasara take kuma daga gareshi muke nema 35 CADA TURBAR GASKIVA --4 MADARKIN GINTUT cikin natunsasdi yartarsa suka Kaure аa kab8aLoaein aa sarakan uky daskuma m mamayes(fbaomina gaiin nasara sun gani da naka lm sa SwSXOREaka natsa da iha da kabafaina kbwane Sansaf? liSadhu TSAMukane jikinsa yand dagamanfib sgsb nilil otil Nan SarkiTamagrda BSdki ipusinh inеM madhman suka kölha KelHan zauna suna RanoH Wan ekh2 da rath cikr ikdmidisuh san Hasara tasdm nanngh kuwa SavAbulZa!Sgush!skKk dubi gabas ya i sújfada ga A ad ya mikë va daga hkrfiry yiadugraKaiean ya shafa ya dubi Sadaukst glgegU TURBARUNGRAVA --4 A-MADAKIN GINUT S MAoiqaskiya ibanda Sarki Abu Zasi daesbrovkumalbai san tsovo ba daswobu sthaeksisay ydlijis tsoron Makanu ddhnskuskunburejilimsSadauki makamu abussaisdaduwat ugaba neшрasкyanda desAsengokeanawa16u26alakaisikacels wata bijimar Mesa demakelkwamto raka nuvfdrfasi, obwarwans kardaid Adolesyasa Babnugighdakisal sladowaryid igabaşb müsammansrii makami näakaresdangi sdav yaale bulimumsay sanithal list Amma shi Sarki AbuZaiyan kó ldra2 dakh dayilba fataasa kawal stbja daga aikyw adiTadaninoVkaton uyadsshamamnales Sa Zalyint yadwdbulmasaukatuwar garkwarsaundalshiyanutaiy GallawalAbud Zalyan bayangut BY TaVin sb slisri ses Koda SarkiAbplaiyasyauba gahowaak wannan garkowa uamkaMansbakaubwari an habotavsaboda isananin gudon dahake ares waki ithskinakara nakeniammas kafini kuw2 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI ya ankara tuniSarki Abu Zaiyan ya tafi ga garkuwar nan sai da ya kusa isa gareta sannan ya daka tsalle ya takata ta kowa kara masa karfin ta shi sama koda ya tafi cikin iska tamkar an har ba shi bai sauka ako ina ba da kafafuwansa biyu ya doki kirjin Sadauki Makanu. Sarki Abu zaiyan ya fado kasa baya da taku biyar saboda tsananin bugun da ya yiwa Makanu shi kuma Makanu ya yi amfani da karfin kirijinsa ya yi cille da Sarki Abu Zaiyan. Koda Sarki ya gansa a kasa ga kuma Sadauki Makanu a tsaye tamkar ba shi ya yiwa wannan dukan ba, sai ran Sarki ya 6aci, kafin ya yi aune Makanu ya ta so masa haikan da niyar ya rugaza shi da katuwar gudumar dake hannunsa. Gudun da Makanu yake shi ya tsorotar da zuciyar su Yarima Zaiyan da sauran jama'a domin tun kafin Sarki ya 38 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI farga ga shi kuma ya fargar amma bai yi wani yunkuri ba duk da cewar saura kiris Makanu ya isa gare shi abinda basu sani ba kofar ragowa ya yi masa sai da Makanu ya gama bada karfinsa guri guda sannanne Sarki Abu zaiya ya yi katantanwa ya fille kafafuwansa. Aikuwa sai ga Makanu ya tashi sama tamkar wanda aka saka kugiya ta shilla sama da shi, kana ga gudumarsa ita ta yi sama. Ganin haka Sarki ya yi sufa ya dauki Gudumar kafin Su iso kasa, sai ya saita tsakiyar kan Makanu ya buga masa ita ai kuwa ID DCsai jini aka gani ya yi tsartuwa a filin gurin, gawar Makanu ta silalo kasa sai ga shi jini sai zuba yake ta ko'ina yana shuri-shiru mutuwa. Nan take Hangaren Sarki Abu Zaiyan aka hau tafi da shewa ana kabbara da kiran sunan Allah, shi kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya shiga zarya yana jiran wani mai 39 TURBAR GASKIYA--4 karar kwanan a tsakiyar fili MADAKIN GINI Wannan al'amari ba karami mamaki ya bawa kowa ba a cikin sahun sahun kafurai da manyan adawan da aka tanada dan maganance musulunci da kautar da TURBAR GASKIYA. Amma sai suka sauri suka turo wani Narkeken kato wanda ake masa lakabi da suna Jaura, shi dai wannan Sadauki an haife shi a na lokacin da ake muku-mukun sanyi wanda kuma saboda tsabar haihuwarsa da a ka yi da abubuwan al'ajabi a wannan lokaci haka ya kasance har sai da Lokaci ya wuce sannan aka saka masa riga da wando kai sannan ne ma aka fara gasa masa cibiya, wannan dalili ne aka saka masa suna Jaura, kuma a duk lokacin da wannan Sadauki ya fi saukaka al'amuran al'umma shi ne lokacin Jaura, baya fada ko mai ka yi masa. Dan haka Sai Jaura ya fito a cikin 40 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI hargitsantsan gudu da niyar ta take Sarki ya yi tamole da shi. Kowa dake filin sai da ya ji faduwar gaba da fitowar Jaura domin girmansa ya yi Makanu sai biyu sannan kumarinsa ya ninka na Makanu ga shi baki wuluk ko dan haske rahma babu a fuskarsa uwa uba ga irin makamin da yake rike da shi, wani dogon mashi ne amma bakinsa mai tsini ne da shi wani fataitane mai baki shi da wanda idan aka su ke ka da shi babu mamaki sai ya zaftaro duk wani abu da yake cikin cikinka. Koda ya nufo Sarki Abu Zaiyan da wannan makami cikin tsananin gudu wanda yasa kasa girgiza, koda ya rufo Sarki sai Sarki abu Zaiyan ya juya da baya ya fita da gudu kamar ya ji tsoro wannan al'amari ya saka su Sarki Tarmas dariya suna ganin Sarki tsorata ya yi, koda Suka zuba tsare tsakanin Sarki Abu Zaiyan da Jaura sai suka ci gaba da falfalawa Sarki 41 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI yana zagayawa da Jaura a fili har kusan rabin sa'a a wannan lokaci kuwa sai Jaura ya tsaya yana haki, shi kuwa Sarki Abu zaiyan sai ya tsaya a gabansa ya ce. "Yanzu ne ya kamata mu yaki juna ni da kai." Kafin Jaura ya yi wata magana tuni Sarki ya yi kansa nan take suka kauri da hargitsantsan yaki suna kai sara da suka babu ji babu gani, dukka wani sara da jaura ya ke kaiwa Sarki sai Sarki Abu zaiyan ya kauce, a haka nan ma Sarki ya Kara wahalar da Jaura har ya zamana jaura ya fara yin laushi da kai sara da suka, amma saboda tsananin taurin rai da karfin hali bai fasa ba, shi kuwa Sarki Abu Zaiyan sai ya tikirkire ya dunkule hannu ya shammace Jaura ya dokan masa mukamuki da hannun nasa. Sadauki jaura ya shamye dukan tamkar sauro ne ya cije shi ya kawowa 42 TURBAR GASKIYA -4 MADAKIN GINI Sarki cafka da niyar ya daga shi sama ya jefar da shi sannan ya bi shi da suka, aikuwa sai Sarki ya kauce jaura ya kara kai hannu nan take ya yi sa'ar damkar Sarki Abu Zaiyan ya daga shi sama sai ya daga shi ya dankara Sarki da kasa, maimakon Sarki Abu zaiyan ya fadi kasa ya ji ciwo ko ya karkarye sai kawai aka ga Sarki ya dirga akan kafafuwansa daram, ganin haka Jaura ya kawo suka, Sarki ya rike mashi da hannunsa tamau. Jaura ya ja mashi da iyaka karfinsa mma sai ya ji ya kasa kwace, dan haka sai ya kawo mangari da Garkuwarsa, shi kuwa Sarki Abu zaiyan sai ya yi matattakala da Garukuwa ya tafi a sama ya doke Jaura a fuska, wannan dalili ne yasa Jaura sakin Mashin ya tafi taga taga zai fadi nan take Sarki Abu zaiyan ya loma masa wannan mashin a ciki, ya kuma zaro Mashi lokaci guda, Sai ga Jaura yana ihu,'ya'yan 43 TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI hancinsa hanta kuda da sauran kayan ciki sun yi fitar burgo Koda faruwar Wannan al'amari sai kuwa da ihu ya cika gurin baki daya aka kama Kabbara, mamaki irin Sadaukantakar Sarki Abu Zaiyan ta cika zuciyar Yarima Zaiyan da Sarkin yaki Safwan da Kuma Lushmaira da kuma Shadilat da sauran jama'ar da suka taho dan yi jahadi. Su Sarki Tarmas kuwa sai suka ji kamar su fashe da matsanancin kuka saboda ganin 6arnar da Sarki ya yi musu a dan kankanin lokaci ya karar musu da sadaukan da idan da fadan Yamutse akai da tuni sun kashe ya kai Dubu goma amma sun salwanta batare da sun ji gabata Sarki ba, nan take Sarki tarmas ya dubi Sarki Madham ya ce, "Ai kuwa ba

Chapter 9 of 11