Sarki ya zuba
idanu ya sa aka zuba dakarun tsaron ako ina
cikin wannan birnin ana mai tabbatar da tsaro
amma kuwa dake cikin wannan birnin bai san
dalilin da yasa aka sa wannan tsaro ba, dan
Sarki ku Sarki yaki bai sanar dashi wannan
dalili ba,
Da dansa Arfan ya tambayeshi dalili sai
yace akwai dalilin yin hakan idan abun ya
bayyana zaka gani" da wannan koya ya samu
kansa cikin shakkar zamansa ko ina acikin
kasar. A haka kwanaki ashirin day a Ansaru ya
furta cewa masifa zata fara kankama acikin
wannan kasa, dan haka sai tsaron yafi na
koyaushi kuma hankalin Sarki ya gaza
kwanciya gaba daya rana har akayi sallar
magriba babu abinda ya faru a wannan lokacin
sarki ya fara ganin cewa kawai Ansaru ya fad
wannan maganane dan ya tsaoratar da ni dan
35 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
haka sai hankalinsa ya fara kwanciya.
Misalin karfe goma na dare labari ya
isarwa Sarki cewa anzo cikin garinsa duk masu
gadin kofar shigowa an yakesu an fatattake
wasu wasu kuma sun sha da kyar.
Koda jin wannan batu sai hankalin sarki
ya tashi zumbur ya mike daga kan gadonsa na
mulki ya fito waje ya tsaya ya kuma umarce da
akawo masa dakarun da suka sha kyar,?
Nan da nan aka gabato dasu gaban Sarki
ya zuba musu idanu daga bisani sai ya dubi
daya daga cikinsu yace "yakai wannan
badakaren ko zaka iya sanar dani abinda ya
faru daku a halin kuna zaune abakin kofar
wannan birni namu"
Badakaren ya daga kai gami da
numfasawa yace "ranka ya dade kware zan iya
sanar da kai iya abinda ya faru damu a halinmu
na shiga cikin wannan hali, muna zaune kamar
yanda muka saba idan dare yayi mukan kunna
wuta dan mu ji dimi haka kuma muna hirarmu
36
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
tare da kula da aiyukanmu muna cikin hakan
kwatsam sai muka ga wani mahayi bisa doki
ya fito daga cikin gari fuskarsa arufe da wani
jan mayafi hannunsa rike da wata sharbebiyar
takobi koda yazu inda muke cikin mamakinmu
mu azatonmu ko wani dan aikine daga cikin
gari kawai sai ya sauka daga kan dokinsa ya
kuma rataye takobinsa ajikin dokinsa ya nufo
mu cikin wata iriyar guguwar bala'I domin a
yanda ya nufo mu mu a zatonmu bashi bane
iska c eta biyo ta bayansa ta kawo mana hari
sai kawai muka ji duka babu kaukautawa cikin
tsananin zafin nama saboda tsananin razana
babu iya daukar makamanmu ba sai muka
shiga kare kanmu wasunmu kuma suka ruga
suka tsallake katangu suka haure duk kuwa da
cewar katangar wannan birnin tafi gaban
mutun ya haureta amma sai gamu muna tsare
kama Katanga wanda sukayi kokarin kare
kansu kowa suna can sun samu raunika saboda
azabar da suka sha awajen wannan mahayin
37
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
dokin daga karshe kuma ya gargadesu da
cewar gobe idan ya dawo yaga dayasu to da
takobi zai yakemu kuma sai ya kasha
dukkaninmu, sun ce yana gama fadin hakan ya
koma yah aye kan dokinsa ya dawo cikin
wannan gari.
Koda Sarki yaji wannan al'amari sai ya
shiga cikin wani irn hali na damuwa yayi shiru
na dan tsawan lokaci daga bisa ni sai ya dago
kai ya ce ya dubi Sarkin yakin Asbaz yace
"gobe ka je ka zauna abakin wannan kofar
birnin kaida jama'arka sannan kayi dabarar da
zaka kamamin wannan mahayin dokin araye ba
a mace ba.kazo dashi izuwa cikin wannan
turakatawa da kaina zan hukantashi.
Koda Sarkin yaki Asbaz yaji wannan sai
yai gaisu ga Sarki ya kuma nufi kofar fita daga
cikin gidan.
Washe gari kowa alokacin da jama'a
suka kasance cikin cin kasuwancinsu anata
hada-hada kwatsam ba sai ganin wasu dawakai
38 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2 SAYDIАД ЯАДЯТ
akai guda hudu bassun shigo cikin kasuwa
acikin masifaffanngudu hannayensu dauke da
taköbil tsirara kai tsaye saijsuka jufin rumfunar
Sarkin garin suka ifara bari da kayan shaguwa
wanda: damaenlayiulguda no duk masarki
Mahaddad ne manrda nan suka tashi layin pikia
dam kankanini lokaci kasuwar ta rude hankulan
mutane syasadügunzumawakaltinka BHÍALBAİS
gami da iface iface, kafin kace kwabo luni an
korivnskowasndake arkasuwari sainswadannN
mahayan guda hudui bisa dawakai ana cikin
wannan abuner sairga wasu Dakarunan sa
dasvun arba'in bisa dawakai sunnufu sikiД
kasuwar asukwaned ridio ageb soad sala is
Koda wadannan mahayan suka
wadannan Dakaru sais u dukaisukadsaya kuma
sukais gyaration takobbansu 2 SURAI TIR
wadannan idakanu, koda eisuwar dakarun
suka bnufo su idaltiyarnsuw yakes28 ik
tsanánin fusata daya daga oikin Mahayan yayi
fitar burgu cikinsud cikin matsanencin gud
39 inGAM inse sisA'luhAbdul'Aziz Sani M/Gini OA
TURBAR GASKIYA -2
tamkar guguwa ya fara ragargazassu, idan kaga
yanda yake fada dasu kai kace basu hororwa
yake domin baya bari ya samu su kaifin
takobinsa sai dai kotar takobinsa baya bugunsu
a makasa sai dai dai duk fuskokinsu sun
wulakanta domin yayi musu munanan rauninka
duk yawansu sai suka zama na banza domin
dukkaninsu sai sukai wanwar a kasa daga mai
dafe kunci sai mai dafe kogu sai mai dafe kai
ko rike hannu, koda gama yi musu wannan
aika aika sai ya zaburi dokinsa saura suka rufa
masa baya cikin tashin kora suka bar gurin
dukkaninsu fukokinsu arufe suke da jan mayafi
bat suka 6ace daga cikin birnin aka nemesu
sama ko kasa aka rasa
Alokacin da Sarki yazo ya ga barnar da
akayi masa sai hankalinsa ya dugunzuma ainun
har wata kwalla ta fito masa daga cikin
idanuwansa, a wannan lokaci sai ga dansa
Arfan tare da hadimasa a baya suma sun shigo
cikin kasuwar, cike da bakin cikin faruwar
40
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
wannan al'amari, Arfan yana zuwa gaba
mahaifnsa sai yaga wannan kwalla da take
duga daga idanun mahaifinsa nan da nan
hankalinsa ya tashi ya dubi mahaifinsa yace
"ya abbana ya kake zargi da yin wannan
mummunan aiki ga dukiyarka wa kake zargi da
6arnatar da wasu daga cikin dakarun ka, lallai
nayi imani da Allah day a halicceni idan kayi
mini izinin neman wannan la'antaccen
makiyan naka sai na kamo maka shi har
gabanka aduk irin yanayin da kake muradi ya
mhaifina kayi mini lamuni daga wannan sa'ili
na tafi izuwa neman wannan kaskantaccen
bawanka ko amace ko araye,
Sarki Muhadda ya daga da kai ya dubi
dan nasa kana ya sunkuyar da kansa kasa,
tabbas yasan cewa yarima Arfan zai iya duk
yanda zai yi ya gano wanda yake yin wannan
aika aikar amma sai dai da ranar da yaga cewar
amininsa ne kuma shakikinsane da yin wannan
dan yan aiki to ya tabbata ba zai iya kama su
41 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
ba kuma koda ya gano shi to babu makawa
rabuwarsa da dan nasa ya zo domin Ansaru
yana da hujjujin da zaiyi amfani dasu dan
yajenye dansa yabi shi su hada kai domin sanin
cewa shakuwar da ke tsakanin Arfan da Ansaru
bata tsakanin sa dashi koda ma akwai haka
azcuiyarsa yasan cewar dan nasa ma yana
adawa da irn mulkin da yake gudanarwa
akasarsa na tilastawa da yin dole ga bin
addinin musulunci wanda tun shekaru masu
yawa malamai masu ilimin suke son ganin sun
kure wannan 6arna daga kasar sa amma sun
kasa, dan haka sai ya kara dagowa akaro na
biyu ya dubi Arfan yace
"Ka kwantar da hankalinka ya kai dana
abin muradina ba kada ka damu kanka da
wannan aikin kafi karfinsa bazai yiwu na saka
acikinsa ba tunda ba yaki bane da zamu tunkari
rundunar mayaka miliyan dubu dan haka ka
kwantar da hankalinka Sarki yaki ya zuba
matakan tsaro dan binki tamana wadanda suke
42
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
mana mummunan ta addanci,
Koda Sarki yazo na azancensa sai yarima
Arfan ya dago ya dubi sarki cikin alamun
gamsuwa kana y ace " ya abbana ya maganar
binkicin da akiyi gami da bata dan uwa Ansaru
sanin kankane idan har rayuwa taa ci gaba da
tafiya batare da Ansaru akusa dani ba tabbas
zan iya rasa rayuwata dan haka ina son ka bar
ni nayi tattaki izuwa makobtaka wannan yanki
dan gano inda yake,
Koda Sarki yaji wannan batu daga bakin
dan sa sai yayi tunanin mai zurfi daga bisani ya
dago kai ya ce nayi maka izini ka tafi har
tsawan kwanaki goma neman Dan uwanka
Arsaru kuma ka tafi nan da kwanaki uku masu
zuwa, ba wani tunanin sarki yayi bay a bar
yarima ya tafi neman Arsaru said an kawai
yasan cewa Ansaru yana cikin kasar nan yayi
hakane domin yarima yayi nesa dashi dan
gudun kada watarana Arfan su hadu da dan
uwan nasa tabbas duk alokacin da suka hadu
43
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
sai ya shaidashi musamman idan suka gaba da
gaba da fara yin Artabu wanda kuma indai
Arfan yana cikin birnin watarana zai je kai
dauki ga gurin da yaji sanarwar Ansaru ya kai
farmaki dan haka yayi wannan dabara yasan
cewar kafin cikin kwanaki goma sha uku sai an
ZO
י Ansaru" ma da
Da wannan Sarki ya koma gida tare da
zugarsa shi ma Yarima ya tafi gida cikin
takaicin wannan mummunan abinda yake
faruwa amma sai ya bari azuciyarsa kafin ya
bar birninsu sai ya fara dan yin bincike akan
wannan lamari.
Washe gari tun sassafe labara yaje wa
Sarki cewar an sace wani babban limamin
garin sannan an rushe wani gidan gonarsa gaba
daya tare da tafiya da amfanin gidan gonar
duka, sannnan awannan karan ansanar das hi
cewar wadanda sukayi wannan 6arnar suna da
yawan gaske dan akalla zasu kai sama da
mutun arba'in sannan kuma suna rike da tutar
44
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
musulunci a hannunsu basa kisa basa tabа
kayan kowa face kayan da wannan masarauta
ta tanadar.
Lokacin da Sarki Muhadud yaji wannan
batu sai da yayi shiru na wasu lukuta sannan ya
dawo daga duniyar tunaninsa ya dubi dakarun
da suka kawo masa wannan labara y ace "ku je
ku sanar da Sarki yaki Asbaz ina nemanshi
yanzu kuma ya sameni anan fada kafin na tafi
cikin gida ya kuma waigawa gefensa ya ce da
Wazirinsa da galidima koma idan da wanda
yake da uzuri yanzu ya kamata ace yaje yayi
domin dole zamuyi zama na musamman mu
hudu galadima waziri tare da ni Da Sarkin
yaki,
Koda suka ji wannan sai suka jinjina
atare suka ce da sarki babu wani uziri da muke
dashi ayanzu face wanda zai tabbata anan dan
haka aje akera Sarkin yakin muna nan muna
jira.
45
Suna nan zaman jiran Sarkin yaki sai ga
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Badakaren da Sarkin ya aika tare da wasu
manyan yara Sarkin yaki sun s shigo cikin
fadar hankalinsu tashe,
Koda isowarsu sai suka zube suka bada
gaisuwa ga Sarki suka kuma mike zaune daya
daga cikinsu kamar yayi kuka saboda tsabar
takaici ya dubi sarki yace "ya shugabana kayi
sani cewa ayanzu haka Sarki yaki bamu san
inda yake domin a dasu da safiyar yau muna
zaune a bakin kofar wannan gari da tabbatar da
tsaro kofar shigowa cikin wannan birnin sai ga
mahaya dawakai daga cikin garin nan
fuskokinsu arufe babu inda kake gani ajikinsu
face idanuwansu sun kai kimanin arba 'in da
doriya, koda muka gansu duk sai muka
tabbatar da cewar wadannan makiya namu ne
wanda suke ta fama 6arnatar mana da
dukiyoyinmu suka kawo mana farmaki.
Koda shugabanmu sarkin yaki yaga
wannan abu sai ya zare takobi shi kadai ya
kuma fito gabanmu ya tsaya, bisa mamakinmu
46
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
sai wani daga cikinwadan nan mahaya shima
ya fito daga cikinsu ya shiga gabansu ya tsaya
kekam, tamkar gunki yana ruke da takobi
wannan abu shi ya fusata Sarikin yaki yayi
gurnaninsa na mazaje yace da wannan
mahayin,
Kayi gagganci babban da ka baiyana
agabana ayanzu domin na tabbata duk burin da
kake dauke dashi daga wannan rana yak au
domin a yanzu ne zan yake ka kai da sauran
mabiyanka kuma na tusa kiyarka izuwa gidan
Sarki dan cikin umarninsa"
Koda Sarkin Yaki yazo nan azancensa
sai wannan mahayin dokin ya tuntsire da
dariya, daga bisa kuma ya turbune fuska yace
"daga yaune zan cika kaso biyu na daga cikin
abinda na sa agaba na maid a baki daya
jarumar garin nan su zami suna tare da ni kuma
babu gudu babu ja da baya tun da ayanzu nayi
nasara mallakar jarumai sama da arba'in acikin
wannan tafiya tawa tabbas a yau zan tafi da kai
47 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
bisa kafadata bayan na sagarmaka da duk wata
mamaro sannan na tafi da kai, Na tabbata daga
wannan rana kai ma zaka zama makiyin sarki
kamar yadda 'yan dukkanin wadanan mutane
suka zama makiyansa badan kuma basa sanshi
ba sai dan kawai rikon na addinin gaskiya da
son abi hanyar gaskiya a acikin wannan
birnin".
Koda yazo nan azancensa sai Sarki yaki
yayi kururuwa yayi kan wannan mahayin cikin
tsannanin fusata nan suka hau sara da suka
babu kakkautawa nan muka zuba musu idanu
muna kallo wannan artabun wanda yasa muka
manta da cewar wannan fa makiyane ga sarki
wanda kuma ake nema dan ayi masa hukunci
sai muka shiga kauyenci ganin im yanda yake
yaki tamkar jarumi da yafi ko wane jarumi
jarumta aduniya duk da cewar Sarkin yaki ya
tbuka abin azo agani sai ya zamana ya zama
rago domin yanda wannan mahayi yake
yakarsa kai kace yana yaki ne da dabbar ta
48 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
yake son yaga ta samu sannan ya dauketa ya
yanka ta said a ya zamana ya daga Sarkin yaki
sau uku yana bugawa da kasa kuma wani abin
mamaki tun da aka fara fadan sai ya ajiye.
tabkobinsa, da aka dauke dakika goma ana
wannan fadan bayan Sarkin yaki yasha kayi sai
uku sai muka yunkura domin mu shiga mu
kwace sarkin yaki domin ya galabaita ainun,
sai saurn wadannan dakarun suka rufar mana
babu ji babu gani suna duka itakaice maka
wadannan mahayan basu bar wannan guriba
har sai suka ga mun gudu da kafarmu wasu
kuma daga cikinmu suka kamasu suka tafi dasu
acikinsu hard a Sarkin yaki wanda ya kasance
akan kafadar wannan shugaban mahayan mai
rufaffiyar fuska.
Koda wannan mahayin yazo nan
labarinsa sai sarkin Muhaddun yayi wani irn
iho mai firgitarwa hankalin gaba daya mutanan
da suke gurin ya tashi ainun daga nan kuma sai
Sarki ya dubi wadanan dakaru yayi musu
49 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
umarni dasu tashi su tafi kuma su sanar da
kowa kada wanda ya zo fada a halin yanzu
suka tashi dan bin umarninsa suka bar wannan
guri koda suka tashi sai ya maida kansa ga
Waziri da kuma galadima yace "tashin hankali
da gaskie ya tunkaro wannan kasa tamu kuma
duk halin da muke cikin a yanzu kun ji
dalilinsa ayanzu sai dai ina so na kara muku
baya ni akan wanda yake mana wannan mugun
ta annacin wanda ba kowa bane face Sadauki
Ansaru wanda kafin lokacin sai da ya sanar
dani cewar idan har ban janye wannan
munanan aiyuka da nake yi acikin kasata ba
lallai sai masifa ta rufe mu mun rasa inda zamu
tsira daga dukkan alamu haka ta fara bayyana
tun gashí ya tafi da sarkin yaki kuma sanin
kanku ne a yanzu idan ba Ansaru ba ko dana
Arfan ko shi sarkin yaki Azbas bamu da wasu
Sadaukai da ake shayinsu acikin wannan kasa
domin ni yanzu tsufa yazo mini bani da wani
kuzari d tabbata
50
azan iya yaki dashi dan na
Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Ansaru zai iya bani kunya wanda zai iya yaki
dashi shi ne Arfan har ya iya samun nasara
kanshi amma kuma bana son suyi gaba da gaba
dan na tabbata idan ya jashi shima shi kenan
sai dai mu hakura mubishi kamar yanda yake
so muyi asara irin makodan dukiyar da kasar
Assasunnufur suke bamu na tallafi wato kasar
yahudawa wanda da wannan dukiyane kadai
muka tara dukiyar da aduk wannan nahiyar
babu wanda yake da mallakin koda kaso daya
daga cikin kasu goma wannan sirrin mune mu
uku nan babu wanda ya sani dan haka sai mu
nemi mafuta yanda zamu magance wannan
matsala dan haka na taraku anan da naso asanar
da Sarkin yaki ne dan mu kara samun karowa
dan tsaro yafi yawa acikin lamuran nan amma
tunda haka ta faru dashi sai muyi saurin yanke
shawara atsakaninmu
Koda yazo nan azancensa sai duk su
dukan sukayi shiru na dan lokaci, Galadima ya
gyaran murya yace "wannnan abu shi ake kira
51 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
sarkakiya kuma dole bazamu ci gaba da
rayuwar da ta bakunce mu ba kuma baza mu
yarda kasar Assasunnurfur su janye tallafin da
suke bamu ba illa kawai mu shirya makarkashi
ga Shi Sadauki Ansaru na nuna cewa mun
janye wannan dakokin da ake ammafani dasu
acikin wannan Kasa munan cewar yafi mu
gaskiya daga wannan lokaci sai musa akamashi
bayan ya bayyana kanshi idan kun aminta da
wannan shawara to babu shakka zamu iya
cimma nasara idan kuma akwai wanda yake da
wanda tafi wannan sai ya sanar da ita mu ji".
Waziri yayi murmushi yace hakika ka
kawo shawara amma sai dai ina son ku sani
cewar a halin yanzu Ansaru ba zai yarda ya
sake jiki damu koda an kamashi an daure muka
dawo da wannan dokoki za akara zamu 'yan
tawaye daga cikin wannan birnin fiye da na
yanzu aciki ina kyutata zato Yarima Arfan ya
shiga ciki kuma sai sun futo da Ansaru daga
cikin wannan kurkuku da zamu kaishi kunga
52 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
kenan idan aka samu wannan rarrabuwar zai
kasance za ayi yaki ne mu dasu abinda nake so
muyi shi ne mu ci gaba da da awar cewar duk
wannan dokoki daga da suke faru daga fadar
Allah s(S.A.T) suke sannan mu je izuwa
babban gidan littatfan Allah da manzonsa
acikin wannan Kasa tamu mu konesu mu yi
tattaki izuwa Kasar Assasnunufuf don su juwar
da zancinkan Allah na wannan littafi ya dawo
izuwa iri daya ga littattafan mu idan yaso sai
mu mu nemi taimakon Dakarun yaki daga
kasashen da suka daure mana gindi dan su zo
sukawo mana tallafi mu murkoshe wannan
Sadaukin yaron kun ga she kenan koda bayan
ranmu a haka za aci gaba da tafiya batare da
asirinmu ya tuno ba,
Koda
a Sarki Abu zaiyan yazo nan
labarinsa sai yayi kabbara sau uku jama'ar
dake gurin sai suma suka kaure da kabbara
sannań aka ci gaba da ti da wadannan
shuwagabannin hawaye fce face afuskarsa ya
53 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
ci gaba da bada labarin
Koda suka ji wannan shawara sai sukayi
imani da ita suka kuma yarda sannan waziri ya
kara da cewar yana da kyau a yau Ka shirya
danka ya bar wannan garin dan mu yi shirin
cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.
Sarki yace ai dama munyi dashi ayau zai
bar wannan gari domin tafiya neman Ansaru
dan ban sanar dashi ba abinda ya faru
tsakaninmu ba kun ga kenan faduwa tazo dai
dai da zama. Da wammam wadammma
shugabanni suka tashi taga wannan taron Sarki
yaje gida ya sukayi sallama da dansa Arfan ya
hadashi da dakarun 'yan rakiya mutun ashirn
da biyu
Lokacin da Arfan ya nufi hanyar fita
daga cikin birninsu sai ya yi sha awar ya shiga
cikin kasuwa ya danyi siyayya kai tsaye sai
yayiwa 'yan rakiya Magana akan su je kasuwa
dan haka sai suka huya suka nufi kasuuwar
garin da zuwansu sai Arfan ya shiga siyayyan
54 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
abubuwan da yake da bukata wanda yake son
ya tafi dashi yana cikin wannan siyayyane sai
ya hange Huwailat ta nufoshi da kunshi
kayanta a hannu idanuwanta na zubar da
hawaye,
Ita dai Huwailat wata kyakkyawar
budurwa ce wanda suka taso tun yarinta cikin
tsananin son juna ta da Ansaru dalili kuwa tare
da Ansaru sukay zaman maraici agidan Sarki
dukkaninsu basu da iyaye Arfan shi yake
taimaka musu da kuma mahaifinsa wato sarki
Muhadudu tun za ilin da ta nemi Ansaru ta rasa
hankalinta ya tashi ainun dan haka kullum dare
da rana sai ta zubar da hawaye n abkin cikin
rabowar ta Ansaru kuma ta ji labarin cewa
yarima Arfan zai je dan nemo shi wannan
daliline yasa ta biyo bayanshi dan yi masa
rakiya.
Koda ta karaso inda Arfan yake sai ta
dubeshi ta yi masa gaisu ta kuma ce dashi "ya
babban abokin amini'na hakika ban ziya jure
55 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
rashin ganinka ko ANsaru acikin wannan kasa
ba domin kai daya ne kake sharemin hawayen
rabowata dashi dan haka na yanke shawara
nabi bayanka dan na tayaka neman masoyina
aduk inda yake kuma komai ruwa komai iska,
ina mai neman yardarka idan kwa har kaki
amincemi na tabbata zuciyata baza ta ci gaba
da zama jiranku ba dole ne nima na tafi
nemansa a duk inda yake.
Har Yarima ya bude baki zai yi mata
Magana kenan sai kawai ya hango taron
jama'a daga nesa suna ta faman rubdugu aguri
daya koda ganin wannan abun sai ya tura
dakarunsa dan gane masa abinda yake faruwa.
Batare da 6ata lokaci dakaru biyu suka ji gurin
suka karbi abinda jama'a ke dubawa ba komai
bane face wani Sako arubuce, koda ganin haka
sai suka garzayo suka kawowa yarima wanan
takarda.
Yarima ya karba ya fara karantawa afili
kowa yana ji abin dake kunshi cikinta,
56 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
Jama'a duk wanda yake jinkan wadanda
aka kashe ta hanyar mummuna kisa wanda
ubangijin mu bai bada umarnin hakaba to
muna masu yi masa maraba da ya shirya dan
binmu aduk inda yaga munzo mun kawo har
acikin wannnan birnin dan kifar da wannan
masarauta da take ci mana kasha kuma take
ammafani da son zuciya ta kore zamanzancen
Allah ta kawo nata.
Aduk inda ku ga mahayan doki masu
rufaffiyar fuska to ko garzayo ku bi sahunmu
dan hada karfi da karfe muga bayan
shugabanmu.
Yarima yaji gabansa ya fadi lokacin da
yazo karshen wannan karatun wasikaya dubi
sauran dakarun dake gurin da sauran jama'ar
da suke wajen sai faman gyada kai suke suna
jin dadin batu wannan wasikar dan haka sai
hankalinsa ya tashi tabbas ya san cewar
mahaifinsa bayayin aiki da ilimi amma bai
kamata ace ta haka za abiyo masa bay a kamata
57 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
ace an samu gagarumi zama da manyan
malamai, dabadan yayi sallama da mahaifnsa
ba kuma yana kan hanya ne ta neman dan
uwansa da sai yace sai ya zauna yaga bayan
wannan al'amari amma tabbas yasan idan yaje
ya samu Ansaru cikin saukin lamari sai
ANsaru zai kawao karshen wannan abu domin
sanin da yayi masa na da durcewa akan abinda
ya zama hakkin Allah ne da al'umma dan haka
sai ya dubi Huwaila yace "dole na tafi dake tun
da kin shirya sai ki bi bayanmu nan ya
nandade takadar ya sata aljihunsa kuma yayi
gargadi akan kada wanda ya sake ya kara yawo
da zancen daganan suka dausa suka ci gaba da
tafiya har suka zo tsakiyar gari.
Alokacin da suka zo tsakiyar garine sai
suka ga dandazon jama'a bakin gurin da ake
yanke hukunci ga wanda suka yi laifi ga sarki
wani katon mutun yana shirin zai fille ma
wannan mutun kais a boda laifin day a aikata
na satar wa wata mata abinci alokacin da
58 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
yunwa ta koreshi.
Koda ganin wannan al'amarin sai yarima
ya tsaya yana kallon cike da tausayawa, kamar
walkiya wani farin doki ya bayyana asukwane
babu shiri yazo gaban wannan mahaunin
wanda zai yaanke kan wannan mai laifin sai
wannann Mahayin ya dokin makoshin wannan
Mahaunin sannan ya dauke wannan mai laifin
ya gudu dashi akan dokin koda ganin haka sai
Yarima shi ma yayi sauri ya hau yabi bayan
wannan mahayin doki nan da nan suka kasa
tsre cikin tsannain gudu tamkar walkiyace take
giftawa
Adai dai nan Sarki ya dubi taron jama'a
yace lallai mu shagala da wannan labarin har
gari ya waye dan haka sai dai mu kara hakuri
har zuwa filin wannan yaki idan mun samu
sarari sai mu karasahi na san duk da rashin
karsashinsa da yawanku kun tsinci abubuwa da
yawa acikin wannan labara domin ayanzu mun
gane cewar duk wani musulmi wanda yakc
59 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
aikata aiyuka munana wanda Allah bai
umarceshi da aikatawa to bamu shakka shi
kansa bayahude ne kuma bayahuuc basa kunar
musulunci sannan kuyi koyi ga yanda mutun
daya yake kokarin ganin bayan taron sarakai
marasa tsoron Allah, dan haka anan gaba zaku
ga yanda aminci tsakanin Yarima Rfan da
Ansaru sai mun.
Alokacin da Sarki yakai dubansa izuwa
kowane rukuni na rundunoninsa sun hallara sai
ya kai dubansa ga Likitansa wanda yana kusa
dashi yace "yakai amintaccen likitane yaya
akai da na gaya maka cewar kada ka taho da
sama da mutane duba dari biyu naga kuma
kazoo da ninkinsu? Ko da jin wannan tambaya
sai Zauwad ya rissina cikin biyaya y ace
"tunani nayi naga cewar wannan yaki da zamu
je yakine irn wanda bamu taba yi ba, idan
bamu da isassun likitoci wadanda zasu rinka
duba dakarunmu zamu wayi gari babu sauran
60 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
dakarun a tsaye wadanda zasu fuskanci abokan
gaba. Koda jin wannan batu sajikin Sarkin yayi
sanyi amma day a sake duban tawagar yaga
tarin guzurin da aka taho da ita wanda ya kusa
kai wa adadin. na dakarunsa sai ya cika da
mamaki har ya budi baki zai yi Magana sai
yarima yace "yakai Likita Zauwad hakika
kasamu taimakon guziri da yawa daga wajen
jama'ar gari,
Koda jin haka sai yace "kwarai kowa ai
jama'ar gari suna kwadayin ladan da zasu
samune a wannan jahadi da zamuyi. Koda jinw
annan batu sai Sarki ya samu nutsuwa a cikin
zuciyarsa, Alokacin ne yarima ya shiga cikin
tawagar likita Zauwad ya fara kallon
mutanensa daya bayan daya kuma takan maza
ya fara. A wanan lokaci Shadilat da Lushmairat
ne cikin sahun likitoci mata kuma kowacce ta
rufe jikinta gaba daya da fuskarta idanunsu
kawai ake gani amma dudda haka sai
zuciyoyinsu suka kama dakan uku-uku suka
61 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
kama sunkuyar da kai kasa don kada yarima ya
shaidasu, bayan yarima y agama duba mazan
sai ya dawo kan layin matan, su Shadilat akan
sawun gaba daga gaba kawai sai suka ga
yarima ya wucesu baiyi ba yana mai ci gaba da
duban fuskokin matan wasu ma idan yazo
kansu sai ya bukaci su bude idonsu ya gani
sannan yayi gaba. Al'amarin da yasa su
Shadilat suka sami kwanciyar hankali kenan da
suka ga an wucesu ba ace dasu su bude
fuskokinsu ba.
Bayan yarima yaje kan mace ta karshe
dake kan layi sai kuma ya dawo farkon layin
ya tsaya agaban Shadilat y ace da ita dago da
fuskarki na gani, zuciyar tan a dakan uku uku
da dago kai ta dubeshi itakuwa Lushmaira tana
baya ta sunkuyar da kanta kasa har jikinta ma
ya kasa tsuma domin t agama Saddakarwa
asirinsu y agama tunowa
i aLokacin da Shadilat taď ago dakanta
sukai Yarima yayi arba da dararan idanunta
62 Abdul'Aziz Sani M/Gini
TURBAR GASKIYA -2
masu tsananin haske sai zuciyarsa ta buga da
karfi, har ya budi baki zai ce da ita bude
fuskarki ya gani sai Sarki ya kwala masa kira,
acikin hanzari yarima ya juya ya ruga izuwa
wajen mahaifinsa da zuwansa sai Sarki ya
dubeshi yace lokacin tafiya yayi imaza ka hau
doki mu tafi,
Batare da gardamar komai ba Yarima
yah aye dokinsa suk jera shi da sarki suka
wuce gaban gaba dayan dakarun yakin. Kaji
mazajen kwarai wadanda basa tsoron yaki bare
mutuwa kuma basa kwadayin duniya tunda
gashi sun wuce kan gaba suna jagorantar
al'ummars sun sallama rayuwarsu don daukaka
addinin Allah sabanin su Sarki madhan da