Lokacinda za ku
yi wannan abu da baka bari daga kai sai
Wilson ba, wannan ne dalilin da ya sa ya
gudu, wato maana an sayeshi dole ya bata a
duniya kafin a tona asirinka wanda in har ya
jima da narkewa a wata kasa zai yi wahalar
fitowar sunansa ta cutar da shi".
Ya rage surutun ganin wanda ake wa
ya kasa cewa uffan, ya duba agogo ya mike.
"Na gayyaci wasu kwararru don jin
raayinsu, amma fa a iya tawa kwarewar, halin
kasa kawai za a iya yi a yi ruf da ciki kan
wannan lamari, amma zai yi wuya a tsira
hannun hujjojinda na ga an ajiye a kasa, a dan
duba lamarin Master, na bar ka lafiya"
Ya juya ya fice daga duhun falon
78 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
wanda gunkin Na'ibin ne kawai ke zaune
yana wurga ido har zuwa a kalla mintoci hudu
a yayinda kwatsam abin mamaki gareshi ya
faru wato bayyanar Farida a gabansa. Itama ba
maganar take jin yi ba wucewa tayi har inda
katon katakon tara kayan shay-shayen yake ta
zauna a karbunsa ta sunkuyar da kai na dan
wani lokaci.
"Me yasa baka gaya min kai ka kashe
shi ba ka bar ni a duhu father?"
Ta furta cikin sanyin murya na
amincewa da aikin gama ya gama.
"Ban kashe Hadi ba, ban kuma yi niyar
kashe shi ba, Wilson ne yayi,na kuma nuna
damuwa a kan haka"
Tayi murmushi sannan ta dago kai ta
dubi wanda har yanzu baya duban ta.
"Ka daure ko rana daya father ka gaya
min wata gaskiya da ko ina na tuna ka na san
gaskiya ce ta ratsa tsakanin `ya da uba"
Ya kashe tabar a hankali wadda ta fara
lashe masa hannu.
"Gata nan na gaya miki....Ban kashe
Hadi ba, Wilson ne ya kashe shi, ban kuma ce
a kashe shi ba, na dai ce a koya masa
darasindea shi da dansa ba zasu sake yin
hanyarkı ba. Wannan ce gaskiyar da zan iya
6
79 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
gaya miki yau, ko ba don Allah da kauna ba
na fada don duniya ta gaya miki wadda ta fi ta
a kaina"
Sun hada ido a yanzu da farida me
murmushi da hawayen zafin zuciya.
"Kenan Bally na da gaskiya, ba
tsautsayi ne ya kashee mahaifinsa ba,
gidanmu ne... kuma kuka yi abin ta yadda zai
zaci da hannuna ya ki ni
"na gaya miki Wilson ne yayi shi
kaďai, ba zan yi raguntar laka masa ba don na
kubuta na wuce haka...a yanzu na gane cewa
an sayi yaron ne ya gudu domin ya cutar da
ni..."
"Amma ba Bally ne zai sayi makashin
mahaifinsa su kulla aminta don ya cutar da kai
ba, muddin duk soyayyarmu zai iya jin ya ki
jini na a kan zargi kawai"
Na`ibi ya kada kai.
"wannan tohon ciniki ne... ina jin ma
an yi shi ne tun kafin Wilson ya fara aiki tare
da ni. Tsohon shiri newanda ina da
alammominsa da aynzu nake hangowa kuma
su ne suka hana ni magana tun jiya da ake
baza wannan zance...Amma Richard zan
dulmava kafin komai ya cika da ni"
Bai rufe baki ba suka ji karan Maman
SO Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Farida daga kafar bene da wata shakakkiyar
murya me nuna gajiyawa. Babu wanda ya
kalli wani suka rankaya a gujc zuwa sama.
Tana tsaye da remote a hannu tana
nishi a zagayayyen falonda ke jikin kafar
benen inda take kallon Italabiji, duka suka
dube ta, amma ganin idanuwanta na kan faifan
sai su ma suka raja'a a kai, cikin zumudi tana
tariyowa.
"Dubi abinda ubanki yayi
Farida...wannan kwafin a gidan mai aka bani
cewa in jira zuwa dare zan gan shi a labaru
don tuni CNN ma na da kwafe ballantana
gidajen talabijin din gida".
Faifan ya soma aiki a yayinda ya nuna
Merry tana kuka cewa ita daduron Na`ibin ce
duk da kawar 'yarsa fiye da shekarunda suka
yi suna daduro, bai bar ta tayi aurere ba amma
ya ce ba zai aureta ba ta zubar da cikin da take
da shi don bai son haihuwar shege.. da dauke
wannan jawabi sai aka fara nuno faifan
bidiyon Na'ibin da Merry wanda suke kan
gado suna daf da soma masha`a. Farida ta iya
barin wurin a guje inda amai ya tirnike ta ta
karaso kan matattakala ta zube tana amai da
mummunan kak ari. Wannan ne ya dauke mata
ganin faduwar mahaifiyarta wadda ta taho don
ST Mafiyan Masoyа-2 Ralima Abdulmajid
tambayar mijinta da yake tsaye a yanzu yana
hawayen da bai san na menene ba, ta iso gare
shi don ta cakume shi ta ji dalilin cin
amanarta, sannan jin mutuwa kusa da
makogwaronta sai ta ji bukatar shakeshi su
tafi tare, sai dai duk cikin burirrikanta babu
wanda ta cika domin faduwa tayi kasa da rai
ko babu, amma dai ba nunfashi. Duk da
halinda Farida ke ciki zaune kan matattakala
tana fama da kirjinta, jin ihun mahaifinta da
ke kiran matarsa cikin kuka ne ya sa ta dafa
matattakalar tana gsanin bibiyu don ta karasa
inda suke
*** *** ***
Kamar yadda su Richard suka tsara
haka komai ya wakana. A wannan rana
mutuminda dama ba a gama yayinsa ba wato
fan takara da postersa ta yadu ko ina,ga shi
kuma an ja hankalin mutane da yi masa
tuhumar kisa, sai gashi a daren ana kallon
masha`arsa da wata yarinya, har ma an yi
posta na wani sashi ana likawa, tuni a daren
mlamai da manyan mutane da sauran talakawa
suka fara Allah wadai da yada zanga-zangar
su fa garin addini da shara`a ba zas zauna da
fajiri ba ballantana a ce ya mulke su.
Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Wayewar gari kuma aka tashi da wani sabon
labarin, shine na faifan kisan gilla da wasu
matasa suka yi wa Merry a matsayin `yan aike
daga wanda ta tonawa asiri wato Mansur Bici.
Tattaruwan labaran ya sanya har mkwabtan
jihohin sai da suka taya wannan jiha jimamin
wanna abu.
Duk wannan badakala bata sami iyalin
Na`ibi a gari ba, domin kuwa jirginsa na
musamman ne ya debe su da gangar jikin
matarsa zuwa kasar Ghana inda aka wuce da
matar asibiti don ceton ranta da ake tun a
cikin jirgi inda shi ya tsaya yin wayoyi don
ganin yadda zai laddafa abin, amma hakan ta
bai wa `yansanda damar cafke shi, musamman
ma ganin cewa a wannan awoyi tuni bai da
gata, domin kowa ya nisanta kansa da shi
babu wanda yake kira a waya ya dauka,
kamar yadda aka je aka yi zdai-dai da
ofisoshinsa da kamfaninsa da na iyalinsa
83 Mafiyan Masoyа-2 Rahma Abdulmajid
Babban
BAKWAI
asibiti ne a birnin Acra
wanda an san babu mai dosan hanyarsa sai
masu mulki da iyalansu, nan mahaifiyar
Farida ke kwance take jinya cikin matakan
tsaro na musamman tare da suturta zaman
nasu ga kowa, daga ita sai Farida sai kanin
Faridan wanda ya baro makaranta ya zo taya
ta jinya da jumamin wannan rayuwa da suke
ciki.Sati biyu dattijuwar na ci gaba da yin
nunfashi ne da taimakon na`urar zuko
nunfashin bata san a inda takc ba. Kenan
bata san halinda iyalinta ke ciki ba,
musamman mijinta wanda a halin yanzu
yake sakayc hannun yansanda bayan da
mutanen gari suka kona kusan duk wasu
gine-gine da a ka san karara nasa ne kafin
jami`an tsaro su farga, wanda ba wai lallai
masu kishi bane suka shirya hakan ba sai
abokanan siyasar sa.. Ya dan sami damar
yin magana da su Farida a waya wajen sau
uku sai dai basu tattauna komai kan halinda
yake ciki ko musababbabi ba illa va kan
tabbatar wa Farida cewa ta gaya wa matarsa
S4 Mafiyan Masoyа-2 Ralma Abdulmajid
cewa, yana son ta kuma ta yafe masa,zancen kenan, kuma shine Farida bata saba da shi
ba take cin kuka in ta saurara, amma a
maganar su ta karshe ya kara da wasu
kalamai guda biyu sune na tabbatar wa
Farida cewa shi bai kashe Hadi ba, bai kuma
kashe Merry ba, sannan ya jaddadda
kaunarsa garesu da kuma neman gafara.
Washe garin wannan hira a waya ne
aka tashi da wani mummunan labarin cewa
Allah Yayi wa Mansur Na`ibi rasuwa a inda
yake tsare hannun jami`an tsaro sakamakon
bugun zuciya mai tsanani.
Shafik kanin Farida ne ya koma
Najcriya don halarta jana`iza mai radadi da
ban tausayi ta mahaifisnsu sakamakon
kasancewar Farida da mahaifiyarsau duka a
gadon jinya domin Faridar ta sami bugun
zuciya daga jin wannana labari wanda ya so
kai ta lahira daf da mahaifin nata. Duniya
kenan. Fadan kamfani ya lashe Hadi ya
Lashe Na`ibi saura Farida da Balala abokan
gaba biyu wanda a kafar leken asirinsa ya
sami labarin inda farida take ya silalo ya zo
don yi mata gwalo, da ner an ta daga farar
tuta don ya gama ramuwa, amma hada ido
85 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
da Faridar wadda bata jima da farfadowa ba
ya sanya shi zubar da makamansa ya shiga
wani yanayi da bai san ma`anarsa ba.
Faridar wadda tayi kama da me jinyar
kanjamau din da ta tsere wa mutuwa a
watanni shidan farko saboda ramewa, baki,
muni da rashin kula da kai. Ta juyo ta dube
shi kanta jingine da gwiwarta sannan tayi
murmushi ga mutumin da bai iya motsawa
daga inda yake tsaye ba, ta dan nisanta
kwayar idanunwasa da inda yake.
"Ka zo ne ka gaya min ka yi nasara a
kaina Bally? Na amince ka yi nasara. Ka
kashe, Father, ka kwantar da mahaifiyata, ka
kwantar da ni, ka bata wa duk me rabe da
sunanmu suna. Wannan babbar nasara ce
kwatankwacin babbar hasararka"
Ta tashi dakyar zuwa jikin wundon
ta dafa tana kallon waje inda ta ba da baya
wa mutumin da baya iya kifta idanunsa sai
don su bi ta duk inda za ta cikin satar so da
tausayi da bai san lokacin da suka iso masa
ba.
"Ka yi hasara ta duk dukiyarka da ka
dilmiyar don ruhe Nalibi. wadda ina da
tabbacin ka yi mata sarar da ba za ta sake
So Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
tashi ba. Kayi hasarar hana zuciyarka
kusantar abinda ta fi so a duk duniya inda
kayi musu shingen da ba za su sake haďuwa
ba har abada duk da ita ma zuciyar taka ba
za ta dena son ba har a bada..."
"Ta tattako zuwa gabansa a yanzu
cikin kwalla da zafin rai.
"Mafi girman hasararka,ita ce ta hada
karfi da makasan ubanka da kake daukar wa
fansa don ku kashe ku dulmiyar da wanda
bai da hannu a kisan.... Hasarar da ya kamata
ka yi min gori da na yi wanda ba zan warke
daga faduwar da nayi a gabanta ba itace ta
son ka da nayi...Bally, daya-dayar hasara ta
itace mika wuya da zuciyata tayi ga
soyayyarka wanda na kasa denawa.Wannan
soyayyar ce ta sa na sanya matukar tausayi a
yakinmu inda ban yi saurin hallaka ka ba
kafin ka hallaka min iyaye da suna, ita ce ta
hana ni ganin fatar dabban da ke
kwalkwalwarka ta inda na kasa fahimtar kai
wane irin naman daji ne...na zamo duk wani
karamin duka inna yi maka sai na koma gida
nayi jinyar radadinsa a naman zuciyata
...ban san cewa kana dauke da dutsen da ba
ji ne kawai baya yi ba, a a! Har gangarowa
か
87 Mafiyan Masoya-2 Rahma Ahdulmajid
yake son yi ya fasa kaina..."
Kuka ya ci karfin Farida a yayinda ta
sanya hannunta na dama tana dukan 6arin
zuciyar Balala tana nunawa.
"Nan ne inda na taba dauka a
matsayin laimata idan duk duniya ta zamo
rani a gareni, nan nake shiga na sami
yanayin damuna, ban san cewa a she
gobarata wadda za ta zo daga kogi bayan ta
kona duk wani ruwa da zai iya kashe ta za ta
sami hanyar zuwa gare ni ne ta wannan
mafaka tawa wato zuciyarka Bally"
Tayi kamar ta kifa a kan kirjinsa don
jin lallai tana bukatar mabuya daga azabar
da take ciki, kuma mafakar ta zamo irin
wadda ta yarda da ita take jin dadinta jiri ya
fan zari zaren kwanyarta amma ta kada kai
ta ja jikinta da karfi cikin kuka. Kasancewar
idanuwanta a rufe suke a yanzu bata san
Balala ya riketa ba sai da ta ji bata tafi ba
kamar yadda ta bukata, ta bude idanunta a
kan nasa wanda suke zubar da hawaye fiус
da nata, yana nishi kamar ransa zai fita.
"Farida har a yanzu kina gaya min
baki da hannu a kashe mahaifina?"
Ta karkatar da wuya abinda ya bai wa
NN Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
hawayenta damar sauka ta dama inda ta dan
yı murmushi.
"ka sani sarai ban kashe shin ba
Bally, ka rike wannan hujjar ne don ka cika
zuciyarka da Kıyayya me hujja. Amma ka
sani Baba Naibi har ya mutu yana shaida
min cewa bai kashe mahaifinka ba...Na
kuma yarda, saboda na san wanda ya kashe
din,
Balala wanda yake raba idanu cikin
kuka har da majina a yanzu a kanta. bai sake
ta ba.
"Na san da kunya na fada... Na san ba
lokacinda ya dacc ba ne...watakila lokacin
fadın ya wuce na yi latti...amma bani da
zabi dole in fada, shine Farida ban taba dena
son ki ba... Na azabtu matuka a yayinda so
da ki suka hadu a zuciya daya tak da take
kirjina kowanne ya kasa kayar da dan
uwansa don zaben abu daya, wannan ya
sanya na kasa samar da ingantaccen zabi a
rude nake Farida, a rude nake..."
Ya kamo kumatunta da tafukan
hannunsa.
"Farida i yi min alfarma, koda ban
dawo da jiya yau ba a rayuwar mu ki bari na
89 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmujid
sake sanya ki a mafakarki,a laimarki, a
matsuguninki wato zuciyata, tana nan da
duk adon tarairaya da tausasawa da kika yi
mata, ki bari na cire ki daga wannan azabar
da bata yiwa idanuwanki da labban ki da
zubin fuskarki kyau ba.Farida ki bari sashin
soyayyarmu ya biya wajibinsa na nema miki
sassauci"
Tayi murmushi sannan a hankali ta
zarc hannayensa daga fuskarta ta sakar masa
su a kasa.
"Haka na so a lokacinda na nemi kada
mu yi wannan karawar amma ka ki, yanzu
an yi latti. Bally ka kwatanta yadda ka ji a
yayinda mahaifinka ke kwance cikin azaba
kana jin wani ne ya kashe shi. Shin
soyayyata ta tsirar dani a wurinka? Sam!
Bata yi tasiri ba har saki na ka yi...Dubi
gefen can uwata ce kwance babu tabbacin
tashi, mahaifina ya mutu har an binne.
sunanmu ya juya daga launin fari zuwa fin
baki duhu...Yaya kakc jin ina jin ka yanzu
Bally? Je ka, na gan ka na kuma ji sakonka.
amma ka sani kiyayyata ga wuta da azabarta
za su iya yin takara da Kiyayyarka
zuciyata, ina da tanadin inda zan karya ka.
O Mativan Masorа-2 Rahma Abdulmajid
cikin ruwan sanyi,yakin farawarsa kenan"
Ta juya ta bar wajen a hankali inda ta
shige dakinda mahaifiyarta ke jinya ta rufo
Kofa
*** *
**
Daga shi sai singileti fara da jan
gajeren wando yana kykyata dariya ya juya
yana kallon wadda ke rataye a bayansa a
goye wato Farida.... Wannan ne hoton kawai
da ya sami hasken fitila a cikin duhun faicn
da Balaia ke kwance a doguwar kujera
tamkar matacce in ka cire idanuwansa dake
kan wannan hoto nasu da Farída cikin
hawaye.bai san me yake ji ba baya da tuna
halin da Farida ke ciki. Zai dai iya tuna
cewa an zo an ce Richard na son ganinsa
yace ya shigo amma koda ya shigo ya tsaya
kansa, ya jima kafin ya tambaye shi duk da
bai juyo gareshi ba.
"Me kake so Rich?"
Richard yayi murmushi.
"Na zaci zan same ka cikin farinciki
kana biki, sannan a yi murnar dani na karbi
sauran balane dina na bace dga wannan
rayuwar...Ban sani ba ko Faridar da ta fice a
91 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
karo na karshe a rayuwarka ce take son baka
kewa"
Har yanzu Balala bai juyo ba ya sakc
magana cikin gajiya.
"Me kake so Richard, me zan baka
bayan abinda na baka? Ginin kamfanin kake
so na baka tunda komai ya kare?"
"Tunda baka son magana zan takaita,
Nayi aikina na cika duka bisa alkawari, kai
ne ya rage baka cika min ba, wato ragowar
hannun jari hudu da za ka bani...ina jin
wannan kuma hakkina ne da duk da abinda
za ka biya ni zan karba"
"Kangon ginin kamfanin mu zai isa
ya biya hannayen dai?"
Balala ya tambaya ba tare da ya juyo
ba.
"Abinda zai ragu babu yawa, zan iya
yafewa"
こ
Balala ya tashi, kwanyarsa da
zuciyarsa motsa shi kawai suke babu tunani
ko digo, ya dauko wasu takardu ya zo ya
rattaba musu hannu sannan ya mika su ga
Richard.
"Ga su in za su ishe ka, kadai suka
rage min bayan gidaje, da motoci, da
92 Mafiyan Masova-2 Rahma Abdulmajid
Kananan abubuwanda za su ishe ni cin
abınci har komawata ga Allah. Wannan
ginin idan ma na rike hutun jaki ne da kaya
a ka don ba zan iya kula da shi ba a yanzu,
sannan ba zan iya wani damben tara abin
duniya ba a tsayin rayuwata, tunda lokacin
da nake dasu, basu cece ni daga bakin cikina
ba. basu bani abinda nake so ba, basu
shiryar da ni ga abinda ya dace ba, basu
kuma sanya ni a kan hanya ba...kenan kai da
su kake so ba abinda za su samo maka ba
gara ka rike su"
Richard ya karbi takardun cikin
farinciki.
"Sorry, da alamar kana cikin wani
hali na kunar zuci, amma ba abinda ya shafe
ni bane. Na gama nawa zan kuma bace daga
rayuwarka don na san zai yi wuya ka sake
mallakar abinda zai ishe ka nemana, don
haka ina maka fatan ci gaba"
Ya juya ya fita ba tare da Balala ya ko
kalli wajen ba, sai da ya fice ne ya ji yana
bukatar dukufa yayi kuka tamkar yaro
Karami.
*** *** ***
Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Farida ta sami halartar gagarumar
addu'ar ukun da akayi na mahaifinsu bayan
da `yan uwar mahaifiyarta na jini suka iso
daga kasarsu don tsayawa tare da ita a
asibiti. Addu`ar ukun bata sami halattar 'yan
siyasa da marigayin ya rikide zuwa zamowa
daya daga cikinsu ba a yanzu, sai dai ya
sami halartar daruruwan abokanan sana` arsa
daga ciki da wajen kasar sai ma`aikatansa da
dangunansu da wadanda ya taimakawa da
wasu Fandations dinsa musamman wadanda
suka ci gajiyar gidauniyarsa ta tallafawa
marasa karfi don yin karatun kimiya a
matakin jami'a wanda Allah Yayi yawa
dasu. Wannan ya sanya wasu `yan siya babu
shiri cikin borin kunya suka dan leko ganin
cewar bai sami irin kyarar da suka guda ba.
Ganin abin ya hada da masu addinai
daban-daban sai addu`ar ukun ta kasu gida
biyu, wato daga masu addu`ar fidda`u sai
masu ranar bangirma ga Gwarzo Na`ibi.
Farida da Shalik cikin rakiyar aminai
da suka hada da su Farid, suna sahun gaba
wajen taryar jama'`a iri daban-daban. Faridar
wadda ke cikin din auta kasancewar a yau
ne ta iso gidan da babu mahaifinta sai
94 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
hotunansa sanyc da bakaken kaya da bakin
tabarau don gudun nuna idanunta, itace ta
fara hango Balala wanda ya iso da `yar
tawagarsa cikin bakaken kaya da kin
tabaran shima wanda bai boye gajiyar dake
fuskarsa ba. Babu Gata lokaci ta bar layin
jama`a don shigewa inda zata iya nisanta da
hotunan a yayin da ta kasa jurewa.
Koda ya gama gaisuwarsa a waje ya
so saduwa da iyalin marigayin, sai dai abin
bai samu ba kamar yadda ya bukata. Ya san
me ya janyo hakan sai bai matsa ba ya
koma.
A cikin falonsa ya hadu da Wilson
wanda ya sanya duk da mutuwar zuciyar da
ya zo da fatan zaman da yake ya ji ya kasa
da ya sami Wilson din a zaune a falon jira.
"Daga ina me ka zo yi a nan?"
Wilson ya mike da dariyarsa ta keta.
"Na zo nayi maka barkan rasawa da
muka..."
Fita min daga gida kafin na yi wani
abu da bai dace ba"
"Allah Ya gani sai na gaya maka
abinda ke tafe dani kafin na fita...Ina so ne
nace maka yanzu mun zama daya...Su
95 Mafiyan Masoya-2 Raıma Abdulmajid
Na`ibi duk sun rasa rayukansu yayinda mu
kuma muka rasa Farida ni da kai"
Ibrahim Balala ya tsaya cak a yanzu
dan ya ji abinda Wilson ke son cewa don
duk haushin da yake ciki kamar fa zai ji
abinda bai taba ji ba. Sai ya sami kansa yana
turo iskar murmushin raini.
"Ni da kai mun rasa Farida kace?"
Wilson ya zauna ya dora kafa bisa
`yar uwarta.
"Haba Bally! Kana zato kafi kowa
ido? Doguwar kyakkyawa kamar Farida
dake zagaye da samari ke baibaye da ita a ce
ni ba zan ga mafarkina tare da ita ba? Kawai
dai duk cikin samarin kai na ji na ki jini
kasancewar kai ta baiwa zuciyarta, don haka
nayi amfani da ofishina wajen saukar muku
da hasara...Bayan ka auri Farida har ina da
tabbacin ta je da kai inda ban je ba a
ilahirinta har kun sami ciki, na yi amfani da
mahaifinta wajen shirya kashe ku...Ba da
sona ba ka ci sa`a ka tsira, amma ban fadi
ba, domin Farida ta rabu da kai da"
Ibrahim Balala yayi cikinsa da sauri
don neman mutuwar kasko, amma tuni ya
nuna masa bindiga yana kada kai.
o Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
"Um-um! Ban da garaje Bally, daga
baka tarihi sai ya zama fada...Me zai hana
ka tambaye ni cewa...me yasa azabar bata
tsaya kanka kawai ba na hada da Megidana
da masoyiyata? Da na baka amsa cewa,
wanna 6angaren ba nawa bane Fansar
Richard ne wanda yayi amfani da kai da
kudinka ya dauki fansarsa a kan Na`ibi har
ya ci riba saboda kai wawa ne.Richard,
Merry, da Wilson duk gamayyar `yan
daukan fansa ne wadada sune ainahin
Mafiyan Masoya ba ku ba.Richard, ya so
mahaifiyar Farida, wadda aji da addini ya sa
ta zabi Na`ibi Mansur tayi fatakali da shi,
wanda adalilin soyayya da nuna mata
iyakarta ne ya taso Na`ibi a gaba ya kuma
ingiza shi gasar kasuwa da Ubanka don
dukiyarsa ta kare...duk wani abu da ka ga
muna yi har zuwa kwana uku baya a tsare
yake shekaru masu tsayi, wato Richard ya
kashe Na`ibi ya tozarta matarsa da
mutuncinsu a idon duniya ya kuma ci ribar
kudi, yayinda ni nake son ganin bayanka kai
da ka kwace min lFarida"
Yayi nishu da kakari sannan atishawa
a yayinda Balala ke ta hankoro bindiga na
97 Mafiyan Masoyа-2 Rahma Abdulmajid
tsorata shi, domin tuni har ya soma hawaye
na takaici da rashin mafita
Kasan me ya sa nake bayar da
wannan dogon labari? Ka san me yasa na
zabi na baka labarin ba Farida ba? Saboda
ka fi Farida jahiltar lamarin...Saboda
awoyinda suka rage min ba zasu isa na sami
zama da Farida har na fayyace mata ba kafin
ta mutu, domin yadda ka ganni
KUAnan...Mintoci suka rage min a duniya...Nida
Richard mun sammace junanmu saboda hadama da gudun kada wani ya fara kashe
wani...Bikinmu na farincikin nasara a gidana
na sanya wa Richard magani don ya mutu
yayinda nima ya sanya min wani a Cocain
don na mutu. Duk da ba shiryawa muka yi
ba, amma dabarar mu ta zo daya ta mu
sanya maganin da zai debe mu a woyi bamu
mutu ba don kada mu cika a gidajen juna,
wannan ya sa bayan mun fahimci mun
ha`inci juna ni da shi, mun gaya wa junanmu
cewa mun sammace junanmu cikin mayen
kayan da buguwa da tuna Merry ta ukunmu
da muka kashe, mun zabi mu mutu a wurin
wafanda muke so mu kara goga wa kashin
kaza"
8o
Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Yayi wani yunkuri a yanzu da
idanunsa ke kara yin jajawur na azaba.
"Zan mutu a hannunka bayan da na
sanar da duniya ka sammace ni don ka mutu
a sarka na kara nisanta ka da Farida, kamar
yadda Richard na hanyarsa ta isa Gahana
don dubo masosiyyarsa ya cika a kusa da
ita...Kada ka musa haka don in ka yi wani
yunkuri Za ka riga ni tafiya don haka ka
tsaya kawai ba so nake na kashe ka ba tunda
na riga na kashe soyayyarka da Farida za ka
iya ci gaba da zama a duniya in har baka
matso kusa dani ba"
A yanzu Balala ya kasa amincewa da
ya jira umarnin kamar yadda Wilson ya
tsara, amma yaya zai yi? Ji yayi tau! An
harbe hannun Wilson bindigar ta fadi inda
ya sunkuya ya rike hannunsa yana kallon
gefen Balala cikin mamaki abinda ya ja
hankalin Balalan shima ya juyo
Farida ce rike da bindiga.Duk da tana
cikin bakaken shiri bai hana ta juyo cikin
dauriya tayi wwa Balala wani kallo na
soyayya da ya sanya hantar cikinsa kadawa
ba, sannan ta dubi Wilson a yayinda ta
lalubo hannun Balalan da ya zama
99 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
mutummutumi ta rike tana murza su a nata.
"Ashe kai ba gwani bane Wilson...Da
kai gwani ne da ka san cewa ko mutuwa
bata daukan ran ran soyayya sai dai ta raba
ran masoyin da masoyinsa. Kenan kayi
kuskure na barin Farida da Bally a raye,
domin wata dama ka basu ta sake kara wa
soyayyarsu nunfashi"
Ta sanya kai jikin kafadar Balala a
yayinda ta yi wani murmushi na nuna
Kauna.
"Bally na sona, ina son sa har yau duk
da wannan Garna da kuka yi...Ina fatan
wannan sako ya isheka zuwa lahira"
Wilson ya rike zuciyarsa yana kakari
cikin kallonsu, a yayinda jami`an tsaro suka
iso falon don tattara shi kafin ya karasa.
Ana ficewa da Wilson Farida ta
mayar da fuskarta murtuke ta zare hannunta
daga na Balala wanda yayi maza ya rike
ragowar yatsarta ta tsakiya
"Farida"
Ya ambata cikin tafasar nunfashi. Ta
juyo suka hada ido da nasa mai yayyafi.
"Farida da gaske ne abinda kika fada.
ina son kilIUHU! Farida na yarda ni na yi
100 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
asara ni na sha kayc a wannan fadan, ba da
kudi ko suna ko wani abu ba, na sha kayc ne
da na rasa igiyar aurenki wanda na salwantar
da ita da hannuna a wannan cacar...Farida
yaya za ayi na sake samin wata dama da ba
zan baki kunya ba a cikinta?"
Tayi murmushi sannan ta karbi dan
yatsanta
Wannan wasan kwaikwayon da nayi a
gaban Wilson nayi ne a matsain sakon
hasara da zan iya ba shi na karshe ya je
lahira dashi ba don wai lamarin haka yake
ba.Bally na dauko bindigar nan ne na zo har
gidanka don na karar da wannan wasan dake
tsakanina da kai ta hanyar kasheka na kashe
kaina don gudun bai wa wata soyayya damar
rayuwa wadda na lura a cikin nunfashin mu
take. Na yarda da hukumcinka a lokacinda
babanka ya mutu na kokarin yanke duk
wwata zumunta tsakanina da kai...Amma na
kasa kashe ka ne bayan da na ji sakon
Wilson na cewa na sauya dabara, na kayar
da kai a wani sabon yakin Mafiyan Masoya"
Ta juya za ta fita amma Balala ya
sako tareta.
"Idan ko haka ne kada ki fita sai kin
101 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
kawo karshen rayuwata, muddin kin san
cewa ba zaki sake rayuwa da ni ba kamar
yadda na san ba zan iya rayuwa bakkc ba.Ko
da baki kashe kanki ba ki kashe ni Farida ko
kuma ki sake bani wata dama ta so"
Farida ta juya tana dariya ta fitar da
waya inda ta buga asibitin mahaifiyarta dan
jin ko Richard ya iso kamar yadda suka ji a
bakin Wilson? Kanin mahaifiyar ya tabbatar
da cewa, lallai an ce wani mutum ya iso har
ya saci hanya ya shiga dakin mahaifiyarta
inda ya mutu a jikin gadonta kuma an same
ta ta bude idanu