to ni zan karantar da kai. Har yaushe Maryam
za ta yi maka waya ta cika ka da karairayi sannan ka dauki kudi ka
aika mata, amma in nice kudin cefane ma sai an ji mu, to in ka ga
dama ka biya kudin in kuma ba ka ga dama ba in yaso a je a daure
ni.
Yaya ya taso min da fada wai yana magana ina mayar
masa. Wai me muke so mu mai da shi ni da Maryam kullum mun
mai dai shi sai ka ce banki, sai gasar karbar kudi. Ni ma zuciyata
kawo min iya wuya, na so na mayar masa da magana, amma sai
naga bai kamata na yi masa tsaurin ido ba. Kuma bai kamata muna
32
tashin hankali a gaban yara ba. Hawaye ya cika min ldo, na nufi
dakina.
Tun daga wannan lokacin Yaya ya ari fushi ya yafa wa
kansa, ko magana ba ya yi min, sannan ko da safe na gaishe shi da
kyar yake amsawa, da zaman hakan ya ishe ni sar kawai na raba
mana dakin kwana na koma dakina da kwana, amma duk da fushin
nasa ya je ya biya kudin kayan da na karbo.
Kwanan mu biyar Yaya yai fushi da ni bai sauko ba, ni ma
na yi burus da shi, ban nemi mu shirya ba. Ranar alhamis cikin
fushi Yaya ya same ni yace "Rukayya kishirya gobe zamu tafi
Nijeriya" Ba tare dana daga ido na ganshi ba na amsa "T" Daman
komai da komai nawa a shirye yake don haka ba na bukatar komai
sai dai tafiya.
Ranar juma'a muka isa Nijeriya, mun sauka ne a Abuja, a
nan gidan Yaya na so drived, amma a gidan saukar bakinsa don a
lokaçin nan ana gyara babban. Gidan saukar bakin gida ne mai daki
biyu sai falo da kuma kicin; ni a ra'a yina na fi son mu wuce zuwa
Kano, saboda da 'yar tsamar da muke yi da Yaya. Amma tunda na
ga har saukar mu a Abuja ma Yaya yana cika yana batsewa, ni ma
sai na yi masa diban karan mahaukaciya, na ce in ya matsu da ni ya
name ni, na kyale shi kawai.
Kwanan mu biyu ranar lahadi Yaya ya ce min zai je Kano,
na ce masa mu ma mu shirya da mu za a tafi, Ya ce, A da ke zan tafi
ba zan dai tafi da yara, ke ki zauna a nan Abuja". Ban yi masa
gardama ba, ko musu, na ce Allah ya kiyaye hanya a dawo lafiya,
kuma gaida su Inna Sa'a"
Bayan tafiyar Yaya Kano, Alhaji Suleman ya zo gidanmu,
bayan mun gaisa yake tambaya ta ina Yaya, na ce, dazu ya tafi,
Kano, Nace ina Kubra? Ina fata dai ba ta riga ni saukewa ba don
muna rige-rige. Suleiman, ya ce "Ai daman abin da na zo gaya miki
ke nan, Kubra ta haihu, jiya, ta haifi 'yarta mace, saura ke. "Na ce
Kubra ta huta, Allah ya raya, in Yaya ya yi waya zan fada masa, ka
yi mata barka kafin na zo" Ya ce "To zan yi mata".
Kwanan Yaya uku da tafiya Kano, ranar laraba da dare na
yi shirin barci, ina kwance a kan gado, waya ta yi kara kurr, na
dauka, na ce "Assalamu alaikum". Sai na ji muryar, Yaya ce take
amsa min sallamar. Ya ce, "Darling sister, kinanan lafiya?. Yaya
gida? Na ce; "Ba dai ni kanwar taka ba sai dai wata, ni da kake
33
fushi da ni, Ya ce, Kike fushi da wanki dai, don Allah a yi hakuri,
na tuba", Na ce" Haba Yaya ni daman ban yi fushi dakai ba, kai ka dauki abin da zafi". Ya ce "Kanwata lallai kin karantar da ni munafuncin mata, ashe duk abin da Maryam ta yiwo waya ta fada min wai Hajiya Hauwa ta dauko mata dan sanda akan kudi, karya take yi, a zuwana na yi bincike na tabbatar da hakan, don har wajen Hajiya Hauwan na je, kuma har gaban Maryam din na dauko ta muka zo, wanan ya tabbatar min, ba gaskiya ba ne, wannan ya dada tabbatar min da munafunta ta Maryam take yi, amma na yi mata kashedi wannan ya kasance na karshe. Wallahi Rukayya ba don Inna Sa'a ta sa baki a maganar ba. Da na yanke wa Maryam danyen hukunci, "Ni ma na ce" Yaya sai hakuri, ka san aure da haihuwa, ya wuce komai, "Ya ce, "Haka Inna ma ta ce min, amma
wallahi ta ci albarkar 'ya'yanta.
Yaya ya ce, "Yaya baby na yananan yana boxing ko? Ina
fata dai ba wani problem". Na ce" Ba problem lafiya ta kalau'.
Na shaida masa labarin Alhaji Sulaiman ya zo ya shajda
min Kubra matarsa ta haihu, Yaya ya ce "Allah ya raya, Kubra ta
riga ki, amma ya kamata Inna Sa'a ma ta zo ta yi musu barka,
saboda irin mutuncin da Sulaiman yake nuna mana. Na ce ya
kamata".
Bayan Yaya ya dawo daga Kano, ana gobe sunan Kubra Ya
sa Usman direba ya taho da Inna Sa'a da Yaya Aisha don su halarci
sunnan kubra, Maryam ta shirya ta biyo su, wai ita kuma da shirin
zama ta zo, don ita ba za ta yarda ta zauna a Kano ni ina Abuja ba.
Sun iso gidanmu misalin karfe biyar na yamma, a lokacin nan Yaya
ba ya gida, na yi musu sannu da zuwa, na gaishe su tare da kawo
musu ruwa da lemo, amma tsakanina da Maryam sai kallo da ido,
don ko amsa gaisuwata ba ta yi ba, sai dai harara.
Yaya ya dawo, ganin Maryam ransa ya dan sosu amma sai
ya dake bai ce komai ba. Bayan ya gaishe da su Inna, ya се "Ya
kamata in an jima ku je ku gaida mai jego, mun sayi kayan barka
suna sai ku tafi da su, don gobe suna, ne kuma jibi za ku tafi Kano"
Kawai sai Maryam ta taso da fada wai wane irin wulakanci
ne daga zuwan su har ząi fara cewa gobe za su tafi, ai ba ita yake
wulkantawa ba sai dai mahaifiyarsa, don dai mace to shanye shi shi
ne zai rinka wulakanta mutane, to ya sani ita da zama ta zo ba tafiya
za ta yi ba, "Don ba yadda za a yi aure na kake yi sannan kana tare
34
da wata matar ni kuma aka bar ni a Kano, zaman ya ishe ni"” Ni dai
na yi shiru ina kallon ikon Allah. Yaya zai fara magana, Inna ta
shiga tsakani. Ta baiwa Yaya hakuri, ta raba, don Inna ba ta son
tashin hankali, ta baiwa Maryam ma hakuri. Da dare je muka ye
barka gidan Alhaji Sulaiman tare da su inna, ba mu dawo ba sai
misalin karfe goma da rabi. Dawowarmu daga gidan Sulaiman Inna
ta shiga daki ita da Yaya Aisha suka kwanta, ni ma na shiga dakin
na shimfida bargo na kwanta. Na bar wa Maryam dakin Yaya,
daman kun san gida ne mai daki biyu. Mun kwanta ke nanYaya ya
dawo ya zauna a falo yana kallon setlite, can Yaya ya kara kira na
ina jin sa amma, sai na yi kamar barci nake yi, na ki amsawa,ya сe "Rukayya! Rukayya!" Har sai da ya zo bakin kofar da muke kwance
ya ce "Rukayya ki tashi ki je can dakin ku kwana, ba za ki zo ki
takura wa Inna ba, ni kin ga a falo zan kwana", Ni dai na ki na kula
shi, sai Yaya Ai'sha ta ce, "Rukayya kina ji Yaya yana yi miki
magana, ki tashi ki je mana". Na ce Yaya Ai'sha kin san fa wata
rigima Yaya yake son ya taso". Yaya Ai'sha ta ce ke dai tun da shi
ya ce ki je ki kwana a can ai sai ki je ba komai". Na ce "To"!.
Na tashi na fita, na sami Yaya a falo ni dai ban kula shi ba,
na wuce zuwa dakin da Maryam take kwance na kwanta a kan gado,
kawai sai Maryam ta tashi ta daka tsaki ta dauki bargo ta canza
wajen kwanciya, a kasa.
A ranar ban yi barci mai dadi ba don Maryam ba ta bar ni
nayi barci ba, ta dinga tashi tana shiga bandaki tana doka kofa, duk
don kada in yi barci, sai da asuba lokancin da aka fara yin sallah,
Yaya ya shigo don yin alwala, bayan ya yi alwala ni ma na shiga na
yi, na fito na dauki abin sallah na nufi falo don yin sallah. Bayan na
idar da sallah, na samu na dan mike har barci ya debe ni kanfin gari
ya waye, na shiga kicin don yin abincin breakfast.
Na gama abincin brerakfast ina rabawa misalain karfe tara,
sai ga Maryam, don iya kinibi da kisisina, ta ce Rukayya ina abincin
Sadiq ya ce na zo na amsar masa". Ni dai na san 'yar tsama suke yi
da Yaya, amma don ta nuna min sun shirya, shi ne ta zo ta ce wai
na ba ta abincin Yaya, kuma shi da na san bai damu dayin breakfast
ba sai dai ya sha madara da 'ya'yan itatuwa, sai na ce “To ai ban
gama shirya breakfast dinsa ba sai an dan jima”. Na shirya kayan
breakfast, ba tare da na kira Maryam ta kai ba, na dauka na kai wa
Yaya, na sami Maryam a bakin gado tana zaune, shi kuma yaya
35
yana yin brush din hakoransa a bandaki, na ce, "Yaya ga breakfast
dinki" ai nan zan ajiye ko kuma a kai falo? Ya jiyo ya ce", "Wa
yace miki zan yi breakfast yanzu? Na ce "Maryam ce ta ce a kawo
maka".
Ya juya, ya kale ta ya tabe baki, ya ce "Ni ba zan yi
breakfast ba, ki koma da shi", na dauki kayan abincin na koma da
shi. Haba Maryam sai cika take yi tana batsewa, na kai wa su Inna
da Hajiya A'isha nasu, mu kuma na hada mana namu a falo, amma
Maryam ta ki zuwa mu ci sai ni na ci nawa na tashi na bar mata
nata.
Da rana ne misalin karfe sha biyu muka tafi gidan suna,
gidan suna kam an hallara domin gogaggun 'yan boko ne, ga
kowace tana Ji da kanta don kowace ka gani matar mai mulki ce ko
kuma ita ma mai mulki ce. Da la'asar ne aka kayatar da bakin
sunan da liyafa, daya da daya wace ta kayatar da kowa a wannan
ranar ni ce uwar biki, don ni ce babbar aminiyar Kubra, Maryam ta
yi mamakin ganin yadda a dan kokaci kankani na saba da yawancin
mutane, da suka zo sunan, don duk yawanci matan abokan su Yaya
Sadiq ne, kuma muna haduwa da su a London.
Ba mu bar gidan suna ba sai misalin takwas na dare, don
sai da kowa ya watse, mu muka zauna daga karshe, sai da na
tabbatar masu aiki sun gama kintsa gidan sun shashshare sun kuma
wanke duk kwanukan da aka yi amfani da su, sannan muka tafi
gida.
Muna komawa gida kasancewar na gaji, ga tsohon ciki ina
turawa da kyar, na samu na kokarta na yi sallar isha da shafa'i da
wutiri, sai na mike a falo, tuni barci ya debe ni na bar Maryam tare
da su Ina suna kallon setlite, ban san lokacin da Yaya ya dawo
gidan ba, har lokacin da su Inna suka shga daki don su kwanta.
Misalin karfe sha daya da rabi na ji Yaya yana tashi na wai
na tashi na shiga daki na kwanta, na farka nace "Don Allah Yaya ka
bar ni na yi barci na a nan don barci nake yi", ina magana ne cikin
magagain brci, sai nji Yaya faa ce "Rukayya, ya za' yi ki kwana a
falo bayan kina da ciki, ai bai yiwau ki kwana kan kujera ba don
aaki takura, bayanki zaiyi ciwo, ni dai na nace akan ya barni barci
nake ji. Daga karshe Yaya yayi hakuri ya barni.
Na riga nayi barci mai nauyi wanda ban san mai duniya
take ciki ba, kawai ina kwance a falo a kan kujera sai na ji an rufe ni
36
da duka, tamkar wadda aka aiki mutum don ya doke ni, na yi zunbur
na mike, wa kuke zatan zai yi mini wannan danyen aikin sai naji
Yaya yana cewa "Ke ba ki da hankali ne, mace da cikinta ki hau ta
da duka so kike ki kashe ta? Yaya ya zo ya rike Maryam yana
zazzagin ta, ya ce, "Wallahi Maryam ina tausayi miki, shi ya sa duk
abinda kike yi min nake kyale ki, amma yanzu don rashin hankali a
gabana za ki zo ki hau Rukayya da duka, to ware lefi tayi miki.
Maryam ma ta hauro tamkar wata 'yar maguzawa tana dura
min zagi, wai ni ce na raba ta da mjinta yau sai dai a yi wacce za a
yi. Yaya yace "Maryam don ba ki da hankali, kin san Inna tana
gidan nan amma za ki zauna kina irin wannan masifar.... Su
Inna ma da suka ji fadan ya yi yawa sai suka fito daga dakin da
suke, Innan ta ce "Yau kuma mai zan gani haka gidan nan ya koma"
su Inna ta kara cewa "Maryam ki wa Allah ki yi wa Muhammadu
Rasullillahi kiyi hakuri a zauna a sasanta abu cikin ruwan sanyi, kai
ma ka yi hakuri " Amma me zai faru Bude bakin Maryam ke da
wuya sai cewa ta yi Ai Inna ke ce babbar munafuka tun da ke kika
sashi ya auri Rukayya "Inna ta fashe da kuka tace "Yanzu wannan
yarinya ki rasa wace za ki ce wa munafuka sai ni" Kawai Yaya
ganin In tana kuka bai san lokacin da ya daga hannu ya share
Maryam da mari ba, daga hannun da Maryam za ta yi ita ma sai ta
kai masa mari, Yaya yace "Maryam ni kika maran lallai kin isa
amma yau zan koyar da ke hankali" Mu dai ni da Inna da Hajiya
A'isha sai salati muke yi" Muna juya hannu don mamakin wannan
irin rashin hankali na Maryam, kawai Yaya ya cire wayar C.D din
falo ya ding tsola wa Maryam ita ajiki amma Maryam bakinta bai
mutu ba tamkar wacce aka aiko ta sai zagi take dura masa gundum -
gundum, marasa dadin ji.
Mu dai mun kasa kwatar Maryam daga hannun Yaya, sai
Inna ce ma cewa "kai kashe ta zaka yi, ba ka da hankali ne? ka ber
ta haka". Yaya bai bar bugun Maryam ba sai da Inna ta fashe da
kuka, ta ce ita kam zata tattara kayanta ta bar masa gidansa a cikin
tsohon daren nan, Yaya ya hakura. Amam duk da bugun da Maryam
ta sha bakinta bai mutu ba don zagi take ta yi min ni Rukayya. Yaya
yace "ke Maryam tun da ban isa mai mutunci a wajen ki ba kuma
uwata ba ta isa mai mutunci a wajenki ba, to ki je ki nayanke igiyar
aure na daya a kanki". Duk muka debi salati, to sai a nan Maryam ta
bar zage - zagen da take yi ta fashe da kuka wai ta shiga ukunta,
37
'ya'yanta, daga nan Inna da yake uwa tagari ce ka kuma surkuwa, ta
gari wacce ba ta son gidan danta ya watse. Inna ta ce "Yanzu а
gabana ba tare neman shawara ba za ka yanke wannan danyen
hukunci.ka ce ka saki mace?, Ai ana yin abin da ya fi haka ma kuma
a zauna, don haka ayi hakuri ka maida ita kafin wani ma ya ji". Yaya ya ce, "Ai ko mata sun kare Maryam kam na yafe"
Maryam ta hada kai da gwiwa tana ta riskar kuka, ni kuwa
da Yaya A'isha sai hakuri muke baiwa Yaya, Inna taga Yaya suka shiga daki ta ba shi hakuri, ni da Yaya A'isha sai hakuri muke
baiwa Yaya, Inna da Yaya suka shiga daki tana ba shi hakuri tana
tausar zuciyar sa don yayi hakuri ya maida Maryam amma Yaya ya
yi mursisi ya ki, Inna ta ce "Yanzu so kake jama'a su ce don ni
mahaifiyarka ka saki matarka, ko?, Ai na san Maryam kam ta yi
rashin mutunci amma sai ka dubi girman Allah ka maida ita ko don 'ya'yanta"
Ranar dai kwana muka yi ba mu yi barci ba har garin Allah
ya waye. Lallami da roko Inna ta taushi zuciyar Yaya kasancewar
mai din maganar Inna ne dole Inna tasa shi yace ya hakura ya maida
Maryam kasancewar ba wanda ya san abinda yake faruwa daga ni
sai Hajiya H. A'isha sai Inna, don haka muka rufe zancen mu ka
dai, amma duk da haka Yaya yayi matukar fushi da Maryam wanda
ba ya misaltuwa.
Karfe takwas na safe Yaya ya ba da mota ya ce su koma
Kano, amma Maryam ta ce wai ita sai ta je asibiti, Yaya yace ba
asibitin da za ta a Abuja in ta je Kano ta je. Haka dai Maryam ta
tafi Kano, kai Maryam ta bugu, don cewa akayi da ta koma Kano
sai da ta debi sati guda tana kwance a cikin daki ba ta fita ko tsakar
gida, to dama dai an ce kaikayi koma kan mashekiya, wannan abin
da Maryam ta yi shi ya kawo faduwar darajarta da mulkinta da
kuma mutuncin uwar gidanci a idon Yaya, don koma yana yi mata
ne don darajar aure sannan da darajar mahaifiyarsa Inna sa'a, amma
ba wai don ta isa ba.
Tun da Yaya suka sami sabani da Maryam sai da ya shafe
wata guda bai je Kano ba, ko ni na yi masa maganar ya dace ya je
sai ya yi burus da maganar har sai da Allah Ubangiji ya sauke ni
lafiya, ranar wata laraba na haifi 'yan biyu, dukkan su maza, kamar
Larabawa saboda kyau tamkar Sadiq ya yi kaki ya ajiye.
38
Farin ciki a gun Yaya kamar bai taba haihuwa ba sai a kan
wadannan yaran, tun a asibiti Yaya ya yi wa Inna Sa'a waya ya
shaida mata batun haihuwar, sannan ya shaida mata muna nan zuwa
da zaran an sallami Rukayya daga asibiti, Inna ma ta yi wa Yaya
murna tare da nuna farin cikinta.
Washegari ranar alhamis aka sallame ni dag sibiti ranar
jumma'a muka isa Kano, a ranar nan abin mamaki, Maryam har
dakina ta zo ta gaishe ni ta yi min barka, sannan ta ga 'yan biyu.
Kuma ta turo su Nusaiba da saima da Rukayya karama su zo su ga
kannenensu. Kowa wannan abin na Maryam ya bashi mamaki, har
shi kansa Sadiq sai da ya jinjina wa abin, lokacin da ta yi masa
murnar haihuwar.
Komai yana tafiya yadda ya kamata don Maryam ta
kwantar da kanta ita take tafiyar da komai na hidimar gida har ranar
suna ta zagayo,. aka radawa yara sunan Fahad da Abdul'aziz
kasancewa suna ne na Sarakunan Saudiya sai ake kiransa King
Fahad da king Abdul'aziz.
Duk yadda ake son uwar gida ta gari ta yi Maryam ta yi a
sunan nan, don ita take shirya komai, kuma ita take tafiya da komai,
a gaskiya kowa ya yi mamakin wannan sabon canji na Maryam.
Da la'asr ne aka yi gawurtacciyar liyafa, wacce komai da
komai daga Otal din Nicon na Abuja suka dauki kwangilar girkawa
da tsarawa. Duk wani abin da za a nema su suka kawo, hatta
cokala, da Farantai da rumfuna da za'a zauna a ciki da kujeru su
suka taho da su. Kai hatta tsinken da za a sakuci hakori su suka taho
dashi. Liyafa kam ta kayatar, don takanas Hajiya Kubra matar
Alhaji Sulaiman Hafiz ta aika har Niger Sa'adu Bori ya zo ya yi
wasa, sannan Barmani Coge ma ta zo ta yi nata wasan.
Wannan bikin suna dai sai wanda ya je wajen ko kuma ka
ga kasat din don a ranar anyi wasa da naira, a ranar Yaya da Dalar
Amerika yake yin kari.
Duk hidimar bikin da ba'a yi ba a lokacin bikin aurenmu
shi ne yanzu akayi a lokacin haihuwar. Bayan suna, Yaya ya tara
mu ni da Maryam a falo yake nuna mana farin cikin sa a kan yadda
aka tafiyar da komai na suna cikin hadin kai, yana fatan zamu ci
gaba dayin hakan. Yaya yace "Kun san a duk inda aka sami zaman
39
lafiya da kwanciyar hankali, za ku samu a wajen nan da akwai
bunkasar arziki sannan da kosasshiyar lafiya.
Muna cikin hira ne Yaya ya kawo zancen komawa London
yace yanzu tunda watan azumi ya kusa kamawa ba na sai mu yi
azumi a gida Nijeria, sannan kuma ga bikin Balarabe da za a yi sai
mu bari sai an gama tukunna-mu koma [Balarabe dan kanin Inna
Sa'a ne].
To a nan Maryam ta kawo bukatarta ta zuwa England,
Yaya yace, "A gaskiya Maryam ba wai ba na son tafiya da ke ba
ne" Ya daga ido ya dube mu, ya ce "Kin san ba na son tashin
hankali Maryam tayi dariya ta ce "Haba Sadiq ai Kasan na gane
kurena yanzu" Sadiq ya ce, "To kin dauki alkawarin ba tashin
hankalin" Ta ce, "Ina tabbatar maka da hakan".
Yaya ya ce, "To Allah ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar
hankali, sannan Allah ya raya mana zuri'armu ya sa masu jinkai
ne".
Muka ce "Amin
Sal mun hadu a wani sabon littafi mai suna
DAKAN DAKA
Ina cikin yi wa masu aiki bayanin abubuwan da za su yi sai ga Maryam ta fito da fadanta, wai ikon me zan zo na yi mata a cikin gida, har da zan zo na baiwa 'yan aikinta umarni
“ Sai ki bari in kin koma can Londondin ki yi iko amma ba a nan ba, don wadannan ‘yan aikin ni na dauko su".
Ni kuwa na се “Ke kika dauko su ma, ai
ba ke kike biyan su ba, kuma iko yanzu na fara shi tun da ina auren maigidan". Maryam ta ce “Ahayye! Me Kwacen miji, me ya hana ki auren naki?"
ISBN 978- 2149 - 69 -1
GIDAN DABINO PUBLISHERS
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels