ba za ta ki ni ba". Duk aka debi
dariya. Inna ta ce "To in ta ki ka fa yaya za ka yi?", Yaya ya
ce, "Haba Inna, ai na san ba za ta ki ni ba, don kanwata ce"
38
Yaya Aisha cikin zumudi ta ce "Yaya wace kanwar
taka?". Yaya ya сe "RUKAYYA".
Kowa abin ya zo masa a bazata, tun ba ni ba da nake
cikin daki, sai na ji tamkar an watsa min wani abu a cikin
jikina. Kawai sai na ji wani yar kamar wuta ta ja ni. Su Yaya
Maimuna da A'isha sai cewa suke "Wallahi Yaya ka kyauta
da za ka auri Rukayya". Inna kuwa ta ce "To Allah ya sanya
alheri, kuma Allah Ya sa a yi da mu".
Yaya ya ce "Daman Inna abin da ya kawo ni garin nan
ke nan, maganar auren, ina son a daura auren jibi, wato
kanar laraba ke nan, don ranar lahadi nake son barin
Nijeriya, kuma tare da Rukayya zan tafi, ita kuma Maryam
za ta zauna nan Kano, ba zan tafi da ita yanzu ba, sai dai ta
gane kuren ta".
Inna ta ce, "To Allah ya sa ta gane din".
Yaya ya ce "Gobe zan je na sami Baba Ado na yi masa
bayanin komai in ya so sai ya daura auren".
Inna ta ce "Ni na sha'afa ma ban shaida maka ba,
kwanakin baya ya zo yana ta godiya a kan irin dawainiyar
da kake yi da shi".
Yaya ya duba agogonsa karfe sha daya ta yi, ya ce
"Kai, dare fa ya yi, ku tashi Usman direba ya mai da ku
gidajenku kada mazajenku su ce kun yi dare". Ya kawo
alherin da ya saba ba su ya ba su, suka yi godiya, sannan
suka yi sallama suka tafi. Na fito na raka su har kofar gida,
sannan muka yi bankwana.
Na dawo daga rakiyar su A'isha na tarar da Inna da
Yaya suna tattaunawa a falo, na wuce su na shiga daki na
gyara shimfidata na kwanta ina tunanin abin da ya wakana
da kuma yadda rayuwata za ta kasance a matsayin mtar
Yaya Sadik, da kuma Anti Maryam a matsayin kishiyata,
kai lallai wannan shi ne rana zafi inuwa kuna.
Ina kwance ina tunanin yadda zamana zai kasance &
gidan Yaya Sadik a matsavin matarsa wanda a da yake a
39
matsayin uban goyo na kuma wana, sannan na tambayi
kaina, shin auren Yaya Sadik kwanciyar hankali zai sama
min ko kuwa tashin hankali zai kara haddasa min don na san
wani abu ne da Anti Maryam ba za ta taba amincewa,
wannan kaddara daga Allah ne ba, kuma abin da Allah Ya
kaddara ba mai iya kare shi. To don haka zuciyata ta kasu
kashi biyu, daya tana ce min kada ki amince da auren Yaya
Sadik gara ya aurar da ke ga wani da ki aure shi ku zo Anti
Maryam ta mayar da ke 'yar borar tsakar gida. Daya zuciyar
kuwa ta ce min haba Rukayya ai faduwar gaba asarar
namiji, ki auri Yaya Sadik don ke ma ki rama abin da take
yi miki.
Kash! Mai karatu labarin RUKAYYA bai kare ba, don haka
sai mu hadu a littafi na biyu don jin yadda za ta kaya tsakanin
Rukayya da Sadik da kuma Anti Maryam. Littafi na biyu yana
kunshe da dimbin Soyayya, rikici, matsaloli da kuma sakayya
daga wajen Allah. Kada ka bari a ba ka labari, gara ka mallaki
naka na kanka.
Ku Huta lafiya.
Jummai Disina Muhammad (A'ishatu)
Tel: 09-2343393, Abuja
Area 11, Black 17 Flat 7,
Ekot Abasi Close, Garki, Abuja
KADAN DAKA CIKIN RUKAYYA 2
Ina çikin yiwa masu aiki bayanin abubuwan da za su yi sai ga Maryam ta fito da fadanta, wai ikon me zan zo na yi mata a cikin gida, har da zan zo na ba wa 'yan aikinta umarni "Sai ki bari in kin koma can London din ki yi iko amma ba a nan ba, don wadannan 'yan aikin ni na deuko su".
Ni kuwa na çe "Ke kika dauko su ma, ai ba ke kike biyan su ba, kuma iko yanzu na fara shi tun da ina auren maigidan". Maryam ta ce "Ahayye, me kwacen miji, me ya hana ki auren naki?".
40
Duk da irin wadannan wahalhalu da nake yi na gida har wata doka ta kafa mini, wai ba ni
na
da
hankali
yi mata
domın idan ta dawo daga unguwa ba
ce, duk lokacin
sannu da zuwa. Don haka dokar ita da na ji dirin motarta daga unguwa, ta dawo komai nake yi, to in tabbatar fita waje da na gudu na bude mata mota, sannan na karbo jakarta, na yi mata sannu da zuwa.
ROKAYYA
OMMAYDTSINA MOUD
RUKAYYA
NA BIYU
Jummai Disina Muhammmad
Hakkin Mallaka (M) Jummai Disina Muhammad, 2000
Ba a yarda a juyi wannan littafi ko asarrafa
shi ta kowacce irin hanya ba sai da izini
An fara bugawa a shekarar 2000
ISBN 978 - 2149 - 69-1
Kamfanin Da Ya Yi Dab'i:-
Gidan Dabino Publishers,
No. 570 S/Titi Dandago,
P.O. Box 1597, Jakara,
Kano.
Tel:-064-636839.
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, mai kowa mai
komai, wanda ya halicci mutum ya koyar da shi magana. Tsira da
aminci su tabbata ga shugabanmu Annabin rahama Muhammad
[S.A.W] tare da Sahabbansa da 'yan gidansa baki daya. Bayan nan
ina mika godiyata ga dukkan iyalen gidan:
Alhaji Babangida Mohd. Beli
Alhaji Disina Mohd.
Alhaji Idris Sale Doguwa
Alhaji Abubakar Imam
Alhaji Mohammed Sarki Beli
Alhaji Bello Maitama Yusuf
Ina mika godiyata ga Ado Ahmad Gidan Dabino da dukkan
makaranta littafin Rukayya wadanda suke yi min waya da masu
tasowa su zo don su gan ni da ido, na gode, Allah ya kara dankon
zumunci, kulawarku ita ta sake ingiza ni da son wallafa wadansu
littattafan.
Jummai Disina Muhammad [A'ISHAТ]
Tel: 07.2343393.
GABATARWA
Wannan littafi mai suna RUKAYYA, ya fito a daidai
lokacin da ya dace. Littafin wa'azi ne babba musamman ga matayen
da ba sa wadatuwa daga irin alheri da kyautatawar da mazajensu
suke yi musu, su dai burinsu a kowane lokaci shi ne su mallake
mazajensu don su dinga fifita su fiye da abokan zamansu
(kishiyoyi) ko 'yan' uwansu na jini.
Duk wanda ya karanta wannan littafi kashi na daya ya
kuma ga irin wahalhalun da Maryam ta gana wa Rukayya
(Tauraruwar labarin), idan ya karanta kashi na biyu ya ga irin
matsayin da Rukayya ta samu dole zai yarda da karin maganar nan
da aka cewa, "Abin da ya ba ka tsoro wata rana shi ne zai ba ka
tausayi".
Jummai Disina Muhammad, sabuwar marubuciya ce amma
ta yi amfani da basirar da Allah ya ba ta da kuma kwarewa da
fahimtar halaye na matan aure wadanda suke zaune gida daya da
kishiyoyinsu ko 'yan' uwan mazajensu, ta kago labarin da ya dace
da rayuwarmu ta yau da kullum.
Muna taya Malama Jummai murnar fito da wannan littafi
kashi na biyu ga jama'a masu karatu don nishadi da kuma
manazarta harshen Hausa.
A gaida Jummai
Ado Ahmad Gidan Dabino,
Shugaban Kungiyar Raina Kama,
Kano- Nijeriya.
6/6/2000
SADAUKARWA GA
Hajiya Hauwa'u B.M. Beli da Alhaji B.M. Beli da Alhaji
Disina Mohammed, da Maifata family Kaltume Habu Kudu da
Hajiya Halimatu Sa'adiya Allah ya saka wa kowa da Jannatul
fiddausi.
Ba zan manta da ke ba watau kanwata Fatima B. M. Beli,
Allah ya saka mata da alheri, Amin.
Da safe,misalin karfe tara Yaya Sadiq ya je asibiti don ya
duba Hajiya Sala mahaifiyar Anti Maryam, ya shiga asibiti ya samu
an sallamo ta, sai ya ce wa Usman direba su wuce zuwa gidan su Maryam.
Sun je gidan su Maryam, Yaya ya shiga gidan ya yi sallama, lokacin nan duk 'yan gidan suna zaune a dain mahaifiyarta,
anti Maryam ce ta-amsa sallamar, sannan ta leko, abin ya ba ta
mamaki da ta ga Yaya Sadiq ne a gidansu, don ta san ta taho ta bar shi yana fushi da ita.
Ta ce "La! Sadiq sannu da zuwa, shiga mana, "ya shiga
dakin mahaifiyarta ya gaishe da Hajiya Sala, ya yi mata jajen rashin
lafiya, bayan 'yar hira a game da jajen rashin lafiya. Yaya ya tashi
zai tafi yana rike da hannun Nusaiba da Sa'ima ya tashi zai fita ke
nan sai ga mahaifin anti Maryam ya dawo Yaya ya durkusa ya
gaishe shi ya yi masa jajen rashin lafiyar Hajiya sala sannan ya yi
sallam ya ce shi zai tafi, T.z. Hamma ya ce "A a har za ka tafi?
"Maryam ta ce "Ga kuma ruwa da da lemo an kai maka falon ka zo
ka sha mana" Sadiq ya bi ta falon mahaifinta, sun zauna a kan
kujera sannan Nusaiba da Sa'ima daga gefensa, Sa'ima tana yi masa
korafin wai Nusaiba ta mare ta a kunci, Sadiq ya ce "Ke Nusaiba
mai ya sa kike marin ta, kada ki sake marinta, kin ji ko, Nusaiba ta
ce "Baba ni fa karya take yi min ban mare ta ba."
Maryam ta ce, "Baban Nusaiba ka sha lemon mana, "Sadiq
ya ce" Ki bar shi kawai wallahi a koshe nake, daman ina son
magana da ke ne shi ya sa natsaya." Maryam ta yi shiru tana
sauraron sa donta ji abin da zai ce, ya ce "Kin san na yi miki
zancen tafiya London cikin wannan satin, Anty daga jin zancen
London har wani dadi ya kama ta ta fara rausaya da ido tana
murmushi "To don laka yanzu dai ranar lahadin nan zan dafi, shi ne
nake son ki tafi Abuja yau din nan, ki shirya kayanki duk don na
bada mota ta kwasar kaya, zasu kwaso muku kayanku su dawo da
su nan gidana na unguwar Sani Mainagge, a nan nake son ku zauna
kusa da gida, kin san gidan da muke ciki na Abuja, gidan gwannati ne.' Anti Maryam ta bata fuska ta ce, "E! Sadiq kana nufin kai daya
za ka tafi England ban da mu, sannan kuma mu komo nan Kano mu
zauna,? Sadiq ya ce E nufi na ke nan, kin san in ba ki manta ba kin
ce ke ba za ki ba, don haka na fasa tafiyar da ke", Ta ce, "To in
6
haka ne ka bari mana mu zauna a gidanka da yake Aso drive amma
ba mu koma nan. Kano ba" Sadiq ya ce; "Ke Maryam, ba wai
shawara na zo yi da ke ba, na zo na gaya miki abin da na yanke wa
zuciyata ne, don haka dabara ta rage wa mai shiga rijiya, kafin nan
da karfe gome sha biyu na dare ki tattaro kayanki daga Abuja zuwa
Kano, ina jiranki a gidana na Sani Mainagge. Don haka Umar
direba ya kai ki Abuja, matar debo kaya kuwa tun da asuba ta tafi",
Anti Maryam ta tsaya tana ba shi hakuri a kan in ma ba zai tafi da
ita London ba, to ya bari ta zauna a Abuja, Yaya ya ce "Ban amince
ba, ke Maryam ina da abin yi zan tafi, don haka sai kun zo, Allah ya
kiyaye hanya".
Bayan tafiyar Yaya Anti Maryam ta hada kai da hannu ta
zuba tagumi tana tunanin zaman Kano tun da ta riga ta saba da
zaman bariki, ba ma wannan ya fi damunta ba sai yadda ta bi duk ta
gaya wa 'yan 'uwa da abokan arzikin ta wai za su tafi England sai
bayan shekara huda, sai dai ta zo ganin gida, to yanzu me za ta ce da
mutane yan ba ni na iya, iyayen bin kwakwaf.
Haka dai ta tashi ta je ta shirya ta doshi hanyar Abuja don
ta shiryo kayanta, amma ta daura aniyar ko da malamai sai ta bi
sadiq zuwa England,. ba yanzu ba ko bayan ya tafi ne sai ya aiko
shi da kansa ta tafi.
Sadiq yana barin gidan su anti Maryam bai zame ko ina ba
sai gidansa na Sani Mainagge, gida ne sashi biyu tamkar Hussan da
Husaini duk abinda yake cikin wannan sashi da akwai a daya
sashin, gidaje ne masu dakuna uku da falo, a saman kowane da
makewayi sannan a kasa daki daya da falo da kicin da sito, ga
makeken fili a gaban gidan wanda aka shuka furanni.
Sun iso gidan a inda ya sami abokansa su uku suna zaman
jiransa wato Ibrahim babban abokinsa kuma amininsa wanda sun
tashi tare kuma sun yi makaranta tare, sai kuma Mahmud wato
abokin aikinsa ne a nan gida Nijeriya, sai kuma Aliyu shi ma abokin
harkarsa ne a wajen kasuwancin sa, kun san mutumin Kano ba shi
iyawa da aikin ofis kawai, dole sai ya hada da kasuwa.
Yaya Sadiq ya ce wa Usman direba maza ya je gidan Inna
Sa'a ya dauko masa Rukayya yanzu.
Daman tun da na tashi na yi wanka na bata lokaci a wajen
shafe - shafe, sannan na dauko dinkina na shadda kamfala launin
ruwan ja baki ayi mata dinkin buba da wasu 'yan duwatsu a jikinta,
7
daman a dinke ake saida ita, don a dinke ya sai min, na tubke gashina ban daura dankwali ba sai na yafa dan gyale na wanda ya dace da kayan, sannan na sami sarkata da dankunne da abin hannu
na da zubba na zuba, kai duk wanda ya gan ni a wannan lokacin zai dauka zan je wani kasaitaccen biki ne, sannan ga takalmi da jakata, wato darino Italian design.
Ina zaune a daki ina kallon wani fim da ake yi a sky
movies, Usman direba yayi sallama, Inna ce ta amsa, daga tsakar
gida, Usman ya durkusa ya gaida Inna ya ce "Alhaji ne ya aiko na
zo na dauki Rukayya", Inna ta ce "To", Rukayyar ma tana daga ciki, yi mata magana mana".
Usman ya daga labule ya ce, "Rukayya ina kwana". Na ce
da Usman, Lafiya kalau" ya ce "Oga ne ya ce na zo na dauke ki
zuwa Sani Mainagge" Na ce "To Usman gani nan fitowa". Na fito
muka tafi da Usman. Mun isa mun iske Yaya a falo tare da su Alhaji
Ibrahim suna ta hirarsu, na gaishe su, sannan na wuce sama ina
zaune ne a falon sa ni kadai, na kunna talbijin ina kallo, sai ga
Tukur yaron gidan Yaya na Kano ya shigo, ya gaishe ni, ya ce "In ji
Yaya na kai masa lemo kasa, Na sauka kasa na bude firij na dauko
lemon Serof na zuba a cikin dogon kofi na kara ruwan sanyi a kai,
na hado da kananan kofuna, na kawo masa, abin mamaki sai na
tarar duk abokan Yayan ba kowa,na zuba masa a kofinsa Yaya ya се
Yauwa, madalla na gode, nemi waje ki zauna ina son muyi wata
magana ni da ke" Yaya ya dauki lemon ya kurba sannan ya yi wata
irin ajiyar zuciya, ya dago idonsa ya kalle ni sannan Ya yi
murmushi wanda ya sanya na saukar da kana kasa, don murmushin
da ya yi min ni kaina na rasa yadda zan fassara shi. Don a gaskiya
tunda nake ban taba sani cewa Yaya kyakkyawa ne ba sai yau da ya
yi min wannan murmushin, domin a da kallon tsoro nake yi masa, a
gaskiya duk wacce ta samu ta mallaki Yaya Sadiq matsayin mijinta
lallai ta yi sa'ar mijin aure, don namiji ne har namiji don ya mallaki
duk wani abin da da namiji yake takama dashi na kasancewarsa
cikakken namiji ina nan na fada cikin kogin tunani sai na yi Yaya
yace min "To Rukayya ina son a yau na miko kokon barata zuwa
gare ki don ina son a kau da maganar Yaya a kawo ta aure a
tsakanin mu, ko ke me kika ce? Ina fatan ban takura miki ba, kuma
ban danne miki hakkinki ba”. Ni dai na yi shiru kaina a sunkuye ban
ce komai ba.
8
Yaya ya ce; "Rukayya Yaya kika yi shiru, ko dai ba ki
amince da ni ba ne, ba ki so na, na dago kai na na dubi yay na ce,
"To Yaya me zance ai kai da kaya duk mallakar wuya ne? Yaya ya
yi murmushi ya ce, "Rukayya kin san ni mutum ne wanda ba na
son danne wa dan uwana hakkin sa shi ne nake so na ji wai shin kin
yarda ko a'a, don ni ma hankali na ya kwanta". Na yi murmushi na
sunkuyar da kaina ina wasa da zubban da suke hannuna, amma duk
a lokacin nan na san idon Yaya yana kaina ne. Nace, "To Yaya na
amince" Yaya ya ce "Yauwa, Alhamdulillah, Alhamdulillahi.
Rukayya na gode. Abin har ya ba ni mamaki yadda Yaya yake farin
ciki tamkar an aiko masa da busharar gafara.
"To Rukayya kin san dai kamar yadda na yanke ina son a
daura aure gobe don kin san nan da kwana hudu wato ranar lahadi
za mu bar Nijeriya zuwa England don haka sai ki yi hakuri ba za a
yi wani biki ba tun da dai a kura ren lokaci auren ya zo "Nace" Ai
ba komai Yaya, daman daurin aure ai shi ne wajibi, biki kuwa bidi'a
ne.
"Don haka yanzu sai mu tafi cikin gari gidan Inna ina son
na sami Baba Ado na yi masa bayanin daurin auren".
Yaya ya maida ni gidan Inna Sa'a shi kuma ya wuce gidan
Baba Ado.
A ranar da misalin karfe goma na dare Anti Maryam ta iso
tare da kayanta daga Abuja. Ba su sami kebewa da Yaya ba sai
lokacin kwanciya, Yaya ya shiga dakinta ya same ta ta yi shirin ya
ce Maryam ina son mu yi wata magana da ke, ina son kuma ki
fahimci ni da kunnen basira, Maryam ta zauna a bakin gado, ta ce
"To ina sauraron ka!', Yaya ya ce; "To marya, ina son ki ba ni aron
hankalinki da hakurinki nan, inda hali ina son ki aro wani hakurin ki
kara a kan wanda kike dashi, ina son da ni dake da'ya'yan mu mu
zama tsintsiya madaurin mu daya; don haka nake so nie shalda mijkti
ina son na kara aure".
Anti Maryam ta yi wata ajiyar zuciya ta dago kai ta kalli
Yaya tana wani uban tagumi, ta ce "Daman wulakanein da ka yi
niyyar yi min ke nan? Yaya ya ce "Haba Maryam n da le babu
maganar wulakanci har abada, kuma na san ko kwarya ta fashe ai
tana da sauran zane. Haba uwar gida turken gida," Maryam cikin
9
da
yake
gaske
tana
kake
magana cikin shagwaba, ta ce, “Ka ga Sadiq ba na so, wai yi ne ko kuwa wasa ne?" Ya ce, "Wallahi babu
fuskarta,
maganar
Maryam
wasa da gaske nake yi." Yana yin magana yana kallon
tawa?" Yaya ya ce
ta
"Haba
daure fuska ta ce, "To na ji, wace ce kishiyar uwar gida, ai kanwarki ce, ki daina cewa kishiyarki don in ta zo ma ai Yaya za ta rinka ce miki". Maryam ta ce, "Ni ba na neman matarka ta ce min Yaya, don me za ta ce min yaya? Ta kira ni da Maryam dina ma ya isa". Yaya ya ce, "Ai haka girmamawa ce ta kira ki da yaya". Maryam ta ce, "Ni dai ba ka amsa mini tambayata ba, na ce wai wace ce kishiyar da zaka aura din?".
ke ma kuma
Yaya
kanwarki
ya yi murmushi ya dubi fuskarta, yace "Kanwata ce ce, wato RUKAYYA". Anti Maryam ta taso wa Yaya da masifa wai daman munafuncin da yake kulla mata ke nan shi da 'yan uwansa wato tagoya yarinya a gabanta sannan daga baya ta zo ta zama kishiyarta, to ita wallahi ba za ta yarda ba, sai dai ya zaba ko ita ko Rukayya. Tashi daya Maryam ta rikice wa Yaya a daki da kuka tamkar wata karamar yarinya, wai ya cuce ta ya kuma ci amanarta don haka ita kam ba yadda za ta yi ta zauna da shi da Rukayya sai dai ya sake ta, Sadiq ya tashi ya ce. "Maryam, “ina son ki fahimce ne", Yaya ya fara yi mata magana cikin lallashi wai duk don ta fahimci, abin da zai ce mata, amma ina ai wanda yayi nisa ba ya jin kira, sai ma Maryam ta nemi ta daga murya da kukanta, wanda duk mutanen da suke gida za su iya fahimtar cewa wani abu yana faruwa a gidan,
don haka Yaya, ya lura da cewa rashin mutunci take son janyo masa, sai ya tashi ya ce "To Maryam sai ki zabi abin da kika ga shi
ne mafi alheri a wajen ki". Ya bude kofa ya tafi dakinsa ya kwanta.
Washegari tun da sassafe, tun kafin ya tashi daga barci Maryam ta fice da mota ta tafi gidansu.
Bayan Sadiq ya fito ya kintsa ya hau teburi yana karyawa, tukunna ya yi kiran Tukur mai aiki ya tambaye shi ina Maryam, ya
ce tun da safe ya ga ta ita da mota. Yaya ya kada kai ya yi shiru.
Ranar 9-12 bayan an fito daga sallar la'asar, Baba Ado ya daura aurena da Yaya Sadiq a kofar gidan Inna Sa'a.
Bayan sallar magriba ne anti Maryam ta zo gidan Inna Sa'a, amma ba ta shogo ba sai ta wuce zuwa gidan Baba Ado. Ta je
ta sami Baba Ado, bayan ta gaishe shi ta kai masa karar Yaya Sadiq
10
wai ya san zai yi aure amma bai shaida mata ba sai jiya, sananya
tabbatar mata da Rukayya, kuma duk wani sirrinta Rukayya ta sani,
ita ba a yarda da tsarin da ya shirya ba, wai ya tafi da Rukayya
England sannan ita ya bar ta a Nijeriya, tun daga yanzu ma ya fara
nuna banbanci a tsakanin su, ai wannan zai janyo Rukayya ta raina
ta.
Baba Ado ya sa a kirawo masa Yaya a lokacin yana kofar
gidan Inna Sa'a tare da mutane, ya tashi ya je kiran Baba Ado.
Maryam tana tsugune daga gefe daya Yaya ya same ta.
Baba Ado ya kwashe duk bayanin da Maryam ta yi masa ya fada wa
Yaya. Sadiq ya ce. "Baba na ji, to mene ne laifina a nan? In dai
tafiya England ne ai tun farko ke kika ce ba za ki ba, ko ba ke ba
ce? Kuma maganar ban gaya miki zan yi aure ba, to ita ma
Rukayya da na aura sai jiyan na gaya mata zancen auren, kuma ta
amince, to balle ke. Wai kuma Rukayya za ta raina ki. Ni na san
Rukayya yarinya ce mai ladabi, in dai har kika rike girman ki to na
san ba yadda za ayi ta raina ki. Maryam ta taso zata fara yin
magana, Baba Ado fa tsaftar da ita ya ce "Tsaya niba tone - tone
nake so ba, gyara nake so ba barna ba, don haka abinda nake so a
koyaushe shi ne ku sa hakuri a al' amuran ku, kai Sadiq, kai ne
baba, komai za kayi ka dubi girman Allah, ka yi tsakani da Allah,
ke kuma Maryam ina son ki sa wa zuciyarki hakuri, sannan ba na
son gutsuri - tsoma don ba shi da amfani, sannan komai za ku yi ku
sa Allah a gaba shi ne daidai". Ya sallami Maryam ta tashi ta tafi.
Ya zaunar da Yaya yana kara yi masa nasiha, ya ce "Sadiq, abin da
nake so da kai shi ne, zama da mata biyu sai ka yi hakuri sannan ka
toshe kunnuwanka ka ki ji, ka ki gani, duk dai don a zauna lafiya"
yaya ya yi godiya ya tashi ya yi sallama ya tafi.
Kasancewar gidan Inn Sa'a a cike yake da mutane, sannan
Yaya yana tare da baki, ya sa ango da marya ba su ga junan su ba a
ranar da aka daura aure, sai dai ya aiko min da wasika ta hannun
Usman babban direbansa.
Amarya Rukayya.
Yaya amarci, kodayake dai amarci bai kammala ba tun da
ba ki ga ango ba. Don Allah ki yi hakuri kin sanin fama da jama'a,
sannan cikin gidan Inna da jama'a shi ya sa ban samu na shigo ba, I
hope dai ba wata damuwa, in ma da akwai to ki rubuto ki baiwa
Usman. 11
Angonki Sadiq. Washegari ne da safe bayan na yi karin kumallo na yi wanka na yi kwalliya da wata atamfa Holland, wace aka yi min
dinkinta shape wanda ya fito min da surar jikina a hade da skirt,
kuma ban daura dankwali ba amma sai na tubke gashin na dauko
wani tabkeken rebon na daure shi, ina zaune a tsakar gida a kan
kujera yar tsugune tare da Inna mun sa hirar mu, sai muka ji
sallamar Maryam tare da yara, suna shigowa gida, Inna ta amsa
mata sallama. Ta tarbi 'yan jikokinta su Sa'ima da Nusaiba suka zo
suka fada jikin Inna, Inna ta yi musu sannu da zuwa tare da jasu
zuwa falo.
Ni ma na yi wa Maryam sannu da zuwa amma ko amsawa
bata yi ba sai dai harar da ta yi min, a cikin raina na ce oho! dai.
Yaran kuwa dama can sun fi shakuwa dani akan mahaifiyarsu tunda
daman nice mai kulla da su. Sai suka bar wajen mahaifiyarsu a falon
Inna suka dawa juna sun ta ba ni labarinsu irin na shirmen yarinta,
ni kuma ina ta yi musu dariya, don ni ba ni ganin lefin yaran, kuma
ni har ga Allah ina son yaran ba don komai ba sai don mahaifinsu
yana sona. To mai zai hana ba zan so 'Ya'yansa ba?.
Can daga cikin daki na jiyo muryar Maryam tana yi wa
Inna korafin ita kam ba ta amince Yaya ya tafi da Rukayya England
ba ita ya bar ta a Nijeriya ba, to ai ga shi tun ba taje ko ina ba ya
fara nuna banbanci, ita kam, wallahi sai dai ko a bakin aurenta. Inna
ta ce "Haba Maryam ai ana barin halas ko don kunya. Hakuri dai shi
ne nake, ku duka an san da ciwo kam, amma ai sai a yi hakuri wata
rana sai ki ga kamar ma ba' a yi ba. Kuma ai kinsan ance zaman
duniya iyawa ne". Maryam ta ce "To Inna ni dai ko na hakura na
zauna sai dai ya debi ‘ya'yansa ya tafi da su". Inna ta yi murmushi
ta ce "Kai! Yaro dai yaro ne, yanzu Maryam sai ki