An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
MAFIYAN MASOYA
RAHMA A.MAJI
HAUSABOOK.COM
2
Rahma A. Majid
2
Mafiyan
MASOYА
2 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Copy right(C):
Hakkin Mallaka (M)
Rahma Abdul Majid
An fara bugaawa: 2014
GARGADI
Ba a yarda a sarrafa ko a kwafa ko a juyi wani
bangare na wannan littafi ba tare da rubutaccen
izinin mai hakkin mallaka ba. Kazalika wannan
littafi ba labarin wani ko wata bane illa kagen
nishadi daga basirar mai shi.
ISBN:978-978-52359-9-9
3 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Gabatarwa
Hanyoyi da musabbabai na rubuta labarai sun
bambanta kuma sun yawaitá da ba za a iya kirgawa ba.
akwai masu rubutu don fadakarwa ko nashadantarwa ko
rikitarwa ko tsoratarwa ko ban tausayi ko ban dariya, kana
akwai masu bayar da labari don habaici ko zagi ko yabo ko
fallasa ko girgiza sha`awa ko kashe ta. Har ma da masu
rubutu don daukaka wani addini ko wata akida ko wani
imani. Gasu nan babu iyaka. Sai dai Rahma Abdul Majid a
wannan karo ta zo ne ba da daya daga cikin wannan dalilai
ko wasunsu ba, dalilina daya shine taya makarantana hira
wadanda sau tari sukan yi kewar rubutuna saboda dadewa
da akan yi ba a ji duriya ta ba. don haka mai karanta littafin
MAFIYAN MASOYA ya shirya yin hira ne da Rahma
AbdulMajid a majalisar hirarta ta alkalami da takarda.
A bangare guda kuma ina son yin amfani da damar
nin in bai wa masu jiran DA HANNUN MAZA 2 hakuri na
rashin ganinsa. Hakika labarin yadda hannun mazan yake
yana cikin na biyu kuma shine ma ginshikin littafin. Sai dai
wasu dalilai sun sanya ba zan ci gaba da labarin kamar
yadda na so ba, maimakon haka na bar masu karatu su zana
yadda suka so karshen littafin ya kasance wa zukatansu. Ina
mai bayar da hakuri bisa faruwar hakan kamar yadda nake
bayar da hakurin kan rashin jin filin masoya a wannan
karon, wannan ya biyo bayan yawan da shafukan littafin ke
da shi wanda ba zan so na kara muku nauyi bisa kudin sayar
shi ba. Ga masu jiran jerin labaran DUHU kuwa kada a
karaya. inshaAllah in da rai da lafiya za su ga guzirinsu
bayan wannan hira ta kare. Da fatan za mu yi hira lafiya mu
kare lafiya.
Rahma AbdulMajid
28/01/14
4 Mafiyan Masoya-2 Ralma Abdulmajid
DAYA
a cire wayar daga kunnensa a Y hankali yana kallon gabansa
cikin sanyin jiki. Can cikinsa
yana jin wani jiri mai tausayi da cakuda
kwazo da kasala wuri guda.
"Farida na gaya min ta zubar da
dana? Bata raini cikin ba...bata haife shi ba,
ta kashe shi?"
Dogon dake tsaye yana kallon sa rike
da wasu takardu shine Mai Kudi, ya sake
mai da hankali kan Ibrahim.
"Ranka ya dade kana son ta kenan har
yanzu?"
Ibrahim ya mike tsaye a hankali ya
zuba hannu a aljihu sannan ya yi ajiyar
zuciya.
"Kamar yadda na san har yanzu ita
ma tana sona...Sai dai ba wannan ne abin
damuwa ba.. abin da ya sanya Farida tayi
asarar wannan da namu da hannunta ba
karamin yaki ta shirya da ni ba...ta kuma
soma nasara da kashe min da, amma zan yi
A
5 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
nasara ta hanyar hana ta mallakar wani dan
a duniya. Amma Na'ibi shine abokin wasa
na ko ta ki ko ta so"
Ya dogara kansa jikin makarar kafar
benen.
"Amma sun cuce ni sun kashe min
uba sun kashe min da. Zasu biya ta hanyar
da basa so"
Ya juya ya hau sama.
*** *** ***
Na ibi da ke zaune a a hannun
kujerar yana duba wata takarda ya dubi
Farid da ya shigo ofishin wanda shi ma ya
dan dube su duka biyu, wato Farida dake
zaune tana juya kujerar ta ta me kamfani da
mahaifin dake nasa muhallin na zaman bako
a hannun kujera.Na`ibi ya dago ya kara
duban shi.
"Farid, ina so ka wakilce mu a wurin
mitin din samar da sadarwar otel da
GLOBAL SHARE suka shirya, ni kamar
yadda ka gani zan dauki hutu na na karshen
shekara wanda ogata Farida ta ba ni don ita
ce za ta ja akala har nan da wata biyu in
dawo. Sai ka taya ta aiki kamar yadda ka
Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
saba, amma abinda na ki jini shine kada ka
je ka sanya hannu a wannan takardar ko ka
saki wasu kudi sai da sanya hannun
shugabar mu Farida"
Ya jefa takardar a teburinta sannan ya
daki kafadar Farid wanda tuni ya amsa
masa.
"Best of luck"
Ya fice daga ofishin ya bar su.
Farid ya sake ya kalli Farida wadda
bai gani ba tsayin wata guda, amma ba
wannan ne abin damuwarsa ba, ramar da
tayi da karin haske wadda maimakon ta fitar
da wahala sai ta kara mata kwarjini da kyau
da yarinta a idonsa.
"Ranki ya dade barka da dawowa"
"Zauna Farid ina da hira da kai kafin
mu duba wannan abin da Dady ke kira aiki"
Ya dan balle maballai biyu na gaba
kwat din sa don ya zauna babu takura.
Ta cura hannayenta cikin juna tana
juya kujera.
"Kana da labarin abubuwan da suka
same ni kuwa?"
Ya dan kura mata ido. Ba za ee
asuwar sirikinta ba don kamar sun yi
7 Mafiyan Masoya-2 Rahma Ahdulmajid
gaisuwar wannan amma mene ne sabo da ya
same ta baya da ya ji an ce tayi jinya kuma
tun daga wancan loikaci kafar tsaigumi ta
toshe masa?
"Na ga dai kamar kin yi fama da jinya
kuma ya fito a jikinki kwarai"
Tayi murmushi sannan ta sunkuyar
da kai tana hangen wata majalla a damarta.
"Na rabu da mijina Bally na kuma yi
asarar dana sune abubuwan da suka same
nu
Ya ji gabansa ya rikito kasa...Lallai
sabon labari ya ke ji fil...Ba zai iya tantance
matsayinsa na me murna ko akasi ba saboda
sabuntar lamarin a gare shi duk da ya fara
iya kimanta girman lamarin ga Farida. "Deal!!!"
Wannan ce kawai kalmar da yake
maimaitawa ya kasa sauke idanu daga kanta.
Farida ta dago da yalwar murmushi
"ba na gaya maka ne don hankalinka
ya tashi ko ka tausaya min ba ina so in yi
matashiya ne kan babban aikin da ke
gabanmu"
Ta dan nil baya a kujerar
"Alakarmu da Bally ta tsinke kamar
F
5
S Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
yadda nayi asarar dana duk da girmansa a
zuciyata da zuciyarsa, sai dai a yanzu mun
fahimci cewa mummunar alakar dake
tsakanin kamfanoninmu biyu ta fi karfin
kyakkyawar alakar soyayyarmu don haka
dole mu bi me karfi,daga ni har shi an raine
mu ne ta hanyar biyyya ga abinda ya fi
Karfi...Abin da nake so kawai ka karanta a
wannan magana tawa shine jan aikin da ke
gabanmu.
Sati biyu kenan da muka kulla
alkawarin gasa da ganin bayan juna
tsakanina da Ibrahim, kuma za mu yi hakan
ne karkashin jagorancin kamfanoninmu.
Duk da cewa irin wannan yakin ba wanda
ko wane bangare zai so ko mafarkin kasa
yin nasara bane, kuma duk da yin nasarar
mu kan su Ibrahim ba bakon abu bane, ina
sane da cewa ya kawar da hannun kowa a
nasa yakin yana rike da linzamin, don haka
ne ni ma na yi kokarin kawar da Father da
Wilson daga wannan fage ina son na rike shi
da sabon hannuna wato gudunmuwarka. Na
zabe ka ne ba don komai ba sai don yarda da
tsarkin hannunka inda ke so sabuwar
tawagar nasarar mu ta zano tana cimma
り Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
burinta ba tarc da tayi sanadiyyar halaka ko
cutar da wani rai ban da na kudi da kadara
ba, haka nan ba tare da ta dilmiya wadanda
basu ji ba basu gani ba. Abin bukata a
wurinka yanzu ba kwarewa ce kawai ba, ina
so in ga kwakwalwarka ta manta da hutu
dare da rana tana mai cikin shirin ko ta
kwana da kiyasta irin ta yadda su Ibrahim za
su bullo mana.Farid ban san asara ba ban
taba yinta ba don haka ba zan so yin ta a
yakin da ban taba yin irinsa ba shiyasa na
hada team din Farid da Farida" י
Lokacinda ta dauka tana magana ya
ba shi damar sanin matsayinsa...yanzu farin
ciki yake, Farida ta zo kusa ta kara motsowa
gare shi, babu shamaki. Aikin da take cewa
a yi don kamfani zai yi fiye da shi ba don
kamfani ba sai don samun dauwamammen
kusanci da Farida. Yayi asarar waccan dama
don bai san kan yakin ba amma shi ma fa so
yake kada yayi mafarkin asara a wannan
sabon yaki nasa....
Ta Kura masa ido
"Farid ina son ganin Ibrahim a kasa a
karo na karshe..ina son darasin da a sh
bai wa mahaifinsa ya zamo na wasa.
10 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Wannan ya zamo na karshe,ina san kawo
Karshen yakin kamfaninsu da namu"
*** *** ***
Can gabar teku madafar gahawar
take an baibaye ta da na`urorin dumama
daki da fitilu marasa haske. Zai yi wuya ka
iya tantance fuskokin kowa ba don duhu ya
kaurc ba sai don fitilun da aka tanada don
kawar da gane fuskoki, hakan ya sanya da
wuya ka ga wani ya doshi teburin wani in ba
an ba shi lamba ya je wurin ba. Kuma ba a
ci ba a sha ban da hadin ruwan gahawar da
akan yi.
Richard ya sosa goshinsa yayi
murmushi ya sake dawo da idanunsa ga
Ibrahim Balala.
"Lallai ni nayi aikin horas da wilson
kuma duk horon da na ba shi na ya iya
kayarwa ne, babu komai a kwanyarsa ban da
ya saukar da asara kuma ya horu fiye da
yadda nake zato... amma ba zan ce kayar da
shi ba zai yi wu ga malaminsa ba, sai dai zai
yi min tsada sosai na kayar da yarona, kuma
zai yi un sada sosai na bariaro na ya
kayar da i1Dan samari bana zaton za ka
E
V Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
iya biyan irin wannan tsada... Ina jin abin
da za ka iya biya bai wuce na in yi masa
nasiha ccwa ya kauce daga hanyarka ba,
amma biyan in ja da shi da wuya don Na
ibi yana biya da kyau amma baya iya biyan
כ2
Balala ya fan dubi gefe ya kalato
Kokari.
"Fadi me zan iya baka ni kuma zan
dora... Ba so nake a kawar da wilson daga.
hanyata ba ina so ne a kayar da shi a gaban
hanyata masu ji da shi su gani...."
Richard ya sake yin dariyar nitsuwa
"kana cike da fishi...baka danu da
asarar ka ba....dama an ce biki da me zuciya
ake yi...idan na in baka wuka da nama ne
kan Wilson ba kudi zan caje ka
ba...ummmm... ka san ni ban iya ciniki ba
ban kuma iya harkar kasuwanci ba,,, wannan
ya sa na ji ina son sayen hannun jari ina
daga kwance ina cin riba...."
Ya daga hannaye biyu
"Kada gabanka ya fadi ba cewa zan
yi mu raba kamfaninka ba ni ba zan ma iya
wa kamfani ba so nake kamfanin ka ya biya
hannun jarin da na yi ciniki da kamfanın
5
12 Matiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Apple... basu da yawa guda dubu sha
bakwai ne duk da dai manya ne....batun
tsarin kayar da Na`ibi ta hanayar yarana
dakc baibayc da shi pan dubu goma sha
biyar ne zai raba ka da kowanne daya, Ina
jin basu da yawa su hudu ne ko?"
Ya tsaya yana lissafi da yatşunsa...
"Dcal!!! "
In ji lbraahim ya ci gaba.
"Ka sanya hannun fara yi min aiki ni
kuma zan saki rabin kudin ta hanyar waya
yanzun nan.
Richard yayi dariya.
"Kawo takarda ina son haka ina son
yin aiki da yara masu kwazo kamar ka..da
haka babanka yayi da ba ku yi asarar da
kuka sha yi ba......"
*****
Ya ji gabansa ya fadi ba don tsoro ba
sai don gudun samun tasiri ko mutuwar jiki.
Da Farida suka yi arba tana shigowa shi
kuma yana fita. Duk suka tsaya baya da ta
fara tsayawa ta dube shi daga sama zuwa
kasa sannan tayi murmushi.
"Bally kehan yo look greate yaya
shiryc-shirye?"
13 Mafiyan Masoya-2 Ralhma Abdulmajid
Shi ma ya tsaya yana kallon ta.
"Mun gama namu shirin In ku kuna
kan yi. Kafin mu fara aiki da zan so yi miki
nasiha ta karshe da cewa kamata yayi ki
nemi ahuwa kan abin da kika yi komai ya
koma kamar da kafin ki shiga yakin da ba za
ki taba iyawa ba"
Ta yi fari da ido.
"Bally kana nan yadda na san
ka.gaggawa da yarda da kai da kankamba,
kafin in yi maka tawa nasihar bari na baka
amsar taka. ka gama yanke cibiyar dake
tsakanin da da yanzu don haka baka da
iyawa ko tasiri kan mayar da yanzu kamar
da. koda yake ba hakan ce za ta hana ni baka
hakuri ba, ina ga ba zan taba bayar da
hakuri ne ga laifin da ban aikata ba don haka
na gwammace karon battar mu da hakan. Sai
dai ni tawa nasihar gareka itace da za ka ja
da baya kada ka shiga yaki da kungiyar
nasara amatsayinka na mai wakiltar
rundunar hasara. Ko ka manta ba ku taбa
nasara ba ne Ibrahim??? ko a fadan
Karashen nan ka duba irin asararka, ka rasa
uba ka rasa shugaba,, ka rasa mata ka rasa
da, ka rasa dukiya ka rasa kwanciyar hankali
14 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
duk ba ka ga rashin ba kan ka kake so ka
rasa dungum?"
Ya matso a fusace.
"Ko ke ki rasa kanki a wannan karo"
Ta daga hannaye sama.
u`um!!!nayi alkawari ba za a yi haka ba, don bana yakina tsarkakakke ne... rai ko jiki bana so su salwanta, kimar kamfani
nake so in yi cacar da shi amma ba zan
mayar da kai Geran masallaci ba kada ka
tsorata wannan alkawari ne"
Yayi dariya
"Farida kin cika wa kanki ido kuma
wannan ne abin da nake son sauke miki a
wannan kwanakin...in kin gama shiri ki
sanar da ni, amma ke kamfani ya dama
saboda imanin ki da gasa ya saba wa
imanina da halakar ku ta ko ina...sai wata
rana
"Sai wata ran Bally duk lokacinda ka
so haduwar wasan na shirya maka"
*** ***
Ta jima rabonta da ta shiga uwar
dakinta, ku'lun a katon falon ko a karamin
ofishinta na cikin gida bacci yake kama ta,
15 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
amma yau tana zuwa sambai ta wuce dakin
don kada ma wani aiki ya ja hankalinta. Yau
rana ce ta zakulo bacci duk inda yake don
kwanya ta sami hakkinta kafin ta soma dasa
Dan ba a a aikin da ke gabantanta.
A cikin dakin ta kunna komai ta zare
rigunan jikinta ta yafa ta wanka don ta watsa
ruwa, amma daga nesa ta hangi hoton sa
yana yi mata murmushi, hannayensa na dage
kuma itace a cikinsu suna sanye da fararen
kaya na aure. Ta jima bata yi arba da hoton
nan ba, da ta san za ta ci karo da shi da bata
shigo dakin ba, wani matsafin hoto ne da ke
jan ta zuwa ga bara abinda bata son
tunaninta gare shi. Ba da saninta ba ta gan ta
daf da hoton wanda tuni ta dauke shi ta
durkusa kan gadonta, da ka gan ta ka san
bata cikin sabon shirin da suke da zuciyarta.
Shafar Bally take da yatsunta can cikinta ta
kasa tuna matsayinsa a yanzu sai kewarsa
kawai. Ta matse idanuwanta da saninta don
ta tuna abinda ya fi mata komai dadi wato
zamansu da Bally.
Ta dan yi sama da idanuwanta don su
haďu da nasa da ta san suna kanta, ta ko yi
sa`ar yana matso da bakinsa don ya sunbace
16 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ta.
"Yaushe za ka gaji da yi min kiss
Bally?"
Ya dan yi dogon tunani.
"Umm! Nan da busa Kahon Karshe
zan fara rage kwadayin la66anki Reeda"
Ta dada masa duka a kirji sannan
cakulkuli, yana dariya.
"kenan ma za ka dena din kenan kо?
Sai na zane ka tsaf"
Suna dariya ya na kare dukan wasan
da take masa a kirji har ta gaji suka sake
komawa kallon juna.
"Farida kin ga so yayi nasara kan ki
ga shi ya kawo ki kan kirjina, na zamo na
mijin farko a rayuwarki kamar yadda kike
macen farko a rayuwata? Me ake da kiyayya
da su Father za su gane?"
Ta sa hannu ta toshe bakinsa.
"Kada ka tuno mana da makiya a nan,
bari mu more farinciki ba tare da sirkiya ba"
"Kuma kin san so ne kawai ke da
Karfin haka...Musamman irin soyayyarmu
da ka iya dauke radadin duk wani gyambo"
Ta bude idanunta ta kalli hoton, ta ji
tana bukatar rungume shi a naman kirjinta
17 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
na dan lokaci cikin radadin kewa da so.
Bata san iya mintocin da ta shafe a hakan ba
sai dai sun ingiza ta ga lalubo wayar ajiye a
dakin inda ta lallatsa lambobin da ta jima da
hardacewa ta kwanta kan gadon ta sanya
wayar a kunne.
Ya jima da dauka da nanata hellohello, amma sassarfan hawaye da ratsa ta da
muryar take ta hana ta cewa komai. Yayi
tambaya "Me kike son gaya min da za ki
kira ni kiyi shiru? Kin sa ranar fara wasan
mu ne?"
"Bally don Allah ka da ka yi wannan
fafatawar da ni"
Kwance yake a kan gadonsa, amma
asirin yanayin Farida da ya bayyana a
muryarta ya zaburar da shi zaune.ya jima
yana rintse ido na jin yanayinta a tiririn
kirjinsa.
"saboda me?" ya tambaya da muryar
shauki.
"Bai, kamata ba... Bana son yin
wannan fafatawar da kai Bally kana son
takura min. Bana son ji maka ciwo?"
Haushi dao duka suka tirmike shi,
bai fasa jin shasshakar Farida a kunnensa ba
18 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
amma an ya ba wani makirci ne daga
makirar Faridar me kashc masa uba da za
ba.
"Kada ki damu babu ciwon da za ki ji
min sai dai ni na ji miki in kin shirya"
"Bally baka son yin abinda kake shirin yi..
rufe idonka ka tuna Faridarka a gidan
wanka, a kan gadon mu a kicin, a kan doki,
a kan titi, cike da soyayya, duk za ka iya cin
amanar wadannan ranakun? Hotonmu kawai
na ranar biki na gani ya zubar min da
makaman yakina, ka tuna fatanka na so yayi
nasara a kan ki, ka duba rayuwarmu, ko da
ba mu da aure a tsakanin mu mu bai wa
soyayya mutuncinta Baby muna da rayuwar
da ba za mu sake maimaita ta da waninmu
ba. Ka tuna rana guda muka san yadda ake
sarrafa juna tsakanin zuciya da gangar jikin
namiji da mace. So da tarayyarmu akan
junan mu muka fara...."
"Ya isa makircin... idan tsoro kika ji
fito ki yi saranda ba kissa ba"
Ya kife wayar da karli ya tsinke layin
sannan ya zauna yana nish Bai yi aune ba
sai ji yayi hawaye na zub masa. Ya fadi
19 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
kashangare idanuwa a rintse.
"Gaskiyar Farida, ke ce abin sona na
sani har gobe, bana son yin wannan fadan
amma dole sai nayi. Dole sai nayi Reeda ki
yafe min kada ki kashe min jiki. Ban bai wa
mahaifina komai ba yana raye, wannan cе
Kawai hidimar da zan masa ya ji dadi"
Ya dubi gabas da yamma.
"Da gaske bana son yin wannan
fafatawar kin sani Farida, amma kin kashe
min uba kin kashe min da, duk da wannan
kina karyar so yayi nasara? Don dai nine
wawa soyayyar ki ta mayar da ni wawa?"
Ya zabura cikin kuka ya doshi wani
hoton Farida na katako karami zubin ofis da
ke ajiye ya soma wurgi da shi.
"Ban son ki ban san ganin ki ki fita
min daga rayuwata"
Abubuwanda yake nanatawa kenan
yana jifa da hoton yana takawa wanda ko
gezau bai yi ba har ya gaji zai tsaya ya huta
amma suka sake hade ido da Faridar hoton
da ta kashingida kan tafukan hannunta tana
yi masa murmushi.
"Me ya sa nake son ta? Me yasa nake
jin ta, Me yasa na kasa cire ta daga
20 Mafivan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
rayuwata?"
Ya dauki hoton ya rungume a yanzu
kuka yake wiwi
*** *** ***
Farid da Mahdi da wasu mutane uku
ne kawai a daukacin gidan abincin sin din
wato Chines restaurant hakan ta sanya shiru
kake ji musamman da ya zamto ba da cokula
ake cin abincin ba.Mahdi ya debi wannan
tsinken ya tsiyaya a bakinsa ya bi shi da
wancan tsinken, amma mai gayyar sai daura
taliya a tsinke yake yana kwancewa
"Malam Ka ci abinci mana"
Itace kalmar dake yawo a zuciyar
Mahdi amma sai ya maye gurbinta da cewa
"Yanzu da Farida bata da ciki bata da
aure kuma kana 2.1.C dinta wace dabara za
ka shirya wa damar ka ta yi nasara?"
Farid
Ya tsayar da katakon a nuna idanun
"Na san dai ba cewa za ka yi ba za ka
aure ta ba tunda kai saurayi ne"
Farid ya zubar da tsinkayen sa dama
abinda yake ta faman so kenan
"1Dabarar farko shine rokon Allah da
2
21 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Ya bar Farida cikin kadaicin da take ciki har
ta gama amincewa da cewa ni ne kadai me
kare mata kewa....Farida na da fadin zuciya
za ka iya fadawa tarkon zaton son ka take
saboda karamci yayinda sam! Zuciyar bata
doshi nan ba a fadi kasa babu nauyi,shiyasa
na ke ta bi a hankali, amma ina fa hangen
nasara, ina hangen zan zamo namiji mafi saa
idan maki daya da ya rage min ta cika wato
Farida ta amince da ni...."
Yayi ajiyar zuciya.
"Yarinyar tana shiga matsala tana
kara shiga raina...Amma fa tana ban tsoro,
yadda ta iya danne son ta ga Ibrahim lokaci
daya take aiki da manufofin kamfani kawai
na nuna cewa za ta iya take duk wanda ya
biyo kan titinta am telling you"
"To shi Balalan yaya yake? kada fa
ya zo ya bata muku tafiya ka san halin so".
Farid ya 6ata rai
"Malam Yaya kake wannan magana
na ce maka mutum an rabu da saki uku da
zubda ciki amma shegen bakin ranka fata ka
ke ya dawo"
Mahdi ya fashe da dariya
"ba fata nake ba tambaya nake"
22 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Wayar Farid tayi kara, ya dauko ya
duba ya zare ido yayi wa Mahdi rada
"Itace"
"Hello ranki ya dade... Aaa! Bana
komai na zo ne?...To gani nan zuwa"
Ya katse wayar ya mike da sauri ya
dauki hankici ya goge baki da hannu.
"Ta kira ni, ka biyasu in ka gama ni
na tafi".
Mahdi ya bi shi da kallo na mamaki
da tsokana
"Malam yaya za ka gayyace ni cin
abinci kace kuma na biya, Yama ma za a yi
ka ce mata baka komai abincin fa muke ci?"
*** *** ***
Tana tsaye a jikin wundon ofishinta
tana leken shukoki a yainda ya shigo. Ko da
yayi sallama da gaisuwa ta amsa amma bata
juyo ba ta ci gaba da magana.
"Gobe za mu raba bulk sms da
labarai a jarida kan shakku da ake da shi kan
faduwar hannun jarin kamfaninn man fetur
na Ondowa...ina so mu tabbatar da labarin
za kuma mu kash kudi ya shiga kunnuwan
jama`an da wannan shakku ya dama don
:
23 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
dole hannun jarin ya fadi kafin sha biyun
daren gobe"
Ya ji gabansa ya fadi muryarsa ta zakulo kanta ba tare da umarninsa ba
"Ban gane ba.. kamfanin da muka
sayi hannun jarin sa na wannan shekara
sama da kashi ashirin cikin dari? Ribarsa ce
fa nake jin kawai ribar mu a wannan karon
da ake gasar sadarwa ba neman riba ba"
Ta yi murmushi sannan ta juyo ta
dube shi.
"Kai sabo ne a wannan
tafiyar...Kamfanin Na`ibi Ya saba asarar
riba don janyowa abokin gaba asarar uwar
kudi. Ban ce za mu yi asarar uwar kudi ba
י riba na ce mu yi asara"
Ya dan yi murmushi na hango inda za
ta.
"Kashi nawa su Ibrahim Hadi suke da
shi a hannun jarin yau”.
Bally ya sai hannun jari uku a wannan
satin don samar da kafar tsayiwa a yakin mu
saboda yana da tabbacin a fasahar
makamashi da sadarwa zan kayar da shi don
haka ya fara leka wasu kasuwanni don
neman tudun dafawa in na yi tsiyata. Amma
24 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
yayi latti, don tuni na amince da bana son
tsiyata shi a makamashi sai na sa masa ido a
hannuwan jari"
Ta zaro wata takarda mai zane iri
daban daban.
"Sun sayi hannun jari akamfanunuwa
uku a wannan sati kamar yadda su ma suka
sayar da nasu wa sama da kamfani bakwai.
na kamfaninsu bai dame ni ba don na san
ragon da nake yaki da shi, idan na