komai sanye take da farar T.Shir hade
da shudin siket din jeans kanta babu dankwali ta saki
gashinta domin dai ba ta da karfin da za ta iya gyara shi, sai
ta hada ta cukwikwiye shi ta kanannade shi ta cusa tamkar
dai nadin gammo.
Fuskarta babu komai bayan powder da ta fan shafa
ta kasa aiwatar da komai saboda hakin da ya dame ta, ya
shigo rike da katon tray a hannunshi sanye yake da riga da
wando na jeans ta dube shi sai kuma ta kautar da kai, ina
kwana? Karan farko ta gaishe shi, ya amsa mata, kin tashi
lafiya? Ya ku fan jiki? Be jira amsarta ba ya shiga kokarin
harhada mata brcak. Ya fara da miko mata ruwan tea. Ba
da son ranta ba ta karba, don dai babu yadda za ta yi ne, ba
ta gama ba ya shako mata plate da 'Burger Bread (hadin
biredi mai nama) hade da chips&baked beans (hadin
soyayyan dankali, kwai da kuma waken gwangwani) gefe
guda kuma ga ruwan tea nan a flask, ta hada fuska kamar
za ta yi kuka in ban da keta ya za a yi ta iya cin wannan
abincin? Sai ka ce wata jaka? Tana ji tana gani ya matsa
mata sai da ta ci kusan rabi. Kamar ta ce kai ba ka ci ba sai
kuma ta tuna meyè damuwarta? Cikinsa ko nata?
Ta ja Drower ta dauko magungunanta tab torasına
tare da Erythromyan tablets. 500m6 wanda yake dauke da
vitamins da minerals akwai bukatar mai wannan ciwo ya
dinga shan magungunan da yake kawo lafiyar jiki.
Tana shirin barewa ya ja hannunta ya rike, menene
wannan za ki sha? Ya dube su da kyau, sannan ya miko
mata za ta kai ruwa bakinta ya dakatar da ita ki bar shan
74
ruwa mai sanyi, tsiyayo ruwan dumi ya yi dakecikin flask
ya mika mata, sai da ya tabbatar ta sha sannan ya watso
mata tambayar daman kina da Asthma ne (sanyin kirji) ko
da yake, tun jiya ya fahimci hakan, kai ta dagamishi, shima
kan ya girgiza, amma ko kina shan wuya wannan ciwo kam
akwai wahala, wallahi haka nake ta fama in ya tayar min
kamar ba na kai ba.
Lallai kam na yarda da hakan, jiyan nan fa na
tsorata ainun, wallahi ban yi zaton za ki wayi gari yau ba, ta
dan saki fuska, haka momy take cewa duk lokacin daya
tayarmin, gaskiya kam ciwon da yake kokarin tafiya da numfashinka, ai ko akwai hatsari a cikinsa.
Yanzu dai maza shirya mu je asibiti, na tsorata
wallahi. Mika mishi ta yi ba ma sai na je ba, wadannan
magungunan ma da na sha sun wadatar. Ya dube ta da sauri
da Allah tashi mu je yaushe zan bari mu kara kwana a
haka? Zuwa na da rashin zuwana duk daya ne ko na je din
abin dai za a yi min magungunan ke nan ga shi kuma ina
sha.
Be kara ce mata komai ba ya fita, zuwa wani lokaci
ya dawo kintso sako hijabi ga Doctor nan ya zo duba ki. Ta
dan 6ata rai alamun ba ta so hakan ba. Ke nake jira. Ya ce
mata. Mayafi ta dauko ta yafa tun da ita ba ta da hijabin da
ya fada.
Kallo ya bi ta da shi ba haka dai ya so ba, to amma
dan dai ta je din sai ya kyale ta, sai dai yana jin wani irin
abu a zuciyarshi,. gaba ya sa ta kamar Raramar yarinya.
Sun gaisa da likitan ta shiga yi mishi bayani yadda
ya dace ya kuma gamsu da magunguna da take sha.
75
Ya dube shi shike nan babu wani abu da za ka yi?
Kafadarshi ya dafa kar ka damu abokina na aminta da
magungunan da take sha, na kuma aminta da likitan da take
gani.
Dr. Samuel kwararren likita ne a I.D.H. (Infectious
Disease Hospital). Babu kamar shi a duk fadin jihar nan a
fannin cutuka masu harbuwa (infectious diseases). To haka
ya ci gaba da jinyar ta har zuwa lokacin da ta wartsake ta
koma bakin aikinta. Zaman nasu muna iya cewa ya fi na da,
yana ba ta kulawa gwargwadon hali ita din ma babu lefi ba
dai kamar shi ba. Ya rage abubuwan da yake yi na rashin
kyautawa, yawan dare, caca da sauransu, duk ya dan ja da
baya da su,"yakan yi kokarin zama a gida, duk da rashin
kulawar da ta dace da ya gaza smu, ba dai ya damuwa.
Kamar ko yasuhe ya dauko ta daga wurin aiki, ya
karya kwana zuwa Gwarzo Road. Ya yi parking a harabar
Jujin Labu Store. Ya dube ta, zan sami rakiya? Ta gintse
fuska ka je kawai, ta lura da kyau a 'yan kwanakin nan
yana zuwar mata da wani sabon salo be sani ba a duk
lokacin da ta dube shi takan tuna da yankan kaunar da ya yi
mata, ko da ya yi mata wani abu na kyautatawa wannan abu
yakan share komai har ma kiyayyar nan tasa ta motsa mata.
Ba za ta taßa amince masa ba har abada domin ya gwada
mata cin amana, ya ma gama da rayuwarta.
Be dai damun ba ya fice to ki jira ni ba jimawa zan
Viba-tun-da an ki a yi min rakiyar. Dada hade fuskar tayi
koya kula domin yana cikin wani yanayi ne me kama da
zumudi.
76
Kudin ne ke masa kaikayi ko menene? Sakamakon shopping da ya yo kusn cikin but guda duk da dai akwai
amfanin kayan gida a ciki.
Ki yi hakuri na dade ko? Ta ce uhm, ya tashi motar
yana tuki yana dan jan ta da hira amma ta ki ba da hadin
kai, kamar ko yasuhe.
Kowanne sashen sa ya nufa ta yi wanka ta kimtsa ta
shafe jikinta da Ivana Cream man da aka yi shi da ganyen Alocvera ganyen da yake gyara fata.
Powder (Gervenne) kawai ta shafa sai man sanya
lebe sheki (wait lips) ga shin nan nata ya sha gyara sai
sheki yake, sanye take cikin fararen riga da wando me tsayawa a iya gwiwa sakar kasar Indonisia.
Ta yi kyau ainun ita kanta ta san ta hadu har ma ta
haďe. Tana haramar farewa gado ya turo kofa ya shigo, ta
mance ma ba ta saka key ba hannunsa rike da kaya nikiniki ya yi ta fiddo su yana jibge mata. Yawancin kayan
shafa ne (cosmetics) da kayan kyale-kyalensu na mata, sai
kayan kwalam tun da ya san ita ma'abociyar zaki ce.
Daya bayan daya ya bude mata ta kuma yaba da
kayan musamman bangaren kayan bacci (sleeping dress)
sai dai ta ki nuna hakan a idanunta. Har sai da ya ce, ke in
an miki kyauta ba kya gode wa ne? wani? ban dauka nawa
ba ne, to an gode. Ya dan murda bakinta, to da na wanene?
Akwai wanda ya dace na bawa wadannan kayan nan bayan
ke matata. Ya fada cikin wata siga.
Ranta ya yi mummunan baci sam ba ta kaunar ya
rabi jikinta, sararshi ke nan a 'yan kwanakin nan. Kuma
meye zai zo mata daki cikin daren nan, tashi sai tsam ina
zuwa, harara ta bi shi da shi dama dai kar ka dawo ya fiye
77
maka. Ya kuma fiye mini, ba ta jin bacci ya yi kawai ta saki
music cikin DVD Kirar Laptop. iri Ita daman kallace-kalace be dame ta ba kowa ne
ne in fa ba kade-kaden turawa ba, to a nan fa gwana ce.
muna iya cewa ba ta da na biyu a wajen sauraron kade
kaden turawa.
Awnnan karon akaset din zabiyarta ne 'Shakira
cikin wakarta ta Hips Don't Lie' kishingida ta yi tana
sauraro, domin ba ta cika ma kallon ba ita dai ta ji sautin
waka, ko dayake ba ta cika son aikin wahalar da kai ba,
zuciyarta ta yi kal, tana jin wani irin nishadi, idanunta a
lumshe suke so take kawai ta ji karkarar madara a
makoshinta (Ice Cream) domin dada sanyaya zuciyarta.
Idanunta na lumshe tana bin wakar ya shigo rike da
cups da plate a hannunshi, daddadan kamshin turaransa ne
wato ya sanar da ita isowarshi, buda idon da za ta yi sai ta
gan shi cikin yanayin da ba ta taba ganin shi ba, sanye yake
da sleeping dress sakar kasar Indonesai, (Kasar Indonesia
gwana ce wajen saka kayan baccі).
Wandon iyakacinsa tsakiyar cinyoyinsa, haka nan
rigar budaddiya ce, shatin kirjinsa gaba daya a bude yake
sai dan wan yanki da ya hafa rigar wuri guda, ma'ana aka
kulle haskenshi ya dada fita kyawun nan nashi na jinsin
Shuwa ya dada bayyana kabilar da ake danganta ta da
jinsin Larabawa, gashin nan nashi ya kawanta gwanin ban
sha awa baki wuluk, shi daman dukkanin gashin da ke
jikinsa daga na ka har zuwa na idanunshi, girarshi da ma
jikin sa baki daya gazar-gazar ne sai dai kuma ba su da
karfi, hakan ne ya ba su damar kwanciya gwanin ban
sha'awa.
78
Zumbur ta yi ta mike har ma ta so ba shi dariya,
na dauka ka tafi mun ma yi sallama sai da safe, to
meye aibu dan megida ya dawo wa matarshi? Ta gimtse. To bari dai in juya da tsarabar da na zo miki,
tun da ba a maraba da bako. Ya dan yi mata nuni da
shi zuwa bakinta, ta dan saki fuska, game da jin wani
sanyi a zuciyarta, idan dai tsarabar ta gaskiya ce (ta kai
zuci) ai sai a bawa wanda a ka yo tsarabar domin shi,
ya ji dadin kalamanta ya sami wuri ya zauna gefen
gadon dab da ita yana gani ta yi kokarin janye jikinta
cikin dabara, miko bakinki in san miki. Ya debo Ice
cream din cikin cokalin shan shayi (Tea Spoon). Ta
kau da kai in dai za a ba ni a bani, in dai kuma ba son
rowa ba ne. kumatunta ya janyo duka biyun da
yatsunsa, babba da dan tsakiya sai kuma ya kwantar da
kanta jikin kafadarshi, ya shiga dura mata, sha take a duk
laokcin daya zuraro mata tana jin tun da take ba ta taba
shan ice cream mai dadi haka ba, ko ko ita ce take ganin
hakan? Tun yana tsiyayo mata da cokalin har ya matsa
bakinta yana tsiyayo mata da bakin cup din, tar
jin wani irin sanyi har cikin makoshinta. Yana gab da c.n
lagonta zuciyarta ta shiga gargadarta kada fa ki manta shi
ne fa mutumin nan da ya ci amanarki, ya keta alfarmarki ya
ma kawar miki da abin da kike takama kike tunkaho.....
bayan ko ba shi ya dace da wannan matsayi ba....
furuce-furucensa.... kin da nake miki ya shallake turanin
dan'adam, ki ji ki sani kiyayarki a jinina take, shashasha
yarinya mara tarbiyya. 79
Haka fa ya ce mata wai ma me ke damunta ne? ina
alkawarin su da Tahir yake? Wane ne Waheed?" meye
matsayinsa a rayuwatta? Gagarumin makiyinta, ta bawa
kanta amsa.
Wani irin karfi ne ya zo mata ta ture shi guri guda
yarude ya kidime yana lallashinta, tsawa ta daka mishi, Na
tsane ka, na tsane ka Waheed, sam-sam ba zan taba son ka
ba, muddun ko kana tunanin hakan ka ko yi kuskure.
Ya marairaice haba Heedaya ki bar fadar haka ina
son ki, ina kaun.... ta datse shi ka yi gaggawar kuskure
bakinka daga wadannan kazaman kalmomin da suka fito
daga bakinka. Nufo ta dai ya kar ayi yana neman afuwarta
a lokacin da ya yi kokarin cakumo ta. Ta yi kokarin daka
tsalle ya tsa ta nuno shi da shi bari ka ji, da na kwanta da
kai gwanda mutuwata, saboda kiyayyar da nake maka, na
tsane ka! Na tsane ka!! Ba zan taba son ka ba Waheed.
Tahir nake so, Tahir nake so shi ne zabina shi ne ra'ayina
shi ne kuma wanda zan iya sadaukar da zuciyata, rayuwata
gami da gangar jikina ba ki daya, kar fa ka macne Tahir ya
ba ka amsa, kana ganin ka mallake ni ne kawai, amma
zuciya gami da gangar jikin baki daya tana ga abin
kaunata Tahir, ko a yau ka sake ni zan je in auri abin
Kunata Tahir mu ci gaba da ni'imtawa junanmu
rayuwarmu...
Mari ya sakar mata ya kuma kara sakar mata tsuma
yake kanar ya ci babu, ke da Tahir din kun ci kaza-kazan
ku, ya shiga ashariya ni za ki gwadawa iskancin banza da
wofi 'yar iska mara mutunci mara tarbiyya kar ki dauka
wai so ne ya janyo min haka, a'a sha'awa ce kawai domin
80
daman amfaninki ke nan shi ne ma dalilin da ya sa na
hakura na kasa yakice bakar kafa, to amma yanzu na
yinazari na gane sam-sam ma ba ki dace da wannan
matsayi ba, za kuma ki gane hakan ne yayin da na nuna
miki ke ba wata tsiya ba ce a wajena ke kuma da auren
Tahir fin har karshen rayuwarki, saki dai ba a hannuna
yake ba to na ga ta yadda za a yi shi, duk kuma ranar da na
kara jin kin ambaci banzan yaron nan a gabana saina
targada ki, stupid girl. Ya fada ya kuma fice cikin fusata.
Muna iya cewa zuciyarshi ta fi wuta kuna sakamakon cin
zarafin da kankanuwar yarinyar ta yi mishi.
Kai tsaye mashayarsu ya wuce, wurin ya cika ya
batse ya'yan iska masu caca na yi masu shan kayan maye
na gefe wasunsu kuma suna cashe rawa da 'yan matansu,
wasunsu kuma ba rawar suke ba suna kebance a gefe.
Samir na daga rukuninsu yana tare da yarinyarsa
Lancy 'yar kabilar Ibra daman dai a nan ya fi kauri, ko da
yake be cika jumawa da yarinya ba, da ya yi sabon kamu
shi ke nan sai ya watsar da ke.
Yana hango shin be nufe shi ba sai ya nufi bangaren
caca, inda ya fi gwanancewa ke nan, fuskar nan tashi babu
walwala bare lumana, kallo daya za ka yi mishi ka tabbatar
yana cikin matsanancin bacin rai.
Kimanin awa daya suna bugawa kamar dai ko
yaushe shi ke da nasara, ta tawo da baya da baya ba tare da
ya sni ba ta saka hannayenta ta sakalo kirjinta ta hado shi
da jikinsa, yajuya da zummar cin mutunci ko wacece dan
ba ya ra'ayin kadangarun barikin, a dai-dai wannan lokaci,
laifin mace daya ya hada duk ya shafe su.
81
Ya buda baki da niyyar magana harshe ta zira mishi
take ta mantar da shi duk wani bacin rai da yake ciki, kamr
yadda ta saba Farida sabuwar yarinyarshi da take mutukar
Kaunarshi, ta juri wulakanci da halin ko in kulan da yake
gwada mata, har zuwa yanzu da ta yi amannar ta riga ta
gama cin lagonsa har ma a yawancin lokuta shi yake neman
ta.
Yana rike da Kugunta suka shige ta gabansa harara
ya sakar ınasa, shi ma hararar tasa yake, yana jin wani irin
takaici a zuciyarsa, ji yake kamar ya tashi ya shake shi.
saboda zalunci ya bar yarinyar mutane ya taho gurin
Kadangarun bariki.
Yakan ji wani irin faci a zuciyarshi a duk lokacin
da suka hadu a irin wuraren nan, tun bayan aurenshi, a da
kan shi ne ke musu jagora a yanzu kam akwai rashin
dacewar zuwansa yana jin cewa duk ranar da ya yi aure ya
bar wannan harka.
Lamcy ta shiga hilatarsa, tsawa ya sakar mata kama
gabanki da Allah malama, ba na ra'ayinki, wani banzan
kallo ta sakar masa, a'a ka ce dai wulakancinka ne ya
motsa, to ka sani na fi karfin a wulakanta ni zaka zo da
Kafarka kana nema na. dauke kai ya yi tana ta masifar ta
har ta yi ta fice.
Karfe biyu dai-dai na dare suka fito daga dakin ya
nufo matattarar gefenshi Farida ce ta wani narke a jikinsa
ya hango shi yana yi mishi wani irin mugun kallo, ja ya yi
ya tsaya, jira ni Farida zan je wurin Samir, kona daki
kawai ina zuwa. Hannunshi ta janyo ta baya ta kas o bakinta
saitin kunnansa, abokin nan naka ya tsane ni, ban san me ya
sa ba. dan Allah kar ka bari ya zuge ka, ka guje ni.
82
Murmushi ya sakar mata, da kin san yadda kika kankane
zuciyata da ba ki ce haka ba.
Ya ja ya tsaya a kan shi sai kuma dai ya zauna yana
yi mishi irin kallon da shi ma yake mishi, aikin banza
kawai meye ne tun shigowata za ka dinga yi min wani
banzan kallo.
Kallon shi ya yi fuska a daure, ya ba shi amsa,
banzan ne kai so meye don na yi maka banzan kallo? Ni ne
banza?" ya fada cikin fusata, kwarai kuwa in ban da banza
waye zai bar matarsa ta sunan ya taho wurin kadangarun
bariki.
Murmushi ya fan saki, so na gane abin nufi dai
dukkanmu banzaye ne, abin da ya kawoni gurin nan
kazalika shi ya kawo ka, so meye maraba? Akwai maraba
kuwa, domin ni ban ajiye yarinyar mutane ba bare in
ha'ince ta, ajiya ka ce so ka bawa kanka amsa. Abin da
kawai zan ce maka shi ne ka ja kunnanta ka kuma gargade
ta shiga taitayina, wallahi wallahi ni din nan na fi karfin a
yi min wulakanci, har akwai yarinyar da ta isa ta yi min
wannan kaskanci har ma a nemi kaskantar da ni a kan wani
Kaskantaccen mutun da ban dauke shi a bakin komai ba.
fada yake sosai da sosai, danma dai da yake kowa harkar
gabanshi yake yi ga kuma sautin kida na tashi don haka
babu wanda ya san me suke eiki, ya lura dai ya fusata ya
harzuka ba ma yanzu ba, tun farkon shigowarsa ya lura da
Gacin ran da yake ciki. va Gan sassauta da Allah ya ishe ka
malam wai mene: shi kam ya kasa fahimtar inda
zancensa ya dosa, ciza lebe ya yi cikin kunar rai ya labarta
mishi iya abin da yake ganin zai iya.
83
Shiru ya yi yayi tsit yana jinijina lamarin, gaskiya
kam ba ta kyauta ba, to amma dai ya gwada gajen hakuri,
Kila da ya bi ta sannu ahankali, wata rana sai su daidaita.
Abin dake cutar ka zuciyar nan taka, ka cika saurin
yanke hukunci, dan menene ba za ka yi hakuri, ka shawo
kanta sannu a hankali ba.
Ya ishe ka malam ba cewa na yi ka lalubo min
hanyar da zan samo kanta ba, ita wace ce? Na riga na gama
da ita na ma yasar da ita baki daya, sharar gidana sai ta fita
daraja, za ta gane cewa ni dìn nan na fi karfin a kawo min
raini da wulakanci, yar iskar yarinya mara tarbiyya.
Ai kai tarbiyyar ce ya sa kake fadin wafannan
mugayen kalamai a kanta? Aikin banza ma'malam ka je ka
yi duk abin da kake so, kar Allah ya sa ka daina ya fice
gami da jan tsaki.
Kuka take haikan, zuciyarta ta riga ta gama tukewa
da kiyayyar ınutumin. ya gama da ita ya cuce ta ya gama
cutartaba ta dada tabbatar da hakan ba sai yau.
SABON SALO
An Shiga sbaon salo a yadda zainan nasu ya kaya,
domin ba mu san wane iri za mu kwatanta shi da shi ba, shi
dai ba a ce zaman doya da manja ba, ba a kuma ce zama ne
na nuna halin ko-in-kula sai dai muna iya cewa zama ne na
rashin arziki da rashin ganin kimar junansu. Kowanne na
tatawa dayansa rashin arziki nau-nau'i babu mai ragawa
dayansa, to sai dai duk da hakan muna iya cewa ya fi
84
kuntata mata. Kai ta ma fi jin jiki a cikin sabon salon,
Karshen dai rashin arziki ke nan a shigo da mace har cikin
gidanta a kwana da ita ba kuma ya shayi ko shakkar ta, duk
da tana ikirarin ba son sa take ba amma kuma abin yana yi
mata ciwo, ai ko safwan din bilkisu da take kwatanta
halayyarsa da shi ba ya iya kawo mace gidansa, duk abin da
zai yi sai dai ya yi shi a waje. Amma shi ko saboda tsabar
rashin tarbiyya har cikin gidanshi yake kawo kadangarun
bariki.
Zaune take a falon ya dawo ko da tsammani ba ta
yi zaton zai dawo a irin lokacin ba, karfe takwas? Ina wane.
shi mutumin da sai cikin talatainin dare yake dawowa? Kila
dai akwai abin da ya dawo da shi.
Ya yi wanka ya kintsa ya feshe ya hade cikin suit
bakake, ya matse wuyanshi da blue neck tail. T.shirt din
da ke ciki ma blue ce, ya saka mudubin ido (Ronson glass)
agogon da ke hannun shi ma samfurin Ronson ne. Ronson
Bracelet watch) sajen nan nashi ya kwanta gwanin ban
sha'awa, ya zo zai shige ta gabanta ko kallo ba ta ishe shi
bha, zuciyarta ta kawo wuya tana jin wani irin bakin ciki
da takaici, wai me wannan mutumin yake nufi ne? ba ta son
sa ba za ta taba son sa ba, to wai zaman me take yi ne?
Karewar bariki mutum ya bi uwa duniya ma domin
yawan tambada, babu abin da ya shalle ni, be saurare ta ba
ya ci gaba da takunsa duk da ya san da shi take, kai ya ma
lura fitsarc-fitsaren na yarinya ya karu a 'yan kwanakin
nan, ba ta sani ba shi dai-dai da ita ne.
Ta ga ba shi da niyyar sauraron ta ya mai davita
banza ke nan, ja ta yi ta tsaya a gabansa, ta rike kugu,
malam zaman kaddararren gidan nan ya ishe ni, na gaya ma
85
ka ko sallame ni in tafi gurin mai kaunata, na gaya maka na
Kara gaya maka ba na son ka, ba na ta'ayinka, ba ma zan
taba son ka ba.
Wani kallo ya sakar mata na raini. kin kwa taimaki
kanki, abu daya ya rage ki Karasa taimakar kan naki wato
ki je ki sanar da iyayanki su janye wannan aure, kin san ba
ni na gani na ce ina so ba lika min aka yi da karfi da yaji.
ga shi ni kuma ina da da'a da tarbiyya ke ko da kika rasa
wadannan abubuwa kina iya tarar su ki bayyana musu
ra'ayinki, kuma ki bijire duk da za ki iya, tun da kin rasa
da'a da tarbiyya wannan abu ne mai sauki a gurinki, shi ke
nan kin ga sai ki je ki auri abin kaunarki, idan bai riga ya
gama yayinki ba, kin san kullum sababbin mata yara masu
jini a jika 6arkowa suke sai wacce ka gani ka yi ra'ayi ka
kuma za6e ta. Tsakaninmu da ku kin san babu batun so
balle a kai ga Kauna sai dai ko mu kore sha'awarmu.
Wayyo Allah, wayyo Heedaya rasa abin da za ta ce
masa ta yi sai kawai ta barke da kuka, Allah ya isana A Hah
ya isa na-mugu kawai. Ni ma haka Allah ya isa, Allah ya
isa muguwa kawai da ta yi saken da har aka hada ni da jan
gwwan-gwam. Ya Karashe maganar da kwaikwayon
muryarta yana dariya.
To irin haka ta sha faruwa a duk lokacin da ta takalo
shi abin ya kan kare a kanta, duk wani abu da ta san baya
so ba ya ra'ayi ta bi ta haddace shi tana kuma aiwatar masa.
amna ko a jikinsa, domin yana yi mata wandaya fi nata.
Wajen ya cika ya batse da kadangarun bariki.
gefenshi Samir ne da yarinyarshi Sera tun daman sh bai
cika dadewa da yarinyaba. Shi ko gogan sun zube a bar ana
86
ta faman karawa. Shi dai gwani ne ba a kayar da shi in dai a
kan wannan fanni ne, caca ba.
A kan idonshi suka shigo suka yi wa junansu
mugun kalllo, shi kansa faisal din gaisawa suka yi sama-
_ sama, saboda jin zafin abokinshi, natarshi ta sunan yake
nemanta, kai! ya gama da shi, komai zai mishi bai huce ba.
to sai dai abin da be sani ba shi Tahir din ya ma fi shi jin
zafinsa, kai jiya ke ma kamar ya sa wuka ya datse kan dan
iska, duk shi ya hana mishi ruwa gudu, babu Zeenatun babu
Heedaya yarinyar da ya fi kaunata, ya kuna kasa samun
hadin kanta, dan ko ita Zeenatun duk da ya san ya so ta be
wani damu ba can, tun da ya san ya gama da ita, ita ko
Heedayan fa? yarinyar da yake mutukr kaunata yake kuma
mutukar sha'awar kasancewarsu tare.
Ya gama da shi zai kuma ci ubansa a duk ranar da
ya shigo tarkonsa a duk bayan minti biyar yakan duba
agogonsa ya bi ya damu saboda rashin isowarta yana son ta
yana matukar sonta domin tana farantamasa fiye da
kowacce mace, a tunbayan Heedaya babu yarinyar da so
irin ta.
"Fareeda! Ina mutukar kaunarki." Ya fada lokacin
da ya hango ta ta yi ado ta cakare cikin English wears masu
mutukar nuna surar jikinbila'dama. Faisal na kallon shi ta
gefen ido yana sambatun Faridansa, shi kam tunbinsa yake
cikawa da ruwan barasa domin shi a nan ya fi wayo, duk da
cewa matan ma ana damawa da su, to sai dai ba kamar a
bar ba.
To sai dai a yau shi kansa Faridan ta tafi da
tunaninsa yarinya ce ta kere sa'a, kai ta ma shallake duk
kanin 'yanmatan da y ayi abaya har ita Heedayan da yake
87
kwakwarta har yanzu. Hakika zai yi matukar bakin ciki
idan sankaceciyar yarinyar ta subuce wa abokinshi muddun
ya mallake ta ta gama wanke masa takaicin duniya har ina
ya gama cunkusawa su o'o haushi, har sumutu ba za su
taba samun kamar Faridan ba. Faisal din ya fada ya ji wani
sanyi har cikin zuciyarsa, lallai kam hakika tun a yau din
nan zan fara gwada masa irin fintin kau fin da na yi musu.
Good abokina Faisal din ya fada.
Ta taho tana tafiya cikin rausaya da karairaya
duk mahalukin da ke wajen ta tafi da tunaninshi tun da
daman duk mutanen banza ne. Kai! yarinyar ta hadu fa
abin da suke fada ke nan, yayin da da dumfaro wajen.
Mikewa ya yi cikin isa da kasaita da nufin
nunawa 'yan adawa iyakarsu. Sai da ya zo dai-dai da
inda suke sannan ya ja ya tsaya, hannu ya bude da
nufin taryar ta wato ta shige jikinsa. Zururi ta shige ta
gefensa ta fada wurin mutumin da take mutukar kauna
ta, har ba ta iya kwatanta son da take mishi, akan shi
ne ta ji za ta iya barin harkar da take ta raya sunnar
Ma'aiki. A daya barin kuwa an bar shii da hannu bude
cikin matsanancin kunya da bacin rai, har ga Allah