Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 8
ba ta ganshi ba kai ba ta ma lura da shi ba, tun lokacin da ta hango Waheed gaba daya hankalinta, tunaninta, ganinta kai da ma zuciyarta ta tattara gare shi, tana son sa tana mishi wani irin sọ mai ban mamaki. Kasa motsi ya yi ko da da kafafunsa ne kai sai ya ji duk ya bi ya muzanta a idanun al'ummar wajen. Dariya ake masa, wasun su kuma na cizon yasa, kai yarinyar nan ta 88 bonsa Tahir, abin da galibi suke fada ke nan. Shi ko gogan naku ya harde yana yi mishi wani kallon rainí me kunshe da sakon na riga na yi maka fintinkau, sai dai hakuri kawai. Tana sakale da shi ya zo shigewa ta gabansa ya ja ya tsaya yana yi mishi wani dubana raini, kai ko ba ka da sa'a abokina, me zai sa ka nemi sa'a ko ko jininka ne baki? ban sani ba dai, na dai fahimci sam-sam ba ka da farin jinin jama'a, musamman ma gurin 'yan mata, hakika ina jajanta maka ba karmain tawaya ba ne mace na gudun mutum. Yatsu ya shiga daga mishi, one. two, three ya Kidaya hannunsa duk na yi maka fintin kau. Murmushi ya saki na tura haushi, ya shige abinshi har yanzun dai tana manne da shi. Zahhirin gaskiya sai yanzu ne ta lura da shi? Tahir ne, sai kuma ta fan tabe baki to menene ai shi ne ya jawa kansa? daman ai tana ciki da shi na nuna zarin shi ga 'yan mata, kare da doki duk shi ne ta sha yi mishi korafi amma sai ya share ra'ayinsa ke nan. Amsar da yawanci yakan ba ta don haka ne ma hankalinta ya fi karkata ga Waheed duk da wulakancin da yake nuna mata da fari, ta lura da kyau ko da yake dan bariki ba kowa ce karya yake kulawa ba, shi gentle man ne, be cika ma sauraron Kadangarun barikin ba saßanin shi Tahir da yake tamkar bunsuru, in dai akan mace ne. Dariyar aka kara sawa, kai wanda ma be yi dariyar ba da fari ya dara din, yau rana ta kwacewa Tahir, wane irin tsautsayi ne ya kai shi gå afkawa tarkon Abdulwaheed? Abin da galibin abokanansa suke cewa ke nan. Shi kansa Samir din da ke gefe dariyar yake, daman dai babu komai a tsakaninsu sai tsantsar adawa, lefin Wahced ya shafe shi kai ba ma ya wani tantance tsakaninsu dan haka shi ma Samir 89 din ya fita harkarsa, ko da yake koma ba haka ba muddun za ka taba dan uwanshi (dan kam ya fi danganta shi da wannan matsayi) tamkar ka tabo shi ne. Kada kai yake, kai fan uwanshi ya yi mishi kata i a yau ya yi musu maganin tsageran yaron me shegen fangimar tsiya, to amma dai a wani 6arin yana jiye mush tsoro, Tahir fa ba kyau, kai tamkar ma ba shi da imanı wani sa in. Ranshi ya yi masifar baci na tozarcin da aka yi wa Tabokinshi, cikin matsankancin bacin rai suka baro mashayar. Ya dube shi da bacin rai, na rantse da wanda raina ke hannunsa sai na tagayyara mutumin na sai na kuma wulakanta rayuwarsu, domin zan nuna masa shi Karamin dajn iska ne, in ga kuına uban da zai kwace shi, matsiyaci dan matsiyata. zan gwada mishi na dare shi da komai. komai yake takama da shi na fi shi, be ko isa hada kafada da ni ba ballantana ya ja da ni. Fada yake tamkar yana wajen, shi kansa Faisal din a wannan karan ba ya ganin laifinsa, a yawancin lokuta musamınan lokacin rikicin Heedaya, ya kan ga laifinshi har ma ya dinğa tausar shi a ganinsa akasi ne kawai aka samu amma ba da gayya ya yi masa haka ba, idan aka bi abin da idon basira to amma a yau duk ta kau ya daina ganın laifin shi kai da gangan ma yake ganin laifin abokin nashi, gaskiyarshi tsabar rashin mutunci ne da raini kawai Waheed din yake gwada musu, in ban dahaka har ya za a yi a ce 'yan mata har uku ya yi masa kwacen su? In ban da daman akwai wata a kasa, tabbas wannan karon yana goyon bayan abokinsa. 90 Alwashin tozarta shi ya ci gaba da yi kai babu sauran alamun mutunci fa a tare da Tahir hannu ya sa ya dafa kafadunsa abokina ina bayanka sai dai fa duk hukuncin da za a-zartar a yi tsinkaye a cikinsa, kada mu zo mu yi aikin da-na-sani. Kishingide take kan kujera hannunta rike da littafi da alama karatu take, ya shigo bayan da ya yi salama, Assalamu alaikum. Amarsu ta ango in shigo ko ko in juya? Na ga aląma yau amarcin ne ya motsa, angon yana gida. Yau da gobe ta ki wasa, har sun saba ta ma saba da halinsa, ta fahimce shi kawarai yana da halin kirki ga barkwanci ya kuma fi abokinshi da'a da mutunci, duk da cewa ta fahimci jirgi daya ne ya kwaso su. Ta mike da sauri me zan kawo maka ne tun kafin a ishe ni? kullum a ka zo sai an cinye mana abinci. Ta kada kai matarka dai kam ta shiga uku da wannan ciki naka mai kama da mazurari, komai aka miko mishi sai ya lashe dariya ya saka, ke zauna ni yau na wutasshe ki, na biya gidan amaryata na ci dadddan girki ba jagwalgalo ba irin naki. Ta yi kwafa haka ka ce to in an yi zuciya a satin nan ta tare mana mu gani, ko a bar kwanoninmu su huta. Baki iya tabe ke da wasa nake, ni fa har yanzu a duk cikin'yan matan garin nan ban ga wacce ta yi min ba. Sai dai ku lalata rayuwarsu? Ta ba shi amsa. Baki ya kara budewa, a'a Barrister kada ai mana sharri, ina mu ina wannan aiki? Sai ku gayawa karamin yaro ina jinshi zai fi yadda da hakan, tun da yana da raunin tunani. Dariya yake to ya isa dai a bar maganar kada a Saro mana wani sabon aikin, domin na lura yau sharri ake shirin yi mana. Sharri ko gaskiya abin da kuke aikatawa ne. Ya sauya maganar, wai ina kawar nan taki? Ni fa da gaske nake na ga kina yi min wani wala-wala, Allah ya tsare ta da faďawa hannunku. Ya shiga magiya Allah da gaske nake, ita 91 ma ta zama serious, kai Allah ba ta nan ta tafi yi yo wani course na shekara daya a kasar faranša, kada kai ya yi, cabdijan ki ce an shiga uku, domin a hakanma ya aka cika domin ba wai course din da ya kai ta kadai za ta yi yo ba har ma da na rashin kunya da fitsara, har yanzu fa ina tunawa da murguda bakin nan da aka yi min ana yi min wani iriin kallo kamar kashi don haka nake tuna ranar da duk na aure ta zan saisaita yarinyar na ga ta bakin tsiwa. Ya ishe ka haka ai damanna gaya maka Allah ya tsare ta da fadawa hannun irin ku. To shi ke nan na ji abar dan kara mana magana ni ma ina nan ina shirin kawo zankadediyar yarinya ba irin kawarki ba mai gajeren hanci, mita ta fara yi mishi ai wallahi karyarka haushin rashin samu ne, samun mace kamar Sameera sai an tona. To na ji dai a bar maganar kada ma a kai gaba tun tonowar kin san muddun aka yi tonowar kawarki za ta yi kwantai ne. Ya dubi littafin hannunta, yauwa ni kin tuna min ma, karasa min labarin 'BILKISU MAI GADON ZINARE'. Dago mishi littafin ta yi ba ka ga yanzu an fara kashi na ukun ba ga shi kuma ka zo ka hayyace ni ballantana in Karasa karanta shi, in zo in karashe maka labarin duk dai da hakan a dan gutsura min na kagauta da sauraron labarin nan. Ka dai takura min bayan ba wani abin kirki na karanto ba face kayan takaici, ta riga ta fada tarkon yayanta yana cin zarafinta son ransa bayan ya raba ta da masoyanta na gaskiya. Ta dube shi kai kusan dukkanku maza haka kuke babu komai a cikinku face keta da mugunta, burunku ku tagayyara rayuwar 'ya mace ku sanya ta cikin kunci da wahala ku kuma yasar da ita. 92 Maganarta ta raunana indanunta ya ciko kamar za ta yi kuka sai kawai ta sunkuyar da kai hawaye na zubo mata, shi ma sunkwi da kan ya yi jikinsa ya yi la'asar, tabbas ana zaluntar yarinyar, abokinshi ya ki ya yi adalci a kan yarinyar, ya gwammacewa kadangarun bariki, gaskiya ne abin da ciwo. Ya fara magana cikin kyakkyawan lafazi kai ba ka ce shi ba ne. Hakuri za ki ci gaba da yi Heedaya, komai kika gani mai wucewa ne babu abin dayake dawwama face sarki Allah Mai girma da buwaya, na san abokina ba ya kyauta miki, to amma fa gaskiyar magana ke ma da naki lafiin, kai kusan ke ce da daukan kaso mafi tsoka, kin kasa ba shi hadin kai, kin kasa ba shi fuska kin kasa yi mishi biyaya, ya karyar da kansa duk da shi ne ke sama da ke, ya nemi sulhu amma duk kika turje kika nuna adawarki da hakan. Saboda Allah me kike so ya yi miki? Duk fa halinda ya shiga kina fa da kamasho a cikinsa me ya sa za ki nemi jefa kanki cikin halak Heedaya? Kar fa ki manta ita aljananr mace a karkashin kafafun mijinta take, manzon Allah (S.A.W) ya bayyana mana da da wani abun halitta da za a bautawa da ya umarci mace ta bauta wa mijinta saboda mutukar kimar dayake da shi a wajenta. Kar fa ki manta ga iyaye da sauran dangi be ambace su ba sai fa miji. Ya sassauta murya, so, a gaskiya laifi naki ne Heedaya, ya zama dole ki yi masa biyaya, ki manta da komai ki share ya wuce kawai ku yi kokarin shimfida kyakyawar rayuwa, wacce 'ya'ya da jikokinku za su yi alfahari da ita. Kanta na sunkuye hawaye na zubo mata, jama'a da damà na ganin laifina ne bayan ko mutumin nan ya sha 93 fada min ba ya sona, ba ya kauna ta, bama zai taba sona ba, so, ya za a yi zamanmu da wannan bawan Allah ya fore? Kada ka mance kiyayya fa wata aba cemai illa. Kuka ta fashemishi don Allah ku bar ganin laifina, mutumin nan fa na gasa min aya a hannu, sam-sam ba shi da halin kirki, mutumin arziki ne zai dauko mace yakwana da ita cikin tsakiyar iyalinsa? me ya fi wannan kuna? A da abin kam ba ya damuna amma yanzu kam ya dame ni, ni da za ka taimaka min da ka neme shi ya sahale min, zamanmu ba zai taba armashi ba, ba zan taba ganin kima da darajarsa ba, saboda wani abu da ni kadai na sani, wannan abu shi ya hana har ma na kasa yimasa biyayya har ma yakan kıra ni da yarinya mara tarbiyya bayan ko shi ne ya aikata rashin tarbiyya mafi muni, ba na son sa, ba na son sa zamanmu ba zai taba đorewa ba domin ba zan taba daina ganin shi da wannan abu ba. A tunaninshi bai wuce abubuwan da suka gudana a baya ba, don haka ya shiga lalhashinta yana ganin abin is easy be- sani ba babba ne, kai dungumeme ne ma. Yawancin jama'a na ganin laifinta musamman a lokacin aurensu, bayan ko ita ta san abin da ya shuka mata. Harara ya sakar masa, ca nake ai sai gobe za ka fito? Bai saurare shi ba don ciki yake da shi, aikin banza ana yi ma magana kana ji, ko ko ka je ta gama zuge ka ne? dan na san kai karamar Kwakwalwa ce da kai. Kila da ba dan harkar karuwa ba ce da ba ka fito ba yanzu? Be dai tanka mishi ba yanufi cikin motar. Sai da ya harare shi sannan ya ja akatar in tar, aikin banza mutum kulum in za a je wajen arziki sai daa ya buge da motar aro, wayo ya hana ya sa kudi ya shrga motar 94 kirki, in ma mutum ba ci ba ai zai mutu wasu su ci ne. Wai yaushe ma za ka yi aure ne?" Banza kawai, ya kasa daurewa sai da ya kwashe da dariya. Sai san damatsoratan maza suka kauce suka bawa maza na hakika da ba sa tsoron matansu. Fuska ya daure me kake nufi ne? cikin gatsali ya ce, a'ah, inanufin matarka barrister Heedaya. Ko ko daurin su na lauyoyi kake tsoro ne, ban dai tantance ba, uban waye ya ce maka ina tsoron ta bare wani aikinta? Lauyan banza da wofi. A'a, ban da fa cin mutunci abin da idona ya gane min ne, kai ka kasa shiga sashen matarka, don kana tsoron hukukcnin da za ta zartar maka. Ya harzuka zan kwa ci zarafinta, haka ta ce maka? Ya yi kwafa za kwa ta gane ni ba sa'an wasanta ba ne, kamar gaske bayan a gidan kamar zabo kake. Ya dada harzuka, komai dai meye na fi ka kai kuwa fa da ruwan ido ya hana ka auren? Ai ka sanni namiji ne mai aji har ma baa iya kyautar da ni sai dai na zaба па darje, kuma ni dole ne mace ta bi sharudfana, ni zan juya ta ba wai ita ta juya ni ba, sai kuma abin da na ce mata shi za ta yi. Ita za ta yi min wanka, ta tarairaye ni ta ma ba ni abinei a baki, ba wai in tsaya ina sanda ba har ma ina shayin shiga wajen ta. Idan kuma mutum ya yi zuciya daga yau ya fara in har yana son shiga rukunin maza na hakika, ba wafanda suka yi yowa mata rakiya ba, rakiyar ma da be fice ta rikon jaka ba. Burki ya ja ji take kиииuuии! Ya fa ishe ka, ka fice ka bar min mote Malarn get out. Ya fada da sauri, ban da raini ma shi za a cewa dan rakiya, rakiyar ma ta mace? Macen ma har irin fitsararriyar yarinyar nan? Ya zaina dole ya sake sabon salo a kanta, don ta san shi fa ba na wasa ba 95 ne. Abin da yake nufin sa shin ba zai yi ba in dai a kan fitsararriyar yarinyar ce, ba rukon jaka ba a ce mishi ma abin da ya fi haka in dai sai ya aiwatar da haka ne za a janye mishi wannan suna. Yau ya riski kansa cikin wani irin yanayi na farin ciki, yarinya me aji da ya mato akanta (Zeenatu) ta ce ba ta ra'ayinshi, sai fa shi tsadaddan yaro, dayar da yake kwakwa yake mata mayataccen so (hidaya) ya riga ya mallake ta har ma tana rabe a inuwarsa, ita ko dayar dungurungum ta nuna ba ta ra'ayinsa shi take so, domin tuni ta riga ta gama yayinsa. Tahir na yi maka kata'i zan kuma ci gaba da kasancewa da taurarin nan naka uku duk dai domin in kuntata maka. Zahirin gaskiya dukkansu ukun babu wata da zai ce yana yi mata wani mayataccen so, shi daman bai iya wannan ba, ba kowane lokaci ne matan ma suka damke shi ba, ita daman dayar babu batunwani so a tsakaninsu, face tarin rikici kala-kala tun daga farkon haduwarsu, ita ko Zeenatun ba zai iya cewa yana yi mata wani mayataceen soba ya yarda dai yana son ta ne dan faranta mishin da take, ita ko dayar da ake tsaka da rikici a kanta ba wani son ku zo mu gani yake mata ba, kai yana ma son ta ne yana kuma kasancewa da ita ne duk dan ya kuntata masa, duk da cewa yarinyar ta mallaki duk wani abu da mace za tayi alfahari da shi daga dai kyawun halitta. Ya daga wayar a lokacin da yake kokarin gano wanda ya kira shi saboda rashin fahimtar nambar (no number). Cikin kakkaurar murya aka fara magana, abokina ka daukowa kanka da kanka ruwan dafa kanka, kada fa kа yi tsammanin kai mai cin galaba ta ne, a'a, bari kaji ba haka 96 bane, tun farko na hakur ana bar maka Zeenatu ba, wai don fin karfina ba a'a sai don na san tuni na gama yayinta, don haka na bar maka sidi ka san a yadda nake din nan na fi karfin a bar min sudi sai dai ko sabo dallele. Karo na biyu na hakura na kuma janye dan na san bani da wata barazana a kanka wanda har hakanya ba ka damar ka aure ta to sai dai fa kada ka mance Heedaya ni kadai take so a fadin duniyar nan, ni kadai ne mutumin da ta yi amananr zai ni'imta mata rayuwarta don haka ne ta mai da kai soko sha ka tafi da bai san ciwon kansa ba, domin zuciya da gangar jiki tuni ta danka su a hannun Tahir, abin da nake so ka fahimta anan Tahir shi ke dealing da zuciya da gangar jikin yarinyar da kake ikirarin matarka ce, don haka ne ma ta kasa ba ka hadin kai ta mai da kai wani sha-ka-tafi, ka duba gaban durowar teburin office din ka za ka ga sakon da zai tabbatar maka da hakan, in kuma har kana musanta haka to ka je ka tuhume ta cikin da ke jikinta mallakin wanene? Na tabbata za ta ba ka gamshasshiyar amsa don ba ta kaunarka ba ta kuma shakkun ka. Tahir ne abin kaunarta don haka za ta bayyana maka tsiron da ke cikin mahaifarta mallakin Tahir dinta ne. Kashedi na gaba da kuma karshe zan maka, ka fita harkar yarinyar nan (Farida) dan ba ajinka ba ce ko kadan baka dace da ita ba, kai ka tsaya dai a second hand finka, shi ya fi maka alheri, ka sani ka kuma sani ina son Farida ina son ta, yes dole ne kuma in mallake ta ko da tsiya ko da arziki ne. kashedi na karshe a gare ka ka fita harkar yarinyar nan idan ka ki bin umarnina ka samawa kanka lafiya idan ko ka sa kafa ka shure ka kwasowa. kankа masifa har da bala'i. Da fadar haka ya katse layin. Tsayawa 97 ya yi wani sororo kamar wani gaula duk cikin kalaman nashi babu wanda ya fi tayar mishi da hankali ya ma tafashe zuciyarshi baki daya irin maganganunshi na tsakiya wato a kan matarsa. Biye mishin kuwa ya yi kamar mahaukaci ya shiga bincika dirowar da ke jikin teburinshi, gaba daya ya hargitsa takardun dake ciki hankalinsa ya kai kan wata Katuwar, envelope, hannu ya sa ya dauko ta, cikin matsanancin sauri ya bude hannunsa har kakkarwa yake. Hotunan kam babu ko kyawun gani, wani a kwance wani a zaune, wani kuma a kishingide, a wani hoton kuma ga cikin nan har ya tura. Jifa ya yi da su ya bi ta kai ya taka, ya tattaka, kai sai ya dauko ashana ma ya kyatta musu zan kone ku kamar yadda zan kone ma mallakan cikin hotunan, na tsane ku, na tsane ku, yau za ku tabbatar da tsanar da nake muku don zan raba ku da duniyar, maciya amana, masu keta haddin Ubangiji. Zaune take ta hada kai da gwiwa, Tahir din ya riga ya gaına fanfata, ji take zuciyarta na yi mata wani irin tafarfasa, wane irin cin zarafi ne wannan? wane irin ki ne mutumin nan ne yake mata? Har zai je yana ta gayyara ta a gari yana 6ata sunanta. Ciki! Ciki!! Uban waye ya yi mata cikin? Har yana ikirarin ba nasa ba ne? tun da take in ban da shi din da ya keta haddinta ba ta taba kadaitaka da wani namijin ba, duk lalacewar tata ba ta kai nan ba, haka nan duk rashin tarbiyyar da yake ikirarin ba ta da shi ba ta ko kai nan ba. bayan cin zarafin da ya yi mata ya keta alfarmat a shi ne har zai je yana yi mata wannan dungumemen 98 sharrin? bayan ko shi ne lalataccen a kan idanunta ına lalacewar yake. Hotunan da shi Tahir din ya ba ta ba su wani ba ta mamaki ba, tun da akan idon tama yana aikata hakan. To sai dai fa hotunan sun mata ciwo, galibanshi da wata kyakkyawar mace ce kai don kyau kamar aljana take, ba wai hotunan ne ma suka fi bakanta mata ba face yanayin shigar dake jikinsu da kuma sigar da aka yi hoton karshen lalacewa kam sun yi ta a nan. Bayan wannan din ma akwai wasu hotunan da wata yarinyar dai duk da dai ba su kai wadancan muni ba to amma şu ma ba su da wani kyawun gani, fitsara cе tsagwaron ta aka yi ta ita din ma yarinyar kyakkyawa cc sai dai ba ta kai fayar ba. Zeenatu haka ya ce mata sunanta ita kuma dayar Farida ko menene, to ta dai fi jin zafijn Faridan, tana jin wani irin kishinta a zuciyarta, mutumin nan ya cuce ta ya cuce ta. Ya magana da rayuwarta. Tana cikin wannan dumamar ne, wacce ta kira kanta da Faridan ta neme ta a layi, babu batun sallama, ta ce, cin zarafi, kai hakika ta ci zarafinta ta kuma goronta mata rashin kaunar da maigidan yake mata har ma ta kira ta da kaska mai bakin naci in ta raße kai da kacire ta sai an sha bakar wahala Cacar baki suka tsaya yi har ta gaji ta kifa layin, zuciya kam ta gama kawo mata wuya, takaicinta daya wanda a ka ci zarafin nata a domin sa bayan ko ba su san cewa ta ma iowa Riyayyarsa a duniya ba. Zamanta kam ya zo karshe ya ma kare a gidan nan dole ne ma ya sahale mata ta je ta auri abin kaunarta. Ya shigo cikin fusata kai tsaye sashienta ya wuce, bugu ya kawomata da kafa sai da ta hantsila sannan ta kifa 99 bai saurara mata ba ya kara kawomata bugun da dai kafar idanunsa ya kada ya yi jawur sai tsuna yake, uban waye ya yi miki ciki? Uban waye na ce? 'yar iska matsiya ciya mara tarbiyya, uban waye na ce ya yi miki ciki ya kara nanata tambayar. Duk da tana cikin dimuwa hakan be sa ta kasa jin wani karfi a zuciyarta ba, cikin daga murya ta ce uban waye kake ganin ya isa ya yi min ciki a duk fadın garin nan da ya wuce abin Kaunata Tahir. Mari ya sakar mata ya kuma kawo mata marin kai ya haukace ma dukanta yake ta ko ina har da kansa ya gaji ya dakata, ja ya yi ya tsaya ya nuno ta da yatsa cikin masifa da bala'i, zan je in fara kawar da masoyin naki daga doron kasa da duk ma wani mai hannu a cikin lamarin nan, daga bisani sai na juyo na aiko mishi da ke can lahira dan babu shegiyar da ta isa haife min cikin shege a cikin gidana, never..., never... na tsane ki, na tsane ki... ya fice cikin fusata. Durkushewa ta yi tana kuka babu wanda ya ja mata wannan face iyayanta, ita ta riga ta san mutumin maketaci ne mara halin kirki, yana kinta yana mutukar kiyayyarta don haka zai iya yi mata kowane irin sharri, duk domin ya batą mata suna. Tabbas Tahir ya yi gaskiya, mutumin nan fa sam ba ya kaunar ta, in ban da rashin kauna har yaushe zai aiwatarmata da wannan aiki ya kuma zo ya bi ta da wani dungumemen sharrin bayan 6ata mata sunan daya yi? Tun daya san sharri ya aiwatar mata meye kuma zai zo yana tuhuamr ta? Shi da ya riga ya kagi abinda kansa ai ko ko za a sata a turmi a kirba zainansu ya kare da mutunin nan. Tahir dinta take so dole kuma a bata, kai sai yanzu ne ma take jin haushin kanta, me ya sa tun farko ta ki amincewa bukatar Tahir din, na su gudu, ta ba wa kanta amsa duk dai Aunty Na'ima ce ta ja mata saboda ta riga ta hango irin musibar da za ta afka muddun ta auri maketacin mutumin. 100 Burinta ke nan su tagayyara kamar yadda momin ta sha gaya musu, wani lokacin tana ganin bekenta ashc ko da gaskiyarta. To sai dai ta dau alwashin wutar rikicin ba fa wai kanta kadai za ta tsaya ba, a'a har da ita wacce ta shiryo mata wannan gadazzaren sai ta gwammace wa zaman cikin garwashi da dai zaman gidan mahaifinsu. Kai tsaye mahadarsu ya nufa, kai duk inda yake tunanin zai ga Tahir din ya je amma kuma be gan shi ba, zuciyar nan tashi kamar wuta dan Kuna. Farida ce ta kira shi a waya ya zo da gaggawa tara son ganinsa, be yi niyyar zuwa ba amma dai sai ya tafi don su shirya wace za ta fisshe su, zai aure ta kamar yadda wannan shi ne ra'ayinta ba don komai ba sai don ya Kuntatawa abokin hamayyarsa, tun da ya hakikancewa zuciyarsa yana kaunarta kamar yadda yabayyana mishi. Kai da da hali ma har ita Zeenatun zai hada ya aura duk dai a lokaci guda, to amma kuma sai ya gano rashin alfanun hakan, tun da ya riga ya san ra'ayinsa a kanta (wato ya gama yayinta). Ita ko dayar zai sahale mata ne bayan ya tagayyara ta kamar yadda tayi mishi wannan tozarci, daga nan sai ya ga ta karshen so ta je ta gani idan shi Tahir din zai yadda ya aure ta, kai wannan yarinya kam ta riga ta gama da rayuwarshi, zai kuma yi mata tozarci irin wanda ta yi masa. Ciki! Matarsa da cikin wani, wanin ma makiyinsa. Hotel din da take da zama ya nufa wanda shi ya kama mata daki a ciki. Ta nuna matukar mamakin ganinsa, ban yi tsammanin zuwanka ba yanzu don haka ne ma nake haramar kwanciya. Duk da ranshi a Gace yake amma ta sami nasarar ssasutar da zuciyarshi daga kaso hamsin 101 cikindari, saboda tsabagen farin cikin da ya tuna nan da sa'o'i kalilan ta zama mallakinsa wanda hakan ke nufin ya gama karshen kuntatawa abokin hamayyarshi. Shi kam ba wai tsabar kyanta ne yake rudarsa ba face wannan dalili. Duban shi ta yi, Da gasken fa nake ban sa rai da kai ba a dai wannan lokacin. Harara ya sakar mata cikin wani salo, amma kika ishe ni da waya. Zaro idanu ta yi? Ni? ke mana. Wayc yake da zazzakar

Chapter 7 of 8