Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 7
ta kunshi yawancin 'yan Nijeriya sai kuma Girkawa, a nan muka sha yinin mu, don Sulaiman yana daya daga cikin manya- manyan abokan Yaya, haka ni ma na amince wa zuciyata, Kubra ita ce babbar aminiyata a London. Da daddare ne bayan na kintsa yara a dokinsu na yi musu brush na yi musu wanka kowa ya sa rigar barcinsa, sannan na ce su yi addu'a su yi barci sai da safe. Na kasha musu lantarki tare da rufe musu kofa, sannan na nufi dakin maigirma Abubakar Saddiq na shiga da madara a cikin kofi, na ajiye masa kofin, ya gama lazumin da yake yi ya sha don madara tana, daya daga cikin abin da yake sha kullum darce kafin ya Kawanta. Ina kwance, har Yaya ya gama dukkan abin da yake yi na al'adar reyuwarsa, tukunna ya zo ya kwanta kusa da ni muna hirarmu irin ta Ma'aura mai dadi, Yaya ya ce "Rukayya bana ya kamata ke ma ki je ki sauke farali don ya kamata ki je ki aikin Hajji tun da saura wata uku a fara tafiya, zan fara yi miki shirin tafiya in yaso sai ki tafi daga nan Na yi murmushi na ce" Yaya na gode, Allah ya kara arziki. Yaya kada ka sa na kasa yin barci don murna" Sai Yaya ya yi murmushi ya ce. "To kin ga kuwa in kika sami ciki kafin tafiyar ai sai dai a fasa don ba za a je a lahantamin da ba" Na ce "Haba Yaya, ai bai yi wani girma ba, abin da zai faru" "A'a ban farda ba, ko don lafiyarki". Yaya ya ce "Yauwa, daman Rukayya ina son na fada miki wannan maganar amma don Allah kada ranki ya baci, kin san dai ku biyu ne ke da Maryam ko? Kuma kin san tun da muka zo ban je Nijeriya ba, shi ne ga za ya kamata cikin satin nan na je na dubota, kin ga na bar ta da ciki, ko Yaya kika gani.?" Na ce, "Haba Yaya, wannan ma sai ka tsaya ka nemi amince wata, ai hakkin ta ne a kanka dole ka cika mata, don haka ni wallahi har ga Allah don ka je gun Maryam raina ba zai baci ba, ai matarka ce, kuma uwar 'ya'yanka Washegari na kasha zuwa Lectures dina makaranta, muka tafi sayayyar kayan tsaraba, komai wanda ya kamata a saya wa iyali, na ce Yaya ya sa ya Maryam, haka kuma duk wani abu na fanning baby na ce a saya a tafi mata da shi, sannan tsarabar mahaifiyarsa da kannensa da baba Ado da iyalinsa. 22 Yaya ya tafi Nijeriya ya bar ni ni da Yara, amma duk dare sai ya yi min waya mun bata kusan awa guda muna hira koyaushe ya yiwo min waya yakan ce wai ya yi missing dina, sannan ya kan ce wai anya kuwa Rukayya ke kuwa kin damu da ni kamar yadda nake begen ki a kullun, don Allah ki yi ki haifa min baby wanda ya yi kama da ni, ni kuwa nakan ce to “Yaya Allah ya bamu. A cikin wayar da yake yi min ne ya shaida min wai baba Ado ba shi da lafiya har an kwantar da shi a asibiti, na ce Allah ya sauwake, ya sa zakkar jikin ce. Ranar da Yaya zai dawo daga Nijeriya na shirya masa abinci na musamman, sannan na tafi airport don taren Yaya tare da su Nusaiba da Sa'ima. Daga saukar Yaya daga jirgi muna haduwa ya kamo ni ya rungume tsamtsan, na ce Yaya ga fa su Nusaiba suna yi maka sannu da dawowa, Tukunna ya sake ni ya dauki Sa'ima, ya sumbace ta a fuska, haka ma ya yi wa Nusaiba, muka jero muka shiga mota sai gida, a lokacin nan ni nake jan motar. Don tsananin kulawa ta musamnan a wannan ranar abinci ma ni da kaina na rinka diba ina ba shi a baki yana ci, har ya koshi. Yana cin abinci ne ya ce "Rukayya ai a Kano na ci wani Special abinci, Maryam ta yi min, "A gaskiya fadin da Yaya ya yi wai Maryam ta yi masa special abinci har ya sa raina ya baci, wai shin yaushe Maryam ta ajiye kalacin nata ta iya abinci har da Yaya zai ci ya zo yana yi min santi. "Kai Rukayya na gode Allah da kika kasance mace mai tsabta da iya abinci, ai abincin da Maryam ta ba ni ranar da na sauka a Kano Kasa ci na yi, don kuwa ina deban miyar sai ga kuda a cikin abincin, wallahi har na je na dawo abincin Otal nake ci, don kuwa abincin ko an yi shi ba shi da dandano. A wannan ranar lokacin kwanciya da yayi tare muka yi wanka da Yaya sannan na ba shi hakkin sa iya son ransa, a nan na tabbatar ya yi missing dina, komai yana tafiya yadda ya kamata tsakanina da mijina, duk abin da na san ai dadada wa mijina rai shi nake aikatawa, wato yin na yi, bari na bari, sannan ladabi da biyayya, duk kuma abin da na san zai bata 23 masa rai tsakanina da shi katangar karfe, ba ni taba aikatashi ko da wasa. Bayan sati daya da dawowar Yaya daga Nijeriaya aka yiwo masa waya aka sahida masa jikin baba Ado ya tsananta don har an sake mai dashi asibiti. A nan Yaya ya yanke shawarar mu tafi tare mu je dubo shi, tun da ana hutu a makaranta. Washegari karfe biyar na yamma mun sauko a filin jirgin Malam Aminu Kano, mun sami diręban Yaya wato Usman yana jiran mu a filin jirgin, mun wuce zuwa cikin gari gidan Inna Sa'a, amma tun daga kofar gida ganin taron mutane ya tabbatar mana da cewa baba Ado ya rasu, sai mu ce Allah ya jikansa, mu kuma Allah ya kyauta namu karshen in ya zo. Na wuce cikin gida tare da yara na bar Yaya yana gaisawa da mutane a kofar gida, cikin gidan ma a cike yake da mata, duk ana ta sharbar kuka ni ma na shiga cikinsu, na yi wa iyalen mamacin gaisuwa tare da addu'ar Allah jajikansa. Kwanan mu bakwai muna zaman makakin mutuwar baba Ado, ina nan zaune a gidan Inna Sa'a don ban tare na tafi gidan Yayà na Sani Mainagge ba. Yaya ya shigo gida bayan sun gaisa da Inna, ta sake yi masa gaisawa, sannan suka shiga labarin irin zaman da aka yi da baba Ado, mutum mai mutunci da riko amana ga hakuri, a zamanin yanzu samun irin su baba Ado da wuya, To sai dai mu bi shi da addu'a, shi kadai ya rage a tsakanin mu da shi. Bayan sun gama hirar su da Inna, Yaya ya shiga daki inda nake kwance ya same ni, ya ce "Madam, ai ya kamata ki shirya mu tafi gida ko, na fara 'yar gardama don ba na son zuwa Sani Mainagge, ba don komai ba sai don masifar Maryam, amma Yaya ya ki amincewa, dole na shirya muka kafi. Mun isa gida, Yaya ya bude min daya sashen da yake rufe na gidan, ya mallaka min, ya ce,. "Wannan shi nehe sashen kwanana sai na wuni a gidan ban ga idon Maryam ba ita ma ba ta ga idona ba, kowa yana shiyyarsa, a kwana na biyu ne a cikin gidan da dare ina kwance na ji ana buga min kofa, na farka daga a barci, a tsorace, na ce "Wane ne" Sai na ji Murya Yaya yana cewa, "Rukayya bude". Na byde kofa na ce "Yaya lafiya kuwa," Ya ce Lafiya, yanzu na kai Maryam asibiti, ta haihu, ki zo ki yi mata shayi "Nace "Yaya Maryam ta haihu, mai ta Haifa? "Ya ce Mace" Na ce "Allah ya raya "Yace, kin ga na sami Rukayya Junior", Na ce, "Kai Yaya kada ma 24 ka fara wannan hadin" Ya ce "Allah Rukayya zan sa mata, don har na yi mata hudu ba ma da sunanki daga haihuwarta" Na ce " Tо Allah ya sa ta amsa sunanta," Ya ce "Amin" Mun isa asibitin, muka sami Maryam a kwance a kan gado ita mayar a kwance a kan gadonta, na leka na gan ta na yi wa, Maryam sannu na gaishe ta; amma Maryam ko ta daga kai ta kalle ni sai dai ma hararata da ta yi. Yaya ya ce na hada mata shayi amma Maryam ta ce wai ita ba za ta sha ba, sai da Nurse ta zo ta hada mata ta ba ta sannan ta sha, Yaya ya yi wa likita magana a kan ya sallami Maryam, tun da dai ita da jarriyarta duk lafiyarsu kalau. Likita ya rubuta mana takardar sallama muka tafi gida tare da Maryam jaririyarta. Bayan mun dawo daga asibiti ne, gidan mu ya cika da baki duk kannen Maryam suka zo, su Amina da Farida da kuma Fa'iza, sannan da iyayenta, haka ma, su Yaya Ai'sha da Maimuna da Hadiza su ma sun zo. Gidan ana ta aikace - aikace saboda baki don Yaya ma ya yi baki abokansa daga Sokoto, don haka mun hadu har da masu aikin gidan muna ta girke - girke. Kannen Maryam duk inda na juya sai harrara ta suke yi, ni kuwa a cikin raina na ce "Oho dai, ku kuka sani kuma." * Ana sauran kwana uku suna Yaya ya zo ya same ni a dakina, ya ce na yi masa lissafin duk abubuwan da za a bukata na suna, sannan da wanda za a yi na kauri don ya ba ni na je na sayo komai da komai, Na ce, "Yaya ba haka za ka yi ba, ka samu mai jego ita ta san irin abubuwan da take bukata na hidimar sunanta, ko kuma ka kira Yaya Ai'sha ka ba ta ta sayo komai da komai tun da daman ita ce mai hado kayan hidimomin suna a kowane suna in Maryam ta haihu". Ya ce "To yanzu ban ga damar kiran Aisha ba ke na ga damar sawa, ko ba za ki yi ba?". Na ce, Yaya zan yi mana, "Ya ce" In ke ce kika haihu ai Maryam ce za ta yi komai na hidimar suna, ai 25 magana, ya ce; "Na tara ku ne ba don komai ba, sai don na yi muku magana a kan abin da ya faru yau, ina son in sanar da ku cewa, ba zan dauki fada a gidana ba, don haka wannan ya kasance na farko kuma na karshe, ku yanzu baku jin kunya a ce wai matana da girma na da mutuncina a ce wai kuna fada har da kokawa, wannan ai rashin mutunci ne. don haka ku sani, ba zaman fada na tara ku mu yi ba, zaman lafiya na tara ku mu yi, kun ji ko, don haka ku yi sulhu a tsakanin ku tun daga nan". Sai a nan Yaya ya numfasa ya bar magana, ya tsaya yana kallon mu,... Maryam kuwa don tsaurin ido sai cewa ta yi "Yo ai fada kai ka janyo a yi a gidan ka, tun da ka auro Rukayya, kuma yanzu aka fara fada tun da ba zan dauki isa da mallaka da iko ba". Yaya ya ce, "Maryam, ina magana kina maida min don kin mai da ni ban isa na yi muku magana ba ko? To sai ki yi abin da ka ga ya fi zamar miki alheri a gare ki, ai ke za ki sha wuya ni ba ruwa na". Da dai na ga ran Yaya ya baci sai na kwantar da kaina, na ce, Yaya ka yi hakuri in Allah ya yarda irin haka ba za ta sake faruwa ba". Maryam ta kalle ni ta ce "Kinibibi kawai, to tun da ya zama mijinki menene na ce masa Yaya Ai sai ki kira shi darling kawai" Na kalle ta na yi murmushi cikin kissa, na rangwadar da kai, na ce "Mantuwa ta sa na ce masa Yaya, darling ka yi hakuri... "maryam ta doka tsaki ta fice ta bar dakin. Yaya ya daga kai ya bi ta da kallo yana girgiza kai. Cikin rana kunnan kafin suna, muna ta harkar arziki ni da mifjna, yadda Maryam ta tsame hannunta daga al'amuran Yaya shi ma ya yi burus da ita. Ranar suna ta zo aka rada wa jaririya sunana, wato Rukayya; wai --wai-wai ranar nan Maryam tamkar za ta kasha kanta don bakin ciki, ita da kannenta. Don haushi ma lunchin da aka hada za'a yi Maryam kin halartar wajen ta yi. Ni kuwa tare da kannen Yaya da aminansu, tare da bakin da Inna Sa'a ta gaiyato, zuwa matan bokan Yaya. muka kayatar da liyafar, ga kuma Barmani Coge ta zo, ina rawa, Yaya ya zo ya dinga yi min likin wazobiya. Haka dai muka sha hidima har biki ya watse. Bayan suna da kwana uku muka tattara ya namu ya namu muka koma England. Zama da kishiya abu ne mai wuya don ni ba an sami mace mai hakuri da wayo da kuma iya kissa, ba to kinaji 27 kina gani sai a raba ki da mijinki kuma ba yadda kika iya, don wani abin in za a yi miki ba za a yi miki yadda za ki gane ba, ta bayan danga za a yi miki, wato kisan mummuke. Haka dai muka kasance da Maryam, ina London amma tana shirya min mugunta a Nijeriya daman tun da na je Nijeriya Hadiza take sha da min ko da malamai sai ta fitar da ni daga gidan Sadiq, don haka kullum tana hanyar gidan bokaye da malamai. Amma wai Inna Sa'a ita ma ta tsaye a akaina ni da Yaya, tana nan tana taimaka mana. Bayan mun dawo daga Nijeriya ne da wata daya muka tafi Makka ni da Yaya don aikin Hajji. A can Saudiya ne aka tabbatar min ina da ciki na wata daya, wanda Yaya ya muna min farin cikinsa wanda ba zai iya misaltuwa ba. Bayan mun dawo daga aikin Hajji na fara shiga wasu 'yan matsaloli a tsakani na da Yaya, kamar yadda na gaya muku duk wata, Yaya yakan aika wa Maryam kudin cefene da sauran hidimomin gida, to haka ne, amma Maryam duk lokacin da ta bushi iska sai ta yi wa Yaya waya ta ce tana bukatar kudi za ta yi wasu hidimominta na daban, Yaya ko duba nawa ne ba binci ke, haka zai dauki ya aika mata, in na yi magana sai ya ce wai ni bai aika ba yanzu sai ya zame masa masifa shi da ita, shi kuma ba ya son abin surutu. To amma in ni ne na ce ya ba da kudin cefane ko na wata hidimar gida sai mun kai ruwa rana, kafin ya bayar ya dinga cewa, wai yaushe aka yi cefane har ya kare, ko kuma Rukayya kin cika kasha kudi, da dai sauransu. Wannan ya dada tuna min da wata rana na dawo daga makaranta, na zo na sami Yaya a gida ya dawo daga wajen aiki, nace, Yaya "Yau har ka tashi daga wajen aiki?" Yace "Wallahi ban tashi ba check book dina nake nema na bankina na Nijeriya, Inland bank, ko kin gan shi?'! Na ce, "Ai yana cikin Jaka a rufe;" Na je na bude na dauko masa. Ya ce "Yauwa, daman Maryam ce ta yiwo min waya, wai wannan satin za a yi bikin kannenta, shine ta ce na aika mata da kudi don za ta yi sayayya, "Na kale shi kawai na ce "To!" A gabana ya rubuta mata check din zunzurutun kudi Naira dubu dari biyu, ya aika mata. To me zai faru" Washegari ne muna cin abincin dare, na yi kwalliya da wani skirt da rigi, wannan dai shigar Turawa ce, Yaya yana ta yabon kwalliyata, sanna yana ta ji da ni, yana ririta ni. 28 Bayan mun gama cin abinci muna zaune a falo muna kallo, na ce "yaya ya kamata mu je yau mu yi shopping, saboda kayan abincin gidan nan ya kare, kuma dama ka sani yau ne ranar da muké zuwa yin shopping." Kawai sai yaya ya daure fuska ya сe "Rukayya kin cika son kashe kudi, yaushe muka yiwo shopping a gidan nan da har za a ce sun kare?. "Abin mamaki, yaya fa a gaban yara yake cewa wai na cika barna ta kayan abinci. Da na ga abin zai yi yawa. Kuma bai kamata yana fada ina mayar masa ba a gaban yara, a sai kawai na tashi na bar masa falon na tafi daki na kwanta. Har lokacin barci Yaya ya shigo, amma bai tanka min ba, ni ma ban tanka masa ba. Ya gama komai na al-adar rayuwarsa, kamar yin wanka, da nafila dá shan madara, sannan ya kwanta, amma sai ya juya min baya, ni kaina ban iya nayi barci ba don wani abu ne mai daci yake zuwa ya dawo a kirjina. Haka shi ma yaya bai iya ya yi barci ba. Da na ga bazan iya wannan kwanciyar ba sai kawai na tashi na sa yar saman rigar barcina na bude kofa zam bar dakin, yaya ya ce "Rukayya! Rukayya" Ban dai amsa masa bai na wuce zuwa dakina na yi kwanciyata. Da safe ma ban jira yaya ya tashi ba na shirya masa breakfast, daman shi da safe madara yake sha, sai Ya'yan itace (fruits) na ajiye a kan tebur, ko gaishe shi ban yi ban na shirya su Nusaiba muka tafi makaranta. Da yamma ne bayan na dawo daga makaranta, na shiga kicin na ga an yiwo shopping an ajiya min komai da komai an sayo, har abin da ba na bukata ma an sayo. Na tambayi Esther (wato mai aikina) wa ya kawo, ta ce "Oga ne da kansa ba dan aike ba." A raina na cewa ya gaya maka Barno gabas take?". Na idar da sallar magriba ina jan carbi, Yaya ya turo kofa ya shigo dakina ya zauna daga bakin guda, sai da na yi addu'a na shafa sannan na juya nace sannu Yaya, ya ofis?. Ya ce Alhmadu lillahi yau kam". Daga nan Yaya ya ce " Kin ga kaya a kicin ko?, to ki duba ki gani in da akwai abin a ba da saya ba, sai ki fada a je a sayo" Nace to". Yaya ya ce Rukayya har yanzu fushin ne na ji ko amsa min ba ki yi ba?. Na ce "Yaya na ce maka to" Cikin shagwaba da kissa nake magana. Yaya ya ce "Haba, Rukayya, abin da bai kai ya kawo ba ki rinka fushi a kai, Yau wallahi kin hana ni sauraron meeting a ofis, don ana yi hankalina yana tunaninki, ai kwakwalwata rikicewa 29 ta yi tun da na tashi da safe na ga kin tafi makaranta ba tare da na tashi mun gaisa ba. Don Allah Rukayya kada ki sa ni na shiga wani hali a dalilin ki Na ce "To Yaya ka yi hakuri”. Sannan na ya yi murmushi ya ce. Dadina da ke ko ba ke ce da lefi da kin iya bada hakuri. Kin sa kuwa an ce matar na tuba ba ta rasa miji. a ya sa a kullum, kike kara shiga raina. Kawai sai Yaya ya janyo ni zuwa barin jikinsa. Na ce "kai" Yaya, Shi ma ya ce, Ke Rukayya." Muna dariya muka rikice a kan gado. Muna kwance ne Yaya ya ce na shirya zan yi masa rakiyar aiki zuwa China za mu yi sati daya a can, don haka sai na shirya mana kayan tafiya don gode za mu tafi, yara kuwa daman ya shirya da Sulaiman a gidansa za su zauna. Hakan kuwa aka yi, washegari muka tafi China, mun sauka a babban birnin China wato Beijin, a Yamasite, a wani babban otal mai suna, chang Hong leq hotel, yana daya daga cikin manya manya otal na kasar China. Tun da muka je China ba abin da ya dame mu sai dai in Yaya ya je meeting da yamma ya dawo mu fita yawon shakatawa, sai kuma soyayyar mu wacce ita ta fi damun mu a wannan lokacin fiye da duk wani abu na rayuwa. shida. A China ne aka tabbatar min da cewa- cikina ya shiga wata Sannan har ranar haihu wata sai da likita ya shaida min. Satin mu daya muka dawo daga China. Bayan mun dawo daga China da sati biyu, Yaya ya yi shiri ya tafi Nijeriya gun Maryam. Zuwan Yaya Nijeriya ne Maryam ta matsa masa a kan sai su je Umara tare, amma Yaya ya nuna mata shi ba shi da niyyar zuwa Umara yanzu, amma Maryam ta matsa sai sun je, amma da Yaya ya tashi sai ya biya mata zuwa Umara ita da Yaya Ai'sha da Maimuna da Hadiza da Inna Sa’a sannan da matar marigayi Baba Ado, wato gwaggo Kulu. Kodayake Maryam dai ba haka ta so ba, tun da ita dai ta fi son zuwa da oga kwatakwata. * Sanin irin zaman da muke yi da Maryam ya sa duk sati nake sauke wa kaina Al-kur'ani, sannan nafilar cikin dare wannan kullum ne ba fashi, tare da addu'ar Allah ya shiga tsakanina da 30 makiya, ba na rabuwa da wuridin ya Haiyu ya Kaiyumu, kullum na yi sallah. Sannan kullum dare nakan karanta suratul Mulk da Suratul Iklas da Falaki da Nasi, don tsari daga sharrin mutum da Aljan. Tun da muka sami sabani da Yaya yanzu in marayam ta yiwo masa sako sai ya bincika in gaskiya ne tukunna yake yi mata aiken kudi, to da Maryam ta ga haka ne sai ta canza dabara. Lokacin cikina Yaya da wata takwas na shada wa Yaya ni fa a Nijeriya zan hai fu don haka ina son na yi sayayyar kayan. Yara, Yaya ya dauki kudi. Ya ba ni wanda zan yi sayayya ta baby kuma wacce zan yi tsaraba, To me zai faru, da yamma ne Yaya ya dawo daga ofis ya ce "Rukayya don Allah ba ni kudin nan da na ba sayayya, ki yi hakuri in mun je Nijeriya ma yi shopping din don yanzu zan yi amfani da kudin." Nace "To Yaya ni na dauka shi zai yi amfani da kudin, sai cewa ya yi. "Wallahi ban san yadda zan yi da Maryam ba yanzu, wata rigima ta dauko min, wai business din da suke yi da Hajiya Hauwa shi ne kudi ya bata a wajen ta, to yanzu suna ta rikici da ita Hauwan har ta dauko mata dan sanda shi ne ta yiwo min waya a kan na taimaka na aika mata kudin ta biya". Na ce "To yanzu kudin da ka ba ni su za ka ba ta ta biya kudin rikicin da take yi yace "Haba Rukayya kin san yanzu ba kudi a wajena kuma kinsa gobe asabar ba za'a bude banki ba, kuma Hajiya Hauwan ta ce a yau take son kudinta in ba haka ba 'yan sanda za su tafi da ita, to kin ga kuwa da girma na da nmutumcina bai kamata a ce an tafi da matata" police station ba a kan 'yan kudin da ba su taka kara sun karya ba. Haushi ma ya kama ni, na rasa abinda zan ce masa, sai kawai na tashi na bar masa falon. Ina kwance a dakina ina tunanin abin yi, wai shin me Yaya yake nufi ne zai ba ni kudi don in yi shopping din haihuwa, sannan ya karba ya aika wa Maryam bayan na san karya take yi ni na san ba gaskiya take fada ba, ni fa abin da Yaya yake yi min ya fara isa ta, koyaushe sai ya debi makudan kudi yana aika wa Maryam a kan karyar banza, amma in ince nice yi magana daidai da kudin cefene sai mun kai ruwa rana kafin ya ba da kuına yanzu yana nufin ba zan yi shopping din baby ba sai na je Nijeriya tukunna? Sannan ita Maryam lokacin da take da ciki ni da kaina muka je muka yi mata shopping din haihuwa tare da Yaya. Kai ba za ta yiwo ba a ce a kan karyar banza in zauna ana kwarata ba. 31 Na yi niyyar in yi waya na gaya wa Inna Sa'a amma sai na yi tunanin ai bai kamata ba don sirrina ne zan tona. A ranar nace komai za ta faru sai dai ta faru. Da yamma ne na dauki motata na nufi loveal shopping complex, wajen mary ked wadda mun riga mun zama abokan ciniki don kullum a wajenta muke zuwa yin shopping, don haka na ce mata, ina son kayan jarirai, daga baya Yaya zai kawo mata kudin in ya taso daga ofis. Na shiga na debi kayan yara iya son raina, sanna na yi wa su Inna Sa'a tsaraba, shi kansa Yaya sai da na yi masa sayayyar kayan sawa. Na sa aka debi kaya aka sa min a mota, wanda loveal sai da suka ba ni wata motar ta rako ni da wasa kayan. Na zo na ajiye kayan a gida ba tare da' na gaya wa Yaya cewa na yi shopping ba, wanda na sayo masa kuma na jera masa a cikin carboard din sa, * "Wai shin Rukayya mai kika saya ne a loveal haka suka yi min waya wai na kai musu kudin? Yaya ne yake yi min wanna tambayar bayan kwana biya da zuwa loveal yin sayayya, na ce Yaya, shopping din haihuwa da na tsaraba na je na yi? "Ya ce "Rukayya ba na ce ki bari in na je Nijeriya sai mu yi ba tun da kudin da na ba ki na karba," Na ce "To shi ke nan Yaya in ba za ka biya ba ai sai ka bari inya so in 'yan sanda suka zo suka tafi da ni kaje ka yi beli na" ya ce wai Me ya sa ne Rukayya ba ki fahimta? Na gaya miki rigima Maryam ta shiga shi ya sa na karbi kudin na aika mata. "Na ce Yaya tsaya na gaya maka, in kai ba ka san munafuncin mata ba

Chapter 6 of 7