kama shiri
tana mai caba ado da nufin taje unguwar 'yan
gudun hijira tana cikin yin adone mahaifiyarta ta
shigo dakin nata ta dubeta cikin mamaki tace
yake "yata ina zaki je da yammacinnan haka
alhalin magariba ta kusa?
Lushmaira ta juyo ta dube mahafiyattata
cikin murmushi tace "Ina sone naje naga ikon
Allah wato naga kyakkyawar fukar da tafi tawa
wacce a halin yanzu zancenta kawai akeyi a
birnin nan da kauyikan kasar nan,
Koda jin wannan batu sai Karimat
mahaifiyar Lushwaira tayi murmushi sannan tace
"yake 'yata kiyi sani cewa zuwanki wajen
wannan 'yar attajiri bash. da wani amfani domin
bazai haifar miki da komai ba face kishi, ban
son a samu wani sabani tsakaninki da wannan
bakuwar budurwasaboda musulunci yaharamta
gaba da hassada, kada kiyi kiyayya ko hassada
gareta saboda ta fiki kyau.
49 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
Lokacin da Lashmaira taji haka sai tayi
murmushi tace yake Ummina na rantse da
girman Allah babu wani abu a gabana face cika
umarnin mahaifina ba wani abu bane yasa nake
son naje naga wannan 'yar attajiri face gudun
kada zuwanta garinnan ya hanani cika wasiyar
mahaifina".
Da jin wannan sai karimat ta dubi
Lushmaira cikin alamun damuwa t ace "tayaya
Shadilar zata hanaki cika wasiyar mahaifinki?
Lushmaira tace "baza ki fahinta ba sai anan gaba
idan lokaci yayi amma dai yana da kyau yanzu
naje nayiwa al'amarin rigakafi, gama fadin
hakan ke dawuya sai Lusmaira ta fita daga dakin
da isa harabar gidan inda tai ski hadimen gidan
nasu ruke da doki yana jiranta, da zuwa sai ta
karbi dokin ta hau ta fice daga cikin gidan
Kai tsaye Lushmaira ta nufi gidan 'yan
gudun hijara, tana isa ta tambaya gidan da
Shadilat take take aka nuna mata. Lushmaira ta
kunna kai izuwa cikin gidan tana mai yin
sallama, wata kuyanga e eta amsa mata sallamar
wacce ta isketa zaune a falo tana hidima,
Lashmaira ta dubi kuyangar tace "je ki ki
gayawa uwar gidanki tayi bakuwa, ba tare da
50 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
garda ma komai ba kuyangar ta mike tsaye ta
shiga cikin turakar sannan ta sake fitowa tace
"shugabata t ace ki baiyana kanki, Lushmaira
tace "Kije ki gaya mata cewa gimbiya Lushmaira
ce 'yar marigayi Sarki yaki Hizanu, nan take
kuyangar ta koma ta isar da Sako da jin haka sai
Shadilat ta mike zumbur ta fito falo cikin farin
ciki, Koda suka yi arba da juna ita da da
Lushmaira sai kowannensu ya kurawa junansu
idanu ko kiftawa basa yi,tsawaan 'yan dakiku
suna tsaye kikam kamar gumaka sannan Shdilat
tayi murmushi ga Lushmaira tace "lale
marhabun da 'yar Namijin duniya dodon
macijiya Burukul karsum, ga kujera ki zauna mu
gaisa hakika yau ina da babbar bakuwa,
Lushmaira da Shadilat suka zauna a tare
akan kujeru da suke fuskantar juna a lokacin
Shadilat ta umarci kuyangarta da ta kawo musu
abin sha ta tafi cikin umarni, Shadilat ta dubi
Lsuhmara cikin nutsuwa tace "hakika kina kama
da mahaifnki a fuska, cikin alamun mamaki
Lushwmaira taçe "taya akai kika san mahaifina
hard a kamaninsa alhalin baki sanshi ba kuma
baki taba ganinsa ba, Asalima ni kaina da nake
'yarsa ban taba ganin sa batunda aranar da ka
51 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
haifeni ya mutu?
TURBAR GASKIYA
Shadilat ta gyara zama tana mai yin
murmushi tace "yake Lushmaira kiyi sani cewa a
rayuwata babu abinda yake burgeni sama da
jarumi don haka sa'adda na sami labarin
mahaifinki bisa jarumtakar da yayi sai na aiko
manzo musamman izuwa ga nan birnin yazo
yayi mini bincike akan tarihinnsa hard a
kamaninsa ma sai da aka sa wani masanin zanen
ya yazana min taswirarsa aka kawo min, domin
ki gasgata zancena yana da kyau kiga zahiri.
Nan take Shadilat ta mike tsaye ta shiga
cikin turakarta, jim kadan sai ta fito da rike da
wani allo a hannunta na Karfen zinare ta mikawa
Luswairat,
Koda Lushmaira ta dubi kan allon sai tayi
arba da hoton mahaifinta yana yaki da macijiyar
Burukul Karsum a alokacin day a sami nasarar
suka mata takobi acikin idonta, hakika
kamannin fuskarsa sak irin ta sarki ce banbamci
kawai shi yana da dogon saje wanda ya zagaye
fuskarsa, nan take Lushmaira ta kurawa fuskar
mahaifinta idanu aikuwa sai kwallah ta cika mata
idanu har hawaye ya zubo daga idanunta tad ago
kai ta dubi Shadilat ta ce Nawa zaki siyar min da
52 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
wannan hoton?
TURBAR GASKIYA
Koda jin haka sai Shadilat tayi sauri wuf
ta karbe hoton daga hannun Lushmaira t ace "ai
idan kika ga na siyar da wannan hoton sai idan
nima nayi irin jarumtakar da mahaifinki yayi na
soke daya idon na Macijiyar Burkul karsum an
zana taswirata kamar yanda aka zana wannan.
KOda jin haka sai Lushmaira ta tuntsire da
dariya, al'amarin da yai mutukar baiwa Shadilat
mamaki kenan ta dubeta tace menene dalilin yin
wannan dariya taki?
Lushmaira ta hade rai tace "gani nayi iska
na yawo da mai kayan kara domin kuwa kina
mafarki ne wanda bazai taba zama gaskiyaba,
yaya abin day a gagari duk jaruman mazajen
nahiyar nan gaba daya za kice ke zakiyishi? Ina
son ki farka daga dogon mafarkin da kike ki
fuskanci abin da zaiyiyo na zahiri yanzu ki gaya
mini dinari dubu nawa zaki siyar mini da
wannan hoton?
Koda jin wannan batu sai ran Shadilat ya
baci ta mike tsaye ta zaro takubi daga cikin
kufensu guda biyu dake rataye ajikin bangon da
cillawa Lushmaira guda daya ta café sannan ta
ajiyc wannan hoto a tsakayar falon ta dubi
53 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
Lushmaira ta ce "kudi baza su iya baki wannan
hotan ba amma idan zaki iya karbarshi ta kaifin
takobi ko karfin damtsenki ya zamana ki na
samu labara ke ma kin kuyi yaki a sirranci ba
tare da mutane sun sani ba kama yadda nima na
koya tun ina yarinya, Na sani cewa nayi miki fin
tin kau a fagen kyau amma, a fagen bangaren
jarumta ban sani ban a dade ina jiran wannan
rana, kuma gashi tazo idan har kin cika 'yar
marigayi Sarkin yaki Hizanu ki dauki wannan
hoton ki fita dashi daga cikin gidannan.
Koda jin wannan batu sai mamaki ya
kama Lushmaira bisa yadda akayi Shadilat tayi
wannan bincike akanta da mahaifnta haka kuma
sai zuciyarta ta kama tafarfasa bisa jin tace idan
ta cika 'yar marigayi ta dauki wannnan hoto da
karfin damtse, nan take Lusmairat ta daga
takobinta sama tana mai gyara tsayuwarta kawai
sai ta falfala da gudu izuwa inda Shadilat ta ajiye
wannan hotn ta sunkuya tana kai hannu domin ta
dauki hoton,
Koda ganin haka sai Shadilat tad aka tsalle
daga inda take ta doki kafadar Shadilat da
kafarta guda ta hantsaila can bayakafin tad au
hoton, cikin zafin nama Lushmaira ta mike tsaye
54
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
zumbur ta tareta suka ruguntsume da azababban
yaki tamkar kafiri da musulmi na kokarin
hallaka juna ya zamana cewa suna kaiwa junansu
sara da suka juriya da bajinta, nan fa suka tashi
hankalin barori da kuyangi dake cikin gidan,
Kuyangar ma da taho kawo musu kayan abincı
taga ana irn wannan tashin hankalin sai ta saki
faranti dake hannunta komai ya tsiyaye akasa ita
kowa ta sulale kasa sumamiya.
Said a Lahsmairat da Shamdilat suka shafc
kusan rabin sa 'a suna kaiwa juna sara da suka
amma dayanrsu bata sami nasarar koda lakutar
jikin dayaba, Al'amarin daya fusatasu kenan
sukayi watsi dad a takubbansu sukka ja da baya,
kowacce ta duhkule hannayenta kuma suka sake
rugowa da gudu da nufin su kacame da sabon
fadan hannu kwatsam ba zato ba tsammani sai
suka ga Yarima Zaiyan ya dako tsallac ya shiga
tsakaninsu bisa dole kowacce ta ja da baya suka
jifa da takobban dake hannayensu kuma suka
kama murmushi kamar ma babu abin ya faru,
Lusmaira ta dubi Yarima cikin alamun
mamaki t ace mene ya kawo nan wajen a
awannan lokacin, yarima ya daka mata tsawa
yace" aike ya kamata ki gaya min dalilin da
55 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
yasa kika zo nan kike son ki hallaka daya daga
cikin bakinmu mai daraja? Kafin Lushmaira t
ace wani abu sai idanun Yarima suka kai kan
wannan allon hoton na Sadauki Hizanu wanda
aka ajiyac a tsakiyar falon, ciikin tsananin
mamaki yarima ya kurawa hoton idanu ya
karaso wajen ya dauki hoton, koda yaci gaba da
kallon hoton sai nan take idanuwansa suka fara
zubar da hawaye, kawai sai ya dago kai ya kale
Shadilat yace "yaya akai kika samu wannan
hoton kanin mahaifina?
Shadilat ta num,fasa tace "nice nasa aka
zanashi saboda bani da burin da yafi na zamo
kamarshi akan wannan hoton muke wannan yaki
kuma nici na baiwa Lushmaira damman ta
yakeni domin na jarraba karfin jarrumtakata
akan tata saboda nasan cewa itama ta koyi yaki a
sirrance tun tana yarinya, Tabbas na na sha
gabanta afagen kyau amma afagen Jarumta
yanzu na tabbata cewa munyi kunnen doki bazan
taba wuce tab a face Sarki ya amsa zai min
alfarmar da na nema awajens.
Lokacin Shadilat tazo nan aazanceta sai
kan yarima ya daure ya cika da tsanannn
mamaki kawai sai ya dubi Shadilat yace "to ke
56 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
A
TURBAR GASKIYA
menene dalilin da yasa ba kyason Lushmaira tafi
ki Karfi ko jarumtaka?" Koda jinwannan
tambaya sai shadilat tayi ajiyar zuciya sannan
tace saboda na fuskanci cewar zata iya lalata
mini babban burina na duniya na son nd zama
jarumar da babu kamata, a tunda ita kuma
babban burinta shi ne ta auri jarumin da babu
kamarsa a jarumtaka idan har yazamaía cewa ba
n ice jarumar da tafi kowa jarumtaka ba lallai
wanda zata aurane, babu wanda zaifin kowa
jarumka a wannan zamani face wanda ya soke
daya idon na Macijiya Burkul Karsum da izinin
Allah nice zan samu wannan nasarar sa'adda
Sahadilar tazo nan a zancenta sai tabmikawa
Yarima hannunta tace bani hotona na jarumin
jarumai, batare da gardama ba ya mika mata ta
Raroa yarima ya dubi Lushmaira sannan ya dubi
Shadilat sai yayi murmushi ya ce "Hakika duk
ko biyun akwa wani abu a karkashin zuciyarku
da kukë boyewa amma koma menene in ya mina
yatube za muji wari, abin da nake so ku fahinta
shitheryanzu abin dake gabanımıu yakiner tunda
dał Sarki ya aika wad a Sarakunan can uku
takardar raddita yaki babu makwan sai any!
wannan yaki saboda haka ina mai shawartark
57ТNID\М ІMA2 SISA'JUCABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ku bi yun nan daku ajiye duk wani bure burenku
sai bayan wannan yaki yanu ke Shadilar nawa
zan biya na fita da wannan hoton na Sarkin yaki
na kaiwa Sarki shi domin ba kara min farin ciki
zai yi ba idan ya mallakeshi don na tabbatar da
cewa zai debe masa kewar marigayi, sa adda
Shadilat taji wannan sai tayi murmushi tace
"wannan hoton nawa ban a siyarwa bane da
kudi sai dai siyeshi da jarumtaka idan har kana
son na sai maka shi sai dai ka koyi mini yadda
akeyin hawa dogowar ganuwar nan wacce ke
tsakiyar gariinan har ka isa Karshenta aranar da
kai da mahaifnka kka hau kan ganuwar har kuka
rasa yadda zaki yi ku sauko kasa sai raga aka sa
muku ku ka fado kanta,
Loakcin da Shadilat tazo nan azancenta sai
yarima ya cika da tsananin mamakin adda akayi
tasan wannanal'amarin alhalin ba agabanta akayi
ba asalima awanan lokacin tana can uinguwar su
ta 'yan gudun hijira basu san abinda ke wakana
ba tunda acan karshen gari unguwar take,
Yarima Y ace Da ita "Zanyi tunani tukunna idan
naga ya dace na koya miki hawa kan ganuwar sai
na koya miki, Dajin haka sai Lushmaira tatari
numfashinta sa. Ta ce "aikuwa sai dai ka koya
58 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
mana tare"
TURBAR GASKIYA
Kafin yarima yabuſe bakinsa yayi
Magana sai ya ga wani badakare ya shigo cikin
gidan da sauri, da zuwansa sai ya risina ga
Yarima yace "ya shugabana Sarki yace kazoo
yanzn da sauri fada ana gabatar da taron
gaggawa, Koda jin haka sai yarima ya dubi
shadilat yace "kuyi hakuri sai kuma mun kara
samun lokaci sannan zamu warware wannan
matsala, nan take Yarima ya juya ya fice daga
cikin gidan da sauri yabi wannan badakare abaya
suka nufi fada,
Da isarsu fada suka iske sarki tare da
dukkanin 'yanmajalisa da kuma gaba dayan
dattijan garin wannan jama'a sai jikinsa ya bashi
cewa lallai yaki ya tsao domin duk sa'adda akayi
irin wannan taro a afada in ba batun wata anno
bad a ta shigo gari sai dai ko batun yaki, kai
tsaye yarima ya nufi inda Karagar sarki take ya
zauna daf da Sarki
A lokacinne Sarki ya dubi gaba dayan
Jama ar dake fadar y ace "yaku kjama'ata kuyi
sani cewa labara ya zo mana daga bakin 'yan
lekken asiri mu cewr kasar birinin Hizuba da
birnin, Dakful da Birnin, Karsum sun tara
59 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
dakarun yaki sama dana mutun Miliyan goma
acikin birnin Hizuba domin su zo su yakemu tun
kafin amsar wasikar da suka aiko mana ta
samesu, wannan yana nun da cewr daa so suke
su baje kasarmu su kawar da addininmu a
awannan nahiya gaba daya, lallai ba zamu zauna
muna jiran so iso ba har nan bas u cimu da yaki,
bazamu ji tsaronsu ba koda yawansu ya
kaiyawan gaba dayan mutanen duniyar nan
saboda munsan cewa muna kan TURBAR
GASKIYA su kuwa suna kan turbar karya
Koda Sarki yazo nan a zancensa sai fadar
baki daya ta kauri da kabbara sannan Sarki yaci
gaba da bayaninyace "kun sani cewa tunda na
hau kan wannan karaga ta mulki ban taba yin
yaki ba azamanina sai yanzu, rabon da ayi yaki
awannan Kasa tun mulkin mahaifnna sa adda
Dan uwana ya rike sarautar sarkin yakin a
garinnan tun daga wannan alokaci kawo I yanzu
amu da Sarkin yaki a garinnan saboda haka ni
yanzu na nada yarima Zaiyan akan matsayin
sabodan sarki yaki wanda zai iya
jagoranciwannan yaki da zamuyiu saboda na
gamsu da jarumtakarsa juriyarsa da hikimarsa da
Allah ya bashi, uwa uba kuma ya kasance mutun
60 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
mai mutukar Sa'a bisa duk abin da yasa
aagabansa.
Lokacin da sarki yazo nan ab batunsa sai
fadar tayi tsit 'yan Majalisar suka kama kus, kus
kowa na fadin albarkacun bakinsa alamar cewar
da yawansu suna da shakka akan jagoranci da
yarima zaiyi na wannan yaki, Koda Sarki ya
fuskanci abinda ke faruwa sai yai gyaran murya
kowa ya nutsu sannan yace duk wanda yake da
korafi akan wannan bayini nawa. bisa hukuncin
da na yanke ya fito yayi hawabi tunda amfamin
taruwarmu anan kenan domin mu zartar da
hukunci da muke ganin cewa shi ne zai fishemu.
Koda jin wannan batu sai waziri ya mike
tsaye ya fuskanci jama'a y ace ni korafina guda
dayane a tunanina bai kamata ace mutumin da
bai taßa fi a yaki ba kuma bai taba fita filin daga
ba ac yazamana cewa shi zai jagoranci mayaka
sama da miliyan daya saboda bai san yadda ake
yaki ba baisan irin dabarun da ake yi ba donin a
yaudari abokan gaba asami nasara yaki akansu.
Koda jin wannan batu sai Sarki yayi
murmushi y ace ai ba yarima kade ne zai
jagoranci wannan mayaka ba domin hard a ni za
ayi wannan yaki duk wani abu day a shige masa
61 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
ni zai taimaka
TURBAR GASKIYA
duhu masa, Koda jin haka sai
hankalin kowa ya tashi ya dugunzuma, waziri ya
dubi Sarki cikin alamun tsananin damuwa yace"
ya shugabana abune mai tsananin hadari ka shiga
wannan yakin domin jiya bay au b ace tabbas
yanzu girma ya fara kamaka jaurmtakar da kayi
a ada yanzu bazaka iya taba da zarar abokan
gaba sun kyaila ido sun ganka acikin mayaka
kokarin za su yi suyi maka rubdugu har sai
sunga cewa sun gama da kai sannan hankalinsu
zai kwantakasani cewa kaine mayakin da babu
kamarsa awannan kasa tamu gaba daya idan
gaba daya dakarun mu suka ga ka fadi zasu iya
samun karayar zuciya su kasa ci gaba da wannan
yakki yadda ya kamata idan kuwa haka ta raru
cikin kankanin lokaci za amurkushemu tunda
dama bamu da yawa.
Sa adda sarki yaji wannan korafi na na
Waziri sai ya sake yin murmushi yace "yakai
Waziri kayi sani cewa kafin na yanke hukunci
fita wannan yaki said a nayi la'akari da duk
wadannan matsalolikuma nayi tunanin mafita
akan su saboda haka ina mai tabbatar muku da
cewa nasan abin da zanyi domin na kare kaina
daga wadannan matsaloli a bin da nake bukata
62 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
daga gareku kawai shi ne ku tayi ni da addu'a.
idan kuma akwa mai sauran korafi ya tashi yayi
Magana.
Fadar ta sake yin tsit har izuwa tsawan
'yan dakiku baa sake samun wanda ya sake yin
wani korafin ba, Asannane Sarki ya dubi Yarima
yace "kaje ka fara shirya dakarunmu gobe da
Asuba bayan munyi Sallah zamu fita daga cikin
birninmu mujes mu tari abokan gaba lallai
Ashirya guziri duk da abin dake bukata ayau
kafin ya raba. slinsd inidi bawuR"
Yarima lya rissina yace an gama ya
shugabana, Nan take Yarima ya mike tsaye ya
fice daga cikin fadar ya tafi izuwa can fadar inda
ya tura akirawo masa gaba dayan dakarunsa da
zasu fita wannan yaki, mud onaya появява
nuniiNan da nan kuwa labara ya bazu ko ina
acikin birnin da kauyeka, Nanfa jama'a suka
dukufa wwajen yin addu'a suna ta rokon Allah
akan ya bayar da nasara akan wannan yaki da za
fitanie s inesb sова и по вast swao idasi
Al'amarin Gimbiyar Lushmairal kuwa
lokacin da taji za afita wannan yaki amma banda
mata face matan da mazajensu zasu fita domin
tu taimakamusu wajen dafa musu abinci da kula
63ИТСМЕИAR SISA'JUQBABDUL'AZIZ SANI M/GINI
な
TURBAR GASKIYA
da lafiyarsu alokacin da suka sami raunika sai
hankalinta ya dugunzuma cewar komai rintsi da
tsanani sai taji wannnan yaki domin ta bayar da
gudummawarta ga addainin Allah kuma ta
jarraba jarumtakarta da horon da ta samu na
yaki nan fat a kasa zaune ta kasa tsaye ta dinga
kai kawo tana tunanin mafita, said a ta shafe
lokači mai tsawo sannan dabara ta fado mata
Nan take Lashmaira ta shirya ta tafi izuwa gidan
shugaban likitocin birnin wanda ake kira da
Zauwad ibini hanifa.
- Da isar gimbiya Lushmaira gidan likitan
sai ta iskeshi tare da likitoci da yawa yaransa
wadanda yake kintsasu domin su bi rundunar
mayaka lokacin da gimbiya tai so tana sanye ta
bakaken kayane kuma ta rufe fuskarta idanunta
kadai ake gani da yake tare da wani hadiminta
tazo wanda yake rike da dokinta sai ta umarci
hadiman nata akan yaje ya radawa Zuwwad
zuwanta batare da kowa yaji ba kuma ya sanar
dashi cewa tana son su gana dashi a sirrance, nan
take kuwa Bawan na yaje ya cika umarnin.
Lokacin da likita Zuwad yaji cewar
Lashmaira tazo har har tsoro ya darsu acikin
zuciyarsa amma sai ya tura wani
64 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
hadimansayayiwa gimbiya jagora har izuwa
cikin turakarsa.
Da isar gimbiya cikin Turakar Zuwad sai
tayi arba da abin da yasa zuciyarta ta harba da
sauri da kuma buga.
Ana zan dakata alittafina na daya sai mu shiga
cikin littafi na biu don son ci ganan wannan
labarin da kuma: yanda zata kasance mai
Lushmara ta gani haka har yasa gabanta faduwa
shin wace bukata tazo da ita gurin likita zauwad
ina labarin Shadilar shin zata iya cika burinta na
soki idanuwan Macijiya burukulb karsamo duk
wannan amsashi suna cikin lit na biyu wanda
a tare suka fito da na daya u2 onss UHS
Daga marubucinku madakin ginos
Hira tsakanin madakin gini da A a bature akan
littafin Hikayoyina arabuan t whajara.
aAbudul aziz madakin gime yane mai
yabawa matashin maruci Abuduj salam adam
shitu bature da cewar "agaskiya nayi mutukar
farin ciki alokacin da na kasance mai karanta
wannan littafin mai suna hikayiyin abu shajjara
musammam hikayar kanina kuma dan uwa na
Abudulsalam adamu shitu ya fara gabatarwa.
Ban yi tsammani haka daga gareshi lallai na
65 иIXARABDUL'AZIZ SANI M/GINI
jinjina masa mutukar jinjinawa,
TURBAR GASKIYA
shi wannan matashin maruci shi ne
wanda ya kirkiri wannan labara kuma yazo min
da batu alokacin azumi, nayi farin cki sosai gami
da wannnatunanin da yayi kuma na yabawa
kwanyarsa ta dalilin kawo min wannan bayanin
cewar sa "Ina ganin ogana kamar yadda yake
cewa dani ya kamata ace mun' tsaya mun fitar da
littafi guri guda ma'ana tare dakai" lokacin da
naji haka sai nayi mamakin batunsa atunanina ya
za ayi ace muyi lattafi tare kuma guri guda.
Bature ya ce da ni "ba ina nutin yazamana
munyi labari daya tare da kai ba a'a ina nufin
zamu zamo masu yin hikayoyin daya da daya
acikin kowane littafi kuma zai kasance lattafin
ya dinga fita aduk kan wata biyu biyu. Anan na
fahinceshi na kuma sanar dashi cewa wannan ba
matsala bace dukkaninmu sai mu dau damara
yin dan muga inda zamu kama bakin zaren
ayinni biyu kacal na kamala labarin kuma nayi
mamakin yanda shima y agama nashi labarin
ayini guda daga nan na tabbata lallaai bature ya
dama danba nan take na tambayeshi wane suna
za asawa littafin, batare da bata lokaci ba ya
sanar dani cewar HIKAYOYIN ABU
66 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
SHAJJARA. Koda muka rabu dashi na jima ina
nazarinsa da akan wannan labari wanda duk
jimawata a harka littafi ban tabayi yin wânnan
tuanniba na hada kaina da wani marubucin da
mukayi zamani dasu kamarsu marigayi yaron
malan da Shehu usman mohd dan haka sai na
fara duban hikayarsa day a kawomin,
Akwai rubuce rubuce da yawa agabana na
so ne na dan duba labarinsa amma bisa
mamakina ban tsahirta ba sai da yazamana ina ta
faman bude faijika ina ganin faran takarda
agaskiya na yaba masa mutuka dan haka ne yasa
na barshi ya karasa wannan hikaya tashi har
zuwa littafi na hudu sai ku saurareni da karashen
tawa hikayar gami da sabowar d azan dasa a
sabon labarina mai taken ARTABUN
GUMURZU.
Kadan Daga
FARMAKIN ABOKAN GAMA
Ya ku iyayena ni na tafi kuma bazan taba
dawowa ba tunda na yarda da mutuwa Lallaai
nayi da na sańi zuwane Birnin Basara kuma nayi
danasani abinda na aikata badan tsoron yawan
laifina ba said an kawai na so nayi tsawan rai
67 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
don in dauki fansar ran kakata da aka rataya tun
a baya bisa laaifin kisan mahaifiyar Sarkin dan
uwarka kuma makiyaki agare ka a yauzu tunda
ayau nima na gurfana agaban inda suke rataye
wanda suke aikaya laife a garesu sun rataye ni
duk da cewar na kasance da ga dan uwansa
Lallai mahaifin ka dauki dan uwanka
abokin gabarka kuma kada ka taba yafe masa
laifinsa ka dauki fansa akan daukacin
al'ummarsa kada ka raga musu wannna shi
kadaine zai nuna kai masoyinane acikin kuma
shine zai nunawa masoyanka cewar
mahaifiyarka ta haifeka a matsayin da mai
Kaunarta
Koda Sarki yazo nan a karatun sai ya sake
fashewa da kuka mai tayar da hanakalin mai
saurare ya kuma kwarara ihu mara dadin ji ya сe
cikin kakkausar murya
"Dana Kuhiaf zan dau fansa ko taw ace
hanya zan dau fansar ranka akan Ulaisat Yar
sarki Abulbashara,
Sannan zan dau fansa bakan ta min zuciya
da akayi akan duk wani raid a ke wanzuwa А
Birnin BASARA
68
Zan kuma dau fansar ran mahaifiyata a
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
akan Dan'una Sarki Abulbashara.
Koda yazo nan kashedinsa sai ya. zare
takobi daga jikin Zairul ya nufi Dakaru gami da
kuyangun da Sarki yayi masa kyauta dasu
Kuyangu da Bayi ya fara Sarewa kai
Gaba daya hankalin jama'ar dake gurin
hankalinsu ya tashi.
WANNAN KENAN DAGA
LITTAFIN MATSHIN MARABUCINKU
AA BATUREGADON KAYA
YANA NAN TAFE NAN BDA
JIMAWA BA 08162707231,
07041591141,08124173211
Kadan Daga
GASAR GWARZON KARNI
K
urdawa yake cikin kataren gidan sarauta
sarautar hannunsa rike da muggan makai
mai masu barazana ga rayuwar bil'dama,
Duk yawan dakarun da aka zuba domin
yimasa Katanga ga shiga cikin gidan, sunata
kewaye kewaye yayin dashi kuma yake
sadadawa a hankali cikin hikima irin tasa ta
babban jarumi kuma gwarzon shekara a wanna
lokaci duk badakaren da yayi rashin nasarar yin
69 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ido hudo dashi to wannan ya zama tarihi karshe
na rayuwarsa da haka har ya isa cikin turakar
mahaifiyarsa,
Lokacin daya isa ya sameta akwance
amma bisa mamakinsa idanuwanta abude tarwai
kuma kamar bata tare da wata cuta,
Cikin ladabi ya ajiye makamansa yayi
tattaki zuwa gareta a yayin da ita kanta ta zuba
masa ido kuma batare da mamakin zuwan nasa
ba awanan lokaci,
a
Koda karasuwarta zuwa kasaitaccan
gadon sai ya duka ya gaidata, cikin irin nasu
salon, kana ya dora da cewa "ya ummi nay
naga kin kasance cikin halin rashin nuna
mamakin ganina awanna lokaci duk da kuwa
cewa rabon nasa idanuwa akan nake na dan
tsawan lokaci,
Koda taji shi wannan kalami sai yaga ta
fashe da kuka al'amarin da yayi mutukar daure
masa kai kenan ya dubeta cikin rudu" ya
ummina ina dalilin wannan kuka nake nayi
tsammanin cewar zakiyi farin ciki da ganina
acikin wannan dare har hakan yazamo waraka
cutar dake addabar zuciyarki, hi kuma na samu
kwanciyar hankalina a gujewata ta barautar da
70 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
akemin, kuma da son ganin matata da fana,
Sa'adda yazo nan ažancensa sai mahaifiyarsa
taja dogowar majina ta dubehi a tausayi tace
"Yakai dana hakika ka fada tarkon dan
uwanka Ruhas domin suna sane da cewar zaka
zo wannan birnin kota nalin kaka dalilin da yasa
akayi shilar rashin lafivata kenan alhalin ni babu
abinda ya sameni lallaı suna sane da shigowarka
kuma bamu makawa sai sun samu nasara na
kamaka kamar yanda suka kudurta da.domin da
kansa sarki ya bada ammana akamaka a kashe
saboda suna da labarin kana nan kana hada
RUNDUNAR DAUAR FANSA, wanan daliline
yasa ni zubar wanan hawaye
Sa'adda Gwarzo jarumi Jamal yaji wanna
batu sai ya dubi mahaifiyarsa batare da wani
tashin hankali ya ce
Kada ki damu ya Ummina ai tuni sun yi
sakaci dan Zaki ya girma babu wata guguwar
bala'in dazan yi shakkar tunkara a wanna lokaci
dan haka yanda suka shirya nima na shirya A dai
dai wannan lokaci dakaru gidan baki daya sun
cika bakin kofar turakar mahaifiyarsa da kansa
yaraima Ruhas ya shigo dakin cikin fusata Jamal
bai dubeshi ba sai day agama sallama da
71 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
mahaifiyarsa ta cewar ta kwantar da hankalinta
kamar ya tsira ya gamane.
TURKASHI WAYE BAI KARANTABA
WANNAN KASAIТАТТАCCAN
LABARINE DAGA ABDULSALAMA ADАM
SHITU BATURE GADON KAYA LALLAI KA
NEMA DAN JIN WANNAN LABARI YANA
NAN A KASUWA 1&2 NE.
72 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TurbarGaskiya
2
diaM DUL'AZIZ SANI
KIN GINI
TURBAR GASKIYA -2
a wani abu bane yasa zuciyarta ta buga B
face Shadilat a zaune kan kujera ta
harde kafafu tanna shan ruwan inibi
acikin kofin zinare kuma fuskarta cike da
annuri, Koda Lushmaira taga Shadilat sai ta
juya da baya da nufin ta koma sai kawai taji
Shadilat ta kirawo sunanta tana mai cewa
"dawo 'yar uwata mu zauna tare aabin day a
kaolo nan shi ya kawoni.
Koda jin wannan batu sai Luhmaira ta
tsaya cak sannan ta juyo a hankali cikin
mutukar sanyin jiki da mamaki taje ta zauna
akan kujerar dake fuskantar ta Shadilat ta cire
mayafin day a rufe fuskarta suka dubi juna
sosai tace "yaya akayi kika shai dani al halin
fuskata arufe take? Da jin wannan tambaya sal
Shadilat tayi murmushi tace "ai ko daga barci
na farka bazan kasa tantance idanun kiba
domin kece mutun na farko wanda na taba jin
shakkarsa arayuwata.
Kafin Lushmaira ta bude baki tace wani
Abdul'Aziz Sani M/Gini
a
t
TURBAR GASKIYA -2
abu sai Shadilat ta zuba mata ruwan inibi
acikin wanikofin ta miko mata cikin alamun
dari dari, Lushmaira ta karbi kofin ta