kurbi dan
kadan sannan ta dubi Shadilat tace "saboda me
kike shakkata kuma saboda me kike son kije
wannan yaki"?
ebo Sa adda Shadilat taji wannan tambaya
sai dariya ta subuce mata tace "ba komai
yasanake shakkarki ba face ina ganin cewa ke
kadaicee zaki iya hanani cika burina kamar
yadda na gaya miki da farko dalilina da yasa
nakee sona naje wannan yakin kuwa za ayi
yakine irin wanda ba a taba yin kamarsa ba a
nahiyar nan gaba daya tarihin wannan yaki
bazai taba gushewa ba domin za ayi asarar
miliyoyin rayuwaka fiye da has ashen mai
hasashee, aawannan yakine manyan jarumai
zasu yi jarumtakar da sunayensu zasu daukaka
asallama musu aako ina acikin duniya, kuma
arubutu sa acikin kundin tarihin kowace Kasa
ta düniya lallai ina son sunanan ya zamu daga
Abdul'Ażiz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
cikin sunayin wadannan jarumai. Koda shadilat
ta zo nan azancenta sai Lushmaira ta tuntsire
da dariya tace "ai wannan burin nake daidai
yake da tatsuniyar yara. Gama fadin hakan ked
a wuya sai ga likita Zauwad ya shigo cikin
turakar.
Likita Zuwada ya kasance dattaijo wanda
she karunsa a akalla zau kai saba in da 'ya'ya
ya kasance dogon mutun mai matsakaicin
kaurin jiki, yana da dogon faring emu kuma
mutun ne mai gwagwar mayar duniya.
LIkita Zauwad ya zauna agefe daya bisa
kan wata kujera dabam sannan ya dubi
Lashmaira cikin girmamawa yace "ranki ya
dade zamu iya tattaunawa agaban wannan
bakuwa ko kuwa ta bamu guri?"
Lushmaira tayi murmushi t ace "ai irin
bukatar da tazo maka da ita nima na kawo.
Koda jin wannan sai hankalin likita ya
dugunzuma ainun ya dubeta su duk su biyun
cikin alamun tsoro da damuwa y ace "waishin
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -
me kuke so ku jifani acikine? Kuna so na zama
makaryacii ne ko kuma na zama mai karya
dokar Sarkin? Idan har na na batar da
kamininku kuka shiga cikin yarana aka je
wannan yaki a tare daku wani abu ya tba
lafiyarku sarki bazai yafe mini ba kuma
girmana da mutuncina zai zube a idon kowa,
wacce hujja zakuuuuuu gaya mini wadda zata
kawar min da wannan fargaba har na amince
da bukatarku?
Koda jin wannan tambaya sai Lushmaira
da Shadilat sukayi shiru suka dubi juna sannan
Lushmaira ta numfasa tace "maganar gaskiya
bamu da wata hujja ta zahiri wanda zamu iya
gabatar muku da ita amma ina mai tabbatar
maka da cewa na rantse da girman Allah babu
abun na sharri acikin zukatanmu sai alkairi
bisa zuwa wajen wannan yakin zamu bayar da
gaganumar gudun mawa wacce zata baiwa
kowa mamaki, ka tuna da cewa ni 'yar
marigayi Sarkin yaki ce na karanta tarihin duk
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
yake yaken dad a mahaifina yayi a cikin
kundinsa don haka na sami ilimi mai yawa
acikin wannan littafin, lallaii zan bayar da
shawara wadanda. Ita kuwa Shadilat 'yar
attajiri ce da babu kamarsa acikin wannan
nahiya, ita kanta mashahuriyar attajira ce don
haka zata taimakamana da guziri mai yawa
kuma koda muna cikin yakine guzurin ya
yanke zata iya tawa ko ina daga cikin
Kasashen dake kusa a kao mana, ina mai
alkawari zamuyi kokarin ganin mun kare
mutunci da kimarka acikin wannan al'amarin.
Sa adda wannan sai jikin likita Zuwad yayi
sanyi yayi shir ya sunkuyar da kansa Rasa
yana tunanin tsawan "yan dakiku baice komai
ba al'amarin day a dugunzuma hankalin
shadilat Da Lushmaira kenan suka fara
atunanin ko Zauwad ba zai amince da bukatar
suba daga can sai Zauwad ya daga kai ya dubi
Shadilat yace
"Mutun nawa jama'arki wadanda
8
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
kikeson su je acikin jama'ata suyi wannan
tafiya? Shadilat tace " ai akalla sun kais u dari
uku, cikin alamun tsoro Zauawad yace "mutun
dari biyu ne kacal sarki ya bani izinin tafiya
dasu kinga kenan idan kika kawo nake jama'ar
mun kusan linkuwa kenan bana zaton Sarki zai
aminta da hakan" Shadilat tayi murmushi tace
zai amince idan har ka sanr dashi cewa wannan
yakin saboda na musammane tunda za atafi da
mayaka sama da miliyan daya dan haka likitoci
dari biyu sun yi kadan.
Zuwad ya gyada kai sannan ya dubi
Lushmaira yace ana dawo gareki shin
mahaifiyarki tasan zakiyi wanan tafiya? Idan
bar bata sani ba baza iya tafiya tare da keba
domin zata sanar da Sarki cewa bata ganki ba
kuma kin sani cewa da kansa zai duba accikin
tawagar kinga kenan duk sharinmu ya wargaje
kenanjin kunyane zai biyo baya Lushmaira ta
numfasa ta ce "aimahafiyata tasan dukkan
shirina kuma ta amince da nayi wannan tafiya
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
saboda wani babban sirri wanda bazan iya
sanar daku shi sannan ya dubi Shadilat da
Lushmaira y ace "kuje ku kamala duk shirye
shieyenku na tafiya sannan ku dawo nan
gidana bayan Sallar Isha'i Anan zako kwana
tare da jama'ata tunda asuba zamu dunguma
zuwa kofar gidan Sarki don na tabbata akwai
wani labari da Sarki zai bayar kafin wayewar
gari wanda tun mahaifnsa yana raye idan yana
so yasa ka zuciyoyin mayakansa su karfafa
yana sanar da so wani labara day a taba faruwa
na manyan Mazaje dan haka kada mu bari ko
daya wannan labara ya shge mu dan yana da
mutukar anfani ga dukkan wanda zaije wannan
yaki.
Koda jin wannan batu sai Shadilat da
Lushmaira suka kamu da tsananin farin ciki
nan take suka yiwa Likita Zauwad godiya
sannan suka mike tsaye a tare suka fice daga
cikin turakar suka fito kafar gida ajere suna
hira cikin nishadi tamkar sun kasance 'yan uwa
10
Abdul'Aziz Sani M/Ginl
TURBAR GASKIYA -2
juna ko kuma minai.
Wannan shine ya faru a birnin baitul
harwal baya ga wasikar yaki ta riski sarki
Abul zaiyan.
A can kuma birnin Hizuba, kuwa Sarki
madhan, Sarki Tarmas, da Sarki Husaka na
tsaitsaye afilin kofar birnin suna kallon
miliyoyin dakarun yakinsu dakae tsaitsaye
asahu saho ruke da makamai jagoransu na basu
horo sai aka hango wani ya matso kusa sai aka
ga ashe wannan manzo en da aka aika shi
birnin Baitul Haural nan take Sarki madkan ya
kama murmushi yana mai duban Şarki Tarmas
da Sarki Husaka yace "Ai da ganin yadda
wannan manzo ya dade bai dawo ba sai yau
nasan cewa Sarki Abu zaiyan yaji tsoro, tabbas
ba zai yarda yayi yaki da mu ba tun yana da
hankali, tunani da hangen nesa ni nasan cewa
dole ya bamu mutanenmu da dukiyaoyinsu.
11
Koda jin haka sai Sarki Tarmas ta
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Husaka suka bushed a dariyar farin ciki Sarki
Husaka y ace "to aima ko ba a gwadaba
linzami yafi karfin bakin Kaza ka dubi yawan
akarun nan namu ka gani ta yaya za a
kwatantasu da Dakarun birnin Baitul haural
wadanda 'yan liken asirinmu suka ce basu fi su
miliyan daya ba da doriya shi kuma sarki
Tarmas sai y ace to ai koda ma yawan dakarun
yakai namu.dolene mu sami nasara akansu
tunda su rabonsu da yaki ankai shekaru ashirin
baya. Duk manya zakakarun mayakansu
wadanda suka san kan yaki sun mutu wasu
kuma sun tsufa tukuf yaddama ba zasu iya fita
filin daga ba.
Koda jin wannan batu sai Sarki Madha
ya girgiza kai yace "Ai ba anan take ba
mahafina ya gaya mini cewar mutane birnin
Baitul Harwal suna da zuciyar zaki wato basa
gudu kuma basa ja da baya sannan sunyi
imanin da ubangijinsu bisa cewar indai suna
ambatonsa bakinsu sai sun sami nasara abinda
12
Abdul'Aziz Sanl M/Ginl
TURBAR GASKIYA -2
suka sa agaba su dolene muyi amfani da
dabarun yaki na musamman wajen ganin mun
sami nasara akansu kamar irin su kai hari na
mamayar bazato a. lokacin da basu taba
tsammaniba amma idan mukayi la'akari da
tsananin yawanmu akansu mukace ayi gaba da
gaba zasu iya bamu mamaki".
Koda jin haka sai Sarki Tamas da Sarki
Husaka suka dubi junansu cikin alamun
mamaki sannan suka dubi Sarki Madhan cikin
alamun rashin gamsuwa, kafin daya daga
cikinsu yace wani abu sai ga wannan manzon
ya iso daf da Sarki.
Da zuwansa sai ya sauko daga kan
dokinsa ya zube gaban Sarki ya kwashi
gaisuwa sannan ya mika masa wasika.
Nan take Magatakarda ya karbi wasikar
ya budeta ya shiga karantawa a fili kamar
haka-:
13
Sako daga sarki Abu zaiyan na birnin
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
baitul Haural zuwa ga Sarakuna uku ma'abota
jahilci da toshewar basira, koda magatakarda
yazo nan akaratunsa sai Sarki madhan ya daka
masa tsawa.....
Magatakarda ya tsuke bakinsa ya kama
karkarwa saboda tsoro Sarki Madhan Sarki
Tarmas, da Sarki Husaka kuwa suka jikinsu ya
kama tsuma saboda fishi zuciyoyinsu kuwa
suka kama tafarfasa kamar zasu kone jin
aibatawar da Sarki Abu zaiyan yayi musu kai
hatta miliyoyin dakarun da suke gabansu said a
suka nutsu suka shiga taitayinsu akayi tsit har
izuwa tsawon 'yan dakiku sannan Sarki
madhan ya baiwa Magatakardar umarnin yaci
gaba da karanta wasikar hannun magatakarda
yana karkarwa bakinsa na tuntuben harshe
yaci gaba da karanta wasikar yace-;
Yaku wadannan Kazaman Sarakuna
kuyi sani cewaa komai zai faru bazan baku
jama arku bad a dukiyarksu saboda sun zama
14 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Dakarun dake gabansa yace" Na rantse da
darajar iyayena da kakanina daga cikin ku duk
wanda ya saro kan Sarki Abu Zaiyaan ya kawo
min sai na raba dukiyata gida biyu na bashi
rabi.
Koda jin haka sai gaba daya dakarun
yakin suka kama ihu gami da shewa, kowa ya
fara tunanin sallama ransa da lafiyarsa domin
samun wanan gagarumin matsayin, nan take
akakirawo Sarakan yakin kasashen uku suka
gaba ta wajen su Sarki Madhan aka basu
Umarni suje su fara suje su fara shrye shiryen
tafiya domin a adurfafi kasar Baitul Harwal,
Nan take kuwa Sarakan yakin suka bi umarnin
sukab farab shiryajama'arsu.
Idan mutun yaga kayan yakin da aka
tanada da kuma dinbin abincin d aka taho dashi
sai yayi zaton cewar wannan duniya tamu da
wata duniyar daban za afafatayaki. Haka dai
dawakairakuma, da alfadarai, sula dauki
hanya sahu sahu zuga-zuga suka bar birnin
16
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Hizuba, Tawagar su Saarki Madhan ce
atsakiya, Dakarun tsaro sun kewayesu ta ko ina
ko tsuntsu bai isa ya gifta ta samansu ba face
ma giwa,
Komai dakewar zuciyar mutun da
jarumtakarsa idan yaga wannan runduna
dolene ya firgita domin yasan cewa duk
abinda ta tunkara sai buzunsa, haka dai wannan
runduna taci gaba da tafiya hart a kustsa cikin
daji ta nausa sosai aka daina hangota daga
birnin Hizuba.
A can birnin Baitul harwal kuwa kamar
yadda likita Zauwad ya tsara haka al'amarin
suka kasance wato gimbiya Lushmaira da
Shadilat 'yar babban attajiri agidansa suka
kwana kuma shadilat tazo da ma'aikatant
mazaje guda dari uku dauke da guzuri n abinci
mai yawan gaske ninkin wanda zasu iya
amfanin dashi sau goma sama da kwanaki
ashirn, shi kansa likita yaga yawan wannan
17 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
abinci guziri sai ya dubi Shadilat cikin
tsananin mamaki ya ce "mai za ayi da wannan
guzirin abinci mai yawa haka?ba kya tunanin
cewa yayi yawa kuma ba kananan kudade zaki
kasheba wajen tafiya da wannan kaya.
Shadilat tayi murmushi tace "indai akan
daukaka lamarun Allah ne banki na salwantar
da duk abinda na tara", koda jin haka sai
Zauwad yayi murmushi yace "Allah ya saka
miki da mafi tsoka. Batare dad a 6ata lokaciba
Zauwad ya nunawa kowa dakin da zai kwanta
gimbiya Lushmairat da Shadilat kuwa sai ya
kaisu dakin guda,
Dakine yalwatacce dauke da shimfido
guda biyu irin na attajirai Atsakiyar dakin daga
sama jikin rufin an sakale wani dankaramin
Keji mai dauke da wani dan Karamin
kyakkyawan tsuntsu abin sha'awa.
Shadilat da LUshmara suka je suka
kwanta akan shimfidon biyun suna masu
fuskantar juna. Adai dai lokacin wata kuyangar
18
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Likita Zauwad ta shigo cikin dakin da sallama
tana dauke da faranti abinci da tambalun ruwan
inibi da na ruwa, Lushmaira ta amsa mata
sallamar ita kowa Kuyangar nan sai ta ajiye
faranti atsakiyarsu ta fice,
Fitar Kuyangar ked a wuya sai Shadilat
da Lushmaira suka mike zaune a tare kamar
hadin baki kowacce ta kai hannu domin ta
bude kwanon abinci sai gashi kowacce ta ruke
murfin kwon, Al'amarin day a basu dariya
kenan suka kyakyta a atre sannan Shadilat t ace
ashe dai ita yunwa bata da hankali kuma ba ayi
matajuriya sai hakuri,
Shammilat tayi murmushi t ace abin da
kika fada gaskiya ne amma amma dai mu
mutane yanzu dai muna da mutukar lalaci
kuma muna da rauni zuciya shi yasa yunwar
ma take galabartar damu amma bayin Allah na
gari wadanda suka gabacemu kwana suke su
yini da yunwar amma saboda ko yaushe tsoron
Allah da gudun duniya acikin zuciyoyinsu
19 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
yunwa batayi musu illar komai.
• Lushmaira ta numfasa tace "hakane 'yar
uwata amma mu dinma tamu da sauki nan
gaba wadansu daruruwan shekaru da za su zo
bamu san yadda zuciyoyin musulmai zasu
kasance ba domin kawa dukiya da mulki zasu
iya sawa su bar kan TURBAR GASKIYA sai
dai kawai muyi musu fatan gafarar Allah.
Shadilat tace "ameb sannan suka fara
cin abinci acikin nutsuwa da kwanciyar hankali
kai kace babu wata matsala atsakaninsu.
Bayan sun kare cin abinci suka bude
babin hira Shadilat ta dubi Lushmaira tace
"yake 'yar uwata naji kince ke baki da burin
day a wuce ki auri jarumin da babu kamarsa a
wannan nahiya shin zaki iya gaya min dalilin
da yasa kika sa wannan babban buri aranki
mai wuyar kasancewa? Na yarda cewa jarumi
da yafi kowa nuna jarumtaka a wannan yakin
da zamu muje zaiyi suna duniya amma hakan
bata nufin cewa shi ne yafi kowa jarumtaka ba
20
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
tunda baiyi irin jarumtakar da mahaifinki yayi
bat a soke idon Macjiya barukul Karsum, ina
mai tabbatar miki da cewa da izinin Allah n
ice wacce zata soke wannan dayan idon na
macijiyar Burukul karsum kinga kowa idan na
samu wannan nasara na ruguza dukkanin
burinki tunda na kasance 'ya mace babu halin
ki aureni.
Koda Gimbiya Shadilat tazo nan
azancenta sai Lushmaira ta kyalkyale da dariya
har sai da kwalla ta cika mata idanu sannan
nutsu ta dubi Shadilat tace "aini gidanmu
kirarin sa'a ake mana tunma kafin a haifeni,
ko kakana, babana da ni kaina bamu taби за
wani abu a gabanmu face mun sami nasara, na
gayawa Allah wannan bukata tawa tun ina
yarinya karama har na girma na cika budurwa
balagaggiya ban taba fashin addu'a ba dare da
rana akan wannan buri nawa an sha nuna min
biya bukatata a mafarki babu adadi shin kina
zaton wani furuci na bil adama zai san a sare
21 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
har na fitar da rai ga samun nasara?.
Koda jin wannan batu sai Shadilat tayi
wa Lushmarai murmushi t ace "tabbas na yarda
kin riga ni gabatar da bukatar ki awajen Allah
to amma ai naji ance shi Allah maji rokon
bawansa ne a kowane lokaci kuma ako ina
koda kuwa a bakin kura yake, idan Allah yaso
zai iya biya mini tawa bukatar kamar yadda zai
iya biya miki taki in yaso tunda arzikin sa
bashi da iya in ya bamu ma atare babu abin da
zai rageshi daga cikin arzikinsa ni dake duk sai
mu jira loakaci domin shi ne kadai zai iya
awarware mana wannan kullin dake
tsakaninmu.
Lokacin da Shadilat tazo nana zancenta
sai jikin Lushmaira yayi sanyi tayi shiru bat
ace kalaba kawai sao ta mike tsaye ta shiga
kewaye tayi alwala ta dawo ta fuskanci alkibila
ta fara sallar nafila itama Shadilat sai ta mike
taje tayi alwalar tazo ta kama nafilar kamar
masu yin gasar ibada.
22
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Bayan yin Sallar asuba Sai likita Zauwad
tare da dukkanin tawagarsa sukayi hawa suka
nufi filin fada a inda Zau hadu gaba daya
kuma a inda Sarki zai hau manbari ya fara bada
wannan Hikaya.
Koda zuwansu sai suka ga kowa ya zo su
ka dai ne basu halarci gurin ba sarki ya hau
kan Mambari ya na shirin farawa dab haka su
kai sauri suka karasu wajen, Awannan lokacin
sarki da yarima sunyi gagarumar shigar yaki
mai tsananin ban tsoro da kwarjini duk su
biyun sanye da bakaken kaya na sulke rigar
karfe gami wandon karfe kuma sun rataya
zabgegeyar takubba a bayansu, A wannan
lokaci yarima ya tattare gashin kansa ya
daureshi ya zuba a gadon bayansa har izuwa
kasan kafadunsa. Nan fa kyawunsa da shigar
da yayi suka ribaci zuciyoyin Lushmairat da
Shadilat, take kowacce taji ya burgeta ainun
amma sai suka kasa tantance irin bugewar
acikin zukatansu shin burgewa c eta kamau da
23
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
sonsa ko kuwa rudewa ta kyan adon da yayi
amsar da suka kasa baiwa kansu kenan. Nan
kowa ya dukafa yana jin amon muryar sarki
cikin tattausar murya.
Acikin wannanlabarin d azan baku a
halin yanzu kafin mu fara yin tattaki izuwa
wannan gagarumamin yaki lallai ina mai
umartarku da ku nutsu ku saurari wannan
labari kasancewar aduk lokacin da irin wannan
ta tashi acikin wannan birnin namu mai tarin
albarka Idan za a tafi yaki duk wanda ya samu
shugaba awannan lokacin yakan kasance yana
mai tausar dakarunsa da Kara musu karfin
gwiwa gami da abinda yake gabanmu da
wannan dama ne Sauran sarakan da suka
gabata suke bada tahirin Annabawa ko kissoshi
daga irin Kissar ma aiki dan muuyi kuyi da
juriya da kuma dadurcewa afilin daga, wasu
kuma sarajan suna bada tarihin wasu jarummai
dan suka rike amana juna ko wasu sarakai da
24
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
suka bata da kuma yanda karshensu ya zo to
ayau dai, zan gabatar da wani labara gareku
mai nuni da rikon amana da kuma dadrucewa
awajen ganin ka samu nasara a duk inda ka
dosa, musamman ko dan jimawar da mukayi
bamu fita filin daga ba sai ku saurara kuji
wannnalabari wand azan baku hi a yanzu kafin
wayewar gari,
Acan wata daula baya da shekaru ashirin
da bakwai baya anyi wani attajirin kuma
hamshakin Karkarfan Sarki wanda yake mulkin
kasar Garzab ana kiransa da suna Muhuddu ibn
Asar, shi dai wannan Sarki ya kasance
musulmi kuma mai tsananin kaunar musulunci
da ci gabansa, wannan daliline yasa ya tsaurara
ra ayi akan adanninm musulunci har yazamana
idan akwai tarin laifika da idan mutun ya aikata
na sabon Allah ya tanadar maka iziya mai
tsananin wanda uban gijinmu bai tsaurarawa
bayinsa kamarsa ba domin shi ko sata aka
kama kayi sai an fille maka kayi idan kowa
25 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
zina kayi sai yasa an tsire ka kuma an kama
iyalanka an tafi dasu izuwa wata fursuna inda
anan ne zasu Kare rayuwarsu.
Wannan Sarki manyan malamai masana
Addini musulunci sunyi kokarin gaske
awannan lokacin akan ganin sun ganar dashi
gaskiya dan bazab manta ba mahaifina ya taba
bani labarin cewa har sai da kakana wato baban
mahaifina ya so ya yakeshi, duniya ta hana
saboda ana ganin musulmine kuma mai bada
gudunmawa akan wannan addininmu idan aka
yaki shi baza aci nasara akanshi ba kuma anyi
wa musulunci mummunan 6arna da domin a
Nahiyar da yake kasar sa ce kawai kasar
Muslul mai dan haka sai aka kyaleshi aka
dinga tura masa da malamai ta karashin kasa
dan su ganar das hi gaskiyar lamarin amma
fafu yake daukar abinda suke gaya masa. Da
haka aka zuba masa idanu dadintama jama'ar
Kasarsa basu fiya aikata laifiba sai yazaman
hukunci shi yafi yinshi akan kafurai masu
26
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
zuwa kasarsa yin kasuwanci ko kuma yin wani
abun daban,
Sai yazamana duk wanda yazo kasar
yayi wani addin daban to babu shakka sai yasa
an fille mishi kai da wannan aka samu dan
sauki tunda jama'arsa sun yarda kuma suna
kiyayewa.
Shi dai wannan Sarki dan sa guda daya
ne Wato Arfan, kamar yanda Sarki yazama
gagara badau ta fannin Sadaukantaka sai ya
zamana Aufan shima aduk cikar birnin da
batsewarsa babu wanda yake iya koda wasa
jini dashi saboda gudun kada ya wahalar da kai
face Ansaru ibin Tamkar, Ansaru Abokine ga
Aufan wanda su dukan Suka koya horarwa
daga wajen Sarki Muhaddud tun suna yara
suka taso ta babu wani abu day a taba shiga
tsakaninsu koda wasa wanda zai sosa zuciyar
dayansu da yake shi Ansaru ya taso ne daga
cikin gidan maraya ne bashi da iyaye tun yana
karami iyayensa suka rasa rayuwarsu, dan haka
27 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
komai Sarki idan zaiwa Arfan tare yake musu
yana kaunar Ansaru kamar yanda yake kaunar
Arfan,
Shi idan ubangiji idan ya kawo gyara
babu ta inda baya bayyanar da hanyarsa dan
daidaita tsakanin al'umma da shuwagabaninsa,
Lokacin da Ansaru ya zama babban
Sadauki acikin wannan masarauta ya zamana
sewa shi da Arfan sun zama man yan zakuna
aduk nahiyar wannan kasa baki daya, Sai
yazamana Ansaru ya kasance cikin bakin cikin
irin yanda sarki yake tafiyar da mulkinsa a duk
ilimin day a koya daga gurarin malamai da
yawa bai taba cin karo da inda Allah (S.W.T)
ya bawa wani bawansa dammar yin hukunci
irin wanda wannan Sarki yake,
Dan haka sai ya tafi izuwa ga Sarki har
cikin turakarsa ya sameshi a zaune ya gaisheshi
sannan ya dubi shi cikin ladabi da biyaya cikin
murya atausashi ya ce "Ya abbana wata
28 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
muhimmiyar Magana ce na zo da ita gareka
kuma ina son ka karbeta kuma kayi aiki da ita
domin kaucewa fushin ubangiji da samun
nutsuwa ga wannan addini namu na musulunci
wanda shugabanmu Annabi mohd yake
jagoranta,"
Koda jin wannan batu daga bakin Ansaru
sai ran Sarki ya fara 6aci domin ya san cewar
karshen zancen domin shi kansa yasan cewar
tunda yaron ya fara neman ilimi sai watarana
yazo ma sa da zance makamancin haka, don
haka cikin nuna bacin rai ya dubi Ansaru yace
"zan saurareka idan har maganarka baza ta zo
daya da manyan malamai suka sha sanar da
niba sai dai kuma zan gargadeka akan cewar
idan har kasan wannan Magana tayi kamancеce
niya da irn kalamansu to kayi gaggawar barin
wannan guri ko kaifin takobina ta ratsa jini da
tsokar ka alokacin da ba ka zaci haka ba"
Tun tasuwar Anwaru ya kasance mutun
mai tsananin taurin kai da nuna isa awajen da
29
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
aka ce wani ya sabawa mahaliccinsa ko waye
sai ya gaya masa Magana koda zai rasa ransa
dan haka sai yayi murmushi ya kara duban
Sarki akaro na biyu, ya ce "yakai mahaifna
umarnin Allah zan sanar da kai ba umarni ba
kuma idan zan fadi umarnin Allah bana
bukatar ace sai na tsira da rayuwata, tabbas
koda zaka kasheni sai na sanar da kai" koda
yazo nan azancensa bai yi aune ba sai jin hucin
takobi yayi ta nufo kanshi da niyar za asare
kanshi, cikin tsananin zafin nama ya rike kaifin
takobin batare day a ko daga kai ya kale Sarki
ba ya ci gaba da cewa "kabi turbar da
ubangijinmu ya umarcemu da shuwagabannin
su ladaftar da al'umarsu kana izaya da wuta
face babu wanda yake wannan face Allah
mahaliccinmu kana kasha rai aka aikin da
ubangiji bai bamu umarnin kisa ba kana yanke
hukunci akan musulmai wanda hakan zai sa
dayawan kafurai su ji tsoron shiga cikin
wannan addininmuidan har ka sake ka mutu a
30 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
haka to na tabbata ba kai ba rahamar ubangiji
ka daina ganin wannan yawan ibadun da kake
yi zasu fisheka idan har akwai hakkin wani
akanka dan haka ka tsayar da wannan dokokina
naka dan ba na Allah bane," cikin tsananin
fusata Sarki ya kwarara wani uban iho ya sake
takobin wanda jinin jikin Ansaru ya mai da ta
ja ta rine da sauran gurin da jininsa yake
kwarara. Ya nufi jikin bangon dakinsa ya
dauko wata falleliyar takobi guda ya ja daga ya
ce "Ganin isa yasa kake wannan dagiya agareni
yau zan tabbatar maka da cewa tsofana bai tafi
da juramtata ba don haka ka rike takobin
hannunka yanzu ni da kai gawar dayanmu cе
zata fita daga cikin wannan turaka idan kuwa
ba haka sai na sa an kama an azabtar da kai
mafi munin azaba waninka bai taba gani ba"
Koda Ansaru yaji wannan batu sai
hawaye suka zubu daga idanuwansa jikinsa
yayi sanyi ya sunkuyar da kansa kasa yana mai
31 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
sheshshekar yin kuka, Sarki na tsaye yana jiran
yaga ya dauki wannan takobi sai yaga shi cikin
wannan hali koda faruwar hakan sai shima
sarki jikinsa yayi sanyi kuma ya kamu da
tsananin mamaki ya dubi Ansaru cikin sanyin
murya, y ace dashi "tun kana karamin ka taurin
kai yake dawaniya da kai ya kai wannan da
nawa banda abinka ina kai ina kawo min
wannna bataccen zace ina so kayi sani shi ilimi
ilimine a wani lokacin mutane suna fassara
alkur ani a wata fassarar daban dan haka ka
kiyaye na yafe ka ka tafi"
Koda jin wannan zance na Sarki sai
Ansaru ya yi taku bakwai acikin falon sarki
wanda shi ne ya kaishi har izuwa bakin kofar
fita said a ya je wannan gurin sannan ya juo ya
dubi sarki ya'ce "hakika kayi nisa da yin kira
agareka zai zama 6ata lokaci dan haka ina son
kasani daga wannan ran azan bar maka wannan
gida naka na tafi can wani gurin inda zanci
gaba da rayuwata cikin rainon muluncin da
32
Abdul'Aziz Sa
TURBAR GASKIYA -2
yanda manzon shugabanmu ya koyar. Amma
ina mai sanar da kai daga bari na wannan kasa
zuwa kwanaki ashirin masifa zata sauka acikin
C
birininka wanda za a rasa hanyar maganceta
zai zamana idan baka aminta ta dadi rai ba
zaka aminta ta wahala, sannan ina mai rukonka
akan kada ka sanar da Aufan cewar munyi
Magana da kai maka manciyar irin wanda
mukayi yanzu da kai domin ni kaina da badan
hurumin Allah da ka taba babu dalilin da zaisa
nayi maka gardama har takai ranka ya baci
saboda bani da wani uba face kai kuma bani da
wata uwa face kai,
Koda yazo nan azancensa sai ya sa kai
ya fuce idanuwansa na masu zubar hawaye
Sarki Muhadud ya tsaya ya bishi da kallo cikin
takaicı nan take kuma sai wani tunanin ya fado
masa koda yin wannan tunanın sai ya kira wani
hadimansa yayi masa umarni da yake gidan
sarkın yaki Asbasya sanar dasni cewa yana mai
33 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2 S- AYIНГА ЯАДИТ
kiran gaggawa. sy unsdsgudг поsпв sbnEV
tennow sir ind sgeb is sh se is
Nan take wannan hadimi ya tafi yaje ya
sanar da Sarkin yaki Asbaz kafin ma hadiman
ya koma gida tuni Sarkin yakin ya iso cikin bin
umarnin Sarki koda zuwan sai saarki yaja shi
izuwa cikin turakarsa suka kebance nan take ya
MC SIA БО ТБПS2 БК EDEX USKS
shada,masa cewar yana son duk yanda zasu
kada su bar Ansaru ya bar wannan garin su je
su kamashi su kaishi kurk goinyana kurkuku
kyautata zaton ya samu matsala 2. 60 Hing i ivea
b ine Aikuwa kafin wani. yunkuri na sarkin
yaki tuni Ansaru ya baci daga cikin birnin an EIR eCSI BWU BI
rasa kuma ta inda yabi domin masu tsaron 29ε gyeuconρς USD. λSNO κοσς
kofar birnin sunce basu ganshi yazo ya wuce
ba koda faruwar wannan abu, sai aka, shigi 129di 5 Mb 25LK
cikin mamaki.Aufan ya shiga neman abokinsa 2SP KAB ISKC USU KSICI
Ansaru har ya gaji bai ganshi ba kuma da ya nςικς migs y kogς usas
sanar da mahaifinsa sai ya ce"aishim
nemansa Acas yake kuma ya shiga, wani hali, na
rashinsa dan haka sai aka koma nemanshi
34 insd zisA'lubdAbdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
asirrance batare da an gano inda yake ba da
wannan hali har akwa kwashe kwanaki goma
sha takwas daga nan kuma sai