inda harin sumamame ne
dab azan so na sanar da kai ba ni zanje nayi
maganinsu, shu'umar macjiyar nance Burukul
karsum ta shigo take ta cinye mutane, koda jin
wannan batu sai mahaifin Lashmaira ya juya da
baya aguje ya shiga cikin wani daki agidan
gonar, jim kadan sai gashi yya dawo acikin
gagarumar shigar yaki, kawai sai ya tukari inda
dokinsa yake da nufin ya kwance shì ya hau.
25
Koda ganin haka sai Sarki Abu zaiyan ya
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ruga gareshi ya rike dokin nasa ya dubeshi
alokacin da kwalla ta cika masa ido yace "haba
yakai dan uwana shin ka manta ne da wasiyar da
mahaifinmu yabar mana cewar kada mu kuskura
muyi gaba da gaba da wannan macijiya banzo na
sanar da kai zuwan tab a dan kaje ka yaketa
saboda tuni na dauki mataki, na tara malaman
garinnan suna ta yin addu'a kuma na tura dakaru
da yawa suna yaki da ita"
Lokacin da sadauki Hizanu mahaifn
Lashmaira yaji wannan batu sai sai shima kwalla
ta cika masa idanu ya dubi Sarki Abu zaiyan
yace "yakai dan uwana shin ka mantane cewa
nine Sarkin yakin wannan garin" hakkine akaina
na futa na tari wannan muguwar macijiyar nasan
baka sone na mutu shiyasa kakė so ka hanani
naje na yaketa, shin su dakarun daka tura su
yaketa basu da 'yan uwane agarin?
Suna da 'yan uwa suna da mataye da
'ya'yaye kamar yadda nima nake dasu, raina
baifi nasu darajaba, saboda ni su zaka turasu su
hallaka amma ni kaki turani? Koda sadauki
Hiziyan yazo nan ajawabinsa sai Sarki Abu
zaiyan ya rungumeshi kuma ya fahe da kuka
yana mai cewa "yakai dan uwana hakika duk
26 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
abin da ka fada gaskiya ne amma idan baka
manta ba mahaifinmu ya gargademu akan cewa
duk mutumin da yai gaba da gaba da wannan
shu'umar macijiyar sai ta hallalashi, Hizanu ya
janye jikinsa daga cikin na Sarki Abu zaiyan
yace "wannan gaskiya ne amma kuma ya gaya
mana cewaa duk ranar da ta shigo garinnan babu
abinda zaisa ta dainafarna ta juya da baya ta fice
face anyi mata rauni ajikinta kuma kasani cewa
ni kadaine zan iya yiwa wannan macjiuar rauni.
Koda jin. Koda Sadauki Hiziyan yazo nan a
zancensa sai jikin Sarki yayi sanyi ya kasa cewa
komai, nan take Hiziyan yaje gaban mahaifiyar
Lashmaira tana rike da jaririyarta a hannu ta
kura mata idanu alokain da kwalla ta ciki mata
ido,
Al 'amarin da kara karya zuciyar Sadauku
Hiziyan kenan ya sumbaci mahaifiyar Lushmaira
sannan ya sumbaci jaririyar sannan yace "yake
matata idan 'yata ta girma na umarce kid a ki
gaya mata cewar ina mai neman ga fararta bisa
na maid a ita marainiya tun kafin ta taso ta san
mahaifinta, ki gaya mata cewar na sallama
rayuwata ne dan na cici rayuwar miliyoyon
al'umma musulmai idan Allah ya rayata kuma ta
27 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
isa aure ina son ta auri gagarumin Jarumi wanda
yayi jarumtaka kwatankwacin wacce nayi ko
wadda tafi tawa, wannan shi ne burina kuma shi
ne fatana da na dade ina yiwa wannan jaririya
tamu".
Sa'adda Sadauki Hizanu yazo nan
azancensa sai hawaye ya zubuwa mahafiyar
Lushmaira ta sumbaci goshinsa t ace "Ubangiji
Allah ya cika maka burinka, yakai mijina kayi
sani cewa wannan yaki da zaka je kayi yanzu da
wannan macijiya aikin ne na sahahada saboda
haka zakayi mutuwa irin wadda akeso abar
alfahari agareni da kuma 'yarka dama dukkanin
musulmai kayi sani cewa wannan hawaye da
kaga ina zubarwa ba wai ina zubarwa bane dan
zaka mutu ba said an kawai tsananin
sabo,shakuwa, da kaunar dake tsakanina da kai.
Koda tazo nan azancenta sai ta rungume
shi a jikinta da kyar Hizanu ya banbareta daga
jikinsa ya koma wajen dan uwansa Sarki Abu
zaiyan suka rungume juna suna kwalla sannan
sukayi bankwana na karshe. Nan take Sadauki
Hizinu ya kama dokinsa yah aye kuma ya
zabureshi da gudun zuwa cikin gari cikin sauri
28 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
shima Sarki yabi bayansa aguje,
Alokacin da Sadauki Hizanu ya isa ciki n
gari sai ya iske garin acikin mugun hali, domin
mutane sun dimauce iface iface da guje guje yai
yawa ya cika dodon kunne gidaje ma bata barsu
ba domin bi take ta kansu tana rugujewa kamar
antsalitse man shanu akan dutse hakika girman
wannan macicijiyar ya wuce tunanin mai tunani.
Jinin mutane kuwa sai malala da gudu
yake akasa tamkar teku ta balle, Koda ganin
wannan ala'amarin sai Sadauki Hizinu ya fusata
ainun ya kama kwarara uban ih ya zaburi
dokinsa da gudu izuwa hanyar da yaga mutane
sunfi tahowa dagudu, ashe kowa macijiyar nan
na wannan bangaren,
Koda Sadauki Hizanu va iso inda
macijiyar take tana tahowa da gudu mutane na ta
kokawar neman boya shi sai ya tsaya cak ya rike
linzamin dokinsa alokacin da dokin nasa ya
tsorata ainun ya kama tirjiya da haniniya bisa
ganin macijiyar,
Koda macijiyar taga Hizau ya tsaya cak
agabanta ko alamar tsor babu a tare das hi sai
itama ta tsaya ta daga kanta cansama izuwa
29 ABDUL'AZIZ SANI.M/GINI
TURBAR GASKIYA
kololowa suka fara kallon kallo,kawai sai
Hizanu yayi bisamilla yana mai zare takobinsa
cikin bakin zafin nama macijiyara ta kawo masa
sura da bakinta da nufin ta hadiyeshi.
Hizanu ya wuf ya bar kan dokin yana
maid aka tsalle can gefe daya aikuwa sai
macijiyar ta gatsa dokinsa Hizanu ta rabashi gida
biyu tamkar wuka akasa akai yankashi nan take
jinin dokin yai fallatsiakan fuskar Hizanu yayi
masa wanka duk jikinsa ya rine da jinin dokin,
cikin hanzari Hizanu ya goge jinin fuskar ya
gyara tsayuwarsa yana mai fuskantar macijiyar
acikin shakka da fargaba domin ya fuskanci
cewar masifar wannan macijiyar ya wuci duk
yanda yake tsammani aikuwa sai macijiyar ta
jeho jelarta ta baya izuwa kan Hizanu da nufin ta
makeshi, cikin shammace.
Kawai sai taga Hizanu ya daka tsalle sama
ya dira ajikinta yana mai falfala gudu domin ya
isa inda kanta yake, kai kace kanwani tsauni
yake hawa.
Koda macijiyar ta gane cewa so yake ya
isa inda kanta yake domin ya cutar da ita sai ta
rinka mako jelarta don da bugoshi kasa amma
saboda bakin zafin manasa sai ya rinka shawagi
30 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
akanta yana kaucewa jelar tata sai dai kaji shu..
faf.. fat..tana zane jikinta da kanta amma ta kasa
makoshı kasa, sai da aka dauke lokaci mai tsawo
a haka gashi dao Hizanu ya kasa isa inda kan
macijiyar take ita kuma ta kasa makoshi
kaasakuma saranta yake da takobi amma kamar
dutse yake sara sai dai kaga taratsatsin wuta na
tashi.
Itaanta macijiyar al'amarin yai tsananin
bata mamaki domin bata taba haduwa da
takadirin jstuni ba wanda ya zame mata
alakakaia kasa hallakashi acikin abinda bai
wuce dakaika dari da tamaninba sai yau.
Koda macijiyar ta rasa yanda zatayi da
Sadauki Hizanu sai wata dabara ta fado mata ta
kama birgima akasa, ind ba don Hizanu na
mutukar zafin nama bad a tuni ta turmusheshi
aksa tayi rugu rugu dashi,
Koda yaga ta fara wannan birgima sai ya
falfala da azababban gudu ya nufi inda wata
doguwar ganuwa take, nan fa suka kasa tsare
tana kai masa cafka da bakinta yana gocewa
kuma tan a kai ma sa maka da jelarta yana
kaucewaduk abinda nacijiyar ta buga sai ya
wargazaa haka har suka isa inda ganuwar take
31 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
sai Hizanu ya kama hawa wannan ganuwar
kamar yanda kadangare ke hawa bango aikuwa
sai itama wannan Macijiyar ta fara kanannade
wannan ganuwar ta rinka yin sama suka kasa
tsere ita da hizanu yana azababbabab gudu akan
ganuwar tana biye dashi yazamana cewa tazarar
da ke tsakaninsu bata wuce kamu biyar ba,
kokarin macijiyar shine ta kamo kafafunsa da
bakinta ta fara hadiyeshi amma sai abu ya gagara
har suka kusa isa karshen Ganuwar
Ita wannan ganuwar an ginata ne da wani
rin dutsen wuta mai tsananin kaurin gaske dalilin
da yasa Macijiyar ta kasa rugozata kenan domin
agaba daya birnin na Baitul Haural babu wani
gini mai kaurin wannan ganuwa.
Hizanu yasan da hakan shi yasa yaja
macijiyar izuwa can, abinda bata sani ba shine
dabara yayi maya doin ta kawo kanta kusa dashi
yasamu inda zai yi mata illa, koda ya isa karshen
ganuwar sai ya sake jikinsa ya nufo kanta yanda
shi ma kansa ya san idan ya runtumo sai ya
karairaye saboda nisən dake tsakaninsu saman
ganuwa da kasanta,
Hlzinu yana sama ya saita talobinsa
izuwa dio guda na wannan macijiyar. Aikuwa
32 ABDUL'AZIZ SÁNI M/GINI
TURBAR GASKIYA
kafin macijiyar ta dauki wani mataki tuni tsinin
takoin nan ta shiga cikin idon nata, take ruwan
ido ya fashe jini ya kama bulbulowa Macijiyar
tayi wani irin ruri mai tsananin firgitarwa
alokacin shi ma hizanu ya kama iho alokacin da
yaga ya taho kasa lu....kawai sai macijiyar tayi
amfani da jelarta a cafke Hizanu da
kanannadeshi kawai sai ta dinga matseshi yana ji
yana gana: ta dinga karairaya masa dukkan
kasusuwan jsa, in yana ihu da motsi har sai
da ya daina
Ita kuwa wannan macijiyar bata daina
wannan ihu da ruri ba sakamakon tsannain zugi
da take ji, said a ta tabbatar da cewa Hzanu ya
zama gawa sannan ta warbar da gawarsa a kasa
ta kama jan jiki a hankali a hankali ta nufi
hanyar fita daga cikin birnin gaba daya cikin
tsannain bakin ciki ta zama mai ido daya.
Duk wannan abu day a faru Sarki Abu
zaiyan na labe abayan wani rusanshe gini yana
kallo. Tun sa'adda yaga macijiyar ta sami nasara
r kanannade dan uwansa Hizanu sai ya fara
kuka domin yasan cewa muuwazaiyi.
Koda macijiyar ta fuce daga birnin gaba
daya saiSaarki Abu zaiyan ya ruga izuwa inda
33 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
gawar Hizanu take ya dauketa ya rungumeta a
kirjinsa ya fashe da matsanancin kuka tamkar ba
zai daina ba.
Tun daga ranar da wannan abu ya fau
macijiyar Burkul karsum bata sake shigowa
cikin wanan birnin ban a Baitul Haural dare da
rana tana cikin kogi na dajin siril maut. wannan
shine asalin yadda mahaifin Gimbiya Lushmairat
ya sara rayuwarsa.
Said a sui Sarki da Yarima suka shafe sa'a
daya da rabi suna wannan bakin gumurzun har
suka fice daga cikin gidan sarauta suka tsinci
kansu a tsakiyar filin birnin inda wannan
doguwar ganuwar take, koda yarima yay Arba da
wannan ganuwa acan nesa dashi kadan sai ya
mike zumbu ya falfala da gudu izuwa inda
ganuwar take aikuwa sai yarima ya kama
hawanta tamkar kadangare na hawa bangokamar
yanda marigayc Sadauki Hizanu yayi ya hauta
ashekarun baya da kyar sarki ya dinga
kwakkwayan Yarima har ma yaringa zamewa
kamar zai fado kasa amma saboda naci da juriya
sai yaci gaba da bin yarima.
A wannan lokaci gaba daya mutane garin
suka fito suna kallin ikon Allah cikin tsannan
34
BDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
mamakidomin a tarihin wannan ganuwar in
banda marigayi sadauki babu wanda ya taba
hawanta har ya kai karshenta, idan ana so a hau
ganuwar ta dole sai anyi amfani da igiya, haka
dais u Sarki da yarima suka ci gaba da hawa kan
ganuwar Koda suka iso rabin tsawanta sai Sarki
ya kakare wato ya kasa ci gaba da hawan har
said a ya isa can samanta ya dirge acikin gininta,
Koda yarima ya leko kasa yaga irin nisan
dake tsakanin ta sama da kasanta sai ido ya raina
fata, hankalinsa ya dugunzuma ainun domin bai
gat a hanyar da zai iya saukowaba, shi kansa
Sarki da ya makale atsakiyar tsawan ganuwa
idan ace zai saki hannunwansa ya fado kasa
hallaka zaiyi, jama'arjama'ar dake gurin suna
kallon abin dake faruwa sai suka kama sallallami
domin suna ganin cewa tabbas a yau dai Sarki da
yarima sun tafka babban ganganci wanda zai
zamo sanadin ajalinsu, lokacin da sarki ya dubi
kasa kuma ya dubi can sama inda yarima yake
sai hankalinsa ya dugunzuma ainun domin ya
fahinci cewar Yarima ba zai iya saukowa ban an
fa ya fara tunanin mafita, kawai sai ya daga kan
sa sama gami da daga hannunsa guda daya
dayan kuma na rike da ganuwar yayiwa yarima
35 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
day a sallamo kasashi kuma ya café shi.
Koda ganin haka sai zuciyar Yaarima a
karaya yaga cewa ta yayay Sarki zai iya café shi
da hannun daya alhalin shi kansa ma lilo yake
ajikin ganuwar a inda yake.
Nan fa yarima ya npke a lokacin da Sarki
key a fitoshi da hannu
Adai dai lokacinne labara ya riski
Gimbiya Lushmairat cewar ga yarima da sarki
sun hau kan ganuwar har ma yarima ya kure
karshenta, koda jin wannan batu sai Gimbiya ta
mike zumbur ta ruga da gudu izuwa filin da abin
yake faruwa.
Tsakanin gimbiya da Yarima Zaiyan ba'a
ga maciji banda kushe da hassada babu wani
fahintar juna ba wani abu bane ya janyo hakanba
face yadda Lusmaira take yiwa mazaje gori
agarin tana cewa duukkkaninsu matane babu
namiji ko guda daya daya tunda an rasa jarumi
da zai iyayin irin Jarumtakar da mahaifnta yayi,
wannan tsa duk inda suka haďu da yarima sai
'yar tsama. Bugu da kari shi ne Yarima Zaiyan
ne koda wasa bai taba nuna son Lushmairat ba
duk da cewar kaf samarin garin sun kidime sun
dimauce saboda ita wasu ma har nema suke su
36 BDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
zauce dan basu da aiki sai sai begen ta da rera
mata wakoki abinda ya daurewa Lushmaira kai
kuma ya fusata ta ainun shine ko a hanya suka
hadu da Yarima sai yak au da kai kamar baiganta
ba wanni lokacin bangazar juna suke ta wuce,
kai in ba don ma alakar musulunci bad a Magana
ma basa su dinga yi ba duk da kasancewarsu
'yan uwa juna,
Ita tana takama da kyaunta da kuma
kasancewarta jinin sarauta shi kuma yana
takama da jarumtakarsa da saurauta.
Har Gimbiya Lashmaira ta isa filin gurin
Yarima da sarki sun kasa saukowa daga kan
wannan ganuwar kuma asannann hankalin kowa
ya dugunzuma ainun an rasa yadda za ayi a ceto
rayuwarsu Sarki wasu sun fara bayar da shawara
a samo igiyoyi a cilla musu su kuma su daura
ajikin ganuwar amma kuma Sai akaga cewar yin
hakanma abune mai wuya domin kafin su samu
nasara cafkar igiyoyin ko kuma a akokarin kama
igiyoyin zasu iya subutowa kasa, musamman
Sarki wanda tuni ya fara gajiya saboda reto yake
ajikin Ganunwar,
Koda gimbiya Lashmaira ta fahinci abinda
ke faruwa sai tayi murmushi nan take ta
37 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
kwalawa wasu dakaru si goma kira wadanda
suka kasance majiya karfi ta umarce su das u
ruga su dauko raga. Cikin abinda baifi
rabin sa'a ba suka je suka dauko raga, da
zuwansu sai tayi musu jagora suka je daidai inda
ganuwar take suka yi kawanya ruke da ragar
A sannanne ta daga kanta can sama kuma
tayi musa nuni das u fado cikin ragar, batare da
fargabar komai ba Sarki ya fara sallamowa kasa
shima yarima sai ya dako tsalle ya subuota kasa
shu.... Kusan lokaci iguda duk su biyun suka
fado kan wannan ragar a cikin koshin lafiya, koda ganin haka sai mutane suka rude da
kabbara aka kama farin ciki da yiwa Allah godiya.
Koda yarima ya dira daga kan ragar sai ya
matso gaban Lushmaira ya dubeta fuskarsa a
murtuke yace "me yasa kika cec rayuwata
alhalin kince kin tsani duk samarin garinan?
Koda jin wannan tambaya sai gimbiya ta dubeshi cikin murmushi akaro na farko tun da saninsa da ita t'ace "na ceci rayuwarka ne saboda
dalilai guda biyu,
Dalili na na farko shi ne ina son na сеci
rayuwar Sarki a matsayinsa na kanin mahaifina
38
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
kuma wanda yake mutukar kaunata tamkar shi
ya haifeni, dalili na biyu kuwa shi ne na cece ka
ne kawai saboda naga kayi irin jarumtakar da
mahaifina yah aù kan wannan ganuwar ne ya
kure karshenta kamar yadda kayi ya sallamo
kasa ya soke idon macijiya Brukul karsum ya
ceci rayuwar al'ummar birnin nan wato ya
sadaukar da rauwarsa domin ceto rayuwar
jama'a. kai ne mutun na biyu da ya iyahawa
karshen wannan ganuwar, yanzu abin day a rage
agareka na daina kyararka da tsanar ka shi ne ka
soke daya idon macijiyar Burukul karsum.
Koda gama fadin hakan sai gimbiya
Lushmaira ta juya da koma izuwa cikin gari,
jama'a kuwa sai suka rugo izuwa wajen yarima
suka dagashi ana kabbara ana yi masu jinjina
bisa wannan jarumtaka da sukayi tahawa kan
wannan ganuwar wanda ta gagari kowa hawa,
Ana cikin wannan haline manzo ya iso
daga birnin Hizuba daya daga cikin masu gadin
ne yayi masa jagora a kasa suka durfafo inda su
Sarki suke yana ruke da wasika, da isowar
manzon gaban Sarki sai ya zube kasa cikin
girmamawa ya kwashi gaisuwa sannan ya
mikawa wasikar.
39 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
Sarki Abu zaiyan ya karbi wannan wasikaar da hannunsa ya budeta ya karantata
yana gama karanta wannana wasikar sai ransa ya
baci nan take zuciyarsa ta kuma tafarfasa kamar
zata kone. Koda ganin haka sai yarma yai wuf ya
zare takobinsa da nufin da nufin ya sare kan
wannan amnzo day a kawo waskar saboda zargin
ko sakon ne ya dake cikin wasikar ya aibata Allah.
Cikin hanzari Sarki ya ruke shi y ace "ai
ba akashe manzo ko afilin yaki idan basu taба
addininmu ba, Mafarkin da kayi ne ya tabbata,
lallai lokacin yaki ne yazo domin bukatar da
suka zo mana da ita indai nki biya musu ita sai
munyi yaki dasu Nan take Sarki ya sake
karantawa su Yarima wannan wasika afilin kowa
yaji, bayan y agama karanta wasikar sai ya dubi
wani hadimansa yace dashi "akai wannan Manzo
masauki a bashi abinci" sarki ya sake duban
wani Hadiminnsa daban yace "kai kuma kaje ka
sanar da 'yan majalisa su sameni a Dakin Gani
kuma kaje Unguwar 'yan gudun hijira
Ka gaya masu har iyalansu suzo fada,
Hadimin ya duka yace angama ya shugabana
40
ABDUL'AŽIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
nan take shima ya ruga domin cika wannan
umarnin na Sarki,
Sarki da Yarima kuwa tare da wasu
tsararun Dakaru sai uska nufi Fadar Kai tsaye.
Lokacin da 'yan majalisa suka cika a
dakin Gani gaba dayansu ga Sarki da Yarima
zaune agabansu sai aka bude taro da addu'a
sannan Sarki yai gyaran murya yace "To
wasunku dai sunji abindake cikin wannan
wasikar da Sarakunan da suka makwantaka
damu suka rubuto ga wanda bai jib a yanzu zan
maimatabayan nan kuma ai ku kawo shawarwari
bida abin da kuke ganin zai fishshemu.
Nan take Sarki ya zaro wannan wasika ya
sake karantawa afili kowa yaji, nan fa Dakin
gani yayi tsit aka rasa wanda zaice komai sai
yarima ne ya numfasa ya mike tsaye ya dubi
'yan majalisa daya bayan daya yace "ni atawa
shawarar kada mu kuskura mu mikawa
wadannan jama'a mutun miliyan bakwai
wadanda suka karbi addininmu tare da
dukiyoyinsu da iyalanu, dalilina shi ne idan
muka mika sum un nuna muna jin tsoro
wadannan abokan gaba namu sun sami logonmu
kenan da nan gaba masu zo su iya kawo mana
41 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
hari, abu na biyu idan muka mika wadannan
mutane addinin musulunci zai sami rauni a
Nahiyar nargaba daya, yakamata ace duk kanin
musulmi bazai ji tsoron komai da kowa ba akan
addininsa tunda ya tabbatar da cewashi ne akan
TURBAR GASKIYA baza muje tsoron abokan
gaba ba koda kuwa gaba daya wadannan
kasanshin da ke kewayae da mu zasu yi mana
rubdugu, mun dogara ga Allah kuma kun yi sani
cewa duk wanda ya dogara ga Allah zai iya masa
abinda ya gagareshi".
Koda yarima Zaiyan yazo nan azancensa
sai dakin taron ya rude da kabbara kowa ya nuna
cewayana goyan bayan dari bisa dari, Al'amarin
day a jefa Sarki da yarima cikin tsananin farin
cikikenan, Sarki ya sake yin gyaran murya a
akaro na biyu sannan yace yanzu idan har yaki
nan ya tabbata ina son Yarima ya jagoranci
rundunar mayakanmu saboda kun sani cewa tun
da mutuwar Dan uwana Sadauki Hizanu ban
dana wani Sarkin yakin ba in har Yarima ya
samu nasarar wannan yaken to shi ne Sabon
sarkin yakinmu".
Ko da jin wannan batu sai fadar ta rude da
kabbara da kuma fatan samun nasara, shi kuwa
42
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TUPBAR GASKIYA
Yarima ji yayi kamar aan yaye masa dukkanin
bakin cikin san a duniya sai ya ayyana aransa
cewa komai rintsi da tsananin sai ya san yanda
yayi ya sanu nasara awannan yakin.
Nan take Sarki ya salami 'yan majalisar
bisa cewa za aika da wasikar raddi ta yaki gasu
Sarki Madhan.
Bayan yan Majalisa sun waste daga cikin
dakin Gani ya rage daga sarki sai Yarima kadai
sai Sarki ya tura aka kirawo masa wadannan
mutane su miliyan bakwai wadanda sukayi hijira
daga kasashen makotan guda uku suka karbi
addinin Musulunci, gaba daya wadannan mutane
sai suka taro a fada gaba Sarki da yarima.
Sarki ya dubesu ya ce "yaku wadannan
baki namu masu albarka kuyi sani cewa
Sarakunan kasashenku da kuka baro sun aiko
mana da wasika akan ma baso ku da iyalanku da
dukkanin dukiyarku ko kna su zo su yakemu,
shin kun zaci ku ci gaba da zama damu anan da
dukiyayoyinku da iyalanku?
Koda jin wannan tambaya sai gaba dayan
mutanen sukayi shiru aka rasa wanda zaice kala,
kawai sai suka dare suka bayar da hanya a
tsakiyarsu. Nan take sarki da yarima suka hango
43 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
wata mace acikin bakakin tufafi idanunta kawai
ake gani,
Koda tai so daf da Sarki da yarima ai ta
rissina ta gaishesu cikin girmamawa sannan ta
yaye fuskarta,
a
Koda Sarki da yarima sukai arba da
fuskarta sai suka cika da abin al'ajabi saboda ko
tarihi basu taba ganin macen da ta kaita kyau
ba, kai hatta inda gimbiya Lashmaira zata zo ta
tsaya a kusa da ita da sai kyawun Lushmaira ya
disashe ta zama mummuna.
Kyakyawar budurwa ta bude baki cikin
zazzakar murya mai dan karan dadi da zaki tace
" sunana Shadilat, mahaifina kuma shine attajirin
da yafi gaba dayan attajiran dake wannan
nahiyan arzki kuma yana zaune açikin birnin
Hizuba, sannan ya kasance dan uwa ga Sarki
Madhan, ko shi kansa Sarki Madhan bai san da
wanzowata ba a duniya domn tun daga ranar da
aka haifeni mahaifina ya boyeni bai yarda wani
mahaloki ya sake ganin fuskataba ko jikina face
shi da mahaifiyata har na girma na zama
cikakkiyar budurwa idan kuwa mahaifina zai fita
dani izuwa kasuwa ko wani guri sai na rufe
idanuna yadda babu wanda zai iya ganin fuskata
44
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
hatta wadannan mutane da suka kasance abokan
hijirata basu taba ganin fuskar tawa ba gaba
daya wadannan jama'a da kuke gani basu samu
dammar yin hijara daga garuruwansa said a
taimakon mahaifina domin kuwa said a ya biya
dakarun kowane birniyakai wannan Sarki mai
adalci mahaifina ya shaidamin cewa anan
garinne kadai zan iya baiyana kaina ga jama'a na
zauna lafiya nayi rayuwa yadda kowane da adam
yake yi aduron kasa cikin zaman lumana idan
bah aka ba kowa masoya su za su sace ni, ayanzu
mahaifinawa yana so ya kwaso dukiyarsa gaba
daga birnin Huzuna ya dawo nan da zama domin
ya karbi addinin musulunci wato addinin gaskiya
amma ya kasa saboda Sarki ya zuba masa
matakan tsaro ya sa ido akanshi sosai sama da
komai na rayuwar sarki matakan tsaron da yasa
masa sun yawaita har takai da koda numfashinsa
akan idonsu yakeyi dan haka bai isa ya ketare
suba.
Daga cikin dukiyar mahaifna abin da nazo
dashi nan nake juyawa akasuwa daga cikin
arzikinsa baifi kaso daya daga cikin goma ba ina
tabbatar maka da cewa in dai mahaifna ya samu
dammar dawowa nan tare da manyan hadimansa
45 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
da dukiyarsa sai wannan birnin mai albarka ya
habaka a akasuwanci ninki yadda yake a yanzu,
ina mai neman alfarma guda daya jal a wajenka
yakai wannan Sarki mai daraja,
Koda jin haka sai Sarki ya dube Shadilat
cikin tsananin mamaki alokacin da gaba dayan
sauran 'yan gudun hijirar keta kokarin leken
fuskarta suna dimaucewa bisa ganin tsananin
kyawonta da yadda boye kanta acikin sub a tare
da wani ya taßa ganin taba az ahiri,
Sarki yace "yake wannan ma abociyar
kyawun fuska ke kuwa wace irin alfarma kike da
ita haka kike son nayi miki ita? Koda jin
wannan tambaya sai fuskar Shadilat ta fadada da
murmsuhi nan take kyawunta ya ninku na da
alokacin da Wushiryarta ta bayyana, Shidilat
tace "Yakai Sarki mai adalci kayi sani cewa ni
tun ina kara mata da na taso babu abin da yake
burgeni sama da jarumtaka don haka sai nakawai
naji burina na zama jaruma mai dakakkiyar
zuciya, juriya, naaci, da iya yaki, tun asannan
mahaifina aya dauko hayar wani mayaki ya
koyar da ni har na girma amma duk da haka ban
yarda da kwarewata domin mahaifina ya bani
labarin Sarkin yakin garinnan wanda ya rasu
46 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
wanda ake kira da suna HIzanu. Mahaifin nawa
ya gaya min cewa idan har ina son na sami
gagarumar jaraumtaka sai na sami irn horon da
Sadauki hizanu ya samu kuma babu mai kwatan
kwacin irin horon nasa face kai da ka kasance
dan uwansa, mahaifin nawa ya sanar da ni cewa
shi ya kori Macijiya Baurkul karsum a lokacin
da ta shgo birnin nan take kokarin ta hallaka
kowa.
Koda Shadilat tazo nan ajawabinta sai
idon Sarki ya ciko da kwalla nan take al'amarin
da ya sa jikin kowa yayi sanyi kenan a fadar,
Koda Yarima yaga Sarki ya sunkuyar da kansa
kasa har hawaye ya fara zubo masa sai shima
zuciyarsa ta karaya ya kama hannun Sarki ya
damke a alokacin das hi ma idanunsa sun ciko da
kwalla ya dubi shadilat wacce itama jikinta yayi
sanyi gaba daya ta kamu da nadamar tunowa da
Sarki dan uwansa, yace "yake Shadilat kyi sani
cewa kin famawa Mahafina tshon ciwon da har
abada bazai taba warkewa acikin zuciyarsa face
ya tafi inda dan uwansa ya tafi. Tabbas a yanzu
Sarki bazai iya bakı amsar akan alfarmar da kika
nema amma wata kila nan gaba idana zuciyarsa
tayi sanyi yayi bayani. Yanzu sai ku koma
47 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
uzuwa unguwarku, idan Sarki izinin ganinki zai
turo a kirawo ki, Koda jin haka sai Shadilat ta
dubi Yarima ta dan yi masa wani murmushi
wamda ya kasa fassara ma'anarsa a cikin
zuciyarsa, Ta ce nagode Allah da yazama Sarki
yana da dakamarka kuma ina fatan zaka taimaka
min akan alfarmar da nake nema ka janyo ra
ayin Sarki akan.bukatata.
Hakika jini jinine kamar yadda aka
siffantamin kamanin marigayi Sadauki Hizanu
sai naga babu mai kama dashi a birnin gaba daya
face kai, ina maiyi maka fatan ka zamo
gawurtattcen jarumi kamarsa, na barku lafiya.
Koda gama fadin hakan sai Shadilat
tayiwa sarki sallama cikin biyayya ta juya ta fice
dafa fadar gaba daya 'yn gudun hijira na take
mata baya ba tare da ta sake rufe fuskarta. Nan fa
jama'a suka rinka binta da kallo hart a fito daga
cikin gidan sarauta suka shiga garis, duk inda
suka gifta kallinta kawai akeyi maza da mata,
nan da nan labarinta ya bazu a ko ina acikin
birnin Baitul Haural harda kauyika.
Lokacin da Lushmaira taji labarin ai ga
wata kyakywar budurwa 'yar wani mahsahurin
attajiri wacce ta fita kyau ta bayyana acikin
48
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
birnin Baitul haural sai ta cika da tsannan
mamaki kuma ta kamu da tsananin kishi bata san
sa'adda tta mike tsaye ba zumbur ta kira wani
hadimin gidansu tace yaje ya ya dauko mata
doki,
Nan take ta shiga turakarta ta