yarda a raba ki
da 'ya'yanki a kan kishin banza da wofi, ki zauna ki riki 'ya'yanki
shi ya fi miki" "Sallamu alaikum" Sallamar Yaya ce tun da ga
zaure, take wannan sallamar ta katse min jijiyoyin jikina saboda
tsinin sautin muryarsa. Yana shigwa cikin gidan wani kamshin
turare ya gaureye harabar tsakar gidan, su Nusaiba sukayi wajensa
da gudu suna cewa "Baba, Baba" ya sunkuya ya dauki Sa'ima, ya
zo ya tsaya a gabana yana yi min murmushi, na yi murmush na ce
"Sannu da zuwa yaya". Ya lumshe ido ya ce "yauwa!" Sannan ya
juya gun Nusaiba yana tambaryar ta yaushe suka zo, Nusaiba ta ce
12
"Yanzu muka zo tare da mamarmu" Sai na ga ransa ya dan baci
amma bai nuna sosai ba, ya wuce falon Inna, ya yi sallama ya shiga.
Bayan sun gaisa da Inna, Ina ta fara yi masa bayanin abin da Maryam ta ce wai sai dai ya debi yara ya tafi da su England, in ya
so ita ta zauna ita daya. Yaya ya ce Inna ba za ta yiwu ba, ba inda
zan debi yara naje da su, wa take nufin zai kula mata da su, Rukyya?, Ai wanda ta yi mata a da ya isa, yanzu Rukayya fi karfin
ya ta miki renon 'Yaya'. Maryam ta taso za ta fara magana Inna ta
dakatar da ita, ta ce. "Tsaya Maryam, in yaran ba ku so ku ba ni ai
ni ina so, 'yan yaran guda biyu za ku zauna kuna surutu a kan su. To
na yanke magana ka debi yara ka tafi da su England, ni na tabbatar
Rukayya ba za ta ki rike su ba". Yaya zai yi magana Inna ta ce "Ва
na son jin wata magana na kashe wannan, Allah kuma ya kare na
gaba. "Dole dai Yaya ya hakura da tsarin da Inna ta yanke, ba wai
don ransa yana so ba. A ranar dai har karfe takwas na dare Yaya
yana gidan Inna, duk dai yana tare da jama'a yana sauraron
bukatunsu. Bayan sallar isha ne ya samu ya kauce wa mutane ya
shigo cikin gida, a lokacin nan na idar da sallah na daga hannu ina
addu'a Yaya ya zo ya zauna daga gefena, ya ce "A dai roka da
mu", Nan naji kunya ta kama ni na sa hannuna na rufe fuskata,
Yaya ya ce "Rukayya ina Inna? "Nice ta shiga gidan Baba Ado tare
da su Saima. "Yaya ya ce "Rukayya ban so ba Inna ta yanke
wannan hukuncin wai sai na tafi da yara, ni na fi son ke ma ki tafi ki
je ki huta, ba na son kowa ya takura miki, "Na yi murmushi na ce
"Yaya ba komai ni ai nafi son ma mu tafi tare da yaran don za su rin
ga debe min kewa" Yaya ya ce "Ko za ki raka ni gidan Umar Tahir,
ma'aikacin Nigerian Airways, don saboda takardun su Sai'ma ba su
gam cika ba, kum a gobe nake son mu tafi lagos".
Mun je gidan Umar tahir a inda ya cewa Yaya gobe su hadu
a Lagos don a samu a kammala visa din su sa'ima. Misalin karfe
tara da minti arbain muka baro gidan.
Bayan mun kamo hanyar gidan Inna, Yaya ya biya da ni
Beirut road a inda muka shiga kantuna muka yi sayayyar su
chocolate da biscuits. A hanyá ne muna tafiya tamkar Yaya ba ya
son tafiyar, sai ya ce "Rukayya, muna zuwa England ina son ki ci
gaba da karatunki ko kuma ke ba ki da sha'awa kin fi son ki yi
kasuwanci "Na ce "A ina na fi son in yi karatu, don ina son na ga na
zama likita" Yaya ya ce "Kai da kyau, daman ni ma abin da nake yi
13
miki sha ‘awa ke nan" Yaya ya ce “Rukayya bare min chocolate din nan man". Na bare na mika masa, kawai sai ya bude baki wai na
sa masa, kawai sai kunya ta kama ni na ce "Yaya ga shi "ya ce "In ba za ki ba ni a baki ba to na fasalci" Na ce "Kai Yaya". Shi ma ya ce "kai Rukayya!!" Sai duk muka yi dariya, kawai ban zata ban nufa ba sai naji Yaya ya rike min hannu yana wasa da ‘yan yatsuna tare da shashshafa bayan hannuna, can an jima sai na ji ya kai hannuna kirjinsa yana wasa da shi, kawai sai ji jikina ya yi sanyi ya dibi wata rawa, na ce "Don Allah Yaya ka sakar min hannu ka ga fa tukin mota kakeyi, “ Yaya ya ce "To mene ne Rukayya? Don na kama hannun matata ai ba wani abu ba ne”. Ni dai na kwace hannuna daga cikin nasa. Ya juyo ya kalle ni ya ce, "Lallai ina da aiki a
gabana Rukayya”.
Kafin mu tafi Legos don tafiyar mu England sai da Yaya
ya tabbatar va kintsa gidansa ya tabbatar duk wani abu da Maryam
za ta nema na fannin hidimar gida sai da ya bar mata, duk wata karya da ta san za ta yi ta yi don ta karbi kudi a hannun Yaya, ya
kuma dauka ya ba ta, don dai kada ya tafi ta ce bai bar mata kudin
cefane da na kashewa ba da sauran hidimomin kanta, sannan kuma
ta dawo ta ce Sadiq ka san fa ciki ne da ni in ka tafi kuma ka san
zan fara zuwa asibiti Yaya ya ce "To Maryam, batun zuwa asibiti (Clinic) ai ba sai kin gaya min ba, tun da daman ina sane da cikin kuma na san dole ne ki je asibiti, tun da ga motar kina nan ta ishe ki
zuwa, amma fa ba ni son yawo, don haka duk inda za ki ba ya ga linic] ki aika ki tambayi Inna in ta amince to sai ki je. Ko kina da
ni abu, da za ki ce ne? "Maryam ta ce "Babu, amma ai ka san
ma [clinic] din ana karbar kudi ko? yace "Kai Maryam, duk din nan da na ba ki ba su isa a je asibiti ba har sai na karo wasu;
o in kin je su yi bill din komai a cikin [file] fayel dina In na dawo zan biya ko nawa ne”.
Yaya ya ce “To ni zan tafi, ina fatan ba wata matsala Don Allah aMaryam ki kula da kanki da gidan kuma a rinka rufe kofar gida, da wuri, ba na son yawan yawo".
Jirgin karfe goma muka shiga zuwa Lagos da ni da Sadiq da Nusaiba da Sa'im, misalin karfe sha daya tuni mun tsufa a
Lagos, mun sauka a gidan saukar baki na Ma'ai katar su Yaya, gida
ne mai dakuna hudu, sannan da katon falo a tsakiya da kicin, kai gida ne dai mai kyau.
Tun da muka isa Lagos, bayan Yaya ya kawo mu gidan
mun ci abinci, ya ce zai tafi wajen Umar Tahir batun Visar su
Sa'im, Sadiq bai dawo gida ba sai misalin karfe goma na dare, a
lokacin nan mun shiga daki muda su Sa'ima muna kallon fim a sky
movies, dukkan mu muna zaune a kan gado, Sa'ima tana kwance a
kan cinyata tana cewa "Anty Rukayya zan sha belinco Yogout, "Na
ce To Sa'ima bari na dauko miki, ai da akwai a cikin fridge"
Na sauka daga kan gado na bude fridge na dauko Belinco Yoghuot
a cikin robar sa, ya yi sanyi, na zuba mata a kofi na mika mata, ta
kurba ta ce "Kai anty amma wannan Yoghout din tana da gardi ga
zaki, anty kamar ta fi dukkan wata Yoghout da na taba sha dadi,
nayi murmushi na ce "kai Sa'ima ban da santi dai, ai sai ki gaya wa
Yaya kullum ya rinka sayo miki belinco yoghourt""Salamu
alaikum" Yaya ne ya yi sallam tare da turo kofa ya shiga, muka
amsa masa sallamar tare da yi masa sannu da zuwa.
Yaya ya ce "Yaya na ga har kun shigo daki tun da ga yanzu, ba dai
har za kayi barci ba? Na ce "A a, mun dai gaji da zaman falon ne shi
ne muka shigo daki don munga nan ma ai da akwai talbijin sai mun
yi kallon mu kawai".
Yaya ya ce "Ina fata dai kun ci abinci "Na ce" Mun
mana ai kukan ya zo ya yi abinci, naka ma yana nan bari na ka
maka "Yaya ya ce "To kawo".
Na kawo masa abinci na ajiye a kan kafet, ya zauna ya ci, sannan
ce na zuba masa belinco yoghout, na zuba masa ya sha, yana ba t
labarin visar su Nusaibu, ya ce Har yanzu ba a samu ba don a
samu "yan matsaloli a ofishin da suke ba da visar don gwamnat!
tana tuhumar su da ba da visa ba bisa ka'ida ba. Amma nan d
kwana uku ko hudu wata kila za a sama musu visa." Nace To Allah
ya sa a sam. Bayan yaya yaci abinci ya gama na kwashe kwanukan
na kai su kicin.
15
Ina zaune a bakin gado Sai'ima ta zo ta kwantar da kanta a
kan cinyata tana son ta ji barci, sannan Nusaiba tana daga gefena
tana kwance, Yaya yana zaune a bakin madubin kwalliya (dressing
Mirror) yana kallo na, duk motşin da na yi a kan donsa tamkar bai
taba kallo na ba sai yau, wanda har ya sa na rinke jin jikina yana
kyarma.
Nusaiba ta ce Anty Nace, "Na'am ". To ce "Anty kin ce za
ki yi mana tatsuniya yau in mun zo kwanciya." Na ce "To ai yanzu.
kin ga kallo muke yi ko? "Yaya ya ce tun da dai an ce za a yi musu
ai sai ayi musu, ni ma ina son ji". Na ce "To ai ni yanzu na mance
wace tatsuniya zan yi, sai ko gobe Ina tuno", Yaya ya ce " To shi ke
nan, ni bari na yi muku ki ji, Yaya ya yi musu tatsuniya kamar guda
biyu sannan ya ce "To ya isa, dare ya yi ku yi addu'a ku kwanta ku
yi barci sai da safe". Yaya ya lumshe idanunsa ya ce "Rukayya
barci nake ji” Ni dai na yi shiru ban ce komai ba. Yaya ya sake
maimai tawa, "Rukayya zan je in kwanta". Ni dai ban daga kaina
ba, sannan ban ce masa komai ba, Yaya ya tashi ya yi murmushi,
ya bude kofa ya tafi dakinsa, ni kuwa a gaskiya ina jin kunya shi ya
sa na noke na yi kwanana a dakina tare da su Nusaiba.
Da safe bayan na yi sallah na yi wanka na yi kwalliya da
wani less fari mai filawowi da 'yan duwatsu a Jikinsa, na daure
gashina ya kwanta a bayana tamkar wata 'yar karamar yarinya
sannan na yi wa su Nusaiba ma wanka da kwalliya mun fito mun
sami Yaya a falo ya shirya, yana sanye da kufta da wando na
shudiyar, shadda kuma ina jin sabbi ne. Na rusuna na ce " Yaya ina
kwana? "Ya kalle ni sannan ya amsa, ya ce "lafiya", Su Nusaiba ma
suka gaishe shi.
A lokacin nan kukun gidan yana yi mana abincin karin
kumallo.Bayan ya gama, muka hadu har da Yaya muka ci. Da muka
gama cin abinci Yaya ya ce zai fita damma zai dawo da wuri, don
haka mu shirya zai zo ya kai mu yawo.
Da yama ne muka fita yawo da Yaya a inda ya kai mu
beach don mu yi kallon ruwa, a inda muka shiga ruwa, muna
wasanni da kwallo, yaran suka yi ta wanka a cikin ruwa. Bayan mun
fito kuma muka zauna a cikin lema muna shan ice- cream tare da
‘yar hira a tsakanin mu. Ba mu bar bakin beach ba sai da aka fara
kiran sallar magariba sannan muka nufi masaukinmu.
16
A masaukinmu, bayan mun yi sallar magariba da isha muka
hadu da Yaya muka ci abinci da kuku ya girka mana, sannan muka
zauna kallon setlite, shi kuma Yaya yana ta waya da abokansa,
daga baya koma ya koam karatun jaridun ranar. Can bayan ya kare
karatun sa ya ce' 'Rukayya don Allah a hada min tea cup daya tare
da cake ki kawo min daki na "Ya tashi ya nufi dakinsa ba tare da ya
kalli fuskar ta ba' Na je na hada masa tea na kai masa na yi sallama,
Yaya ya ce "shigo, haba Rukayya, mutum da dakin mijinsa amma
ya rinka sallama."
din in fita Yaya ya riko hannuna ya Na ajiye masa tea zan juya
dawo dani cikin dakin, ya ce "Haba antinsu Nusaiba, in kuma ba so
ake'a rikita min kwakwalwata ba ai yakatama a ji tausayina haka, ai
jan ran kuma ya isa. Idona yana kallon 'yan" yatsun kafata, duk
kunya ta lullube ni na rasa inda zan sa raina don kunya sai kawai ji
na yi Yaya ya janyo ni zuwa jikinsa, ya shiga sarrafa ni iya son
ransa, tun muna tsaye sai na ji tsayuwar tana neman ta gagare mu,
na yi dabara na karbi kaina da kyar, ina murmushi, na kalli Yaya
duk idanunsa sun kada sun yi ja, Yaya ya ce "Rukayya me ya sa
kika kwace kanki daga gare ni? "Nace Haba Yaya, ka san fa su
Nusaiba idon su biyu ba su yi barci ba kuma suna nan a falo. "Yaya
ya yi murmushi yace "anty su Nusaiba kin fison su Nusaiba a kan ni
ko? na yi murmushi na ce haba Yaya ai ka san su yara ne Yaya ya
ce "To ai yan kan za a fi tausafina ta yabni kwanan don inayin
tsoron kwana ni daya, yiyama daure wa na yi " Na kale shi kawai na
yi girgiza kaina. Yaya ya ce "To muje wajen su Nusaiba tukunna"
munje mun samu yaran har sun yi barci, Yaya ya dauki Nusaiba ni
kuma na dauki Sa'ima muka hada su a dakinsu muka kwantar
sannan muka kashe musu wutar lantarki tare da rufe musu kofa.
Tun daga kofar dakin nan Yaya ya dauke ni cak har gadon
barcinsa, ya kwantar da ni, ya zauna a bakin gadon yana kare min
kallo tun daga kasa har samana, ya yi ajiyar zuciya, ya ce "Rukayya
ya kamata kafin komai ya wanzu a tsakaninmu muyi sallah raka'a
biyu wadda Annabi ya kwadaitar da dukkan ma'auratá suyi don
samun zaman lafiya tare da samun zuri'a ta gari" Bayan mun yi
sallah muka kwanta don yin barci, Yaya ya janyo ni jikinsa, na ce
"Yaya ba ka ce in taya ka kwana ba ne kanajin tsoron kwana kai
daya,?" Yaya ya yi dariya ya ce E, amma kin san tsoron bai fita a
17
jikina
da
sai in na jiki a jikina sosai tukunna." Dukkan mu muka fashe dariyar rikita, yaya ya kashe fitilar da take jikin gadon. Sai da safe na farka na tashi na yi wanka, na zo na tashi Yaya, na ce "Yaya za ka makara Yaya ya yi salati, ya ce “Rukayya ya aka yi kika riga ni tashi, ni ina cewa ni zan tashe ki "Na yi murmushi na ce "Ai Yaya, ka san an ce niyya ta fi kwanan masallaci". Ya ce "Kwarai kuwa" Ya tashi shi ma ya shiga bandaki don ya kintsa ya zo ya yi sallah. Bayan mun idar da sallah na rusuna
na gaida shi ya amsa min tare da juyowa yana yi min murmiushi, ya ce "Rukayya kin shayar dani farin cikin da ba zan taba mantawa da shi ba a rayuwata wanda sai dai in ce Allah ya yi miki albarka, tare da fatan zuri'a ingantacciya daga gare ki, daman abin da ake nema daga kamilar mace ke nan." Kunya ta kama ni na sunkuyar da kaina ina murmushi Yaya ya zo ya sa hannu ya dago fuskata ya shiga kissing dina, can na cira fuskata na ce "Yaya bari na je na dubo su Nusaiba ko sun tashi daga barci."
S Yaya ya ce "Haba, ai ba su farka ba bar su kawai ai kanwa
muke nema masu", "Na ce kai Yaya." Ina dariya na fice daga dakin.
Tura kofar da na yi shi ya tashi Nusaiba daga barci, na ce "Nusaiba kin tashi ne?”", Ta ce "Anti yanzu na tashi." Na ce, "То
maza a tashi a yi sallah ko, tun da an tashi daga barci" Bayan sun yi
sallah ne na yi musu wanka tare da shafa mai na sa musu wasu riga
da wando dinkin Indonesia, wadanda sun yi musu kyau sosai,
sannan nima na yi tawa kwalliyar na fito a cikin wando da riga
dinkin kasar Dubai, a gaskiya kayan sun yi min kyau, don ina shiga
dakin Yaya ya dago ya kalle ni ya ce "Gaskiya amarya kin yi kyau,
kayan sun burge ni". Na ce "Allah Yaya" ya ce "Zo na tabbatar
miki kwalliyar ta burge ni" Ya janyo ni zuwa gare shi. Na ce "Yaya
na fa shirya breakfast kuma ka ce min za ka fita da safe don batun
visar su Nasaiba" "E haka ne, amma Rukayya in ina kallon ki sai in
ji har tsigar jikina tana tashi don tsananin son da nake yi miki,
amma zan zo in an jima mu fita don ina son mu yi celebrating din
wannan ranar don bai kamata mu bar ta ta'tafi a haka ba; Yakamata
mata mu sami wani abin da za mu rinka tunowa da ita a
kodayaushe". Mun fita mun hadu a dining tebur duk har da su
Nusaiba muka yi breakfast. Bayan mun gama, na yiwa Yaya rakiya
har bakin mota sannan na ce a dawo lafiya, ya ce "Allah ya sa," Ya
kara da cewa "ki zauna da shiri in an jima fa zan zo mu fita".
18
Misalin sha biyu na rana Yaya ya dawo, ya ce. "To kin shirya mu fita ko ?" Na dauko jaka ta da gyale wadanda suka dace da kayan, na rataya, muka fita tare har da su Sa'ima. Yaya ya biya da mu gidan wani abokin aikinsa, Alhaji Sulaiman Hafiz wanda su
ma sunzo hutu ne Nijeriya tare da matarsa kubura da Yayan su
sa'oin su Nusaiba, muna zuwa su Sa'ima suka hadu da su Jalila da
Humaira suna ta wasan (computer game) tamkar sun san juna, a nan
ni ma na sami Kubura muna ta labari, don ita ma mai son mutane
ce, a nan na tabbatar na sami abokiya ko da mun je London. A nan gidan muka bar su Nusaiba, muka fita ni da Yaya ba mu tsaya a ko ina ba sai a Lagoon Restaurant wanda yake a Ozumba Mbadiwa
Street, babban restaurant ne, ga kyau, sannan ta ko ina iska tana
ratsawa cikin sa kuma duk wani abu da ake cikin restaurant din anyi
masa ado da ja da farin launi sannan kujeru da teburan su ma cikin
launin ja da fari da baki, kai gidan cin abincin ya hadu sannan suna
girka abinci ne irin namu na gida Nijeriya da na Chinese da kuma
na Lebanese, amma da za mu ci abincin mu a bakin ruwa muka
zauna aka hadu mana lunch dinmu irin hadadden abincin lebenese.
Muna cin abinci muna hirarmu, a nan Yaya yake shaida min wai ya
sami visar su Nusaiba don haka gobe kamar yanzu mun yi nisa a
cikin gajimare. Na ce "To Yaya, Allah ya nuna mana goben". Yace, "Amin". Yaya shi yake debo abinci yana bani, ni ina ba shi a baki.
Da haka muke cin abincin, Yaya ya ce; Wai shin antin su Sa'ima
tun yaushe kika ji kina sona a ranki?" Na yi murmushi na ce "Ai
Yaya kai zan yi wa wannan tambayar don da kai tayi daidai". Yaya
ya ce "E; haka ne, amma ni ina jin na fara son ki ne tun lokacin da
aka maido da ke wajen Inna Sa'a, amma a lokacin nan na dauki abin
ne kamar son kuruciya ne amma daga baya, bayan na kamala
karatuna na sakandare sai na ga ba haka ba ne, don a kullum karuwa
son ki yake yi a cikin zunciyata, shi ya sa ma na ce ki zauna a
gabana don kada wani ya yi min fin karfi".
"A gaskiya Rukayya Allah ya kasha ya ba ki don tunda
nake ban taba jin son wata ya mace a zuciyata in ba naki ba. Ina son
ki fahimce ni, na san za ki ce to ai ina da wata matar, abin nufi a nan
shi ne, kin san so daban kuma kauna daban, sannan rikon amana
daban, don haka sai ki yi kokari ki tarairaye ni don cim ma burin
rayuwarki ta duniya da lahira baki daya, ni dai na zama rakumi da
akala sai Rukayya. Kai har Yaya ya rinka ba ni tausayi yadda yake
19
Zayyana min irin son da yake yi min, tamkar ni daya ya mallaka a
duniya bai da kowa sai ni, kai Allah ya bar mu tare da 'ya'ya har
karshen rayuwarmu.
Bayan mun kare cin abinci muka fito don mu tafi, Yaya ya
biya su kudin. Da akwai wajen sayar da pizza da sweets a bakin
gidan cin abincin amma ba mu da bukatar shan alawa, sai muka
wuce muka nufi Victoria Island, don zuwa gidan tariha dar da zuwa
kantunan da ake saida kayayyakin tarihi, irin kayayyakin sassakesassake, da kayayyaki irin na jima. Mun fara zuwa African pride
and craft of Nigeria a Ilasan market wanda yake a jakande hausing
estate, sannan muka wuce zuwa Time Art Gallery, duk dai a
Victoria Island sannan daga karshe muka wuce zuwa out of Africa a
kowane kanti mukan yawata mu ga irin kayayyakin tarihin da suke
da shi, ba dai wani abu muka saya ba tun da dai mu da muke kan
hanyarmu ta tafiya, amma mun sayi 'yan kananan abubawa na tarihi
wadanda za su rinka tuno mana da wannan ranar.
Misalin karfe takwas da rabi ne muka nufi Imperial
Chinese Restourant don yin dinner, wanda shi ma yana nan a
Victoria Island din.
Ba mu koma mun debi yara a gidan Alhaji Sulaiman bá sai
misalin goma da rabi na dare muka je muka samu har sun yi barci
na dauki Sa'ima, Yaya ya dauki Nusaiba, muka yi wa mutannen
gidan godiya, muka yi musu sallama a kan sai mun hadu a London.
Mun isa gida na wuce na shiga bandaki na yi wanka na fito, Yaya
ma ya shiga ya yi wanka, ina shirin kwanciya, bayan na sa rigar
barci na, Yaya ma ya fito ya yi shirin kwanciya a cikin kayan
barcinsa pyamus.
Mun kwanta muna shirin barci, Yaya ya sa min wata
rigimar wanda a lokacin nan ba abin da nake so irin ya barci na yi
bard don shi nake ji, na ce " Haba Yayana ka bar ni mana na yi
barci don na gaji " Ya ce a haba Rukayya so kike na hadiye raina ne
saboda ke? Kin san fa tun da rana na matsu da ke amma na yi
hakurin wannan lokacin, kuma" Sai kawai naji ya jiwo da ni gaba
daya, to Yaya zan yi, dole na karba masa, kuma na san a ranar na
biya shi dari bisa dari (100%) don na lura Yaya ma ya yaba mina
fuskarsa.
Ranar goma ga watan janairu muka doshi hanyarmu ta
zuwa England, mun shiga cikin jirrgi, bayan mun sami waje mun
20
zauna, jirgi ya tashi ya daidaita a sararin subahana, na raba jikina a
gefen jikin Yaya na shiga barci ina rama barcin da banyi ba na
kwana biyu. Yaya ya dauki kwat dinsa yayi min mayafi da ita.
Ban farka ba sai da muka isa babben birnin England, wato
London, na ji cikin butun magana ana yi mana mabara da zuwa
London. wato a Heathrow airport.
Bayan duk an gana wani cuku- cuku da ya
kamata a yi mana a filin jirgi, Yaya ya nemo mota ta debe mu tare
da kayanmu sai gidan Yaya wanda yake zaune a Elephant and
castle, a kudu maso yamma a layin peckham High a nan cikin
London.
Zaman London dai ko ban fada da kowa ya san zama ne
mai matsayi tare da jin dadin rayuwa tun da dai ba ruwan wani da
wani, in ba dalili ta yi ba, jin dadi na duniya ba irin wanda Yaya bai
nuna min ba, don wani lokacin in yana yi min wasu abubuwan
soyayya sai inji kamar ni kadai ya mallaka bai da wata matar, duk
wani waje na shakatawa Yaya ya kai ni, ni da yara.
Muna da wata daya a London Yaya ya yi kokari ya nema
wa yara makaranta, ni ma ya sama min makaranta, amma ba karatun
likita nake yi ba, na canza layi zuwa na'ura mai kwakwalwa, wato
(computer).
Wajen cin abinci na Onbalende suya restourant
yana daya daga cikin wuraren da muka fi zuwa da Yaya don cin
abinci, saboda yana kusa da gidanmu, kuma waje ne na dan
Nijeriya, sannan suna girka abinci irin namu na Nijeriya, kuma
matattarar 'yan Nijeriya ke nan a London, don duk wani dan
Nijeriya in dai a London yake da zama ko kuma ya kai ziyara. To
lallai kuwa zai je cin abinci Obalende suya restourant.
Duk bayan sati biyu Yaya yakan yi sakon kudi da sulura ga
mahaifiyarsa da kuma Maryam, don cefene da sauran hidimomin
gabansu. Sannan a koyaushe yana cikin yin waya, don ya ji lafiyar
gida kuma ya tabbatar komai yana tafiya yadda ya kamata.
A ranar wata juma'a ne bayan an sauko daga
masallaci, muna gama cin abincin rana, Yaya yace ya kamata yau
kam mu kai wa Sulaiman Hafiz ziyara gidansa tun da sun zo mana
kusan sau uku amma mu ba mu je musu ko sau daya ba. Mun shirya
mun je gidan Alhaji Sulaiman da matarsa Kubura, gidan su wanda
yake a anguwar Dolston a karshen gabas da garin handon Dolston a
21
karshen gabas da garin London, Unguwa ce wace