da na ke son
sayarwa har aka samar da wadda ta fita
wanda na san ba G Hadi ne suka samar ba
su ma sayowa suka yi don su karya ni.
Farida bamu hankalinki koda na dan lokaci
ne sai a gama wannan sannan ki zo da duk
irin tuhumar da kike son zuwa da ita. In b
haka ba Farida kun 6annatar da
makamashin k mfaninmu da yawa ta inda
ba zamu iya faukar hasara ba...In aka
5
و
53 Mafiyan Masoya-2 Rahma Ahdulmajid
same ni da laifi ba zan iya biyan wannan
diyya ba"
"Don haka ne nake cewa ka nemi
Wilson ka ba shi hakuri ka mallaka masa
ofis tunda ni ban iya ba, ko kuma nawa
yayi tsarki da yawa tunda ba zan iya kifar
da rai ba"
Ta juya ta fice yana kira amma bata
juyo ba. A gajiye ya kunna tabarsa ya dubi
matarsa da ta zauna a kujera me
fuskantarsa cikin hucin fishi.
"Da baki mare ta ba, ba a magance
matsala da irin su Farida da hannu sai kace
'ya'yan tsakiyar gari...bana bukatar karin
abokan gaba...."
"Ta ban haushi ne, amma ka san za
ta dawo babu fishin da za ta iya yi da kai"
4 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
BIYAR
Richard ya dubi Wilson sannan ya
mayar da idanunsa kan tarin hotunan dake
hannunsa
"Zai yi barin kudi kada wannan
bayanai su fito,don haka daga kwabo zuwa
taro har Dala na wannan kudi naka ne, kuma
don kada yayi wani tasiri a gaba bayan ya
gama kashewa din zamu fitar da su, wannan
ne zai kammala fitar da shiyar kudina dake
hannun Ibrahim Hadi yaro me kwazo"
Wilson ya karci kasumbarsa.
"kafin na je aski Oga baka ganin
wannan cacar za ta karya Hadi da Na`ibi ta
inda ba za su sake tashi baa karo na karshe,
Lokacin da akadiba din yayi ne ko kuwa
idan lokacin bai yi ba kuma haka ta faru kai
da me za ka tsaya? Ko an sami sabbin
kamfanonin bayar da hayan yara ne?"
Rchard yayi murmushi.
"Ko daya na ma gama bayar da hayan
yara. So nake ma a yi bikin yaye ku ta
wannan hanya... Ba an ce ka manta tsarin
ba, an dai sami ka in abubuwanda suka
55 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
sanya komai ya zo mana gidan sauki ne.
Ban da abinda zan iya godewa irin soyayyar
Balala da Farida wadda ta zo ta rage wa
burina tsayin shekarun cika da kuma
saukaka min hanyoyin isa gare shi. Gaskiya
na ji dadin wannan soyayya .Kamfanin Hadi
da na Na`ibi duk sun tashi aiki domin suna
dauke da dimbin bashin da in suka kara
wasu taki a wannan yakin kamfani da suke
duka za su durkushe, abinda yasa suka zaku
kowanne ya kawo karshen daya kenan ko ya
fuskanci farfadowarsa, wanda ni kuma ba
zan bar hakan ta faru da wuri ba don
faduwarsu ita ce za ta kawo jinginata a
jikinsu da jinginar yarana. Ka dubi duk inda
kake son mallaka a kamfanin da kayi aikki
ya kusa zama naka,. Don fadan kuruciyar da
ake ya gama karya ginin guda biyu. Ni ko
yanzu na gama tashi da hannayen jarinda
Dan Hadi ya sai min, kawai `don kada ya
dame ni ne nake son ya kwanta, kuma ku ma
ku yi naku `yancin ba a kudina ba"
Wilson da Merry suka yi dariya har
da tafa hannu. Merry tace.
"amma sir ni ta ina zan y nawa
yancin?"
56 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Ko kallon ta bai yi ba.
"Za a biya ki la`adar ki ne da abu
biyu. Daya shine ramuwar da kika jima kina
neman yi a kan kawarki Farida, sai kuma
kason da Ibrahim zai biya na batancin da za
ki yi wa Na`ibi wanda ko sisi ba zan dauka
ba naki ne dukа"
Ta tashi tayi tsalle duk suna kallon ta
suna dariya.
"Master ka ce ka yarda cikinnan da na
6oye na Na`ibi ne?"
Ya gyada kai.
"Shaidar DNA da likita ya kawo min
ta tabbatar da haka, kuma hotunan da muka
sanya camera tayi muku zasu wadatar,
muddin ba zasu 6ata miki suna ba"
Ta girgiza kai.
"wane suna kuma ga kudi?"
Wilson ya mike yana sosa kasumba
ko kallon Merry baya yi.
"in irin wannan ta samu dole na yi
askin Kasimba"
Duka suka mike.
"Ban da fita dai Wil. Karfe uku
jirgink a zai tashi don haka, karfe daya ka
zamo ikin shiri na batar da kama"
57 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Suka watse daga yar farfajiyar shan
iskar Cikin fara` a
*** *** ***
Karfe biyu da rabi na dare Richard da
Wilson suna zaune cikin zungureriyar motar
suna shan lemo a dakin shakatawar cikinta.
Bai kalli Wilson ba ya mika masa takardu
"Yanzu ka koma ainahin sunan ka
Dimetri. Ka ci gaba da irin rayuwar da ka
zaba a a kasar tsibirin Thaiwa.
Nan a hannunka akwai takardun Acс
na inda Na`ibi zai dinga zubo kudi"
Wilson bai ji wani abu sabo ba don
haka ya shafi kasimba.
"Yaya za a yi da Merry Master?
Gaskiya na ki jininta
Ya dauko kofi tafasasshiyar giyar ya dan tsotsa.
"Ni ba kin jinin ta nayi ba, amma na zargi kada barinta ya zamo wautar farko da
zan yi wa aikina. Don haka da ta gama
aikinta za ta ci dukiyarta na sati sannan ta
wuce inda babu me sake ganinta"
Suka dubi una shi da Wilson inda ya
sa yatsunsa a kafafen hancinsa ya toshesu,
Mafiyan Masoyа-2 Rahma Abdulmajid
wanda alama ce ta cewa zasu kashe mutum
wato rasa nunfashi, wato kashe ta za su yi.
Wilson ya gane karatun har da tintsira dariya
asıri
"Kenan ya kashe ta don ta tona masa
*** *** ***
Farid tsaye yake da a tsakiyarsu,
amma ganin yadda karan ya kaure sai ya
koma gefc ya zama matsoracin dan kallo.
Ba dole ne Farida na da gaskiya a tata
muhawarar ba, amma shi dai ya fi yarda da
maganganunta da hujjojinta.
"Ke wace irin yarinya ce da kawai
daidai ake cewa kin yi ki amsa, amma ba
zaki taba amsar kuskure ba? Me zai hana ki
amince da cewa kin yi mubazziranci da kupi
a wannan yakin kin sanya zuciya da fishi da
yawa wanda shine ya janyo mana wannan
asarar?"
Farida ta cakuda kanta ta saki ta kama
zagaye ofishin cikin fishi.
"Saboda a wannan yakin ne har dan
da yake jinin zuciyata an kashe min
balantana wasu milyoyi da ba a jin za su
taba iya tunanin sayensa, wanman sunansa
59 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
fishi ko hankali? A wannan yakin na rasa
komai da nayi mafarkin mallaka saboda
abinda ba inda ya shafe ni sai kai
Father...Duk da haka ban yi kasa a gwiwa ha
na zo baka lokaci na don kada ka rasa naka
abinda ka fi ganin mutunci....Ina jin daidai
da rana daya na cancanci a ce min son barka
maimakon yawan tono laifuka na ko da na
rana daya?"
Na`ibi yayi dariya wadda ta nunfashe
ragowar hayakin tabarsa.
"Na ce miki son barka Farida saboda
kin karar da asusun ajiyar kota-kwana kin
karar da ajiya maganin wata rana na
ofishina, kin karar da baital malin zahiri ta
inda ga duka na nan bani da wata garkuwa
da za ta tare shi, in na ga na kai labari to
mu`ujiza ce ba aikina ba...Wannan zan
godewa Farida?"
Farida tayi dariya ta dawo gabansa.
"Ba shi za ka gode wa ba, bincike za
ka yi a kan yaya aka yi karen ka ya bar
bayanka ya je yana tona ka? Me yasa baka
son ganin laifinsa hasali ma tsoron sa ka ke
ji Father, Wane sirri ne ya sa ya fata, baka
ganinsa sai dai ka ji asirinka a wajc? Na san
Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
a iya aikin mu wata takwas ni da team dina
babu inda muka yi abinda ba a taba yi ba a
kamfanin nan...Wilson ya taba dilmiyar da
asusu uku don a kayar da Hadi da Messi
lokacın ina karatu wanda bayan sun zama
tarihi kadan ka zama tarihi baba da badan na
dawo ba...Amma in ban manta ba har bikin
cika shekara ka shirya masa a Bon....Amma
nawa ya zama najasa wadda ta ma hana a
duba me ya jawo ta...Ka bincika Father, in
har ka gano yadda aka yi cinikin Screen
wanda kai da Wilson ne kuka sani ya zamo
matsala a yanzu... Tabbas na gane cewa ban
cancanci godiya ba. Kafin nan na ajiye aiki
zani hutu"
Ta juya ta kwashi wasu takardunta
daga kan tebur ta kama hanyar fita da sauri.
Farid ya bi ta da kira da sauri amma Na`ibi
ya kwalla masa kira.
"Bar ta ta je na gaji, zan rike aikin da
kaina...Je ka ka gaya wa Sakatariya a hada
min meeting da daraktocina da sashin
ود shara`a"
Jikinsa a sanyaye cike da nemar
damar magana ya fita isar da sako.
61 Mafiyan Masoyа-2
***
Rahma Abdulmajid
*** ***
A dakin taron Naibi ya zama dan
kallo inda manajojin da lauya ke bugawa
kan matakin dauka. Farid wanda ya zama
sakataren Karfi da yaji kwafar wa Farida duk
abinda ake yake yi ba tare da ta sanya shi ba.
Babban lauyan ya gaji da karakaina da
manajojin ya mike ya dubi Ma'ibi
"Ranka ya dade. Hanya daya ta
kubuta daga wannan annoba itace, a nemi
kotu ta gaggauta samun mu da laifi mu biya
diyyar nan, za mu yi haka ne ta hanyar
amincewa da laifinmu da neman sasantawa
ba tare da ja ba. Lallai jan wannana shari`ar
kamar yadda ma`aji ke hanga zai iya sayo
mana lokaci har mu juya kudin da muke da
su a sami riba sannan mu biya diyyar, amma
kada a manta, zamu biya diyyar dai a karshe
wanda watakila ma a lokacin da za abukata
kudin basu dawo ba, sannan jan lokacin ya
jawo hankulan kafofin yada labarai kan
lamarin wanda asarar da zai yi wa sunan
kamfanin nan, bana jin wani kudi zai iya
sake sayo masa"
Kafin Na'ibi yayi magana Manajan
kudi ya tsomo baki yana yunkurin fishi da
62 Mafiyan Masoya-2
son ci gaban musun.
Rahma Abdulmajid
"Amma kada a manta abinda muke da
shi ranka ya dade, in har muka zare muka
biya wannan diyyar aiyuka za su tsaya cik,
sannan akwai yiwuwar mu kasa biyan
ma`aikata na tsayin watanni shida..."
Na`ibi ya daki tebur cikin fishi.
"Solomon, nine a kan gaba ba
ma`aikata ba, idan ko nine a kan gaba to
sunan kamfanina ne zai zo farko kafin yadda
komai zai gudana...muddin babu wata
shawara da za ka kawo da za ta tsirar da
sunan kamfanin nan daga durkushewa, to
saki kudinnan" יי
Ganin inda hankalin me gayya ya fi
tafiya ne ya bai wa sauran manajojin damar
magana inda manajan talla ya fara da cewa.
"A na iya rage yawan ma`iakata don
tsuke bakin aljihu"
Farid ya sako baki a yanzu ganin
cewa an dawo inda Farida ke son a je.
"Ko kuma a maye gurbin wasu
ma`aikatan da kananan injiniyoyin da suka
yi aiki a kamfanonin sadarwa, suna nan
birjik suna neman aiki, ina ga idan muka yi
haka sannan sashen talla ya samo mana
63 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abhdulmajid
wasu kana nan kwangiloli da a da bama
karba zai rike mu matuka har watanni shida
da nakc ga maganar ta mutu kamfani ya
koma komadarsa"
Na`ibi ya mike yana duban sakatarc.
"Tattara shawarar lauya, da ta Farid
da ta Otimi ka baiwa head of staff a fara
aiwatar da su cikin gaugawa"
Ya sake duban wani saurayi dake
tsaye bai ce uffan ba can kusa da kujerarsa.
"A binciki ta inda aka sami
gurfataccen screen dinnan da yadda aka yi
batun ya fita ta wani salon binciken daban,
bana son wanda security din mu ke yi.
Kowa ya tafi"
Suka tashi simi-simi daga dakin
taunawar suna ficewa
*** *** ***
Balala yana tsaye yana duba
kwalliyarsa wadda komai banda hular
malafa fari ne kala jikinsa. Waka yake
rerawa don murna.
"Master ina za ka ne haka? Ya kmata
kafin a shakata a bamu ladan taya murna ko
Katar mu je"
o4 Mafivan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Balala yayi dariya.
"Zan je ganin idanun me asara ne
Farida wadda ta zaci bata kayuwa, ko yaya
za ta gan ni yau? Batun saka muku kuwa
kada ku ji komai, yanzu masassara Na`ibi ya
soma, da ya kai kasa warwas zan daďada
muku"
Ya juyo ga yaran ya dubi wani me
murmushin.
"Nabigator, ina GPS ta hango maka
Farida?"
Yaron yayi dariya.
"ai da ta fice daga ofis yanzu haka
bakin ruwa ta je tana jefa duwatsu."
Balala ya daga musu hannu.
"sai na dawo"
Ya fice yana fito, suna binsa da
kallon dariya.
*** *** ***
Tunda Farid ya fice ofis Farida yake
kira a waya, amma ta ki samuwa, da alamar
ko bata kashe ba ta katse wayar daga
shigowar kowane kira, idan tayi irin haka to
bava tababa ta tafi gindin ruwa ne huce
haushi don haka ya karya kan motarsa don
2
65 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ya cin mata.
Tana tsayc tana sarkafa sandar kamun
kifin a cikin ruwa ba don ta kamo komai ba
sai don tayi wasa ta sassauta wa zuciyarta.
Ta ji taku, kuma ta raya wurinta ake zuwa,
amma kunne ta bayar bata juyo ba, mutane
da yawa zasu so sanin inda take kuma su zo,
Farid, babanta ko lauya duka zasu so ganinta
bayan ta huce, kuma daya cikinsu take zato,
amma kusan isowarsa bayanta sai ta ji
gabanta yayi mugun faduwa bayan ta shaida
takunsa, takun da ba za ta taba mantawa ba
don yana cikin abubuwan da ta fi so a
ilahirin jikinsa. Kunya ko nauyi ko kokarin
boye yanayi kowanne na iya zamowa dalilin
kin juyowarta, amma tana ta zumudin ta ji
abinda ya kawoshi watakila hakan ce ta sa
take jin ya dade a tsayc ko kuma dai da
gaske ya dade dinne bai ce mata komai ba
sakamakon kallon da yake yi wa Faridarsa a
wurin da suka saba kasancewa tare a lokutan
bakin cikinsu tare. Ga shi yau Farida na
tsaye ita kadai kuma shi ya iso ba da niyar
ya taya ta bakin ciki ba sai don ya kara
mata...Me yasa Farida ta zabi wannan wuri?
Ya ji yana tambayar kansa maimakon ya
66 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
amince da karaya da sabon yanayin da ya
sami kansa na tausayi da so.
"Baka ce min komai ba har yanzu"
Ta karya bille tayi magana ba tare da
ta juyo ba, a yayinda ta ji alamar kamar yana
shirin juyawa ya koma.
Yayi karfin hali ya tsaya ya furta
daya daga cikin kalmomin da ya tsarasu a
gida cikin karsashi don ya gaya wa Farida,
amma gashi yanzu yana zakulo daya dakyar
yana fadi babu dandano.
"Na zo ne na yi bikin daddadan rana
ta ta yau a bakin ruwa shine na same ki a
wurin, zan koma don kada ki bata min jin
dadina da ganin fuskar ki"
Sai da ta lumshe ido na raďadin
kalmomin sannan ta juyo tana me saurin aro
murmushi kan fuskarta.
"Ni kuwa ka ga bakin ciki nake,
amma juyowa na kalli fuskar me hasara zai
iya sanya ni farinciki"
"Farida kenan! Yau fariya ba za ta
kara miki komai ba sai kama da mahaukata.
Farida wannan ne irin duka na guda daya da
nake wa masu giggiwa irinki, na san indai
da kwankwaso ake yunkuri to na karya naki
P
67 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
da wuya ki sake tashi"
"ka ji inda za ni sabon shiga...da za ka
gyara ka ce sojan haya sun karyani da na fi
jin dadin zancen don haya kayi a zo a taya
ka fada da Farida wanda wannan kadai ya
isheni shaidar faduwarka don kai kanka ka
yarda ba za ka iya karawa da ni ba sai da
agaji. Karin haske gare ka shine masana
irinmu sun san ko me babban jari irin
Mansur Na`ibi ya hayi fasahar da tayi
wannan aiki naka zai iya karyewa warwas
ballantana 6eran masallaci irin
kamfaninka.Allah Ya sa ba sai da babban
lamuni daga baki ka karasa biyan wannan
makami ba, wanda abin tausayi shine Na'`ibi
G zai iya riga ka murmurewa. Idan wannan
faduwar kake nufi ga Farida gaskiya nayi
maraba da ita"
Yana ta dariyar da a kan fuskarsa
kawai ta tsaya don tuni kalamai da yanayin
Farida suka sure me iya ketarawa
"Idan na fahimci maganar ki da kyau
shine kin gane kin sha kaye, duk saura
kalaman lallashin kai ne"
"Ko kuma kai da baka gane zaurance
bari a yi maka gwari-gwari, tana nufin kun
68 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
fadi tare amma bata kai kasa ba yayinda kai
har ka suma"
Farid ne ya amshi zancen a fusace da
manufofi iri daban-daban karkashin
jagorancin kishin ganin Farida da mazan
jiya. Ibrahim Balala ya kalleshi cikin
mamaki me zaman kansa da karanta.
"daga ina Dan hausa? Har Farida tayi
faduwar da irin ka zasu fara tare mata fada?
Lallai nasarar tawa ta tsallake inda na zata?"
Farida ta dan lallabi hannun Farid
wanda ya so yin magana me kaushi yayi
shiru sannan ta dauki taku zuwa inda Balala
ke tsaye wanda ya bata damar samin abin
gaya masa bayanda ta lakanci wani sauyi da
ya kara samu a yayinda ta lakaci hannun
Farid. Ta iso ga kunnuwansa tayi rada
"Na fadi warwas har na rabu da
namiji irinka na hasarantar da danka don na
raya soyayyar wancan Kaskantaccen da ta sa
zuri`ar... Wannan ma wata faduwa tace da
baka sani ba, ina fatan za ka ji dadinta"
Ya kame kamar gunki bayan da ya
sami tabbacin duk wani motsinsa a nan gaba
na raba Farida da motsine har abada. Bai
juyo ba sai da ya ji tashin motarsu ita da
69 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
Farid wanda suka bashi iska
*** *** ***
Richard ya sunkuyo cikin ladabi yana
murmushi.
"Sir! Ni da wannan karban Kananan
sana'ar in har za ka iya karban karamin abu
gara ka karbi mukamin gwamna. Sanin
kanka ne neman ka a ke ba kai kake nema
ba...."
Na`ibi ya kada kai.
"Babu wanda ya san ni Richard
ballantana ya jefa min kuri`a, hasara ta
Naira bana da shirin sake yi yanzu"
"Kuma ma ba za ka yi ba, don a
Najeriya ba a jefa kuri`a don an san mutum,
kawai iyayen gida yake bukata, gashi kuma
Allah Ya baka yaran gida ma masu fada a ji
a kasa ba iyayen gida ba...Sir ina hango
maka siyasa ne saboda za ka amfanu ba tare
da mutane sun yi hasara ba. Za ka iya juyar
da hankalin mutanen jiha guda zuwa sana`ar
ka ta sadarwa, ka basu guraben karatu da
tallafi a kudin gwamnati zuwa waje sannan
in sun dawo su zo su yi aikin kyauta a
kamfaninka da sunan suna biyan gwamanti
70 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ladar daukan nauyinsu, sannan za ka iya
daukan baital mali na wata guda ka zuba a
jarinka ka juya ka biya ba tare da kowa ya
sani ba. In kayi haka karuwar mu cе
karuwar al'umma ce fiye da wadanda kc
zare musu kudin su cinye ba tare da sun sai
musu komai ba ban da baro da keken dinki"
Na`ibi wanda ya kura masa ido cikin
gamsuwa da shawawarinsa cikin takatsantsan da tuhuma ya yi ajiyar zuciya.
"Bana so in zama dan siyasa na fi so na
a dan kasuwa, ga ta siyasa aiki ne da ba a
ritaya,musamman ma a kasar mu, yaya zan yi
kenan?"
"In tayi maka dadi baka ba ritaya sir, in
ko bata yi maka ba, to a kanka za a fara ritaya
don sai ka karya tarihi abinka"
Na`ibi ya taso yana dariya.
"In kana bani shawara Richard ina jin
tsoro, musamman ma in ba ta kudi na
bace...ban taba ganin ka dage kana bai wa
wani abinda zai yi amfani ba tare da ya biya
ka ba...Richard kada ka yi wata rawa da za ta
Gata tsallenka"
"Sir! Ka wuce haka a wurina... Na san.
matsalar bata wuce zargin da kake min tun
71 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
6acewar Wilson ba... Wilson ni ne me case da
shi don ya saba umarnina, kuma ba zai buya
ba"
"Me kake'so kafin ka sake dawo min
da Wilson?"
Richard ma ya mike ganin Na'ibi na
nuna ya gama hirar.
"Ba abinda nake so ban da ya shiga
hannuna, a lokacin ne zan fadi me zan
karba...Sir duk garin nan babu me iya saya na
sai kai...in ka karye alkadarina ne zai karye
don zan dena tsada...wannan abu ne da ba zan
taba bari ya faru ba"
Na`ibi ya zuba hannu a aljihu.
"Zan yi nazari kan maganarka na gode"
Ya bar masa falon taunawar ya haye
sama.
*** *** ***
"Me kika gaya wa Balala ne na ga ya
daskare?"
Farid yayi ta maza ya tambayi Farida
bayan da ya raba tsakiyar tsaigumin da yake
mata gida biyu don ya shigar da bukatarsa ta
jin sirrin bakin Farida
Har ga Allah ba za ta so ya ji ba, tayi
maganar ne don ta sanya wa Ibrahim
72 Mafiyan Masoyа-2 Rahma Abdulmajid
bakincikin da zai rike mata shi har ta wuce ba
tare da ya ga karayar da take son ruguza ta ba,
amma ba ta da dashin wani abu kan Farid,
kuma bata zaton hakan a wurinsa, don haka
me zai sa ta gaya masa.
"Ba wani abu bane. Lambobin da ba
zasu sake shi ba na manna masa...ina jin ka
yanzu Father ya amince da shawarar tamu?"
a
Bashi da zabi sai su...ya ce ma mu fara
aiwatarwa, amma bana jin za a iya yinsu
tsarkake in babu ke don haka ki daure ki..."
Ta tare shi.
"Kada ka roke ni abinda ba zai yiwu ba
Farid..ban ce na rabu da father ba, ina son
bashi dama ne ya bambance jini da kudi.
Rashin son faduwarsa a jini na yake, sannan
ina da horon da zan iya zaunar da kamfanin
mu in fadar da duk me adawa da shi cikin
tsarkakken yaki, amma father yayi imani da
masu yin aikin don kudi da kuma son hanya
kazama, hanya daya ta rage min ita ce na
koma gefe na ba shi dama yayi kuskuren da
zai gane bambancin ni da su, in ba haka ba na
dinga komawa ina bari kenan...Ranar da kake
cewa farkon ranar da ka san ni kenan, irin
wannan ce ta farU
Wilson ya kawo tsari da za mu bigi me
73 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
ciwon zuciya da kwaf daya zai mutu, a
ganinsa za mu huta...na bada shawarar me zai
hana mu kyale shi da yada ciwonsa ya tafi
jinya mu kuma mu raraki inda zai samo
kwangila? Father ya zabi Wilson a kaina har
yana yi min wayon cewa soyayyata da
Ibrahim ta sauya ni na zo na koma London mu
hadu da dan minista mu fara soyayya. Ni
Farida soyayyar Bally bata raba ni da tunanin
aikina ba sai ta dan minista?Hum! Shine na
bar su. Bayan mutumin ya mutu neadalilin
dukan arziki da bashiba tare da mun sami
jarinda muka haka bane father ya gane ya
dawo da ni shine ka sake gani na a ofishinsa"
Farid wanda yayi shiru yanzu yake
sake sanin Farida wadda ashe a cikin najasar
ma bata wuce tusa a gaban kashi da fitsari ba
muddin haka take tunani. Yau ya ji ya
wanketa tas daga tambayar da ya rasa amsa na
karan tsayen da take wa mahaifinta.in har
haka ne..shi fa me nasara ne in ya so Farida.
Ya dinga satar hanya yana kallon Faridar dake
cikin fishi tana kara yi masa kyau.
***
al Daga Ibrahim har Richard a tsaye suke
suna yi wa juna kara.
74 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
"Idan kana zaton fishi ko kishi su nc za
su baka abinda kake so, ko sai ka cusa su a
kwanya kafin kayi wani abu to lallai bana
cikin wannan aiki, amma zan baka duk kayan
aikin da ka saya da kudinka, amma fa idan har
nine zan yi aikin, kuma na bada lokaci to dole
ka jira,wannan ne duka na farko, lokacin na
biyu ya kusa sosai, wanda in aka yi garajen
jefa kwallon zai golin zai kama kuma
dukanmu zamu kwana ciki"
"Farida bata karaya ba, tana ma yi min
barazanar za ta sake duka na. Tana ci gaba da
murnar ta kashe min da za kuma ta sami wani
da wani na mijin. Duk wannan kana nufin in
jira har su faru?"
Richard ya juya ga kofa.
"Kana iya kace ba Za ka jira ba don ba
ruwana da wannan abubuwa da ka lissafa
naka ne. Aikina shine in kayar da Na`ibi ba in
hana Farida aure ko haihuwa ba, idan ka sa
wannan ciki ka bata min tsari ba ruwana da
wasan yayi nasara ko bai yi ba za ka biya ni
kudi na yadda muka yi alkawari"
Ya juya ya bar falon Ibrahim Balala na
binsa da kallo cikin huci da tunanin kamar
bashi da zabi fa ban da jiran. Amma fa da
CIWO.
75 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
2
SHIDA
Kamar komai ya koma yadda yake a
da, Ibrahim Balala ya yi lamo yana jiran
Richard, ofishin Na`ibi sun sasanta da farida
ta koma kujrarta musamman da babu wanda
ya fi ta cancanta, sannan ga babu gasa da za
ta sanya ta yin abinda mahaifin ya fi tsoro
wato 6arin kudi.Wani abu da ya so sake
gwama kansu ita da mahaifinta shine takarar
gwamna da ya fito rana tsaka,maatsayinda
Farida tayi wa yakin cacar baki mai tsayi,sai
dai ba ta yi nasaraba musamman kasancewar
mahaifiyarta mai son harkar girma fiye da
kasuwanci ta dawo gida ta kafa sabuwar
soyayya fil da mijinta don zamowa Uwar
gidan gwamna, wanda lallai ba za ta taba
barin kafa ga tasirin Farida ba, ba za a manta
da tasirin karbuwa da Mansur Bici ya samu a
wurin gaggan `yan siyasa ba har ma ya zamo
uban gida ga gwamnan da ke kan gado, inda
babu wani dan takara da ka iya tunanin zuwa
kusa da shi sai dai kawai ya lika posta dan a
san shi ba don ya ci zabe ba, wannan abu ya
Kara wa Na ibi kwarin gwiwa inda ya fito da
1
a
a
T
a
in
in
an
ra
an
on
Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
abinda ya rage masa na kudi ya bannatar a
siyasar da aka share watanni takwas ana
zazzafan kamfe da kowa ya sallama ya shige
ya gama, amma sai me?
Dan takarar da Ibrahim Balala ya samu
don mara masa baya ya fake da shi ya karya
Na`ibi sai ga shi kwatsam ya yada manyan
tuhumomin kisa da ake wa Mansur Bici a
kafofin yada labaru ciki kuwa har da kisan da
aka yi wa Hadi baban Balala. Abin ya soma
tamkar tuhuma mara tushe wadda cikin
kwanciyar hankali Na`ibi ya nemi lauyansa da
ya shigar da lamarin kara kotu don biyansa
kudin bata masa suna, amma sai ga alamun za
a yi musayar hujjoji na karfafa abin wanda
cikin awa ashirin sai da suka sanya Na`ibi bin
dare ya bayar da cin hanci har da na daya
daga cikin manyan ofisoshinsa, amma ina duk
da an karba an lash, hujjojinda `yan jaridu
suka buga a shafin farko na washe gari sun sa
babu inda 'yansanda zasu iya labewa ba tare
da sun je sun kamo Na'ibi don yi masa
tambayoyi ba.
Bayan tsayin awoyi tare da 'yansanda
lauyansa ya samo belinsa zuwa gidansa inda
suke taunawa kan lamarin.
77 Mafiyan Masoya-2 Rahma Abdulmajid
*** *** ***
Na'ibi wanda ya kunna kakkaurar
tabarsa amma rikon kansa ya sanya ya manta
da tana ci sai hayakinta kake gani a sama
hankalinsa na tare da lauyansa mai bashi
zafafan bayanai.
"Master a tsarin lauyanci in za ka kisfe
gari guda muddin baka so a ga hannunka ciki
ya kamata lauyanka ya sani domin lauya ba
liman ne ko malam ba, lauya wakili ne na kare
wanda yake karewa daga fadawa mummunan
yanayi da gaskiya ko babu.