ango. Suka kara amsawa arnarya..." ko kafin ya kara
cewa wani abun ta kawo mishi bugu da kafa tana fadin, "ya
ishie ka Samir wannan ma ai wulakanci ne aikin kawai
haka kawai ku dinga sa yarinyar mutane kuka. Dariya ya
saka a`ah, kawar amarya daga kuma ina wake amaryarımu
sai kuma bugu."
Kyale ta Samir abin 'yar taron dangi ce, cewar
yassar. Mahbub. Ya ce to ai sarkin yawa ya fi sarkin karfi
ko ya kuka ce. To fa ta ga dai ba ta da yadda za ta yi musu
sai ta ja bakinta ta yi shiru. Lallai kam kawarta ba karami n
ikin jidali ta shigo ba, yadda yake haka nan abokanan nasa
suke.
Misalin Karfe goma sha biyu da rabi ta ci kuka har
ta gaji, kowa ma ya watse ya bar ta, zuciyarta ta gama
dugunzuma da kiyayyar mutumin da aka yi kasassabar
hada su, lallai kam duk wanda ya yi wannan kasassa6ar
gaba kadan zai gano kuskurensa. Ta gama ta yadda za a yi
wannan zama da mutumin da take tsananin kiyayyarsa, har
abada ba ta fatan ta so shi sakamakon mikin da ya dasa
mata da ba zai taba gushewa daga zuciyarta ba.
Sai kuma kuka ya kwace mata lokacin da ta tunano
masoyinta shi ke nan an raba su, never, never wallahi Tahir
kai nake so kai kuma nake ra'ayin zama da kai nan da
lokaci kanknai zan dawo gare ka. Wannan aure kam babu
inda zai je balle ya kai, domin babu komai a cikinsa face
tarin rikici da fitintinu kala-kala, don haka ta gana shirya
wace za ta fisshe ta.
Har zuwa lokacin ba ta ji motsin mutum ba ba ta ma
damu ta ji din ba, duk da tsoron da ya cika zuciyarta
18
sakamakon tangamemen gidan da take ita kwal a cikinsa da
haka har bacci ya kwashe ta, ba ita ta farka ba sai safiya
misalin karfe bakwai da rabi.
Ta yi wanka ta kintsa zama ta yi zugum ta rasa abin
da yake mata dadi misalin karfe tara dai-dai aka
kwankwasa kofar ta. Kamar kar ta bude sai dai ta mike don
ta ga vanene. Dogo ne baki me manyan kofofin hanci
sanye yake da fararen kaya nau'in na masu hidima a hotel.
Ya russura yana gaishe ta cikin gurbataccen turanci.
sannan ya jiye katon tray da ke hannunsa ya shiga gabatar
da kanse, "Sunana Peter, ni ne me hidima da abincin gidan
nan. Muna maraba da zuwanki matar Oganımu, da fatan za
mu kasancc cikin farin ciki a tare da ke." Duk dai cikin
gurbataccen turancin ya fada. Wani kallo ta sakar masa sai
dai be kula ba ya sa kai ya fice cikin girmamawa. Ko kallo
abincinta be ishe ta ba, domin ba zaman cin abinci ta zo yi
ba, jira take ya zo a yi wacce za ayi, ko ta yi gaggawar bar
mishi gidan.
Misalin karfe goma dai-dai abinci na alfarma ya iso
daga gidan surukanta, shi din ma ba ta ci ba, domin duk
kanwar ja ce, zaman kadaicin ya ishe ta yunwa ta addabe ta
sai dai ba ta iya cin abincin gidan mutumin, gwanda ma
yunwa ta kasheta kowa ma sai ya huta tun da kowa ma ba
yá son ta an ma manta da ita kwata-kwata, wayewar gari
har kawo yanzu babu wanda ya tuntube ta ko ba a fada ba
daman ta san an daina son ta.
Gefin azahar kannan mijinta Lubuna da Lubabatu
suka iso gidan, a cikin katafaren falon nata suka same ta ta
yi zugum. Gwanin ban tausayi, kallo daya ta yi musu ta
19
gane su dan tsananin kama da suka yi da yayansu, ta dan
saki fuska barkanku da zuwa? Ya kuka baro Hajiyan?
Lafiya lau Antinmu, in ce ko kin tashi lafiya? Muna
can muna ta kokarinmu isowa da wuri don mun san antin
namu a yau gwauruwa take, ba ta dai fahimce su ba, lubuna
ta ci gaba da cewa, Mum tana gaishe ki ta ce a gaishemata
da 'yarta idan kuma da abin da kike bukata ga waya nan sai
a sanar mata. Iko sai Allah su kuma haka tsarin nasu yake?
Ta ayyana hakan a zuciyarta, gaskiya anti mun so a ce yaya
ya tafi da ke ashe wai kuan da wani case ne a nan ofis
dinkuhaba Antinmu ba sai a dau hutu ba. Ni kam ban ga
dalilin da zai sa kwana daya cal da aurena angona ya gudu
ya bar ni saboda kawai uzurin ayyukan ofis ba. Cabdijam
aikin me? Irin wannan time yana da mutukar mahimmanci
a rayuwar ma'aurata, har abada ba za su taba mancewa da
wannan lokaci ba. Duk dai in ji lubabatu.
Take ta soma fahimtar inda zancen ya dosa, ai
mommy ma ta so tafiyar nan da ke ta yi ta fadan ya hakura
da tafiyar har zuwa lokacin da za ku kashe case din da ke
ofis naku, to dan dai uzurin yayan babba ne shi ne ma har
Dady ya kyale shi ya tafi.
Ajiyar zuciya ta yi bayan da ta gama fahimtar
komai, kai! Ina ma ya wuce har birnin Sin ya yi zaman sa
muddun rai, da hakan ya fiye mata komai lallai kam ba
karamin hasashe ya yi ba na nisantar junansu, kila da tun a
daren jiyan an yi dan karamin yaki a gidan, domin ba za ta
taba yadda ta zauna da mugun mutumin ba don ba ta
kaunar sa ba ta ko kaunar ganinsa.
Zuciyarta ta yi fari tas duk wani damuwar da take
ciki ma sai ya gushe, fatanta ya zamanto cewa ya wuce ke
20
nan ita da shi haihata-haihata (lallai "KI" ya yi “KI”). Nan
da nan ta saki hankalinta suka shiga hira da kannen mijinta,
abincin ma da ta ki ci ta janyo ta ci ta yi kat abinta wanda
take ki din ba ya nan shi ke nan bakin cikinta ya gushe.
Shi dai daren angon tun a
ranar da za a kawo
amaryar ya yi bankwana da gidan dungurungum ya tare a
Hotel tare da abar kaunarsa Zeenatu cikin dan kankanin
lokaci ta kawar mishi da 6acin ran da yake ciki har ma yake
jin wannan aure shi da babu duk daya ne, nan da lokaсі
kankani komai zai zama tarihi inda zai maye gurbinta da
abar kaunarsa, Zeenatu me sanya shi farin ciki me gusar
mishi da 6acin rai.
Wayewar gari ya yi sallama da iyayensa da abis
zatonsu ya yi salama da iyalinsa ma'ana a gidansa ya
kwana tare da iyalinsa ba su san ba hakaba ne iyalin
nasama ba su saka shi a ido ba ballantana su san da tafiyar.
Ko da yake tafiyar ma kafin a yi ta ya fuskanci rashin
goyon baya daga gurin iyayansa, don dai sun san abu ne
mai muhimmanci daya riga ya fado a cikin lokacin, jinkirin
zuwan nasa ka iya sa su yi asarar abin da za a samu baki
daya, sai dai babu wanda ya san cewa da tsohuwar
budurwar tashi ya tafi ba sai fa babban aboki Samir, ko shi
din ma bai so hakaba, don dai babu yanda zai yi da shi ne.
A kullum ta Allah a kan kawo mata abinci na
alfarma daga gidan General duk da cewa a nan dinma
kukun gidan na iya bakin kokarinsa a duk safiya mommy
Fatima ta kan kira ta ta ji lafiyar surukarta, haka nan
kannan mijin nata suna mutukar daraja ta gami da debe
mata kewa sai suka zamo ma tamkar kawayenta, sun yi
21
sabo ainun a cikin'yan kwanakin da suka yi, hakan ce ma ta
sa ta kwantar da hankalinta ta yi kyau ta yi fresh.
Kimanin makwanni biyu ke nan da zuwanta gidan
wanda ya yi dai-dai da kwanaki goma sha uku da tafiyar
angonnata, misalin karfe hudu na yammacin ranar lahadi
suna zaune ita da su lubabatu a babban falon da zai sada ka
da sassan gidan falo ne mai kama da aljannar duniya dan
Kayatuwa sanye take da cotton lace mai mutukar kyau, ita
daman shigar ta ke nan ta sa leshi, leshin ma mai mutukar
tsada dinkin da akai wa leshin shi ya yi mutukar fito da ita,
babbar riga ce mai gajeren hannu (Bubu) da siket wanda
aka yi mishi dinkin zamani, kanta ba dankwali domin ba
al'adarta ba ce, illa gyara da gashin ya sha. Ta yi kyau
ainun.
Sallama suka jiyo yayin da dukkaninsu suka waiga,
ya kalle ta ta kalle shi sai kuma ya yi saurin kawar da kai
gami da tamke fuska, murna suka sa oyoyo Yaya barka da
zuwa. Barkanku dai in ce ko kuna lafiya? Yana tafiya ya ci
gaba da cewa, kawai kuma sai ku tare a nan ku bar mummy
ita kadai, saboda farin cikin wata? Ba su dai fahimci inda
ya dosa ba domin suna hargowar fairn cikin ganinshi ita
kam da a kai abin domin ta ta sani ta ma fahiinta, zuciyarta
ta kawo wuya be sani ba ta ma fishi tsanar shi kai ita ko
kaunar ganinshi ba ta son yi, don haka ne ta fauke tunanin
dawowarshi har ma ta kwantar da hankalinta. Anti ai si а
tashi a tari yayan naınu da alama dai antin namu akwai
kunya. Cewar Lubuna. Ta mursuye kamar ba ta ji su ba.
antinmu ki tashi mana yayanımu yana bukatar kulawarki.
Ta dan harare ta sai dai ba ta sani ba da gasken hararar ta
take, har ma da jin zafinta. dariya ta saka ni kam ina
22
mamakin antin nan namu ko mu da muke youngers ba za
mu yi haka ba. Cabdi jam, yaushe ma zan yi haka rawar kai
ma kawai ta ishi angon ke kila har ma sai na gundure shi,
cewar lubuna. Ta rasa yadda za ta yimusu kawai sai ta mike
suka hau sowa yauwa antin tamu haka muke so.
Daki ta shige abinta ta ma fare gado ta vi
kwanciyarta to sai dai fa ba bacci take ba, lalubo hanya
mafi, auki da za ta rabu da kallagaggen mutumin ta ke yi.
La'asar sakaliya ya kintsa ya fito sanye da bakin
trouser hade da farar T.Shirt wace a ka yi wa ado da fenti
me cuw an azurfa (silver colour), ya yi kyau ainum kamshi
ne kawai ke tashi a jikinshi da gani ka san yana cikin
kwanciyar hankali, akwai alamun hutu a gare shi, babu
alamar walwala a tare da shi ya ce idan kun gama kintsawa
ina jiran ku. (Da yake momin ce ta ce ya turo su gida).
Daga haka be kara cewa komai ba ya sa kai ya fice.
Sunkuyar da kai ta yi wani irin kululun bakin ciki
ya turnike zucıyarta har suka gama kintsawa suka zo yi
mata sallama ba ta hayyacinta ta dan girgiza ta lafiya anti?
Babu komai lubuna, haba! Anti ji bi, fa inda kika yi. Cewar
lubabatu, hannunta ta riko ina kewar tafiyarku ne, za ku tati
kubar ni ni kadai. Dariya suka saka, ka ji anti da wata
magana, ai in muka ci gaba da zama sai rashin hankalin
namu ya yi yawa, ba ki ga yadda yaya yake wani cika yana
batsewa ba? wai shi an hana shi sake wa da amaryarsa.
Ta tarbe su da farin ciki 'yan matan momy an dawO
lafiya? Kun tafi ko neman momin naku ba kwa yi, in ce ko
'yar tawa tana lafiya? Allah ya sa dai ba ku buwaye ta ba.
don na san hali. Dariya suka saka haba momy antin namu
za mu buwaya? Allah Mum antin namu akwai kirki ba ki
23
ga yadda ta dinga yi mana ba, kamar ma kar mu taho don
wallahi ba ki ga yadda ta damu da za mu taho ba. Allah
sarki ashe da ban sa an dauko ku ba tun da tawowar taku ya
Gata ran 'yata. Eh Allah momy ko mu kona? Cewar
lubabatu da yake ta fi wauta. Dariya ta saka lubabatu na ga
ran da za ki daina wautar nan.
Yana jin su duk be ce komai ba ya hada rai gaba
daya haushin kananan nasa yake ji, masu karamar
Kwakwalwa daga ganin yarinya har za su fara yabonta,
bayan ko ba su san ba karamar tsagera ba ce. Ta katse shi
daga tunanin da yake. To kai ka ji sai fa ka gode Allah ka
kuma rike matarka hannu bibbiyu, ba karamin alheri bane
katari da mace ta gari yana daga cikin alheran da manzon
tsira ya lissafa mana, sai fa kai hankali ka kula ka rike
amanar da Allah ya danka maka. Jin ta kawai yake, bayan
ba ta sani ba shi ne mafi rashin sa'ar abokiyar zama, babu
wani alfanu a cikin aurenshi da yarinyar da ko kadan ba ta
da tarbiyya.
Ta rasa me yake mata dadi duniyar ta gama kuntata
a gare ta. karan farko ta yi kokarin neman masoyinta a layi
(Tahir) duk da cewa wayoyinsa da dama sun shigo ta dai Ki
dagawa ne, text message kuwa har ba ta iya kidayawa.
Take bakin cikinta ya gushe, ilahirin bacin ranta ya
kau farin ciki gami da nishadi ya mamaye zuciyarta,
lokacin da ta jiyo muryar masoyinta take ta manta da komai
ta shiga babin masoyа.
Da dare ta yi wanka ta kimtsa ta yi kwanciyarta
bayan ta gama karance-karancen da ta saba da yake
ma'abociyar karance-karance ce, musamman ma Hausa
24
Novel. Har zuwa lokacin da bacci ya kwashe ta ba ta san
sanda ya dawo ba ba ta ma damu da san da ya dawo din ba.
Zaman dai na su ya ci gaba da tafiya a haka babu
girma bare arziki, tun da babu ko me iya tankawa dayansa,
a haka har hutun da ta diba ya kare, ta rasa hanyar da za ta
bi ta fara zuwa ofis, domin tana kyashin 6ata yawun
bakinta ta nemi izininsa, sai kawai ta yanke shawarar yi
mishi letter ta je ta ajiyc a kujerar da ta fuskanci yakan
yawaita zama a kanta.
Ilai kuwa da dare misalin karfe tara .da rabi ya
dawo, tun da shi zaman gidan ma be dame shi ba, ya yi
wanka ya kimtsa yayi duk abin da ya dace ya fito sanye da
farin trouser da farar singileti idanunshi ya kai kan takarda
a lokcin da zai zauna kan kujerar hannu ya sa ya dauka
sannan ya zauna ya kuma kunna TV cikin tashar NTA yana
kallon labarun Kasa.
Daga can kuma hankalinshi ya kai kan takardar,
karamin note ne da bai wuce layi biyu ba, abin da kawai
takardar ta kunsha shi ne, "Hutuna ya kare ina son fara
zuwa aiki idan har zan sami damar hakan." W
Tana kallon shi ta window be ce komaisbanya ajiye
takardar ya ci gaba da kallon sa.
Da sanyin safiya Mr. Obi ya shiga knocking din
kofarta, rissuņawa ya yi ya gaishe ta, bayan da ya bayyana
matsayinsa ną matsayin Driver da zai dinga kai ta wurin
aiki Ya miką mata sakon da Ogan ya ce a kawo mata.
v Wraper biyu ce sababbi ful wato dubu isihirin hade
da wata 'yar guntuwar takarda ga abin da takardar ta kunsa:
"Ga Direba nan ki fito ku tafi amma fa ba zai lamunci jira
ba don ba bawa ba nе."
25
NIJ.
I
ps e
Kalaman nashi sun mata mutukar Kuna har ma take
ji kamar ta fasa zuwa to sai dai da yake ta san kanta ta cuta
babu abin da ya rage shi sai kawai ta tītobayan da ta
kimtsa, sai dai kafin ta fita din sai da ta bi ta ajiye mishi
kudinsa a kan dai inda ta ajiye mishi takardar, tana jin cewa
ta fi karfin ta karbi kudinshi ko da ko wace irin fatara take.
Yana kallon su ta gilashin motarsa suka fice kwafa
ya yi yarinya gwanda ma ki iya bakinki.
Amarsu ta ango, lallai kam wannan amaryar ta ci
sunanta, wai kin ga inda kika yi kuwa? Kamar wace ta tafi
honeymoon a birnin Paris. Sera abokiyar aikinta take
tsokanar ta. Har ma ba a bar Haj. Fatima, zubaida da kuma
idris a bayaba duk dai zolayar tata suke, dukkaninsu
abokanan aikinta ne, cikin shagwa6a-shagwa6a ta shiga
fadin momy Fatima ke fa mamana ce ki bar biye musu, to
na yi shiru diyata amma fa kyawun da kika yi ne ya wuce
misali. Meye sirrin ne? fada min 'yata kona taimakawa su
zubaida gwagware.
Cikin dan gudu-gudu ta shige ofishinta momina ba
ki dai daina ba, yau har dake a zolayata? Hankalinta ya
dada kwanciya tun bayan da ta koma bakin aiki, yinin
gidan ba yin shi take ba. Ya fice ta fice san da za ta dawo
daga ofis shi kuna be dawo ba kafin ya dawo din ına tuni
ta shige dakinta sai dai ko ta ji motsinsa idan ya dawo, da
yake tsarin gidan kusan guda ne, kayataccen plat house ne
na ganina faďa da aka yi mishi ginin kece raini akwai
faffadar haraba a gidan shi ainihin gidan a cikin tsąkiyar
farfajiyar gidan yake akwai 6angren ma'aikatan gidan daga
can barin haka nan akwai boys quarters a can kuryar gidan.
26
Sashen mutanen gidan tun shigar ka za a ka fara
shiga wani dan ziririn hanya ne (corridor) da aka lulube
kasansa da ledar nasara (tiles) daga nan kuma za ka tarar da
matsakaicin falo me dauke da kayan alfarma aka tanade shi
don baki wadanda bana jiki ba musamman ma abokanan
me gidan daga shi kuma matsakaicin lambu ne me dauke
da bushiyoyin 'ya'yan itace kala-kala, kama daga tufa,
inibi, fase dabur, 6aure, lemo da sauran su. A cikin lambun
ne za ka terar da kofar da za ta sada ka da ainihin cikin
gidan nan in ma kankarerren falo za ka tarar ya fi na farko
komai da komai, dukiya kam an zubar da ita a wajen, to a
cikin falonre kofofi kamar guda hudu suke, daya shi ne
ainhin barin megidan me kunshe da katon room akwai
bedroom, sitting room, toilet da sauran su.
Daya kofar kuma nan ne 6angaren matar gidan
kamar inda bangaren megidan yake haka nata 6arin yake
ita ma. Daya kofar kuma da ke manne da tata bangaren da
aka tanade shi don yara ne, dayar kuma da ke can kurya a
nan kitchen da store yake.
Ya yi sa'a ya same shi a gida ko ko suna da agender
ne? daga shi sai `yar karamar farar riga me gajeren hannu
hade da bakin gajeren wando me fauke da sunan ADIDAS,
sautin kida ne kawai ke tashi a falon ko da yake daman ya
san shi ma abocin sauraorin wake-waken turai ne, dakin
gaba daya ya sanyaya da na'urar sanyaya daki (AC) har ma
ba ka iya tunawa da yanayin zafin da ake ciki, zafin ma irin
na Kano.
Ya dube shi bayan da ya sami waje ya zauna kana
hutawar ka mutumina, lallai amarci da dadi yake, harara ya
sakr masa don ba ya son ya na yi masa irin wannan
27
magangar, wai ina amaryar ne ma ta zo in cashe mata?
Yinin yau ta hana mana ganin ka har sai da na biyo sahu in
ga lafiya. Ya dada 6ata rai ka bar 6ata rai ba zuwa na yi na
sure maka ita ba, zuwa na yi kawai mu gaisa. Tana ina ne
dan Allah?" oho! Da sauri ya ba shi amsa. Okey. Na
fahimta tana cikin nan. Ya nuno dakinsa da baki, ya ci gaba
shi ya sa ake min rowar ganinta, don ana shan amarci, cikin
kufula ya ce, Karya kake ba ta kai nan ba wallahi, ta kai har
ma ta huce za ku ma ka gasgata hakan nan gaba. Shi ma ya
ba shi amsa, dauke kai ya yi ya na fadin shi dai mutum
kulum cikin abu guda yake saboda ba shi daaikin yi.
Ya tashi yana dariya na ji dai ko mameye na fada na
kara fada ta kai har ma ta wuce nan din.
Ta taso don ganin wanda yake mata bugu da rana
tsaka, ko shi Peter ta gargade shi ya bar zuwar mata sashe
tun da kawo abincin ya zame mishi dole sai ya yi parking
din su a nan babban falon in ta yi ra'ayi ta fito ta di ba,
domin lefin maigidan ya shafi kowa ma na gidan.
Ta dada tamke fuska bayan da ta fahimci ko
wanene, in ban da ta bude da ba ta bude din ba, amma da
yake ta bude din sai ta ba shi wuri ya shige fuskarta duk
babu annuri amam shi ko a jikinsa domin ya iya tafiyar da
ita. Da zamansa ya fara amarsu tango, amaryar da ba ta lefi,
ta bi ta kankame ko ina a gidannan har ma da mamallakin
gidan, ta hana shi sakat ta hana zuciyarshi sukuni. Ta dada
tamke fuska ina gajiya ta ce mishi duk dan ta kauce wa
maganganun da yake.
Gajiya kam mu ne da ita amaryarmu, domin mu
kam har yanzu muna nan a ma'auninmu ba mu da mai
lallashin mu balle ya tarairaye mu, an bar mu da yawan
28
gidan abinci (restaurant) da gidan gashin fulawa (bakery)
ba mudamai girka mana. Shiru dai ta yi ba ta ce masa
komai ba, ya ci gaba, wai shin dan Allah me ake wa abokin
nan namu ne na ga ya canja ya yi kyau yayi haske ya yi,
fresh? Ko ba ki ma fada ba an san yana samun kulawar da
ta dace daga gurin iyalinshi, kai muma Allah ya bamu ya
tashi.
Da sauri ta datse shi, dakata Samir cin fuskar ya
ishe ni haka fa ta ja tsaki mtssss! Allah ya tsare ni ya kuma
yi min katangan Karfe a tsakanina da. mugun mutumin da
kake alakanta ni da shi Ta dube shi da kyau, kama shaida
mishi ba zan so shi baba zan taba sonshiba muddun
rauwata.:
Mikewa ya yi yana kada kai, lallai kam yau hirar ta
fi kwarfina bari in bar miki dakin tun kafin ki kai ga
kwankwatse min kwakwalwa. Harara ta bi shi da shi bayan
da ta tabbataneta yi maganinsa, in ba haka ba yanzu ya ishe
ta han ma ya cika mata ciki ta ji kamar ta tashi ta shake shi.
YADDA ZAMAN NASU YA KAYA
Suna kasaa zama guri guda: ballantana su fahimci
junansu ko sa afuwanta wa junasu tun da zama ne Allah ya
riga ya hada. Watanni takwas babu abin da ya sauya, babu
me kula wani balle ya shiga hurumin sa, irin zaman nan ake
na ban ma san da kai ba.
Yau babu aiki don haka tana gida yayin da ta yi
wanka ta feshe ta hade cikin suit na mata launin ganye,
kyawunta ya dada bayyana tana jin fitarshi a mota ta ji
29
wani sanyi a zuciyarta, ta kan kasance cikin matsi da takura
har ma ta ji tamkar a kan garwashin wuta take a duk
lokacin da yake gidan, dan ma Allah ya so ta zaman gidan
be dame shi ba ko da a ranakun Karshen mako ne
(weekend).
Ta baje a babban falo kan 2 seater, ko dayake ba ta
iya zaman falon kai ba ta iya ko kusantar sa muddun yana
gidan, tana jin wani irin nishadi, kiran farko ta same shi a
layi take duk wani kunci da take ciki ya gushe ko da yake
hakan ce take kasance wa duk lokacin da take waya da
Tahir. Tsawon lokaci suna hiirarsu ta soyayay tare da
bayyana kaunar da suke wa junansu, har credit dinta ya
kare ya kara kiran tata nan ma sabuwar hirar aka dasa.
"Tahir kai nake so kai na zaba kai nc kuma zabina
don haka nake so nake kuma kara gayamaka ka kwantar da
hankalin Heedaya ba ta kowa ba ce face Tahir dinta. Tuni
na riga na gama mallaka maka zuciyata har da gangar jikin
baki dayanta....
Finciko ta aka yi bayan da aka yi cilli da wayar ya
doka ta da kasa ya kuma doka ta da kasa sannan ya bi ya
take ta. Danko dantsanta ya yi ainun idanunshi ya kada ya
yi jawur, cikin masifa da bala'i ya nuno ta da yatsansa, ni
din nan da kika gani na fi karfin kowa ne dan iska balle fa
ke fa kucaka ce ko a cikin yaran iskan, na kuma fi karfin ai
min wannan iskancin a gida. Ya yi facali da ita cikin fusata,
babu alamun tsoro ko fargaba a tare da itata shiga fadin
komai ka yi ka yi a banza don ba na son ka ba na kaunarka,
wanda nake so din nan dai shi nake so babu kuma me hana
ni kaunar sa, ko ka sake ni ko kar ka sake ni duk dai daya
ne Tahir dai shi ne zabina shi ne kuma abokın rayuwarta.....
30
Tasssssss! Ya wanke mata fuska. Hajijiya ta yi har ma ta ji gidan baki daya na juya mata ya sa kai ya fice cikin fusata.
A duniyar nan ya rasa me yake masa dadi wannan
rashin mutunci haka. "Tuni na riga na gama mallaka maka
zuciyata har da gangar jikin baki daya...." wadannan
kalamai su suka fi komai tsaya masa a zuciya, to wai me
yake jira ne ma da ba zai sake tan ba? 'yar uban wane ne ita
da ba zaı sake tan ba? take kuma wani sashe na zuciyarshi
ya shiga tu nasar da shi irin mummunan 6acin ran da zai
fuskanta daga mahaifinshi, kai an cuce ni ya sa hannu a ka
ya dafe.
Zucivarshi ta saukaka ne lokacin da ya tunano cewa
wannan aure fa babu inda zai je ba ya son ta ba ta son shi
don haka zaınan ba zai taba yiwuwa ba. Fatan shi dai koma
meye ya bullo daga gare ta inda ko kadan mahaifinshi ba
zai ga lefinsni ba gashin kuma kam zai yi wa yarinyar za kuma ta gane shi ba sa'an yin ta ba ne.
Ta kimtsa ta shirya tana jiran isowar direba shirushiru har misalin Karfe tara, har ma ta hakura ta kwanta
abinta, wayewar gari ma hakan ce ta kasance, kai wasawasa sai da aka yi kwanka hudu cur babu direba babu batunshi, me hakan ke nufi ne? ta tambayi kanta. Da yammaci ta hango Obi yana goge motar ogan, Peter ta sa ya kira mata shi ta shiga bin bahasin rashin zuwan nasa cike
da girmamawa ya shiiga bayyana mata ogan ne ya ce ta
samu hutu wajen aiki don haka ya jira har zuwa lokacin da
za ta koma. Ta gane shirinsa wato ya hana ta zuwa aiki ke
nan ai ko ya yi kadan ta dube