ya wuce a cillar a bola, to haka kike a
gare ni, don haka ki bar yi min wani firiritar banza. Kuka ta
saka Allah ya isa na, ai daman na san ka cuce ni ba kuma
zan taba daina yi maka Allah ya isa ba har karshen
rayuwata.
Daga yau ka bar kara gani na a gidanka, macucu
azzalumi kawai, na tsane ka na tsane ka sam ba na Kaunar
ka. Ba kuna zan taba kaunatarka ba. Da ko kin kyauta min
domin da ganin wannan rana gwanda in bi uwa duniya,
kukanta ya tsananta, yayin da shi kuma yake kara sautin
dariyarsa.
Hankalin Hai. Kaltum ya yi mnummunan tashi, ta
saka 'yarta a gaba sai faman tuhuma take, kuka take bu
kakkautawa, ita dai ba ta son sa, ba ta ra'ayin zama da shi,
a raba auren nan kawai shi ne samun nutsuwarta.
59
Cikin lallashi ta shiga fadin haba Heedaya kin taßа
ganin an yi abu kai tsaye ba tare da tushe ba? bare batun
aure, idan dai wani abin ya yi miki ki fadamin sai a gaya
masa ya gyara.
Ni dai babu komai, kawai ba na son sa ne nomy.
Zama ta gyara lallai kam Heedaya kina son daga mana
hankali ne kawai, kowa na murna kin kwantar da
hankalinki za kuma ki daga mana wata fitinar. Haba
Heedaya, a ce kuma ana girma ana cin kasa.
To da yake Ambassador ba ya kasar sai ta jira ya
dawo domin ya yanke hukunci sai dai ta bayyana masa
konai a waya.
A kwanakin da ta yi uku a gida ta sake tama manta
da komai, jira take kawai dadinta ya dawo ya raba
tsakaninsu da wannan kallagaggen mutumin, ta tsane shi ba
ta sonsa ba za ta gajiya da fadar haka ba.
A cikon kwana na hudun ne Ambassador ya dawo,
duk da cewar ba keammala abin da yakai shi ba, dole ya
datse saboda wannan matsalar. Kanta na sunkuye tana
faman kuka a lokacin da yake tuhumarta. Amsar dai daya
ce ita dai ba ta son sa a raba wannan aure shi ne kwanciyar
hankalinta, an kada an raya babu wani dalili sai wannan, to
me za ta ce? Domin duk abin da za ta ce din dole ne batun
Tahir ya shigo, ita ko ba za ta so haka ba, domin za su dafa
tsanarsa har ma su Kara hana ta zabinta a lokacin da ta rabu
da wannan kallagagggen mutumin.
Lallashi ya shiga yi amma sam-sam ta ki ta ji ta
kafe ta nace a kan ra'ayinta, ya ma rasa yadda zai 6ullo
mata shi da'yar cikinsa ya kasa controlling dinta (to ice ne
60
tun yana fanye ba a riga an tankwara shi ba sai bayan ya
riga yabushe, anya ko hakan zai yiwu?).
Ta cikin wayar sadarwa ne ya kira General
Abdullah, to fa General din ya nuna mutukar mamakinsa,
sam-sam be san da wannan maganar ba, sai kuma ya shiga
fadin, haba Sa'adu na dauka duk daya muke har yaushe
yarinya za ta yi kwanaki har hudu a gida a kyale ta, aibana
gari ne, ka fahimce nimana, in ba ka gari ita Hajiyan fa
dukkansu ba 'ya'yanta ba ne, don menene ba za ta kira shi
ta ja mishi kunne ba, lefin dai be wuce nashi ba. a'a
General ba a saurin yanke hukunci idan ka bibiya lefinta ne
ka san halin yaran zamanin nan.
To ko ma dai menene yanzun nan zan turo Fatima ta
taho min da 'yata kafin mu haďu da shi na ci zarafinshi.
A'a General a dai bi komai sannu a hankali na gaya maka
kila lefin duka nata ne.
Da yammaci Haj. Fatima ta iso Heedaya na falon
mahaifiyarta ta jiyo muryar surukarta, sai ta ji ba dadi, tana
ganin kimar dattijuwar wanda hakan ke nufin tilasta ta abin
da ba ta ra'ayi, hannunta ta janyo bayan da ta zauna zo nan
'yata, taho maza ki fada min abin da yayan naki ya yi miki?
kar ki rufe ni gaya mini, wannan karon kam zan sassaba
masa. Sai kuma ya gurfana gaban diyata yana neman
afuwarta.
Don son kai bayan wata kila ma 'yar taki ce ke da
lefin. Cewar Haj. Kaltun, babu wani ni na san diyata
yarinyar kirki ce lefin dai be wuce na danki ba ne sun dade
suna barkwanci da raha daga bisani ta shiga ban hakuri
bisa sabanin da ya shiga sam-sam ba su sani ba, sai fa da
Ambassador ya yi waya. Haka nan kuma ta nuna bacin
61
a
ranta a kan abin da Hajiyan ta yi to Haj. Kaltum fin ban
hakuri take,
Ga Heedaya ta kasa cewa komai sai hawaye kawai
ke zubo mata, ko da tsiya ko da arziki ita dai ba za ta koma
wa wannan aure ba. Zulumin Haj. Kaltum din ke nan kada
ta botsare musu a gaban surukar tata, to dai Allah ya
taimaka din ba ta botsare din ba sai dai faman kuka da
take.
Ki yi hakuri kin ji 'yata koma me ya yi miki ki bar
ni ni da shi ne zan ci kaniyarshi ba zan ma tafi dake din ba
sai ya zo da kanshi ya yi ban hakuri ki kintsa daga nan
zuwa dare sai ya zo ku tafi.
Ya gurfana a gaban mahaifinshi fuskar nan tashi
babu sauran walwala, ka kyauta ko? Ka kyauta ke nan abin
da ka yi Waheed? ka sani ban ba ka 'yar mutane domin ka
wulakanta ba, this is the last warning ya karashe maganr
cikin kaurara harshe.
Gabanshi ne ya ba da wani dammmm! Shi kam tuni
ya mance da abin da ya gudana ya ma mance da wata
Heedaya, a zatonshi iyayanta sun yi fushi har ma suna
shirin zuwa kwashe kwamatsansu, sauran me ya rage su
nemi takardar 'yarsu, shi ke nan ya rabu da kaya ba tare
da mahaifinsa ya ga lefinshi ba ashe be sani ba akwai
sauran rina a kaba.
Shiru ya yi yana sauraron mahaifin nashi yana cin
zarafinshi ainun a kan fitsararrriyar yariniyar. Ya kare
mishi ta tas, ya kuma gargade shi a karshe ya ce ka je
maza ka taho da matarka ka kuma nemi afuwar iyayanta,
ita ma Hajiyan ba ta kyale shi l ba sai da ta wank e shi.
62
Ba shi da ta cewa zuciyarshi kam sai tafarfasa take
yama za a yi a yi mishi wannan yankan kaunar, sannan
kuma a zo ana cin zarafinsa? Abin mamaki ya kasa cewa
uffan a kan abin da ya yi silar rikicin nasu why? Shi kansa
ya kasa gane sanin hakan, kila ko kwarjinin da ma haifinshi
ke mishi ne? ya ayyana hakan a zuciyarsa.
Kai tsaye Samir ya nema a waya, maza ka zo 'yar
iskar yarinyar nan ta hada min bom. Dad sai cin zarafina
yake a kan ta shi kađai yake iya fadawa damuwarsa saboda
amintar da suka yi wa junansu, tiryan-tiryan ya labarta
masa komai ya kuma kara da cewa saboda Allah an min
adalci ke nan? Ka taba ganin yarinyar da suke tare da Tahir
ya kyale ta haka? Ai ka san zance ne ni dai kawai an cuce
ni.
Cikin shakku ya ce Heedayan? Anyako Heedaya za
ta yi haka? Zan mata karya ne? ya kada kai babu yarinyar
da ta isa in mata karya don ba tsoron ta nake ji ba. kai
amma abin da shakku. Cewar samir ya ba shi amsa. kar fa
ka mance yarinyar fa ba ta da tarbiyya, gaskiya ne na yarda,
sai dai fa ta wani 6angren kam akwai tarbiyyar, na lura da
hakan ina da hujojina a kan hakan. Jinjina abin yake shi
kam sam be yarda ba, to amna fa Tahir ba kyau, ya ayyana
hakan.
Babu yadda zai yi yabi umarnin mahaifansa to
amma fa zai ci gaba da gasa mata gyada a hannu har sai ita
da kanta ta nemi h..myar tsira, shi ke nan ya rabu da kaya ya
je ya auro zabinsa.
Ita dai Haj. Kaltum dai ta hadu da aiki ta yi fadan ta
yi lallashi duk a banza, ta shiga fadin haba Heedaya meye
aibun yaron nan ne? me kika nema kika rasa a gidansa?
63
Allah ya rufa miki asiri ya kai ki inuwa kina neman,ki kai
kan ki rana. In ba ki sani ba ki sani yara nawa ne 'y'a'yan
manya suke son yaronnan ba don komai ba sai don
kasancewar sa yaro me tashen naira daman kuma an ce
yaro da kudi abokin tafiyar manya ne to me zai sa ki nemi
kwaye mana sutturar da Allah ya yi mana kowa fa kika
gani a garin nan JARI HUJJA ta ra ratsa zukatansa. Ba fa a
yin komai da kika gani don Allah sai fa don zinar duniya a
wannan dai zamani da muke ciki don haka ki kwantar da
hankalinki Allah ya yi miki suttura ya kai ki gidan hutu
burin kowace 'ya mace ke nan.
Maganganun mahaifiyarta suna dada tunzura ta a
yawancin lokuta tana mai jin zafin halayyar mahaifiyar tata
mace ce 'yar jari hujja kimarka a gun ta kudi ba tun yau ba
ta fahimci me ya dada ribatar ta ga aurenta da dan gidan
Gencral din ta sani tana son karfafa zumuncin da ke
tsakaninsu da a halin General din to amma fa jari hujjar shi
ne kan gaba wajen amincewa auren nan, to sai dai fa ba
kowa ne ya fahimci halin Hajiyar ba ita din ma kila don
mahaifiyarta ce.
Ta yi yo salama ta shiga, wani banzan kallo ta biyo
ta da shi ta gaishe ta cikin girmamawa, Hajiya ki yi mina
fuwa sam ban san abin da.ya faru ba sai dazun nan Alhaji
yake min maganar, sam ban ji dadi ba*wallahi. Idan ma kin
ji za ki bayyana ne? tun da dai gulam da kinibibi gadon
gidanku ne. Ta ayyana hakan a zuciyarta. Ta dubi ‘yarta
irin abin danake nuna miki ke nan ba fa mu kadai bane a
gidan nan ko me muke yi a kan idanu yake a ja gefe a yi
dariya, to koma meye dai da da ne, kai ma kuma kana da
64
yaran idan yau a kan dan wani ne gobe kuma a kan naka
yake, mai dariyar bayan fage sai ya yi hattara.
Jikinta ya yi sanyi ta dube ta ban zoda wani sharri
ba fa ce alheri Hajiya. Heedaya da maridiyya duk daya
suke a waje na. A wajena babu wani banbanci, na sha
sheeda miki ki fahimci hakan. Ta karkato da hankalinta
gare ta ta shiga yi mata nasiha, Heedaya ki kwantar da
hankalin ki bi umarnin mahaifanki ki kuma yi biyayya ga
maigidan domin samun tsira ranar gobe kiyama, halin
rayuwa sai an yi hakuri a cikin ta ballantana ga mutumin da
zama ya hada ku zaman da muke fatan ya dore har gidan
aminci, to amma ta yaya za a saımu hakan? Amsa ita cе
hakuri, ladabi, biyayya da kuma juriya, idan kika mallaki
wadannan halayya kin gama da komai na rayuwa domin za
ki kasance cikin kwanciyar hankali da duk wanda Allah ya
hada zamanki da shi.
Cikin yanayin kuka ta ce, "Anti Na'ima, yaya za a
yi na iya zama da mutumin da ba na so wallahi sam ba na
kaunar shi." Hakuri juriya, ladabi da biyaya Asu za ki ci
gaba da yi har wata rana ma ki 'WAYI GARI' dumu-dumu
cikin kaunarsa, muddun dai kika bi shawarar da nake baki.
Anti ba zan iya ba, a'a za ki iya muddun kika sa kanki, za.
ki mallaki komai ne ta hanyar hakuri, hakuri dabi'a ce ta
kwarai dabi'ar da manya-manyan bayin Allah da Manzanni
suka fifita da shi har suka zama abin koyi a gare mu, abin
kwatance ga dukkanin abin halitta.
Rayuwar nawa take? In mu ne yau ba mu ne gobe
ba, kamar yadda babu abin da yake dorarre, komai kin da
kike amsa wata rana da yardar allah zaki WAYI GARI
65
cikin kaunarsa. Allah ya kiyashe ni. Ta fada da sauri, bana
son shi ba zan so shi ba abadan abidina.
Heedaya akwai wauta da kuruciya da uwa uba
rashin tarbiyya a tare da ke, dan haka dole a biki sannu a
hankula ta ayyana hakan a zuciyarta, amma da yake babu
damar fadar hakan nasihar da lalashin ta ci gaba da yi har
zuwa lokacin da ta sauko.
Haj. Kaltum dai tana kallon ta ta yi kasake tana
ganin hikimar kankanuwar yarinyar da ba ta fice 'yar
cikinta ba, cikin kankanin lokaci ta shawo musu kanta
bayan tsawon lokacin da suka dauka suna tata-burza da ita.
Inda abin da anti Na'iman ta yi mata na yabawa be wuce
wannan ba dan haka har a fuska sai da ta gwada mata.
Misalin karfe takwas na dare Wahced ya isa gidan
surukansa, ya yi shirin zuwa da duk wacce a ka zomasa,
don ya daina jurar kaskanci gurin kowane a kan dai
fitsararriyar yarinyar, cin zarafin da aka yi masa ya isa
haka nan, ga mamakinsa karbar karamci da girma ya samu
daga wajen mahaifanta, Ambassador Sa'ad da Haj. Kaltum
domin har cikin tsakiyar falon Ambassador aka shiga da
shi, nasiha yake masa tare da ban hakuri, a bisa abin daya
afku, duk da cewar har yanzu bai san takamaiman abin da
ya hada suba, to dai ba ya bukatar bincike fatanshi a shirya
su zauna lafiya da junansu.
Itama Hajiyan dai ban hakurin take, babu wani
alamun 6acin rai ko wani abu a tare da su, Ambassador
yana jan shi ajika shi kam yana nonnokewa, kunya kam
duk ta bi ta baibaye shi har yanan cewa abin da ya yi wa
'yar tasubai kyauta ba. Kai be ma Lyauta din ba ya ıyyana
hakan a zuciyarshi. 6€
Wraper naira dari biyar (50,000) ya mika wa su fa'izu, Ambassador ya hana, ya ce babu komai Abba ai
kannena ne. su suka yi mishi rakiya zuwa cikin motarsa, ya
sake da su ya yi hira da su sosai.
Ta ci kukanta har ta koshi ta shiga tattara inatainata, Anti Na'ima ce ta shigo da farin cikinta Hajiya yanzu
su mardiyya suke gayan Abdulwaheed ya zo za su tafi ko?
Eh! Ta fada fuska a daure, sam ba ta so ta sakar wa
yarinya, ta tsane ta tun da ta yi mata shisshigi a rayuwarta,
tana tsananin kishinta, diyar cikinta suna auren miji daya?
Kai! wannan abu da kunya.
Kai amma na yi farin ciki zo mu je in miki rakiya.
Anti Na'ima ta fada cikin rawar kafa. Wani kallo ta sakar
mata, ke! Daka ta fa, ba na son isar da ba ka isa ba, da fadin
haka ta gintse fuska gami da dauke kai. Ja ta yi ta tsaya
jikinta ya yi sanyi ainun to Heedaya Allah ya kiyaye hanya
bari na je Allah dai ya kiyaye gaba.
Ya ma kiyaye din tun da ya kwance kulin
masharranta. Ja ta yi ta tsaya ta dube ta alamar maganar ta
yi mata ciwo kada kai ta yi sai kuma ta tafi abinta. Ranta ya
dada baci, irc-iren halayyar mahaifiyar ta sun soma isarta,
an tsangwami baiwar Allah babu siddan babu dalili,
wannan hali kaım ya isa haka.
Yana tare da su fa'iza suna ta hirarsu, kallon inda
suke ba ta yi ba, ta murda murfin kofar gidan baya ta shige.
Ya sallamesu ya shiga cikin motar yayin da suke yi mata
sallama anima san babu walwala à tare da ita.
Tafiya suke babu wanda ya cewa wani kala, sai dai
shi fuskarshi ba a daure take kamar tata ba, sun iso gidan
ya yi parking da motarsa juyowa ya yi ya dube ta, ki yi
67
hakuri da abin da ya gudana, ina fatan komai ya shige,
kallonshi ta yi ba ta dai ce mishi komai ba sai dai ta, nuna
alamun sassauci ga fuskarta.
Wayewar gari mislin karfe bakwai da'yan mintina
ya shiga knocking kofarta ta fito ita ma ta gama kintsawa а
zatonta Peter ne ko kuma Direbansu, domin jikinta ya ba ta
cewa ba zai taba barinta ta fita ita kadai ba.
Idan kin gama kintsawa ina jiran ki, ba ta iya ba shi
amsa ba domin har yanzu tana cikin fushi ne, ta dade tana
nazari, ta karfi da ya ji ana so a dai raba ta da Tahir dinta
bayan hakan ba mai yiwuwa ba ne.za ta dai bi shi sannu a
hankali har zuwa lokacin da zai sauwake mata, ba ta son
shi ba yason ta don haka take da kwarin gwiwar zaman
nasu takaitacce ne.
Ya yi parking a harabar kotun tasu da ke titin Kotun
(Court Road) ya dan waigo ya dube ta ya kamata ki gyara
mayafinki ki ma san irin shigar da za ki yi idan za ki fita, ki
tina fa akwai wani nauyi akanki. Dauke kai ta yi ba ta son
sauraron sa balle har wani abu ya hada su. Ya dauko ta
daga gida ya ajiye ta wurin aiki, shi ke nan kalas. Ya tafi
abinsa babu ruwansa da rayuwarta.
Ya ci gaba ina fatan kada ki kara maimaita
kuskuren daya afku a baya gaskiya za ki ga tsantsar 6acin
raina a duk ranar da na gan ki da dan iskan yaron nan.
Magana yake cikin lumana amma da ya zo nan sai ya
kaurara harshe.
Ba ta dai ce masa komai ba har ya yi ya kare, duk
da matukar kuna da kalamansa da suka yi mata a zuci,
"Dan iskan Yaro." Kalmar kam ta yi mata kuna.
68
A ko da yaushe shi yake kaita ya dauko ta duk da
tarin ayyukan da ke gabansa amma dai ya jure wa hakan,
sakamakon zargin da ya shiga tsakaninsu kai ya wuce zargi
ba zargi banc abin da idanunsu ya gane masa ne, hatta da
direbansa bai amince masa ba ji yake za ta iya tafiya wurin
fan iskan yaron don haka ya zama dole ya sa ido a kanta.
yana jin wani irin kishi a zuciyarsa why? Why? Ya tambayi
kansa. Dalilin be wuce kawai igiyoyinsa a kanta ba, don
haka yana kishin wannan igiyoyi nasa. Ranar da duk suka
tsinke shi ke nan ta je ta yi duk irin rashin tarbiyyar da za ta
yi babu abin da ya shafe shi, igiyoyinsa yake kishi, sun
kuma tsinke, fakat ta kare.
Zaman nasu dai ga shi nan ne babu wani cigaba da
aka samu sai dai babu tashin hankali kamar da, haka nan
halayyar nan ta ko in kula ita ta fi gwada mishi, shi kam ya
sassauta mata har ma a wani zubin yakan ba ta kulawa duk
da rashin fuskarta.
A 'yan kwanakin ba ya zuwa daukar ta da wuri
sakamakon ayyuka da suka cunkushe masa, yakan gota sa'a
biyu zuwa uku kafin ya zo daukar ta kusan kullum ita се
karshen tafiya wannan abu nai mata ciwo, tsabar wulakanci
ne kawai da keta irin nashi duk dan ya kuntata rayuwarta
ya bi ya kankame mukullayen motarta babu ko fuskar da za
ta tambaye shi. Ta tada fitina, wato ta kai kararshi ya tona
asirinta tun da ita ta fi kowa sanin dalilin da ya hana ta fita
a motar ta.
Idan hakan ko ta fasu masoyin nata (Tahir) na iya
kara bakin jini a wurin iyayanta har ma su dada tsanarsa,
wanda hakan wata barazana ce a gare su baki daya dan
haka ta yi hakuri ta bi shi a yadda yake so duk da gashin
69
kuman da yake mata. Har zuwa lokacin da zaman zai kare
ta je ta auri abin kaunarta, ra'ayinta, zabinta kana
masoyinta.
ZUCIYA NA SO.....
/un safiyar yau ta tashi da rashin kwarin jiki ciwon ta L
na shirin tayar mata, haka dai ta daure ta tafi. Ofis
din ma ba ta iya tabuka abin kirki ba, ta zube
Mominta fati da su zubaida na ta tsokanar ta, jinsu take
kawai, su ba su san ma me ke tsakaninsu da mutumin ba,
ballantana har abin da suke zargi ya tabbata. Zazzabi mai
zafi ya rufe ta ga kuma kirjinta da ya fi matsa mata sai
faman haki take, zai zo ba zai zo ba har mislin karfe hudu
da kusan rabi na yammaci, alhalin tun misalin karfe biyu
suke tashi, kifa kai ta yi kawai a jikin faffadan teburin
gabanta. Ciwo kam ya ishe ta.
Misalin karfe biyar dai-dai aka turo kofa aka shigo.
ja ya yi ya tsaya yana dubanta, shi kansa ya san bai kyauta
ba duk da cewa lefin bana shi ba ne face yanayin karfen
nasara da aka ce bashi da tabbas, tafiyar gaggawa ce ta
kama shi zuwa Abuja tun mislin karfe goma sha biyu ya
baro garin a hanyar dawowarsa ne ya gamu da sharrin
karfen Nasara ya sha wuya kafin a shawo kan matsalar.
Wannan tunani nashi ya hana ya bawa wani damar
dauko ta. A tunaninshi babu idanunshi za ta iya zuwa wurin
70
dan iskan yaron, yana matukar adawa da hakan, sam-sa be amince mata ba, ba ma zai amince matan ba.
Matsawa ya yi jikinta ya kare mata kallo, ya san
sam bata ma san ya shigo ba, bacci take, ko menene? Ko ko
ta gaji da zaman jira ne? Tausayi ta ba shi, karon farko ya
ambaci sunanta, Heedaya? Cikinfirgici ta fago ta dube shi,
idonta yakada ya yi jazur ki yi hakuri don Al.... be Karasa
ba ta dakatar da shi da hannu, jakarta ta dauka ta kuma
kwashe tarin takardun gabanta da zummar in ta je gida ta
karasa aikin. Ji ta yi tana hajijiya takardun ma sun runjaye
tana kokarin waduwa, da sauri ya kai hannu zai tare ta, ta
yi saurin gocewa, harara ta sakar masa ta daure ta cije ta taka da kafafunta.
Suna zuwa bakin motar hannu ta sa ta bude ta shiga
ta zauna babu walwala a idanunta har dai yanzun hakin shi
ya fi damunta. Ya dube ta jiki a sanyaye ba kya jin dafi ne?
ba ta dube shi ba ta ba shi amsa lafiya ta Kalau, na dai gaji
ne ya dube ta yakuna duban ta kamar dai be yarda ba sai
kuma yadan girgizsa kai yatashi motar suka tafi, har suka
isa yana lura da yanyinta.
Misalin karfe tara na dare yana zaune ya yi zugum
ta rasa me' yake masa dadi, fitar ma ya kasa yin ta duk da a
dai-dai lokaein yana dawalkawarin da Zeenatu, party ne zа
su je shi na yarinyar abokinshi, kana Rawar ita Zeenatun
domin taya tá nturnar kemmala karatunta na Degree. akwai kuma alkawarin faranta wu junansu rai da suka yi.
Yana jin waya .a ya share ya ki fita, whyi? Dalili be
wuce yanayin da yaga matarsbi a ciki ba, zuciyarshi ta bit shi amsa duk da ya yi Rokarin musanta hakan to anma dai
ya kasa cin galabar zucihi
71
Ya afka cikin kogin tunani ya tuna da yanayinta na
dazu, tabbas akwai abin da ke damun yarinyar duk da
kokarin Boye mishi da ta yi. Zumbur ya mike kada yarinyar
mutane ta mace masa, ya shiga uku gurin Dad dinsa kila
ma ya ce shi ya yi ajalinta. To amma dai wata zuciyar na
kokarin karyata wannan zargin.
Ja ya yi ya tsaya lokacin da ya yi nufin shiga
bangarenta, saboda gudun abin daka je ya dawo to amma
dai ya yi ta maza ya shiga. Kwance take a kan gadon juyi
take dakanta hannunta na kan kirjinta, numfashin ma samasma take yi, tamkar zai fita, da sauri yakarasa cikin
matsanancin tsoro, Heedaya! Heedaya!! Lafiya? Lafiya?
Ya kidime a lokacin da ya yo kanta, ya tallafe ta a
cinyoyinsa jikinsa sai bari yake, shi daman matsoraci ne,
menenc? Menene! Duk da cewa ba ta cikin hayacinta ta yi
kokarin nuno mishi da hannu wurin da 'inhela' dinta yake
taimaka min, taimaka min zan mutu, mikon, miko min... ya
kasa fahimta ya ma rasa me take nufi, hargitsa ward robe
din ya shiga yi hannunsa ya kai kansa cak! Yaja ya tsaya ya
fahimci ko menene.
Rayuwarta na cikin hatsari, cikin matsanancin sauri
ya shiga shaka mata a makoshinta, nan da nan numfashinta
ya soma daidaita, sai dai har yanzu ba ta cikin hayaycinta,
kamkame ta ya yi kam, kamar mutuwar ce ta zo daukar ta.
Bacci mai nauyi ne ya dauke ta a hankali-a hankali
numfashinta ya dai-daita, sannan ne ya yi ajiyar zuciya
gami da jan gwauron numfashi.
Misalin karfe biyu da mintuna na dare ta farka,
yunkurin tashi ta yi amma kuma ta kasa sam babu kuzari a
tare da ita, komar da ita ya yi kwancen, ya rankwafo da
72
kanshi nagana yake a hankali, koma ki kwanta babu karfi a
jikinki, me kike bukata? Ruwa ta ce mishi cikin sanyin
murya, ki fara dai da dumama cikinki sannan ki sha ruwan
ko? Ruwan tea ya hada mata daga suger sai lipton ya hado
ta da jikinsa ya zaunar da ita yana ba ta ta shanye tas,
sannan ya zubomata hadin soyayyen dankali da aka cakuda
shi da su hanta da kwai, ta kasa ci ko da cokali daya ne ya
damu ainun to yanzu me za ki ci? da alama tun safe ba ki sa
komai a cikinki ba.
Quaker Oats ya hado mata ya cika madara don ta
rike cikinta to shi ma din dai kadan ta iya ci har yanzu
akwai matsala a kirjinta duk da cewa numfashinta ya daidaita, ya lallabata dai ta yi bacci. Kafin wayewar gari suje
asibiti. Karon farko ya kwana a dakinta duk da cewar ba ta
da masaniyar hakan tuni bacci ya kwashe ta.
Da asubahin fari ya nufi sashensa ya gabatar da
raka'atul fajri kamar yadda ya saba, ita wannan sallah
sunnar Manzon Allah ce, kuma tana daga cikin sunnoninsa
masu karfi domin tana da martaba da falala, har ma akа
kwatanta wanda ya yi ta da wanda bai yi ta ba kamar
misalin mutum ne ya kwana ya wuni yana tafiya a kan doki
sannan kai kuma ka zo daga bya ka ce wai kanka son ka
riske shi. Sannan ya zauna yana lazimi har zuwa lokacin da
aka yi assalatu ya nufi masallacin da ke daura da gidansa.
Ya kimtsa ya yi komai ya mufi sshenta, har yanzun dai
bacci takè, yaduba agogo karfe bakwai na safiya, ya
kamata ta tashi ta yi sallah kamar tana da masaniyar
shigowar tashi ta farka, ya kusance ta kin farka? Yajikin
naki? Yayi nufin taimaka mata bar shi zan iya mikewa. Та
yunkura ta yunkuro amma kuma ina kirjinta yana yi mata
73
wani irin ciwo, tana ji kamar katon dutse aka dora mata.
dago ta ya yi be ko saurare ta ba yanufi toilet da ita. Ta yi
wanka ta kimtsa ta yi