wuka muka
dauka muka dabawa kanmu ba ya ya kuke
ganin zamu samu nasara alhalin a cikin
44
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
majiya karfin talatin da muke ji da su, biyu
sun tafi, ta hanyar Sarkinsu kadai. Kada ku
manta a kwai Sarkin yaki Safwan mun san
kwazonshi ba tun yau ba, ga kuma Yarima
Zaiyan wanda labari ya zo mana cewar shima tsakwakurine."
Koda ya kawo nan a cikin batunsa
sai Sarki Husaka ya ce, "Haba ya kai Sarki
Tarmas kada ka manta, da waye Sarki abu
Zaiyan ai ku da za a samu lagonsa ba
yanzu ba, kai da ka zuba ido akwai ribar a
nan gaba.
Kafin su ankara sai suka ji ihu wani
Barden ya fito ganin wannan katon da ake
Kira Rislalu sai hankalinsu ya kwanta
domin kuwa shi kuma bai da wani lokaci
da aka taba nasara akansa, duk irin yaki da
ya yi a duniya wanda a kalla ya yi yakukuwa dari biyar, ba'a taba samun
lokacin da aka lakuci koda yatsansa ba,
saboda tsananin masifarsa a filin daga ko
45
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
jinin makiya bai taba wanke masa fuska,
saboda zafin namansa kuwa sai ya kashe
mutum biyar a sa'ili daya
Dan haka ko da ya fito sai suka kara
mai da hankali a fili, bai Kai Jaura tsaho
ba amma dai ya fi Jaura kauri shi a cure
yake guri gudu, ya kware wajen raba hanta
da jini, sannan ya kware wajen sarrafa
masana iya yaki, takobi ce guda biyu a
hannunsa dukkaninsu basu fi kamu uku
uku ba, yana tafiya yana jijjiga kwanjinsa
yana motsa ga66ansa dan karamin bante
ne a jikinsa kawai dan haka surorin jikinsa
duka a waje.
Sarki Abu Zaiyan ya na rike da
mashin da Ya hallakar da Jaura, sai ya
wullar da shi gefe, a wannan karon sai ya
tsaya yana murmushi, shi kuwa Risalu sai
ya tsaya yana hararar Sarki. Wannan
al'amarin ne ya fusata Sarki Abu Zaiyan
ya kukan kura ya yi kan Risalu, aikuwa
46
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
yana isa gare shi sai Risalu ya daga
kafarsa cikin a zaba ya doki Sarki a kirji,
Sarki ya tafi da baya ya fadi kasa.
Cikin fushi Sarki ya mike tsaye ya
fursa da yawu, ya kara yin kan Risalu da
gudun koda ya isa kan Risalu sai Risalu ya
soke Takobin ta shi guda biyu a jikin
bantansa ya kama Sarki ya daga shi yasa
ya wujijjiga shi ya cilla shi can gefe daya.
Abin da Sarki ya fara lura da shi ga
wannan Sadauki ba a yi masa shigar burgo
domin a kasa yake, yana iya fahintar duk
da irin yunkurin da ka zo masa da shi, dan
haka sai ya daina binsa, shi kuwa sokon
sai yake tsammanin Sarki tsoro ya ji dan
haka sai ya nufo Sarki yana mai kiran
Sarki da hannu wato yazo Sai Sarki yake
ja da baya har ya zamana Ya takure Sarki
Abu Zaiyan ya kai shi karshen inda jama'a
su ka yi musu da'ira, Sarki na ja da baya
shi kuma na kusanto Sarki, ai kuwa sai ya
47
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
yi sufa ya kamo Sarki da hannu daya ya
daga shi sama, koda Ya daga Sarki sama
ya kama jijjiga shi yana kokarin ganin ya
runtuma shi da kasa, shi kuwa Sarki a she
ya dauke takobi daya daga jikin bantai din
Risalu aikuwa nan take Sarki ya
shammace ya soka masa takobin a cikin
hammatarsa.
Wani abin mamaki sai Risalu ya yi
cilli da Sarki ya kuma kama kotar Takobin
ya cirota daga hammatarsa ya kurma wani
uban ihu na fusata yabi Sarki da niyar ya
danne Sarki ya ja daga ya daina ja da baya
lokacin da ya iso gaban Sarki sai Sarki ya
kama kai masa duka da hannu da kafa
aikuwa sai salon fadan ya sauya nan suka
shiga kaiwa junansa duka da hannun da
Kafa suna karewa a wannan lokacin ne
kowa ya samu naushi a baki har sau uku.
A sannane suka ja da baya, kamar
wasu Zakaru, wannan al'amarin ba
48
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
karamin yiwa Sarakan uku dadi ya yi ba
domin ganin yanda Risalu kawai ke walar
da Sarki.
Shi kansa Sarki ya yi mamakin
yanda Risalu yake fahintar dukka irin
abinda ya yi niya, amma sai ya sauya
dabara, cikin zafin nama Sarki Abu
Zaiyan ya yi kansa, shi kuma Risalu sai ya
tsaya yana tunanin ya tare shi, amma me a
lokacin da Sarki ya isa gare shi sai ya zabe
daga waftar da ya kawo masa ya kuma
sace wukar ta daya kubin ya soka masa a
dokin wuya.
Lokaci guda Su Sarki suka ga Sarki
ya wuce salin alan shi kuma Risalu ya yi
tsaye, ya kuma daina motsi, suna tunanin
wani karfin shifin yake sai kawai suka ga
Risalu ya fadi riga ji a kasa ku shurawa
bai yi ba sai a sannnne suka ga ashe soka
masa wuka Sarki ya yi ta dokin wuya.
Wannan al'amarin ne ya jawo
49
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
hankulan Sarakan domin a tsai da fadan
haka kowa ya kuma ya kara shirin.
Nan da nan suka bukaci haka Sarki
ya yi farin ciki da haka domin dama
lokacin Sallah ya yi, dan haka kowanenesu
sai suka koma nasu sansanin.
Lokacin da Sarki Tarmas da kuma
Sarki Husaka da Madhman suka kebance
sai Sarki Madham ya dubi Sarki Husaka
ya ce, "Hakikanin gaskiya akwai gyara a
cikin wannan yaki, saboda haka ku saura
shawara, ni dai ina da ita in ma baku da ita
abin nan dole a samu a bi ta karkashin
kasa, ba komai nake nufi ba face, a cikin
Sadaukin da zasu kara da Sarki Abu
zaiyan akaro na hudu ya kamata a ce, An
samu wata guba da za'a yi amfani da ita a
shakawa Sarki, idan ya so shi Sadaukin sai
ya yi farat daya ya kashc shi, ka ga dai ku
dai fili ya hautsine mun samu babbar
nasara.
50
TURBAR GASKIYA--4 MADAKIN GINI
Koda jin wannan shawara ta Sarki
madham Sarki Husaka da Sarki Tarmas sai
suka hada baki suka ce, "Kai da kana da
wannan dabara amma baka yi sauri zuwan
mana da ita ba.
Da jin haka sai Sarki Madham ya yi
murmushi ya ce, "Hakika a baya bani da
wannan dabara amma a yanzu da wahala
ta kai wahala (sai ta fado min dan haka
yanzu abinda za ayi shi ne mi yi umarni
da ahada huda da gumar da zai shaka, ya
mutu.ua
LHAikuwa nan take su Sarki suka yi
umarni da aka hada wannan abu, Sadaukin
da Za'a yi wannan fafatawa da shi, aka ba
shi aka kumà sanar da shi yanda zai yi aiki
da ita, nan take sai suka ci abinci suka
samu hutu, sannan suka komafili пто0
wwed Avcan kuwa 6angaren Su Sarki Abu
Zaiyan an yi sallah an ci abinci, dan haka
Sarki ya karayin bayanit dan Karawa
251
TURBAR GASKIYA --4 WMADAKIN GINI
jama'ar imani da tsoron Allah sannan ya
Kara yin shirin yaki, aka fito filin daga
Koda fitowarsu sai suka ga ashe tuni
Sadaukin da za a yi karawar da shi ya fito
yana tsaye a filin daga yaña ta dage dagen
hannu ana tafa masa.ie aled ni Д
ab ing Shi kuwa Sarki sai yayi sallama da
jama'arsa ya shiga tsakiyar filin batare da
shakka ba, Yarima zaiyan a wannan
lokacin suna zaune da Shadilat suna hira
mai dadi ita kuma Lushmaira tana can
bayansu kishi duk ya hanata sukuni, banda
harara babu abinda take aiko musu da ita.
Amma lokacin da aka fara kwafsawa sai
hankalin. kowaya koma kanfilin
fafatawar. busy ide eb tausz sok eks ida
sduAna shiga fili sai aka fara fafatawa
domin kuwa kowa a huce yake, lokacin da
suka fara artabu sai fadan ya fara bawa
kowa mamaki domin yanda suka kasance
cikin kaiwa juna bara hannu da kafa suna
1252
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
shillo tare da kaucewa dukan juna, tun da
aka fara wannan karafkiya babu wanda aka
taba Sarki shi kansa wannan fadan yafi
burgeshi da yakin da su ka yi a baya
domin kuwa a wannan yakin yafi zagin
damtse a dirji juna abinda ya fahinta da
sabon Sadauki shi ne masani ne wajen iya
yaki da hannu ga takubba a hannunsa
amma bai damu da ya kai suka da ita ba, a
na cikin haka Sarki ya yi sa'ar naushinsa a
fuska.
Ya tafi daga taga zai fadi sai ta tirje
ya gyara rikon Banjo din da aka ba shi a
hannunsa ya kusanto Sarki Sarki ya yi
alkafira ya doke shi a kirji sadauki ya kara
yin baya, amma saboda naci ya kara
dawowa nan suka kara kaurewa da sabon
yaki, domin ya sanja salon fadan ganin
Sarki ya fahinci inda ya dosa anan ne ya
samu lagun Sarki har ya naushi a fuska sau
biyu kuma a cikin naushin ne ya yi sa'ar
53
TURBAR GASKIYA --4
shaka masa wannan Banjo din.
MADAKIN GINI
Aka ci gaba da yakin kamar Sarki
bai ji komai ba, suna cikin yaki Sarki ya
shammace Sadauki ya karya masa wuya
6aras.
Ai kuwa kafin ya sake shi wani
Sadauki da ake kira Hirnanu ya fusato ya
fito da karfi ya taka Sarki, Sarki Abu
Zaiyan ya mirgina kasa ya mike cikin
dauriya, kafin ya kara yin wani yunkuri
Hirnanu ya kara yin dirango a bayan Sarki
ya kirbawa Sarki naushi a mukamuke ya
kuma zare takobi da niyar ya sare masa kai
amma sai Sarki ya baje a kasa ya kuma
kwashe kafafuwan Hirnanu.
Nan take Hirnanu ya zube kasa,
Sarki ya ya kama kansa ya danna a cikin
kasa, aduk girman Hirananu sai ga shi ya
kasa kwacewa ga shi kuma sai tirjjiya yake
saboda tsananin walaha babu damar
shakkar numfashi sai dai kasa da yake
54
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
shaka Sarki Bai daga shi ba sai da ya ga ya
daina motsi.
Nan ma Sarki bai daga Mataccen ba
wani sadauki ya kara yo sufa ya dake shi
ta baya Sarki Abu zaiyan sai ya fadi kasa
kuma ya kasa ta shi. A wannan yakin da
(aka yi su Sarki tarmas suna ganin cewar
gubar bata samu shiga Sarki ba amma
ganin ya kasa ta shi sai suka kama murna
domin sun san aikinta ne.
Koda Wannan Sadauki ya kara yo
tsalle sai ya kama Sarki da niyar ya jashi a
kasa, amma sai Sarki ya cije, yaki ya jawo
shi kuwa Sadauki sai kokarin janshi yake
a cikin wannan lokaci ne aka ga jikin Sarki
ya saki nan take ya fara yin amai, aikuwa
nan Sarki Yaki Safwan da kuma Yarima
Yazid suka kamo da tsananin firgici har ya
zama sun yi rige rigen tasowa amma Sarki
na ankarewa da su sai ya daka musu tsawa
da su dakata, shi kuwa wannan Sadaukin
55
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
koda ya jawo Sarki Gaban Sarakan Sai ya
cire wani katon gatare daga jikinsa ya daga shi zai sare kan Sarki, har idanuwan jama'a ya rufewa kawai sai gani akai
Yarima Yażid ya taho cikin iska ya doki
wannan Sadauki ya fadi kaka ya fada kan
gatarin ya cire masa makogaro cikin sauri
ya dauke Mahaifinsa da yake ta faman a
man jini ya kaishi sansaninsu. Kafin ya dawo filin dagar kuma sai suka ji wani irin nishi mai karfi ya karade filin gurin baki daya, wannan al'amari sai ya dugunzuma
hankalin duka jama'ar da suke wannan
gun, suka saka idanuwan sosai.
Aikuwa kafin kiftawar idanuwa Sai
ga Macijiya Burukul Kursum ta bayyna cikin tsananin tashin hankali.
A nan take Yarima Zaiyan ya dakata da yunkurinsa domin daga zuwanta har ta yabcari kadan daga cikin al'ummarsu ta yi
musu loma daya.
56
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Daga Abdul aziz sani madakin gini
mai debe muku kewa akowane lokaci sai
mun hadu a cikin littafi na biyar dan jin ci
gaban wannan labari na TURBAR
GASKIYА
SHIN SARKI ABU ZAIYAN ZAI
SAMU LAFIYA?
WAYE ZAI KARASA KARAWA
DA WADANNAN ADAWAN DA SU
SARKI HUSAKA SUKA ZO DA SU?
SU WAYE ZA SU NASARA A
CIKIN WANNAN GAWURTACCEN
YAKI A TSAKANIN RUNDUNAR
MUSULUNCIN DA KUMA
RUNDUNAR KAFURCI?
YA YA ZA AKWASHE DA
MACIJIYA BURUKUL KURSUM A
CIKIN WANNAN HALI.
A TSAKANIN SHADILAT DA
GIMBIYA LUMSHAIRA WACECE
TAFI KAUNAR YARIMA YAZID.?
57
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
WANE NAMJIN КОKARI
GIMBIYA LUSHMAIRA ZA TA YI
HAR TA ZAMO YARIMA YAZID ZAI
AMINTA DA JARUMTAKARTА.
Sai mun hadu a littafi na biyu
58
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
TALLLA! TALLA!! TALLA!!!
A wani zamani can baya mai tsawo da ya
shude bayan shudewar mulkin fir'auna na birnin
misra an yi wata azzalumar sarauniya mai suna
Zuhaira bin Masrud.
Sarauniya zahuira tana mulkin wata
babbar kasa ce dake bakin gabar tekun bahar
sufiya kuma ta gaji sarautar ne a wajen
mahaifinta sarki masrud bin Zaurid
Sarki masrud ya kasance gawurtaccen
mayaki wanda yai shuhura zamaninsa kuma shi
a rayuwarsa babu abinda ya tsana sama da
ma'abota addinin musulunci ba komai ne ya
haddasa mummunar gaba tsakaninsa da
ma'abota addinin musulunci ba face akwai
watarana da wadansu fatake ma'abota addinin
musulunci da suka zo giftawa ta birninsa, sai
suka yada zango a gefen garin domin su yada
zango.
A wannan lokaci akwai wani takadirin
aljani a cikin birni na Sufras wanda muatena ke
59
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
bautawa a matsayin ubangijinsu. A kullum sai an
yankawa wannan aljani raguna uku, shanu, uku
da rakuma uku, kuma Sarki masrud ne da kansa
yake jagorantar wannan hadaya da ake yiwa aljanin mai suna burrata.
A ranar da wadannan fatake suka ya da
zango a bakin birnin Sufaras ne wata annoba ta
zo birnin ya zamana cewa gaba daya dabbobin garin da tsuntsayensu sun kamu da wata irin cuta
ta gudawa don haka sai suka rinka mutuwa wasu
kuma suka lafke ya zamana cewa ko ta shi basa
iya yi.
Bisa ka'idar hadayar da ake yiwa aljani burrata ana yanka masa lafiyayyun dabbobi ida
kuwa aka kuskura aka yanka masa mara lafiya
koda guda daya ne kacal a ranar babu wanda ya isa ya yi barci a garin kuma duk kanannan yar dake garin sai sun kamu da cutar da zasu yi ta
mutuwa haka kuma idan aka saba lokaci na yin
wannan hadaya to fa sai wannan bala'i ya afko. Sarki marud. yana samun dukkan biyan bukatarsa a wajen aljani Burrata bisa wannan
dalili ne baya yarda a sami matsala a ko kadan akan yi masa hadaya.
60
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
Lokacin da ake yin wannan hadaiya ga
aljani Burrata da yammaci ne sakaliya daf da
magruba tun da rana wannan annoba ta afku a
cikin birnin na Sufras al'amarin da ya
dugunzuma hankalin Sarki masrud ke nan ya
baza dakarunsa ko ina a cikin birane da kauyuka
na kusa a kan a nemo lafiyayyun dabbobin da
za'a yankawa aljani Burruta kafin rana ta fadi.
Ai kuwa har gefen la'asar ba'a sama
dabbobinba sai ga Dakarun da aka tura sun dawo
cikin gigita da dimauta, shugabansu ya zube
kasa a gaban Sarki masrud ya ce, Ya shugaba
mun duba ko ina a cikin biranc da kauyuka dake
kusa da wannan kasa tamu babu inda wannan
annonba bata je ba, mun rasa lafiyayyun dabbobi
amma akan hanyarmu ta dawowa mun ga
wadansu bakin fatake kuma suna da dabbobi
lafiyayyu fiye da adadin da muke bukata.
Koda Sarki jin wannan batu sai farin ciki
ya lullube Sarki Masrud ya ce, "Maza ku koma
wajen wadannan fatake ku siyo daddbobin da
muke bukata a wajensu komai tsadarsu kuwa,
idan suka ki siyar muku ko kwato su da karfin
tsiya ku zo mini da su, domin mu hanzarta zuwa
61
TURBAR GASKIYA --4
dakin bauta.
_MADAKIN GINI
Koda jin wannan batu sai Shugaban
dakaru ya mike tsaye da sauri yana mai cewa an
gama ya shugabana, nan take ya jagoranci
dakarunsa kimanin su dari biyu suka hau
dawakansu suka zaburesu da gudu izuwa gfen
gari
Su dai wadannan fatake da suka ya da
zango a gefen birnin sufras gaba dayansu basu fi
su ashirin ba kuma duk zur'a dayane na wani
attajiri da ake kira Abu Salhaif.
Acikin wannan Zuri'a akwai matarsa guda
daya da kuma dansa shima guda daya jal wani
matashin saurayii wanda baisfi shekara goma sha
hudu ba, shi ake kira da suna Salhif, sauran
mutane goma sha bakwan daga kannensa sai
matansu, da 'yayansu.
Abu Salhif na tsaye tare da dansa Salhif
yana koya masa yadda ake yaki wato suna kaiwa
junansu sara da suka cikin gwaninta a gefe daya
kuma matarsa da sauran abokan tafiyar na tsaye
suna kallonsu sai kawai suka hango kura daga
can nesa ta turnuke sama, sannu a hankali suka
hango dakaru bisa dawakai a sukwane sun
62
TURBAR GASKIYA --4
durfafosu.
MADAKIN GINI
A zaton su Abu Salhif yanfashi ne suka
kawo musu hari, har mazajen cikinsu sun
yunkura zasu zare makamansu su tari mahayan
sai Abu Salhif ya daka musu tsawa, ya hana su,
don haka sai kowa ya tsaya a inda yake har
mahayan suka kara so daf da su suka yi turjiya
suna sanye cikin kayan yakin dakarun birnin
Sufras.
Koda Abu Salhif da jama'arsa suka ga
cewa ashe dakarun birnin Sufra ne sai hankalinsu
ya kwanta suka mayar da takubbansu cikin kufe.
Cikin biyayya Abu Salhif ya risina ga
shugaban dakarun ya yi gaisuwa sannan ya се,
"Ya ku Dakarun Sarki Masrud me kuke bukata
daga garemu har da zaku kawo mana ziyarar
bazato a irin wannan lokaci alhalin ko shigowa
cikin birnin naku ba mu yi ba?
Koda jin wannan tambaya sai Shugaban
Dakarun ya sauko daga kan dokinsa ya matso
daf da Abu Salhif ya ce, "Ya kai wannan attajiri
tsohon abokin cini kinmu ka yi sani cewa Sarki
ne ya tro mu gareku domin ku siyar mana da
raguna uku, shanu uku rakuma daga cikin
63
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
dabbobinkudomin mu bayar da jinin su ga abin bautarmu gunku Burrata."
Koda jin wannan ba tu sai hankalin Abu Salhif ya dugunzuma ya ce, "Subhanallahi ya kai
wannan badakare ka yi sani cewa mu musulmai
ne wadanda suka yi imani da bautar Allah Sarki guda daya wanda shi ne ya halicci komai da kowa har da shi gunkun da kuke bautawa, ta yaya zamu bayar da dabbobinmu kuje ku aikata
wannan mummunan sabo da su, ai idan muka
baku tamkar muma mun yi imani da abin da kuke bautawar ke nan, ku koma ku gayawa Sarki Marud cewa ni attajiri Abu Salhif nace ya yi hakuri ba zamu iya siyar masa da dabbobinmu a,
koda jin wannan ba tu sai shugaban dakarun ya tari numfashin Abu Salhif yana mai daka masa
tsawa ya ce, "Sarki ya bamu umarni idan har baza ku bamu wadannan dabobbi ba lallai mu
karbe su da karfin tsiya koda jin haka sai Mazajen ayarin na Abu Salhif suka zare takubbansu da nufin su yaki dakrun Sarki Masrud, amma sai Abu salhif ya sake daka musu
tsawa a karo na biyu ya ce, "Baku da hankali ne ta yaya zaku iya yakar dakarun kimanin dari
64
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
biyu alhalin gaba dayanmu bamu wuce mu goma
sha ba."
Nan take mazajen suka sake mayar da
takubbansu cikin kufe suka koma bayan Abu
Salhif suka tsaya a wannan lokacin ne bakin ciki
ya lullube Salhif har zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone jikinsa ya kama tsuma koda
shugaban dakarun ya lura da halin da Salhif ke
ciki sai ya bushe da dariya mugunta sannan ya
dafa kafadar Salhif ya се.
"Yaro ka yayyafawa zuciyarka uwan sanyi
idan ba so kake yanzun nan jini zuri'arku gaba
daya ya zube anan ba."
Koda jin wannan ba tu sai Saihif ya sake
fusata ya yunkura zai kaiwa badakaren Sara da
takobin hannunsa amma sai Saihif ya yi wuf ya
ruke hannunsa kuma ya zabga masa mari har ya
fadi kasa, cikin tsananin mamaki Salhif ya shafe
kuncinsa sa'adda hawaye ya zubo masa ya
kurawa mahaifinnasa idanu saboda wannane
karo na farko da ya taba marinsa amma ko bakar
magana bai taba gaya masa ba, nan take Abu
Salhif ya dubi Shugaban dakarun ya се.
"Za mu baku dabbobin da kuke bukata
65
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
amma ka gayawa Sarki cewa bukatarku ba zata
biya ba ta hanyar amfani da da dabbobin
ma'abota addinin musulunci koda gama fadin
hakan sai Abu Salhif yasa aka kwanto raguna
uku shanu uku da rakuma uku aka baiwa
dakarun suka tafi da su.
Bayan tafiyars ue Abu Salhif ya mikawa
Salhif hannunsa ya kama ya tashe shi tsaye
sannan ya dube shi ya ce, "Ka yi hakuri ya kai dana inda ban mareka ba bisa kuskuren da ka
aikata da tuni an kasheka a gaban idanuna kasani
cewa kai ne ka dai a gareni ni da mahaifiyarka don haka ba ma son mu rasaka ku ta shi mu kimtsa mu
bar garin nan domin abin da zai biyo baya ba mai kyau bane,."
Koda jin haka sai kowa ya ta shi aka hau
kimtswa nan da nan kowa aka gama shiri aka kama
hanya domin ci gaba da tafiya izuwa birnin na
gaba.inda za'a gudanar da harkokin fatauci.
Al'amarin Sarki Masurd ana kai masa
wadannan dabbobi sai yai shiri ya tafi izuwa dakin
bauta aka yanka dabbobin aka bayar a jininsu ga aljani Burrrata kamar yada aka saba
Faruwar hakan ke da wuya sai suka ji aljani Burrata ya kwarara uban ihu al'amarin da ya janyo
66
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
dakin bautar ya kama rugujewa, mutane dake ciki
suka dimauce suka rinka zubewa kasa sumammu,
Cikin firgici Sarki Masrud ya zube kasa
gaban gunki Burrata yana tuba.
Nan take gunki ya bude baki ya ce, "Maza ka
tura dakaru su je su kashe wadannan bakin fatake
domin jinin dabbobinsu bai magance mini
kishirwata ba face Karuwata kuma ka sani cewa
lallai sai an yi asarar dubban rayuwaka a cikin
Kasarka saboda fishina idan baka hanzartaa samomin
jinin da na saba sha ba ko wa sai ya dandana
kudarsa."
Koda jin wannan batu sai Sarki masrud ya
sake dimaucewa ya mike tsaye zumbur yana mai
kwalawa Sarkin yakinsa kira ya fice da gudu.
Kadan ke nan daga cikin littafin
JAHADI wanda zai zo nan bada jimawa ba.
Naku har kullum Abdul'aziz sani madakin gini
Dukkan mai son wannan labari da kuma
sabon labarina WASIKAR JINI SAI KU SAME SHI
A SABON BRANCH NA JAKRA CITY BOOK
SHOP DAKE KASUWAR SABON GARI
MARKET KUSA DA MADAKIN GINI BOOК
SHOP ДБЕМ
Sai mun ji daga gareku za a iya samunmu a
wannan numer kamar haka
67
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
08162707231-08069524699
TALLA! TALLA!! TALLA!!!
SAKON MUTUWA
A tsakar dajin mai yalwar korayen
ganyayyaki suke tsaye su biyu a tsakiyar
koraye ganyayyaki wasu jibgajibga aljanu
suna tsaye a gefensu kowane su rike yake
da jariri a hannunsa cikin tsananin farin
ciki da ganin juna.
Sarakuna ne masu ji da sarauta
suturun dake jikinsu kawai zai tabbatar
maka da haka kowane yana rike da jariri a
hannunsa
Sarki
2
Madhan shi ne Sarki kasar
Arfat, sai Sarki Azkam shi ne Sarkin kasar
Yuhud abokane ne su wadanda aka yi
68
L
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
shelar a duk duniya babu abokai masu
kaunar juna da amincin sama da su,
sannan babu wasu sarakai masu girman
masarauta da tumbatsar arziki face su,
kuma duk da sun kasance abokan gugayya
a bangaren sarauta dukiya gami da jin kai,
basu zame masu yiwa juna bakin ciki ba
haka ma shi yafi musu dadi a rayuwa
domin basa so ace a cikinsu wane yafi
wani, sun fi son su zama suna tafiya daidai da juna.
Abu guda ne ya banbanta wadannan
Sarakai Sarki Madhan yana mutukar son
ganin ya haifi 'ya mace ya yin shi kuma
Sarki Azkam kuma ba shi da burin da ya
wuce ace ya samu haihuwar da namiji,
amma sai aka samu akasi a shekarar da
matarsa zata haihu sai ta haifi 'ya mace shi
kuma Sarki madhan sai matarshi ta haifi
da namiji, wannan dalili ne yasa suka yi
wa juna alkawarin musayar yaran ta yanda
69
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
babu wanda ya san da haka, face aljanunsu
guda biyu kuma masa rike sirrikansu.
Ranar daya lokaci guda aka samu
wannan haihuwa a lokaci da matan suka
haihu sai Sarki Madhan da Sari Azkam
suka badawa matansu hodar banjo sukа
kama barci ta wannan yasa suka saka
aljanunsu suka kwashe su zuwa wannan
daji.
Koda Sarki madham da Sarki Azkam
suka dubi juna sai farin ciki ya baibaye su,
Sarki Madhan ya ce, "Ya kai Aminina hakika
godiya ba zata kare ba bisa yanda muke
mututta juna kuma muke daraja juna lallai
daukakarmu da boyayaryamu ba zata taba
rugujewa face an samu ranar da dayanmu zai
ji bazai iya rufe sirrin dayanmu ba, dan haka
ina mai horonka da ka yi yaki da zuciyarka
wajen gujewa wannan, sannan ina mai kara
jadda maka akan ka tsare wannan sirrin
kamar yanda zaka tsare rayuwaka dana ya
zamai naka 'yarka ta zama tawa, har abada
70
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
babu wata rana da zamu saka ido akan wani
daukaka da zata biyo baya a lokacin da yaran
nan suka girma, in har mun kawar da wannan
to babu shakka amincinmu zai cika gaba da
daurewa har abada."
Koda Azkam ya ji wannan ba tu sai ya
mika jaririyar dake hannunsa ga amininsa shi
ma amininsa ya mika masa jaririn. Sannan
Sarki Azkam ya ce, "Babu wata rana da
zuciya ta isa ta kawo mana sukar junamu
halas malak na bar maka wannan yarinya
kamar yanda halas malak ka barmin wannan
yaron, dan haka koda masifar wuta da ruwa
zasu cudu a cikin kasata ya zamana bani da
maganin wannan masifar face ďanka to ina
mai tabbata ba zan taba bukatar shi daga
gareka.
Da jin haka sai Sarki Madhan ya yi
murmushi ya rungume Sarki Azkam suna
masu murmushi. Da haka kowannensu ya
koma ya haye kan aljaninsa.
Suka Bace daga cikin dajin cikin
tsananin farin ciki da nishadi.
71
TURBAR GASKIYA --4 MADAKIN GINI
n
Tirka shi, kirarren labari ne da na
ratattako muku shi mai suna
SAKON MUTUWA yana nan tafe
daga ni Abdulsalam Adam shitu bature gadon
kaya
D
A
08162707231
Ni Abdulsalam ina kara yiwa makarantana
tuni da fitowar littafin DAKARU KASHI NA
HUDU SANNAN NA BIYAR SHI MA YA
FITO TARE DA WANNAN LABARI IN
BAKA SAMU GARAZAYA KA NEMI NAКА.
MUNA KARIN SANAR DA
SHAHARARREN MARUBUCIN YAKIN NAN
MARUBUCIN GIMBIYA ZAHRA DA
ADDININA WATO MUKTAR KWALISA YA
ZO MUKU DA SABON LITTAFI MAI SUNA
RANAR GAMO YANA NAN A
KASUWA
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da