suna hawaye. Wannan sako
ne ya sanya Farida ta mance da Balala don
ta bar wurin da sauri....
102 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
TAKWAS
Ta kalli faffadan farin falon da babu
komai sai fitilu da kura, tayi ajiyar zuciya.
Koda kuka bai zo idanunta ba amma ta ji
wata karaya hade da kewa sun yi wa
zuciyarta dafa-duka. ta dafa karfen wundon
tamkar tana neman agaji na ya taya ta tilasta
kanta yin murmushin da zai 6oye wa har
zuciyarta irin karayar dake tattare da ita.
Nan ne gidan da ta zabi ta koma nesa da
garinda aka santa ido-da-ido. Wannan ya
faru ne bayanda suka amince da kulle duk
wani abu da yaragu da sunan mahaifinsu
kasancewar komai ya kare saura wanda in
za a rike za a sha wuya ne kawai a kiyaye
sunada a ganinsu tuni an yi masa illa. Don
haka fatansu a kashe sunan Na`ibi don
mancewa da abinda ya faru ma dashi.
Mahaifiyar Farida ta yi doguwar jinya a
Paris inda tana fara samin sauki ta koma
kasarsu don zama cikin jama arta ta karasa
murmurewa da kuma son yin nisa da inda
zai dinga tuna mata danasaninta na jefa
mijinta a mummunan hali da tayi wanda ko
103 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
da ba shi ya kashe shi ba shi ya kashe masa
suna. Kanin Farida Shafik wanda ta mallaka
masa duk ragowar gadonsu don ya je ya
gina rayuwarsa, shi ma ya koma inda ya fi
kauriwato kasar Jamus don soma sabuwar
rayuwa nesa da duk wani bakin ciki da
tambarinda suka fuskanta. A nan gida Farida
ce ta tsaya tayi hudubar bankwana ga
dimbin ma`aikatansu bayanda ta biyasu
hakkokinsu na aiki da sallama, sannan ta yi
musu fatan samin aiki a wani wuri.Akasari
sun zubar da hawaye musamman matan ciki,
amma wanda idanunsa ya bushe bai yi kuka
ba kuma hakan ta baiwa kowa mamaki
saboda kusancinsa da Farida shine Farid,
wanda ashe shirinsa ba na tafiya bane, na
bin Farida ne duk inda za ta, kuma hakan ya
gabatar mata, duk da tayi musu da shi
karshe dole ta amince masa cikin godiya.
Ko a yanzu tare suka iso wannan sabon
matsugunin na Farida
"Gida dadi...gida dadi. Ko da bamu
tsira da komai ba a karshen game din nan,
koda na rasa har mahaifana a wannan karon
battar,na tsira da usilina wanda ko ba komai
zai dinga zura ruhi a cikin rayuwar tuna-
104 Mafiyan Masoya-2 Ralıma Abdulmujid
baya"
Ta shari wata kura a jikin wundon
tana dubawa.
"Nan ne gidan Father na farko... Koda
ba a haife ni a gidannan ba nan aka haifi
Kanina Shafik, lokacinda Father ya sai
wannan gidan bamu da wani suna ban da
`ya`yan dan baiwa kuma `yan baiwa... Babu
wata me aiki da muka dauka duk da an
kawo mu daga Turai. Ni da Father da
mummy muka zba Omo da ruwa muka
wanke, abin sha`awa abin dadı, mum da dad
na komai tare babu wata husuma ko nisa da
juna a tsakaninsu, ni `yarsu ina taya su da
abinda zan iya daidai shekaruna"
Ta kakkane ido don ja da hawayen da
ya ciko kwandon idanunta ya fara tsiyayewa
ba tare da izini ba. Ta bar jikin wundon da
sauri domin ta doshi wata mfakar. Farid
wanda bai ce komai ba don bai da abin cewa
a fatar baki sai a zuciya ya ci gaba da binta
da kallo.
"Yau babu Father, babu mom ba dan
karamin kanina, daga ni sai wannan gida,
amma ba zan karaya ba zan wanke shi ni
adai don na sake farawa daga farkon faifai
105 Mafiyan Masoyа-2 Ralma Abdulmajid
دو
na rayuwar Farida kadaitacciya a rayuwarta
Ta shiga bayan gidan da aka tanada a
falon don baki ta dauko roba cike da ruwa ta
fito. Bata iya foyc mamakinta ba a yayinda
ta ga Farid tsayc ya nade kafafun wandonsa
ya cire rigarsa ta sama sauransa singileti ya
dauko soso da Omo. Bata iya ce masa komai
ba kallonsa takkc a hankali ta ajiyc ruwa.
"Bakc kadai bace ko yanzu a
rayuwarki.. kina da Farid wato ni...ko zaki
amince min mu wanke sabon gidan
rayuwarki tare don fara sabuwar rayuwa
tare?"
Ta waro manyan idanunta ta tayi
sama da kasa da kanta na al`adarta ta neman
tafsiri kan wani abu da bata gama ganewa
ba. Ya dan lumshe ido ya yi murmushi
sannan shima ya gyada kai na nuna mata
lallai yana nufin abinda ta fahimta.
"Me zan ce maka Farid?"
Ya karbi bokitin ruwan ya fara yayyafawa a fadin falon.
"Kada ki ce komai so nake ki
sunkuya mu wanke gidan nan tare"
Sama da mintuna goma sha biyar
suna zube a Kasan falonnnan suna goge shi
10o Mafiyan Masoyа-2 Rahma Abdulmajid
da wasu kananan tawulai hudu da Farid ya
fita ya sayo musu, amma gaskiyar lamari
Farid ke wankewa da iya karfinsa, ita kuwa
Farida jikinta a mace take dan goge-gogen
babban aikinta shine satar kallon sa da
mamaki da tuhuma da shauki da neman
tafsiri kan dalilinsa na taimakonta har zuwa
wannan mataki na karshe da ma`aikatanta
duka basa son hada sunansu ma da
kamfaninta balle ita.Da alamar Farid ya lura
da hakan shiyasa yake kara samin allurar
zage karfi musamman ma da duk lokacinda
yake tsayawa ya share gumi sukan hada ido
da Farida su yi wa juna murmushi. A haka
suka kammala wankewa da tsanewada busar
wa sannan Farid ya wuce ya kunna fankar
tsaye mai karfi wadda iskar farko ta fara da
kado rigarsa da ya rataye jikin `yarsandar
ratayar suite da ta ragu a falon. Farida ta fi
kusa da rigar don haka a guje ta cafe don
kada ta fada jikakken falon ta jike, amma
hakan sai ya haifar da wani abu da zai bude
sabon shafi a ryuwar Farid da Farida, wato
dan karamin akwatin zobe ja ya fado
wanda Faridar ta bi shi da kallo ta kuma
gane shi da abinda ke cikı a yayinda Farid
107 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ke saurin daukewa. A karo na farko kenan
da ta dan ji kishi taa son tambayar abinda ba
dole bane ta so jin amsar ba.
'Za ka'nemi aure ne Farid?"
Ya goge akwatin a jikin wandonsa
yana murmushi.
"zan dai nemi soyayya kafin aure ko
Allah Zai sa na samu?"
Tayi murumushin da ta saba a duk
lokacinda take son danne wani ciwo.
"Bana jin ba Za ka dace ba don duk
macen da ta sameka dacentaaa ya fi naka
yawa"
Yanzu kallonta yake da iya hangen
idanunsa yana tattaro dauriya ta karshen
tika-tika.
"Har ke Farida?"
Ta dube shi ta yi fari da ido ta koma
za ta rataye rigarsa.
"Ni ce kan gaba"
"to ki karbi zoben nan a hannuna in
har zan iya samin soyayyarki"
Ta jima tana jin nauyin juyo wa har
da ma rikicewa da jin sabon yanayi, amma
da ta samu ta juyo din sai ta sami idanuna
cike da soyayya suna kanta, yana mika mata
1
19
IL
108 Mafiyan Maxoya-2 Rahma Abdulmajid
zoben.
"Ka ce min wasa kake Farid?"
"Ban taba wasa da gurbin kia
zuciyata ba. Gurbi ne da wanin ki bai taba
shiga ba, na kuma gama tabbatar da ba bu
me shiga... Ban taba kasancewa kusa dake
don wani abu ba sai don kada na nisanci
abinda zuciyata ke son kusanta. Mota gida,
albashi da matsayi a ofis bai taba zamowa
muradina sama da ke ba Farida, wannan ne
matsayinki a zuciyata a tun gani na dake na
uku har zuwa yau, har kuma gobe"
Farida ta dinga kada kai na rikita tana
kallon sa tana daukewa.
"amma me yasa baka gaya min
ba... Oh God! Me yasa za ka kunshe wannan
kunshi a ranka kai kaďai? Farid a ina
soyayya ta taba kunsuwa a zuciya daya rak
babu ko agajin fatar baki ballantana ido?".
"saboda bana so na rasa ki, bana so
neman kusanci ya janyo na kasa ko
ganinkiSaboda kin mini nisa... ba a dukiya
ba Farida lokacinda na zo da neman hadin
soyayya kin riga kin bai wa wani..Na zauna
ina gaya wa zuciyata karyar wata ran za ki
zo gareta in kika gane ta, amma a da ranar
109 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ban tayi da auren soyayya kika zo... san
yaya zan yi ba. Ko a yanzu da nake gaya
miki, duk da ina fatan ki amsa soyayyata
din, amma in baki amsa ba din ya isheni na
sauke nauyi....ya ishe ni na ji na baki
gudunmuwar tarayya da baki tabbacin ba ke
kadai bace a rayuwar da kike zaton ke kadai
ce, ki sani wani na tare dake yana neman ku
yi tarayya a duk daci da dadi na rayuwarki"
Farida a yanzu murmushi take tana
kallonsa, zuciyarta ta kwanta da shi matuka,
ta ji dadin abinda yake fada mata kuma tana
son ganin hakan a aikace
"Farid kana sona?"
Ina son ki Farida... Ina son in rayu
59
dake a sauran abinda ya rage wa rayuwata
"Ka ko same ni da yardar Allah...Ban
taba kinka ba, amma ban taba bari zuciyata
ta yarda ta soka ba don kada na sauya wa
yadda ka zo gare ni matsayi, amma yau zan
fara son ka a sake babu kaukautawa, zan
bude sabon shafin rayuwa don kai"
S
da
da
1a
k
1
32
31
a
*** *** ****
Tarihin fara soyayya tsakanin Farida
da Farid ya tsaya inda masoyan suka shiga
Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
sabuwar rayuwa ta farinciki ta inda bacci ke
raba su. A yayinda duniya ke jiran sake
Sullowar Faridar wadda tun bayan me
aukuwa ta auku aka dena jin duriyarta, ba a
fitar da ran za ta sake motsi ba kasancewar
an santa da salon daukar gayya, amma ga
mamakin jama`a bacewar Faridar ta ci gaba
ba tare da kowa ya san me take ciki ba
kasancewar sun lullube soyayyar tasu ita da
masoyin nata har suka amince da yin aure
babu wanda ya ji sai a ziyarar da suka kai
wa mahaifiyar Farida wadda har yanzu take
kwance a kasar Faransa ban da ido babu abu
me motsi a jikinta
*** *** ****
Farida zaune a hannun kujerar
guragun da mahaifiyarta ke kai hannayenta
na matsa hannun mahaifiyar tata tana matse
hawayenta cikin murmushi. Suka kalli Farid
wanda ke tsaye cikin tagumi Maman tayi
murmushi ta dan motsa baki kamar tace
wani waani abu amma babu dama. Farida ta
amshi maganar da alamar ta san me take son
tambaya
"Shine mum...shine sabon masoyina
11 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
da zamu yi aurc nan da wata guda in kin sa
albarka....muna són junanmu fiye da inda
kike zato, zamu sake gina kanmu nesa da
rigingimu, zamu sake zama' iyali a lokacin
kin sami lafiya ki zo ki zauna fare'da mu da
jikokinki Ko Fidi?" bokm : i
Farid ya gyada kai.
"insha Allahu Mama..Allah Zai baki
lafiya ki kasance tare damu ckin annishuwa"
*** *** ****
Wannan haduwa a asibiti ce ta isa
hannun yan jarida har suka dauka suka
sami na bugawa cewa Farida ta zamio
sabuwar mutum za ta yi aure.
Ibrahim Balala na zaunc a mazaunin
da ya saba zama wato Rafar beneyana
motsa shayinsa kahsa a sunkuye yana
sauraron sakatare. mesa kin godiva
"Me nene;abarin Faridan sohon
"Jiya ta bayyana wasu jaridu sun
kawota"
Da sauri Ibrahim ya ago kaf.
"Me suka ce a kanta? Bani jaridar"
Sakatare ya jatyo jaridai a aljihunsa
yana murmushi ganin ya kamabin faranta
12 Mufiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ran me gidansa.
"Ta bayyana a faduwar karshe inda ta
amince da Kaddararta za ta auri tsohon
yaronta mara asali wai shi Farid"
Ibrahim ya saki kofin shayin ya bude
jaridar yana dubawa a haukace. Bai san ta
inda kishi fishi da haushi ya shige shi ba
"Farida za ta yi aure? Farida za ta so
wani kenan bayan ni?"
Sakatare ya tsaya yana kallon
mamaki.
"nan da wata daya Farida za ta yi
aure? Farid da na sani shi za ta aura? Son sa
take?"
"Ranka ya dade kana sonta ne har
yanzu kake so ku yafe wa juna bayan duk
abinda ya faru?
Maimakon ya amsa sai ya haukace a
falon ya fara yayyaga jaridar yana dukan
kirjinsa.
"wa ya ce maka bana son ta? Bata isa
tayi wani aure ta bar ni ni kaďai ba"
113 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
TARA
Ango da Amarya sun yi sallama da
masu taya su murna suka hau motarsu su
biyu don kai kansu ga sabon gidansu su
kadai. Farid ke tuki yayinda Farida ke
jingine da jikinsa cikin wani nashadi da ya
hana hakoransu gajiya har zuwa kofar
gidan nasu inda suka sami mota ta kakare
kofar gidan da mutum a gabanta tsaye.
Farid bai gane ko wane ne ba sai kashe ido
yakc yana lekawa a yayinda Farida ta tashi
zaune zumbur don ta gane Ibrahim Bally.
A waje suka faka motar Farid yayi
ta maza ya sauko don ganin ko wane ne
amma Farida ta gagara zama a motar ta
biyo shi.
'Bally? Me ka zo yi mana a daren
amarcin mu ?"
Tayi saurin fara magana kafin Farid
Ya dube ta yayi murmushi ya kada
kai sannan y dauko farar tuta yana
kadawa
"Na zo1 na ba da gari na yi miki
114 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
murna cewa kin cinye fadan namu, kin yi
nasara, kamar yadda kika ce kin san ta
yadda za ki kayar da ni a ruwan sanyi"
Ya juya baya a yayinda Farid ya
doshi bayan nasa, amma Farida ta rike shi
da kada kai don ta fahimci sanyin da
mutumin nata ya zo da shi.
"Na zo ne na mika wuya na yarda da
kin yi min dukan karshe da ba zan iya
ramawa ba"
Hakika kudi, da suna, da rayuwa
duk sun tafi a kan yakin mu Farida, amma
ban taba mafarkin ke za ki tafi ba sai yau
da na ga da gaske kin yi aure za ki bar
duriyata da gani sai wajc. Ko ba komai ke
in kin tuna zafin abinda ya faru za ki iya
samin me kawar miki da shi yayinda ni
יי bana jin zan samu"
Ya dan lakaci hancinsa a yayinda ya
Karaso gaban Farid dake hucin jiran artabu
"Farid kai ne zan ma murna don yau
za ka san Faridar da ba ka san ta ba a da.
Farida a matar namiji ya kammala kamalar
kamilallu. Kada ka yi wisa da magana ta
Jomin ina da shaidar nine na mijin farko a
115 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
rayuwar Farida kamar yadda take matar
farko a rayuwata ta waycwa da magega
matsayin mace. Wannan Wani gwaji ne da
ba za mu manta da shi ba amma ina s,kа
kwatanta mantar da Farida ranakurк
na rayuwarta in har kai na miji ne, ba
faura auren ba ne nasarar ba, mantar daa
wannan mintocin farkon a nan yakin yake"
A yanzu ne Farida ta fahimci
muhimmancinta na shiga tsakanin mazajen
a yayinda ta lura da Farid na dunkula
hannunsa na dama bayan da yansaki
hannunta da ya rike da fari.Tar kamo
hannun ta sake zura duka nata bjyn a cikin
su Bb Bent sti
"mun gode da shawarwarinBalala, ka
je gida muna bukatar lokagin junan yshe
ni da miji na ba na 3rd party ba1
Ta wuce da Farid wanda ke waigen
Balala zuwa cikin gida suka bar shitsayg
KS ***** ωςλ λς κ «
1..A gefen gadonstaune yakhiyana
ake kamar, harsyanru kalmomin Balalgina
yanshiramma bayanso amarya ta gang ya
araya musamman nda lake la zumudvida
116 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
nuna murna tana ba shi labaran muhimman
abubuwanda suka faru a bikin.
Farida ta Karaso da dan karamin
kofi na energy drink ta tura shi gefen
gadon ta zauna kusa da shi
"Baby na ba dai batun Ibrahim ne ke
rarraba hankalinka ba?"
Ya dan juyo yana neman abin gaya
mata a yanzu amma ya rasa sai turo
nunfashi.
"ba abu ne me sauki ka iya
mancewa da wani babban abu mafi dadi
daya taba faruwa a ajuwarka ba Farida?"
Ya dan kamo fuskarta ya matso da
ita kusa da tasa.
"Ina mia à ce hine wannan na miji ná
farko a ravuwarki"
Farida ta lumshe ido na dan wani
lokaci sannan ta lalubi mazaunin zuciyarsa
ta dora kanta.
<<7a ka iya mayar da kanka in ka so
Farid. Kavi komai ka zamo namijin farko
da zai bani wani salon a rayuuwa da zai
yaudare ya juya mafarkina. Na san za kaа
iya tuma
1
Mafiyan Masoya-2 Ralma Abdulmajid
tunaninka kai kaďai. Farid kada ka manta
mutumin da yayi maka takamar shinc
namijin farko a rayuwata shi dinnc dai
wanda ya koya min darasin bakin cikin da
sai kai ne ka goge shi, shi ya kakkarya
zuciyata ya gustsittsira wanda sai kai ne ka
sake hade min ita wuri guda. Don Allah ka
yi komai na karkade wannan darussansa
daga kwanyata. Na shigo rayuwarka ne
don ina so in zamo sabuwar Farida wadda
bata da tarihi sai Farid"
Farid ya dago ta ya sake zuba mata
ido da kallon nacin kauna.
"Farida ki yarda zan yi komai, in
nace komai ina nufin kowace irin dabarata
don mayar da kaina na farko na karshe a
rayuwarki"
"Komai Farid kayi, ni ma ina nufin
komai kayi ka karasa sauyanin da ka
dauko yi, na san inda na kai yanzu ba za
ka sha wahala ba"
*** *** ***
Tatsiyayo giyar wuskin a dan siririn
118 Mafiyan Masoya-2 Ralma Abdulmajid
kofi ta dunfaro shi, ganin idanunsa a kanta
baya kiftawa ya sa ta rage sauri a tafiyarta
zuwa mazauninsa domin ta sami damar yin
duk wata tafiyar rausaya da ta san ta taba
yi ta ja hankalin namiji da ita har ta iso
gare shi ta dogara da gwiwarsa bai dena
kallon ta ba
"big boy, ka kora wannan kofin ka
hada da ni ka ga in za ka kwana da tuna
wata abu Farida"
Ibrahim yayi murmushi ya karбi
kofin ya zura masa ido.
"me nene aikin wannan shi kadai kafin
naki
"Aikinsa shinc ya mantar da kai
rayuwar baya da nauyinta, ya sa ka zamo
sakayau a hannun dadin ka wato ni
"A cikin rayuwar baya har da
Farida?"
Ya bukata
Ta langaba wuya
"ita ce kan gaba"
Yayi murmushi a hankali ya saki
kofin kasa ya fadi ya fashe.
Ban taba neman abinda zai mantar
119 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
da ni Farida ba ko a halal ballantana a
haram irin giya, masoyin da ya nemi manta
masoyinsa bai kai rukunin so ba Fresh
Lady.Tun 'a baya ban nemi abinda zai
mantar da ni Farida ba ballantana Faridar
yau, wadda ke cikin kwalliya da farinciki
na amarci.."
Ya ture ta ya mike tsaye yana duban
sama
"Tayi kyau ta tuna min kyawunta na
farko a ranar amarcinmu, amma wai yau
tana jikin wani namiji ba Bally ba kuma
tana farinciki. Ni kuma gani a nan ina
cikin kadaicin da ko a Stadium nake me
cike da dubban jama`a zan dinga ji na ni
kadai don babu Farida a jikina a lokacinda
na fi bukatarta"
Ya daki teburin gilasin da hannunsa
wanda ya fashe ya yanke shi, amma bai ji
ba ya soma kuka.
"Farida mc yasa kike samin hanyar
ci na da yaki ne kullun? Duk nasarata yau
kin zubar da ita da nasarar da ba zan taba
yi ba.Kin sake shuka min rayuwar
kadaicin da zan ji tamkar a kabari na nake
120 Mafiyan Masoya-2 Ralma Abdulmajid
tunda ban zaci akwai me irin ciwo na ba,
ko matar da a kayi wa kishiya a daren da
mijinta ke wajen wata in ta gan ni za ta
gode wa Allah da Ya tsirar da ita daga
tafasa irin tawa... Me yasa kike nasara a
kaina Rida? Ko dai sirrin shine don ba zan
iya dena son ki ba?"
Jinin da ke zuba a hannunsa da ke
6ata fararen kayansa ne ya tsorata Fresh
Lady ta dan karaso don ta agaje shi, amma
ga mamakinta sai ta ga ya shako ta ya zare
ido yana nishi dai dai. A tsorace ta kasa
cewa komai har lokacinda ya zaro wasu
daurin daloli ya watsa mata.
a
"Wannan kike so? To ga su kwashi
ki fita, amma ki sani ni ba mace nake nema
ba, Farida nake nema, ita nake so
matsayin abin son zuciyata ba mace ba. Ki
bar nan kafin nayi wani abu da ya fi haka
lalacewa"
Tana makyarkyata ya daka tsawa, ta
kwashi kudin ta fice. Bally ya tafi da
durkuso a cikin jininsa da ya dige ya fara
kuka wiwi
121 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
**** ****
****
Mahdi yayi dariya har da tintsirawa.
"kana nufin sai da kayi arba'in
sannan ka fito sai kace me jego?"
Farid yayi dariya
יי
"in kana zaton wasa nake lissafa
mana ka gani...yau auren mu kwana
arba'in wallahi, ba za ka fahimta bane
tunda kai ban da kanka babu wanda kake
so, ni ko ban da Farida babu wanda nake
so.. .yanzu haka da ba dan kada na gundire
ta ba inna koma Allah wani arba'in din zan
kara yi"
Suka tafa
"To dakata. Yanzu ba batun arba`in
ba, ka ce Farida ta baka wuka da`nama na
ka sauya ta don ka zamo na mijin farko a
tare da ita kana ga haka zai yiwu?"
Farid ya kada kai.
"zai yiwu ko ba zai yiwu ba ba
bukata ta ba kenan. Bukata ta ita ce in
sauya Farida daga irin matar da Ibrahim
Hadi ya taba sani zuwa irin nau'in macen
da zan iya zama da ita"
122 Mafiyan Maxoya-2 Rahma Abdulmajid
Mahdi ya jima yana gyada kai
"Ko za ka iya zana min irin matar da
kake so?"
"Kana nufin kace ka manta zane
na?"
"Wancan na da lokacin da muke
kauye ban manta ba, amma tabbas na san
ya sauya tunda ka auri irin Farida don..."
"Ko daya cikin zanen babu wanda
ya sauya,kuma Farida nake son mayarwa
hakan da karfin soyayya"
Mahdi ya fara kidayar yatsu cikin
mamaki.
"zanen ka fa shine kamar
haka...Mace mara aiki sai rainon yaranka,
macen da bata kwalliya sai daddare in ka
dawo,Macen da bata ja da kai a komai sai
yi na yi bari na bari...Macenda bata hulda
da kowa sai wanda ka yarda ko biki ko
gaisuwa ko jaje sai wanda ka amince... ina
jin sune zanen ko ka sauya wasu ne?"
Sune dai mutumina ka cika shegiyar
kwanya wallahi sai ka сe CD"
"Kuma su kake son ka mayar da ba
ma wata 'yar Sakandire ba Faridar da ta
2
123 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
san duniya duniya ta san ta? Farida me
kwana a ofis duk da tana shugaba don son
aiki.. Faridar da a da da tace ina zuwa bari
in je gida in yi wanka za ka ji ta bugo
waya da ga China? Duk ita za ka yi wa
wannan sabon horon ba ma wata yar
jami`a da asalinta daga kuayenku take
ba?"
"Kwarai kuma zan sake baka
mamaki kamar yadda na baka mamaki da
na auri Faridar da ka zaci ba zan taba
isarta kallo ba"
"mutumina kayi hattara! Ka kunna
hasken aurenka kada ka kashe shi kwana
kusa da taurin kai da son ra'ayin rikau"
"Ba ruwanka malam. Kai naka ido..
komai sai ka ce mutum ba zai iya ba anya
ma ba zan' dena shawara ko gaya maka
sirrina ba kuwa?"
"Allah Ya baka hakuri, da alamu dai
bana tababa zaman kwanaki arba'in na
soyayya zai sake nanata adadin a zaman
tinkiya".
*** *** ****
Farid na tsaye a kicin din yana yanka musu
124 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
lemo Farida ta garzayo da gudu ta
rungume shi ta baya.
"Ridy tayani murna.... taya ni raba
murnan nan kada tayi min yawa"
Ya liko hannayenta a kirkinsa ba
tare ya juyo ba yana dariya..
"Me muka samu Baby na? Kasa
murnan hudu ki ba ni kashi uku kada ta
wahalar min da murmushinki"
Ridy.. na sami Offer. Mister
Kosvisky abokin Father ne yake son ba ni
Merketting Manager na kamfaninshi ba
tare da an yi ko interview ba, yace yana
son ya ga yadda zan kayar da kasuwar
kowane me gasa da shi ne wannan zai
zamo dalilin samin kason farfado da
kamfanin mu na....
Bata karasa ba Farid ya ajiyc wukar
a hankali ya juya zai fita. Da sauri Farida
ta ruko shi.
"Hey! Ridy me ya faru ne? Na bata
maka rai ta wani wuri ne?"
Ya langaba kai na tausayin kai.
"Ban san duk kokarin da nake na in
yalwata miki bai isa ba sai yanzu"
125 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
A gigicc Farida ta soma kada kai.
Nooo! Sam! Ba haka bane
baby...Wallahi ba kudi ko wani matsayi
nake yiwa ba...me zan nema bayan duk
abinda kayi min..Farid ko wanke gida na
da muka yi tare a ranar da ka gabatar min
da soyayyarka ya ishe ni koshi ballantana
abubuwanda kake yi min. Don Allah ka yi
hakuri ba haka nake nufi ba"
Ya ruko hannayenta yana dubawa.
"To me zai sa ki je ki wahalar da
kanki kina wani aiki?, ki takura wadannan
kyawawan yastun da rubutu bayan na
dauke miki komai kuma zan iya ci gaba da
kwadago don ki ji dadi har iya rayuwata
um Ruhina"
Farida ta tallabo fuskarsa a zarazaran yatsunta.
"Baby na san kana komai ne don ka
faranta min rai, amma aiki ba don komai
nake so ba, sai don an raine ni da aiki, sai
na ji kamar bana nunfashi in babu
gwagwarmaya a gabana wanda ina jin
dadin yin ta fiye da duk wani wasa. ka
daure ka bar ni na yi aikin nan ko da
126 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
kyauta ne"
Ya kura mata ido na iya lokacin da
ya janyo maganadisun kaunarsa da ya
janyo karaya a zuciyarta.
"Baby bana so kiyi aiki...ki daure ki
bar abinda zai dami masoyinki mana um
rayuwata? Kada ki manta kin bani wuka
da nama na in iya sauya rayuwarki, kuma
ina son na cire ki daga irin rayuwar da za
ta sanya na ji akwai wani na mijin da bani
ba a wata tsohuwar rayuwarki,ina so in
nisanta ki da duk wani zubi naki na da da
zai iya farfado da waccan Faridar da kika
ce na cire a zatin ki...Don Allah kiyi min
wannan alfarmar mana"
Suka sumabci juna na tsayin lokaci
sannan Farida ta tsawaita dubansa cikin
karaya
"Ina matukar son aikin nan.. ban san
za ka hana ni ba.. amma tunda baka so na
bari"
Da sayuri ya rungume ta idanunsa a
lumshe yana nanata godiya, Fairda wadda
ta karbi rung nar kuwa idanunta kallon
kofa suke do ta kasa rabewa tsakanin
127 Mafiyan Masoya-2 Rahma Ahdulmajid
dumin jikinsa da tafasar ciwon asarar
aikinta da take
*** ***
Katon fili
***
Katon gida a cikin na
shukc-shuke ya ji fitilu da kwalliya irinta
gargajiya, girman ne ya lamushe jama'an
da ke kara-kaina suna ta aiyukan taryar
baki, maza akasari da dogayen riguna da
rawani mata kuwa da laffaya. Babban
falon ko ina ka juya cure yake da manyan
shimfidar abinci da kayan lambu masu iya daukar cikin mutum ashirin-ashirin.
Farida da Farid na can zaune kusa
da mahaifiyarta wadda a yanzu take cikin
gidan nata mahaifin a birnin Asmaran
kasar Eritria wadda tun bayan da wasu
sassan jikinta suka soma motsawa har ta
fara samin baki ta bukaci a kai ta cikin
'yan uwanta dake jibge a gidan gadon don
yin zaman jinya.
Wannan shine zuwan Farid na farko
garin duk da farida ta zo wajen sau uku
duba lafiyar mahaifiyartata tun bayan
dawowarta, wannan ya sanya mahaifiyar ta
128 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
sanya kowa ya taya ta murna da bikin
murna inda dangi suka cika ko ina aka yi
wa Farid da Farida shigar amarya da ango
na kabilar Tigre aka yi rawan gargajiya da
wake-wake, aka ci aka sha aka gaggaisa
har zuwa dare inda Farida ta dauki mijinta
zuwa kallon wata tiyata da za a yi wasu
wasannin kwaikwayon na kan Stage.
A wurin kallon suna makale da juna
ita da Farid cikin annishuwa da duhun
dakin tiyatar dukansu suna cin cingam don
kara gauraya nunfashinsu da kamshi
wanda a yanzu suke shaka. Wannan ya
sanya suka bukaci kara cin wani abu bayan
da aka kammala tiyata ta farko kafin a
shiga ta biyu.
A dan falon kofi da guggurun ne
wani dogon saurayi me