dakin
cikin sassarfa.
*** **** ***
Ba bacci take ko tunani ba kawai
151 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ta yi kasala take ji a yayinda wayarta
kukan da ta tanada don tunasar da me ita
wani muhimmin abu. Har ga Allah bata
tuna komai ba yau don haka da sauri ta
janyo wayar ta duba ta ga mene ne? Cikan
shekarar Ibrahim Balala wayar ke tuna
mata kamar yadda ta tsara wa wayar ta
tunasar da ita a duk karfe takwas na
zagayowar shekarar. Ta riga ta tuna har
jikinta yayi likis amma ta kasa dena kallon
wayar ba don fuskar wayar wadda ke
rubuta kalmomin sirrin da ita ta san su a
matsayin tunin ba sai don kallon ranakun
da suka wuce a baya takwarorin ranar yau
wanda duk rintsi duk tsanani tana yin su ne
da masoyi Bally a gefenta musamman ma
ta karshe wadda ta zo daf da rabuwarsu,
duk da kunci da suke fuskanta na iyayc bai
hana su cin moriyar ranar da duk wani
nau'i na so da sha awa ba. Tayi wa Bally
komai a domin wannan rana kamar yadda
shima yayi mata komai a domin hakan. Ta
ji wata kewa da bata taba fuskantar irinta
ba tun baya rabuwarsu. babu lambarsa a
cikin way rta, amma kwanyarta na
152 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
haddace dasu bata san lokacinda ta ji tana
lallatsa su ba har ta kammala jera su a
fuskar wayarta amma ta kasa danna su sai
shafarsu take cikin dafa-dukar fargaba da
bege.
"Reeda ba kiyayyar mahaifanmu ba
ko ke na gani dauke da wuka kin caka wa
hagun kirjina ya taho da zuciyata, ko kin
saici goshi na kin harba wanda na san bani
da tabbacin sama da nunfashi uku zai rage
min, ina me tabbatar miki da cewa wadan
nan nunfashi uku kacal za su yi miki son
da wani masoyin ki me ikirarin son ki
shekaru dari bai yi miki su ba. Baby na
riga nayi miki son da ba zan taba kin ki
ba...."
Wasu kalmomi ne da Balala ya taba
gaya mata a wata tuhuma da tayi masa na
ko bi mahaifinsa ya dena son ta ne kafin su
yi aure? Su ta tuno a yanzu take ganin
lokacinda ya fade su a kan fuskar wayarta
tana wani nishi na azabtuwar zuciya da
bata san ya sata hawaye ba sai da ta ga
saukarsu kan fuskar wayar.
"Da kai na na gasa miki hanta da
151 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
kasala take ji a yayinda wayarta ta yi
kukan da ta tanada don tunasar da me ita
wani muhimmin abu. Har ga Allah bata
tuna komai ba yau don haka da sauri ta
janyo wayar ta duba ta ga mene ne? Cikan
shekarar Ibrahim Balala wayar ke tuna
mata kamar yadda ta tsara wa wayar ta
tunasar da ita a duk karfe takwas na
zagayowar shekarar. Ta riga ta tuna har
jikinta yayi likis amma ta kasa dena kallon
wayar ba don fuskar wayar wadda ke
rubuta kalmomin sirrin da ita ta san su a
matsayin tunin ba sai don kallon ranakun
da suka wucc a baya takwarorin ranar yau
wanda duk rintsi duk tsanani tana yin su ne
da masoyi Bally a gefenta musamman ma
ta karshe wadda ta zo daf da rabuwarsu,
duk da kunci da suke fuskanta na iyayc bai
hana su cin moriyar ranar da duk wani
nau'i na so da sha awa ba. Tayi wa Bally
komai a domin wannan rana kamar yadda
shima yayi mata komai a domin hakan. Ta
ji wata kowa da bata taba fuskantar irinta
ba tun baya rabuwarsu babu lambarsa a
cikinwayrta, amma kwanyarta na
152 Mafiyan Masoyа-2 Rahma Abdulmajid
haddace dasu bata san lokacinda ta ji tana
lallatsa su ba har ta kammala jera su a
fuskar wayarta amma ta kasa danna su sai
shafarsu take cikin dafa-dukar fargaba da
bege.
"Rceda ba kiyayyar mahaifanmu ba
ko ke na gani dauke da wuka kin caka wa
hagun kirjina ya taho da zuciyata, ko kin
saici goshi na kin harba wanda na san bani
da tabbacin sama da nunfashi uku zai rage
min, ina me tabbatar miki da cewa wadan
nan nunfashi uku kacal za su yi miki son
da wani masoyin ki me ikirarin son ki
shekaru dari bai yi miki su ba. Baby na
riga nayi miki son da ba zan taba kin ki
ba...."
Wasu kalmomi ne da Balala ya taba
gaya mata a wata tuhuma da tayi masa na
ko bi mahaifinsa ya dena son ta ne kafin su
yi aure? Su ta tuno a yanzu take ganin
lokacinda ya fade su a kan fuskar wayarta
tana wani nishi na azabtuwar zuciya da
bata san ya sata hawaye ba sai da ta ga
saukarsu kan fuskar w ayar.
"Da kai na na gasa miki hanta da
151 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
kasala take ji a yayinda wayarta ta yi
kukan da ta tanada don tunasar da me ita
wani muhimmin abu. Har ga Allah bata
tuna komai ba yau don haka da sauri ta
janyo wayar ta duba ta ga mene ne? Cikan
shckarar Ibrahim Balala wayar ke tuna
mata kamar yadda ta tsara wa wayar ta
tunasar da ita a duk karfe takwas na
zagayowar shekarar. Ta riga ta tuna har
jikinta yayi likis amma ta kasa dena kallon
wayar ba don fuskar wayar wadda ke
rubuta kalmomin sirrin da ita ta san su a
matsayin tunin ba sai don kallon ranakun
da suka wuce a baya takwarorin ranar yau
wanda duk rintsi duk tsanani tana yin su ne
da masoyi Bally a gefenta musamman ma
ta karshe wadda ta zo daf da rabuwarsu,
duk da kunci da suke fuskanta na iyayc bai
hana su cin moriyar ranar da duk wani
nau'i na so da sha'awa ba. Tayi wa Bally
komai a domin wannan rana kamar yadda
shima yayi mata komai a domin hakan. Ta
ji wata kewa da bata taba fuskantar irinta
ba tun baya rabuwarsu. babu lambarsa a
cikin wayarta, amma kwanyarta na
152 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
haddacc dasu bata san lokacinda ta ji tana
lallatsa su ba har ta kammala jera su a
fuskar wayarta amma ta kasa danna su sai
shafarsu take cikin dafa-dukar fargaba da
bege.
"Reeda ba kiyayyar mahaifanmu ba
ko ke na gani dauke da wuka kin caka wa
hagun kirjina ya taho da zuciyata, ko kin
saici goshi na kin harba wanda na san bani
da tabbacin sama da nunfashi uku zai rage
min, ina me tabbatar miki da cewa wadan
nan nunfashi uku kacal za su yi miki son
da wani masoyin ki me ikirarin son ki
shekaru dari bai yi miki su ba. Baby na
riga nayi miki son da ba zan taba kin ki
ba...."
Wasu kalmomi ne da Balala ya taba
gaya mata a wata tuhuma da tayi masa na
ko bi mahaifinsa ya dena son ta ne kafin su
yi aure? Su ta tuno a yanzu take ganin
lokacinda ya fade su a kan fuskar wayarta
tana wani nishi na azabtuwar zuciya da
bata san ya sata hawaye ba sai da ta ga
saukarsu kan fuskar wayar.
"Da kai na na gasa miki hanta da
8
153 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
koren tattasai da karas da kayan kamshin
da kike so don ki san ko babu me aiki zan
iya yi miki me dadi don in har kina nan to
komai ya dinga dadi kenan don dadin
rayuwa dake"
Wannan ne surutun da Farid ke yi a
yayinda ya shigo dakin dauke da karamin
tiren abinci me kafafun tebur dauke da
hadin hanta da madara mai hadin kayan
lambu da yayi wa Farida da kansa. Da
alamar ya kammala shirin ofis tsaf abinda
ya rage shine tai din da ya rataya a wuya
ba tarc da ya daure ba. Yayi nasarar kawar
da hankalin Farida cikin sauri da tsarguwa
daga kan tunaninta amma ba yanayinta ba,
musamman ma da ta kafar da hawayenta
sai ta sami kafar da idanunta a kansa ba da
kallon so ba sai da wasu manufofin daban.
Tunda ta sami ciki Farid ya sauya ya
zamo namijin arziki da biyayya da in za ta
ajiye kara da wuya ya tsallake. Duk wani
abu na faricikinta shi yake yi cikin rawan
kai tare da yi mata alkawarin so da kauna
muddin rayuwarsa, sai dai dafin da yayi
wa zuciyarta har tayi tsatsar da ta samar da
154 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
hujin da soyayyar Bally ta yi amfani da shi
wajen kutsawa cikin zuciyarta a matsayin
sabuwa fil ya sa baya birge ta, hasali ma
fata take ya bata mata ba kamar da ba,
kamar yadda a yanzu ta sami idanun hango
duk wani wallensa da fahimtar nufinsa na
cewa ba yana yi mata wannan tarairaya ne
dan so zalla ba sai don ta zamo irin matar
da yake so wadda bata fita bata aiki a
dalilin hutun ciki, abinda ta tabbatar ba zai
dauwama ba muddin ita Faridar ba wadda
aka raine ta da raunin da namiji ke zana wa
rayuwa bace, don haka ta riga ta hasashi
ranar da wannan soyayya za ta kare wato
in ta haihu ta murmure ta so koma wa
rayuwarta. Da wannan take kallon Farid a
matsayin na miji me tsattsaura son kai.
"Baki daure min tai din ba mana ko
shi ma wani aiki ne na sauke miki?"
Haka yace don ya katse kallo mara
dalili da a zatonsa take yi masa.
"Na gode da abincin hannunka na
san zai yi dadi".
Ta fadi tana kokarin janyo abincin
zuwa ga kirjinta.
155 Mufiyan Masoyа-2 Rahma Abdulmajid
"Bari na yi sauri na je ofis yau
muna da baki babu latti"
Ya fadi yana shirn daure tai dinsa
da kansa. Ta matso ta kamo wuyansa ta
janyo kusa da kirjinta don ta daure masa
tai din.
"Ni zan bai wa kaina abinci kenan
yau ba me ba ni ? dakata ma kai ka
karya?"
Bai damu da kansa ba a wannan
yanayi da Farida ta kawo shi kusa da ita da
kanta.
"Zan iya zama na baki in haka kika
fi so"
Tayi murmushi sannan ta sunbace
shi.
"Dafawar ma ta ishe ni-gata, ka je
abinka Allah Ya bada sa`a, amma kafin
nan sai na yi maka loma uku"
Da kanta ta ba shi har lomar abinci
hudu sannan ya sha kusan rabi na madarar
ya sunbaci goshinta ya fice da sauri. Tayi
shiru tana tunani ba tare da ta iya cin
abincin ba, shin rayuwa tsakaninta da
Farid ta fara zama tausayi ba soyayya ba a
15o Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
yayinda zuciyarta ta fara kagewa ga son wanda ba a sonta za ta sake son sa ba. Ji
take kamar fa itace da laifi, amma kuma
wani layi can a kwanar zuciyarta na tuna
mata da cewa Farid din bai bar ta ta sake a
soyayyarsa ba.
Bata iya cin abincin ba ta dai shanye
madarar dakyar sannan ta tashi ta bar
dakin don sauya yanayi. Tana zaune ne a
falon farko ta jiwo hayaniyar me aiki
wadda cikin murdadden turanci take
kokarin hana wani shigowa abinda ya ja
hankalinta kenan don ta ji ko za ta iya
wani abu, amma muryar wanda ake
hanawar ce ta daki kirjinta inda ta tsinci
kanta a tsaye ba da shiri ba.
Balala ya bayyana yana me mata
kallon kamar ya shekara tsaye, jikinsa ya
yi la'asar yana kallon cikinta.
"So da gaske ne kin kashe min nawa
dan kin zo za ki samar da irin wanda kike
so ya rayu ko? Kuma kina zaton ni din zan
kyale hakan?"
Ya soma matsowa cikin cizawa da
matukar fishi.Farida wadda a yanzu ta juya
스
157 Mufiyan Masoya-2 Rahma Ahdulmajid
zuwa matukar tsoro ta fara magana cikin
in-ina.
"Bally shigowar ka gidan nan bai
kamata ba, nan gidan wani ne ka tuna
babu"
Ya fashe da dariyar haushi.
"ke Farida ce kika san ma'anar ya
kamata? Lokacinda kike kashe jininki jini
na da ransa don yana jikinki kin tuna
kamaci-kamata? A yanzu ne da kike ganin
kin gama da tawa rayuwar za ki kafa taki
yadda kika so? Bana jin zan bar hakan ta
faru Farida"
Faridar matsawa take baya a hankali
yayinda shi duk da yana zuwa ne a
hankalin amma ya fi ta sauri don har ya iso
kusa da ita inda za ta iya jin nunfashinsa
me cakude da warin kayan sa maye.
"Bally shayc-shaye ka koma yi?
Haba! Duk rayuwar da ka shiga a duniya
baka sha komai ba sai yanzu? Bally
kokarta ka fahimci abinda ke faruwa a
rayuwarka ya yi nisa da dacewa"
"Abinda nake son kararwa kenan,
wato rashin dacewar rayuwata ta hanyar
1
k
k
y:
da
SC
Ry
ma
158 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
kashc ki na kashc kaina kamar yadda kika
taba yin aniyar da baki cika mana ba"
Tunda me aiki ta lura da sanayya da
tsoro da ma yanayin dake tsakanin Balala
da Farida ta yi sauri ta fice ta dauki waya
ta kira Farid, wanda yake gaisawa da
mutane a ofishinsu cikin fara'a da jin
dadin yadda ya baro gidansa, don haka
daga jin abinda ke faruwa bai kara kalma
daya ba ya kwasa a guje sai cikin motarsa
inda yayi mata jan sukuwa yana gudu yana
tsige abubuwan da za su iya tankwara shi
kamar tai da belt ji yake baya saurin isa
har sai da ya gan shi a gaban gidansa, bai
jira a bude masa gate ba ya fice daga
motar ya bar ta a bude yana gudu taku
daya zuwa biyu ya iso da shi falon.
Wanda ya zata shi din ne wato
Balala wanda a yanzu yana daf da shake
Farida wadda take makyarkyata da yi masa
magiya a yayinda shi din yake kuka. Cikin
sa Farid yayi ya wawure shi yayi jifa da
shi cikin kayan kallo.
"Shege! Kai ne har cikin gidana?
Yau zan nuna maka kai din ba kowa bane
2
4
159 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
a gidan wani..."
Ya sake kai masa duka da iya
karfinsa a yayinda Farida tuni ta shiga
suman tsoro musamman da ta ga Balalanta
cikin gilasan kayan kallo da suka fara
tarwatsewa suna yanka shi. Farid ne ya
jawo shi daga cikin kayan ba don ceto shi
ba sai don ya kara masa duka, amma
hakan ya ba shi damar tabukawa inda nan
dambe ya kaure irin damben maza na
kawo wuka, duk da Farid kan fi lahanta
Balala wanda har yanzu da sauran maye a
jikinsa. A wannan lokacin Farida ta fara
dawowa hayyacinta inda take iya hasashen
kisan kan da ke shirin faruwa don haka ta
fara kokarin hana su da baki amma babu
me sauraronta har zuwa lokacinda ta yi ta
maza ta shigi Farid don ta janye shi amma
aka yi sa`a Balala ya kawo masa wani
duka da ya sauka a kan cikin ta abin da
yayi kasa da ita a dunkule sannan ta fara
zamowa sumamammiya.
Ganin haka Farid ya kara zuciya ya
dauko wata yankakkiyar gilasi zai buga
masa amma hango Farida na kara yin kasa
1
160 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ne ya saki gilasin ya jc ya tallabe ta. Balala
wanda ake damben da shi tuni ya girgije ya yi wo kan Faridar shima babu shiri.
"Farida.. Farida.. Farida kalle ni
Shine kiran da ya kaure a falon daga
bakin mazan da kasa da minti daya suke
dambe da junansu amma a yanzu cikin
rikita Balala ne ya je ya debo ruwa ya
kawo wa Farid yana yayyafa wa Farida.
"Idan wani abu ya sami matata sai
na ci namanka danye na rantse"
Farid ya fadi yana kuka a yayinda
yake shirin daukar Faridar wadda bata
farfado ba.
"Ka bar magana ka dauko ta mu je
asibiti, in wani abu ya same ta ba zan
kyale ka ba shege"
Balala ke fadi a yayinda yayi gaba
ya wangale kofa yana gudu.
Farid dauke da Farida Balala ne
direba suna gudu dukan su a iya tafiyar
kiranta suke a mota a rikice suna hawaye.
Har zuwa asibiti inda Balala ya faka motar
ya fada asibitin a guje ya na ihu likitoci
suka biyo shi da gado aka dauki Farida
Sun zo juna kamar yadda iyayensu suka ki juna.
Sai dai soyayyarsu tayi ragunta a gaban kiyayyar
mahaifansu, gashi har a karon farko qiyayya tayi
nasara mai karfi a kan soyayya wadda ta haifar da
yakin basasar zuciya da ya janyo asarar duk abinda
masoyan suka mallaka. Abin tambaya shine; wai
haka soyayya za ta sanya ido tana kallon kiyayya
nayin fata-fata da fadar ta? Mu kutsa cikin littafin
Mafiyan Masoya don ganin yakin karshe tsakanin
soyayya da kiyayya.
MACE MUTUM
MACE MUTUM
BOOKSHOP
Block J. No 121 layt uku, Bayan Gadar Yan Kura
Kasuwar Sabon Gart Kanо
08063800300, 08064533577, www.manuwa.com
ISBN 897898709-5
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels