An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
TurbarGaskya
ABDUL'AZIZ SANI
MADAKIN GINI
TURBAR GASKIYA
TAFIYA CE MAI dauke da yanayi Sgwanin ban sha'awa domin Babu
sanyi kuma babu zafi, mutane sun fito
daga cikin gidajensu sun fara aiwatar da
harkokin kasuwancinsu na yau da kullum kamar
yanda aka saba acikin birnin mai tarin al'umma
ma'abota addinin Musulunci.
kowa ka gani a nutse yaka babu ashararai
a ko ina kima babu gdajen da ake aikata
masha'a a ko ina, baza ka taba ganin mata da
maza ba aguri daya ba kuma indai mace ta kai
minzalin balaga zaka gat a rufe ko ina na jikinta
sai dai kawai fuskarta da tafikan hannayenta da
Kafafunta a waje.
Kaso tamanin na lukotan wannan mutanen
wannan birni yana tafiya ne awajen hidimar
addini kamar nafilfilo ama sallatai karanta alkur
ani da wa'azi a ko ina har kasuwanci da wararen
sana'o'i
Babab abin da zai fi burgeka mutun
dangane da rayuwar mutanen wannan birnin mai
albarka shi ne yadda zaman lafiya ya yawaita
atsakainsu sannan babu babanci tsakanin mai
mulki da talaka, malami da attajiri, kowa daidai
yake da kowa kuma komai girman mutun idan
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ya ketare haddin Allah ko ya karya doka sai anyi
masahukunci kamar yanda addini ya tanadar.
wannan birnin ya bunkasa da harkokn
kasuwanci da ci gaba na kere kere, gamio da
ma;adanan kasa kuma yana karkashin jagoranci
wani adali Sarki mai suna Abu zaiyan.
Abu zaiyan ya kasance gawurtaccen
Sadauki gwarzan mayaki mai tarwatsa maza
afilin daga, amma atarihin rayuwarsa sau uku
kawai ya 6a yin yaki duk da cewar ya shekara
arba'in akan karagar mulki.
Ykuna ukun da Sarkin Abu zaiyan ya taba
yi yayi sune bisa dole da wadansu Kasashen
kafirai dake makobtaka dashi kuma sune suka
takaleshi, Abin ya samu asali tun a farkon hawan
sarautarsa bayan rasuwar Mahafinsa wanda ya
gaji sarauta awajns.
Shi dai wannan birnin na Abu zaiyan ana
kiransa da suna Baitul Haural kuma duk
Kasashen dake zagaye dashi kasashen na kafirai
ne ma'abota tsafi da bautar gumaka, rana, da
sauransu.
Ko kadan mutanan Baiti Haural basa zuwa
tallan addininsu izuwa sauran Kasashen amma
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
kuma a hankali mutanan sauran Kasashen kafiran
suna zuwa har cikin wannan kasa dan karbar
addin Islan ba koma bane ya janyo haka face
sha'awar yanda suka ga mutaneb birnin suke
tafiyar da rayuwarsu bisa jin dadi, kwanciyar
hankali da nutsawa akan TURBAR GASKIYA.
Lokacin da sauran Kasashen suka ga
hankalin mutanensu suna bijirewa addininsu har
ma ana shigo da addinin musulunci 'cikin
Kasashen a aboye ana yada su sai suka dauki
mataki mai tsauri yazamana cewa duk wanda aka
kama yana addinin musulunci sai an kasha shi ko
kuma akwace duk abin day a mallaka,gidansa da
dukiyarsa hatta iyayalinsa sai an maishe su bayi,
NEWь no
bnKoda ga nin irin wannan barna sai
mutanan da suka musulunta daga cikin wadansu
birane uku da ake kira HAUZUBA, DAKFUL,
DA HASNAM suka dingayan kaura cikin dare
suna koma cikin birnin Baitu haural.
nKafin a ankar a 'yan gudan hijara sama da
miliyan bakwai sun gudu birnin Baitul Haural
kuma da yawansu manyan mutane ne awadancan Biraneа 2
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
Wasu mashahuwar attajirai ne wasu kuma
manyan manomane dam asana ilimin sarrafa ma
adanan kasa.
Lokacin da aka tara wadannan 'yan
gudun hijira afadar Sarki Abu zaiyan sai ya
karbesu hannu bibbiyu kuma nan take yasa aka
raba musa gidaje da gonaki kyauta domin su
zauna su fara sabuwar rayuwa, Aikuwa cikin
wata daya jal da zuwan wadannan 'yan gudan
hijira sai arziki birnin Baitu Haural ya kara
bunkasa ninkin ba ninkin yana ninka na da
yazama cwa agaba daya nahiyar ma babu wata
kasuwa maı girman da kao arziki sama da
kasuwa Birnin Baitul Haural kasuwannin dake
cikin birnia hizub, Dakful, da Hisnam kowa duk
sai suka mutu, baki suka daina zuwa, arzikinsu
ya raunan kuma talauci ya yawaita.
Al'amarin day a dugunzuma hankalin
sarakunan wadannan kasashe uku kenan, Koda
suka yi bincike suka gano cewar wannan masifa
da ta samesu a sanadiyar hijirar da jama'arsu
sukayi ne suka koma birinin Baitul Haural sai
wadannan sarakuna uku suka shirya taron
gaggawaa birinin Haizuba inda Sarki Madihar.
yake mulki.
7
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
Sarki Madhan na Birnin Haizub ya dubi
sarki Tarmas na birnin Dakful da Sarki Husaka
na Birnin Hasnam ya ce "yak u manyan
abokaina kun sani cewa muna cikin masifa da
tashin hankali bisa yadda tattalin arzikin
Kasashen nan namu uku ya lalace muka fada
cikin fari yunwa, da talauci kuma duk wannan
abuu ya samu ne sakamakon attajiranmu da
kwarrarun masana sana'o'in niu duk snyi hijira
sun koma birnin baitul Haural da zama kuma
sun karbe addinin mutanan can, nasara daya
muka samu ta shafe wannan addinin acikin
biranenmu to amma fa mun kasha muciji ne
bamu sare kanshi badomin na sado da bokana
ajiya yayi bincike ya gano cewa idan har ba
bamu shafe birnin Baitu haural ba nan gaba sai
sun sun mallake duk kasashinnahiyar nan gaba
daya sun Kone allolinmu da muke bautawasun
kafa adddininusu yanda har abada baza akara yin
tsafi ba da wani addinin daban awannan Nahiya
sai nasu!
Shin haka zamu zuba ido muna ji muna
gani har mukai ga wannan lokaci, ni yanzu
babban abin da bakin cikina ma shi ne dan
uwana da muke uwa daya uba daya kuma
8
trve sJ ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
attajirin da duk nahiyar nan babu kamarsa ta
.fannin dukiya, Abu shadalat ma so yake ya koma
Birnin Bautl hural amma na mafa masa matakan
tsaro na hana shi zuwa ko ina,yana fakewa da
cewar kasuwanci zashi yayiamma ni nasan cewa
so yake ya krbi addinin mutanan birnin Baitul
haural, yanzu dai mecece shawararku? Mai ya
kamata da muyi dan mu ma gance
wannanmatsala?
Kodda Sarki Madhan yazi nan aazancensa
sai Sarki Tarmas ya numfasa y ace ni aganina
babu wani abu day a kamata muyi face mu hada
runduna ta mayaka, ina nufin mu hada karfi da
karfi na mayakanmu mu kaiwa birin baitul
Haural harin mamayar BAZATO,cikin dare mu
kama Sarki Abu zaiyan muyi masa kisan gilla
agaban mutanensa, daga wannan rana duk wanda
ya sake yin addinin nasu mu kasheshi muyi
musu dole su koma irin addininmu na bautar
gumaka, Duwtsu, Rana, da sauransu ka ga kenan
sai mu raba birnin nasu kasu uku kowannanemu
sai ya yagi rabonsa kun ga kenan mu jifi tsuntsu
biyu da hoge daya wato mun kare addinimu da
Kasarmu kuma mun dawo da tattalin arzikinmu
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA Yayin da Sarki Tarmas na birnin Dakful
yazo nan azancensa sai Sarki Madhan yayi ajiyar zuciya sannan yace hakika kazoo da shawara mafi alkairi agaremu to amma menen tabbacinka
cewar zamu iya sami nasarar yaki akan wadannan mutanen wadanda tsawan shekaada
shekaro tun kafin a haifemu bamu taba ganin iyayenmu da kakannunmu sunyi yunkurin yakarsu ba kuma ba musan dalilin ba,? Bamu
san karfin mayakansu batunda ba ataba yin yaki da suba,
st staask Sarki Tarmas ya ce "Kodai ba musan Karfinsu ba amma dai kasan Sarkin yawa yafi Sarkin Karfi indai ni na kao tawa rundunar kaida
Sarki Husaka kuka kao nakuku rundunonin muka
hada rundanar kare dangi ai dole ne mu gama
dasu, Koda jin haka sai sarki Madhan ya sake
yin ajiyar zuciya akaro na biyussannan ya dubi
Sarki Husakaaace и ai küme mecece
shawararkausm sq anai uziwp.sleg
Sarki Husaka ya gyran murya yace ni
atawa shawarar ba harin sumame ya kamata mu
fara kai musu ba, kamata yayi mu rubuta wasika
mu aikawa da Sarki Abu zaiyan muyi masa
gargadi akan cewa yayi gaggawar bamu
1012 JUDBAABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
mutanenmu gaba dayensu wadanda suka hijira
suka koma birninsakuma ya hadosu da duk
dukiyar da suka mallaka in ba hakaba za mu zo
mu yake shi har gida mu karbesu da karfin tsiya,
ina tabbatar muku da cewar Sarki Abu zaiyan
mutune wanda ko kadan baya son tashin hankali
kuma yana son kasarsa da jama'arsa sun kasance
acikin nutsawa da wadata, kun sani cewa indai
za ayi wannan yakiwanda baa san ranar daina shi
ba sai jama'ar tasa da yawa sun rasa rayuwarsu
da dukiyarsu kuma sai kasar ta shiga cikin fari
da talauci,
Sa'adda Sarki Husaka yazo nan a
bayaninsa sai Sarkin madahan da sarki Tarmas
suka kamu da tsananin farin ciki cikin hadin
baki suka ce tabbas kazo da shawara da ta kore
ta farko. Nan take aka rubuta wasika aka tashi
manzo ya tafi izuwa birnin Baitul Harwal.
Acan birnin Baitul Haural, bayan anyi asuba
amasallacin anyi aaddu'a kowa ya waste sai
Sarki Abu zaiyan ya shiga cikin gidansa domin
yaje ya zauna a aharabar gidansa inda ya saba
zama dan yin lazimin har izuwa lokacin da rana
ta fara fitowa,
11
KOda Sarki yaje inda zai je ya zauna sai
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ya jiyo takun tafiya acan bayan bargar dawakain
gidan kuma ya dinga jin karar haduwar takubba
alamar cewa mutun biyunie ke yaki. Arude
kuma cikin mutukar mamaki Sarki ya karasa da
hanzari izuwa wajen yana zuwa yaga ashe dansa
ne YarimaZaiyan da abokinsa Safwan suke
wasa jini har Sarki ya bude baki zaiyi musu
Magana sai ya fasa ya samu guri ya rakube inda
basa hangoshi yaci gaba dakallonsu cikin murna
sakamakon ganin gagarumar bajinta da Yarima
Zaiyan yake yi, kaafin Safwan ya kawowa
Zaiyan hari guda daya Zaiyan ya kaima sa goma
saboda tsananin tsafin namaduk da cewar shima
Safwam ya kasance Sadaukin gaskė kuma yafi
Zaiyan cika ido murdewa da girma amma sai
gashi Zaiyan din yana daka mada gumba a
hannun, shi kansa Sarki Zaiyan lokacin da yaga
Yarima yana yin iri n wannan gagarumar bajinta
sai ya cika da tsananin mamaki domin bai taba
sanin cewa yarima yana da irin wannan
jarumtaka ba, nan take ya aiyana aransa cewar
sai ya jarraba tasa jarumtakar akan ta yarima
domin ya banbance tsakanin aya da tsakowahaka
dai Sarki ya ci gaba da kallon gumurzu yarima
Zaiyan da abokinsa Safwan ba tare da sun sani
12
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ba har Zaiyan yashammaci Safwan ya doki
hannunsa takobinsa ta fadi kasa kafin Safwan ya
juya da dauki takobin tasa tuni Zaiyan ya doki
kafafunsa cikin bakinsa zafin nama, yai
katantanwa asama ya baje akasa.
Koda ya yunkura zai tashi sai Zaiyan ya
rintsashi da tsinin takobinsa a wuyansa, kawai
sai suka ji ana rafka tafi, cikin sauri duk su biyun
suka waigo suka dubi inda sautin tafin ya fito
koda suka ga ashe sarki ne atsaye fuskarsa cike
da murmushi yana tafin sai Safwan ya mike suka
ruga gareshi suka kwashi gaisuwa, Sarki ya dafa
kafadun yarima Zaiyan ya tashi she tsaye sannan
ya dubeshi cikin nutsuwa ya ce "yakai dana
menene dalilin da yasa kuke bawa kanku horon
yaki alhalin ni ban taba ganinku kuna yi ba?
Koda jin wannan tambaya sai Yarima yayi
ajiyar zuciya fuskarsa ta juye izuwa yanayin
damuwa nan take sannan yace "yakai Abbana
kayi sani ba wani abu bane ya saka ni cikin
wannan tunani ban a baiwa kaina horo yaki face
wani mugun mafarki da nake yawan yi acikin
'yan kwanakinnan, abinda ake nuna min acikin
mafarkina shine wdansu manyan kasashe gudu
uku dake cikin wannan nahiyar sun hada karfi da
13 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
karfi suna son su rushe wannan birnin namu maj
albarka kuma su shafe addinin,ana hiyar gaba
daya kafin Zaiyan ya gama rufe bakinsa tuni
Sarki ya tari Numfashinsa yana mai daka masa
tsawa yace "akul na kara jin kayi irin wannan
furuci domin har abada TURBAR GASKIYA
itace hanya mai dorewa, nasani cewa akan
gaskiya muke su kuwa suna kan turbar karya
don haka bza su taba samun nasara akanmu ba
mun saki Allah mu kama abin da suka kama ya
kai dana ina so ka sani cewa nima Allah ya
nunanimin abin da ya nuna maka acikin barcina
fiye dad a kwanaki biyar da suka shude kuma
tun daga sannan kullum sai nayi addu'a na
neman tsari daga saharrinsu da kaidinsu. Lallai
zamu zauna acikin shiri ko da ta kwana duk
wanda ya takalemu zamu tareshi afafata, ba tsoro
kuma ba gudu ba ja da baya, hakika ka bani
mamaki mutuka bisa ganin irin wannan
gagaarumarjarumtaka don haka ni yanzu ina so
na wasajini na tare daku.
Koda gama fadin hakan sai Sarki ya karbi
takubin Safwan ya fuskanci Yarima yace
bisimillah, cikin tsananin alamun tsoro Safwan
ya dubi Yarima yana mai masa inkiya akan kada
14
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ya yarda yayi yaki da Sarki saboda yasan cewa
ruwa baa san Kwando bane,
Shi kuwa Yarima ki ajikinsa bai damuba
kawai sai ya gyara tsayuwa ya daga takubinsa
sama yana mai ruketa da hannun biyu,
Sarki ya ya futo Yarima da hannunsa yana
mai masa nuni day a fara kawo masa hari, shi
ma Yarima ya yafuto Sarki da hannun yana nufin
sai dai shi Sarkiya fara kawo harin,
Koda ganin haka sai kuwa Sarki ya falfalo
da gudu izuwa kan Yarima ya kawo masa
wawan sara tamkar yana yaki da wani
Kasurgumin kafiri, koda yarima ya kaucewa
wannan saran sai takubin sarki ta tsarge wata
bishiya dake bayan Yarima ta rabata gida biyu,
saboda tsananin firgitar da Safwan yayi bai san
lokacin day a dafe kai baya durkushe yana mai
zazzaro idanuwa da wangame baki tamkar yasa
kururuwa ya nemi agajin mutane domin tunda
yazo duniya baitaba ganin mutun mai zafin nama
da karfin saraba kamar sarki,
Nan take yaji kamar ya tsandara ihų ko
kuma ya kwalawa mutane kira domin su zo su
tsaida wannan yaki don kada ayi asarar rai
abanza shi kuwa yarima Zaiyan ko alamar tsoro
15 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
babu atare dashi, kawai sai yayi murmushi kuma
shima ya afkawa sarki suka ruguntsume da
azababben fadamai tsananin da ban tsoro
ardiost sush yazamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka
acikin zafin hama juriya juriya da bajinta. Al'amarin
day a Kara daure Safwan kai shi ne, ganin yadda
Sarki da yarima zaiyan suke wannan yaki da
wani irin zafin nama na musamman tamkar
jikinsu bana jin da tsoka bane domin ko kadan
babu alamar gajiya atare dasu sannan kuma irin
salon fada daya suke yit yitamkar dama can
malamansu guda ne súna yakine acikin kaiwa
juna naushi, bugu, sara, da suka duk alökaei
guda da d'an gami da dan tsalle tsalle da kwance
kwance irin na tsofaffun gwanayen yaki, abinda
Safwan yake tambayar kansa shi ne yaya akayi jarumtar Sarki da ta Yarima ta ke neman tazo lri
daya ne alhalin kowa agarin ya sallamawa Sarkf
saboda ko daji aka tafi farauta babu wanda yake
yin irin jurumtar da yake yi agarin kaf sama
dashi. 1 2 пі
Akwai wata rana da aka tafi yin wata
gawartacceWar farauta acikin wani Rasürgümin daji dan kamo wani shu'umin Zaki wanda ya gagari kowa ya hana'shigewaya tsare hanya har
1оианBDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
ma ya kasha kimanin dakaru sama da dari nan
take Sai sarki ya fusata yasa akayi wannan shirin
da farauto zakin alokacin da ya isa cikin wannan
daji cikin fusata sai ya ajiyc makamansa ya tare
zakin suka kaure da azababben yaki, shi da
zakinan Sarki ya turmusheshi yasaka Zakin anan
amakata har said a ya 6abakin Zakin gida biyu
sannan ya watsar da gawarsa gefe.
Daga wannan ranar kowa ya sallamawa
Sarki aka rinka yi masa kirari da makashin
mazan dawa. Lallai ashe masu iya Magana sun
gaskiya da suka ce barewa bata gudu danta yayi
rarrafe.
Lokacin da aka shafe kimanin sa'a daya
darabi ana wannan bakin yakin tsakanin sarki da
Yarima yazama duk su biyun babu wanda ya
samu nasarar koda lakutar jikn dayansu ba sai
suka gaji ainun, babu shiri suka ja da baya
sukayi curko curko suna haki saboda gajiya sai
harara juna suke kawai.
Koda ganin haka sai hankalin Safwan ya
tashi ya dubi Yarima ya yi masa inkiya da kada
ya yarda da suyi fadan hannun shi da Sarki iya
ka wannan bajin tar day a nuna ta is, shi sai
Yarima jikinsa yayi sanyi ya dubi mahaifnsa
17
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
yace "haba yakai Abbana kayi sani cewa ba
zanso ace na cutar da jikinka bad a hannayena,
koda jin haka sai Sarki ya dakawa yarima tsawa
yace "Idan har kaki fadan hannu dani bil hakki
sai na tara maka gajiya koda yaki yazo baza ka
iya fita ba domin alokacin kana kwance kana
jinya jikinka"
Koda jin wannan batu sai hankalin yarima
ya dugunzuma ainun domin arayuwarsa bashi da
wani buri wanda yafi ya fita filin yaki ya fafata
da mazaje domin a nanne zai iya sanin iyakar
*jarumtakars, duk sa adda za afita farauta sarki
baya barin yarima yaje a wannan rana sai dai ya
bashi wakilicin garin dan tafiyar da harkokin
mulki, akwai wata rana ma da sarki ya tafi
rangadi tare da tsirarun dakaru izuwa wani daji
mai nisan gaskea asannane wani ayarin guda na
yanfashi ya kawo musu sumame aka kasha gaba
daya wannnan tsirarun dakarun na sarki amma
shikadai ne yazewa wadannan 'yanfashin
guguwar annaoba ya rinka ragargajarsu sai da ya
kashesu bake daya alhalin adadinsu ya kai dubu
uku da doriya su kuwa dakarun na Sarki ba su
wuce su hamsinba,
Kawaisai ganin Sarki akayi ya dawo
18 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
birninsa. tare da gawarwakin dakarunsa akan
keken dokinsa duk jjikinsa yayi kace kace da jini
tamkar acikin kogim jini aka tsoma shi,
Nan day a bayar da labarin yakin da yayi
abaya da 'yanfashi kuma ya fadi a inada akayi
wannan mummunan karo das u ya kuma bada
umarnin dan aje adauko ganimar 'yan fashin.
Aikuwa da akaje aka ga tarin gawarwakin
'yanfashin sai hankalin 'yan aikin ya dugunzuma
suka rude da ganiin yawansu kuma duk ace
mutun daya ne yazama sanadiyar yimusu
masaukia akiyama, dukiyar da aka samu kuwa a
tare da yanfashin ba karamin yawa gareta ba
domin sai aka yi sawu biyu bayan wadanda suka
je na farko sun dawo aka tura wasu dan suje su
kwaso, lallai suma sun ga abin mamaki mai tarin
yawa.
Lokacin da yarima yaje wannan daje yaga
irin gagarumar bajintar da mahaifinsa yayi sai
takaici ya kamashi har said a ya zubar da kwalla
saboda bakin ciki cewa bashi akayi wannnan
gagarumin gumurzu ba.
Batare da fargaba sai shima yarima ya
dunkue hannuwansa yana mai tunkarar sarki da
19 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
gyara tsayuwa, nan take kuwa suka kaurace da
azababben fada suna kaiwa juna naushi da bugu
da hannu da kafa sai gashi dukkanninsu sun
shanye dukan tamkar jikin nasu bana jini da
tsoka banc, idan Sarki ya gabzawa yarima
wawan naushi a fuska sai kaga har kataantanwa
yake saboda karfin naushin amma sai ya shanye
shimaya maida mada martani,
Nn da nan suka hadawa juna jini da
majina, al'amarin daya kara dugunzuma
hankalin Safwan kenan yaji kamar ya rugu yaje
yak era mutane su zo su raba wannan yaki amma
sai ya kasa saboda yana ganin cewa idan ma ya
bar wajen kafin yake ya samu mutanen, to tuni
daya daga cikinsu ya kashe daya nan fa Safwan
ya fara kuka yà shiga rokan sarki da Safwan
akan su daina wannan fada su kuwa ko kallonsa
basu yi ba kamar ma kara zugashi sukayi don ci
gaba sukayi da gabzar junansu ka kace tsofaffun
abokan gaba ne suke son su kawi karshen gabar
tasu, Tun sarki da yarima suka tsaye suna
kai duka said a suka durkushe akasa suna layi
amma saboda bakin naci da tsananin juriya basu
daina kokarin kai naushi ba har said a da kai
cowa ko daga hannayensu basa iyawa sannan
ABDUL'AZIZ ŞANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
suka zube kasa wanwar suna numfarfahi kamar
ransu zai fita.
Lokacin guda kuma sai suka mike zaune
suka dubi juna suka bushe da dariya a tare kawai
sai sukayi rarrafe kamar kananun yara suka
rungume juna suna dariyar farin ciki, said a suka
dan jima amanne da juna sannen sarki ya janye
jikinsa daga jikin na yarima ya dubeshi acikin
nutsuwa yace "yakai dana kayi sani cewa daga
na sami nutsuwa da kwanciyar hankali tunda
nasan cewa na sami magajin da zai iya ruke
karagata, lallai zanyi alfahari da kai domin
wannan albasar tayi halin rowa Nayl maka
alkawarin duk ranar da yaki ya zo mana kaine
zaka jagoranci dakarunmu".
KOda jin haka sai farin jiki ya lullume
yarima ya sake rungume mahaifinsa yana mia yi
mada godiya domin shi arayuwarsa bashi da
wani buri wanda yafi ya fita filin daga a fafata
musamman dan saboda gorin da 'yar kanin Sarki
wato Lushmaira take yi masa.
Lushamaira wata kyakkyaawar budurwa c
eta gaban kwatance wadda babu kamarta afagen
kyau a birnin baitul Harwal, Samari da yawa
sun nemi auren Lumshmaira amma taki amin
21 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
cewa musu saboda da wani sharadi da gindaya
wanda kuma ya gagari kowa,
Shi dai wannan wannan sharadin kuwa shi
ne bazata auri kowa ba face jarumi da yayi
gagarumar jarumtakar da tafi ta sarki, kowa ya
sani cewa Sarki ya taba kasha 'yanfashi sama da
mutun dubu uku shi kaďai sannan ya kasha
gawurtaccen zakin day a addabi mutane adajin
farauta da hannu bad a makami ba
A halin yanzu akwai wadansu dazuzzuka
guda biyu a yamma da birnin Baitul Harwal.
Daji na farko ana kiransa da suna Sinil maut.
Tun zamanin kakan sarki wato fiye da
shekaru saba'in baya fatake da mafarauta basa
iya wucewa ta cikin dajin Sirril maut domin
akwai wata tsohowar macijiya da ta zama
kangarau kuma gagarau acikin wani kogi dake
tsakiyar dajin ana kiranta da suna Barukul
karsum, mahaifin Sarki Abu Zaiyan ma kafin ya
rasu sai ya gargade shi akan cewa kada yace zai
shiga dajin siril maut yace zai yaki da macijiya
Burukul karsum domin itace sanadin ajalin
kakansa na uku kuma shima dafin tane
ajikinsawanda ya sahi kwanciya cuta ta tsawan
shekaru bakwai, azamaninsa ne yasa malamai
22 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
sukayi istahara suka gano cewar baza ataba
samun nasarar kasha wannan macijiya Burukul
kursun ba sai ashekarar da aka zubar da jini mai
yawan gaske a nahiyar gaba daya irin jnin dab a
ataba zubar wa ba.
Lashraira ta sanar da cewa idan ba
askashe macijiya Burukul kursum to ta hakura
da yin aure har abada kuma wanda ya kasha
macijiyar shi ne zai zamo mijinta kodai kuwayafi
kowa tsufa talauci da muni a nahiyar.
Dalilinta nayi wannan furci shine itama
macijiyar ce sanadiyar ajalin mahaifinta.
Mahaifn Sarki Lashmaira yakasance
gawurtaccen Sadauki harma yafi Sarki Abu
zaiyan Jarumtaka kuma uwarsu daya ubansu
daya, ranar ada ka haifi lushmaira ranace wadda
baza ataba mancewa da ita ba a birnin Baitul
hairal domin ranar ce akayi asarar dubban rayuka
sakamakon shirin maciya Burukul Karsum,
Wata Asabar ce ayammacin sakaliya
mutane nata hidimominsu kamar yadda aka saba
kawai sai aka ga wani abu mai tsananin tsawu
da kauri mara misiltuwa yafaso Katanga birnin
ya zuro kansa ya kama yiwa mutane dauki dai
dai yana ci, sai dai ka ga ana gatsa dan adam
23 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
tamkar ansa addda an daddatsashi, jini kuwa
yarinka fallatsa da malala, sai da abin ya fara
hadiye mutane sannan aka gane cewka macijiya
ce
Nan fa gari ya hautsine mutane suka kama
guje guje da iface iface nan da nan labara ya
riski sarki Abu zaiyan a wannan lokaci kuma
mahafin Lashmaira yana can Karshen gari, inda
matarsa ke nagudaacikin gonarsa inda yake
noma, wata kuyangarsa nayi mata Ungozoma.
Asannan mahaifin Lashmaira na kofar
bukkar da matarsa take nagudar yana tai kawo
cikin zakuwa kuma yana ta addu'ar Allah yas
sauketa lafiya.
Lokacin da labari ya riski Abu zaiyana
cewar gafa wannan muguwar macijiyar ta shgo
gari ta fara mummunar barna sai hankalinsa ya
tashi saboda yasan sharrinta kuma ya sami
cikakken labarinta awajen mahaifinsa wanda ya
gargadeshi akan kada ya kuskura yayi gaba da
gaba da ita,
Nan take Sarki yasa aka tara dakaru
majiya karfi yace suje su yaketa sannan kuma ya
tara malaman garin suka dukufa suna neman
24 ABDUL'AZIZ SANI M/GINI
TURBAR GASKIYA
nauke daga uban giji ta fuskar rukonsa dan ya
magance musu ita.
Byan Sarki Abu zaiyan y agama wannan
shiri sai shima yayi shigar yaki yahau kan
dokinsa ya zaburshi da gudu izuwa can bayan
gari inda gidan gonar dan uwansa take wato
mahaifin Lashmaira,
Yana isa ya iske matarsa ta haifi Lasmaira,
dan uwannasa nata na ruke da jaririya yana ta
murna da yiwa Allah godiya. Koda ya hango dan
uwansa Sarki bisa doki kuma acikin shigar yaki
sai hankalinsa ya dugunzumaya mikawa
Ungozomar jaririyar ya ruga ya tari Sarki ya
tambyaeshi yana mai cewa "shin harin sumame
aka kawo manane? Cikin alamun tsananin
damuwa Sarki y ace ai