An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ME GARI
YA WAYA?
NA ZAINAB KABIR BIROMAN (MRS. SUNISU BRISCOE)
KACIBUS MUGUN GAMO
arkada makullan hannunta take gami da karkada K
Kafa, "Kai ko abokinka ba ku isa ba, ba ku kuma
kai ko matsayin da zan 6ata yawun bakina wajen
magana da ku ba. In ce na gaya muku ba na ra'ayinku a kai
kasuwa? kila har yanzu akwai ragowar matan da suke iya
amsar kyautar saurayi, saurayin ma har saurayi me ji da
kansa amma kuma ya rasa macen aure, kai tir da wannan
abin kaico. Ni kam ga zabina nan." Ta nuno shi bayan da
shi kuma, "Sai dai fa shi ba kyautar shi a ka yi min ba,
a'ah! Ni na gani na ce ina so, kazalika shi ma haka, don
haka muka aminta da junamu."
Taku suke cikin isa da kasaita, ya ja ya tsaya dai-dai
gabansa, da kallon raini cikin halin ko in kula ya ce, to kai
fa abokina sai ka dangana, tun da ta kasa amsa kyautar da
aka yi mata kamar yadda ta ce din dai sai a kai aksuwa, kila
wata ta taya, ka san ba duka mata ne suke iya aınsar
kyautar saurayi sukutum ba. Ko kafin ya furta wani abu sun
shige cikin mota, ita take jan motar kamar ta taka su ta
shige cikin gudu.
Zaune yake a ofis din nasu ya rasa abin da yake
masa dadi, ga tarin aiki a gabansa amma ko ya kula, ya yi
sallama ya shigo da niyar ya cike wasu takardu amatsayinsa
na Director (shugaba). Ja ya yi ya tsaya bayan da ya
fahimci halin da abokinshi ya ke ciki, damuwar dai be
wuce na abin daya faru da yammacin jiya ba,tun ajiyan
babu wanda ya ce wani abu, kowanne da irin tunaninsa,
5
a
dukkaninsu rayukansu a bace yake to amma ko katin
safiyar yau tuni shi Samir din ya mance musamman dayake
safiyar ne suka sami takardar yarjewar wasu kwangilolin
gini da tiți da aka ba su, shi kam in dai a kan harkar kudi ne
ya kan ınance da duk wani bacin rai da yake ciki. Ya fara
magana, Da Allah Waheed kar fa abin jiyan nan ya dame
ka, manta kawai ka share ka hada ka watsa a kwandon
shara.
Cikin matsanancin bacin rai ya dube shi, ka san
Allah duk ranar da yarinyar nan ta sake ta shigo hannuna ta
kade har ganyenta, na tsane ta, na tsane ta na dada tsanar ta
tun bayan da na dada fahimtar me ke tsakanin su da
wannan dan iskan yaron, me zan ci da ita? wallahi kow aye
ya yi wannan hadin ya cuce ni ya kuma gama illata
rayuwata. Kai haba! Wallahi zan ci uban yarinyar nan
muddun ta sake ta shigo hannuna, ko waye ya yi wannan
hadin zai gwaminace kida da karatu. Na tsane ta, na tsane
ta ba zan taba son ta ba wallahi.
a
Hankalinshi kwance ya yi dai-dai a kan katafaren
gadon gefen shi Helen ce yarinyar da yake hutawa da ita
cikin daren hannunshi daya rike yake da karan sigari yana
busawa, cikin matsanancin 6acin rai, ya shiga tuhumar
kansa, me Waheed ke nufi da shi ne? Hakika ana shirin
aiwatar da dan karamin yaki a garin nan, raiin hankalin ya
yi yawa ya zama dole ya yi gaggawar daukan kwakkwaran
mataki a kansa, domin ya gwada mishi shi ba tsaransa ba
ne, be ko isa ja da shi ba. yana son Hecdaya son da baki ba
zai iya kwatanta shi ba, don haka zai iya aiwatar da komai a
kuma kan kowa in dai a kan Heedayansa ne.
6
Hello... hello..., wa ke magana? Shiru ba amsa, har
ma ya dan fusata waye ne domin (no number) daga daya Garin a ka saki wata ‘yar dariyar cusa haushi Rival dinka ne ko da yake ba na kira ka da wannan kalmar ba, tun da an ce
ba a son ka ba a ra'ayinka, kai ba a ma amsa kyautar da aka
yimata ba. Ya ci gaba daman na bugo ne na ja kunnenka na
kuma yi naka albishir wannan karon ka debo ruwan dafa
kanka, ko Ja za a yi tashin dunva na uku ne sai na mallaki
zoar so na heedaya ko da yake ko ma ban fafa ba ka riga
ka sani ni tak so ni ake yayı, domin ni gani na ma aka yi
aka ce ana yi ba gwanjo na aka yi ba. ka fahimta?
Da sauri ya yi kokarin ba shi amsa dan kar ya katse
layin ya bar shi da tarin miki a wuyansa, ya fara so abokina
abin da nake so ka lura ka kuma gane, sai fa na aure ta ba
wai don ina son ta ba a'a ko daya, sai fa don in cusguna
rayuwarka, in saka ka cikin kunci kamar yadda na saka ka a
baya, domin nuna maka cewa ko a cikin gayu kai fa fan
rakiya kake, sli ya sa ma na zo mata a matsayin Bonanza,
tun da na san ba ta kai ko matsayin yarinyar da zan iya
tsayawa da ita ba da dai sigar so, ka ga ko tun da ka ga na
zo mata a bonanza, na san abin da na taka ne domin shi ma
Bonanzar zan kwasa, ka lahimta abokina.... ko kafin ya ba shi amsa ya yi saurin katse layin.
Cilli ya yi da wayar bayan da ya shiga nadar abokiyar shashancin nasa fada yake tamkar ita ta kai
zomon alhal rataya aka bata. Koda yake tamkar mahaukacin kareyake idan zuciyarshi ta baci.
Yau fau lamarin da girma ko dan ya nunawa tsohon
abokin nashi iyakarsa, ai ko ba ya son ta baya ra'ayin
aurenta ya zama dole ma ya so ta ya kuma aure ta
7
ballantana ma akwai abin da yake so yake kuma m uradi
irin ta zama mallakinsa?
Tashin farko ya tuburewa mahaifinsa dangane da
lamarina urensa da abar kaunarsa, iya kokari Dr. ElHussain ya yi gurin mahaifin yarinyar domin akwai
sanayya a tsaknainsu amma fa ba nasara, ya kuma fahimci
lamarin dan haka bai riki Ambassador da komai ba face
alheri, ga Tahir ba haka nan ba ne a gurinshi ya tashi
hankalinshi, kai kila da wani ne zai iya hakura ya bar mishi
Heedayan ya rungumi kaddara to amma da yake babban
abokin adawarsa ne kana makiyin da ba shi da kamarsa, ba
ta yadda za a yi ya iya hakurce masa, zuka-zukan 'yan
matan nasa har guda biyu? tamkar ma wani raini ne wannan
da wulakanci, ya yarda ya kwace masa Zecnatu amma
wannan karon kam karyarshi ta sha karya ko don ya gwada
masa iyakarsa da kuma fifikon son da yake wa yarinyar.
Heedayat da Zeenatu ko kadan ba ka iya hada su a ma'auni
guda a zuciyarsa.
Kwanaki hudu ya rage a daura auransu shiryeshriye sun kammala dagakowane Bangarori amma fa ban da
gurin amaren, dukiya kam an kashe ta ana kuma shirin
kashe ta daga kowanne 6angare, lefe ne na gani na fada da
sai 'ya'yan wane da wane kai ko su din ma sai isarsu ta kai
isa, duk kuma daga aljihun General da mai dakinsa da ma
duk irin hidindimun da aka yi babu ko sisin Angon.
Haka nan a bangaren amarya ma iyaye sun yi
bajinta wajen' gwangwaje 'yarsu da kayan alatu irin na
kasar Italiya, musaınınan a ka tafi donin hado mata kayan
daki, haka nan kayan da za ta ci biki da su, musamman aka
tafi birnin Mumbai na kasar Hindu aka hado mata su, to sai
8
dai fa amaryar ko a jikinta domin sun gama wshirya wace
za ta fisshe su ita da abin kaunarta Tahir.
Amarya ta sha kamshi. Ta fada gami da rangwada
guda, ta dube ta da 6acin rai, ta nuno tada yatsa wallahi
Sameera muddun ba so kike mu yi gagarumin tashin
hankali ba kar ki kara gaya minwannan sunan. Amarya?
Amaryar uban wace ce ni?
Dariya ta saka to Allah yahuci zuciyarki, ta gyara
zamanta, ga shi kuma ni da zuwa na yi mu tattauan game
da bikin, to kuma ga shi an min wannan kashedi? Ba ta dai
ce mata komai ba-ta dada tamke fuska alamar babu wasa.
Sameeran ta yi shiru na wani lokaci domin momy
Kaltum din ce ta wakilto ta, su tsara abubuwan da suke
ganin ya dace da kuma abubuwan da suke bukata. Ta yi
Karfin hali, Heedaya ina ga lokaci ya kure har ma za ki
tsaya batawa kanki lokaci tun da dai haka Allah ya shirya
ba sai a yi hakuri mu karbi zabinsa ba. kuma ni meye ma
abinki a gurin mutumin nan da Allah ki so shi ki manta da
komai.....
Wani kundumemen ashariya ta sako mata, hakika
yau na yarda ba ki da tunani har ma kike danganta ni da
wannan mugun mutumin, to bari ki ji ba na son sa, ba na
son sa ba, zan taba son sa ba domin ba shi da tarbiyya ko
kankani.
Ta yi saurin datse ta a'ah to in dai wannan ce
hujjarki ba ki ko da madogara mai kwari, domin shi ma
wanda kike abin a dominsa ba tarbiyyar ce da shi ba, kai ni
ganina gwanda wannan din, kila in kika yi mishi da'a
kika yi mishi biyayya sai ki ga kun zauna lafiya har ma
wata rana ki so shi.....
a
9
Cikin fusata ta ce, aikin banza kawai na yarda ba ki
da mutunci wai har ke kike fadawa Tahir wannan kalmar....
Ta tari nufamshinta, a to maganar gaskiya ce ina wata
tarbiyya a gurin Tahir?
Shi din wanda kike abin a dominshi tarbiyyar ce da
shi? Ina so ki tina idan ma kin mance ne rashin tarbiyyar da
mutumin nan ya gwada mana tun daga farkon haduwarmu.
Eh na yarda ba kuma na ce tarbiyyar ce da shi ba, to amma
rashin tarbiyyar tasa ta kau na wanda kike hankoro a
kansa ba, har ma kike kokarin bata ran iyayenki a kan
kawai da namiji da ba shi da tabbas.
fanimec Na ji dai duk dai abin da za ki ce na kuma
ki na kuma gane matsayina a gurinki, domin ke munafuka
ce, ne fuska biyu, mara son farin cikina, A baya kina nuna
goyon bayanki ga Tahir a yanzu kuma kin sauya daga wata
fuskar, to ki ji ki sani, ke din nan baki isa sanya ni na canja
abin da nake so ba. Fice ki ba ni waje, ba ni ba ke kar ki
Kara zuwa inda nake duk me so na dole ya so Tahir, duk
kuwa me kinsa dole ne na ki shi domin ni yake ki ba shi
ba.
Kwana daya kacal ya rage a daura aurenta tuni gida
ya cika ya batse da 'yan uwa da abokanan arziki, dangin
mahaifiyarta na Yobe da kuma dangin mahaifinta 'yan
usulin Dajin Falgore su suka fi kowayawa, ko da yake 'yan
Yoben sun bi sun kankane komai 'yan Dajin Falgoren ba su
da wani bakin fada a ji bare fa dangin Anty Na'ima da
matsayinsu baiw uce na 'yan karo ba, ko kuma 'yan kalan
dangi kamar yadda Hajiyan take fada.
Ba ta wani sa wa zuciyarta wani darua ba saboda
sanin abin da ta shirya misalin karfe takwas na dare Aunty
10
Na'ima ta yi kundumbala ta isa sashen Hajiya Kaltume,
kallon biyu ahun da hajiyan take mata be sa ta karaya ba,
haka nan 'yan uwan Hajiyan mutunta ta duk da dai babu
wanda ya isa zuwa sashenta saboda akidar Hajiyan, sai dai
fa in irin haka ta hado su su gaisa.
Sun gaisa cikin mutunci ta ce Hajiya ina son ganin
diyata ne? wa ke nan? Mardiyya ko mabruka? Ta san ta
fahirece ta amma kuma ta cillo mata wannan tambayar
Aunty Na'iman da take ma'abociyar kunya? cikin sanyin
jiki ta ce a'a ina nufini Heedaya. Tamke fuska ta yi in ce ko
lafiy a? Hajiya a tunanina mun zama daya abin da ya yi
Heeday shi ya yi su mardiyya don haka abin da duk zan
iya vi wa mardiyay ko Mabruka zan iya yi wa
Heedaya.nasiha ce irin wacce iyaye ke wa 'ya'yayensu
yayin da aurensu ya taso. Ta tabe baki au to ina ce wani
kinibibin ne. Kwala mata kira ta yi, ta dube ta ki je Na'ima
na son ganin ki, ita din ma wani duba ta yi mata na nuna ba
ki isa ba. Haj. iMariya yayar Haj. Kaltum ce ta daka mata
tsawa ba da ke ake magana ba ne?
Ranta a bace ta dube ta bayan da suka isa dakinta,
in ce ko ba wani abun kika kara kullowa a tsakanina da
Dady ba? (Haka Hajiyan takemusu wannan hudubar, don
cusa kiyayyar abokiyaı zaman nata da 'ya'yayenta).
Zauna mana. Aunty Na'iman ta fada, ko kusa ko
alama babu alaınun bacin rai a tare da ita, abin da ta
Kudurci yi za ta yi shi ne domin Allah, tana zaune da su ne
da zuciya daya haka na za ta iya yi musu komai albarkacin
mahaifinsu, vana iya bakin kokarinsa wajen kyautata mata,
abin da ke guda a tsakaninsu ta sani bayin kansa ba ne, sai
11
dai har kulum ta kan kasance mai shedawa Sarki Allah ba
tare da zargin kowa a zuciyarta ba.
Ta fara yi mata nasiha a bisa wajabcin bin iyaye,
Allah Subhanahu wata'ala ya umarci 'ya'ya su yi wa
iyayansu biyayya, biyayyar Ubangiji yana daga cikin
biyayyar iyaye, sabawa Ubangiji yana daga sabawa iyaye.
Albazzari ne ya rawaito.
Haka nan Manzo (S.A.W) ya fada mana cewa,
“Wanda ya riski iyayensa guda biyu ko daya daga cikinsui
kuam bai yi biyayya a gare sup ba har yamutu, zai shiga
wuta." Sai Annabi ya ceс, "Ки се Аmin." Sai muka ce
Ameen. Hassan bin Malik ne ya rawaito hadisin.
Manzo (S.A.W) ya umarei iyaye da su kasance
masu aurar da `ya'yansu da za6a musu mazaje nagari ga
macen da take budurwa (wacce ba ta taba aure ba). Wannan
hakki a kansu ya rataya, kamar yadda Bukhari ya raiwato.
Yana daga cikin hakkin iyaye a kan 'ya'yansu su sanar da
su littattafai kuma su kyautata sunayensu, kuma su aurar da
su bayan sun girma.
Bayan hadisin Manzo (S.A.W) da suka yi maagana
a bisa wajabcin biyayya ga iyaye akwai kuma wuraren da
Allah (S.W.T) ya yi bayani a cikin littafi mai tsarki
(Alkur'ani) a wurare da dama, misali aya ta 15 a cikin
Suratul Ahkaf.
Don haka ina yi miki nasiha ki bi umarnin iyayanki,
bijircewa hakan tamkar bijircewa umarnin Allah da
Manzonsa ne
Maganganunta sun ratsa ta, zuciyarta ta raunana,
har ma ta takara daga bijircewa iyayenta da ta so yi. Ba ta
12
taba jin kaunar matar ya kama ta ba irin na yau, domin ta
fitar da ita daga cikin halakar da take kokarin jefa kanta.
Wai shin menene dalilin da ya sa suke nuna
kiyayyarsu ga matar? Sai kuma ta tuna mahaifiyarsu ce ke
kokarin cusa wannan akida a zukatansu a ko da yaushe.
mata Cikin yanayin kuka ta shiga bayyana
kudurinta, da sauri ta ce A'uzubillahi, kai amına kuwa da
kin yi kuskuren da zai ta bibiyarki mutukar ba neman
afuwar iyayenki kika nema ba. Ki yi hakuri Heedaya shi
lamarin aure haka yake, ni din nan inda zan ba ki misali a
kaina za ki yi mamaki, to amma da yake ga wanda Allah ya
kadarto shi ne mijina cikin kankanin lokaci komai ya
wargaje, to amma da na yi hakuri ba ga shi har Allah ya
albarkace mu da samun 'ya'ya.
Kuka ta saka, lallai kam Aunty Na'iman ta yi
gaskiya, a ce abin da za ta sakantawa iyayenta da shi ke
nan? Duk da kulawar da suka nuna mata cinta, shanta,
fitsarinta, kashinta, kai da ma komai nata su ne.
Ta yi hakuri ta karbi zabinsu to amma fa wanda a
kai abin a domin shi zai fuskanci masifa da bala'i da tashin
hankali kala-kala, don ba za ta taba kaunatarshi ba, ya riga
ya gama da rayuwarta, ya yi mata babbar illar da har ta
mutu ba za ta taba mance shi ba. "Waheed! Waheed! na
tsane ka sam ba na kaunar ka. Tahir kai nake so, ni kai
kadai nake kaunata." Ta furta hakan a zuciyarta.
Misalin Karfe goma shwa biyu na dare wato
wa'adin da suka yanke za su gudu a di-dai lokacin shirushiru ba Heedaya bayan sun riga sun gama shirya koma,
duk ya bi ya damu ya kagauta kada wani abu ya kawo
musu cikas, wanda hakan ke nufin ya rasa Heedayansa.
13
"Never." Ya furta hakan da karfi, "Heedaya ba ta kowa ba
ce face Tahir dinta.
A dai-dai lokacin ne sakon ta ya shigo ta hanyar
text message. Cikin sauri ya shiga duba sakon. Wani
mahaukacin ihu ya saka game da cilli da wayar,
"Heedayah! Heedayah!! Haka za ki min? me ya sa za ki yi
min haka bayan kin san ke kadai nake so, ke kadai nake
Kauna, never, never, Heedaya ni ne mijinki ba ki da wani
miji face ni Tahir.
Kirjinshi ne ya ba da wani dam lokacin da ya tuna
da babban kalubalen da ya shafe komai, "Waheed!
Waheed!! no... no...,. wallahi karya kake." Gaba daya ya
hauka ce sai kuma ya ja motar cikin wani irin gudu na
masifa ya fice ya bar unguwar.
Zubewa ta yi a kasa kuka take me tsuma zuciya, tun
farkon zuwansa har kawo tafiyarsa a kanidonta ne, wayyo
Tahir kai nake so babu yadda zan yi ne sai kuma ta zube
bayan da numfashi ya shiga gagarar fita.
KARSHEN TIKA-TIKI-TIK
Wayewar gari ne afkuwa ta afku, misalin karfe
goma na safiyar ranar lahadi aka daura auren Engineer
Abdulwahced Gen. Abdullahi tare da Barrister Heedaya А.
Sa'ad. Daurin auren da ya hada gaggan mutanke daga ko
ina a ciki da wajen kasar. Zuciyar angon in ta yi dubu ta
baci, haka nan amaryar babu wani walwala ko nishadi а
tare da su.
14
Da yammacin ranar ne General Abdullah ya umarce
shi da ya je gidan Ambassador ya yi gaisuwa da kuma
godiya a bisa karamcin da ya yi musu (wato kyautar 'ya
sukutum). Babu yanda zai yi kamar yadda be isa ya ja da
batun mahaifinshi ba ya fi kowa sanin shi ba kanwar lasa
ba ne, ba kuma a kawo mishi wargi bare ya juri dauka.
Ransh. a bace babu wani annuri a tare da shi suka isa gidan
tare da Jamir, yau dai mutumin nasu ba ya nan domin yau
aikin safe va yi.
Tsa utsayi ne ko meye ba sai idanunshi ya gane
mishi ita ba sun jero kafada da kafada da abokin adawarsa
(Tahir) za u shiga mota, kai sai idanunshi ya shiga gane
gane mishi abin da ba haka nan ba ne, ta gabansu suka zo
suka shige a cikin mota ko kallo ma ba su ishe su ba duk da
cewar sun san da su din a wajen, abin ya yi mutukar kona
zuciyarshi, hannunshi ya fisgo, taho-taho mu bar gidan nan
na fasa zuwa gan da uban nata, idan Dady ya tambayi dalili
sai ka sheda masa. Haba wannan 'yar iskar yarinyar marar
tarbiyya ake neman kakaba min, wallahi an cuce ni, an
cuce ni, wallahi muddin ba a yi gaggawar janye auren nan
ba za su yi kuka da idanunsu domin zan 6a66alla yarinyar
mutane ne a banza a wofi. Yarinyar dan iskan mutumin nan
ce fa? Wallahi an cuce ni, na fada na kuma fada hadin sam
be hadu ba dama dai-su kwance wannan hadin domin shi
ya fi alherі.
Shi, kansa Samir din ya yi tsai yana nazarin
magangarunshi, lallai kam akwai tarin rikici a cikin
wannan aure, anya ma ko yarinyar tana da tarbiyya? Kamar
yadda abokinshi yake zargi, yaro me tarbiyya dai ba zai yi
haka ba, ko da yake ya fi ganin laifin iyayenta, don menene
15
za su bar ta zuwa wurin mutumin da ba muharraminta ba?
har ma su fita? Alhalin da igiyar wani a kanta.
Duk dai da rashin hadin kan amaren yadda ya
kamata, an gudanar da gagarumin biki na kece raini daga
kowane bangare, a ranar da za a kai ta ne ta gurfana a
gaban mahaifinta tananeman afuwarsa a bisa turjiyar da ta
gwada musu, kuka take me tsuma zuciya tare da bayyana
nadamar rashin da'ar da ta yi musu.
Jikin Ambassador ya yi sanyi yau dai ga ranar
rabuwa da `ya mafi soyuwa a duk cikin yayansa. Cikin
tausasa harshe ya shiga yi mata nasiha tare da bayyana farin
cikinsa a bisa biyayyar da ta yi musu, a karshe ya sakamata
albarka tare da fatan alheri, ita ma Hajiyan ta tofa
albarkacin bakinta cikin karayar murya.
An fara kai amarya gidan iyayen mijinta da ke cikin
Nassarawa G.R.A. kan titin Tukur (Tukur Road). An yi
musu karbar girma da karamci, daga nan a ka wuce da
amarya gidanta da ke Badawa Layout Linck daura da titini
Sardauna Creasent. To fa tashin hankalin a nan yake, kuka
har da kururuwa da haka har aka watse aka bar ta da babbar
aminiya Sameera, ita din ma ta yi iyawarta kukan ne dai ba
ta fasa ba jikinta duk ya yi sanyi saboda tausayawa yar
uwarta, ta sani ba abu ne me sauki ba raba ka da abin da
kake kauna farat daya, a kuma kakaba maka abin da sam
ba ka son sa ba ka ra'ayin sa ba ka ma kaunar sa baki daya.
Duk da cewar angwayen sunshigo amma kuma
hakan be sa ta tsagaita daga kukan da take ba, su kamar
biyar ne duk da dai babu angon a cikinsu, sharif, mahbub,
yassar, yazid da kuma shugaban tawagar babban aboki
Samir, to fa suka fara tsokanarta ke ko an daina wannan
16
yayi kar ki ba da mu mana. Cewar yassar. Kai ko tsiyata da
kai ba ka da saurin fahimta baka san gulmar mata ba ne? ai
duk wanna kukan na farin ciki ne. Yazid yaba shi amsa.
Wai haka? Wai haka amaryarmu? Shi kuma
mahbub ya fada yana zolayarta. Bari mu gani hakan ne? in
dai hakan ne za ta daina yi mana kukan nan koma sami
damar siyan bakin amarya. Ai ko ta kara rushewa da kuka.
Yana daga gefe sai faman dariya yake domin shi ya
fi kowa ma zolayarta kai ku tsaya, ku tsaya ni na ma gano
ko kukan menene bari ku ji ba kukan komai ba ne face na
rashing anin angonta. Ah! Lallai kam dukkansu suka dauka
cikin sowa da. tafi tare da fadin, lallai kam samir ba
karamin tsinkaye ka yi ba da har ka gano mana lagonta. Ya
ce ku tsaya akwai sauran rina a kaba, domin angon namu
mai tsada ne, ke kawar amarya saiki miko kayan sayen
bakin ango muddun da gasken kuna son ganin angon naku.
Dama dai yasha zamansa, domin bamu da
muradinsa cewar Sameera. Ah karya kike, wayo ne kawai
dan kada ku ba mu kudin siyan bakinango, mu ko mun kiya
domin angon namu mai tsada ne. cewar yazid da alama shi
ya fikowa barkwancin idan ka cire samir din suka dada
rikita ta sai faman kuka take lallai kam inda yake mugun
mutum haka ma abokanansa suke.
Ya rissina a gabanta ya dan janye gyalenta yana
dariya yana fadin bari in fanshi ango in sai bakin amarya
tun da kawar amaryar da ma amaryar duk marowata ne. ta
kara rushewa da sabon kuka. Dariya ya saka gami da fadin,
yazid tuna min wakar nan da makadan sudan din nan ke wa
amare, yauwa, yauwa na ma tuna: “Amarya ce, amarya ce,
amarya. A sama ta lalle." Suka amshe, "Amarya!". Ya
17
ci
gaba in ta ki ta zauna, suka kara anshewa amarya, a kira
mata