dora
musu asara a wanda suka saya lallai da
hannun su za su karyar da wanda suka sayar,
ta nan sun hutasshe ni"
Ta zauna da sauri
"Ba mu da isasshen lokaci don in
suka kai sha biyu ko da minti talatin ne na
gobe za su sami riba ko yaya wadda ni kuma
na ke son hanawa. Kana da awoyi goma sha
biyar ka nuna mana kwarewar ka don samar
da hujjojin ga wannan zato da tuni su Bally
ke kashe kudi don kada ya tabbata"
Farid ya gyara tsayiwa don maye
gurbin fargabanrsa da kwarin gwiwaa.
"Bani awa sha biyu kadai ki cire uku"
Farida 1a kwashi Jakarta ta sake tura
masa wata doguwar takarda.
25 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
"Ga jerin jaridun da za ka karanta da
jerin wadanda za ka tura wa sakon hasashen
don sune ma`abota kasuwar hannun jari ke
hulda dasu. kada ka manta wannan ne
gwajin ka na farko...ka kasance online zan
je wani taro, amma zan kasance tare da kai
online"
Ta fice daga ofishin tun kafin ya fita.
"Best of luck"
20 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
☑
C
τ
BIYU
Sanye da jan gajeren wando da farar
singileti yana dauke da kofin jan shayi yana
motsawa ya doso kofar da ake kada wa
Karaura.
"Please am coming"
Budewar ke da wuya sai ga
`yansanda guda uku sun bayyana a gabansa.
"ko kai ne Wilson Albert?"
"Yea nine akwa wani abu ne?"
Wanda yayi tambayar ya juyo ya dubi
ragowar guda biyun.
"Arrest him"
Suka shige shi yana kokarin binciken
ko menene amma basu tanka shi ba suka
jefa shi a mota.
*** *** ***
Ibrahim wanda ya tara jaridu a
gabansa ya duba duka labaran babu sa`Ida
ga kamfanin su ya yi jifa da waccan yayi jifa
da wannan. Baban gida dogon saurayi da ke
aiki da shi yayi biz sai wayoyi yake bugawa
amma babu wadda aka
27 Mafiyan Masoya-2 Rahma Ahdulmajid
dauka. Yajuyo ya dubi Ibrahim
"Ranka ya dade abu kamar hadin
baki? Duk suna ringin amma an ki dagawa.
Ko kuma duka manyan brokas din sun shiga
taro ne?"
Ibrahim ya zaro ido don huce a kalla
rabin fishinsa a kansa.
"Kamar hadin baki fa kace? Bama
hadin bakin bane kama ne? Da alamar ba
inda za ka a wannan aiki don har a gama
halakar da mu ba za ka san ina aka dosa ba.
Hannun jarin kamfani uku da muka dogara
da su a matsayin kadara tun ba a fara komai
ba su taru su fadi ka ce hadin baki? Muna
kiran duka brokas basa dagawa tunda sun
san ceto zan so a kawo ka ce kamar hadin
baki...Baka san aikin su Farida ba yaushe za
ka iya aikin hallaka ta?"
Ya daki tebur ya manna kansa da
bango, Babangida ya biyo shi da niyyar
cewa 'am sorry sir' amma ya dakatar da shi
da hannu ba tare da ya juyo ba sannan ya
daga murya
"Fita min daga ofis wawa, ina so in
ga kaina ni kadai"
Babangida ya fice babu 6ata lokaci.
Σ
ס
a
al
28 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Ibrahim ya gangaro zuwa kujera ya zauna
yana motsa jiki kamar wanda ake mintsina
yana fadın Kalmar.
"milyaan dari hudu duk awa goma
sha biyu. In na bar abin nan haka kamfanin
ma ba zai kai jibi ba. Dole in yi wani
abu...tsaya ma...zaman me nake?"
Ya zabura ya jajibi suite din ya fice.
*** *** ***
Farida wadda take ta 6arzar dariya
tana juya kujera bata kallon Farid wanda
yake duba takardun a hankali yana girgiza
kai.
"Sai da na gaya wa Ibrahim cewa
kada ya shiga wannan wasa da ni ya ki...da
zan kara awoyi ina wasan nan da sai dai
abin da za su yi gwanjonsa. Amma ba zan yi
haka ba... dole in kyale masa abinda za mu
yi haduwa ta biyu"
Farid ya yi dariya ya kale ta da gefen
ido.
"Chairman ya gama zaba miki suna.
Farida wato ta daban. Ke fa ta daban din
ce... na ga aikin abin nan fiye da abin da mu
muka saki".
2 Mufiyan Masovа-2 Ralima Abdulmajid
Ta daga wayar da ke mata kara
"Yes Father"
"Farida ina dawowa jibi, amma yanzu
ki tura Lauyan mu ya je ya nemi inda aka
kai Wilson wai yansanda sun kama shi.
Bana son shi a bayan kanta na ko awa biyar.
.
"Ok Father"
*** *** ***
Yana zaune a kan wani benci yana
kallon kasa a yayinda lauyan ya shigo tare
da rakiyar wani dansanda. Ya tsaya yana
gyara gaban rigarsa har Dansanda ya fita
sannan Wilson ya dago yana murmushi.
"Garkuwa... how may I help you?"
Lauyan ya yi murmushi ya zauna
kusa da shi
"Wilson ka cika pride, har yau har a
nan kai ne mai taimakawa.? Yaya dai ka zo
nan? Chair man yace na zo na yi belinka
sannan na dauki kes din yana dawowa jibı
ko za ka gaya min..."
Wilson ya juyar da kai yana dariya
"Garkuwa kenan ka gayawa Mast
ka yı latti,bana bukatar lauya daga wurinsa"
Mativan Masoya-2 Ralma Abdulmajid
Lauya ya dan taba baki.
"ban gane ba?"
"Ka gane Lauya...na riga na dfauki
lauya dake kula da lamarin kuma nine bana
son fita a yau sai na ga master din ido da
ido, amma kace masa in yana son komai da
tsari kada ya bar haduwar mu ta kai jibi, don
29
ba na so na jira shi har zuwa jibi a nan
Lauya ya dan matsa a kallon sa.
"Wilson ba na jin kana bukatar yin
fadin rai. An kawo ka ne nan da tuhumar
kashe wani babban mutum da ko master din
sai yayi ta maza yakc kayar da shi. Kа
bari....."
"Na fi ka sani garkuwa kuma shiyasa
na ce ka bari master ya zo, don ni ba zan fito
daga nan ba"
*** *** ***
Farida tayi kwalliya iya iyawarta
wadda ta kara maishe ta Farida ta tsaya a
kofar gidan su Farid wanda yayi maza ya
fito yana jin ham dinta. Ta kale shi tayi
dariya
"Let the destruction begin "
Ya dan bude mata kofar motar.
31 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
"Ko za ki bar ni na tuka motaar to?"
Ta mikar da yatsarta na tahiya ta na
kadawa cikin dariya mai janyc hankali
"Ni ce direbar hallakarwar ta yau, kai
me duba hanya ne, shiga na tuka ka"
Ya wuce mazauninsa da yake bai iya
musu da ita....ta ja motar da sauri yana mai
kallon hanya da idanunsa amma zuciyarsa
na satar kallon ta.
Tun da ta shigo wurin bikin akasarin
jama`ar suka mai da hankali kanta ba don ko
wacece ita kawai ba a a har sai don
kyawunta da kwalliyarta da yake jan
hankalin har bani jinsinta mata ba maza
kawai ba, hakan ya sanya mai gabatar da
bikin koda ya gama gabatar da ita ya ci gaba
da yaba wa da yin maganganun da suka
shafe ta a yayinda take bin mutane suna yin
gaisuwa cikin yalwar dariyar da fara`ar
yaushe gamo.
Tana tafe tana gabatar da Farid wanda
shi ma yake nasa kokarin na kada a bar shi a
baya cikin manyan mutanen da akasarinsu
basu san shi ba duk da sun san Farida.
Ibrahim na cikin mutanen da ke tsayc bai
dena murmushi ba duk da hakoransa ne
32 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
kawai a waje, don tunda Farida ta shigo ya
fara hangen ta ya ji ya takura ya matsu da
abinda bai san ma`anarsa ba. Ta yi kwalliya
tayi kyau ko musawa baya yi don ya san
natar tasa akwai kwalliyar asali da ta
kasuwa, abinda bai iya sani ba shine ko
damuwar me take haddasa wa zuciyarsa?
Baya taba yardà amsar ta zo kusa da so don
yana ganin ya yaki haka kamar yadda ya iya
yakar idanunsa da hana su satar kallon ta
duk da kunnuwa da idanun zuciyarsa na bin
ta da duk takunta a wannan falo. Kafada-da
kafada suka karaso inda yake ita da Farid
"Ran Ibrahim ya dade"
Ta ambata can kusa da kunnensa.
Ya juyo rike da kofi ya dube ta
sannan yayi murmushi.
"Hajiya Farida ina gajiya?"
Farid ma ya mika masa hannun suka
gaisa sama sama da yalwar dariya.
"Ashe kin zo bikin manyan
angwanai...."
Tayi dariya sannan ta yi fari
"Irin ku sun zo ai dole mu zo... da
dama abokanmu a ga sun daure sun fito
basu ji faduwar hannun jarin nan uku ba bai
a
A
33 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
hana su zumunci ba"
Ya dan kashe ido daidai yunkurin sa
na бoye adadin kaifin wannan magana.
Yana jijjiga ya dubi yatsunsa
"Ko kadan ba za su ji ba don faduwar
duk cikin shiri ne. dama ai ba za su ce suna
kasuwar gasa ba za su fuskanci irin wannan
ba"
Farid ya ja da baya a yayinda yake jin
kamar yana tsakiyar aljanna da yake umartar
duk abinda yake son ya faru cikin kunfa
yakun. Ita ma tana jijjiga da kofin a
hannunta.
"Abinda na fi jiye wa mutanen shine
yaya za a yi a ce kullun ku ake duka ku
bakwa iya duka?'
"Um`um ba basa iya duka bane suna
so suyi dukan karshe ne kada ki zaku"
to Allah Yasa dai faduwar darajar
bakin karfe a yau ba zai taba su ba, don na ji
an ce wasu sun sanya kudi a bakin karfe
yayinda gwanjon namu a jiya ya fadar da
kasuwarsa wadda za a so dogara a kai"
Ba da saninsa ba ya ji shi sit taye
yana kallon ta Lallai wannan wani babban
duka ne da in fa an kawo masa to dole ya
34 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
fasa masa hanci. A boye a sirri suka yi
cinikin badin karfen kuma ya jida don bayar
da tasa kwangilar ga kamfanonin sadarwa
masu shirin yin wayar karkashin kasa, bai
san ta ina zancen sirrinsu ke ketarawa zuwa
ga Farida har ta bata musu ba. Wannan tana
son ta fi mahaifinta `yan leken asiri... yana
matukar bukatar ya bar wurin don ya ji
labarin kasuwar bakin karfe don ya tabbatar
da abinda baya fatan tabbatar sa.
"Bari na ci gaba da sada zumunci
babban mutum na gaishc ka"
Ta zare jiki ta bar wuriin bayan da ta
janye haannun Farid.
Ya bi hannun Farid dake hannun
Farida da kallo har suka kule abinda ya ja
lokacinsa kafin ya dawo ta kan kasuwar
bakin karfe kenan.
35 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
UKU
Richard ya dinga duba takardun nan
faya bayan daya yana gyada kai, sannan
ya dubi dan sandan da ke tsaye a kusa da
kafadarsa.
"Su za ka lika a cikin kwanon
abincinsa kada ka damu ku zuba miya
akai, zai gane abinda nake nufi ba sai ya
karanta ba"
Dansandan yayi dariya.
"An gama mazaje in dai za ku ce mu
yi ai ba mu da ja"
Richard ya dago damin kudi 'yan
dubu-dubu da dansandan ya dade yana
kallon su kan tebur ya mika masa.
"Ga kafin alkalami, dama ka jima
da sanya musu arwa"
Ya karbe su hannu biyu yana dariya
"ranka ya dade ai na san nawa ne
indai kudi na gabanka kamar a gabana
yake... yau zai ci wannan takardar in dai
Wilson ne kada a damu"
1
1
1
こ
1
1
*** *** ***
36 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Na`ibi tsayc a wurin ganawa da
wadanda ake tsare dasu ya kasa zama duk
da Wilson a zaune yake yana murmushi.
Ya kasa zaman ne a dalilin kasa fassara
matsayin Wilson din gare shi da kuma
alwashin san a rashin yarda da bayar da kai
a gaban karamin yaronsa duk kuwa da
yaron Kashin bayansa ne na can kusa da
keya ma.
"har yanzu sai zaurance kake baka
gaya min dalilin da ya sanya ka ce in zo da
kaina ba, baka kuma gaya min dalilin da
ya sa ka ki karban tayin lauya da kamfani
yayi maka ba"
Wilson yayi dariya a hankali.
"Master kenan uaban gidana...Kana
manta cewa Wilson ya san ka fiye da
Farida yar cikinka. Master tare muke
kashewa mu raya in dai matsala ce, kenan
in dai da hannunka a abu babu wata nakira
י,
da za ka shiga in kasa ganewa...
Ya dan ci farce ya gyada kai.
Wilson ya ci gaba
"ch na san ni bani da basirar
shinshina danja ko jin radarta daga nesa,
37 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
amma fa ina da idanun ganinta kuma na
iya kerata Da a ce na iya wadannan
abubuwa da tun ranar mutuwar Hadi zan ji
kamshinsu a jikinka musamman da kayi
fishi kana zargina da ragon azanci na
kashe shi"
Na'ibi a karo na farko a rayuwarsa
ya nuna razana da duba duk kusurwoyin
dakin kada maganar na fita.
"Wilson maganar me kake ? Me
kake son gaya min?"
Wilson yayi dariya.
"Me gida kada ka ji tsoro ba kowa a
nan, ina mgana ne kan abin da ya kawo ni
nan. Na sami labarin duka sirrin da daga ni
sai kai ne muka san shi yanzu yana hannun
`yansanda. Wani abu da ya hana ni
amincewa tunani na na cewa kо
`yansandan Najeriya ne suka kware a
bincike suka gano lamarin shine rashin
fitowar sunan ka a kowanc daga cikin
laififukan. Idan 6ullarsu babu hannun Me
gida da lallai ya kamata a ce muna nan
tare"
"Wilson kana nufin ni ne na fadi
38 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
laifin da ya kawo ka nan?"
"ko kadan Masta, ina nufin dai
kaine ka bayar da hanyar da za a kawo ni
nan ka ga sai ka huta da ni kada barazanar
da kake jin zan iya kawo maka ta tabbata.
Kuma ga shi ka fara samun hutu. Farida cе
ke juya ofis, ka kade Wilson da Hadi
kenan? Haba Masta na sanwannan dabarar
tare muka kera ta kan tsohon wazirinka da
na maye gurbinsa Madwin"
Na`ibi
Ya dan matso kusa da kunnen
"A sakale a bayan talabijin dina ta
bango a ka sami lambar wayar direban da
ya kashe Hadi, kuma 'yan sanda sun kama
shi. Waya san da wannan lamba ban da kai
masta? Kuma Mujitaba ne dansandan da
ya je bincike gidana wanda in ka so kada
ya motsa ba zai motsa ba. Wani karin abin
mamaki shine an gano ina da hannu wajen
kashe Racheal. Master me yasa duk kisa da
hannunka bai fito ba shi ake tuhuma ta da
shi, amma wanda ka fito karara ba a
thumua ta da shi
Yayi dariya ya kawar da kai.
1
39 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
"Allah sarki! Talaka baya huta ba
sai manya irinku. Sai dai inda baka huta ba
shine baka da me kawar maka da duk wani
abokin gaba, domin abu ne da Farida ba za
ta taba yi ba. Na san hakan kuma ga shi
kana tafe da gamuwa da adawar sabon jini
dake shirin kawo ka gadon asibiti. Anya
baka yi saurin gamawa da ni ba?"
Na'ibi yayi ajiyar zuciya ya kada
kai.
"Wilson ban san ma'anar maganar
da kake ba sannan mamaki ya hana ni
fahimtar ka...Amma ka sani babu abinda
zai sanya na yi maka makarkashiya, kuma
har ma na zo gabanka ina cewa bani bane.
In kayi min wannan zato zan yi saurin
raina tunaninka"
Ya matso kusa da kunnensa.
"Duk da haka zan baka shawarar
kada kayi saurin yin wani abu na kwarewa
kafin ka gama kai wa ga tantance zatonka
don za ka ji jiki, ka san Na'ibi"
Ya bubbuga kafadarsa ya mayar da
hannayensa aljihu ya juya ya fita
a
i
a
a
r
a
1
e
e
e
1
a
40 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
*** *** ***
A bakin ruwa Richard yana dafe da
makaran karfen da ta raba shi da ruwan bai
juyo ba a lokacin da Ibrahim ya iso gare
shi yana masa kallon fishi a yanzu
"Ban san me kake nufi da game dina
ba. Ka karbi alkawarin kudi tsugugu don
ka ga faduwata ne ko me? Farida na ta
narka min tsiya babu wani motsi daga
wurinka".
Har yanzu bai juyo ba kada kai
kawai yayi
"Akwai motsi mana ranka ya
dade...zuwa an jima za ka ji an baza
neman Wilson cewa ya tsere daga wurin
hukumar `yansanda"
Ya juyo a yanzu ya kalli Ibrahim
"Ba zai sake damun ka ba"
Ibrahim Ya kwance tay dinsa har
Karshe yana jijjiga.
"Ba matsalata Wilson kawai ba ka
sani...Hasalima yayi cara ne da yawa in ba
haka ba me zan yi da Karen farauta. Ina
nufin Na'ibi da `yaarsa da suke son fin
karfina..."
ف
41 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Ya katse shi.
"Dakata ranka ya dade, ni ban iya
irin wasan su Farida ba, wannan yarana
suka dauko suke yi musu, amma ni babba
ne na girma bana wasa biyu daya nake yi.
A yanzu maganar da nake gaya maka su
Farida basa samin riba, sun kasa karfinsu
gida biyu ne, daya suna dukan ka da
ribarsu daya kuma zuba shi a sabon abinda
baka bukatar sani ni na san shi. Kuma
duka daya nake so in yi musu duka a huta.
Ba za su sake tashi ba. Trust me..... ni na
rubuta contract din nan da kai ba wani ba,
just give me a braek. Kai fa kana so ne a
karya Na`ibi a cikin gida da waje"
Ibrahim yayi ajiyuar zuciya yana ta
duban inda zai samo hakurinsa a
kusurwoyin ruwan.
"Well na ba da wannan satin ina son
in ga aiki"
42 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
HUDU
Farida ta dinga kade iska daga kanta
tana yawo na takaici.
"Father me ka dauke ni? Father ni
ce 'yarka ta fari ba Wilson ba, ni ce zan
iya tsayawa a matsayin me dukiyarka ba
Wilson ba..."
Ta karaso gabansa ta ritsa shi da
idon fishi.
"Sannan da rayuwata aka yi wannan
wasan ba da ta Wilson ba, ni ce me abin yi
a wannan fadan yaya za a yi rana tsaka ka
zo ka ce na bai wa Wilson kujerar Staff
Head yayi komai na koma gefe?"
Na`ibi sarkin sanya hannu a alihu,
ko gezau yana kallon ta.
"Saboda wannan ne kawai hanyar da
Wilson zai dena zargina da yi masa
makarkashiya a kan daure shi da aka yi"
Ta yi alama da yatsa.
"Dalili na daya, ina son jin na gaba"
"Saboda Farida kina 6arnar dukiya
da yawa a wannan rikicin wanda in Wilson
2
43 Mafiyan Masoуа-2 Rahma Abdulmajid
ne ina ga ba za a kai haka".
"Dalili na gaba, ban da wannan"
"Babu wasu sai wannan
Farida tayi dariya sannan ta gimtsc.
"Bari na kwance dalilan baya
Father. Kawai saboda kada Wilson ya
zarge ka ba dalili ne bane, don ka fi karfin
damuwa da zargi ko na gwamnati ne
ballantana na yaron kamfaninka har ka
gwammace 'yarka ta zarge ka maimakon
yaron naka...Dalili na biyu ko kama da
hankali bai yi ba domin ina da record na
dilmyar da kwantena dari da kuka taba yi
don kayar da Hadi a kwantena biyar kacal,
tun baku zama masu kadara irin ta yau ba,
da wa aka yi wannan ba da Wilson banc?
Me zai hana Father ka fito ka gaya min
dalilin cewa akwai abinda kake boyewa
kai da Wilson wanda baka so nisantarka da
shi ya fito da abin...gara ka gaya wa Farida
tunda ka san 'yarka za ta sinsino"
Faduwar gaba ce ta sanya Na`ibi
dako tsawar da bai yi niya ba.
"Eh! Ina da abinda nake 6oyewa
kuma shine sirrin kamlanina da duk
44 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Wilson ya san su, kina tsammanin idan ban
sasanta da Wilson ba a wannan yakin har
muka rabu abokan gaba suka yi zawarcinsa
ya koma hannunsu za ki iya yakar
kwanyarsa da ta Balala da ta sirrin mu da
ya tafi da su? Farida na kyale ki ki sake a
matsayin yarinyar da ta kware, amma kada
ki raina dabarata...Ni ne me wannan
mulkin kuma na zartas da hukumcin ki
hada karfi da Wilson ku yi aiki wannan ne
hukumcina"
Ya juya zai tafi amma Farida ta sha
gabansa
"Za a yi yadda kace Sir, amma ban
yarda da wannan dalilan da ka bayar ba
Father, Na san ka ba yau ba, abubuwan da
ka nuna na tashin hankali ne basu taba
zama maka tashin hankali ba, dole akwai
abinda yake sama da haka, wanda na baka
damar ka yi shawara ka gaya min gaskiya,
kafin na binciko da kaina"
Ta juya za ta fita daga ofishin a
yayinda suka ci karo da Lauyan da ya fado
a guje.
"Sir, yanzu labari ya iso mana
45 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Wilson ya kubuce daga hannun hukuma,
دو
an baza nemansa...
Na ibi ya juyo da karfi.
"guduwa? Me Wilson ke nema da
batun nan ne?"
"Shine abinda nake tsoro tunda mun
ba shi beli ya ki maimakon ya fito a
mutunce ya kara lalata lamarin da
guduwa...Ina tsoron yaron don ba zai yi
haka da gangan ba sai in da wani tsari"
Na`ibi ya dubi Farida sannan
Lauyan wanda tuni ya gane karatun beben
ya dan dauke bakinsa. Farida ta dube su da
kyau sannan tayi murmushi ta kada kai ta
bar ofishin.
*** ***
A ofoshin Farid take zaune tayi
tagumi bata komai sai nishi da kada kai.
Duk wani yunkuri da yayi zai yi magana
sai ta tsayar da shi 'kada ka watsa min
kwanyata' A haka aka share mintoci
ashirin da takwas inda ta bugo wata
tambaya.
"Me Wilson ya tsorata Father da shi
46 Mafiyan Masoya-2 Ralma Abdulmajid
shine nake son sani, shin batun kamfani ne
ko na cikin gida? Ni ce ba a so in sani
kawai ko duniya?"
Farid wanda babu matsalar da ta
dame shi ban da wadda Farida ta mayar
matsala yanzu ya sami abin cewa don da
alamar ta yanke shawarar yin magana.
"ko ma me ce ina jin ta kare... Oga
Wilson ya gudu ya bar rayuwarkи.
Maganar Chairman ya bukaci ki bar masa
kujcrarki shi da kansa ya kashe miki
wutar"
Ta dubi Farid da haushi.
"Kana zaton kujera ce ta dame ni?
Ina da offer ta aiki a kamfanunuwan da
suka fi Na`ibi G. Karatuna, kwarewata da
sunan Family na za su iya sama min
kujerar da ta fi wannan da nake
kai...Amma bukata ta bata wuce in yaye
murfin da ke rufe da wannan damuwar ta
Father kan Wilson ba..."
Ta dauke murya dan ta karasa
ragowar abinda take jin nauyin fadi a
cikinta.
"Ko dai zargin da Bally ya dage
A
47 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
cewa Father ne ya kashe masa uba akwai
gaskiya ciki? Wilson ana tuhumar sa ne da
kisa amma Father ya hana in ji ko kisan waye...Idan ba Kisan Hadi ba wane babba
za a kashe da zai damu Father? Wane ne
za a iya bin kadin ransa da Father ko
Wilson?....Ina samin Father da Wilson da
nayi suna magana daf da zuwan su Hadi
neman aurena inda suka ki karasa zancen
Wilson ya fita? Lallai ban kara ganinsa ba
ko a ofis sai bayan mutuwar Hadi da
hatsarin Bally"
Ta zabura a haukace, abinda ya mikar da Farid.
i
a
a
ar
ita
m
n
a
a
n
"Lafiya?" Ka Tayi masa ishara da hannu ta fice da
sauri
*** *** ***
kur.
Richard yana yiwa Balala kallon
"ka gaji mahaifinka matuka, fishi ne
ya hana shi nasara kan Na'ibi har ya rasa
ransa, wanda in ka ce da wannan gadon za
ka yi fada da Na`ibi kai ma zai ga
48 Mativan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
bayanka, don mutum ne me kwantar da kai
da zuciya yayi tunani
Ibrahim ya tattara goshi don nuna
damuwa.
"Wanc irin hakuri kake so inyi? Ina
biyanka Milyoyi ina hasarar milyoyi babu
wata riba? Har yau sai...
"Idan dukan a sake tashi a kara kake
son yi wa Group din Mansur Na'ibi to zan
hada ka da yara da za su yi maka, amma
kada kayi mamaki in Na'ibi ya biya ni ka
ga ina ja da kai da yaran nawa, don ni
dankasuwa ne kuma ina zaben abinda ya
dace ne da ribar kasuwancina. Ina son in
dakar maka Naibi inda da kafarsa zai
gudu ya bar ka, abinda ka biya ni nayi
kenan, wannan ko zai dauki watanni don
Na`ibi babban giwa ne, zan baka dama nan
da kwana hudu ka yi wa Na`ibi babban
dukan da zai zamo fashi ko siyasa ne
kawai za su iya farfado da shi, na san a
nan zai zabi siyasa, a nan zai karar da
garkuwar kudinsa inda ana sauran zabe
kadan zamu yi masa fallasar da ko
iyalansa ba za su saura da shi ba ballantana
49 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
masu jefa kuri'a. Idan kayi hakuri Bala
Hadi, Na'ibi ya kare"
Sanyin da Ibrahim ya ji a zuciyarsa
ya bayyana a kan fuskarsa ta hanyar
murmushi da gamsuwa.
"Da me za mu kayar da shi nan da
kwanaki hudu?"
Richard ya fake da fuskarsa yana
kunna kakkaurar tabar.
"Yayi odar Screen din tare haske
daga cutar da ido wanda tuni yara sun
sanya sinadarin kokewa a kan milyoyi
kamar yadda aka sanya gubar cutar da ido
ko nunfashi a cikin wasu dubbai da za su
kasashen ketare masu saurin dago barna
da daukar mataki ba irin kasar nan ba. Nan
da sati za a iza binciken da zai gano cewa
kayansa ne suka yi wannan 6arnar. Sanin
ka ne za ka ci riba da dama kamar shagala
da zai yi da wannan matsalar ya mance da
yaki da kai, sannan zai yi ta 6arin kudi don
kashe maganar inda a karshe dole ya biya
diyar da za ta kara karya shi har ya kai ga
neman manyan kudi cikin gaugawa. ba
shi da zabi ban da lasisin siyasar da yake ji
S Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ya fi karfi wato takarar gwamna. A nan
yara sun samar da kayan karya shi amma
fa sai a na daf"
Bally cikin dariya yake magana
yanzu.
"Idan ko haka ta faru ina jin ko
takarar gwamnan ba zai iya ba don a yau
din nan kamfani na yayi nasarar kwace
babbar kwangilar da suke dauka a
matsayin sabon jari wato na kera wa China
makamashin Sola a jikin cajar waya me
sauki. Ya narka kudi a kai, amma mun
bayar da namu kasafin babu ribar naira
daya a ciki don mu haifar masa da hasara,
sannan mun sayar da fasahar caji da iska
wadda ta karya fasaharsa ta caji babu igiya
rugu-rugu
Suka tafa.
"Yanzu ka fara sanin muna aiki
kenan? Sannan Wilson ya 6ace daga
rayuwarsa ba za a sake jinsa ba ballantana
ya dame ka"
1
4
소
*** *** ***
Ji kake Tau! Sai da kumatun Farida
ر
51 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ya waskace na 'yan sakanni, ita ma kuma
mamaki bai sanya ta juyo ta kalli
mahaifiyarta ba wadda ke cikin fishi.
"Me kike daukan kanki? Fekewa da
iyawa wanne kika fi mu? Ubanki za ki
tsaya kina tuhuma da kisan makiyinsa dan
kin nace kina son dan shi duk da cutar da
kc da yake? Idan ke wata isasshiya ce ba
za ki mayar da hankali kan hasarar da aka
hango za ku yi ba wadda ke son haifar
masa ciwo sai ki kara iza wuta? Kina zaton
sunan kamfaninku zai sake saura idan aka
yada wa duniya cewa har da mutane irinsu
Prof Yinka Bowale da duniya ta ba su
kyautar Nobel a cikin wadanda
kamfaninku zai biya diyya ya bata musu
ido. Kina so ki ce min baki san abinda
hakan ke nufi ba?"
A yanzu Farida na kallon ta ne rike
da kumatu cikin zuciya wadda ta bayyana
a idanunta..
"Na gode Mama, amma ki sani babu
abinda ya kai zuciya yanci na zaben
abinda za ta mayar da hankali a kai. Ko me
dauke da ita a kirjinsa in ya ce miki yana
e
e
n
za
52 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
bata zabi karya yake, balle uwarsa ko
ubansa...Na gode da mari, amma kiyi
hakuri na zabi abinda zuciyata ke mayar
da hankali a kai"
Ta juya za ta fita. Na`ibi dake da
alamar rashin lafiya yayi tari kafin ya
samu ya kira ta. Ta tsaya ba tare da ta juyo
ba.
"Kiyi hakuri da hukumcin mamanki,
tayi ne cikin damuwa da halinda nake ciki
wanda ina ga shi ya kamata a ce kin mayar
da hankali. Farida Na guji bacewar Wilson
saboda rana irin ta yau ga shi kuma ta
auku. Bani da tababa ta wurinsa aka san
batun Screen har aka lahanta ni da shi, ta
wurinsa aka san fasahar Caji